haka fuskarta lokaci ɗaya ya ƙayatu da farin ciki mara misaltuwa.
"Alhamdulillahi Hafizu Alhamdulillah! Barka da arziki. Allah ya raya mana yasa cikon musulunci ne? Yaushe ta haihu?"
Ta sake tambayarsa ta ma manta ya faɗa mata yanzu Bintun ta haihu.
Da fara'a shi ma a muryarsa ya sake amsa mata yanzu aka yi haihuwar.
"Ɗazu da za mu taho asibiti lokacin da take naƙuda ruɗewa da tashin hankali yasa na manta da wayar a gida. Sai da ta haihu na sami nutsuwar komawa gida na ɗauki wayata, yanzu wanka zanyi sai in koma asibitin."
"Ma sha Allah! Allah ya raya mana. Hafizu na ya ƙara girma, ya zama Baba."
Dariya ya kwashe da shi zuciyarsa cike da farin ciki.
Kafin ya katse wayar, kaf yayyinsa da suke cikin ɗakin sai da suka yi masa barka da arziki yana amsawa da matsanancin fara'a sannan suka yi sallama.
Wannan haihuwa da Bintu tayi shi ya dakushe kaifin damuwar da suke ciki na batun fasa auren Zulaikha. Hatta ita Zulan da tun zuwa karɓan kayan auren take cikin uwar ɗaki duƙunƙune akan gado tana kuka babu abinda ke fito da ita
sai ɗauro alwala sai da ta daure zuciyarta ta fito falo cikin yayyenta suna murnar ƙaruwar da ɗan'uwansu ya samu.
Fitar zancen haihuwar cikin gida da maƙwafta yasa ɗakin Innaye ya sake ɗinkewa da mata ana yi mata barka da arzikin samun jika. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Baffa ya fatattaki ƴaƴan masu aure suka wuce gidajen mazajensu.
"Haba Hafizu, raɗin sunan jaririn ne har sai na taka ƙafafuna zuwa Habuja? Ai ina ga wannan duk abu ne mai sauƙi. Ba sai na je ba..."
"A'a Baffa!"
Ya katse shi da sauri.
"Kar ka ce baza ka zo ba don girman Allah! Ka ga fa tunda aka yi haihuwar nan iyaye da ƴan'uwan Bintu ke ta safa da marwa a gidannan, sai ni ne daga ɓangarena babu wani shaƙiƙi nawa da zai zo takanas-ta-kano barka?"
"Kamar ya ba wanda zai zo daga ɓangarenka? Ca nake jiyan nan ka gama faɗa min irin hidimar da Alh Lurwanu da Iyalinsa suke yi tunda aka yi haihuwar?"
Baffa ya faɗa yana murmushi.
"Baffa hidima da ɗawainiyar gidan Abba Lurwanu daban zuwan da za kayi daban. Wallahi ko shi sai da ya tambayeni amma dai za ka zo ganin abokin na ka ko? Babban abin alfahari gare ni shi ne kai da kanka ka taka ƙafafunka zuwa muhallina ka sa albarka, kaga jariri, sannan ka raɗa mishi suna da bakinka. Saboda Allah Baffa ni kenan don ina birni sai kuma ace mahaifana baza su dinga zuwa gida na ba? Ka ga fa Innaye ta ce baza ta sami zuwa ba, gara ma ita ta taɓa zuwa ta ga inda nake. Amma kai tunda na fara aiki shekara bakwai kenan sau ɗaya ka taɓa zuwa Abuja, dalilin zuwan ma ɗaurin aure na ne. Don Allah kayi haƙuri Baffa, duka tafiyar fa ta yini ɗaya ne za kuje ku dawo. Don Allah Baffa, don girman Allah."
Ya ƙarasa maganar da magiya sosai a muryarsa, kamar zai fasa kuka.
Tunanin gaskiyar da ke cikin maganganun Hafizu da yasa shi amincewa zuwan, amma Allah ya sani ba wai don zuciyarsa tana son doguwar tafiya ba. A ganinsa, tunda shi Hafizu yana yawan zuwa ƙauyen, kuma ya ɗauki duk nauyin buƙatunsu dai dai gwargwado, ba ma su kaɗai ba, hatta ƴan'uwa da jama'ar gari suna ɗanɗana daga alkhairan Hafizu. Me yake buƙata kuma bayan wannan? menene zai saka shi da girmansa yayi ta jelar zuwa gidan yaro?
