Share this page
ta ci babu. A Lokaci guda kuma tana shan alwashin kaloli mabanbanta na cin uban Karima da za suyi ita da Bintu gobe a ofis idan an wayi gari. "Kuga min shegiyar yarinya sumumu-kasau ashe ƙasungurmar munafuka ce? Ko da yake ai maganin Bintun ma da ta sakarwa uwarta Hajiya Sauda fuska, ai ga sakayyar sakin fuska nan ta fara gani. Tana niyyar wanke zuƙeƙiyar ɗiyarta ta bashi ya aura." Tana wannan masifar har bata san lokacin da motar Hafiz ya bar harabar asibitin ba. Waigawa kawai tayi taga inda motarsa take ba shi sai filin gurin. Ta ja tsaki ya fi sau hamsin, duk yadda mahaifiyarta take ta biyo bayan kiran wayarta ta kasa ɗauka. Duk da magana ce mai muhimmanci suke yi. Ta sani a yadda take fusacen nan ko ta ɗauka baza ta iya mayar da hankali su cigaba da magana ta nutsuwa ba. A ƙarshe sai kashe wayar tayi, ta figi jakarta da wayar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin asibitin. A zuciyarta take ƙudurta yadda za ta ci uban duk wata nurse budurwa da ta tarar da ita a bakin aiki a wannan daren. 'Munafukai, Algungumai, duk bakinsu ɗaya matsiyata. Ashe bayan kwarkwasa da gwalli da suke yi ma Likitoci maza har mazajen likitoci mata basu bari ba. Duk za su ci ubansu ɗaya bayan ɗaya.' Da wannan ƙudurin ta ƙarasa cikin asibitin zuciyarta cike da addu'ar Allah ya haɗa da ƴanmatan nurses ɗin asibitin, musamman waɗanda ta san sun fi shiri da Karima. ****** Wannan gwaggwaɓar canjin bazata da aka samu bagatatan a cikin tafiyar soyayyar da a farko shi kaɗai yake kiɗansa kuma yake rawarsa ba ƙaramin faranta masa zuciya yai ba. Tuni ya manta da Bintu, ɓacin ran da ta cusa mishi da duk wani abu da ya shafe ta. Ba ma kamar yadda minti ɗaya biyu a hirar da suka gabatar da Karima sai ta ambaci Innaye, ko kuma ta ambaci kirkin ƴan'uwansa. A cikin hirarsu har ta bashi labarin haɗuwarta na farko da Innaye, da yadda jininsu ya haɗu farat ɗaya. Amma ko da wasa bata bashi labarin yadda Bintu ta wulaƙanta Innaye a wancan lokacin ba saboda gudun tayar da husuma tsakanin ma'aurata. Sun yi hira na awa ɗaya cif bayan isarsu gidan Momy Sauda. Kamar bazai tafi ba, sai da Momyn ta kira shi a waya tayi mishi tatas kan cewa baza ta yarda da irin wannan rashin adalcin tun yanzu ba. "Allah ya huci zuciyarki Mummy. Zan tafi yanzu, sai da safe. Gobe idan Allah ya kaimu da yamma zan zo..." "Kar ma ka fara Hafiz, hira sau biyu a sati ya isa. Ga waya nan ku dinga magana, shi ɗin ma ban yarda ya wuce sau uku a rana ba. Ina fatan ka fahimce ni?" "Na fahimta Mummy." Ya amsa a ladabce. Har ya kama hanya zai fita ta kira shi. "Da alama dai kun daidaita da ƙanwartaka. Zan tuntuɓeta yau da dare saboda gudun yin kitso da ƙwarƙwata. Idan ta tabbatar min da amincewarta kayi ƙoƙarin zuwa Faƙo cikin satinnan ka sanar da iyayenka halin da ake ciki, idan sun shirya ko zuwa watan gobe sai ka turo kawai ayi mai gaba ɗaya a wuce gurin. Nima nan zan sanar da iyayenta maza, tunda an fahimci juna kuma da sanayya ta ko wane ɓangare to gaskiya babu wani amfanin ɓata lokaci. Ko kana da wani shiri ne da kake buƙatar