tuwon na tabbata ko an zubo miki a mugun ƙyanƙyamin da muka sanki da shi baza ki iya ci ba, kila ma ya saka ki amai..."
"Zan iya ci."
Bintu ta katse ta da faɗin haka. Fuskarta na ƙoƙarin ɓoye rashin jin daɗin kalaman da Inna Ladiyo ta jingina mata, amma da ta tuno abinda aka faɗa ɗin halayenta ne ada, sai kuma cikin sauri tayi watsi da ɓacin ran da ya fara damunta.
"Ummanmu tana yi ma Daddy tuwon dawa lokaci bayan lokaci, a zubo min kaɗan, in sha Allahu zan iya ci."
Ta ƙara da faɗin haka tana ƙoƙarin maye gurbin damuwarta da murmushi.
Umma Laraba da kanta ta miƙe zuwa kicin, ta yanki tuwon kaɗan ta saka ma Bintu. Wani ƙarin kulawa da tayi ga Bintun shi ne ɗaukar dunƙulen maggi mai star da tayi ta ɗan barbaɗa a miyan Bintu, ta ɗebi yajinta na tafarnuwa da ya ji maggi da kayan ƙamshi ta zuba kaɗan a gefe, sannan ta kai mata tuwon.
"Na dai yi karambanin barbaɗa miki yaji, ban san ko kina so ba..."
"Na gode Umma, Allah ya saka da alkhairi."
Bintu ta faɗa a ladabce sannan ta karɓi tuwon.
Mamakin da Bintu ta sake shayar da yara da manya na gidan shi ne cinye tuwon da tayi tas, ta ɗauki kwanon ta kai gurin wanke-wanke. Kuma ta cigaba da zama a tsakar gidan tana jan yaransu da hira ta hanyar tambayar sunayensu da na sauran ƴan ɗakunansu har aka kira sallar isha'i. Sannan ta sake alwala ta shiga ɗakin Innaye tayi sallah.
Tun misalin ƙarfe biyar na yamma Innaye ta shiga ɗakin da Hafizu ya gina matsayin masaukin iyalansa, ta ƙara gyarawa tas! Magriba na yi ta kunna maganin sauro ta kai ɗakin sannan ta rufo ƙofar.
Sai dai ko da ƙarfe tara na dare tayi, Innaye ta gabatar ma da Bintu ɗakin a matsayin inda za ta kwana, shiru tayi cikin tunani na wasu daƙiƙu.
Can kuma sai ta ɗaga kanta tana kallon gefen Innaye, idanunta ƙasa-ƙasa, da sanyin murya ta ce
"Innaye in dai bazan takura miki ba ni na fi so in kwana anan, ko kan dpguwar kujera ma ya ishe ni. Amma idan zan takura miki sai in je can ɗin in kwanta..."
"Babu komai, ki shiga ciki ki kwanta kawai. Allah ya tashe mu lafiya."
Innaye ta faɗi haka tun kafin ta aje numfashin maganarta.
"Na gode. Allah ya tashe mu lafiya."
Ta faɗa sannan ta shige cikin ɗakin.
Tsohon fallen zanen Innaye da yake maƙale jikin bango ta ɗauka ta ɗaura, bayan ta cire sket ɗin leshin da yake jikinta. Da bismillah a bakinta ta haye gadon Innaye da yasha gyaran zanin gado sabo fil, an lafe shi tas!kamar gadon ɗakin matashiyar mace.
Da yake bata yi tunanin kwana zai kamata ba, shi yasa bata zo da shirin komai na kwanciya barci ba. Ƙuriii tayi da idanu tana kallon saman POP ɗin ɗakin Innaye, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta.
'Lokacin da saƙon text message ɗin Hafiz ya riske ta, daman tana cikin tension, domin ko a lokacin kwananta biyu a kwance bata da lafiya. Kuma ta ƙi yarda sam a kaita asibiti, sai likita ne yake zuwa gida yana kula da ita.
A lokacin da saƙon ya shiga cikin wayarta, suna zaune ne ita, Ummansu, da Aunty Sadiya da ta je gidan ƙara duba lafiyarta. Kamar baza ta ɗaga wayar ba, sai kuma ta ɗauka ta buɗe, duk da wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ƙarar shigowar saƙon da ta ji bazai wuce na kamfanin MTN ba.
