idanunta daga kan miyar suna kallon juna cikin ido.
"Na'am Hajiya"
Ta amsa a ladabce.
"Yau hannunki ne ya suɓuce kika loda nama haka da uban yawa a miya har aka rasa yadda za'ayi da shi?"
Ta tambayeta tana ƙara tsattsare ta da idanu.
"A'a Hajiya. Kawai dai ji nayi Auta ta ce Innayen ba ta da lafiya, shi yasa nayi sha'awar in ɗan ƙara musu naman... kuma ma fa da yanka biyu ne kawai na ƙara kam ukun da kika ce in dinga zuba musu."
Fuska a ɗaure ta buɗe baki za ta daka ma Rabi tsawa ta tuhumi ina ruwanta da ciwon Innaye sai Zulaikha ta sanyo kai cikin kicin ɗin, bakinta ɗauke da siririyar sallama. A hannunta riƙe da kular da aka zuba ma Innaye indomie.
"Barka da dawowa."
Ta faɗa a taƙaice, bayan ta yi ma Bintu kallo ɗaya ta kawar da kanta. Kai tsaye ta nufi gurin ajiye kwanonin wanke-wanke ta ajiye kular hannunta.
"Baba Rabi sannu da aiki. An gama abincin ne?"
Ta tambayi Rabi wacce tun bayan shigowar Zulaikha da kulolin ƙirjinta ke bugun tara-tara.
Ko kaɗan bata so shigowar Auta da kulolin a daidai lokacin da Bintu take cikin kicin ɗin ba. A yadda ta so, bayan ta kai musu abincinsu ne za ta ɗauko kula da farantan ta shiga da su cikin gidan ta wanke a sirrance kamar yadda ta wanke tukunyar da tayi amfani da ita ba tare da Bintu ta san an dafa ma Innaye indomie ba.
Amma yanzu ganin kular ta san dole Bintu ta tambayi me aka dafa saɓanin wanda aka gama girkawa yanzu? Ganin ba ta da mafitar da ya wuce amsa tambayar Zulaikha yasa ta ce
"Eh! Na gama. Je ki, yanzu zan shigo muku da shi..."
"A'a! tunda ga ni mene na wahal da kanki? Sannu da aiki. Bani kawai in wuce mana da shi."
Ta ƙarasa maganar idanunta na kan murfin kular miyarsu da ta gani a hannun Bintu, wacce take tsaye kamar mutum-mutumi, sai idanu kaɗai take iya rabawa a tsakanin su biyun, fuskarta a tamke ƙwarai kamar bata taɓa sanin wani abu dariya ba.
Tun ranar da suka zo gidan, a cikin wannan kular ake zuba musu abinci. Don haka bata tsaya jiran Baba Rabi da ke harhaɗa abinda za ta ce mata ba don ta hana ta ɗaukar abincin kawai ta ƙarasa gaban Bintu ta ɗauki kular da aka zuba farar shinkafar, ta miƙa hannu za ta zare murfin kular miyar daga hannun Bintu da sauri ta janye hannunta tare da aika ma Auta wata matsiyaciyar harara.
"Waccan kular da kika shigo da ita yanzu, me aka zuba a ciki?"
Ta jefa mata tambayar cikin fushi tana aika mata da kallon tsana a fili.
Duk cikin dangin mijin nata ta fi tsanar yarinyar, ko don ta kasance a mafiyawancin lokuta tana yi mata abubuwa na gatsali da raini ne? oho!!
"Au! Wai wancan kular?"
Ta mayar mata da tambaya cikin tambaya a raine, da kuma irin salon da ta san Bintun ta masifar tsana. Sai kuma ta ɗanyi murmushi tana kallonta cikin ido itama da yanayin kallon yadda ba kya so na ni ma ba son ki nake yi ba.
"Innaye, da kika tafi da ita asibiti ko karyawa bata yi ba kika yasar da ita a wulaƙance, ita na saka aka dafa ma indomie da soyayyen ƙwai. Bata isa ba ne ko ni ɗin ban isa in saka a dafa mata bane?"