jinkiri...?" "Ba ni da wani shiri Mummy." Ya katse ta da matsanancin farin ciki bayyane a fuskarsa. "Ai ni Wallahi ko gobe ne a shirye nake a ɗaura auren kawai a wuce gurin. Na gode Mummy. Allah ya ƙara girma." "Amin ya rabb! To ina fatan Bintu dai ta sani?" Ta sake jefa mishi tambayar, tare da ƙure shi da kallo tana ƙoƙarin karantar yanayinsa. Ɗan shiru yayi yana sosa ƙeya, amma har lokacin fara'ar da ke fuskarsa bata ɓace ba. Can kuma sai ya ce "Gaskiya bata sani ba Mummy... Amma zan faɗa mata. A daren nan ma in sha Allah zan sanar da ita. Gobe idan naje Faƙo sai in sanar da su Baffa." "To madallah! Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama mafificin alkhairi. Ni dai don Allah ina roƙonka alfarma... A matsayinka na miji, kasan irin kalaman da za kayi amfani da su gurin faɗa ma Bintu al'amarin. Tsakani da Allah kishiya babu daɗi, amma tunda umarnin Allah S.W.T ne ba mu da yadda za muyi. Ka bi ta sannu a hankali, cikin tausasan lafuzza da ƙanƙan da kai. Sannan ka nusar da ita auro Karima ba shi ke nufin soyayyarta ya ragu a zuciyarka ba..." A matsayinta na Babba, haka ta sake ɓata wasu lokutan tana nusar da shi irin tausasan hanyoyin da zai bi wajen sanar ma Bintu zai auri Karima. Bai bar gidan Mummy ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare. Zuciyarsa cike taf da farin ciki. Yana tuƙi a hanyarsa ta komawa gida sai waƙe-waƙe yake saboda murna da yayi masa yawa. Ya ma rasa wa ya kamata ya kira ya fara yi ma wannan daddaɗan albishir ɗin? Har ya ɗaga waya zai kira Zulai, sai ya ga dare yayi sosai. Sai kawai ya buge da kiran Ibrahim abokinsa ɗan gidan Abba Lurwanu yayi mishi albishir. Kamar yadda ya zata, Ibrahim ɗin yayi murna sosai da sosai. Don yana ɗaya daga cikin ƴan adawar Bintu, masu nusar da shi tun a baya ire-iren kura-kuran da Bintun ke aikatawa amma sam idonsa ya rufe, ba ya ji ba ya gani saboda soyayya da ya rufe masa idanu. "Shi kenan! Ka ga yanzu za'ayi balancing, idan su Aunty Balira sun zo za su samu gurin da za a tarbe su da haba-haba babu wulaƙanci, tozarci, ko kyara." "Ƙwarai kuwa Ibbu" Suna magana a waya Ibrahim ɗin yana ƙara bashi shawara kan kar ya kuskura ya haɗa Bintu da Karima gida ɗaya har ya isa cikin gidanshi. A lokacin sha biyu saura ƴan mintuna. Sallama yayi ma Ibrahim da cewar za su haɗu bayan ya dawo Faƙo su ƙarasa maganar ya katse wayarsa. Yana shiga cikin falo ya tarar da Bintu zaune a kan kujera, idanunta ƙyam akan ƙofar shiga cikin falon tana jiran ganin ta inda zai ɓullo. Saɓanin ɗazu da ya barta sanye da kayan barci, yanzu ta ci kwalliya ne cikin wata ƴar ɓingilar rigar mama da wata yaloluwar ɗan kamfai. Fuskarta da kwalliya raɗau kamar wacce take shirin zuwa gurin perty. Ko kusa baiyi mamakin ganinta ido biyu ba, don yana daga cikin ɗabi'arta da ke faranta mishi rai duk inda ya je in dai yana garin Abuja to Bintu ba ta taɓa kwanciya tayi barci sai ta jira ganin dawowarsa gidan lafiya. Abu ɗaya da ya ɗan bashi mamaki shi ne tattausan murmushin da ta fara watso mishi tun daga inda take zaune, sannan ta miƙe tsaye cikin yauƙi da lanƙwasa, ta