sai take jin kamar iskar ɗakin ne yake neman yi mata kaɗan. Kamar ma dai idan ta cigaba da zama a cikin ɗakin lallai ajali zai risketa a gaggauce. Ga shi yau ita kaɗai ce a ɗakin, Mashkura tana can gidan Yaya Abubakar, balle idan ta yanke jiki ta faɗi Mashkura ta kawo mata ɗauki.
Ba tare da duba kayan barcin da ke jikinta ba ta kama hanyar fita daga ɗakin. Tana tafe tana tangaɗi kamar wacce ta sha kayan maye. Ba tare da duba tsalawar dare ba, kai tsaye ɓangaren mahaifinta ta nufa.
Cikin hukuncin Allah tana shiga falon Daddynta ta tarar da shi zaune a kan dadduma can gefe guda, da alamun sallah ya idar, domin ga Alƙur'ani nan ajiye a gefensa, hannunsa kuma riƙe da casbaha yana ja.
Ƙarar buɗe ƙofar da ya ji ne yasa shi waigawa a mamakance, domin ya san babu mai shigowa ɗakinsa falonsa a irin wannan lokaci sai Hajiya. Ita kuma tun ɗazu ta shigo, ya ma barta a cikin ɗaki tana barci. Ganin Bintu ce yasa motsin tasbihi da bakinsa ke yi tsagaitawa, ya ƙura mata idanu yana kallon yadda ta ƙara yin zuru-zuru a cikin kwanakin, kamar wacce ta ɗauki wasu watanni masu yawa tana jinya.
Bai gushe yana kallonta ba har zuwa sadda ta ƙarasa inda yake ta zube a gabansa.
"Na tuba... Na bi Allah na bi ka Daddy... Ka taimaka min... Wallahi ina matsanancin son Hafeez... Bazan iya rayuwa babu shi ba..."
Tana zuwa nan a maganganunta ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka...
******* *******
Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Tun ana gobe ɗaurin auren Hafiz da Kareema, su Baffa da sauran tawagar maza ƴan ɗaurin aure da ɗaiɗaikun mata ƴan biko suka dira a babban birnin tarayya Abuja.
Biki ne da duk da an saka kwanakin a ƙurarren lokaci amma fa an shirya ta ko wane ɓangare. Kuma ƙarin abin ban sha'awar shi ne ta ko wane ɓangare suna murna da haba-haba da al'amarin. Ga wanda bai sani ba ma sai yayi tsammanin wannan auren shi ne na farko da Hafiz zaiyi a rayuwarsa ta duniya.
Taron biki ne na gani a faɗa aka shirya a gidan Abba Lurwanu, gidan Mummy Saudah, sai dai babban gangamin kuma yana can Faƙo gidan Innaye. saboda Hafiz ya sha alwashin bayan an gama ɗaura aure, anyi dinner a ranar za'a kai Amarya gidan Abba Lurwanu ta kwana, washe gari da sassafe za'a wuce da ita Faƙo. A taƙaice dai, baza'a kai Amarya gidanta ba sai ta kwana ta hantse a ɗakin Innaye, saɓanin Bintu da iyakarta gidan Abba Lurwanu aka wuce da ita gidan Hafiz.
Kamar wancen auren na Bintu, wannan karon ma Abba Lurwanu ne ya zama waliyyin Ango, kuma shi ya biya mishi sadaki. Yana zaune a tsakiyar su Baffa, da mahaifin Bintu, wanda ya ke ta dariyar yaƙe, daga can ciki kuwa yana jin zafin yadda Bintu tayi wasa-rere da damarta har tayi saken da waɗannan nagartattun mutane masu halin girma da kawaici suke neman kuɓuce mata a matsayin surukai.
Kamar Baffa bai samu labarin rashin mutuncin da Bintu taje har tsakiyar ɗakin Innaye ta shimfiɗa ba. Haka ya saki fuska sosai suka gaisa da mahaifin Bintu, kuma wani ƙarin halin girman shi ne duk inda Alh Lurwanu ya ja shi, in dai mahaifin Bintu na gurin kai tsaye yake damƙo hannunsa su gabatar da al'amarin su uku. Wanda bai sani ba sai yayi tsammanin ƴan'uwanta ne mai ƙarfi
Misalin ƙarfe uku na rana, Baffa da ƴan'uwansa maza da suka halarci ɗaurin aure sun gama shirin komawa Faƙo. Daga ɓangaren Abba Lurwanu, mahaifin Bintu, Hafeez an haɗa ma su Baffa sha tara ta arziki. Domin har wannan lokacin mahaifin Bintu na tare da su, yana ta dama-dama da Baffa yana ƙara karantar kirkinsa.
