Share this page
tangaran nan shaƙe da zoɓo, jikin jug ɗin sai raɓa yake fitarwa alamun sanyi ƙarara. "Ku fara ci Aunty, tunda na yi alwalar bari in fara yin sallar, idan na idar sai in ci abincin in huta gaba ɗaya." "To shi kenan! Yi sallar, ni kam dai sai na ci abinci zan sauke farali." Hijabi da sallayar da Hibba take miƙa mata ta karɓa, ta tambayi gabas aka nuna mata, ta shimfiɗa ta tayar da sallah. Ko da ta idar da sallah tayi ƴan addu'o'inta, bata ɓata lokaci ba ta cire hijabin ta ninke, sannan ta ƙarasa kusa da abincin ta ɗiba a ɗaya daga cikin farantai uku da aka ajiye musu. Duk yadda Hibba take ta mata nacin ta tashi ta zauna a gefen gado kamar yadda suke zaune ƙiyawa tayi, nan ƙasa ta zauna ta fara cin abincin, lokaci bayan lokaci take amsa musu hirar da ƙarfi da yaji suke ta tsoma ta a ciki. "Fuskarki za tayi kyau da sassauƙar kwalliya Zulaikha, gama cin abincin in gwada kwalliya a fuskarki mu gani ko za ta zauna miki yadda nake hasashe. Kin san ni fa sana'ata kenan, kwalliya, ɗaurin ɗankwali, lalle, da duk wata harka ta gyaran jiki ba wanda ba na taɓawa. Mamana da kika ganta a waje ƴar maiduguri ce, kin san kuwa mu ne sirrin ƙamshi da gyaran jiki. Da wannan dalilin yasa wasu daga cikin ƙawayena ke ce min Uwar gayu." Ta ƙarasa maganar tana kaɗa idanu tana wani yarfe hannaye don tsabar yanga da firirita. Zulaikha dai sai kallonta take yi, kamar tayi dariyar irin yadda take ta fari da idanu tana wani watsa hannaye kamar za ta tada aljanu, amma sai ta matse dariyar bata yi ba. Ko da ta gama cin abincin, bata ƙi tayin kwalliya da Hibbah tayi mata ba. Haka take ta bin komai da kallon mamaki ganin wani ƙaton akwati da Hibba ta ɗauko wai duk kayan kwalliya ne a ciki. Kamar da wasa, ta zauna a kujerar gaban madubi Hibba ta fara yi mata kwalliya kala daban-daban a fuskarta. Kuma da yake Hibbar ta san aikinta, kwalliya kala huɗu da aka gwada ma Zulaikha ba ƙaramin hawa da kyakkyawar fuskarta suka yi ba. Su kaɗai a ɗaki sai tuntsura dariya suke yi suna shewa kamar ƴan matan Amarya. Duk kalar kwalliyar da aka yi sai an yi mata ɗaurin ɗankwalin da zai hau da ita, Karima kuwa sai aukin ɗaukarta hotuna take yi tana ɗora ta a status ɗin whatsapp. "My luvly Ƙanwa Zuly. Allura cikin ruwa... mai tsananin rabo ka ɗauka." Ire-iren kirarin da tayi ta bin hotunan da shi kenan. "Gaskiya ni dai wannan kwalliya da ɗaurin ɗankwali sun burgeni matuƙa Wallahi. Ashe lokacin auren ɗiyan mai garinmu da aka ɗauko mai mata kwalliya tun daga Kasuwan magani zuwa ƙauyenmu ta cancaɗa mata mukai ta yabo muna zuzutawa ashe ɓata mata fuska kawai ta yi?" Zulaikha tayi maganar fuskarta cike da farin ciki, tana sake ƙure kanta da kallo a gaban madubi ganin yadda ta canja gaba ɗaya. Kamar ba Zulai ƴar Innaye da Baffah ba, ta yi wani irin kyau na musamman da bata ma san zai iya kwatanta shi ba. Kamar wacce ta tuna da wani abu, da sauri ta matsa kusa da Hibba ta riƙe hannayenta, fuskarta a marairaice ta ce "Aunty Hibbah, don girman Allah ki koya min kwalliya da ɗaurin ɗankwalin. Ba kuma wai don in dinga