Tun kafin ta gama karanta mummunan saƙon da ta ɗauke shi a mafi munin wulaƙantaccen saƙo da Hafiz ya taɓa aika mata a iya tsawon rayuwarsu, jikinta ya ɗauki kyarma kamar ana kaɗa mata ganga. Tana gama karantawa ta saki wayar a ƙasa, tayi diri-diri tana zazzare idanu kamar sabuwar kamun hauka, sai kuma ta ƙwalla wani gigitaccen ihu da yasa Ummansu da Aunty Sadiya toshe kunnayensu a tsorace.
Bayan gama ihun, ƙaƙƙarfan kuka ta fashe da shi a lokacin Umma da Sadiya suka taho kusa da ita a gigice suna tambayarta Lafiya? Me yake faruwa?
"Yayarsu ɗauki wayar ki duba mu ji saƙon me aka aiko mata da har ya jefa ta cikin wannan halin?"
Umma ta faɗi haka ga Sadiya bayan ta lura Bintu baza ta nutsu ta faɗa musu abinda ke faruwa ba.
Da saurin gaske Sadiya ta rarumi wayar Bintu da ke yashe a ƙasa, tana gama karanta saƙon, saboda tsananin baƙin ciki da takaicin da Bintu ta ba ta riƙo kafaɗar Bintun ta yi da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ta yi amfani da shi wajen gaurama Bintu wani ƙaƙƙarfan marin da yasa lokaci ɗaya ta ɗauke wuta ɗif! Kawai ƙarar da take ji a kunnuwanta shi ne dummmm!!!
Ta dawo cikin nutsuwarta ne ta ji muryar Aunty Sadiya tana ta zazzaga faɗa kamar za ta ari baki.
Ɗaiɗaikun kalmomin da suka shiga kunnenta su ne
"Idan kin raina ma su Ummanmu hankali ni baki isa ki raina min hankali ba, mintuna ashirin na baki, ki harhaɗo kayanki mu wuce can gidana, idan dai ba dussa bane a cikin ƙwaƙwalwar kanki kwanaki bakwai ya ishe ki koyon yadda ake mu'amala da mutane.
Kasancewar Aunty Sadiya babbar ƴa a gidan, kuma ta mori hankali da nutsuwar da iyaye da sauran ƙannenta gaba ɗaya suke alfahari da ita. Da wannan dalilin yasa a mafiyawancin hukunci idan ta yanke ba'a mata musu a gidan. Kafin Daddy ya dawo, har ta ɗauki Bintu da take sharɓen hawaye da kumburarren kumatu sun wuce gidanta, sai a waya ta kira mahaifinsu ta faɗa mishi duk abinda ke faruwa.
"To babu damuwa. Amma duk yadda ake ciki dai kar ta daɗe, tunda mijinta ya mayar da ita ɗakinta gara ayi duk mai yiwuwa ta koma ɗakinta cikin ƙanƙanin lokaci."
"To shi kenan Daddy. In sha Allah."
Zaman gidan Aunty Sadiya da tayi na kwanaki bakwai, wata sabuwar rayuwa ce ta samu Bintu da taimakon Allah da taimakon Aunty Sadiya.
Aka yi sa'a kuma a lokacin da taje gidan Yar mijin Aunty Sadiya tana gidan tana jinya bayan sun gama jerangiyar asibitoci babu sauƙi sai na Allah. Da farko dai Mummunar hawan jini ne ya haifar ma da mare lafiyar mutuwar ɓarin jiki, daga bisani kuma sai ciwon ya juye kamar asiri aka yi mata, tana kwance sharɓan kamar matacciya, Kashi a kwance fitsari a kwance haka take yi.
Akwai yaran mare lafiyar guda biyu da suke gidan suna jinyarta, sannan ga mai aikin Aunty Sadiya, amma duk da haka ta ga yadda Yayarta ke cin uban aikin kashi kamar Ummansu ke kwance tana jinya. Ganin hakan shi ya fara sanyayar mata da jiki.
Wani abu da ta ƙara lura da shi shi ne wani extra ordinary kulawa ta musamman da mijin Aunty Sadiya mai suna Alh Buba yake mata.
