ta ina sakwara zai ciwu da cokali?"
Ta tambayi kanta a fili tana ɗan murmushi, bismillah tayi, ta gutsuri sakwarar ta ɗebi miya ta kai bakinta.
"Uhmmm!"
Ta faɗa tana jin wani masifaffen daɗi mai barazanar tsinke mata kunnuwa.
"Allah na gode maka da ka rabo ni daga gidan Bintu. Ko babu komai daga irin tarbar da aka min anan na san in Allah ya yarda bazan rasa abinda zan ci ba."
Ta faɗa tana sake yanko ƙaton lomar sakwarar da ya daku luƙwui kamar ba da hannu aka daka ta ba, ta haɗa da miya mai yawa ta kai bakinta.
Bata san tana jin yunwa sosai ba sai da taga cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye manyan ƙullin sakwara guda biyu, duk yawan namomin da ke cikin miyan haka ta cinye tas, ta shanye ragowar miyan ta suɗe kwanon tas kafin ta kwashe su zuwa kicin.
Wanke-wanke kaɗan ta gani a cikin sink, tattare hijabinta tayi ta haɗa da nata farantan ta wanke su tas ta kife a cikin kwandon da ta gani a gurin. Goge ruwan da ya ɗan zuba tayi da mopper kafin ta fice daga cikin kicin ɗin ta nufi ɗakinta don sauke farali.
[1/30, 5:32 PM] Fareeda Abdallah: ***** *****
"Haba don Allah! Ta ina aka taɓa irin wannan rayuwa? Ace mace gandamemiyar budurwa baza ta iya tuƙe tuwon dawa luƙwui ta haɗa shi da lafiyayyiyar miyar kuka wacce ta ji daudawa ba? Ni kam ba haka nake ba, sunana Karimatu aka saka miki amma sam ba haka halina yake ba. Yanzu saboda Allah da Annabi idan Allah ya haɗa ki aure da dattijo maciyin tuwo fa? Ya za kiyi...?"
Wacce ake yiwa sababin ƙara zumɓuro baki gaba tayi ranta a ɓace ta ce
"Allah ma baya sa haka ba Hajja. Ni kam in Allah ya yarda bazan taɓa auren tsoho ba balle kuma ya kasance mai masifar son tuwo, tuwon ma ya wuce na shinkafa, ya tsallake tuwon semo, ya shallake tuwon garin surfaffen masara har sai an gangara tuwon dawa. Kuma da kike ta wannan mitar kina min sababi ca nake sadda za ki fita na tambayeki abinda kike son ci zaɓi biyu kika bani? Ke fa kika ce ko inyi miki sakwara ko tuwon dawa, da naga bazan iya tuwon dawan ba shi ne na miki sakwara. Kuma ki tambayi Mummy ki ji tun bayan fitarki da safe ban zauna ba sai da na gama haɗa miki lafiyayyiyar sakwara miyan agushi, amma da yake ke ba'a miki gwaninta duk gidannan ba wanda bai ci abincin ya jinjina min ba sai ke, kuma saboda tsabar sabo da yi tun kafin ki ɗanɗana za ki sauke min kwandon sababin da kika taho da shi daga gidan Aminiyarki Hajiya Talatuwa mai tuwo-tuwo?"
A fusace Hajja ta buɗe baki za ta mayar mata da martani, sai ga Zulaikha ta shigo cikin falon bakinta ɗauke da siririyar sallama. Ta yi wankanta tsaf! Ta yi kwalliya cikin ɗaya daga dogayen rigunan da Mashkura ta bata. Duk da fuskarta fayau yake babu wani ɗige-ɗige ko jagira sai powder kaɗai, ba ƙaramin kyau tayi a cikin doguwar rigar ba, kasancewarta farar fata, rigar kuma baƙa ce. Abu ɗaya da ya ɗan ɓata kwalliyar tata shi ne, bayan ɗankwalin rigar da ta yafa a kanta, sai ta kawo wani hijabi kuma ta yafo ta bayanta don ya rufe tudun mazaunanta.
"Sannunku da hutawa! Ina yininku?"