Tunda dai acan Habujan akwai Alhaji Lurwani, Baban Ibrahim abokin Hafizu, ya ɗauki Hafizun ɗa kamar yadda ya ɗauki ɗan shi Ibrahim, kuma ba don sun haɗa dangantaka ta jini ba, sai don kawai sun yi karatu tare da ɗan shi Ibrahim.
A taƙaice ma, hatta aikin da shi Hafizun yake yi shi ya nema mishi tare da ɗan shi Ibrahim. Duk wasu al'amura na Hafiz tsaye yake akai kamar ɗan shi na cikinshi, hatta hidimar auren Hafiz acan gidan Alhaji Lurwanu aka gudanar da komai. A ganinsa, da waɗannan dalilan me zai sa shi da ake yiwa kara ya dinga nuna rashin ta ido?
Amma tunda a wannan karon Hafiz ya nace za su shirya shi da ƴan'uwansa uku da Liman da yake Amininsa suje su dawo. Tunda dai tafiyar ta rana ɗaya ce, in yaso daga can ma sa biya gidan Alhaji Lurwanu su ƙara yi masa godiya kan ɗawainiyar da suke yi shi da iyalansa akan Hafizu ba tare da gajiyawa ba.
"Shi kenan! Zan zo. Amma ba ni kaɗai ba. Da su Babanka Abubakar za mu zo da Malam Ahmad Liman. Yaushe ne ranar tafiyar?"
Da murna sosai a muryarsa yake jera ma Baffa kalaman godiya saboda tsananin jin daɗin amincewa zuwa gidanshi da yayi. Har sai da Baffa ya dakatar da shi da cewa godiyar ta isa haka.
"Wallahi na ji daɗi sosai Baffa. Yanzu dai ka ga ƙarfe sha biyun rana. Zuwa ƙarfe biyu Mal Musa zai kamo hanyar zuwa, na san dai duk yadda ake ciki in Allah ya yarda magrib a Faƙo za tayi mishi, idan ya kwana. Gobe da asubah sai ku shirya da wuri ku kamo hanya, yadda za ku iso da wuri, idan za ku tafi sai in yanka muku tikitin jirgi zuwa Kaduna, daga can sai kuyi shatar mota zuwa gida."
"To babu damuwa. Allah ya kawo shi lafiya."
*****
Kamar yadda Hafiz ya tsara, washe gari ƙarfe goma sha ɗaya na safe a gidan Hafiz tayi ma su Baffa. Sun isa yana gurin aiki, baiyi niyyar tafiya aiki a ranar ba. Amma kiran gaggawa da aka yi mishi a Ofis yasa shi fita babu shiri, da misalin ƙarfe goma saura kwata.
Da yake tun kafin ya fita ya jaddada ma Bintu su Baffa suna nan zuwa barka. A gabanshi, da murna sosai ta karɓi maganar har tana cewa
"Lallai abokin na Baffa ya zo da farin jini, daman bai taɓa zuwa gidannan ba. Allah ya kawo su lafiya."
"Ƙwarai kuwa. Ameen ya Allah."
Ya amsa yana dariya. A gaggauce ya sake mata sallama da cewar bari ya je ya dawo kafin su Baffa su iso.
Yana fita daga ɗakin taja wani dogon tsaki ta raka bayanshi da harara. Ranta a ɓace ta fice daga ɗakinshi zuwa na ta, ta kalli Raudha da take zaune gefen gado tana riƙe da Baby ta fara faɗa mata abinda ke shirin faruwa, bayan ta gama faɗa mata ta ƙara da cewa
"Na san shegen iyayin My dear ne yasa shi cewa su zo ganin Baby. Ai kam na rantse da Allah ba baƙauyen da ya isa yazo gidana ya damuƙa min baby da hannuwansu da suka saba damuƙa kayan cuta. Don haka idan suka iso, Raudha ki naɗe baby da showel da kyau sannan ki saka shi a abin ɗaukar can nasa mai kama da gado, ki kulle net ɗin kija zip ki rufe, sannan ki ɗaure belt ɗin yadda baza su taɓa iya buɗewa ba. Kin san ƙauyawa ne sosai, na san basu taɓa ganin irin abin saka jaririn nan ba balle su iya amfani da shi."