Ba tare da jin kunyar idanun Bintu ko ƴaƴansu ba a gaban kowa yake yawan faɗin
"Allah ya miki albarka Sadiyata. Allah ya sani Ina alfahari da ke, amma kulawa da Yaya Asabe da kike yi yasa na ƙara alfahari da ke. In dai Aljannarki a ƙarƙashin ƙafata take, na ɗaga miki ki shiga a sauƙaƙe Sadiyata."
Idan ya jero ma Yayar tata waɗannan kalaman, daga irin murmushi da wani ɗan mirgina kai da take yi, ta san daɗi da matsanancin farin ciki ne ke kai mata karo.
Kafin ta amsa sai ta ɗanyi fari da ido, sannan ta mayar mishi da martani a tausashe
"Na gode Alhajina. Nima ina alfahari da kai. Kuma in banda kai da abinka... Yaya Asabe ai ko ba Ƴar'uwa bace ta cancanci kulawa da kyautatawa saboda jarabtar da Allah yayi mata. Fatanmu dai Allah ya bata lafiya. Ina kuma ƙara roƙon Allah ya barmu tare har a Aljannatul-Firdaus."
"Ameen."
Suke amsawa gaba ɗaya. Bayan haka kuma Kamar ba tsofaffi ba, sai suyi musayar tattausan murmushi a tsakaninsu.
Bayan zama na fuska da fuska da suka sha yi a mabanbantan lokuta ita da Yayar tata tana mata rihazal ɗin munanan halayenta, da irin matakan da za ta bi a sauƙaƙe gurin gyara rayuwarta sannan ta gyara rayuwar aurenta. Ta kuma ƙaru da sake kusanta kanta sosai da Ubangiji, duk inda ƙarfe uku da rabi na dare tayi, Yayarta za ta fito turakar mai gida ta tashe ta, ta saka ta yin ibada, ba ta sake kwanciya sai misalin ƙarfe takwas da rabi idan ta yi sallar Duha.
Daman dai sakaci ne irin namu na ƴaƴan Adam, amma duk inda damuwa da ƙunci haɗe da baƙin ciki suka yi yawa, to babbar mafita da hanyar da za'a kama mai ɓullewa shi ne a kusanta kai da Ubangiji, sannan ayi ta istigfari da hailala.
Waɗannan abubuwa da Aunty Sadiya ta koyar da Bintu cikin kwanaki bakwai, yasa ta samun wani nutsuwa da kwanciyar hankali na musamman, wanda ita da kanta baza ta iya tuna lokacin da ta shiga cikin makamancin wannan nutsuwar ba.
Har yanzu Hafiz da ɗanta Aadil suna cikin sahu na farko a rayuwarta, amma fa kaso saba'in cikin ɗari na yadda al'amarinsu ya dame ta a baya, yanzu ba ya damunta.
Sun tattauna muhimman batutuwa da ƴar uwarta, ta kuma gane kura-kuran da ta daɗe tana tafkawa. Wani abun burgewa kuma shi ne da gaske ta ɗauki aniyar gyara kura-kuranta.
Da wannan dalilin yasa bata yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zuwa ƙauyen Faƙo neman gafarar su Innaye. Ba kuma don barazanar da Hafiz yayi mata ba.'
Nannauyan ajiyar zuciya ta ja ta sauke sadda ta zo nan a tunaninta, ta ɗaga hannu biyu sama ta karanto addu'ar barci ta shafa a fuska da sassan jikinta. Sannan ta lumshe idanu tana sauke numfashi cikin nutsuwa, har zuwa sadda nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Kamar yadda ta fara sabawa da ɗabi'ar da Auntynta Sadiya ta ɗora ta akai na tashi cikin dare yin ibada, ƙarfe huɗu saura minti goma na asubahi ta farka da salati a bakinta.
Ɗankwalin kanta da ya zame saboda barci ta ɗauka ta ɗaura a kanta, sannan ta sauka daga kan gadon ta fito da nufin zuwa waje don ɗauro alwala.