Ta gaishe su da sanyin murya, da ɗan murmushi a fuskarta. Amma kallo ɗaya za ayi mata a fahimci tsoro a fuskarta, domin hayaniyarsu ne ya fito da ita. Da kamar ma baza ta fito ba, sai kuma ta tuna tana wanka ta ji motsin an buɗe ƙofar ɗakinta an shiga, daga bisani kuma aka fita. Wannan shi ne dalilin da yasa ta fito falon, a tunaninta ko Mummy ke son ganinta.
Tun kafin ta fito, duk su biyun Mummy ta riga ta yi musu bayanin wacece ita. Ƙosawa da ɗokin yin tozali da abokiyar hira da Karima take tunanin ta samu yasa ta gaza haƙuri har sai da ta leƙa ɗakin da aka sauki Zulaikha. Da ta fahimci tana wanka ne yasa ta fita ta shige ɗakinta.
Dama ɗakuna uku da suke jere a ɓangaren ɗaya na Imam ne, ɗaya na Karima, ɗayan kuma shi ne aka sauki Zulaikha a ciki.
Ita ma sababin Hajja ne bayan ta buɗe kular abincinta ta ga sakwara saɓanin Tuwon dawa da tayi tsammani shi yasa ta fitowa.
Duk su biyun, a tare suka mayar ma da Zulaikha martanin murmushinta. Karima ta buɗe baki za tayi magana Hajja ta riga ta cewa
"Zulaihatu ko? Amma fa sai dai kiyi haƙuri, ni kam gaskiya Zulai zan dinga ce miki. Zulaihatu yayi min tsawo da yawa..."
"Hajja ba fa sunanta Zulaihatu ba, Zulaikha, haka Mummy ta ce. Don Allah kar ki wani ɓata mata suna da wani Zulai kamar wata tsohuwa."
Ƙanƙance idanu Hajja tayi cikin sababi ta ce
"To ina ruwanki ƴar'iya? Sunanki ko na ta? Ƴanmata akwai wani damuwa ne idan na kira ki da Zulai?"
"A'a! Babu wata damuwa Hajja. A gidanmu ma haka wasu suke kira na."
Ta amsa tana ɗan dariya, don izuwa yanzu diramar jika da kakar ya fara daina ba ta tsoro sai dariya.
"To kin dai ji, aka ce miki kowa irinki ne, ga cikakken sunanki na musulunci Karimatu amma kika yanke shi wai ke nan gayu kika mayar da shi Karima. Ita Zulai ba haka take ba, da ganinta ƴar duma-duma yarinyar kirki ce. Zo nan ki zauna kusa da ni kin ji Zulai? Ina miki maraba da shigowa cikin ahalin Marigayi Modibo, alkhairin da ke tare da junanmu Allah ya sada mu da shi, sharrin da ke tattare da junanmu Allah ya kare mu ya yaye mana."
"Ameen ya Allah"
Zulaikha da Karima suka amsa addu'ar gaba ɗaya.
"Na gode Hajja."
Zulaikha ta ƙara da faɗin haka, fuskarta cike taf da murmushi. Kusa da ƙafafun Hajja ta ƙarasa ta zauna akan kafet kamar yadda ta umarce ta, lokaci guda kuma tana satar kallon Karima, wacce take zaune can gefe ɗaya tana murmushi.
"Ke fa Zulaikha da alamun kin samu shiga a gurin Hajja. Ai kam ina tausaya miki, domin samun shiga a gurin Hajja daidai yake da tsayuwar..."
"Uwar tawa kike yiwa sharri Mamana?"
Mummy da take fitowa daga cikin ɗaki ta katse maganar da Karima take yi.
"A'a toh! Ai gara ki ji da kunnuwanki kuma ki gani da idanuwanki Saudatu. Yau fa tunda na kushe wannan gantalallen sakwarar da take ta tutiyar ta daɗe tana aikinsa ai ni kam na shiga uku. Gaskiya ce kuma sai na faɗa, sakwara ce dai ba ita na so ayi min ba, tuwon dawa na so miyar kuka ke kuma baki iya ba."