Har sun yi sallama, suna tsaye a jikin motar da Baffa zai shiga, Daddyn Bintu yayi suɓul da baka wajen furta maganar da tun ɗazu take mishi ƙaiƙayi a maƙoshi.
"Mal Aminu, ina dai sake baka haƙuri game da kuskuren da Bintu tayi, don Allah idan ka je gida aba Innaye da sauran Yayyen Hafizu da duk waɗanda Bintu ta ɓata ma haƙuri. Ba goyon bayanta nake yi ba, amma ina tabbatar maka a zaman gidan da Bintu take yi ta shiga taitayinta, ayi haƙuri... Don Allah a taushi Hafizu, bayan kwana biyu yayi haƙuri ya maida ita ɗakinta kafin ta gama iddah!"
Da saurin gaske Baffa ya saki hannun ƙofar da yake riƙe da shi, jin kalaman da ke fita daga bakin Daddyn Bintu. Domin ko da wasa Hafizu bai faɗa mishi ya saki Bintu ba, duk da a wancan ranar bayan ya koma gida Rahina da kanta ta faɗa mishi duk irin tijarar da Bintu taje tayi musu.
"Maganar me kake yi Alhaji? Ban... fahimta ba. Kar dai ka ce min Hafizu ya saki matarsa ba tare da sani na ko na mahaifiyarshi ba?"
Lokaci ɗaya aka fara kallon-kallo tsakanin Daddyn Bintu da Abba Lurwanu. Daƙyar Daddy ya iya buɗe baki ya ce
"Tun wancan ranar da taje Faƙo tayi ma iyalinka rashin kyautawa, da kuma washe gari da taje nan gidan ƙanwarsa tayi mata rashin mutunci. Hafizu yaje har gida ya faɗa min duk abinda ya faru, sannan ya bani takardarta na saki ɗaya..."
"Assha! Assha!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Amma kuwa Hafizu baiyi aiki da hankali ba... Wa ya faɗa mishi cikin sauƙi ake sakin matar da aka fara tara zuri'a da ita? Ya sani, da ya faɗa mana zai aikata ni ko mahaifiyarshi babu wanda zai lamunci haka. Ina zuwa, bari in kira shi."
Yana wannan maganar ne yana latsa wayarsa da nufin lalubo lambar Hafiz.
"Abu dai duk baiyi daɗi ba Baffa. Ni kaina bai faɗa min ba sai bayan da komai ya gama faruwa. Kuma tunanin kun sani tunda ance rashin kyautawar ku tayi ma shi yasa na bari sai bayan an kwaranye hidimar bikinnan sai in kira in baku haƙuri in roƙi alfarmar a mayar da ita ɗakinta. Muje daga ciki sai ka kira shi Baffa."
Ko da suka koma cikin falon Abba Lurwanu, kira na farko da aka yi ma Hafiz bai ɗaga ba, sai a kira na biyu ya ɗauka, da alamun yana cikin abokansa ne, don ga muryarsa nan ana ji suna dararraku.
"Assalamu alaikum! Baffa ya hany..."
"Hafizu ka keɓe yanzunnan daga cikin mutanennan. Ina son yin magana da kai me muhimmanci."
Abba ya bashi umarni.
"To Baffa!"
Ya amsa a ladabce, sannan ya katse kiran. Mintuna biyu tsakani ya sake kiran lambar Baffan, yana ɗauka ya faɗa mishi ya keɓe.
Da faɗa sosai a muryar Baffa yake magana.
"Hafizu? Ina ganin ka yi hankali tunda ka fara aje yara ashe har yanzu da sauran rina a kaba? Me yasa ka saki matarka uwar ƴaƴanka?"
"Baffa..."