Tana fitowa Falo, ta ga Innaye tana sallar nafilfili, kamar yadda itama ta saba gabatarwa ko wane dare. Ajiyar zuciya ta ja na ƙara samun nutsuwa, ta ɗauki buta nan lungun kujerar da take kusa da ƙofar ɗakin Innaye, ta buɗe ƙofa ba tare da tsoron komai ba ta fita tsakar gida ta ɗauro alwala.
********
Ƙarfe biyu na rana tayi ma su Aunty Balira a gidan Baffa. Da yake duk basu da labarin zuwan Bintu, turus suka yi da ɗaurarriyar fuska suna aika mata da kallon banza lokacin da suka ganta zaune dirshan a tsakiyar ɗakin Innaye tana cin ɗanwake.
Da farko jikin Bintu ne ya ɗanyi sanyi bayan ta tuna irin tozarcin da tayi musu a haɗuwarsu ta ƙarshe. Sai kuma ta yi ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushi, a zuciyarta take godiya ga Allah da yasa bata bi dokin zuciya da zugar shaiɗan ta miƙa su gurin ƴansanda ba. Yau da ina za ta saka kanta da kunya?
"Oyoyo... Sannunku da dawowa Auntys ɗina. Ku shigo mana?"
Tayi maganar da sanyin murya, har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace ba.
"Uhmmm! Bintu kenan! Wani salon munafurci da kisisinar ce kuma ta saka ki yi mana murmushi? Kar dai ki manta, mu ɗin ne dai warki daidai da ƙugun kowa, la'ada waje za mu ci..."
Idanunta ciccike da hawaye ta katse Rakiya da cewa
"Wallahi Tallahi alkhairi ne ya kawo ni gare ku ba sharri ba Aunty Rakiya. Na zo neman gafararku ne, don Allah ku yafe min."
Dariyar da Rakiya da Ladidi suka saka mata yasa ta ƙara jin duk ta tsani kanta.
"Uhmmm! Bintu kar dai ace a cikin kwanaki bakwai da auren Hafizu da ƴar mutunci da arziki Kareematu har kin nuna kinyi luguf ɗin da za ki gane Borno gabas take..."
"Miye haka Ladidi? Me kike faɗa haka? Wani irin maganganun banza ne haka kuke min a cikin ɗaki?"
Innaye da ta idar da sallah ta faɗi haka ranta a ɓace.
Kafin ta sake cewa komai Baffa yayi sallama a ƙofar ɗakin. Da saurin gaske duk su ukun suka amsa masa sannan suka nemi gurin zama suka zazzauna a ƙasa.
Baffa yana shigowa ya nemi gurin zama kan kujera ya zauna. Bayan sun gaishe shi, barka da dawowa ya fara yi musu, sannan ya tambayesu yadda aka yi taron suna. Bayan sun amsa da lafiya ƙalau ne ya buɗe taron da addu'a. Nasiha mai shiga jiki yayi musu akan falalar da ke tattare da yafiya, sannan ya ƙarƙare maganganunsa da faɗin abinda ke tafe da Bintu.
Ba don sun yarda ɗari bisa ɗari Bintu ta shiryu ba, duk suka yafe mata don ganin idon Baffa da Innaye.
Da yanayin jin daɗi a fuska da muryar Bintu tayi musu godiya. Baffa ya ƙara musu taƙaitaccen nasiha sannan ya fice daga ɗakin, bayan ya jaddada ma Bintu lallai tayi gaggawar gama cin abinci, ga direban da zai tafi Kaduna can ɗan maƙwafcinsu sai ya wuce da ita.
Duk yadda Bintu ta so ganin sakin fuskarsu Aunty Balira abun ya gagara, ko da tayi nakwa-nakwa da fuska za ta saka musu kuka ƙasa-ƙasa Aunty Rakiya ta galla mata harara, ta haɗa da jan siririn tsaki ta kawar da kai.
Ita kuwa Aunty Ladidi don haushi ma buta ta ɗauka ta fice daga ɗakin, a cewarta, bayi za ta je.
"Kin ga Bintu, tunda dai duk mun furta mun yafe miki don Allah kar ki nemi ki takura mana. In banda ma zuciyar musulunci mai cike da imani ta ya lokaci ɗaya bawa zai yafe tozarcin da aka yi mishi shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ba sau uku ba? Ki tafi kawai Bintu. Don yafewa mun yafe miki, amma ɗorewar kyakkyawar mu'amala a tsakaninmu da ke zai biyo bayan yadda kika cigaba da mu'amalantarmu ne. Allah ya mayar da ke gida lafiya.."