Zulaikha da karambani, kamar an saka ta, a hankali ta buɗe kulolin abincin Hajja da suke ajiye akan ɗan ƙaramin teburin cin abinci a gabanta. Ɗaurin sakwarar guda ɗaya ta saka mata, ta zuba miya da namomin a gefe ɗaya, ta miƙa mata farantin, har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace ba.
"Ki daure ki ci sakwarar Hajja. Ta yi daɗi sosai Wlh, kuma ta daku luƙwui, miyar ma ta yi daɗi kamar za ta tsinke kunne. Anjima da yamma idan akwai garin dawar ni sai inyi miki tuwon, in dai za ki iya cin girkin ƴan ƙauye ni kuwa zan tuƙa miki tuwon da duk kalar miyar yauƙin da kike so."
Da idanuwan burgewa suke kallonta gaba ɗaya su ukun. Hajja bata tankwaɓe ƙoƙarinta ba, farantin da ta zuba mata sakwarar ta karɓa, bayan ta yi bismillah ta yanki loma guda ta kai bakinta. A lokaci guda kuma tana tauna sakwarar tana cewa
"Na gode Zulai. Ni ko me zai hana ni cin girkin ƴan ƙauye? Nima fa daga can nake. Ba ma haka ba, duk wani ɗan birni da za kiga yana boƙara idan kika binciki tarihinshi tun tale-tale kakanninshi ƙauyawa ne na asali."
Ita kuwa Mummy cewa tayi
"Da gaske kike yi Zulaikha? Kin iya tuƙa tuwon dawa da ko wace kalar miya ta yauƙi?"
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannayenta.
"Eh Mummy. Kin san mu mutanen ƙauye ba kasafai muka cika yin kalolin abinci na ƴan birni ba, ko da yaushe an fi gane ma tuwo, sai kuma shinkafa ita ma jefi-jefi. Duk ranar girkin Innaye kashi tamanin cikin ɗari na aikin ni nake yi, in dai ɓangaren abincin gargajiya ne na iya su gwargwadon hali..."
"Tubarakallahu ma sha Allah! Ke kuwa Zulai kin huta, Allah ya saka ma Innaye da alkhairi. Babu ruwanta da fargaban aurar da ke ga ko wane irin miji. Takwara don Allah a sauke gwalli da iyayi a koyi kalolin girke-girken gargajiya don gudun gorin miji a gaba."
Hajja ta ƙarasa maganar idanunta na kan Karima.
"Ni dai kam yau na bani da ke Hajja. Tunda dai na ƙi miki tuwo kushe ni kawai kike yi, kiyi haƙuri mana tunda ga ƙanwata Zulaikha za tayi miki anjima. To ya kika ji sakwarar? Ta yi daɗi sosai ko?"
Sai da ta gyatsine fuska kamar wata ƙaramar yarinya kafin ta amsa da
"Ba laifi dai. Ta ɗan yi. Zulai ƙaro min rabin malmala in ƙarasa da miyar nan kar ta min fatalwa na ƙi cin sakwara da yawa."
A tare Karima da Zulaikha suka tuntsure da dariya. Ita kuwa Mummy ɗan murmushi kawai tayi, zuciyarta cike da farin cikin ganin yadda aɗan ƙanƙanin lokaci sabo ya shiga tsakanin Zulaikha da iyalanta. Tabbas kamar yadda Hafiz ya ce, da alamun baza'a samu matsala da yarinyar ba.
Ƙanƙance idanu Hajja tayi tana harararsu duk su biyun, a ɗan fusace ta ce
"To miye kuma abin dariya? Ko don kawai an ga na daure tashin zuciya ina cuccusawa? To tunda haka ne ma ke Zulai bar shi kawai na fasa ƙarin..."
"Allah ya baki haƙuri Hajja. Ba da ke muke dariya ba fa."
Zulaikha ta faɗa tana danne dariyar da ke sake tuƙo ta. Ta rasa dalilin da yasa, bayan dariyar diramar Hajja haka kawai take jin zuciyarta yalwace da farin ciki. Duk wani ƙunci da damuwar Hafiz da mahaukaciyar matarsa ta aje su gefe ɗaya can ƙarshen zuciyarta.
