Ko kuwa su Innaye sun shirya tarbar bala'i da masifarta ne yasa suka yi gangancin riƙe mata ɗa?
Abu na farko da ta fara yi shi ne kallon hannayensa, ganin wayam! yasa ta jefa mishi tambaya da murya mai cike da tartsatsin tashin hankali ba tare da ko sannu da zuwa ta samu sararin furta mishi ba.
"Hafiz ina ka kai min yaro na?"
Da yake Hafiz ɗin namijin duniya ne, ko kallonta baiyi ba. Sai ma hannunsa da yasa a hankali ya matsar da ita gefe ɗaya, saboda bake-bake tayi a gabansa ta tare masa hanyar shiga cikin falon.
Da yake a cikin bala'i take, sam bata lura da yanayin da yake ciki ba. Don haka da saurin gaske ta sake shan gabansa ta ƙara bake-bake har da riƙe ƙugu. Bakinta har yana tartsatsin miyau saboda masifa ta cigaba da cewa
"Babu inda zan matsa, na rantse da Allah babu inda zan matsa sai ka faɗa min in da ka kai min ɗan jaririn yaro na..."
"Bintu...!!!"
Ya ƙwalla kiran sunanta da wani irin tsawa mai taratsi da barazanar fasa mata dodon kunne.
Duk turjewa da daurin zuciyarta bata san sa'adda ta ɗan ja da baya ba saboda firgitan da tayi. A ɗan tsorace ta ɗaga ido tana kallonsa, sai a lokacin ta lura da yadda ƙwayoyin idanunsa suka kaɗa suka yi jajur, kamar ba nashi ba.
Da wata irin gwarjejiyar murya mai cike da fitina ya ce
"A yau! Ke Bintu kin ci albarkacin rayuwar mutane uku mafiya muhimmanci a gare ni. Na rantse da Wallahi! Tallahi!! Billahi!!! Ba don waɗannan mutane uku ba da yanzu tsakanina da ke wani mummunan zance ake yi ba wannan ba. Don haka, ki matsa ki bani hanya in shiga ciki salin-alin ba tare da wani tashin-tashina ba. Idan kuma kin shirya taron Aradu da ka, don Allah ki sake yunƙurin tare min hanya Bintu."
Duk yadda ta shafe tsawon yinin tana shan alwashi kan irin balbalin bala'in da za ta sauke mishi idan ya dawo gidan ba tare da Aadil ba, ta rasa dalilin da yasa maganganunsa suka yi ma sassan jikinta wani irin dukan da yasa lokaci ɗaya tayi laƙwas! Ba ma kamar waɗannan manyan rantsuwa uku da ya jero mata a lokaci ɗaya. Duk da bata gama fahimtar inda maganganunsa suka dosa ba lallai jikinta yayi mutuwar da yasa lokaci ɗaya ta nemi duk wani bala'i da masifa da ta yini tana ji da su ta rasa.
Ita da kanta ta ƙara janye jikinta daga kan hanya. Shi kuma ya shiga cikin falon da wani irin taku na cikakken namiji ya nufi hanyar da zai hau sama ba tare da yayi mata kallo na biyu ba. Saboda wani irin baƙin Bintu da yake gani.
Bayan shigarsa cikin ɗaki, wayar hannunsa da makulli kawai ya ajiye ya faɗa banɗaki. Cikakkun mintuna ashirin da biyar ya ɓata yana gasa jikinsa da ruwan zafi kafin ya fito, jikinsa sanye da rigar wanka.
Wasu mintuna goma sha biyar ya sake ɓatawa gurin shafa mai, shirin barci, ya fesa daɗaɗan turarukansa masu sanyin ƙamshi sannan ya ɗauki wayarsa ya bi lafiyar gado.
Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ya lalubo lambar Zulai, ya tura mata ɗan gajeren saƙo mai ɗauke da kalaman godiya da addu'ar Allah ya ƙara danƙon zumunci a tsakaninsu.
Bayan saƙon ya tafi ajiye wayar yayi, ya janyo lallausan bargon ya lulluɓa har zuwa saman ƙirjinshi. Luf yayi akan filo ya lumshe idanu yana tunanin abinda ya faru bayan Innaye ta tabbatar mishi baza ta karɓi Aadil ta yaye shi ba.