Ta mayar da idanunta kan ƙanwarta Mashkura da take tare da ita tunda aka yi haihuwar ta cigaba da cewa
"Mashku idan kin kai musu Babyn ki matsa su ganshi daga cikin gadon ba sai sun taɓa min ɗa ba. Atoh! Ni kaɗai nasan wahalar da na sha gurin haihuwarsa don haka kwanaki biyar da zuwansa duniya bazanyi sakacin da za'a goga masa cuta ba."
"Kina da gaskiyarki Madam! Ban ga laifinki ba. Malam bahaushe ma cewa yayi taya Allah kiwo ya fi Allah na nan. Balle ƙauyawan nan da tsubbace-tsubbace na tsiya yanzu haka sun ƙullo wani abun da za su shafa ma yaron a matsayin tsarin jiki. Gara su kalle shi daga nesa kallon kura."
Raudha ta faɗa da salon ingiza mai kantu ruwa.
Ita dai Mashkura bata ce komai ba, amma fuskarta kawai za'a kalla a ga yanayin rashin jin daɗi. Kamar dai bata ji daɗin maganganun Yayan nata da na ƙawarta ba. Amma dai bata ce komai ba, domin a ganinta gidan Bintu ne, iyayen mijinta ne, kuma ɗanta ne. Tana ikon tsara duk abinda take so kan iyalanta.
Bayyanannen kamannin da ke tsakanin Baffa da Hafiz yasa tun kafin Mal Musa ya faɗa ma ma'aikatan gidan wanene Baffa a gurin Oga su da kansu suka fahimci haka. Da girmamawa sosai suka dinga zubewa har ƙasa suna gaida su Baffa, bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu Mal Musa yayi musu jagora suka shiga cikin falon gidan daƙyar, domin da sun dage su a shimfiɗa musu tabarma su zauna a harabar gidan ba sai sun shiga ba.
Sai da Mal Musa ya kira Hafiz ya faɗa masa halin da ake ciki, shi kuma ya kira Baffa yai ta masa magiya sannan suka amince da shigarsu cikin falon gidan.
"Mahaifin Oga ne da ƴan'uwansa. Ki kawo musu abin sha da abubuwan taɓawa sannan ki shiga ciki ki faɗa ma Hajiya isowarsu."
Mal Musa ya faɗi haka ga Rabi.
Cikin ƙanƙanin lokaci Rabi ta cika gabansu da lemu kala daban-daban da ruwan gora. Ta haɗo musu da snacks saboda a lokacin bata gama abinci ba.
Jikinta na rawa, ta haura sama zuwa ɗakin Bintu don ta faɗa mata zuwansu Baffa.
"Rawar jikin miye kike yi kamar wasu baƙi ne na musamman suka zo?"
Bintu ta daka ma Rabi tsawa da tambayar haka bayan ta saurari abinda ke tafe da ita.
Sakalau Rabi tayi da baki tana kallonta, sai kuma ta ce
"Ba komai Hajiya. Bari in koma kicin, sai kin fito."
Jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin. Da kunnenta taji sadda Bintun ta raka ta da dogon tsaki. Zuciyarta cike da mamakin halayen Bintu na ƙin iyaye da dangin mijinta don kawai sun kasance ƙauyawa.
Saboda Allah ta ina aka taɓa haka? Kina son ɗansu amma ba kya son iyayen da sukai sanadin zuwansa duniya?
"Allah ya kyauta."
Ta faɗa a fili sannan ta ƙarasa sauka ƙasa ta wuce kicin. Bayan ta faɗa ma su Baffa ga Bintu nan zuwa.
Kafin Bintu ta sauko Mashkura ta fara turowa da ɗan jariri, an naɗe shi a ɗan ƙaramin abin ɗaukansa mai kama da godo kamar yadda Bintu ta tsara.