fara tafiyar mage tana wani yayyarfe yatsu tana karkaɗa mishi ƙirji, lokaci guda tana haɗawa da fari da idanu har ta ƙarasa inda yake tsaye ƙyam yana kallonta. Iya duniya aka ce ya fi iya mota, kamar dai ba Bintu ne suka rabu tana kuka shi kuma ya fita da ɓacin rai mai tsanani ba. Hannu ya buɗe mata yana mayar mata da martanin murmushi, ita kuma a slow motion ta shige cikin ƙirjinsa. A tare duk su biyun suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. Basu tsaya a nan ba, kamar mayunwata haka suka kamo bakin juna suka fara tsotsa tamkar sun samu alawa. Tun daga nan bakin ƙofa, al'amura suka fara kankama, duk su biyun suka watsar da fushi da ɓacin ran juna suka cigaba da ƙoƙarin faranta rayukansu. Daga bisani dai can-cak Hafiz ya ɗauki Bintu suka haura sama. ******* Hafiz ya riga ya karanci Bintu kamar yunwar cikinsa, ya sani tunda tayi alƙawarin yaye Aadil a washe garin ranar asabar, babu abinda zai sa ta fasa aniyarta. Ya kuma sani tun da ta ambaci Ummanta ne za ta yaye shi, to tabbas gurin Ummanta za ta kai shi sai dai duk abinda zaiyi ya daɗe baiyi ba. Da wannan dalilin yasa shi gwada mata babba babba ne. Kuma wanda ya riga ta kwana dole ya riga ta tashi, duk sammakonta, shi a tafe ya kwana. Suna idar da sallar asubah a masallaci, ko da ya koma gida ya tarar da ita har ta idar da sallah ta koma barci. Da wannan damar yayi amfani gurin aiwatar da shirinsa a gurguje, ko da ya shiga ɗakin Aadil, ga manyan jakunkuna nan har guda uku ta shaƙe da kayan sakawarshi da duk wasu abubuwan buƙatarsa. Don haka ɗauka kawai yayi ya fice da su ya zuba a boot ɗin motarsa. Ɗakinsu ya koma inda Aadil ɗin ke kwance can gefe guda a gadonsa yana barci cikin nutsuwa. Bismillah yayi sannan yasa hannu a nutse ya ɗago yaron ya rungume a ƙirjinsa yana ɗan jijjiga shi don kar ya farka. Saɗaf-saɗaf ya fice daga ɗakin don kar ya tashi Bintu. Kuma wani ikon Allah shi ne duk yadda ta kasance ba ta da nauyin barci har Hafiz ya samu nasarar ficewa daga gidan Bintu ko ƙarar motarsa bata ji ba. Sai da ya fara miƙar hanya sosai sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Innaye, bayan sun gaisa, ya sanar da ita ga shi nan ya kamo hanyar zuwa Faƙo, kuma tafe yake da Aadil za ta yaye shi a can. "Ita Fatiman da hankalinta da nutsuwarta ta damƙa maka yaron da cewa ka kawo shi in yaye muku shi a nan?" Tambayar farko da Innaye ta fara yi mishi kenan. Har ya yi niyyar yanko ƙarya ya faɗa mata, sai kuma ya yanke shawarar gara ya faɗa mata gaskiya kawai, saboda gudun abinda zai je ya zo. "A'a Innaye! A matsayina na ubansa ni ne kawai nayi ra'ayin in kawo shi gurinki mahaifiyata ki yaye min shi..." "Bazan karɓe shi ba." Ta katse shi cikin faɗa tun kafin ya aje numfashin maganarsa. Ta cigaba da magana muryarta na rawa kamar za ta saka kuka. "Yi sauri ka mayar mata da ɗanta. Idan ba haka ba Wallahi ko ka zo da shi wahalar banza kawai za ka yi don sai ka koma mata da shi." Ta ja numfashi sannan ta cigaba da cewa "So kake in karɓi ɗan ta ta zo ta tozarta ni a cikin jama'a sannan ta ɗauki ɗanta? Ita da kanta Bintun da take babba yaushe har ta iya sakin jiki tayi rayuwa a cikinmu ƙauyawa balle har tayi kuskuren bari ɗanta ƙwallin ƙwal ya rayu da mu? Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Mayar mata da ɗanta, in da rabon mu rayu da ƴaƴan binni zan rayu da na Zulai, na san Kamalu ko kyauta na ce ina so ya bani ɗansa bazai hana ni ba..." Tsananin zafi da raɗaɗin da maganganun Innaye suka yi masa yasa bai san sa'adda ya katse wayarsa ba. Gangarawa gefen titi yayi ya faka motar. Ya daɗe cikin shiru, zuciyarsa ba abinda take yi sai tafarfasa. Idanuwannsa ciccike da hawaye saboda irin baƙaƙen maganganun da Innaye ta yayyaɓa masa. Lokaci bayan lokaci yana waigawa kujerar baya ya kalli Aadil da yake kwance a ɗan gadonsa na cikin mota, har wannan lokacin barcinsa yake yi hankalinshi kwance. 'Yanzu shi kenan Bintu ta gama cin galaba a kanshi? A matsayinshi na miji bai da iko da gida da iyalinshi sai yadda Bintu ta tsara ko ba ya so haka za ayi? Yanzu yadda ya ɗauko Aadil haka zai mayar mata da shi yana ji yana gani sai dai ta kai shi gurin Ummanta?" Bai taɓa shiga matsananciyar da-na sanin biye ma Bintu da yai ta yi irinna yau ba. Ba ma da na sanin biye mata ba, a yau har da na sanin aurenta ya yi. Wane irin zamantakewa ne ace ƴan'uwa da iyayen miji ba su da ikon zuwa gidanshi su sakata su wala yadda suke so? "Ya hayyu ya ƙayyum! Bi rahmatika astageethu, aslihlee sha'anee kullah, wala takilnee ɗarfata ayn" Ya faɗa a fili idanunsa a lumshe, zuciyarsa cike da sakankancewa da neman agaji. Ya daɗe sosai yana maimaita addu'ar, har zuwa wani lokaci sannan ya buɗe idanunsa da suka canja launi zuwa jajaye. Amma a maimakon ya cigaba da tafiya da motar hanyar da zai fice daga Abuja, revers yayi, ya miƙe hanyar komawa zuwa cikin gari, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan. ****** ****** A karo na saba'in da biyu ta ɗaga waya ta danna kiran lambar Hafiz, amma wani abin takaici shi ne da kiran ya fara alamun zaiyi ringing, sai ya katse, sai su rubuta mata User busy. Bisa ga dukkan alamu Hafiz dai kulle lambarta yayi don kar ta same shi a waya. Haushi da baƙin ciki yasa tayi cilli da wayar jikin bangon gado, a karo na biyar ta sake ɗora hannu bibiyu akai ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka kamar wacce aka isarwa da mummunan labarin mutuwar iyayenta biyu ta hanyar hatsarin mota. Da madungure ta sauka daga kan gadon tana rusa kuka, takai gwauro ta kai mari a tsakiyar ɗakin. Duk tunaninta shi ne ya ƙuƙe ne akan ina Hafiz yake haramar kai mata ɗanta Aadil? Tun bayan da ta farka daga nannauyan barcin da ya kwasheta da misalin ƙarfe takwas da minti ashirin na safe, ta shige bayi tayi brush. Ko da wasa hankalinta bai kai kan gadon Aadil ba balle har ta fahimci ba ya kwance a ciki sai bayan da ta fita zuwa ƙaramin kicin ɗinta na sama, ta haɗo tea ta koma ɗakin tana kurɓa a hankali saboda wani masifaffen yunwa da take ji kamar anyi mata yasa a cikinta. Tunda ta leƙa harabar tsakar gidan taga babu motar Hafiz ta san ya wuce Faƙo kamar yadda ya saba duk ranar asabar. In dai ba ita ta