Har ya kama hanyar komowa gida, zuciyarsa cike da shan alwashin yadda Innaye bata karɓi Aadil yaye ba itama Bintu bata isa ta kai shi gidan Ummanta ba. Sai dai ta yaye shi ita da kanta a gidansu, idan kuma ba haka ba to saidai ta cigaba da bashi nono har zuwa sadda shi da kanshi Aadil ɗin zai yaye kansa.
Har ya kusa isa gida sai ga kiran Zulai ya shigo cikin wayarsa, karo na farko tun bayan da tayi aure.
"Yaya... Yanzu muka waya da Innaye ta ke cemin za ka je Faƙo yau. Don Allah idan baka yi nisa ba ga saƙo ka tafi mata da shi. Nima da yau za mu je, sai kuma bagatatan tafiya ta kama Abban Imam. Allah yasa dai baka yi nisa ba."
"Ban yi nisa ba Zulai. Na juyo ne, yanzu haka ma gani na kusa isa gidana..."
Ya amsa mata da cusasshiyar murya mai bayyana damuwa ƙarara.
"Toh fa!! Lafiya? Me yake faruwa?? Ko ka fasa tafiyar ne???"
Ta tambaye shi cikin sanyin murya, zuciyarsa cike da tunanin me ke damunsa haka? Duk lalacewar ɗan'uwa ɗan'uwa ne, lokaci ɗaya ita ma Zulaikha ta ji ta shiga cikin damuwa. Duk da bai faɗa mata abinda ke damunsa ba.
"A'a! Ba fasa tafiyar nayi ba..."
"To ko baka da lafiya ne?"
Ta sake katse shi da tambayar tun kafin ya aje numfashin maganarsa.
Da yake zuciyarsa cunkushe take da damuwar da shi kanshi ya san tabbas yana buƙatar abokin tauna wannan damuwa. Kuma ƙarin shawara daga wani ɓangare na zuciyarsa da ta tunasar da shi mai shawara fa aikinsa ba ya ɓaci, sai dai ace yana da ƙarancin sirri. Waɗannan dalilan guda biyu suka ja mishi gora wajen zaiyane ma Zulai duk halin da yake ciki.
Da takaicin munanan halayen Bintu a muryar Zulaikha ta ce
"Lallai ma Innaye. Ita Bintun wacece da har za'a ji tsoron riƙe ɗan da ake da tabbacin ba nata ne ita kaɗai ba? Allah yasa dai baka yi gaggawar mayar mata da Aadil ɗin ba?"
"Ban mayar mata da shi ba. Amma ga ni a hanya zan mayar mata da shi. Ya zanyi Zulai? Dole in mayar mata da shi tunda dai ba ni da mai riƙe min shi... Ke dai kin san tunda Innaye ta ce baza ta riƙe shi ba cikin su Aunty Balira ma babu wacce za tayi gangancin riƙe shi. Balle ma yadda baƙin halin Bintu bai tsallake kowa ba..."
"Duk da haka dai Yaya... Ai hannun mutum bai taɓa ruɓewa ya yanke ya yar! Ni idan baza ka damu ba ka kawo min shi in yaye."
Saboda tsabar yadda maganarta ya dake shi bai san sa'adda ya taka burki da ƙarfi ba. In da Allah ya taimake shi shi ne a lokacin ya shiga cikin layinsu, da a kan babban titi yake irin wannan burki da ya taka na ba zato babu abinda zai hana motar bayanshi ta buga mishi.
Da saurin gaske ya gangara gefen hanya sannan ya kashe motar, bakinshi na rawa ya jefa mata tambayar
"Me kika ce Zulai?"
Dariya tayi sannan ta sake maimaita mishi abinda ta ce.
"Amma don Allah da gaske kike yi Zulai?"
Ya sake tambayarta da wani irin yanayi ɓoyayye, shi ba farin ciki ba shi kuma ba baƙin ciki ko fargaba ba.
"Wallahi da gaske nake yi. Amma idan baka amince ba sai in haƙura..."