Aunty Balira ta faɗi haka, da fuska mara walwala.
Innaye bata nemi matsanta musu ba, saboda ta san suna da gaskiya. Bayan haka ma zuciya kowa da irin tasa, wata zuciyar ko ta yafe sai a hankali za ta manta abinda ya faru. Nasiha ta ɗora musu daga inda Baffa ya tsaya har zuwa lokacin da aka aiko yaro wai idan Hajiya Bintu ta gama ta fito su tafi.
Bintu da taje garin daga ita sai ƙaramar jaka rataye a kafaɗarta, sai ga shi ta tafi da buhu guda na tsarabar da iyalan Baffa suka haɗa mata. Tana zaune a cikin mota, tayi shiru tana tunanin halayen Innaye, Baffa, da ahalinsu. Zuciyarta cike da da na sani a karo na barkatai.
Duk da bata taso a gidansu ta ga suna da dangi irinna ƙauyen-ƙayau haka kamar su Innaye ba, ko daga mu'amalar da Ummansu take yi da ƴan'uwan mijinta, maƙwafta da basu da shi da almajirai, ya kamata ace ta koya daga halin arzikin iyayenta.
Ta rasa ta yadda aka yi tayi sakacin da har ta bari shaiɗan yaci galaba a kanta ta dinga tsula irin wannan tsiyar, kamar bata san inda yake mata ciwo ba. Sai ga shi mutanen da ta daɗe tana cuta musu, sun samu damar ramuwa a kanta basu rama ba, a madadin haka ma suka yafe mata, sannan suka bi ta da karamci mai tsayawa a zuciya.
Lallai ta gode ma Allah da yasa ta gane kuskurenta tun lokaci bai ƙure mata ba. Alhamdulillah!
*********
Washe gari da misalin ƙarfe huɗu na yamma direba ya aje Bintu a ƙofar gidan Zulai. Domin can gidan Mummy ta fara zuwa, bata tarar da kowa ba sai Hajja, bayan gaisuwar mutunci da girmamawa da ya shiga tsakaninsu Hajja ta sanar da ita Zulai ba ta nan, ta tafi can gidanta ta ɗebo wasu kayayyaki, saboda gobe za ta tafi Faƙo.
Bata ɓata lokaci ba tasa direba ya juya da ita bayan ta yi mishi kwatancen gidan, zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa kar sake samun saɓani.
Cikin sa'a kuwa ko da ta isa ta tarar da ita a gidan, tana tsaye a bakin ƙofar Falonta da jakunkunan kaya a gabanta maigadi yana kwasa yana lodawa a boot ɗin motarta.
"Ke kuma Lafiya haka wata ƙozai-ƙozai da ke?"
Tambayar da Zulaikha ta fara jefa mata kenan tana mata wani kallo mai cike da wulaƙanci da ƙasƙanci.
Ko kaɗan Bintu bata bari ɓacin rai ya bayyana a fuskarta ba. Ta sani duk cikin ƴan'uwan Hafiz daga Rakiya, sai Zulai, sai Ladidi a rashin haƙuri. Don haka tun kafin ta shigo ta sa ran za ta fuskanci fiye da haka.
"Allah ya huci zuciyarki Hajiya Zulai. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga, na rantse da girman Allah ba tsiya ne ya kawo ni ba. Na zo ne kawai don in nemi gafarar irin abubuwan da na aikata miki a baya, shi kenan ba wani abu ba."
"Bintu?"
Zulai ta kira sunanta da mamaki.
"Ke ce kuwa?"
Ta sake tambayarta mamakinta na daɗa ninkuwa. Domin ita sam ba ta da labarin zuwan Bintu Faƙo, abinda ya wakana da kwanan da tayi.
"Ko dai wani wulaƙancin ne kika sake zuwa kiyi min? Idan ma wulaƙancin ne kin san na dama ki na shanye ki."