Ta buɗe baki za tayi magana cikin masifa da ɗaga murya sai ta tuna Hafiz yana gidan, duk da akwai tazara mai yawa tsakanin ɗakunansu da kicin ɗin lallai idan ta ce za ta ɗaga murya zai iya jiyo ta. A matakin da ta ɗauki aniyar ɗauka kuwa, har su Innaye su bar gidan a fili dai baza ta taɓa nuna mishi wani alamu na tsana da ƙiyayyarsu da ke danƙare da zuciyarta ba.
Duk yadda ranta yakai ƙololuwa gurin ɓaci da tambayoyin rainin da Zulaika tayi mata sai kawai ta ɓuge da girgiza kai, ta saki ƙarfafan ƙwafa sau biyu. A wulaƙance ta saki murfin kular da ke hannunta ya faɗi ƙasa sannan ta fice daga cikin kicin ɗin da sassarfa.
Tana da ƙaramin kicin a jikin ɗakinta da take amfani da shi ita kaɗai, don haka can ta nufa zuciyarta cike da saƙe-saƙen yadda za ta saka aci mata uban Zulaikha la'ada waje kafin su bar garin Abuja, wannan alƙawari ne ta ɗauka ma kanta.
Fuska a dame Baba Rabi ta kalli Zulaikha ta ce
"Auta Ba kiyi kalar yara masu rashin kunya ba. Saboda Allah me yasa kike son ɓata wayon ki da kyakkyawar tarbiyar da nake gani a tare da ke ta hanyar biye ma Hajiya.? Matar yayanki ce fa..."
"Ke baki ga yadda take mana bane Baba Rabi? Don kawai mu ƴan ƙauye ne sai mu zama ababen wulaƙanci da tozartawa a gurinta? In dai za ta taya na rantse da Allah ni kuma sai na sayar mata. Allahn da ya halicce mu bai wulaƙanta mu ba babu wata ƴar adam da zan zauna ta wulaƙanta mu."
Murfin kular ta ɗauko ta rufe ta sungumi kular miyan cikin fushi bakinta a gaba ta fice daga cikin kicin ɗin.
Tana zuwa falo, suka yi kiciɓis da Hafiz shi kuma ya sauko daga sama inda ɗakunansu suke. Duk da yadda ƙirjinta ya buga daram saboda tunanin yadda ya gaji da buga ƙofa ta ƙi buɗe masa da safe har ya gaji ya tafi. Ko kaɗan bata bari fuskarta ya nuna tsorata ba, sai ma ƙara murtukewa da tayi ta ƙara turo baki gaba kamar zai taɓi bango. Ja tayi ta tsaya tana kallonshi kamar yadda yake kallonta.
"Sannu da dawowa."
Ta faɗa cikin guna-gunin da ba ta da tabbacin ya ji ko bai ji ba.
A ɓangarensa kuwa, da mamaki sosai a fuskarsa yake kallonta. Bai manta yadda jiya ya kora mata kashaidin kar ta kuskura ya sake ganinta a ɓangarensu ba. Hallau bai manta yadda ya so ya lakaɗa mata dukan tsiya kafin ya fita ofis Allah ya taimaketa ta hanyar kulle ƙofar da tayi ta bar makulli a jiki ba.
Haushin jiya da yau ne suka taso suka ƙara turnuƙe shi, don haka cikin tsawa ya ce mata
"Me ya kawo ki nan? Ban faɗa miki kar in sake ganinki a ɓangaren nan ba...?"
Da sauri ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa
"Ni ma fa ba son raina na shigo nan ɗin ba. Innaye ce ta ce lallai daga yau ni zan dinga zuwa karɓa mana abinci, idan mun gama kuma in kwaso kulolin in shigo da su, idan kuma baka yarda ba, sai ka je ka tambayeta."
"Barka da dawowa Uban ɗakina."
Muryar Baba Rabi a ladabce ya sauka a kunnuwanshi.
Harara ya galla ma Zulaikha sannan yaja tsaki ƙasa-ƙasa. Ƙoƙarin sassauta murya yayi ya amsa gaisuwar Baba a mutunce kamar yadda ya saba. Karaf! Idanunsa suka faɗa kan sabbin kulolin da ya siyo anan falon, inda ya barsu har lokacin a gurin suke.