"Na amince. Wallahi yanzu zan kawo miki shi Zulai. Na gode. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka. Ga ni nan zuwa."
Bai jira cewarta ba ya tayar da motar da sauri yayi revers ya miƙe hanya. Fuskarsa bayyane da matsanancin fara'a zuciyarsa tumbatse da nutsuwa.
Har ya yi nisa sosai a hanyarsa ta zuwa gidan Zulaikha, sai kuma ya tuna ai duk wannan budurin da suke yi shi da Zulai basu sako mijinta Kamal a ciki ba.
Kuma tsakani da Allah in dai shi matsayinsa na babba yana da lafiyayyen hankali ya kamata ya tuna yanzu fa ba kamar da bane. Hatta Innaye da take kamar mahaifiya ga Zulai Kamal ya fi ta iko da Zulai.
Jikinsa a sanyaye ya ɗauki wayarsa ya buɗo lambar Zulai ya danna mata kira. Yana shiga ta ɗauka, abinda ta fara tambayarsa shi ne
"Yaya ka ƙaraso ne?"
"A'a!"
Ya amsa mata. Sai kuma ya ɗanyi shiru kafin ya cigaba da cewa
"Zulai kar inyi aikin marasa hankali. Kina ga Kamal zai amince a haɗa Amaryarsa da raino alhalin ba haihuwa tayi ba?"
Dariyar da Zulai ta ƙyalƙyale da shi yasa shi ma ya ɗan saki dariyar, amma jikinsa a sanyaye.
"Allah da gaske nake yi. Kin san fa Aadil har yanzu jariri ne. Shekararsa ɗaya ne kacal saboda tsabar fitina irinta Bintu ta tsiro da zancen yaye shi."
Ajiyar zuciya Zulaikha ta sauke bayan ta tsagaita da dariyar da take yi.
"Kar ka damu Yaya! Ko ba ya tafiya za ta iya yaye shi a shekara ɗayan balle kuma yana tafiyarsa ko ina. Batun Abban Imam kuma ka kwantar da hankalinka, sam ba shi da matsala. Ko rantsuwa nayi babu kaffara bazai taɓa yunƙurin hana ni duk wani abu da ya shafi ƴan'uwana ba, saboda ya san muhimmancinsu a gare ni. Ta gwaɓa mishi magana da gan-gar. Kuma yau ɗinnan yayi tafiya, zai ɗauki tsawon sati shida acan. Anjima nima zan tattara ƴan abubuwan buƙata ne in koma gidan Mummy... ka san ta kuma ba ta da damuwa."
"Haka ne! To ga ni nan zuwa."
Ya amsa da sanyin jiki yana jinjina maganar da ta gwaɓa mishi a zuciyarsa.
Yana isa gidan Zulaikha, Aadil ya farka da wani irin gigitaccen kuka kamar wanda aka sa mishi wuƙa a wuya. Da wannan dalilin yasa Hafiz yana shiga da motarsa harabar gidan ko gama daidaita fakin baiyi ba ya sungumi ɗan hankalinsa a tashe ya nufi babban falon gidan.
Sau biyu ya ƙwanƙwasa bai jira an buɗe masa daga ciki ba ya fara murza hannun ƙofar yana ƙwalla kiran Zulai hankalinsa a tashe da irin kukan da yaron yake yi. Shi daman ba irin mutanen nan bane masu masifaffen son yara, duk yadda suke dariya da Aadil da zarar ya fara kuka zai miƙa ma Bintu shi.
Daga can cikin falon, a gigice Zulai ta ƙarasa sako hijabinta tazo ta buɗe mishi ƙofa. Bai saurari kalaman barka da zuwa da take furta mishi ba ya fara miƙa mata Aadil da har wannan lokacin yake tsula kuka.
"Ɗan tsaya mana Yaya."
Tayi maganar a nutse.
A hankali tasa hannunta na dama ta ɗaga fuskar Aadil tasa idanunta a cikin na shi. Daƙiƙu goma bayan nan sai ta haske yaron da lallausan murmushi, sannan ta ɗaga hannuwanta biyu ta miƙa mishi alamar ya zo.
