Share this page
da ake ciki..." "Ko ka faɗa masa shi ma bazai goyi bayan zuwanmu suna ba. Kuma zan kira Hafizun yanzu in mishi kaca-kaca tunda ba ya jin magana, tun rannan na faɗa mishi baza mu je suna ba amma don neman zance shi ne ya tura muku kuɗin mai. To kuwa sai dai yayi asara, ni kam ba ni zuwa ko ina" Baban Yasi dai bai saurareta ba ya fice daga ɗakin ya barta tana bambamin faɗa kamar za ta ari baki. A fusace ta ɗaga filon da kanta yake kai ta ɗauko wayarta, ƙanƙance idanu tayi ta lalubo lambar Hafiz ta danna mishi kira. Second ɗaya biyu sai ta ja tsaki ranta a ɓace. A can ɓangaren Hafiz da yake ya san yadda suka rabu da ita tun sa'adda ya tambayeta masu zuwa suna yana ganin kiranta ya ki daga wayar, a karshe ma sai ya kashe wayar gaba daya don kar ta cigaba da damunsa. [1/4, 7:40 PM] Fareeda Abdallah: Zancen d'aukar shatar motoci da Hafiz yayi ga masu niyyar zuwa suna gidansa yana isa kunnen Baffa ya karbi maganar da hannu bibiyu. Irin yadda ya dinga nuna farin ciki da zumudi, ba karamin mamaki ya ba Innaye ba. Domin tun a daren ya fara kiran mazajen 'ya'yansa mata da suke gidan aure yana nema musu izinin tafiya suna gidan d'an'uwansu a Habuja. Ya kira 'yan'uwansa ya sanar da su lallai su fada ma matansu da yayansu da suke gidan aure, duk wacce take son zuwa suna gidan Hafizu mota kyauta ne zuwa da dawowa. Ya aika gidansu Innaye ya fada ma yan'uwanta. Tun Innaye tana shiru taga iya gudun ruwansa, sadda ta ga ya fara aikawa gidan abokan arzikinta yasa ta kasa hakuri har sai da ta ce mishi "Anya Malam gayyar mutanen nan da kake yi zuwa gidan Hafizu zai haifar mana da d'a mai idanu kuwa? Matar Hafizu ba irin matan birnin nan bane da suke son mutanen kauye fa..." "Ba don ita za su je ba. Don shi ne, tunda dai shi namu bai guje mu me ya dame mu da halinta na gudun mutanen kauye? Na tabbata Hafizu bazai taba bari matarsa ta wulakanta masa yan'uwa ba." Ya katse Innaye tun kafin ta aje numfashin maganarta. "To shi kenan! Allah ya kaimu goben Lafiya." Ta yi addu'ar jikinta a sanyaye. "Ameen." ***** Motoci ukun da Hafiz ya dauki shata sai da suka cika tam da yan'uwa da abokan arziki saboda kara irinta mutanen kauye. Duk yadda Yaya Balira taso zille ma zuwa sunan sai da Baffa ya tilasta ta tafiya, haka nan ta shirya yan kayayyakinta kala biyu a cikin jaka suka kama hanya, duk zuciyarta a kuntace. Domin Allah ya gani sam bata so tafiyar ba. Ita da yan'uwanta da suke daki daya fuskokinsu ba yabo ba fallasa. Su kuwa sauran yan'uwa da basu san dawan garin ba bakunansu har kunne. Sai murna suke suna dararraku, ko wacce tana baje labarin irin nisan tafiyar da ta taba yi a rayuwarta. Dukkansu dai kololuwar tafiyarsu Kaduna ne, hatta yan'uwan Hafiz da suke uba daya basu taba zuwa gidanshi ba tunda yayi aure sai yanzu da za su tafi. Karfe biyar na yamma suka isa gidan Hafiz. Da yake ya shirya ma zuwansu sosai, wadataccen abinci yasa aka dafa musu da ya ji nama zuk'u-zuk'u. Katan-katan na lemu masu sanyi aka tare su da shi da ruwan gora, komai dai sun same shi a wadace sai