sana'ar da kike yi in kashe miki kasuwa ba, don fuskata kaɗai, na rantse da Allah fuskata kawai zan dinga yiwa kwalliya ina ma matan ƙauyenmu burga. Daman kullum idan suka tashi gwaɓa min magana suna cewa don na ga ina da Yaya a Habuja shi yasa nake musu ɗagawa, haka ma Mudan ya ce min kafin ya ce bazai aure ni ba, kuma fa Wallahi ba haka bane." Ta ƙarasa maganar idanunta ciccike da ƴan ƙananun ƙwallah. "Kar ki damu Zuly, ai tunda Karima ta kawo ki gurina babu abinda bazan iya miki ba." Ta mayar da idanunta kan Karima ta ce "Besty kiyi adding ɗin ta a group ɗin da nake koyar da kwalliya da ɗaurin ɗankwali na whatsapp..." Da murna sosai a fuskar Karima ta katse Hibbah tun kafin ta aje numfashin maganarta. "Lallai ke kam Zulaikha kina da sa'a. Besty Allah ya saka da alkhairi, kin gama mana komai. Na san ko iya haka aka tsaya cikin ƙanƙanin lokaci Zuly za ta faso gari, ta zama babbar yarinya." A tare duk su ukun suka sake kwashewa da dariya. A haka suka ƙara cinye fiye da awoyi uku a gidan, har sai da Mummy ta kira Karima a waya tana faɗan daɗewar da suka yi, ga shi a lokacin Hibbah ta kwaɓa lallen zamani ta fara yi ma Zulaikha a bayan hannunta da saman ƙafafunta. Tunda dai tafin ƙafa da tafin hannu akwai lallen aure da Aunty Rakiya tayi mata a gida. Haƙuri Karima tayi ta ba Mummy tana ba ta uzurin lalle ake yi ma Zulaikha har dai aka zirara mata lallen ba mai yawa sosai ba, haka suka fice daga gidan da ɗanyen lalle ko bushewa baiyi ba. Mama sai dariya take musu, bayan ta ba su ƴan ƙananun ledoji ɗauke da turarukan jiki na shafawa irin nasu na ƴan mata. [2/1, 5:15 PM] Fareeda Abdallah: ****** A marairaice ta kalli fuskar Karima da take miƙa mata wayarta, bayan ta gama hidimar buɗe mata Facebook, whatsapp, Instagram. Kuma tayi adding ɗin ta a group ɗin Hibbah, da duk wasu groups da take ciki, waɗanda ta san lallai ana gabatar da abubuwa na ƙaruwar ilimi a ciki. "Ni dai Aunty Allah yasa ba wahalar banza kika yi min ba. Allah dai yasa in iya amfani da waɗannan kafafen sada zumuntar. Musamman ajujuwan da kika saka ni da wanda kika sa shugabannin group ɗin suka saka ni. Ni kin san babbar matsalata shi ne ba na jin turanci, sannan rubutu in dai da turanci ne gaskiya ba lallai ne in iya karanta kalmomin a yadda suke ba, ko na karanta ma gaskiya kashi casa'in da tara cikin ɗari na kalmomin ban san me suke nufi ba..." "Yauwa! Dakata Zuly." Karima tayi saurin katse ta, doguwar hamma tayi, saboda ta kwana a asibiti ba wani wadataccen barci. Tana dawowa da safe kuma maimakon ta kwanta kamar yadda ta saba ita da kanta ta ce Zulaikha ta kawo wayarta ta buɗe mata whatsapp da sauran kafafen sada zumunta. Gyara zama tayi kafin ta cigaba da cewa "Daman tun jiya nake ta so in tambaye ki. Acan ƙauyenku baki yi makarantar boko bane?" "Na yi makaranta mana." Zulaikha ta amsa da sauri. Kafin Karima ta ce wani abu ta cigaba da cewa "Kin ganni nan Wallahi har aji shida na sakandire na gama, kuɗi tsugugu Baffa ya biya min na zana jarabawar WAEC dA NECO a Kasuwar magani, amma gaskiya ban ci ba. A hausa