Tun Zulai tana ƙarama, ba sau ɗaya ba sau biyu ba Hafiz ya sha ji Innaye tana yi ma Zulai kirari da mai baiwar iya sarrafa ƙananun yara. Duk irin ƙwuiyar yaro da fitinarsa sai dai idan Zulai bata so ƙulla harƙalla da shi ba. In dai zuciyarta na son ɗa, to fa ko ke uwar ɗan sai dai kiyi haƙuri, domin idan za ta jera wata guda tana zuwa ɗaukar ɗa ko ƴa zuwa gidansu ana hana ta baza ta taɓa gajiyawa ba. Idan kuwa har yaro ya saba da ita to fa uwa da kanta za ki ji tana aika ma da Zulai yaron ko bata je ɗaukarsa ba.
A wancan lokacin, bai ɗauka baiwar na ta ya kai yadda Innaye take kururutawa ba sai yanzu da yaga ikon Allah. Aadil da kanshi ya miƙa ma Zulaikha hannu ta ɗauke shi. Ƙarin mamakin kuma yana zuwa jikinta ya kwantar da kanshi a kafaɗarta, sannu a hankali yake rage ƙarfin kukansa har zuwa sadda yayi ɗif! Kamar anyi ruwa an ɗauke.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun kwanciyar hankali. Godiya ya fara yi mata haɗe da kyawawan addu'o'i.
"Na gode Ƙanwata. Ubangiji ya baki duk abinda kike nema duniya da lahira. Allah ya jiƙan mahaifanki da gafara."
"Amin thumma Amin."
Ta amsa addu'ar da murmushi a fuskarta.
"Ya yi break fast ne a gida?"
Ta tambayeshi kafin ya ƙara cewa komai.
"A'a! Tun misalin ƙarfe uku na dare dai Mamanshi ta bashi nono, daga nan barci yake ta yi sai yanzu ya farka."
"To ba damuwa. Yanzu dai shigo min da kayayyakinshi, ina zuwa."
Ko kafin ya gama shigo da kayayyakin, Zulai ta haɗa tea mai kauri da zallar madarar peak ta 1,2,3 wanda take ma Imam amfani da shi idan ya je gidan ta zuba milo ba tare da ta sa suger ko ɗigo ba ta fara ba Aadil da ɗan ƙaramin cokali, yana sha tana mishi ƴan waƙe-waƙe da wasanni.
Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga yaron yana ƙyalƙyala dariya. Sai da ya ƙoshi taf sannan ta surka ruwa tayi mishi wanka fes! Kafin Hafiz ya bar gidan, har Aadil yayi barci goye a bayan Zulai, abinda sam bai samu ba a gurin Mamanshi wai don tsoron kar tsayayyun nonuwanta su faɗi.
Ganin ƙarfe goma sha ɗaya saura mintuna kaɗan yasa Hafiz miƙewa tsaye, sai da ya gama kai saƙonnin Zulaikha da zai tafi ma da Innaye cikin mota sannan ya koma a tsaitsaye ya bata abinda ke tsakaninshi da Kareema.
Tsananin murna da mamakin lamarin yasa bakin Zulaikha ya ƙi rufuwa, ta kasa cewa komai, har ya gama yi mata ƙarin bayanin cewa
"Wannan dalilin ne yasa komai rana in sha Allah zan tafi Faƙo ayau ɗinnan. Domin gobe da wuri nake so su Baba Abubakar su shigo su samu Abba Lurwanu aje wajen iyayenta maza. Tunda dai Mummy ta bani dama gaskiya ba na son a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba tare da anyi komai an wuce gurin ba."
"Uhmmm! Ai ni na ma kasa magana Yaya. Allah ya tabbatar da alkhairi. Lallai ma Aunty Kareema, wato shi ne ana ta kwasar love da Yayana ko a gista min..."
"A'a kar ki ga wani laifin Ƙurratul-Ayni.. Ni ne nan na umarceta tayi shiru da bakinta har sai lamarin ya fara nuna. Yanzu da ya kamata ki ji ba ga shi na faɗa miki ba?"