Umarnin kwashewa zuwa kicin yayi ma Baba Rabi bayan ya nuna mata waɗanda ya siyo ma Innaye, ya kuma gargaɗe ta kar a sake zuba ma Innaye abinci cikin tsaffin kuloli saɓanin sababbin da ya siyo.
Ko da ya waiga inda Zulaikha ke tsaye, babu ita babu dalilinta. Abinda bai sani ba tun da ya fara amsa gaisuwar Baba Rabi saɗaf-saɗaf ta fice daga cikin falon.
*******
Ɗabi'a ce da suka taso suka tarar da Innaye a cikinta jiran sallah tun kafin lokacinta ya ƙarato. Har yanzu kuma da ta manyanta bata bar wannan kyakkyawan ɗabi'a ba, sai ma ƙara ƙaimi da tayi.
Ƙarfe shida da minti goma ta shige banɗaki ta ɗauro alwala. Wuf! Zulaikha tayi ta ɗauki flask ɗin da ake zuba musu ruwan zafi ta fice daga ɗakin, daman damar da take jira kenan.
Hatta hijabin jikinta da kusan ko wane lokaci ba ta rabo da shi a jikinta sai a hanya ta sanya. Kai tsaye ta nufi can cikin gidan ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, tana tafe tana kalle-kallen yadda kyawawan shuke-shuken fulawoyi suka ƙara ƙawata tsakar gidan, kuma da yake suna samun kyakkyawan kulawa daga mai aiki na musamman da aka ɗaukar musu, luf-luf suke gwanin ban sha'awa kamar a lokacin damina.
Ko da ta isa ƙofar babban falon, sau ɗaya ta danna ƙararrawar neman izini kafin ta murɗa hannun ƙofar ba tare da jiran izinin shiga daga can ciki ba.
Kasancewar lokaci ne da in dai suna gida su biyun za'a same su cikin nishaɗi ne da yanayi na soyayya. Ko a yanzu, suna zaune akan doguwar kujera, fiye da rabin jikin Bintu gaba ɗaya a jikin Hafiz take, suna sanye da kayan shan iska na turawa. Ga ɗan ƙaramin teburin glass nan a gabansu ɗauke da yankakkun kayan marmari.
A mamakance suka ɗaga idanu suna kallon Zulaikha wacce ta bayyana a gabansu tsulum kamar an jefo ta. Ita kanta sai a lokacin ta lura da irin katoɓarar da tayi, don haka da saurin gaske kuma a daburce ta juya baya tana soshe-soshe hankalinta a tashe.
"A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim."
Ta janyo a'uziyyar a ruɗe, domin duk iya tsawon rayuwarta wannan shi ne karo na farko da taga mace da namiji a cikin makamancin irin wannan halin.
Tsananin ɓacin rai da baƙin ciki cakuɗe da dunƙulallen takaici yasa Bintu ta kasa magana. Sai kawai ta mayar da kanta kan ƙirjin Hafiz ta kwantar, ta lumshe idanunta tana jan numfashi sama-sama saboda ɓacin rai.
A ɓangaren Hafiz kuwa duk da sanin da yayi Zulaikha ba ta da hankali, bai taɓa tsammanin rashin hankalin nata ya kai haka ba. Ko da ya buɗe baki da nufin zazzaga mata bala'i sai ya rasa ma abinda zai ce mata, domin da ace masifa da bala'i ko duka na saka ɗan'adam ya kiyayi lamarin wani, lallai da tuntuni Zulai ta daɗe da fita daga cikin harkokinsa gaba ɗaya.
A karo na barkatai ya sake kallon yadda take ta dawurwura guri ɗaya, ita bata fita daga falon ba kuma ita bata jiyo ta fuskance su ba balle har ta faɗi abinda ya shigo da ita a daidai irin wannan lokacin.
"Me ya kawo ki?"
Yayi ƙarfin halin tambayarta da shaƙaƙƙiyar murya.
"Dama... Dama... Innaye ce ... ta ce... Dama... in zo in karɓi ruwan zafi..."