"Ka ga ni ban nemi jin wani ƙarin bayani daga gare ka ba. Tabbas na sani Fatima bata kyauta ba, amma hukuncin saki ya yi girma sosai akan ɗan wannan laifin. Matar da aka fara tara iyali da ita, an riga an zama ɗaya, da daɗi babu daɗi haƙuri ake yi a cigaba da gungurawa in ba wata muguwar ƙaddara ba da ba'a fata har zuwa sadda za ta birne ka ko kai ka birne ta. Akwai hanyoyin ladabtar da mace masu yawa ba tare da an kai ga saki ba. Don haka ina roƙo tare da umartarka ka mayar da ita ɗakinka, bayan haka na yarje maka ka ɗauki duk irin matakin da ka so a kanta matuƙar bai saɓa ma addininmu ba."
Shiru Hafiz ya yi na tsawon daƙiƙu sittin, a cikin waɗannan daƙiƙun, babu abinda zuciyar Daddy da Abba Lurwanu ke yi sai luguden daka. Aminci ne mai ƙarfi tsakanin su biyun, don haka damuwar da ke damun ɗaya ta shafi ɗayan. Amma saboda adalci da dattako irinna Abba Lurwanu baiyi niyyar tauye Hafiz don faranta ran Amininsa ba.
"Shi kenan Baffa. Ka zama shaida, na mayar da matata Fatima-Bintu ɗakinta."
Hafizu ya faɗa da cusasshiyar murya.
"Na gode. Allah yayi maka albarka. Ubangiji ya haɗa maka kan matanka."
Baffa ya jero addu'o'in da farin ciki a muryarsa.
"Amin ya Allah. Na gode Baffa, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ubangiji ya mayar da ku gida lafiya."
"Amin ya rabb"
Su Baffa suka amsa gaba ɗaya. Fuskokinsu cike da matsanancin farin ciki.
Mayar da Bintu ɗakinta da Hafiz yayi ba ƙaramin farin ciki ya jefa zuciyar Abba da Daddy ba. Shi yasa har Baffa ya shige cikin mota basu daina jera mishi kalaman godiya ba, abin ma sai ya koma ba Baffa kunya, a ganinsa ai ba wani abun azo a gani bane yayi idan aka haɗa da irin gwaggwaɓan karamci da girmamawar da suke mishi da iyali da duk wani da ya shafe shi.
*******
Bayan gama waya da Baffa, jikin Hafiz sanyi ƙalau ya zube a gefen gadon ɗakin hotel ɗin da suke ciki da abokansa.
Allah yana gani bai so mayar da Bintu ba, shi yasa yake ta ɓoye maganar sakin don kar su Baffa su ji. Ko Zulai baiyi gigin faɗa mata ya saki Bintu ba, ya sani idan ta ji, kamar Innaye ne ta ji.
Yana cikin wannan halin na damuwar abokinsa Ibrahim ɗan gidan Abba Lurwanu da suke zaune a falo da sauran abokansu suna shirye-shiryen zuwa dinner ya shiga cikin ɗakin ya tarar da Hafiz a wannan halin.
"Ya aka yi ne Ango? Me yake faruwa..?"
Da ɓacin rai sosai ya amsa mishi
"Uhmmm! Wallahi yanzu Baffa ya umarceni in mayar da Bintu ɗakinta."
"Shi ne kake ta wani ciccin magani kamar ka kurɓi maɗaci? Common guy, kar ka kuskura ka bari wannan zancen ya ɓata mood ɗin ka na farin ciki. Yau kake sabon ango fa, ka aje duk wani ɓacin rai gefe ɗaya ka rungumi farin cikin da ke tattare da kai.
Kawai shawarar da zan baka ɗaya ne, kar ka kuskura ka bari kayi saken da za'a sake samun matsalolin da aka samu a baya tsakaninka da Bintu. Kuma tun yanzu idan kana da wasu tsare-tsare da dokoki ka kira ka faɗa mata tun yanzu, idan ta shirya sake zama da kai a karo na biyu za ta amince, idan bata shirya ba da kanta za ta sake neman ka sauwaƙe mata. Ka ga shi kenan, ka yada ƙwallon mangwaro ka huta da ƙuda."
Yana gama wannan maganar bai jira cewar Hafiz ba ya fice zuwa falo gurin sauran abokansu.