Ya ɗauki laifin komai ya jibga ma kansa don kawai ba ya so a ƙullaci rabin ransa.
Ita dai Zuly ta kasa daina dariya... Abubuwa da yawa ne suka haɗe a zuciyarta.
"Amma kuwa Bintu ta sani Yaya?"
Ta tambaye shi tana hasashen irin tashin hankali da haukar da Bintu za tayi idan ta ji irin gagarumin tashin hankalin da ke tunkaro ta.
"Bata sani ba. Amma zan faɗa mata idan na dawo."
Ya amsa a lokacin da ya kama hanyar fita daga falon.
Sallama suka sake yi, tayi mishi addu'ar Allah ya tsare ya kiyaye hanya sannan ya fice daga cikin falon. Tana tsaye jikin window tana hangenshi har maigadi ya buɗe mishi ƙofa ya fice daga gidan.
Labulen windon ta saki, ta koma tsakiyar falon sannan ta saki wata ƙaƙƙarfar dariya da yasa Aadil da ke bayanta motsawa kamar zai tashi, da sauri ta toshe bakinta don rage ƙarfin dariyar tana haɗawa da ɗan jijjiga shi.
"Bintu ruwa ya ƙare ma ɗan kada bai gama wanka ba, daɗina da gobe saurin zuwa..."
Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya a hankali don kar ta tashi Aadil. Zuciyarta cike da wani irin farin ciki mara misaltuwa.
******
Ƙarfe biyu da ƴan mintuna na tsakar rana ya isa Faƙo. Kamar ko wane lokaci, haka ƴan'uwa da abokan arziki suka tarbe shi da matsananciyar murna. Shi kuma ya buɗe bakin aljihu kamar yadda ya saba yayi musu yayyafin alkhairi.
Daƙyar ya samu ya ƙwaci kansa suka keɓe da mahaifansa, bayan sun sabunta gaisuwa ne yake sanar da su muhimmin abinda yake tafe da shi a wannan rana. Wani abu da ya lura da shi shi ne daga Innaye har Baffa farin ciki ya gaza ɓoyuwa a fuskokinsu daga jin wannan labarin, wannan shi ya ƙara tabbatar mishi lallai baƙin ciki da takaicin munanan halayen Bintu ya daɗe yana damun iyayensa.
Tambaya ɗaya da Baffa yayi mishi shi ne
"Ka faɗa ma Alhaji Lurwanu?"
"Ban riga da na faɗa mishi ba Baffa. Amma ina komawa gida in sha Allah ayau zanyi ƙoƙarin sanar da shi."
Ya amsa kanshi yana ƙasa.
"Lallai ya kamata ka sanar da shi da gaggawa, saboda kar su Abubakar su je ya zama ya ji labari daga bakinsu, ka ga idan aka yi hakan ba'a kyauta ba."
"In sha Allah zan faɗa masa ayau Baffa."
Bayan sun gama magana da su Innaye ya fita da nufin zuwa gidan Anty Balira ya gaishe ta. Wani arashi da ya tarar shi ne acan ya tarar da Aunty Rakiya da Aunty Ladidi sun je gaishe da Aunty Balira da tayi zazzaɓi kwanaki biyu da suka wuce.
Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokinsu, sa'ilin da suka gama gaisawa yake faɗa musu zai auri Kareema ƙanwar mijin Zulai. Addu'o'i kyawawa da fatan alkhairi suka yi mishi, sannan Aunty Balira ta tashi ta zagaya banɗaki.
Kuma kun san irin banɗakunan da ake yi a ƙauye, can nesa da ɗakunan gida ake yi saboda masai ne ake yi na gargajiya.
"Haba! Ko kai fa Hafizu? Amma me ake da mace mai mugun baƙin hali da kafirin munafunci da kissa irin Bintu?"
Kalaman da suka fara fita daga bakin Aunty Rakiya kenan bayan ta tabbatar Aunty Balira ba ta jin me take cewa.
Nan fa kamar an matsi bakunansu su biyun suka buɗe baki suka dinga kora ma Hafiz labarin irin cin kashin da Bintu tayi ta musu ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Amma saboda tsabar munafunci idan yana gurin sai ta dinga musu haba-haba kamar za ta haɗiye.