Bayan farkawarta aɗan gajeren barcin da ya kwashe ta ɗazu, ita da kanta tayi ma kanta karatun ta nutsu, addu'a mai tsawo tayi kan Allah ya tabbatar mata da duk abinda yafi zama mafificin alkhairi a rayuwarta. Damuwa, ƙunci, tunani da baƙin cikin Hafiz ta sama musu matsuguni can ƙarshen saƙon zuciyarta tayi musu mummunan ɓoyo. Ta sa a ranta lallai za ta fuskanci gaba, ga gaban kuma da alamun za ta zo mata da alkhairai masu yawa da farin ciki.
Nan falo suka bararraje suna hira da dariya, Zulaikha da ba ta da baƙunta sai labarin ƙauye take basu suna dariya. Ita ma Hajja da yake ƙuruciyar ƙauye ce kafin aurenta da marigayi Modibo ya tsallako da su cikin birni har suka hayayyafa sai labarin ƙauye take ba su, irinna zamaninsu da can.
Ko da lokacin ɗora tuwon da za ta yima Hajja yayi, ita da Karima suka shige kicin ɗin, sai dariyar maganar Hajja suke yi da take ta jaddada ma Zulaikha kar ta kuskura ta bar ma Karima tuƙa tuwonta.
"Bata iya komai ba, duk sadda tayi tuwo haka za ki ji shi duk gudaji. Sai ki rasa shin ido rufe take tuƙa tuwon ko kuwa ya take yi, kamar dai ba mace ba."
Mamaki ne ya kama Karima ganin yadda Zulaikha ke aikin tuwon cike da ƙwarewa da gwanancewa, kamar wacce tayi zaman birni, kayan miya da daddawa da kayan ƙamshi sai da ta soya su sama-sama sannan ta tsayar da sanwan ruwan miyan. Ta kasa haƙuri, har sai da ta tambayeta shekarunta nawa? Duk da Zulan tana da girman jiki fuskarta kawai za'a kalla a ga zallar ƙuruciya.
"Shekaruna goma sha takwas Aunty Karima."
Ta amsa tana dariya.
"Ikon Allah! Amma gaskiya kin burge ni, yanzu kina nufin duk su dambu, fate, burabusko, ɗanwake, da sauran girke-girken gargajiya masu wahalar nan duk kin iya?"
"Eh! Kin ga duk da Yaya Hafiz yana ƙoƙarin kai mana kayan abincin birni Innaye da Baffa sun fi sabawa da kalolin abincin gargajiya. Shi yasa na fi ƙwarewa a dafe-dafen irin su."
Ta sake amsawa har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba.
"To gaskiya dole za mu koyar da juna, amfanin zaman tare cuɗe ni ne in cuɗe ka. Kar ki wani ji kunya ko nauyi na kin ji? Duk abinda kike son koya daga tsarin rayuwar birni ki faɗa min, ni kuma zan koyar da ke daidai gwargwado. Duk da dai lokacina na zaman gida ragagge ne, domin ni ma'aikaciyar jinya ce a asibiti. Amma ya zama dole in mayar da hankali in koyi girki a gurinki. Kema kuma in sha Allah zan koyar da ke ire-iren girkin birni da na iya, da sauran duk abubuwan da kike buƙata, in sha Allah"
"Allahu yasha Aunty Karima, ai kam na gode. Na ji daɗi ƙwarai."
Cikin ƙanƙanin lokaci sabo mai girma ya shiga tsakaninsu, kamar dama can sun daɗe da sanin juna. Ko da aka gama tuwon, duk yadda Karima ta tsani tuwo musamman na dawa wannan kam sai da ta ci mai ɗan dama. Saboda yadda miyan take ta ƙamshi, ga kuma kyawu da tayi sosai a idanunta. Ta sha mamaki ƙwarai yadda ta ji tuwon ya tuƙu sumul babu gudaji, kamar ba a gabanta aka tuƙa ba.