Ta faɗi maganar a rarrabe tana zazzare idanu a tsorace kamar za ta kife a gurin.
Ta riga ta gama yanke ma ranta lallai mai hana Yaya Hafiz cin ƙaniyarta a daidai wannan lokacin sai dai wani ikon Allah, don haka kawai sai ta fara matsar ƙwallah, ta san ko ta gudu sai ya bi ta har gaban Innaye ya tattaka ta, shi yasa ma bata yi yunƙurin gudu ba.
Sai dai ga mamakinta, tana jiran ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta sai ji tayi ya sake cewa da shaƙaƙƙiyar murya.
"Je ki dafa a kicin."
A kiɗime ta juyo tana kallonsu kamar bata ji abinda ya faɗa da kyau ba. Sai kuma ta sake juya musu baya da sauri tana ƙyaƙƙyafta idanu. A hanzarce kuma sai ta kama hanyar zuwa kicin ɗin har tana haɗawa da gudu-gudu.
"Ke! Ke!! Ke!!! Ina za ki?"
Bintu ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa haɗe da jefa mata tambayar.
Cak! Taja ta tsaya a inda take ƙafafunta na rawa, amma bata juyo ta kalle su ba, kuma bata amsa tambayar da Bintu tayi mata ba.
"Sweethert? Wai ko dai ka manta da wa kake magana ne? Ba fa Rabi ba ce mai aikinmu. Zulai ce da ta zo daga ƙauye kake cewa ta shiga kicin ɗina mai ɗauke da kayan girki na zamani ta dafa ruwan zafi. Ta iya amfani da Gas ko electric cooker ne? Ko kuwa so kake ta haddasa mana gobara saboda jahilci da ƙauyancinta?"
Maganganun Bintu masu kama da saukar tafasasshen dalma a zuciyarta suka sauka a kunnuwanta.
Jikinta a sanyaye ƙwarai ta juyo tana kallon Bintu da tun da ta faɗi maganganun ta maida kanta ta kwantar a ƙirjin Hafiz kamar ba ita ta faɗa ba. A muzance, ta kalli Hafiz da shi ma ita yake kallo, idanunta ciccike da hawaye.
Shi kuwa na shi idanun ɗauke da wani irin yanayi ne da baki bazai iya fassarawa ba. Kawar da fuskarshi yayi daga gare ta ya mayar kan matarshi, kafin ya amsa mata da cewa
"Kuma fa haka ne My dear. Wallahi shaf na manta."
Sai kuma ya sake mayar da idanunshi kan Zulaikha ba tare da wani yanayi na tausasawa ba ya ce
"Ke ajiye flask ɗin nan. Yanzu idan mun tashi Bintu za ta dafa ruwan mu taho mata da shi, daman akwai magunguna da alluranta duk za mu haɗa mu taho da su. Ki gaishe ta da jiki, na dawo ofis ɗazu a gajiye ne shi yasa ban shigo ba."
Baza ta ce ga sadda ta ajiye flask ɗin ba, balle kuma ta bada labarin yadda aka yi har ta fice daga falon. Kawai ta tsinci kanta ne a ƙofar ɓangarensu tana tafe kamar ana jaye da ita saboda tsananin tashin hankali.
Har ta sa hannu za ta murɗa hannun ƙofar ɗakin sai kuma ta fasa, can kusa da famfo taje ta tsuguna, tasha kukanta ta gode ma Allah kafin ta ɗaura alwala ta shige cikin ɗaki. Har wannan lokacin, jin ta take a muzance. Duk da ba yau ne farau da Bintu take ci mata mutunci da tozarta ta ba, amma bata taɓa gurza mata wanda ya tsaya mata arai kuma ya ƙona mata zuciya irin wannan ba.
A yadda take ji a ranta gidan da komai na cikinsa ya gama fice mata arai. Babu abinda take so irin ta buɗe ido ta ganta a ƙauyensu. Ko da ta shiga cikin ɗakin, sai jan gefen hijabi take yi tana rufe fuskarta, sai kuma Allah ya taimaketa ta tarar Innaye na sallah, bata ɓata lokaci ba itama ta kabbarta sallah.