da suka ci suka sha suka bar saura. Dakunan BQ da suke manyan dakuna kuma a wadace tun kafin su isa yasa an gyara ko ina fes! Daman akwai funitures a ciki, duk abinda babu kuma kafin su isa an tanade shi. Gidan Hafizu bai fara d'aukar harama da nuna alamun gidan da za'ayi suna bane sai da suka isa. Duk da tazarar da ke tsakanin inda suke da ainahin inda matar gidan da daidaikun yan'uwa da kawayenta ke zaune har nan ake jin hayaniyarsu. Bintu ta cika tayi fam kamar za ta fashe. Ita kadai sai huci take yi kamar kububuwa, amma ta kasa furta ko uhmm! saboda Hafiz yana gidan. Kamar wata sakarya, da ya shiga dakinta ko kuma ya kira ta zuwa dakinsa sai tai ta washe mishi baki tana dariya duk don dai kar ya ji a zuciyarsa kamar ba ta maraba da zuwan 'yan'uwansa. Tun abinda ya faru ranar da su Baffah suka je a tsorace take. Don ma Allah ya taimaketa Hafiz din ba mutum bane mai rik'o. A sadda abu ya faru, idan ya nuna bacin ransa cikin kankanin lokaci zai warware ya koma da walwalarsa. Shi yasa take iya yinta wajen kiyaye abinda zai sake janyo mata wani bacin rai da ba ta tunanin za ta iya warwareshi cikin sauki. Abu daya da ya aikata ta ji nutsuwa kadan a ranta shi ne bai bar yan'uwansa sun shiga bangarenta ba. Umarnin shiryawa yayi mata sannan ya dauki Baby Al'ameen wanda ake yiwa inkiya da Aadil suka je bangaren da aka sauki bakin suka gaisa. Tana ji tana gani sukai ta damukar jaririn ranta yana k'una, amma ko a fuska ta gagara nunawa har suka gama gaisawa da tambayar lafiyar su Innaye sannan ta fice ta barsu da d'an'uwansa. Har d'an tsayawa tayi ko za'a ce ga Aadil ta wuce da shi amma ta ji shiru, haka nan ta fice ta barsu da Hafiz tana ta jan kananun tsaki a zuciyarta. Gudummuwar naira dubu talatin 'yanuwansa suka hada mishi a matsayin gudummuwa. Sadda Aunty Balira ta kebe shi gefe ta bashi kudin ji yayi kamar zai saka kuka. Zuciyarsa ta kara cika da kaunar 'yan'uwansa. "Mun so mu siya ma Babanmu kayayyakin jarirai sai kuma muka ji tsoron siyan abinda bai dace da ku yan birni ba. Shi yasa kawai muka yanke shawarar taho maka da kudin, kayi hakuri. Ka san yanayin garin..." "Haba! Ba komai Wallahi Aunty Balira, na gode. Allah ya bar zumunci. Na ji dad'i sosai Wallahi. Amma yanzu dai ki ajiye min kudin a gurinki, zuwa safe in sha Allah zan karba." Da haka suka rabu, ya karbi jaririn da ke ta barci hankalinshi kwance ya mayar da shi gurin Mamansa. A lokacin ana ta kiraye kirayen sallar Magriba a masallaci. Washe gari da asubah tafiyar aiki mai matukar muhimmanci ta kama Hafiz da wasu daga cikin abokan aikinsa. Lagos za su tafi, bai so tafiyar ba ko kaɗan, amma da yake kira ne da suka daɗe suna jira daga branch ɗin su da ke Lagos yasa tafiyar ta zama dolen-dole. A gaggauce ya fara shiryawa yana rarrashin Bintu da take ta matsar ƙwalla, ta ci burin taron sunan nan ayi da shi, sai ga shi tafiyar ta bazata ta rusa musu bodjet. Taron suna ne suka shirya shi irinna ƴan birni kuma yan gayu, domin ba ma a gidan za'a yi taro ba. Event center suka kama mai matuƙar kyau da tsada, acan