"Wallahi ba haka bane Zulai, yafiyar dai da kika ji na ce ita nazo nema. Idan kuma baki yarda ba, kina iya kiran Innaye a waya ki tambayeta, don shekaran jiya na je can, acan ma na kwana, ban bar Faƙo ba sai da na tabbatar sun yafe min ita da su Aunty Balira."
"Shi kenan! Shigo, Bismillah."
Zulai ta faɗa sannan ta matsa mata daga hanyar shiga cikin falon, har lokacin mamakin da take yi bai bar kan fuskarta ba. Kafin ta zauna sai da ta shiga kicin ta ɗauko ma Bintu ruwa da lemu.
"Gidanki ya yi kyau sosai Zulai, Allah ya sanya albarka ya ƙara zaunar da ku lafiya."
Bintu ta faɗa fuskarta na bayyana gaskiyar asirin zuciyarta ta tona, kamar ba gidan bane a wancan karon hassada da kishi da baƙin ciki suka rufe mata idanu ta kasa yaba kyawunshi a wancan lokacin.
"Uhmmm! Amin."
Zulai ta amsa a taƙaice.
Ruwan ta tsiyaya a kofi ta sha kaɗan, sannan ta buɗe baki ta sake roƙar yafiyar Zulai cikin ƙanƙan da kai, har tana ƴan ƙananun hawaye.
Ba tare da wani ja'inja ba a mamakance Zulai ta ce ta yafe mata. Don ita ganin al'amarin take yi kamar a shirin film ko kuma tatsuniya, jira kawai take yi taga ƙarshen shi ta samu sararin furta ƙurungus!
Sai kuma ta ga har Bintu ta tashi tafiya bata yi wani yanayi da zai bayyana yafiyar da ta nema ba har zuciyarta bane.
A mutunce suka yi sallama, Bintu tana ta godiya ma Zulai kan yafiyar da tayi mata cikin ƙanƙanin lokaci, har ta fita waje ta koma cikin falon, ga tsammanin Zulai za ta tambayi ina Aadil yake ne, sai ta ji ta ce
"Taimaka min da lambarki mu dinga gaisawa mana Zulaikha? Kin san bahaushe ya ce yawan gaisuwa ya fi yawan faɗa."
"Haka ne."
Ta amsa a ɗarare, da alamun har lokacin mamaki da kaɗuwa bai sake ta ba, ta karanto mata lambar wayar ita kuma Bintu tana shigarwa cikin wayarta. Sai da ta gama tsaf sannan ta sake yi mata godiya ta fita a falon, fuskarta cike da murmushi.
Zulaikha tana jin ƙarar rufe get alamun Bintu sun wuce ta rarumo wayarta da sauri ta danna kiran lambar Innaye, tana ɗauka daga can ɓangaren, ko gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta fara kakabin al'amarin
"In da ranka ka sha kallo Innaye... Wai fa Bintu ce tazo har gidana neman gafara kan irin wulaƙanci da cin mutuncin da tayi min a baya..."
"To menene a ciki Zulai? Ai ta yi kyan kai da bata tsaya girman kai ya hanata aikata abinda ya kamata ba. Mu ma ta zo nan har da kwana. Ina fatan dai kin yafe mata ba tare da tashin-tashina ba?"
"To ya zanyi Innaye? Na dai yafe ba don halinta ba..."
"To madallah! Zan kira ki anjima. Barin sallami Baffanku, kwaɗon rama nake masa..."
Jin sunan kwaɗon rama yasa miyaun bakinta tsinkewa, A shagwaɓe ta ce.
"Innaye ni ma zan ci, a tsinko da yawa gobe da wuri a kwaɗanta min kafin mu ƙaraso."
"Allah ya tsare, Ubangiji ya kawo ku lafiya."
Innaye bata jira ta amsa ba ta katse wayar.
********
Yau kwananta huɗu da dawowa daga Faƙo. Sosai hankalinta ya ƙara kwanciya, kwana biyu ta ƙara a gidan Aunty Sadiya sannan ta tattara kayanta ta koma gidan Daddy.
Yau ne ta yanke shawarar za ta kai ma Hafiz ziyara har Ofishinsa. Saboda idan ba can ɗin ta je ba, babu in da za ta samu ganinsa suyi magana ta nutsuwa fuska da fuska. Ta daɗe da sani ko ta kira shi bazai zo ba, baya ma ɗaukar wayarta, balle har ta sararin faɗa mishi abinda take so.