Da fara'a a fuskar Mashku ta gaishe su sannan ta matsa kusa sosai tana nuna musu fuskar babyn kamar yadda Bintu ta umarceta.
"Sannu yarinya, Allah ya raya. Abokin namu tsoron gamuwa da mu yake yi aka naɗe shi a cikin gado don kar muyi masa rubdugu?"
Liman Malam Ahmad ya tambayeta yana dariya.
Ita ma dariyar tayi, ta kasa cewa komai sai sake riƙe abin ɗaukar babyn da tayi da kyau.
Baffa kuwa kai tsaye cewa yayi
"Ki ciro shi daga ciki a ɗauke shi, raɗa mishi suna za'ayi da addu'o'i."
A ɗan daburce Mashku ta kalli Baffa bayan ta ji abinda ya faɗa, sai taga yayi mata kwarjini sosai baza ta iya musa umarninta ba. Da ɗan rawar jiki ta aje abin ɗaukar akan kafet ta fara warware ɗaurin belt ɗin da aka ma yaron.
Karaf! Akan idanun Bintu da take saukowa daga can sama.
"Ke! Keh! Ke Mashkura? Me kike ƙoƙarin yi haka?"
Ta tambayeta cikin tsawa da ɗan ɗaga murya tun kafin ta ƙarasa sakkowa.
Bib-biyu ta dinga harhaɗa Step ɗin da ɗan gudu-gudu har ta ƙarasa sakkowa. Fuskarnan a ɗaure tamau, ko kallonsu Baffa bata yi ba ta sake daka ma Mashkura tsawar ta daina ƙoƙarin fito mata da Baby da take ƙoƙarin yi.
Da mamaki sosai a fuskokin su Baffa duk suke bin Bintu da kallo. Da farko kamar ba wanda zaiyi magana a cikinsu, sai kuma Baffa ya ce
"Ni ne na ce ta fito mana da shi mu ɗauke shi a raɗa mishi suna ayi mishi addu'o'i..."
"Yi haƙuri Baffa. Umarnin Likita ne ya ce kar a ringa damukarsa da hannuwa mabanbanta saboda jikinsa baiyi k'wari ba bazai yi wahalar d'aukar cututtuka ba..."
"Bintu?"
Hafiz da shigarsa cikin falon kenan ya tsinci maganar da take yi ya kira sunanta da mamaki sosai a fuskarsa.
"A hannun iyayen nawa ne zai kwashi cuta?"
Ya sake tambayarta ranshi a bace.
"Common dallah fito musu da Baby su d'auka in yaso ya kwashi cutukan duniya ba ma ciwo d'aya ba."
Da saurin gaske Mashku ta karasa warware belt ɗin ta fito da shi ta miƙa ma Baffa. Ko fushi yayi ne Allah masani. Bai karɓi yaron ba, sai Malam Ahmad ne ya miƙa hannu ya karɓi ɗan da murmushi a fuskarsa, duk a ƙoƙarinsa na shashantar da abinda ya faru.
"Lallai wannan aboki namu manomi ne. Kai ka ganshi Abubakar har ya fi sadda aka haifi Hafizu girma?"
Yayi maganar yana dariya idanunshi akan ɗaya daga cikin Ƴan'uwan Baffa.
"A lallai kuwa. Da alamun an samu Sarkin noma. Bana damuna za tayi albarka."
Baba Abubakar ya faɗa shi ma fuskarsa cike da murmushi. Idanunsa akan jaririn yana kallonsa cike da burgewa.
Bintu da take tsaye cikin matsanancin girgiza da tashin hankali don bata taɓa tsammanin bayyanar Hafiz a daidai lokacin ba rasa tudun dafawa tayi. Bayan zafafan tambayoyin da Hafiz ya aika mata waɗanda sam ba ta da amsarsu, a ƙarshe ya ɓuge da yi ma tilon ɗan nasu fatan kwasan miyagun cututtuka tana ganin wani mahaukacin kallo da yake aika mata daga inda yake zaune a ƙasa kamar zai cinye ta ɗanye.
Ita kuwa Mashkura daman tunda ta samu aka karɓi jariri daga hannunta ba wanda yasan sadda ta bar falon.