da Islamic ne kawai na samu Credit, sai lissafi na samu Pass. To kin san dai yanayin karatun namu na ƙauye, babu wasu tsayayyun malamai, sannan shi kanshi zuwa makarantar da ɗaukar karatun da muhimmanci duk asha ruwan tsuntsaye muke masa. Don a ƙauyenmu yara mata sa'annina waɗanda muka fara makarantar boko da su ni kaɗai ce ma na jajirce har na gama aji shidda ban tsaya kula samari ba balle ayi min aure. Mu a ƙauyenmu ko a maza ɗaiɗaiku ne suke ɗaukar karatun boko da muhimmanci. Na dai iya karatun hausa da rubuta shi lafiya ƙalau. Amma na turanci kam gaskiya sifili ne, gara in faɗa miki tun wuri kar in dinga kunyataki a cikin ƙawaye da abokan arzikinki." "Don wannan matsalar, kar ki wani damu kanki. Ba ke kaɗai ke fama da matsalar rashin jin turanci ba, har anan cikin birane akwai mutane da yawa sun yi karatu amma ba sa jin turanci. Kin san in banda yanzu da ake ta ƙara gane muhimmanci iya yare mabanbanta, da yawa daga cikin mutanenmu basu fahimci muhimmancin iya magana da turanci da kuma gogewa a karanta turancin ba. Duba da yadda kusan komai an cigaba, Hausa ta game kusan ko ina a Nigeria, kusan babu inda za ki je ki rasa wanda zai miki tafinta da Hausa. A yanzu da aka fahimci rashin iya turancin na janyo matsaloli a wasu ɓangarorin na rayuwa sai mutane suka zaburo suna so su koya, amma kuma da yawa ana jin kunyar komawa makaranta, wasu kuma ba su da lokacin da za su koma makaranta don kawai su koyi turanci. Duba da waɗannan dalilan, yasa da yawan makarantu da kuma wasu manyan malaman turanci suka buɗe fagen koyar da turanci ta kafafen sada zumunta ka'in da Na'in. Akwai pajika da groups da suke yi a kyauta, akwai kuma waɗanda sai an biya kuɗi. Yanzu dai duk ba ma wannan ba, Almuhim shi ne, shin ke da gaske kin shirya dagewa da nacewa wajen koyon magana da karatun turancin ko baki shirya ba...?" "Na shirya! Wallahi Aunty na shirya!! Na rantse da Allah na shirya Aunty." Ta amsa da sauri, bakinta har yana mazari. Da saurin gaske ta ƙara matsawa kusa da Karima kamar za ta hau jikinta. "Aunty? Kin kuwa san yadda rashin iya turancinnan yake ja min tozarci, wulaƙanci, cin mutunci daga gurin Aunty Bintu kuwa?" Tayi ƙwal-ƙwal, idanunta suka cicciko da hawaye. Tsabar damuwa yasa bata san sadda ta buɗe baki ta dinga ba Karima labarin ire-iren cin mutunci da tozarcin da Bintu take musu ba. Domin ita Zulaikha a yadda ta ɗauka shi ne, kawai Bintu tana yi musu haka ne saboda ta gansu ƴan ƙauye, kuma jahilai, waɗanda basu yi ilimin boko ba. "Dakata Zuly. Tun shekaran jiya da na ji kin kira sunan Innaye sunan yake ta min yawo a ƙwaƙwalwa, kamar na taɓa jin sunan, amma sam na manta a ina ne, shi yasa na share zancen a raina. Sai yanzu da kika ɗan bani wannan labarin na tuna inda na taɓa jin sunan, kina nufin Innaye mahaifiyarki ce?" Karima ta tambayeta da mamaki fal fuskarta, a zuciyarta take tuna wancan lokacin da ta taɓa taimaka ma Innaye a asibitinsu, tana kuma sake tuna yadda Dr. Bintu ta wulaƙanta Innaye kamar ba uwar mijinta ba. "Eh! Mahaifiyata ce." Zulaikha ta amsa mata da sanyin murya. "Kin santa ne?" Ta sake jefa ma Karima tambayar. "Ƙwarai kuwa na santa." A taƙaice ta ba Zulaikha labarin haɗuwarta da Innaye a asibitinsu a wancan lokacin. "Allah sarki Innaye. Mutuniyar kirki, ya jikinta kuwa? Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sabo ya shiga tsakanina da ita daga haɗuwa a asibiti kawai, na daɗe ban manta da al'amarinta a zuciyata ba." "Ta ji sauƙi sosai." Zulaikha ta amsa da ɗan murmushi a fuskarta, don jin daɗin an yabi Innayenta. "Ai tun daga wancan lokacin, ni da ita bamu sake zuwa Habuja..." "Abuja ne fa asalin sunan. Haba ƴan mata, ki fara nuna kin waye mana? Kamar baki karanta State and Capitals ba?." Dariya suka yi duk su biyun, sannan Zulaikha ta cigaba da cewa "Bamu sake zuwa Abuja ba tun wancan lokacin, sai yanzu da na dawo. Kuma kin san Innaye ma ta bani labarinki tun wancan lokacin? Ta ce min taimakon da kika yi mata shi ya hana ta wahala da yunwa, tunda sun fita bata karya ba." "Allah sarki... Allah ya ƙara mata lafiya da nisan kwana." "Amin ya Allah." Nan suka cigaba da hira sama-sama, Karima tana danna wayarta. Ta ɗauki fiye da mintuna sha biyar tana danne-danne kafin ta ɗago fuskar wayar ta nuna ma Zulaikha. "Kin gani, an gama komai. Na yi miki register, na biya miki 15k na register. Za ki koyi magana da turanci, karatun turanci, da sanin fassarar kalmomin turancin a cikin watanni uku kacal in Allah ya yarda. Amma fa idan kin dage, kin nace, kin mayar da hankali sosai. Ki duba Whatsapp ɗin ki, za ki ga sunyi adding ɗin ki yanzu, don na basu lambarki." Tsananin farin ciki yasa bata san sa'adda ta rungume Karima tana zabga mata godiya. "Na gode, na gode Aunty Karima. Kin gama min komai, bazan taɓa mantawa da alkhairanki a gare ni ba. Allah ya saka miki da alkhairi ninkin ba ninkin abinda kika yi min." "Ameen ya rabb" Karima ta amsa bayan ta sake jan wata doguwar hamma. Zamewa tayi daga zaune ta kwanta. "Kin ga tun ɗazu ina ta hamma, idan ba runtsawa nayi ba bazan samu nutsuwa ba. Kin san barci, ba'a cin bashinsa. Yanzu dai tunda na saka miki data, kuma na gama saita miki komai, ki karɓi wayarki ki duba kina bin komai sannu a hankali. Duk abinda baki gane ba, idan na tashi barci sai inyi miki ƙarin bayani." "To Aunty. A huta gajiya. Na gode. Bari in tafi ɗakin Hajja muna hira ina daddana wayar..." "A'a ki ce ba danna waya za kiyi ba. Hajja ce za ta barki ki danna wata waya ita tana zaune? Je ki dai ta cika miki kunne da mita da karaɗi, can anjima kya danna wayar." Bata ce komai ba, illah dariya da tayi ta ɗauki wayarta da cajar da Karima ta bata kyauta ta fice daga ɗakin. Kamar yadda ta ce, ɗakin Hajja ta nufa kai tsaye. Don Allah ya sani ba ƙaramin kewar Innaye tsohuwar ke ɗebe mata ba, barkwanci da mitar tsohuwar ita bata taɓa ɗaukarshi abin damuwa ba, ko don bata daɗe bane a gidan? Oho!!! ***** ***** Ya juyar da fuskarsa ɓangaren gabas, ta bishi. Ya sake juyar da fuskarsa ɓangaren yamma, ta sake bin shi idanunta ciccike da hawaye. Yana yunƙurin sake juyar da fuskarsa ɓangaren kudu tayi saurin sa hannayenta biyu