ɗaga Aadil daga kwance ba tayi mishi wanka yana kai misalin ƙarfe goma zuwa goma da rabi na safe yana barci. Shi yasa hankalinta bai kai kan ba ya cikin gadonsa ba. Sai da ta gama shan tea, ta mayar da kofin kicin, ta koma cikin ɗakin ta shige banɗaki ta haɗa ma yaron ruwan wanka. Tana yaye net ɗin saman gadonshi da niyyar ɗaukan yaron sai taga wayam. Da farko ta zaci idanunta ne ke mata gizo, don haka sai ta ɗan mutsittsika idanunta don su ƙara washewa. A lokacin ne fa ta tabbatar ba ya nan. Ai a sittin ta fice zuwa ɗakinta inda ta haɗa kayayyakin Aadil. Suma suka ce ɗauke mu inda kika ajiye. Da yake ta san yadda suka rabu da Hafiz ɗin a daren jiya, bata tsaya wani raba ɗaya biyu ba ta san Hafiz ne ya shammaceta ya ɗauke mata yaro. "Kan ubancan kayyasa. Ni Hafiz zai shammata? Na rantse da girman Allah yadda ka ɗauke shi ka tafi da shi kai da ƙafafunka za ka dawo da shi, zan ga ƴar iskar tsohuwar da take da ƙwarin gwuiwar riƙe min ɗa a ƙauyen ƙayau idan ita ce tayi min naƙuda ta haifo min shi." Tayi maganganun cikin masifa da bala'i, bakinta har tartsatsin miyau yake yi don tashin hankali. Da farko har za ta bari ya isa sannan ya dawo mata da ɗanta, domin tana da tabbacin in dai Innaye da ƴaƴanta ba giyar wake suke sha ba baza su riƙe mata ɗa a ƙauye ba. Can kuma sai taga ai idan ta bari Hafiz ya tafi da Aadil ya wuni mata da ɗa a ƙauye ba tare da amincewar ita uwar ɗan ba ai ya gama cutar da ita, cutarwa ta ƙarshen-ƙarshe. Don haka afujajan ta koma ɗakinsa inda tayi barci ta ɗauki wayarta akan durowar bedside ta lalubo lambarsa ta fara danna mishi kira. Zuciyarta cike da alwashi iri-iri da barazana da rantse-rantsen da za tayi mishi kan idan bai dawo mata da yaronta yanzu-yanzu ba za su samu mummunar saɓani, irin saɓani da balbalin bala'in da bai taɓa tunanin za su samu ba a tarihin rayuwar aurensu. Sau uku kacal ta samu nasarar kiran ya shiga bai ɗauka ba, tun daga waɗannan ukun, duk sadda kiran yayi kamar zai shiga sai a saka mata user busy. A cikin daƙiƙu sittin da suka biyo baya, ta yi kuka, ta yi kuka, irin matsanancin kukannan da tunda uwarta ta haifeta bata taɓa yin irinshi ba. Domin a wannan lokacin zuciyarta ta fara tunanin idan su Baffa suka riƙe Aadil a can Faƙo kamar yadda Hafiz yake so ya za ta yi? Cikin kuka da majina ta fara rantse-rantse tana shan alwashi... "Na rantse da girman Allah... ko sun riƙe shi gobennan zan yi sammakon tafiya in karɓo ɗana, in sama da ƙasa za su haɗe Wallahi Tallahi sai sun ba ni yarona. Idan kuwa sun ƙi ko da ƴan sanda da sojoji ne sai na je na amso yaro na, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba..." Kamar a mafarki sai taji Mai gadi yana buɗe get ɗin gidan, da saurin gaske ta matsa jikin window, zuciyarta cike da fatan Hafiz ne ya canja ƙudurinsa ya dawo mata da ɗanta, duk da wani sashe na zuciyarta na faɗa mata abu ne mare yiwuwa Hafiz ya fasa ƙudurinsa a sauƙaƙe. Ƙuri tayi da idanunta jikin motar da take shigowa sannu a hankali har ta ƙarasa shigowa tsakar gidan. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke, motar Aminiyarta Raudha ce. Tana nan tsaye a jikin window har Raudha ta gama daidaita fakin ɗin motar ta kashe ta fita. Hakan yasa ta saki labulen windon ta fice daga ɗakin da sassarfa, zuciyarta na ƙara ɗugunzuma. Kamar an buɗe famfo sabbin hawaye suka sake ɓalle mata, haka ta sauka ƙasa ta tari Raudha a falo fuskarta kaca-kaca da hawaye, ga idanunta da suka kumbura suka canja launi saboda tsabar daɗewa tana rusa kuka. "Raudha... Hafiz ya kashe ni..." Kalaman da ta fara faɗa ma Raudha kenan cikin matsanancin kuka da rawar baki, bayan ta ruƙunƙumeta a tsakiyar falon. Ita kuwa Raudha ga tsammaninta Bintu ta gano Hafiz yana soyayya da Karima ne. Daman kuma takanas-ta kano abinda ya kawo ta gidan kenan ta faɗa mata. Ashe kaya ne ya tsinke a gindin kaba. Don haka sai cewa tayi "Uhmmm! Kaɗan daga cikin halin maza kenan! Ai da can da muke faɗa miki ba cewa kika yi Hafiz ya sha ban-ban da sauran maza ba? Yanzu wa gari ya waya Bintu?" Bintu dai ba baka sai kunne, illa iyaka ma sai ƙara ƙarfin kukanta take yi tana rerawa kamar tashin jiniyar motar ƴan sanda. Da fuska mai cike da tausayi Raudha ta riƙe kafaɗar Bintu taja ta suka zauna a kujera mazaunin mutum uku, a tausashe ta ce "Kiyi haƙuri Bintu! Na san abin da ciwo to amma ya kika iya da abinda ya gagari wuta? Kukan nan da kike ta rusawa sam ba mafita ba ce. Idan ma za kiyi shiru mu nemi mafita gara kiyi shiru. Yanzu ina shi Hafiz ɗin?" "Ya tafi da shi fa Raudha... Ya tafi da shi... Ni babban damuwata idan Aadil ya farka bai ganni ba kuma bai ga Umma ko Mashku ba wane irin firgita da tashin hankali zai shiga? Na rantse da girman Allah akan ɗaukar min ɗa da Hafiz yayi ya tafi da shi wannan tsinannen ƙauyen ba tare da izinina ba sai munyi gagarumin tashin hankali da shi." Galala Raudha tayi da baki tana kallon Bintu ba tare da ta gane maganganun da take yi ba. Ganin dai ta kasa raba ɗayan biyu yasa ta cewa "A'a! Wai tsaya Bintu, akan me kike magana ne?" Ba tare da damuwa ko tuhumar irin maganganun da ita Raudha ta fara yi ba Bintu ta kora mata bayanin duk halin da ake ciki na tafiya da Aadil yaye gurin Innaye. "Kam bala'i!! Amma gaskiya Hafiz ya gama raina ki Bintu. Ko da yake ni banga laifin Hafiz ba sai na ki, tun farko ke ce kika ba shi yarda ɗari bisa ɗari shi yasa har yaga wallenki ya fara gara ki yana wulaƙanta ki yadda yake so." Raudha ta faɗa cikin tsantsar takaici da baƙin ciki. Kafin Bintu ta ce wani abu ta cigaba da cewa "Saboda in dai ba burin ya wulaƙantaki ya tozarta ki ba ta ya za'ayi ya ɗauki kyakkyawan yaro ajebo irin Aadil kuma ɗan shekara ɗaya kacal ya kaishi wannan ƙazantaccen ƙauyen na su? Wannan burin kashe miki ɗa kawai yake da shi. Idan kuwa kika bari kuka cigaba da tafiya a haka! Na rantse da Allah sunanki sorry...!" Maganganun Raudha babu abinda suke ma Bintu illa ƙara tunzurata. Shi yasa hawaye ya ƙi tsayawa a idanunta, ga wani fitinannen ciwon kai da ya addabeta amma don tsananin baƙin ciki da takaici ta kasa daina kuka. Sai da Raudha ta gama ziga Bintu iya ziga, sannan ta fara rarrashinta da cewar ta adana kukanta ya isa haka. Kawai