Tsakanin Mal Ahmad da Baba Abubakar, Baba Lukman, Baba Hamisu kuma raha suke tayi a tsakaninsu suna karɓa-karɓa da jaririn suna addu'o'i da yaba girmansa.
Ɓangaren Baffa kuwa babu wanda zai ce ga yanayin da yake ciki, fuskarsa a baibai take. Kuma har lokacin bai karɓi jaririn ba. Ya ƙura ma guri ɗaya idanu kamar yana tunanin wani abu.
Hafiz dai yana zaune a gaban iyayen nasa kan kafet, idanunsa a ƙasa kamar zai saka kuka. Idan ya ɗaga kai ya kalli Bintu da take tsaye a gabansu kamar mutum-mutumi ransa a ɓace sai kuma ya sunkuyar da kansa.
Ko da ake faɗin karin maganar nan ta ruwa na neman ƙare ma ɗan kada bata taɓa fahimtar cikakkiyar ma'anarta ba sai yanzu da nata ruwan ke neman ƙare mata.
Lura da tayi lallai idan bata yi gaggawar gyara wannan shirmen da ta tafka ba kwaɓarta na gaf da yin mugun ruwa yasa ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka sannan ta zube a ƙasa. Da rarrafe ta ƙarasa gaban Baffa ta riƙe gefen Babbar rigarshi ta fara jero mishi kalaman ban haƙuri cikin kuka da ƙanƙan da kai.
"Na tuba Baffa na tuba. Don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min. Kai mahaifi ne a gare ni idan baka yafe min ba ina zan saka kaina? Na rantse da Allah ba da gan-gan na so hana ku ɗaukar jaririn ba. Likitan yara Dr. Kauthar da ta fita yanzu kafin shigowarku ita ce ta ce lallai a kiyaye yawan ɗaukarshi saboda gudun kwasar cutuka domin fatar shi babu ƙwari. Don Allah kuyi haƙuri ku yafe min. Baba Abubakar ku ma don Allah kuyi haƙuri. Malam ku yafe min don Allah bazan sake ba. Don Allah kuyi haƙuri. My dear kai ma ka yafe min."
Irin yadda take rusa kukan tana magiyar su yafe mata ba ƙaramin tausayi ta basu ba.
Gaba ɗayansu basu wani ja da nisa ba suka ce sun yafe mata. Har suka sa baki Hafiz ya ce babu komai ya wuce. Bata daina kuka ba har sai da taga Baffa ya karɓi jaririn a hannunsa yayi masa addu'o'i.
Sannan ya miƙa ma Malam Ahmad ya sake yi masa huɗuba ya raɗa masa suna. Kafin ya raɗa sunan ko da ya tambayi Hafiz ko suna da wani zaɓin suna da suke so a raɗa ma yaron da sauri ta riga shi cewa, duk dai a ƙoƙarinta na ƙara share laifinta ta ce
"Malam ka raɗa masa sunan Baffa ne don Allah. Daman tun kafin in haihu na ƙuduri niyyar in dai namiji ne sunan Baffa za'a sa idan kuma mace ce sunan Innaye za'a saka."
Da wannan maganar da tayi yasa Malam ya raɗa ma yaron suna Aminu (Al'ameen).
Rabi da take kicin tana laɓe tana kallo kuma tana jin duk abinda yake faruwa babu abinda take yi sai dariya.
"Iya duniya ya fi iya mota."
Ta faɗa a fili tana sakin dariya ƙasa-ƙasa. Da saurin gaske ta koma gurin aikinta ganin Bintu ta taso daga gaban su Baffa ta nufo kicin ɗin da sauri.
Tun safe, ta saka Rabi tayi mata farfesun kaji a zambaɗa kayan ƙamshi da ɗan daddawa su dahu ruguf, ko za ta iya ci sosai saboda tunda ta haihu bakinta babu daɗi.
Tana shiga cikin kicin ɗin ko kallon Rabi bata yi ba ta ɗauki ɗaya daga cikin kulolinta masu tsada ta juye farfesun gaba ɗaya.
"Ki ɗauko farantai da cokula ki kawo min falo."