Maganganun da Ibrahim yayi mishi, su suka dawo ma da Hafiz farin ciki da walwalar da yake neman rasawa sanadiyyar mayar da Bintu ɗakinta. Wayarsa ya ɗauka da yake ajiye gefensa, ya lalubo lambar Bintu ya buɗe gurin tura saƙo ya tura mata saƙon cewa
_*"Kamar yadda albarkacin kaza ƙadangare ke shan ruwa a kasko. Haka Albarkacin Baffa na amince ma sake zama da ke ayau. Na mayar da ke ɗakinki Bintu, amma bisa sharuɗɗa guda biyu. Na ɗaya shi ne, nan da kwanaki uku masu zuwa ki shirya ki tafi har gida ki ba Innaye da sauran ƴan'uwana da sauran matan Baffa haƙuri kan irin cin mutuncin da kika yi musu. Sharaɗi na biyu kuma shi ne ki shirya komawa zaman Faƙo, a gidan Baffa zan sama miki ɗakin zama, sannan za ki dinga cin abinci da abinsha ƙarƙashin kulawar Innaye ne har zuwa lokacin da ni da kaina zan gamsu za ki iya zama da ni baƙauye da ƴan'uwana ƙauyawa. Idan kin amince da waɗannan sharuɗɗan, ina miki maraba da sake zama matar Hafiz a karo na biyu. Idan kuwa baki amince ba ki faɗa min don Allah, ni kuwa yanzun nan zan faranta miki ta hanyar datse sauran igiyoyin da suka rage tsakanina da ke. Hafiz Aminu Faƙo."*_
Yana aika mata da saƙon, ya miƙe tsaye ya fice zuwa falo gurin sauran abokansa suka cigaba da harkokinsu cikin walwala da farin ciki.
Zuciyarsa cike da tabbacin ƙarshen zamansa da Binto ya zo a sauƙaƙe, domin ko rantsuwa yayi babu kaffara, ya sani a girman kai irinna Bintu, ba ta yadda za ayi ta amince da waɗannan sharuɗɗan da ya gindaya mata. Shi kuwa bazai ɓata lokaci ba gurin cike mata sauran saki biyun da ya rage a tsakaninsu, yana da tabbacin Kareema ita kaɗai, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.
*********
Ana idar da sallar magriba, manyan motoci masu numfashi suka cika ƙofar gidan Mummy don ɗiban Amarya da manawarta zuwa wajen dinner. Daman tun da yamma Zulaikha ta faɗa ma Hafiz kar ya wahalar da kansa wajen zuwa ɗaukar amarya.
"Ni zan wakilce ka Yaya, sabuwar motar da Abban Imam yayi min oder ta iso last week. Tunda aka kawo ta ban hau ba, na tsaya jiran wannan ranar mu fara hawa tare da Aunty Kareema..."
"Zzzzzulai...?"
Ya katse ta da kiran sunanta cikin rawar murya.
"Kin yi hauka ne?"
Ya sake faɗa hankalinsa a tashe.
"Yaushe kika koyi tuƙin mota da har zanyi gangancin bari ki ɗaukar min amarya zuwa wajen dinner? Don Allah ki bari, kar ki fara yi min wannan gangancin, in za ki tuƙa kanki bismillah tunda mijinki da yake can wata ƙasa ya amince. Amma ni dai ban yarda ba, tunda dai ba karen hauka ne ya cijeni ba..."
Da sauri ta katse wayar tana tuntsira dariyar ƙeta, a zuciyarta ta ayyana za kuwa ta bashi mamaki. Wato ita rayuwarta a banza ko? Ai kuwa zai gani, da ɗanshi da Amaryarshi ita za ta kai su wajen dinner, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba.
Ƙarfe shidda da rabi dai-dai ta shiga ɗakin da Amarya da ƙawayenta suke ta ce Hibba da Amarya su fito su tafi.
"A'a! Na zaci Ango da kansa shi zai zo ɗaukar amarya?"
Wata daga cikin ƙawayen Amarya mai kafiɗirin tsiya ta faɗi haka tana wani fari da idanu.