suka shirya za'ayi taron sunan. Duk ɗinke-ɗinken da tayi sunyi ne tare da Hafiz, taron suna ne da suka shirya gudanar da shi kamar gagarumin taron bikin aure. Sai ga shi tana ji tana gani tafiyarshi ya rusa kaso arba'in cikin dari na tsarin da suka yi ma bikin sunan. Ranta a bace ta raka shi har gurin mota yana kara rarrashinta da tausasan kalamai, bata koma cikin gida ba sai da taga direba ya fice da motar sun nufi Ofis inda za su haɗu da sauran abokan tafiyar tasa. Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya tuna da su Aunty Balira, goshinsa ya dafe kadan alamun bai ji dadin mantuwar ba, ya dauki wayarsa ya kira ta suka yi sallama bayan ya jaddada mata in sha Allah a ranar zai dawo. Tun da Hafiz ya bar gidan, sai ya zama kamar an shafe su Aunty Balira da manawarsu a zuciyar Bintu. Ta manta gaba daya da babinsu balle ma har ta tuna da suna cikin gidan, ko kuma tayi kokarin sauke wani hakki na su da yake kanta a matsayinsu na dangin mijinta. Harkokinta kawai take yi cikin yan'uwa da kawayenta. Da kuma matasan yara mata 'ya'yan Alh Lurwanu da suka je gidan tun da wuri, ta kuma karɓe su hannu bibiyu kamar yadda ta saba, domin su ta riƙa a matsayin dangin mijinta na gaske, ba waɗancan gayyar ƙauyawan da ta raina ma ajawali ba. Hatta abin karyawa sai da aka doshi ƙarfe goma da rabi na safe sannan Aunty Balira ta shiga can cikin gidan tayi ma Bintu maganar abin karinsu. "Kin san mutanenmu basu saba ɗaukar lokaci mai tsawo basu karya kumallo ba. Kuma wasu a cikinmu sun zo da ƙananun yara, idan manya sun jure yunwa kin ga yara baza su jure ba." Ba kunya ba tsoro ta kalli Aunty Balira cikin ido ta ce "Na ji ! Ki je, za'a kawo yanzu. Kin san yau ne taron ni har ga Allah na ma ma manta da ku. Kuma dai ya kamata ko ɗan yaya ne ku dinga yima mutum uzuri tunda kun san ranar sha'ani kai ɗaukar zafi yake yi." Ta faɗa da dukkan gaskiyarta, fuskarta babu walwala ko kaɗan. Aunty Balira ta kalle ta da ɓacin rai, kamar za tayi magana sai kuma tai shiru ta girgiza kai, ta fice daga ɗakin ranta a ɓace. Kafin ta isa can inda sauran suke ne tayi ƙoƙarin sakin fuskarta don kar su fahimci da wata ƙasa. Ko da taje tayi maganar abin karin, sai da aka ɗauki fiye da mintuna ashirin kafin aka kai musu abinci, shinkafa ce dafa duka da taji busasshen kifi a cikin wata ƙatuwar kula sai alalen leda a kula daban, sai kuma ruwan sha na gora katan-katan da aka shigar musu da shi. Tun daga wannan abinci da aka basu, Bintu bata ƙara waiwayarsu ba. Ita ma Aunty Balira bata ƙara shiga cikin gidan tayi mata maganar abinci ko wani abu da suke buƙata ba. Ƙarfe biyu na rana kuma suna daga can ɓangarensu suka dinga jin tashin motoci na ficewa daga gidan, ko da suka leƙa da sauri, sai suka ga mata ne ake ta fita da su a mota sun sha kwalliya na gani a faɗa. Akan idanunsu Bintu da tasha wata ƙayatacciyar kwalliya kamar sarauniyar kyau ta saɓo jaririnta tana tafiyar ƙasaita ƙawayenta na take mata baya, ko kallon ɓangaren da suke tsaitsaye baki buɗe suna kallonta bata yi ba ta shige cikin