Tana idarwa ta haye kan gado ta duƙunƙune jikinta da bargo kamar me jin sanyi. Tana jin shigowarsu Hafiz da Bintu ta sake ɓoye kanta, kamar bata san Allah yayi ruwansu a cikin ɗakin ba.
"Zulai barci take yi ne?"
Bintu ta tambaya da karaɗin murnar da Zulaikha ta rasa ko ta mece ce.
Ba Innaye da aka tambaya ba, hatta Hafiz sai da ya kalli Bintu da irin kallon nan na mamakin yau kuma ke ce kike tambayar Zulai?
Lura da irin katoɓarar da tayi yasa tayi saurin gyara maganarta da cewa
"Gani kawai na yi ta kwanta ta rufa duk da zafin da ake yi. Ka san baya ba ta da kaɗan, idan ba ta da lafiya ne ai gara ta faɗa a bata magani. Anyway, Innaye ya ƙarfin jiki?"
A hankali ta ajiye casbahan hannunta a gefe ɗaya ta ƙura ma Bintu idanu. A zuciyarta, addu'a take yi Allah ya kare ta da zuriarta daga sharrin Bintu. Dubi dai yanzu yadda take tambayarta ƙarfin jiki da kulawa da damuwa a fuskarta da yake a gaban Hafiz ne, kamar ba ita ce ta wulaƙantata ɗazu a asibiti ba.
"Auta lafiyarta ƙalau. Ni kuma jiki na da sauƙi Alhamdulillah."
Ta amsa da yanayi na ba yabo ba fallasa, bayan ta yi matuƙar ƙoƙari gurin kawar da tunanin da ke danƙare a zuciyarta.
Irin kallon da Innaye ta ƙure ta da shi, shi ya ɗan sanyayar mata da jiki. Nan take ta fara addu'a a zuciyarta kar Allah yasa Innaye ta tona mata asirin irin yadda ta banzatar da ita ɗazu a asibiti. Ko da taji amsar da Innayen ta ba ta ta kasa sakin jiki ta cigaba da kwarkwasa kamar yadda ta shiga cikin ɗakin da farko.
Ganin har lokacin idanun Innaye na kanta, sai ta fara jin ta a muzance. A dole ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa ƙirjinta na bugawa kaɗan-kaɗan. Ta kasa ƙara cewa komai, sai Hafiz ne ya amsa maganar Innaye da cewa
"Ma sha Allah! Allah ya ƙara sauƙi Innaye. Ga magunguna da alluranki nan Bintu ta taho da su.
Kuma kin ji wani ikon Allah ashe duk irin ciwukan da aka yi tsammanin samu a jikinki ma ba'a samu ba. Zazzaɓin cizon sauro ne kawai sai typhoid da aka samu a jininki. Kin ga a wannan karon dai ya zama dole Innaye ki haƙura da kwanciya babu gidan sauro. Kuma shan ruwan ƙauyen nan ma ya zama dole ki haƙura da shi, zan dinga aika miki da tsaftataccen ruwa duk ƙarshen wata in sha Allah, domin likitoci sun tabbatar da hanya ta farko ta kamuwa da typhoid daga ƙazantaccen ruwan sha ne..."
"Hafizu, wannan ruwan da kake kira da ƙazantacce tun kafin a haife ka shi muke sha, muke komai da shi. Kuma kai ɗin ma kafin barowarka ƙauyen ƙazantaccen ruwan nan dai kake sha, kuma ya rayar da kai har zuwa girmanka."
Innaye ta katse shi da ɗan murmushi a fuskarta na jin daɗin yadda ƙarara ɗan nata ke nuna damuwa da lafiyarta.
Ƙara gyara zama yayi yana cigaba da yi mata ƙarin bayani, a fuska da muryarsa babu abinda ke fita sai matsananciyar ƙaunar mahaifiyarsa.