Albarka kam Zulaikha ta sha shi a bakin Hajja da Mummy babu iyaka. Tun tana amsawa da baki har sai da ta koma sakin murmushi kawai.
A gurin Karima ta samu aron cajar da ta jona wayarta, jikinta na rawa, wayar tana yin 10% ta cire ta lalubo lambar Innaye ta danna mata kira.
"Auta? Auta ke ce? Auta kina ji na? Ina fatan dai kina nan lafiya babu abinda ya same ki? Duk da Hafizu ya rantse haɗe da tabbatar min lafiyarki ƙalau rashin jin ki ta wayar tarho ya saka ni cikin wasu-wasi. Ina fatan babu abinda Fatima tayi miki ko kuma tayi yunƙurin aikata miki?"
Tambayoyin da Innaye ta dinga jera mata kenan da bayyanannen tashin hankali a muryarta.
Idanunta ciccike da hawaye ta nemi guri ta zauna a gefen gadon ɗakin da aka sauke ta, sannan ta amsa Innaye da lafiyarta ƙalau. Kamar za ta ba Innaye labarin abinda ya faru, sai kuma ta tuna alƙawarin da ta ɗaukar ma Mummy cewa baza ta sanar ma su Baffa Yaya Hafiz ya ɗauke ta daga gidanshi ba.
Kuma ko ba haka ba ma a yadda ta fara jin daɗin zaman gidan Mummy baza ta so a raba ta da shi cikin ɗan lokaci haka ba. Ta sani ko da ta koma ƙauye tabbas tsugune ne bata ƙare ba, to da wannan dalilin gara kawai ta bi tsarin Hafiz har zuwa sadda za ta ga iya gudun ruwansa.
Hira sosai suka sha da Innaye, duk yadda Innayen take ta bugun ruwan cikinta don ta ji ko da wata damuwa daga ɓangaren Hafiz ko Bintu sam Zulaikha ta ƙi faɗa mata komai.
"Kin san halina fa Innaye. Idan mutum ba shiga harkata yayi ba nima bana shiga tasa. Kuma batun abinci Yaya shi da kanshi ya jaddada ma Baba Rabi lallai kar ta barni da yunwa, to har yanzu dai gaskiya ban ga wata matsala da za ta takurani ba. Kin san idan da matsala ma da kaina zan kira in faɗa miki."
Ire-iren kalaman da tayi amfani da su kenan ta kwantar ma da Innaye hankali.
Har sai da kuɗin cikin wayar ya ƙare, Innaye ta kira ita ma nata kuɗin suka ƙare, sannan suka haƙura da magana, ta mayar da wayar a caji tana jin yadda zuciyarta ya ƙara cika da matsanancin farin ciki.
[1/31, 5:39 PM] Fareeda Abdallah: Washe gari, da yake Karima aikin dare take da shi. Haka kawai ta ƙirƙiri fita ita da Zulaikha, ba don komai ba sai don kawai ta zagaya da ita taga cikin garin Abuja.
Imam, yaro ɗan shekara shida da tun jiya ya dawo daga makaranta daf da magriba ya tarar da Zulaikha a gidan ya maƙale mata. Duk da ba wata shahararriyar hira ke gudana a tsakaninsu ba, saboda shi turanci ya fi kama bakinsa fiye da hausa, ita kuwa Zulaikha ba turanci. Kasancewarta wacce bata iya ɓoye-ɓoye ba, idan ya takura mata da dogon turanci ba wani kunya a tare da ita ko a gaban su Mummy ne ba ta jin kunyar ce mishi
"Hey Boy! No English."
Da yake su Mummy wayayyu ne sai suyi kamar basu ji me ta ce ba, shi kuma da yake yana da son baƙi haka zai kwaɓo hausar a jagwalgwale, ita kuma ta daddage ta bashi amsa yadda ta fahimta ba tare da nuna gundurarwa ba, domin Allah ya yi ta da son yara.
A haka dai duk inda Zulaikha ta saka ƙafa nan yake mayar da tasa, duk inda ta zauna a jikinta zai raɓu ya zauna. Aikin gida da aka bashi daga makaranta ma takardun ya kwaso gaba ɗaya ya zube a gabanta, yana yi tana kallo duk da ba ta fahimtar abinda yake rubutawa. Ba ita ta samu hutu ba, sai da yayi barci aka kai shi ɗakinsa.