Yatsa manuniya Zulaikha tasa tayi ƙasa-ƙasa da gilashin da ya mamayi kusan rabin fuskarta ta aika ma da yarinyar kallon uku saura kwata, ta yatsuna fuska kamar ta ga kashi sannan ta amsa da
"Idan na ɗauki Amarya kamar Angonta ne ya ɗauke ta, dmin ni ɗin ƙanwar Ango ce. Ko akwai wani banbanci tsakanin ƙanwar Ango da Ango?"
"A'a! Mayar da wuƙar ƙanwar Ango. Ni ban ɗauka da zafi ba."
Ta faɗa cikin waskiya tana dariya.
Ko kafin motocin da za su kwashi jama'a su iso, tuni Zulaikha ta kwashi Kareema, Hibba, Aadil, Imam sunyi gaba, babu abinda take yi sai dariya cikin ranta.
"Yaya, kar kayi wahalar zuwa gidan Mummy ɗaukar Amarya, mu munyi gaba. Amma kana iya tarar da mu a ƙofar event center ɗin don ku shiga tare, Amma fa idan tuƙin rashin ƙwarewa ta bai sa na kashe maka amarya ba."
Saƙon da ta tura ma Hafiz kenan bayan sun isa gurin
*******
Kamar yadda aka tsara, a daren ranar aka wuce da Amarya gidan Abba Lurwanu. Sun sami tarbar girma, tun a daren aka ringa ina aka saka ina aka aje da su har zuwa washe gari.
Bayan sun karya kumallo misalin ƙarfe tara na safiya suka kama hanyar tafiya Faƙo. A cikin tsadaddun motoci guda huɗu da Abba Lurwanu ya bada ayi tafiyar da su.
Sun yi tafiyar ne a wadace, babu takura ko kaɗan. Mota ɗaya aka saka Amarya, Zulaikha, Hibba, sai ɗaya daga cikin ƙawayen Amarya mai suna Maryam. Mota ɗaya aka Matan Abba Lurwanu biyu, matar Ibrahim, babbar ƴar Abba Lurwanu mai suna Aunty Zainab.
Mota ɗaya kuma ƙannen Momy guda biyu, sai ƙannen mahaifin Kareema biyu. Mota ɗaya kuma aka ɗauki ƴan biko da suka zo daga Faƙo. Sai babbar motar Hillux da aka cike bayanta aka shaƙe da kayan garar surukai wanda za a kaiwa su Innaye.
Da yake direbobin an faɗa musu tafiya ce mai nisa a gabansu, shiyasa basu yi tuƙi na wasa ba. Wajen karfe ɗaya na rana suka isa Faƙo. Kun dai san mutanen ƙauye da karamci, balle ma su Innaye da suka samu shaidar kirki da sanin ya kamata. Sun samu tarba ta girma sosai a wajen su Anty Balira da Innaye, abokan zamanta.
Dama tunda bikin ya matso, kasancewar gidan Baffa akwai fili sosai daga can ɓangaren ɗakin Innaye, nan Hafiz yasa aka yanka mishi fili, duk a ƙoƙarinsa na gyara kuren da yayi a zamansa da Bintu, ya ɗauko ƙwararrun magina daga Kaduna, cikin sati biyu aka gama gina uwar ɗaka da falo da bayi, a cikin sati uku kuwa, hatta funitures an zuba a cikin ɗakunan. A ganinsa har da rashin kwana biyu da basa yi a cikin ƙauyen shi yasa sam Bintu bata saba da ƴan'uwansa ba, ya gyara nan ɗin ne a matsayin gurin saukarsa da iyalinsa. Kwana ɗaya, biyu, uku, idan ta kama har sati ɗaya ko biyu za su dinga yi a ƙauyen.
Sannan yasa aka ƙara gyara duk inda ke buƙatar gyara a gidan, aka yi fenti mai masifar kyau, sannan ya canja ma su Innaye da abokan zamanta da Baffa kayan ɗakunansu gaba ɗaya.
Ginin da Hafiz yayi nan aka sauki Amarya da manawarta, kafin ƙiftawa da Bismillah aka dabaibayesu da kayan abinci cima iri-iri da katan-katan na lemuka. Wani abun burgewar kuma shi ne a kayayyakin abincin da su Innaye suka tarbi Amarya da manawarta da shi har da kalolin cima ta marmari, irin wanda ba'a cika samu a birni ba sai a ƙauyuka. Sun ci, sun sha, sun yi hani'an! A nutse su ka yi sallah, fuskokinsu gaba ɗaya cike da farin ciki. Bayan sun huta, suka dauki Kareema zuwa gurin su Innaye domin yin buɗar kai.