mota. Ƙawayenta ma suka shiga mota aka fice da su daga gidan. ****** "Bintu? Sai naji kamar jiya Hafiz yana faɗa ma Abbansu ƴan'uwansa za su zo suna daga can gida. Ya banga ko mace ɗaya a cikinsu ba?" Hajiya Balaraba uwargidan Alh Lurwanu ta tambayi Bintu da mamaki a fuskarta. Ganin tun da aka fara shagalin taron sunan ko ire-iren dangin Hafiz bata gani a gurin ba. Dariyar yaƙe ta ɗanyi, ta ɗan sosa gefen ɗaurin ɗankwalinta da mai kwalliya ta ɓata fiye da minti talatin tana ɗaura mata. Sai kuma tayi saurin wayancewa ta ce "Wallahi Mama kin san abinki da mutanen karkara. Babu yadda banyi da su ba su shirya a taho da su gurin taron nan suka ce baza su zo ba, a cewarsu sun fi so su zauna a gida. Da naji haka sai kawai na bar musu komai da za su buƙata a wadace mu kuma muka taho." "Habawa! Ko da na ji. To don Allah kafin su wuce dai a saka direba ya kawo su mu gaisa, akwai saƙon da nake so in basu su tafi ma da Innaye." "To shi kenan Mama. In sha Allah za a kawo su, gobe da wuri zan saka direba ya kawo su." Da haka suka rabu da Mama ta cigaba da warwasawa cikin ƙawayenta. Ɓangaren Hafiz acan Lagos duk irin hotuna da Vidion taron da Bintu take ta tura mishi kanshi ya ɗau zafin da bai samu buɗe ko guda ɗaya ba. Meeting suke ta shiga da manyan Oganninsu, daga wannan sai wannan. Duk yadda ya so su juya Abuja a ranar ma hakan bai samu ba, saboda basu gama komai da komai ba sai bayan magrib. Daman akwai ƙayataccen masaukin da aka kama musu na kwana ɗaya, su ne dai kawai suka yi tunanin za su gama komai a ranar su juya Abuja cikin iyalansu. Sai da daddare, bayan ya gama duk wasu al'adunsa na kwanciya ya bi lafiyar gado sannan ya samu nutsuwar buɗe data ya hau online. Ko a waya da yaga taron ya ƙayatar kamar yadda suka so, shi kaɗai yake ta sakin murmushi yana sake buɗe hotunan, yana kallon Yadda Bintu da jaririnsa suka yi wani fitinannen kyau kamar a sace su a gudu. Yana daga cikin dalilin da yasa a kullum soyayyar Bintu ke ƙara sabuntuwa a zuciyarsa, kyakkyawa ce ta ƙarshen ƙarshe. Shi kuma a rayuwarsa haka Allah yayi shi da bala'in son mace mai kyau na ɗaukar hankali, kallon dirarriyar mace kuma kyakkyawa kamar Bintu a matsayin matarsa kaɗai yakan saka shi jin alfahari. Mace ce ta nunawa tsara, duk girman taro da ƙayatuwarsa babu inda zai kasa shiga da Bintu a matsayin matarsa. Sai da ya gama kallon hotuna da vidiyin tsaf! Ya kira ta suka ɗauki fiye da awa ɗaya suna hirar yadda taron ya kasance, a gefe guda kuma suna ƙara ba ma fulawarsu ta soyayya ruwa. Daƙyar suka yi sallama bayan kiran Ogansu ya shigo wayarsa. Bayan ya gama waya da Oga sun tattauna kan yadda meeting ɗin da suka yi ya kasance hotunan ya sake buɗewa, yana kallo zuciyarsa na ƙara tunbatsa da farin ciki. Nan take ya ware waɗanda suka yi kyau sosai da zai sa a wanke manyan hotunansu. Sannan ya tsara a zuciyarsa idan ya koma gida lallai dole ya sake shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan taron tsakaninshi da iyalinshi suyi hotuna, domin ya sake ware waɗanda za a bugo manyan kati su maƙala a