"Duk da haka dai Innaye. Kin san yanzu abubuwan sun canja ba kamar da ba. Yanzu cututtuka ba su wuyar shiga jikin ɗan Adam. Ya zama dole mu dinga ƙoƙarin kiyaye duk abubuwan da aka tabbatar suna da rawar da suke takawa wajen ɗabbaƙa samuwar cututtuka a jikinmu. Amma idan baki gamsu ba ga Bintu nan, tunda ita likita ce za ta miki cikakken bayanin da za ki fahimta na abubuwan da ya kamata ki kiyaye."
Ya maida idanu kan Bintu yana jiran tayi ma Innaye ƙarin bayani kamar yadda ya nema. Abu ɗaya da bai sani ba shi ne Bintu dai ba baka sai kunne, sai a yanzu ne duk irin cin kashi da tozarcin da tayi ma Innaye tun bayan fitarsu yake dawo mata arai, a tsorace take sosai kar Innaye tayi suɓul da bakan furta ɗaya daga cikin abinda ta aikata mata.
"Eh! Haka ne My Dear. Uhmmm! Innaye don Allah ki kiyaye. Duk abinda zan faɗa My dear ya riga ya faɗa, yanzu dai bari in haɗa alluran inyi miki in baki magungunan. Ina fatan kin ci abinci?"
Ta ƙarasa da tambayar har lokacin ta kasa ɗaga idanu ta kalli Innaye cikin ido.
"Eh na ci."
Innaye ta amsa idanunta na kallon irin ruɗewar da Bintu take ciki. Duk da tayi hasashen me ya ɗaga hankalin Bintu cikin ƙanƙanin lokaci haka, amma sam bata yi niyyar tona abinda tayi mata ba. Idan tayi haka kamar bata gode Allah da ya dube ta ya haɗa ta da Karimatu a lokacin da Bintu ta so tozarta ta bane.
Tana kallo Bintu ta haɗa allurai har guda biyu tayi mata. Sannan ta ɓallo magunguna kala huɗu ko wanne ɗai-ɗai ta miƙa mata. Hafiz ya buɗe ɗaya daga cikin gororin ruwan da ke cikin ɗakin ya zuba a kofi ya miƙa mata.
Sai da tasha magungunan ta haɗiye sannan Bintu ta fice daga cikin ɗakin bayan ta basu uzurin za ta je ta amsa waya. Nan ta bar Hafiz suna cigaba da hira da Innaye ita dai ta cikawa bujenta iska tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Har lokacin bata daina addu'ar Allah ya kulle bakin Innaye kar ya bata ikon tona asirin tozarcin da tayi mata a asibiti.
Duk abinda ke faruwa har zuwa ficewar Bintu, da ficewar Hafiz bayan an kira sallar isha'i, Zulaikha tana jin su. Ko ƙwaƙƙwaran motsi bata yi bane domin ba ta ƙaunar tozali da ɗaya daga cikin fuskokin su biyun.
"Auta? Wai lafiya kike kuwa?"
Innaye ta jefa mata tambayar lokacin da ta yaye rufar da tayi ma kanta, ta miƙe ta zauna akan gadon tana mutsuttsuka idanunta kamar wacce ta farka daga barci.
"Lafiya ƙalau. Kawai dai ba na jin daɗi ne."
Ta amsa fuskarta ba walwala.
"Wallahi Innaye duk na ƙosa mu koma gida."
Ta sake faɗa fuskarta na bayyana gaskiyar maganar daga zuciyarta ne.
Daƙiƙu talatin Innaye ta ɗauka tana karantar yanayinta. Irin shirun da Auta tayi tun bayan da ta idar da sallah, ta san ba haka kawai bane. Amma tunda bata faɗa mata komai ba sai bata matsa mata da tambaya ba, don wani sashe na zuciyarta na tunanin ko don maganar auren da tayi mata ɗazu ne ya canja yanayinta? Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ce
"Ki kwantar da hankalinki. Kamar gobe ne za mu koma gida in sha Allahu."
*****
Duk da kasancewarta cikin mutane masu nauyin barci, irin numfarfashin da Innaye take ja sama-sama tana saukewa a wahalce ya fi ƙarfin a ce ta gagara farkawa.