Da sassafen ranar ya ma ƙi yarda Karima tayi mishi shirin makaranta, sai tarewa sukai su biyun a ɗakinshi, Zulaikha tana shirya shi Karima tana harhaɗa mishi abubuwan da yake tafiya da su makaranta. Ƙarfe takwas saura minti ashirin motar makarantarsu tazo har ƙofar gida ta ɗauke shi, kamar zaiyi kuka haka yake ta jaddada ma Zulaikha lallai ta jira shi ya dawo, kar ta tafi, ya yi alƙawarin zai kawo mata tsaraba.
Da dariya a fuskarta take jaddada mishi baza ta tafi ba, za ta jira shi ya dawo. Kuma za tayi ta zama a gidansu har sai ya gaji da ganinta.
Ya shige cikin mota yana ɗaga mata hannu tana ɗaga masa har sai da motar ya ɓace ma ganinta sannan ta shiga gida.
Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safe suka gama shiryawa ita da Karima, ta kwashe su a mota suka fice kasuwa yin siyayyan abubuwan gida da basu da shi.
Gurin shirin Zulaikha ne dai haka aka sha dirama da ita gwanin ban dariya, daƙyar ta iya ajiye babban hijabinta ta karɓi ɗan madaidaicin gyalen da Karima take miƙa mata ta saka. Shi ma kafin ta saka sai da Hajja ta ishe ta da gorin ko ita da take tsohuwa baza ta zumbula wannan ƙaton hijabin ba idan za ta fita.
"Kin ga Zulai ki kwantar da hankalinki, nan fa binni ne ba ƙauye ba. Idan kika ji inda ake rayuwa babu ruwan wani da wani to binni kenan. A ƙauye ne suke da masifaffen sa'ido da abu kaɗan ko ba na saɓon Allah bane sun dinga yamaɗiɗi da ke kenan. Bayan wannan zumbuleliyar riga da kika sa saboda Allah menene amfanin sake zumbula hijabi kuma? Ai wannan mayafin da takwara ta baki shi ne daidai da kwalliyarki Zulai. Ko ba kya so Allah yayi miki gyaɗar dogo ki samo mana wani sabon miji ne ɗan binni?"
Ta tambayeta da dukkan gaskiyarta, saboda yadda Hafiz ya faɗa ma Mummy saura sati uku auren Zulaikha mijin ya ce ya fasa haka ta faɗa ma Hajja.
Bata iya cewa komai ba, sai ɗan dariya kawai tayi, ta karɓi mayafin ta yafa tana ta jero istigfari a zuciyarta. Domin ba ta jin za ta iya kware ma ɗan'uwanta baya ta hanyar tona asirin auren da yake tsakaninta da shi. A idanun su Mummy da ta lura sun yarda da shi ɗari bisa ɗari.
Ko da ganin yadda take ta jan gyalen tana ƙara tale shi don ya ƙara sauka mata za'a san bata saba sakawa ba. Ita kuwa Karima me za tayi mata in ba dariya ba
"Kin san Allah? Za ma ki ware ne, sai yanzu na ƙara tabbatar da ina da babban aiki a gaba na. Har na ji na fara addu'ar Allah yasa ko wata biyu ne kacal kiyi a gidanmu, in sha Allah zan mayar da ke ƴar gayu fiye da yadda ba'a zato. Shi fa tsoron Allah a zuciya yake, in dai ba tsiraici mace za ta bayyana ba, babu wani laifi ki saka yalwataccen suturarki sannan ki yafa ɗan siririn gyale. Don Allah ki saki jikinki kin ji ƙanwata?"
"Toh Aunty."
Ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai har suka isa kasuwar ta kasa sakin jikinta yadda ya kamata.