ta riƙe fuskarsa tana ɗan girgiza mishi kai. Suka kalli juna cikin ido na tsawon wasu daƙiƙu. Tasa fuskar a ɗaure tamau, idanunsa babu wani shauƙi ko kewa. Ita kuma tata fuskar a marairaice, idanuwanta ciccike da hawaye, da wani irin sassanyar yanayi mai bayyana So, Ƙauna, Kewa, damuwa da nadama ƙarara. Hawayen da take ta riƙewa tun ɗazu a hankali ta sake su, suka zubo kan kumatunta shar!!! Ya yunƙura zai karɓe fuskarsa daga hannunta da gaggawa tayi saurin matsawa da tata fuskar izuwa tasa, kafin ya ankara ta haɗe bakinsu guri guda. A lokaci guda kuma tana cigaba da aika mishi saƙon tuba da neman yafiya da idanunta. Da fari, datse laɓɓansa yayi ƙam! Ya ƙi bata wani dama da harshenta zai samu isa cikin bakinsa balle ta tsotsa, amma da yake ta san lagonsa, da duk wani salo da take amfani da shi wajen samun kansa ba'a daɗe ba ya saki bakinsa ta fara juya shi yadda take so. Tun yana turjewa yana basarwa har dai ya bada kai bori ya hau, domin babu ƙarya shi kanshi ba ƙaramin kewarta yayi ba a cikin kwanaki biyun. 'Kawai dai ya janye jikinsa daga nata ne don ya nuna mata kuskurenta. Ya sani asalin laifin nashi ne, amma a tsammaninsa akwai fahimtar juna da soyayyar da ko da wasa baza ta taɓa yunƙurin aikata mishi irin abubuwan da ta aikata ba. Wuƙa ta ɗauka za ta caka mishi fa? Wai shi ne Bintu take rantsewa da girman Allah idan ya kuskura ya ƙarasa kusa da ita za ta caka mishi wuƙa, sannan ta jefe shi da iyayensa da baƙaƙe kuma munanan kalaman da ko tana cikin hauka tuburan ne bai taɓa tsammanin za ta iya kallon cikin idanunsa ta furta mishi su ba...' "Kayi haƙuri My dear... Don girman Allah SWT da Darajar Fiyayyen halitta SAW ka yafe min." Ta faɗa cikin kuka bayan ta raba bakinta da nashi, kamar ta san tunanin da yake yi. Da saurin gaske ta zame zuwa ƙasa ta riƙe ƙafafunshi tana cigaba da rusa kuka wurjanjan, kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar iyayenta duk biyu a lokaci ɗaya. Cikin kukan ta cigaba da magana "Na sani ko kusa banyi amfani da hankali da tunani ba gurin aikata irin abubuwan da nayi... Na sani banyi maka uzuri ba, kamar yadda na sha alƙarwarta maka a baya cewa duk juyin juya hali na rayuwa bazan taɓa fahimtarka a bai-bai ba... Na sani ban saurareka ba balle har in baka dama kayi min bayanin gaskiyar abinda yake faruwa... Amma ya kamata ka fahimce ni My dear, ko ɗan yaya ne kayi min uzuri, duk da ni na kasa yi maka uzuri sa'adda idanuna suka rufe ruf da tsananin kishi da matsanancin soyayyarka. Wallahi ban taɓa sanin haka kishi yake da azababben zafi da raɗaɗi ba sai a wannan ranar... Komai na duniyar baƙi-ƙirin yayi min Sweetheart! A wancan lokacin, Wallahi Tallahi ban ƙi duniyar ta kife ayi mutuwar kasko ba duk a wuce gurin." Taja shessheƙar numfashi cikin kuka, kafin ta cigaba da cewa "Babu ma amfanin maimaita abinda ya wuce. Kuskure ne nasan na riga na aikata, bazan gaji da baka haƙuri ba har sai ka furta ka yafe min da bakinka. Wannan shiru-shirun naka neman hallakani yake yi, gara ka ɗauki duk matakin da za ka ɗauka a kaina a wuce gurin. Idan