Bayan ƙarfin nishin kuma kusa da kusa suke kwance. Tun tana jin nishin kamar a mafarki, har dai daga baya ta tabbatar ba mafarki take yi ba don haka ta farka a firgice.
"Innaye? Inna lillahi... Me yake damunki?"
Ta jera mata tambayoyin a ruɗe. Kafin ta amsa da saurin gaske ta miƙa hannu ta taɓa wuyan Innayen, matsanancin zafin da taji yasa tayi saurin ɗauke hannunta a gaggauce.
"Subhanallahi... Jikinki zafi sosai Innaye... Zazzaɓi kike yi ne? Bari in kira Yaya."
Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ta yunƙura za ta sauka akan gadon a galabaice Innaye ta riƙo hannunta.
"Dare... dare ya yi... ki ƙyale.. shi zuwa safe."
Tayi maganar daƙyar, da yanayin da ke bayyana tana cikin mawuyacin hali.
Tafin hannun Zulaikha da ke cikin nata ta sake riƙewa sosai, ta ja hannun a hankali har zuwa kan goshinta, a jiga ce ta sake cewa
"Kaina ciwo sosai kamar zai faɗi, ki kama min Auta."
Ta sake faɗa a wahalce.
Kasancewarta mai saurin kuka tuni har hawaye ya wanke mata fuska. Ta matsa sosai kusa da Innaye ta ɗauki kanta ta ɗora akan cinyarta.
Kamun kai tayi mata kamar yadda ta buƙata, bayan ta gama sai ta cigaba da tofa mata duk irin addu'ar da ya zo bakinta.
Ko da ta ɗaga idanu ta kalli agogon da ke maƙale a bango cikin ɗan madaidaicin hasken da suke bari a kunne idan za su kwanta. Sai taga ƙarfe uku na dare saura minti takwas, sai a lokacin ita da kanta taga rashin dacewa kiran Yaya Hafiz a wannan tsakiyar dare.
Duk irin barcin da ke idanunta tuni ta neme shi ta rasa, a taƙaice ma idanunta bushewa suka yi, idanunta biyu tana hawaye tana tofe Innaye da addu'a har zuwa lokacin da ladanin unguwar ya kwaɗa kiran sallar farko.
A wannan dare, ta shiga cikin gagarumin tashin hankali ne irin wanda bata taɓa shiga ba a rayuwarta. Tun da tayi wayau bata taɓa ganin Innaye cikin ciwon da ya jigatar da ita ya fitar da ita a hayyacinta cikin ƙanƙanin lokaci irin haka ba.
Ko wannan ciwon da take yi har ya zama sanadiyyar da yasa suka baro garinsu zuwa Abuja bai mata tsanani haka ba. Bata taɓa tsammanin Innaye za ta kai asubahi a raye ba, ta gama fitar da rai da cewar Innaye za ta cigaba da rayuwa, saboda yadda numfashin ma a wahalce take ja tana saukewa daƙyar. Amma da yake rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke sai ga shi cikin hukuncin Allah ana tayar da iƙamar sallar asubah wani nannauyan barci yayi awon gaba da Innaye.
Minti ɗaya, biyu, sai ta kara kunnenta a hancin Innaye don ta ƙara tabbatar da barcin take yi ko dai ba barcin bane? Sai da ta tabbatar barcin ne kafin ta iya kwantar da kan Innaye a hankali bisa filo ta sauka daga kan gadon.
Ƙafafunta duk sunyi tsami, idanuwanta sun kumbura sunyi tulu-tulu saboda kuka. Jikinta a sanyaye ta shige banɗaki domin ɗauro alwala.
Ko da ta idar da sallah, bata tsaya yin Azkhar kamar yadda take yi duk bayan sallar asubahi ba tayi addu'a a gaggauce ta sake hayewa kan gadon tana ɗan tattaɓa jikin Innaye. Cikin hukuncin Allah kuma sai taji zazzafan zazzaɓin ya sauka gaba ɗaya, har ma wani zufa ne ya ɗan tsattsafo akan goshinta.
Gefen hijabin da ke jikinta tasa ta goge ma Innaye gumin tana sauke nannauyan ajiyar zuciyar samun nutsuwa.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 40