ta jira dawowar Hafiz suyi duk wacce za suyi, amma tana ƙara jaddada mata ko sama da ƙasa za su haɗe kar ta kuskura ta bar Aadil ya kwana biyu a ƙauyen Faƙo. Wannan tashin hankali da Raudha ta tarar da Bintu a ciki, shi ya hana ta faɗa mata maganar Karima da Hafiz. Tsoronta ɗaya kar Bintu ta sume mata idan ta ji labarin tashin hankalin da ya ninka maganar kai Aadil Faƙo. Ko a yanzu ba ƙaramin tsorata tayi ba da wani irin numfarfashi da Bintun take ja akai-akai kamar mai cutar athma. Shi yasa ta ƙara ɓata lokaci tana rarrashinta da tausasan kalamai, ta gyara mata ɗakunan sama kafin isowar Baba Rabi. Bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Bintu ta ɗan samu nutsuwa kaɗan, ta sha paracetamol ta kwanta barci. Sannan ta samu ƙwarin gwuiwar barin gidan jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da tausayin ƙawartata da sai a yanzu ne namiji ya fara buɗa mata shafi-shafi na munanan halayensa. Babban fatanta ɗaya shi ne, Allah ya ba Bintu ikon fige wannan kazar wahalar a sauƙaƙe. Domin ita shaida ne, duk abinda zai biyo ta kan soyayyar da Bintu take ma Hafiz ba ta ɗaukar shi da sauƙi balle har tayi gangancin ɗaukarshi a wasa. Yarda take da shi mai girma akan irin son da Hafiz yake mata, da wanda ita take mishi, babu kunya babu tsoron Allah take bugun ƙirji a cikin ƙawayensu tana tutiyar mijinta ya fita daban da sauran gama-garin mazaje. Tsakani da Allah ta fara tausayin Bintu. Har ta isa gidanta zuciyarta cike take fal da tunanin mabanbantan hanyoyin da za ta bi wajen taimaka ma Bintu da dukkan ƙarfinta da dabararta. Domin Bintu ta yi mata halarci mai yawa a rayuwa, baza ta taɓa mantawa da taimakon Bintu gare ta ba har zuwa wannan matsayi da take kai a yanzu, sakamakon kyautatawa kuwa kyautatawa ce. ******* Saboda tafiyar da baiyi da wuri ba, kuma ko da ya isa can Faƙo ma bai fito da wuri ba. Ya isa gida ne da misalin ƙarfe goma sha ɗaya da minti biyar na dare. Kallo ɗaya za'ayi mishi a fahimci tabbas a jigace yake. Ga wahalar hanya, ga wahalar tuƙa mota kuma tafiya mai nisan gaske, abinda ya daɗe baiyi baiyi ba. Ko a yanzu don direbansa ba ya nan ne, ƴarsa ta cikinsa Allah yayi ma rasuwa bagatatan a garin Suleja. Dole suka tafi da Hafiz yayi ma iyalanshi gaisuwa, yayi musu sha tara ta arziki sannan ya tuƙa motar da kansa ya koma Abuja. Duk da dare ne, tsakar gidan ko ina haske ne tar kamar rana, saboda wadatattun ƙwayayen lantarki masu haske sosai da aka maƙala guri-guri a tsakar gidan. Duk da tsarabobin da su Innaye suka haɗa mishi a cikin mota ya kasa ɗaukar komai. Wayarsa kaɗai ya iya ɗauka sai makullin motarsa da ya zare ya nufi babban falonsu. Sannu a hankali yake tafiya saboda gajiya, yana isa bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya murza hannun ƙofar ya cusa kanshi cikin falon. Kiciɓus suka yi da Bintu, wacce duk wannan dare da ya fara tsalawa idanunta biyu. Tsayuwar motarsa a tsakar gidan yasa ta ɗauki hijabi ta saka ta sauko ƙasa zuwa falon a gaggauce, ba don komai ba sai don zakwaɗin ganin shin Hafiz ya dawo mata da Aadil?

Chapter 31 of 40