Bata sha wahalar samun iso zuwa Ofishinsa ba, saboda duk an santa a ma'aikatarsu Hafiz ɗin. Tana sanye ne da sutura ta mutunci, hijabin jikinta ya sauka har ƙasan gwuiwoyinta, sai daga can ƙasa ake ganin sket ɗin jikinta na atamfar Super Holland. Duk da fuskarta ta yi fayau saboda rama, amma ta yi kyau abinda, kuma da yake jikinta mai kyau ne babu ma wanda zai kalle ta ya ce ta kai shekaru talatin da huɗu, balle har ayi tunanin ta yi aure ko kuma ace ta haifi Aadil, in dai za'a faɗi gaskiya, Bintu tana cikin kyawawan mata ajin farko. Kuma kyawunta na ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta daɗe tana taka rawa a rayuwar Hafiz.
Tsawon daƙiƙu talatin suka ɓata suna musayar kallo a tsakaninsu. Hafiz da idanu cike da mamaki da yanayin rashin murna da ganinta, ita kuwa Bintu da fuska mai cike da kewa... wata matsananciyar ƙauna da ta gaza ɓoyuwa ta bayyana a fuskarta.
"Ayya mana Daddyn Aadil, baka yi murna da ganina bane?"
Ta faɗa da sassanyar murya.
"Uhmmm! Bintu kenan."
Ya yi maganar da yanayin takaici.
"Me ya kawo ki nan?"
Ya sake faɗa tun kafin tayi magana.
"Zan iya zama?"
Ta kore tambayarshi da na ta tambayar.
"Uhmmm! Idan kin so"
Ya amsa a taƙaice.
Da sanyin jiki sosai ta taka a hankali zuwa inda aka tanadi kujerun zaman baƙin da suka zo Ofis ɗin. Zuciyarta cike da baƙin cikin yadda son zuciyarta ya janyo rugujewar matsananciyar soyayyar da Hafiz yake mata.
'Ya rabbb!'
Ta faɗa a hankali, sannan ta sausauta murya ta fara gaishe shi da tambayar bayan rabuwa.
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah!"
Amsar da ya bata kenan a taƙaice, da yanayin gundura ƙarara.
"Me ya kawo ki nan?"
Ya sake tambayarta a taƙaice.
"Kayi haƙuri Daddyn Aadil. Na sani duk ni na jawo abubuwa suka taɓarɓare har haka a tsakaninmu. Ina mai sake baka haƙuri a karo na uku..."
"Bintu!! Me ya kawo ki nan??"
Ya jefa mata tambayar da murya mai bayyana ɓacin rai ƙarara.
Jikinta ne ya ƙara sanyi, gwuiyawunta suka ƙara saki, kamar wacce ta kwana ta yini tana zawo.
Daƙiƙu talatin ta ɓata tana kallon cikin idanunshi tana karantarsu, ƙirjinta ne ya buga daram!!! Domin babu abinda take gani sai matsananciyar tsanarta.
"Na zo ne in ji makomar zamantakewar aurenmu daga bakinka..."
"Makoma?"
Ya tambaye ta.
"Wace makoma kike magana kuma Bintu?"
Ya sake tambayarta da tsawa-tsawa.
"Na zaci duk makomar da kike magana akai na riga da na bayyana miki ta saƙon text message tun ranar da aka tilasta min ba da son raina ba na mayar da ƙaddararren aurenki...?"
"Ƙaddararre Hafiz?"
Ta tambaye shi muryarta na rawa.
"Auren nawa ne kake kira ƙaddararre Hafiz?"
Ta sake faɗa hankalinta a tashe, bayan ta miƙe tsaye, idanunta a warwaje. Hannayenta duk biyu dafe da ƙirji.
"Kina mamaki ne Bintu?"
Ya tambayeta yana ƴar dariya, amma irin dariyar nan ta zallar takaici.
"Ai idan na kira aurenki da ƙaddararre na yi miki da sauƙi Bintu. Ko dai kin manta irin makirce-makirce da kissa da tuggun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 40