Ta ba Rabi umarni gaf da za ta fice daga cikin kicin ɗin.
Da kanta ta zuzzuba musu farfesun ta ajiye a gabansu tare da basu haƙurin su ci kafin a ƙarasa abinci. Ta miƙe za ta haura sama a fakaice ta kalli babynta da har lokacin yana hannun Mal Ahmad suna hira da Hafiz suna ta dariya.
Kamar ta ce ya kawo shi su ci abinci, amma tsoron kar ta sake ɓallo ma kanta ruwa yasa kawai ta wuce zuwa sama duk zuciyarta a ƙuntace.
Lallai da gaske idan ka ji ƙi gudu sa gudu ne bai zo ba. A irin wannan tsaka mai wuya da ta shiga cikin ƙanƙanin lokaci, bata taɓa tsammanin za ta iya samar ma da kanta mafita cikin sauƙi haka ba. Sai ga shi tsabar tashin hankali da tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Hafiz yasa ƙwaƙwalwarta buɗewa, ta aikata aikin basira, hikima, wayau da bata taɓa tsammanin za ta iya aikatawa ba.
"Hmmmm!"
Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta huro iska mai zafi daga bakinta, sannan ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga da siririyar sallama a bakinta. Duk jikinta a sanyaye, ga idanunta sun canja launi sun kumbura, alamun ta sha kuka.
Kallo ɗaya Raudha da take kwance akan gadonta tana daddanna waya tayi mata ta miƙe zaune da sauri. Idanunta warwaje ta ce
"Ƙawata lafiya? Me ya samu idanunki?"
"Uhmmm! Ke dai bari Raudha. Yau na tsallake rijiya da baya. Sai fatan Allah ya kiyaye na gaba."
Amsar da ta iya ba ta kenan ta shige banɗaki.
*****
Ƙwan zabi ƙwarya uku, kajin hausa manyan zakaru guda goma. Garin kukar miya mai kyau da garin busasshiyar kuɓewa su ne tsarabar da Baffa ya riƙo ma Hafiz da gidan Alh Lurwanu.
Duk yadda suka so tafiya da wuri sai da suka kai ƙarfe ɗaya da minti goma a gidan Hafiz. Sun ci abinci sunyi nak! Sannan Baffa ya ɗiba musu tsarabar ƙwan zabbi ƙwarya ɗaya, kaji guda huɗu, kuka da kuɓewa dai bai ɗiba musu ba, domin bai ga alamun cin tuwo a gidan Hafizu ba.
Baya ga haka ita kanta Innaye da ta bada kuka da kuɓewar da sunan iyalan Alh Lurwanu ta bayar.
"Ita kuma matar Hafizu fa?"
Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.
Sai da tayi dariya kafin ta amsa da
"Matar Hafizu ƴar gayu ce ta bugawa a jarida. Har muka gama zamanmu a gidan ko da kuskure bamu ji ta ambaci tuwo ba."
Dariya suka yi duk su biyun kafin ya sake mata sallama, ita kuma tayi mishi addu'ar Allah ya tsare hanya sannan suka fice daga gida.
Hafiz da kanshi ya tuƙa su a mota zuwa gidan Alh Lurwanu. Ya rabbi! Mal Bahaushe ya ce in da ba ƙasa nan ake gardamar kokawa. Wata irin tarba ta girma kuma ta musamman da basu taɓa tsammanin samun irinta ba suka samu a gidan Alh Lurwanu.
Duk da sun daɗe da shaida shi ɗin mutumin kirki ne. Amma a wannan ranar ya ƙara tabbatar musu da halayen kirki da karamcinsa. Ya kuma ƙara tabbatar musu da fa babu wani banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi, ko kuma banbanci tsakanin mutumin ƙauye da na birni.
Irin yadda ya sake a cikinsu suna hira da ɓaɓɓaka dariya irinta manya suna caccafkewa a tsakaninsu wanda bai sani ba sai yayi tsammanin aminai ne na ƙud da ƙud. Tun ana gobe za su zo Hafiz ya sanar da shi zuwan su Baffa, don haka ya soke duk wasu shirye-shiryenshi na ranar da za su zo.