Abu ɗaya da yayi ma Zulaikha daɗi shi ne ganin kasuwar ma a birnance ne, ba irin kasuwarsu bane na ƙauye da za aga mutane cunkus ana yamutsi tsakanin maza da mata. A taƙaice ma, duk siyayyar da suka yi a cikin manyan kantuna ne, nan taga yadda aka san daraja da kimar kayan miya. A babban kanti anyi packaging ɗin tumaturi irin manyan nan a leda anyi sealing ɗin shi, su tattasai ma da tarugu da albasa ma duk sun samu muƙami na musamman, ba kamar yadda take ganinsu a wulaƙance a ƙauyensu ba.
Basu bar cikin kasuwa ba sai ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Kuma maimakon su nufi gida, juya akalar motar Karima tayi suka nufi gidan Aminiyarta. Sunanta Hibbah uwar gayu. Bayan sun gaisa da mahaifiyar Hibbah wacce ƴaƴanta ke kira da Mama, kai tsaye ɗakin Hibbah suka shige, kan gadonta suka bararraje suna hira irinta aminan da akwai shaƙuwa mai girma a tsakaninsu.
Ita kuwa Zulaikha banɗaki ta tambaya aka nuna mata, ta ajiye mayafin jikinta ta shige da sauri saboda fitsarin da ya matse ta. Hibbah ta bi ta da kallo ƙasa-ƙasa. Sai da ta shige ta rufe ƙofa sannan Hibba ta mayar da idanunta kan Karima, da salon tsegumi ta ce
"Ina kika samo kyakkyawar yarinya haka mai ƙira irinta Hadiza gabon? Ke kin ga wasu manyan kaya da take ɗauke da su a bayanta kuwa?"
A tare duk su biyun suka kwashe da dariya. Kafin Karima tayi magana aka yi sallama a ƙofar ɗakin, bayan sun amsa mai aikin gidan ta shigo da babban faranti a hannunta ɗauke da kulolin abinci da abin sha. Gefe ɗaya ta ajiye tayi musu sallama ta fice daga ɗakin.
Ƙofar banɗakin da Zulaikha ke ciki Karima ta kalla, sannan ta mayar da hankalinta kan Hibbah ta ce
"Kin shiga uku da sa'ido Ƙawata. Ƴar danginmu ce tazo daga ƙauye, kuma za ta ɗan kwana biyu a gidanmu. Kin san me yasa na zo da ita gurinki?"
Girgiza kai Hibba tayi, a zuciyarta take mamakin yadda kyakkyawar yarinya haka mai sanyin kyau za'a ce daga ƙauye take. Irin wannan da a birni take kuma ta san kanta ai ba ƙaramin gwarama za ta haɗa na samari ba. Shi yasa fa wasu mazan ke cewa tsantsar kyawun mace na gurin ƴar ƙauye, matan birni mafiyawancinsu gayu ne kawai da ƙyale-ƙyale.
Ƙara rage murya Karima tayi, sannan ta cigaba da cewa
"So nake ki wayar min da ita a cikin kwanaki ƙalilan, ki koya mata salo-salo na gayu don Allah. Kin ga waɗannan mazaunan da kika hango a bayanta? Baki ga komai ba Wlh, sai yau da na shiga ɗakinta da sassafe, na ganta sanye da doguwar rigar barci da ya ɗan kama ta. Uhmmm! Ke dai abin ba'a cewa komai, ƙiran jiki ne da ita mai kyau Wlh! Ga wani shape da take ɗauke da shi abun sha'awa, ta bakinki dai kamar Hadiza gabon. Duk wannan ƙibar na ta sam ba ta da tumbi..."
Fitowar Zulaikha daga banɗaki yasa suka bar maganarta da suke yi suka shiga wata hirar.
Tana ɗan goge ruwan da ke kwance a fuskarta da gefen ɗankwali tace ma Karima
"Aunty ni fa nayi alwala ne, a taimaka min da Hijabi inyi sallah."
"Ba kya jin yunwa Zulaikha? Ai da kin bar sallar mu fara cin abinci, idan mun gama sai muyi sallah a tsanake."
Sai da Karima tayi maganar, sannan Zulaikha ta lura da kulolin abinci da aka ajiye a tsakar ɗakin. Ga kuma Jug ɗin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 40