falonsu na tarihi. Ƙarfe goma da rabi na dare, Aunty Balira da sauran ƴan'uwansa suka faɗo mishi a zuciya. Da saurin gaske ya lalubo lambarta ya danna mata kira, a zuciyarsa yake jin lallai bai kyauta ba na yadda duk yinin ranar bai samu ya tsuke lokacinsa ya kira ta yaji yadda suka yini da yadda taron sunan ya kasance a ɓangarensu ba. Sai kuma a lokacin ya sake tunawa da ai duk yawan hotuna da Vidion da Bintu ta tura mishi ko mutum ɗaya bai gani daga cikin ƴan'uwansa ba. Haka kawai ƙirjinsa ya ɗan buga daram! A daidai lokacin kuma kiran da yayi ma Aunty Balira ya tsinke bata ɗauka ba, bai gaji ba, ya sake danna kiranta a karo na biyu, nan ma dai har ya tsinke bata ɗaga ba. A taƙaice sai da ya kira ta sau huɗu bata ɗauka ba, kawai sai ya danna kiran lambar Bintu, ita ma dai har ya kira ta sau uku bata ɗauka ba. Ya kuma rasa dalilin da yasa haka kawai ƙirjinsa ke cigaba da bugawa akai-akai. "Uhmmm! Allah yasa dai lafiya." Ya faɗa a fili bayan ya haɗiyi wani kakkauran miyau da ya taru a bakinsa. A can gidan Hafiz kuwa, a daidai wannan lokacin da yake kiran Aunty Balira tana can cikin gidan ita da ƴan'uwanta biyu suna yi ma Bintu wankin babban bargo akan wulaƙancin da tayi musu a wannan rana. Kun san abinku da mai haƙuri bai iya fushi ba. Sannan Bintun ta daɗe tana shiga musu hanci da ƙudundune, su Aunty Ladidi da Aunty Rakiya sun daɗe da burin son su fyato ta Aunty Balira da Innaye suke dannarsu. [1/6, 10:15 PM] Fareeda Abdallah: Yau kam da suka samu dama basu tsaya sanya ba, Aunty Rakiya da duk ta fi su zafin zuciya saboda ɓacin ran yadda Bintu take mayar musu da magana cikin tsantsar raini da gadara sau uku tana yunƙurin janyota don rufeta da duka Aunty Balira da ƴan'uwan Bintu da suka rage a gidan suna shiga tsakani. Cikin fushi da ɓacin rai sosai Aunty Ladidi ta cigaba da magana cikin faɗa tana nuna Bintu da yatsarta manuniya "Ke har kin isa ki ce za ki raba mu da ɗan'uwanmu? Na rantse da Allah baki isa ba. Kinyi kaɗan, kuma kinyi tsururu. Duk take-takenki mun daɗe da gano abinda kike nufi, kar muke kallonki. Hafiz ne tunda kina son shi dole ki rungumi iyaye da ƴan'uwansa da suka kasance ƙauyawa. Gidannan kuma ko kina so ko ba kya so baza mu taɓa daina zuwa ba, idan kin isa kuma kin kai isasshiya, ki saka Hafiz ya kore mu..." "Ai kuwa ko yanzu na nuna muku na isa har nayi yawa." Bintu ta katse ta da sauri kuma cikin raini da gatsali. Da hannu biyu ta riƙe ƙugunta tana karkaɗawa tana fari da idanu sannan ta cigaba da cewa. "Gidannan dai gidan mijina ne, ni da nake matar gidan ni nake da girman ikon sakawa da hanawa ko kuna so ko bakwa so. Na riga na zame muku ɗuwawu, dole ku zauna da ni, tunda ɗan'uwanku ya ce ya ji ya gani ni yake so matsayin abokiyar rayuwa dole duk yadda na dama haka za ku sha..." A zafafe Aunty Rakiya ta katse ta da cewa "Wallahi ƙarya kike yi Bintu. Babu dole a zama da ke, bari in tunatar da ke abu ɗaya idan haukar ƙwaƙwalwarki yasa kin manta... Hafizu namiji yake, ana canza mata, amma ba'a taɓa canja ƴan'uwa. Sannan ana canja mata amma