Kamar wasu manyan baƙi da suka taho daga wata ƙasa, ƙayatattun girke-girke na musamman yasa aka yi musu. Bayan sun ci sun sha ya cika su da abubuwan arziki masu yawan gaske. A dole aka yi asaran tikitin jirgin ƙarfe biyu da Hafiz ya yanka musu aka sake booking ɗin jirgin ƙarfe huɗu.
Wani ƙarin karamci na musamman da yayi musu shi ne tun kafin su isa Kaduna akwai direba na musamman da Alhajin ya tura yake jiran isarsu. Suna isa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kwashe su da kayayyakinsu suka kama hanyar Faƙo a wata luntsumemiyar mota da idanu kaɗai zai bayyanawa mai kallonta mai masifar tsada ce.
Ƙarfe bakwai da rabi na yamma suna ƙofar gidajensu. Wannan tafiya dukkansu ba ƙaramin daɗinta suka ji ba, babu abinda ke fita daga bakunansu sai addu'ar fatan alkhairi ga Alh Lurwanu da duk zuri'arsa.
Ana sauke kayayyakinsu ba tare da ɓata lokaci ba direba ya juya zuwa Kaduna, duk yadda suka so ya tsaya ko abinci ya ci ya ce musu a ƙoshe yake. Ya tafi suna ta bin shi da addu'ar Allah ya tsare hanya ya maida shi gida lafiya.
******
Da mamaki a fuskarta take kallonsa. Da yake har ta fara barci ya tashe ta, sai tayi tsammanin ko kunnuwanta ne basu ji da kyau ba.
"Me ka ce Baban Yasin?"
Ta tambaye shi don ƙara tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiye mata.
"Na ce miki Hafizu ya kira ni ɗazu da rana, ina cikin Kaduna ya ce in sami mai POS a tura mishi da Akawun namba. To a taƙaice dai bayan an tura mishi ba a daɗe ba ya saka dubu ɗari. Bayan ya tura kuɗin ya sake kira na ya ce in samu motocin Bus guda biyu duk da tawa uku kenan musha mai, gobe idan Allah ya kaimu mu kwashe ku da sauran masu shirin zuwa suna mu kai ku Abuja..."
"Shi Hafizun ne ya faɗa maka akwai masu shirin zuwa suna gidansa har mota uku?"
Ta tambayeshi tana ɗan harhaɗe giran sama da ƙasa. Kafin ya amsa mata ta ƙara da
"Ai kuwa za ku mayar masa da kuɗinsa. Domin ko ni da su Ladidi ba ma wani shirin zuwa suna balle sauran ƴan uwa su ce za su je. Suyi sunansu lafiya, mu dai babu inda za mu je..."
"Wani irin zancen banza ne kike yi haka Balira? Matar ɗan'uwan na ku shaƙiƙi namiji ɗaya tilo ta haihu kuma haihuwar farko ku ce baza ku je suna ba?"
"To miye a ciki? Mun yi murna, kuma munyi addu'a Allah ya raya. Zuwa suna Habuja ne dai baza mu je ba."
Ta faɗa da dukkan gaskiyarta.
Kallonta yayi mamakinsa na ƙara girmama, sai kuma ya tuna tun bayan dawowarsu Abuja da daɗewa bai ƙara ji tayi mishi zancen zuwa gidan Hafizun ba. Lallai akwai wani abu da ya faru a wancan lokacin amma bata faɗa mishi ba.
Guri ya nema ya zauna a kusa da ita, a tausashe ya ce
"Me yake faruwa Balira? Ko akwai matsala tsakaninku da matar Hafizu ne?"
"Babu matsalar komai."
Ta faɗa da sauri. Domin a ganinta matsalar da ta shafi ɗan'uwanta daban! Haka zalika matsalar da mijinta zai sani daban. A ganinta babban kuskure ne ta kwaye ma ɗan'uwanta baya a gaban mijinta. Kowa da muhimmancinsa daban!
"In dai kuwa babu matsala suna dole sai kun je. Domin kuɗin da ya turo har mun ciccika tankin motocinmu da mai. Gobe sai tafiya da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe in Allah ya yarda. Bari ma in kira Baffa in faɗa masa halin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 40