yi min duka zai sa ka huce, ka daina fushi da ni..." Da sauri ta miƙe ta isa gurin cajojinsu ta ɗauko cajar kwamfuta da ta kasance mai kauri, ta dawo tasa gwuiyawunta a ƙasa sannan ta miƙa masa. "Ka zane ni My dear... Don Allah kayi min mugun duka har zuwa sadda za ka ji a ranka ka huce kuma ka yafe min." Duk da bai karɓi bulalar ba sunkuyar da kanta ƙasa tayi, hannayenta ɗage a sama tana miƙa mishi cajar, a lokaci guda kuma ta cigaba da rera mishi kuka sannu a hankali. Jikinsa a sanyaye, yasa hannu ya karɓi cajar. Duk da haka bata ɗaga idanu ta kalle shi ba, sai runtse idanu tayi tana jira ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta. A hankali, da wani irin salo na slow motion ya zame gwuiyawunsa zuwa ƙasa bayan yayi hurgi da cajar gefe ɗaya. Rungumeta yayi tsam-tsam a ƙirjinsa. A tare ita da shi suka saki nannauyar ajiyar zuciya. A kunnenta ya raɗa mata da wata irin tattausar murya "Na yafe miki Bintuna. Allah ya yafe mana gaba ɗaya. Ni ma ina roƙonki ki yafe min, tun farko..." Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe mishi baki. A shagwaɓe ta ce "Abinda ya wuce mu barshi a wanda ya wuce Abban Aadil. Mu fuskanci gaba kawai da sabuwar rayuwa mai cike da soyayya da ƙauna." A lokaci ɗaya suka sake ruƙunƙume juna suna ƙyalƙyala dariya, nan da nan kuma dariyar ta sauya salo, daman kwana biyu sunyi kewar juna. Don haka duk ƙoƙari suke kowa ya nuna ma ɗan'uwansa lallai fa ya fi ɗayan wahaltuwa a wannan yajin da suka ma juna na kwana biyu. Tun daga wannan rana, suka dawo da gudanar da kyakkyawar rayuwarsu har ma fiye da da. Suka cigaba da rainon ɗansu Aadil da yake ta kakkaɓa girma tubarakallah cikin ƙauna da soyayya. Basu ƙara tayar da zancen wata Zulaikha ba, balle kuma igiyoyin auren da aka ƙaƙaba ma Hafizu waɗanda yake ɗaukarsu a matsayin wasan yara. Kuma yana waya da Iyaye da ƴan'uwansa. Duk bayan sati biyu yana zuwa ƙauye kamar yadda ya saba, amma ko da wasa bai taɓa ba da wata kafa da zai sa ayi zargin lallai shi da Zulaikha ba sa rayuwa a muhalli ɗaya ba. Domin kamar yadda yake waya da iyayensu da ƴan'uwansu, itama tana waya da su, duk da bai je da ita ƙauyen ba, ko da wasa bata taɓa alamta musu lallai fa akwai gagarumar matsala tsakaninta da Yayan nata ba. "Hafizu ya Zulai take? Don Allah don Annabi kar ka ɓoye min komai. Ka ga dai ni ƴar'uwarka ce, shaƙiƙiyarka wacce za ku kashe ku rufe tare ba tare da wani ya ji abinda muke ciki ba. Na rasa dalilin da yasa duk irin amsar da kake bamu na tana nan lafiya ƙalau, da irin amsar da itama take bamu na kuna zaune lafiya ƙalau ni dai hankalina ya gaza kwanciya. Kuma nayi-nayi da Baffa ya barni ko ni ɗaya in je Habuja in gano halin da kuke ciki ya ƙi, a taƙaice ma doka ya kafa mana gaba ɗayanmu kar wacce ta kuskura ta ce za ta kai ma Zulai ziyara sai ta haihu, idan kuma Allah bai kawo haihuwar da wuri ba sai ta shekara cif kafin muje mu gano halin da take ciki." A lokacin da Aunty Balira take mishi wannan maganar ruwa yake sha, amma tsabar yadda maganganun suka doke shi musamman maganar haihuwar