ba'a taɓa canja uwa da uba. In banda ke jaka ce mare hankali wulaƙancinki har ya iya tsallake kan dangin miji ya haura kan iyayenshi? Duk mugunta da ƙulla-ƙullar da kikai ta yi ma Innaye sadda tazo gidannan jinya babu wanda bamu sani ba..." Da saurin gaske Aunty Balira tayi saurin katse Rakiya, a ganinta yanzu ba muhallin yin wancan maganar bane. Kuma baya ga haka tun a wancan lokacin sun yi ma Baffa alƙawarin baza su taɓa canja ma Bintu kan abinda ya faru da Innaye ba. "Dakata Rakiya dakata! Idan kika sake magana anan gurin ba tare da na gama faɗin abinda zan faɗa ba sai na tsinka miki mari." Saboda tsananin biyayya da girmama na gaba da aka hore su da shi, Rakiyar bata ƙara cewa komai ba, sai baya da ta matsa tana sauke zafafan numfarfashi, tana huci kamar kububuwa. Ita ma Ladidi da ba'a mata umarnin yin shiru ba kusa da Rakiya ta matsa ta tsaya tana d'an karkaɗa kafafunta. Ita ma nata fuskar babu walwala ko kad'an. "Bintu na dawo gare ki." Aunty Balira ta fada bayan ta mayar da hankalinta kan Bintu da take tsaye har lokacin tana wani karkad'a kafaɗu babu alamun nadama ko rusunawa ko kaɗan tattare da ita. "Faɗi duk abinda za ki faɗa dai-dai nake da ku dukkanku. Kunne ke ji, baki ne zai faɗa kuma baki ne zai bada amsa." Ta faɗi hakan cikin gatsali tana wani harare-hararen gefe. Kasancewar hasken wuta ne tar ta ko wane ɓangare a cikin falon kamar rana, shi yasa duk abinda take yi suna kallonta rayukansu na ƙara ɓaci. Nannauyar ajiyar zuciya Aunty Balira ta sauke ta cigaba da cewa "Ki kalle ni da kyau Bintu. Shekaruna a duniya arba'in da biyu. Ina da shekara goma sha uku Baffa yayi min aure. Da ace Allah ya bani haihuwa tun sa'adda nayi aure da yanzu na haifi kamar ki, ko wacce ta girme miki. Sannan baya ga darajar shekaru da ya kamata ace na ci a gurinki, duk mu ukun nan yayyen mijinki ne. A lalace ko Ladidi da take ƙarama a cikinmu shekara biyar ke tsakaninta da Hafizu. Waɗancan gayyar ƙauyawan matan da kike cewa mun kwaso su mun cika miki gida, daga Gwaggwannin Hafizu sai Innoninsa, sai kuma Aminan Innaye da sa'annin haihuwar Hafizu da ƙannensa da suke uba ɗaya. Yanzu duk waɗannan dalilan saboda Allah ke a gurinki basu kai matsayin da za ki girmama mu ki karrama mu don su ba...?" "Don Allah tsaya Aunty Balira?" Bintu ta katse ta cikin fushi. "Wai da kuke ta wannan fuffukar tun da kuka zo gidannan menene nayi muku na wulaƙanci? in dai ba rashin godiyar Allah da son maƙala min laifi ba? Gurin taron suna ne tun kafin ku zo an riga an ƙayyade iya yawan mutanen da ake so su halarci gurin, kawai saboda ni ce ƴar daɗi dangin miji sai in kwashe ku yuuuu zuwa gurin? bayan kuma ba'a tsara gudanar da taron da ku ba?" Ta katse Aunty Balira da tambayoyin cikin hayayyaƙa tana yi tana ɗaga hannuwa sama kamar za ta mare ta. A bazata, idanun Aunty Balira suka kawo ruwa, da sauri tayi ƙoƙarin haɗiyewa. Ɗaya bayan ɗaya ta kalli ƴan'uwan Bintu su huɗu da suke tsaye a gurin suna bayar da haƙuri lokaci bayan lokaci, sai ta tsayar da idanunta akan wacce take ganin alamun ta ɗan fi