Suman zaune kawai Hafiz yayi yana jin waɗannan baƙaƙen labarai masu barazanar fasa mishi zuciya. Tabbas idanunshi sun buɗe, kuma ya fahimci kissa da munafuncin Bintu, amma bai taɓa tsammanin ta daɗe tana wasan kwaikwayo da fahimtarshi har na tsawon lokaci haka ba.
Bai ƙara shiga cikin tashin hankali ba sai da Aunty Ladidi ta ce
"Ni fa duk waɗannan munanan halayen nata abu ɗaya da idan na tuna har yanzu yake min ciwo a zuciya shi ne yadda da gangar ta so kashe Innaye... Yo ta so kashe ta mana. Tunda ai likitan nan na asibitin Nasin Ham (Nursing home) Ya faɗa ma Aunty Balira cutar da ke damun Innaye daban magunguna da alluran da aka yi ta zurkuɗa mata daban, har ya ƙara da cewa lallai duk likitan da ta ba Innaye waɗannan magungunan ta so kawai ta illata ta ne..."
"Waɗanne irin zantukan banza ne kuke faɗa ma Hafizu haka Rahina?"
Aunty Balira ta katse ta cikin tsawa da ɓacin rai.
Firgigit suka yi duk su biyun, sai a lokacin suka dawo hayyacinsu suka lura da wasu zafafan hawaye da ke kwaranya a idanun Hafiz. Duk da sun san gaskiya suke faɗa, sai kuma jikinsu yayi sanyi ƙalau da ganin irin hawayen da ke gudu akan fuskarsa.
Faɗa Aunty Balira ta rufe su da shi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, a ƙarshe ta ce su ɓace mata da gani tunda su ba su da hankali suna so su shiga tsakanin mata da miji.
Sum-sum suka saka hijabansu suka fice daga ɗakin, jikinsu sanyi ƙalau, kamar an sheƙa musu ruwan sanyi.
Kusa da Hafiz Aunty Balira ta zauna ta fara rarrashinshi da tausasan kalamai. Duk da ta nuna ɓacin ran abinda su Rakiya suka yi amma ko kaɗan bai ji ta ƙaryata maganganun da suka faɗa mishi ba.
Sai da ta daɗe tana rarrashinshi sannan daƙyar ya tsagaita sharɓen hawayen da yake yi. Ya ɗaga kanshi yana kallonta da idanunsa jajaye ya ce cikin rawar murya
"Amma... Amma... me yasa baku taɓa ankarar da ni ko ku fito ƙarara ku faɗa min irin abubuwan da ke faruwa ba...?"
"Ta ina za mu samu ƙwarin gwuiwar faɗa maka Hafizu bayan duk mun fahimci irin son da kake mata, sannan mun ga yadda idanunka suka rufe ruf a kanta. Ca nake don a sama maka sauƙi ne Baffa ya ɗauki Zulai sukutun da guda ya aura maka amma ka watsa masa ƙasa a ido?"
A karo na biyu duƙar da kanshi yayi ya cigaba da sharɓen hawaye, a zuciyarsa yake tuna yadda ya ƙeƙashe ƙasa ya biye ma Bintu ya kasa yi ma iyayensa biyayya. Ya daɗe a haka kafin ya iya tsayar da hawayen daƙyar! Ya laluba aljihunsa ya ɗauko damin kuɗi yayi mata alkhairi kamar yadda ya saba, ya bata na Ladidi da Rakiya, sannan ya bata wanda za ta raba ma ƴan'uwansa mata da suke uba ɗaya.
Jikinsa a sanyaye ya miƙe yayi mata sallama zai wuce, har zaure ta raka shi tana sake haɗa shi da girman Allah kar ya kuskura ya ce zai hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.
"Ka gode ma Allah da yasa idanunka suka washe akan halinta. Ka ga yanzu sai ka sake sabon lale akan zamantakewar da za kayi da ita. Mu dai Allah ya sani bamu riƙe ta arai ba."
Da haka suka rabu.