Dangin Hafizu ƙwansu da ƙwarƙwata kowa ya fito. Cikin gidan Innaye cike yake da bil'adama dan-ƙam babu masaka tsinke. Kuma abinda ya ƙara ƙayata bikin shi ne masu kiɗan ƙwarya da aka tafi har garin Kaduna aka ɗauko hayarsu, Sune suka je tun da misalin sha biyun rana, aka ware musu gurin zama ta cikin gidan Baffa suna ta waƙe-waƙensu na gargajiya matan ƙauye suna juya mazaunai.
Fitowar Amarya da danginta da niyyar zuwa ɗakin Innaye yasa masu kiɗa canja salon kiɗansu da yanayi mafi daɗaɗawa, nan take filin rawa ya ƙara tumbatsa da mata, masu girgiza na yi, masu guɗa nayi, masu kirari na yi, abin dai gwanin ban sha'awa.
Wani harkar girma da Matan Abba Lurwanu da Auntys ɗin Kareema suka yi shi ne, kafin su wuce zuwa ɗakin Innaye, sai da suka ɗan tsaya da Amarya a filin rawar, suka yi ma masu kiɗi da mai waƙa da masu rawa yayyafin kuɗi masu yawa, sannan suka ja hannun Amarya zuwa ɗakin Innaye aka bar Hibba da Maryam a fili da Zulaikha, wacce jin guɗar da ke alamta an fito da Amarya yasa ta fitowa daga uwarɗakin Innaye.
Innaye tana zaune cikin ƴan'uwa da abokan arzikinta, ta yi kwalliyarta gwargwado ta mutanen da, saboda kyawun jikinta babu wanda zai ce ita ta haifi su Aunty Balira. Ta sha atamfarta super Holland, ɗaya daga cikin ɗinke-ɗinke masu tsada har kala goma sha biyu da Zulaikha ta aika mata da su, shida Hafiz ne ya siya, shida Zulai ta siya, sannan ta haɗa duka sha biyun ta ba tela da na su Aunty Balira hurhuɗu ya ɗinka musu.
Matan Baffa kuma kala uku-uku, sauran yaran gidan kuma mazansu da mata yara da manya kowa kala bibiyu.
Baffa kalolin shadda da yaduka har bakwai ta ɗinka mishi. Su Baba Abubakar da matansu duk sun shiga cikin kasafi, har Liman da Ladan da suka kasance abokan Baffa sun karɓi rabonsu. Maƙudan kuɗaɗe Abban Imamu ya sakar mata, sannan ya ƙara da jaddada mata lallai ta tabbatar ta yi ma kowa tsaraba, idan kuɗaɗen basu isa ba ma ta faɗa mishi ya ƙara mata.
Wani aikin hankali da Zulaikha tayi shi ne mota guda ta aike musu da shi na kayayyakin ana saura kwanaki uku bikin Hafiz. Shi yasa tun da Zulai ta isa gidan, kamar tauraruwa haka ta zama, kusan kowa so yake ya gaisa da ita yayi mata godiya. Daƙyar ta yakice kanta ta gudu uwarɗakin Innaye bayan ta basu uzurin kanta na ciwo, duk da haka sai da yayyinta uku suka bi ta, bata fito ba sai yanzu da ta ji an fito da Amarya.
Innaye babu abinda take aikin yi sai sakin murmushi a kunyace, lokacin da aka damƙa mata amanar Amarya ita da abokan zamanta. A taƙaice tayi addu'a, bayan haka ta kasa ƙara cewa komai, har zuwa sadda aka fara shigo da manyan randuna na kayan gara da buhuna na kayan abinci, tun matan ƙauye suna ƙirga buhu da kwalaye har bakunansu ya mutu-murus.
Tsakiyar falon Innaye da ƙofar ɗakinta sai da aka shaƙe taf da kayayyaki. Abin dai ba'a cewa komai sai hamdala. Bayan waɗannan kayan abincin kuma, Zannuwa da shaddodi guda goma sha biyar Mummy Saudah ta bayar na su Innaye, abokan zamanta da yayyen ango.
Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Nan take iyaye da ƴan'uwan Hafizu suka fara kwance haɓar zani suna fito da kuɗin da za su haɗa ma Amarya na tarba. Zulaikha ta shigo da fara'a ta haɗa zufa tai sharkaf saboda rawar da tayi, ta ɗan tsallaka ta shige cikin ɗaki, bandir ɗin dubu ɗari ta ɗauko a jakarta ta miƙa ma Aunty Balira cewa a haɗa a cikin kuɗin sallamar Amarya.
Abu dai anyi shi cikin mutunci da arziki. An mayar da Amarya ɓangaren da aka sauketa da kuɗi naira dubu ɗari biyu da hamsin da biyu. Domin matan Abba Lurwanu da Aunty Zainab su ma dubu ɗari suka bada, Innaye da abokan zamanta da ƴaƴansu suka haɗa dubu hamsin da biyu.
Washe gari da safe haka aka yi hidima da Amarya da danginta, hidima ba ƴar kaɗan ba, da yake duk abinda za'a nema Baffa da Hafiz sunyi matuƙar ƙoƙari gurin tanadarsa. Ƙarfe goma da rabi Amarya da danginta da Zulai suka bar garin Faƙo.
Alƙawari Zulaikha ta ɗauka ma Kareema sai ta kaita har ɗakinta na gidan Hafiz, shi yasa ba tare da ta gama gaisawa da Iyaye da ƴan'uwanta ba ta sake bin Amarya suka koma Abuja, bayan ta faɗa ma Innaye kwanaki goma masu zuwa za ta koma Faƙon, a lokacin za tayi sati ɗaya. Kuma lokacin ne za ta tafi da Aadil su Innaye su ganshi.
********
Duk tarin abokansu da suka rufa mishi baya gurin hidimar bikin sun koma gurin ayyukansu, saboda jinkirin da aka samu wajen kai Amarya Faƙo. Yau da ya kasance Amarya ta isa gidanta bayan sallar Isha'i, Ibrahim ne kaɗai yayi mishi rakiya.
Lokacin da suka shiga gidan babu kowa sai Zulaikha. Iyaye da sukai rakiyar Amarya duk sun koma gidajensu. Ƙawayen amarya da suna jin labarin Kareema ta koma gidan Mummy suka dawo, duk ta kore su bayan ta basu kuɗin sallamar da suke yiwa ƙwa-ƙwa. A cewarta, ba za su bata wa yayanta lokaci da zancen kuɗin sayen baki ba, balle har su shiga lokacinshi da na amarya.
Ita da aka bari cire mayafinta tayi ta ƙara gyara wajen ɓangaren Amarya da yayi kyau sosai, saboda an narka dukiya wajen tsara gurin ba kaɗan ba. Ta dauko burner da humidifier duk ta jonasu da zuba abin kamshi a ciki. Gidan ya kaure da kamshi kashi-kashi. Idan ka shiga har ka rasa wanne za ka shaka.
Wajen karfe tara da rabi suka ratsa ta cikin main parlour suka shiga ɓangaren Kareema, Hafiz da Ibrahim sun sha Angon babbar shadda wagambari, fara, ta sha surfani iri ɗaya. Fuskar Hafiz sai sheƙi take yi da annuri irin na angwaye.
Lokacin da suka shiga, Zulai da Kareema na zaune a falonta da ya sha saitin wasu hadaddun leather seats ruwan madara. Hafiz ya kalli Zulai ya watsa mata harara
"Kin shiga uku da masifar sa'ido Zulai. Ke kuma zaman uban me kike yi anan bayan tun ɗazu an ce kin sallami ƙawayen Amarya?"
Ta kyalkyale da dariya, sai kuma ta ɗan kumbura fuska ta ce
"Yaya ai ni tudu uku nake ci. Ƙanwar Ango, Yayar Amarya, kuma ƙawar Amarya. Don haka kuɗin sallamar da baka biya ba ni za ka ba, idan ba haka ba daga nan har gobe Amarya baza ta buɗe maka baki da fuska ba."
Duk da ya san tsokanarsa take yi, da saurin gaske ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 40