sauran shekaru, da sanyin murya ta ce "Baiwar Allah don Allah ki mana alƙalanci. Ni duk ɓacin raina ba akan ƙin zuwa da mu gurin taron suna bane. Ita kanta Bintun ta sani, tabarmar kunya ce kawai take neman naɗewa da hauka yasa take waɗannan surutan. Yanzu saboda Allah ya kyautu ace tun abincin karin safe da aka bamu a gidannan ba'a sake waiwayarmu da ƙwaran abinci ba har yanzu da ƙarfe goman dare ta wuce? Manyan mata da kananun yara mu ashirin da bakwai muka zo gidannan, duk da direbobinmu uku mu talatin. Saboda Allah idan Bintu bata ba mu abinci a gidannan ba ina take so mu sa kanmu? Ko don ta ga ɗan'uwanmu ba ya nan shi ne take wulaƙanta mu?" Ta ƙarasa tambayar wasu sabbin hawaye suna sake cicciko idanunta. "Bintu?" Babbar yayar Bintu wacce Aunty Balira ta gama yi ma ƙorafi mai suna Sadiya ta kira sunan Bintu da yanayin mamaki a fuskarta. Domin ita sai yanzu da Balira tayi bayani a nutse sannan ta fahimci inda aka dosa da inda matsalar take. Kafin Bintu ta amsa ta sake cewa "Da gaske ne abinda wannan baiwar Allahn ta faɗa?" Nan ma dai Bintu ta kasa amsawa, sai zumɓura baki da tayi gaba tana ƙara ƙanƙance idanu. "Daman su ɗin shaƙiƙan mijinki ne amma kika ce mana gayyar soɗin karabitin ƴan'uwan Hafiz ne daga ƙauye? Kuma ca nake a gabana kika faɗa ma Hajiya Balaraba kin sallame su da duk abinda za su buƙata?" Nan ma dai shiru tayi, sai sunkuyar da kanta ƙasa da tayi tana mui-mui da baki alamun gunguni take yi a zuci. Da matsanancin faɗa Aunty Sadiya ta fara zazzaga mata masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. "Baki kyauta ba Bintu, gaskiya baki kyauta ba. Kin ɓata wayon ki, sannan kin bani mamaki. Ban taba tsammanin za'a sami irin wannan halin daga gare ki ba. Wannan mummunan banzan halin na wulaƙanta ɗan'Adam don kawai sun kasance ƴan ƙauye ban san inda kika kwaso shi ba. Kuma na rantse da Allah idan baki gyara ba sai na haɗa ki da Daddy, kin dai san halinshi sarai, ba ya ɗaukar irin wannan iskancin da wulaƙancin, ko da kike ganin kin yi aure kin haihu ke kin san baki fi ƙarfin hukuncin Daddy ba." Ta mayar da idanunta kan Aunty Balira, sannan tayi ƙoƙarin sassauta murya da yanayin da ke nuna nadama ƙarara ta cigaba da cewa "Baiwar Allah don girman Allah kuyi haƙuri. Ba'a kyauta muku ba tabbas! Amma don Allah kuyi haƙuri, a matsayina na Yayar Bintu na ari bakinta na ci mata albasa, kuyi haƙuri don Allah ba don mummunan halin da ta nuna muku ba. Ke Bintu maza basu haƙuri kafin in saɓa miki!" Ta ƙarasa da yi ma Bintu umarnin cikin tsawa. Ta cika tayi dam! Amma sanin halin Aunty Sadiyar na rashin ɗaukar raini yasa ta cewa "Allah ya baku haƙuri. Bazan sake ba." Bakinta a zumɓure kamar zai taɓa bango. Aunty Sadiya ta cigaba da cewa "Aunty yanzu dai ku koma can gurinku, yanzunnan za mu shiga kicin mu sama muku abinda za ku ci a daren nan in sha Allahu. Kuyi haƙuri don girman Allah, kuma ina fatan baza ku faɗa Hafiz abinda aka yi muku ba. Don Allah ku yafe mata, ba don halinta ba." Ko da ace da kissa Aunty Sadiya ta ba Bintu laifi a

Chapter 12 of 40