Ko da ya koma gida gurin Innaye, duk yadda ya so su sake tauna zancen ta ƙi bashi damar haka. Da murmushi a fuskarta take ƙara tabbatar mishi ita bata riƙe Bintu arai ba, kuma bata yafe mishi ba idan ya hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.
A karo na barkatai ya duƙa har ƙasa ya sake neman yafiyarta, ta ƙara jaddada mishi ta yafe sannan ya fita gurin Baffa.
A can ɗin ma dai zancen suka sake taunawa, a matsayin Baffa namiji, ya sake bashi shawarwari masu kyau na yadda zai zauna da Bintu, a yanzu, da kuma bayan ya ƙara aure. Kamar haɗin baki shi ma dai sake jaddada mishi yayi kar ya kuskura ya ce zai ɗauki wani mataki akan Bintu. Abinda ya wuce a barshi a wanda ya wuce.
Yamma liƙis ya bar Faƙo, bakunan iyaye da ƴan'uwanshi cike da addu'ar Allah ya maida shi Abuja lafiya.
Da yake tun yana hanya ya kira Abba Lurwanu ya sanar da shi akwai muhimmiyar maganar da yake so suyi, amma yanzu yana hanyar komawa Abuja, idan Allah ya sa ya koma lafiya kuma dare baiyi sosai ba zai tsaya a gidanshi suyi maganar.
Wannan dalilin yasa ko da ya shiga Abuja ƙarfe goma na dare ya wuce gidan Abba Lurwanu. Acan ya ci abincin dare, bayan sun gama tauna maganar neman aurenshi da Kareema sannan ya kama hanyar komawa gida.
Da wannan gajiya da ɓacin ran ne bayan isarsa Bintu ta so ta kunno ma kanta bala'i shi kuma ya karta mata kashaidi, haɗe da rantsuwar ba don rayukan mutane uku mafiya muhimmanci a gare shi ba (Baffa, Innaye, Aunty Balira) Da yanzu wani zancen ake yi tsakaninsu ba wannan ba.
************
Ta ɗauki tsawon mintuna ashirin a tsaye inda ya barta, jikinta sanyi ƙalau. Zuciyarta a cunkushe, ta ma rasa wani irin takamaimai tunani ya kamata tayi.
A ƙarshe dai da taga tsayuwar bazai fissheta ba sai taja ƙafafunta a sanyaye ta koma cikin falon. Har ta ɗofana mazaunanta akan kujera, sai kuma ta miƙe tsaye tsulum kamar an tsunguleta.
Wayarta da ke ajiye can gefe ɗaya ta ɗauka ta fara tafiya zuwa ɗakinta. A hannunta tana lallatsa wayarta, lambar Raudha ta lalubo ta danna mata kira ba tare da duba tsalawar da dare yayi ba.
Wayar tana daf da tsinkewa Raudha ta ɗauka da magagin barci sosai a muryarta.
"Bintu? Lafiya kike kuwa? Me ya faru?"
Ta jera mata tambayoyin a rarrabe.
"Yi haƙuri Raudha na tashe ki kina barci... Daman zan faɗa miki abinda ya faru bayan dawowar Hafiz ne..."
"Toh! Toh!! Ina jinki!!! Amma Ina fatan dai ya dawo miki da Aadil?"
Ta tambayeta da murya mai cike da ɗoki da sakankancewa.
"A'a! Bai dawo da shi ba."
Ta amsa da rawar murya.
"Alfarmarki nake nema don Allah Raudha."
Ta sake faɗa muryarta na ƙarasa karyewa sosai. Don tsabar fitina da bala'in da ta saka ma ranta duk yadda nonuwanta ke ciwo suna tsikarinta saboda yaye ko jin su ba ta yi. Ba komai ke ƙara karya ma Bintu zuciya ba sai idan ta tuno ita tana nan a birni irin Abuja Aadil ɗanta yana wulaƙantaccen ƙauye irin na su Innaye, ƙauyen da ko ita da girmanta bata taɓa gigin yin kwana ɗaya a ciki ba.
Ta sani aminci ne mai ƙarfi tsakaninta da Raudha. Babu wani alfarma da za ta nema gurin Raudha ta ƙi yi mata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 40