Zulai bai san sa'adda ya shaƙe da ruwan da yake sha ba. Nan take ya fara tari ba ƙaƙƙautawa. "Sannu! Sannu Allah ya sauwake. Ka sha a hankali, ya bi ta ƙaramin maƙogwaro. Sannu Hafizu." Aunty Balira ta faɗa da damuwa a fuskarta, tana zaune kusa da shi tana mishi fifita. "Haihuwa kuma Aunty Balira? Saboda Allah wani irin haihuwa kuma ana zaune ƙalau? Daga yin aure kuma a shekara ɗaya sai haihuwa?" Ya jera mata tambayoyin da dariyar yaƙe a fuskarsa bayan ya samu tarin ya lafa mishi daƙyar. "Ji wani sakarci daga gurin Hafizu. Yo idan rabo na kusa me zai hana Zulai samun ciki ta haihu a cikin watanni tara zuwa goma ?" Sai kuma ta ƙanƙance idanu ta ƙara ƙure shi da kallo, ta sake jefa mishi tambayar "Ko dai akwai wata matsala da kake ɓoye mana tsakaninku ne...?" "Wani irin matsala kuma? Ke dai Wallahi duk kin damu kanki. Babu komai, ina sake maimaita miki babu komai. Lafiya ƙalau muke zaune. Idan ma akwai matsala ko ni ban faɗa ba a yadda Zulai take komai na ta a barbaje ai kin san za ta faɗa muku. Ki kwantar da hankalinki pls! Ki cigaba da taya mu addu'a. Ko yanzu abinda yasa ban zo da ita kun ganta ido da ido ba don kar Baffa yayi faɗa ne, amma lafiya ƙalau muke zaune." "Madallah! To Allah ya ƙara zaunar da ku lafiya ya kawo rabo mai albarka." Tayi addu'ar bayan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Da waɗannan maganganun da ya shirya mata ya samu ya kashe bakinta. Suka rabu lafiya tana saka mishi albarka. Baiwar Allah Innaye kuwa hankalinta a kwance yake luf kamar tsumma a randa. Daman dai babbar damuwa da tashin hankalinta akan auren Zulai ce, to tunda wacce za tayi yaƙin dominta ta bada kai bori ya hau ita mene nata da za ta ja ta ƙume kan cewa sai an raba auren? Sai kawai itama ta kwantar da hankalinta ta cigaba da bin su da fatan alkhairi. Duk ɗaure fuskar da take ma Hafizu yanzu ta daina. Abu ɗaya da ba ta gajiya da shi shi ne a waya suke magana ko kuma ziyara ya kai musu ba ta gajiya da jaddada mishi lallai ya ji tsoron Allah ya riƙe Zulai amana, idan ya kuskura ya ci amanarta tabbas amana za ta ci shi. "To Innaye! Zan kiyaye in Allah ya yarda. A cigaba da taya mu addu'a." Amsar da yake ba ta kenan ako wane lokaci ba don maganganun na ta na shiga kunnensa su zauna a ƙwaƙwalwarsa ba. [2/1, 11:21 PM] Fareeda Abdallah: Duk zuwa ƙauye idan yayi, Innaye ba ta gajiya da harhaɗa mishi tsaraba irinna mutanen ƙauye, musamman waɗanda ta tabbatar Zulaikha tana masifar so. Kuka, kuɓewa, daddawa, garin citta da sauran kayan ƙamshi, garin ƙuli, busasshiyar rama, shuwaka, zogale, magarya, aduwa, goruba, kurna, haka za ta harhaɗa mishi leda-leda gaba ɗaya ta ce ya kai ma Zulai. Sannan ta kawo wasu kayayyakin masu yawa ta ce ya kai ma Matan Abba Lurwanu. Don fita hakki duk sadda ta bashi waɗannan saƙonnin sai tace mishi "Ko za ka kira Fatima ka tambayi idan akwai abinda take so anan sai in baka ka tafi mata da shi? Na san su mutanen birni ba kasafai suka cika cimakar ƴan ƙauye ba. Ita kuwa Zulai rainon ƙauye ce, ta saba da waɗannan ciye-ciyen." "Ai ba ma

Chapter 20 of 40