Share this page
kamar yadda ita ma a ɓangarenta za ta iya yin komai don kare martabar Raudha. "Kin sani kin wuce komai a gurina Bintu. Faɗi duk abinda kike so kawai inyi miki ki ga aiki da cikawa." Cewar Raudha daga can ɓangaren da muryar da ke nuna da dukkan gaskiyarta take magana. Nannauyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke, ta lalubi gefen gadonta ta zauna sannan ta cigaba da magana. "Ina wannan mutumin naki na filin jirgin ƙasa wanda ke samar mana da ticket ɗin zuwa Kaduna a sauƙaƙe?" "Lurwanu? Yana nan. Me kike so yayi miki?" "Ki tura masa saƙo a darennan ya tanadar mana da ticket biyu na jirgin gobe da safe. Bazan iya ba Raudha, Wallahi tallahi bazan taɓa iya barin Aadil ya kwana biyu a ƙauyennan ba. Goben nan zan je in ɗauko shi, duk abinda Hafiz zaiyi ya daɗe baiyi ba..." "To me ma ya isa ya yi? Ai shi kansa ya san ba shi da gaskiya... Duk inda za aje a dawo kin fi shi gaskiya Bintu, kamar yadda kika fi shi girman haƙƙi akan Aadil har a gurin Allah... Don haka kar ma ki wani ɗaga hankalinki. In banda ma tun safennan bamu yi tunanin zai iya barin Aadil acan ba ai da tun ayau za muje mu ɗauko shi. Ki kwantar da hankali ƙawata..." Waɗannan maganganun na Raudha, su suka zaftare kaso arba'in cikin ɗari na damuwar da ke danƙare a zuciyar Bintu. Da wannan dalilin yasa bayan sun gama waya da Raudha har ta iya samun ƙwarin gwuiwar zuwa kicin ta haɗa tea mai kauri ta sha. Ta ɓalli paracetamol guda biyu ta haɗiya, ta sake yin wanka sannan ta bi lafiyar gado. Ko tunanin Hafiz bata yi ba balle tayi gigin zuwa ɗakinshi su kwanta. Abinda bai taɓa faruwa ba tsakanin su biyun raba makwanci tunda suka yi aure, in dai ba tafiya Hafiz yayi ba. ********* Washe gari tunda sassafe Hafiz ya ji ƙarar tada motar Bintu, yana kwance a kan gadonshi. Tunda ya tashi yayi sallar asubahi a makare saboda rashin barci da bai samu yi da wuri ba, ya kasa fita ya duba ta tashi ko bata tashi ba? Azkhar ma sama-sama ya yi ya sake bin lafiyar gado da nufin yin ramuwar barci. Ya kwanta kenan ya ji tashin motar Bintu, mamaki ne ya kama shi har ya tambayi kanshi. 'Ina Bintu take niyyar zuwa ba tare da ta faɗa mishi ba?' Sanin ko daga can asibitinsu ne aka yi mata kiran gaggawa tana faɗa mishi kafin ta fita yasa shi yin mamakin fitar tata a yanzu. A hankali ya ya ye bargon da yake lulluɓe da shi ya sauka daga kan gadon, ko kafin ya fita daga ɗakin ma har mai gadi ya buɗe mata get ta fice daga gidan. Don haka bai ɓata lokacin duba ɗakinta ba ya san ita ce ta fita, tunda direbansu ba ya nan. Idan ba ita ba wa zai ɗauki motarta ya fita da ita da sassafen nan. Ko da ya koma cikin ɗakinsa, har ya kwanta, sai kuma yayi tunanin bai kamata ya riƙe Bintu har ya banzatar da al'amarinta haka ba. Tunda su kansu iyayenshi sun roƙe shi alfarmar kar ya kuskura ya hukunta Bintu da laifukan da suka gabata. Wayarsa ya ɗauko, ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sannan ya kara wayar a kunnensa yana jiran ta ɗauka ya ji me yasa ta fitan sassafe haka? Don a saninsa yau ba ta da aiki in dai ba wani muhimmin abu bane ya taso mata. A can ɓangaren Bintu, tana ganin kiran ta jaa wani dogon tsaki ranta a ɓace. "Aikin ɓur in ji tusa! Ai kuma sai ka yi. Na rantse da Allah idan za ka kira sau dubu bazan ɗauka ba. Kai ma ka ɗanɗana ka ji idan a kira mutum ya ƙi ɗauka da daɗi. Don ma dai ni da hannuna bazan iya blocking ɗin ka bane kamar yadda ka yi min." Ita kaɗai a cikin mota tana tuƙi tana masifa har ta isa gidan Raudha. Ko da ta shiga ciki basu wani ɓata lokaci ba suka fito, domin a shirye ta tarar da Raudha. Motar ta suka sake shiga mai gadi ya buɗe musu ƙofa ta figi motar a guje suka bar gidan. Kamar yadda suka tsara, komai ya tafi musu daidai yadda Bintu ta so. Ƙarfe goma sha ɗaya da minti hamsin na safiya mai taxi ɗin da suka ɗauki shata tun daga Kaduna yayi fakin a ƙofar gidansu Innaye. Tana gyara zaman ƙwamemen baƙin gilashi no respect da ta siya a Kaduna ta saka a idanunta take cewa da direba. "Malam ka ɗan jira mu kaɗan, kamar yadda na ce maka ba daɗewa za muyi a ciki ba. Yaro kawai zan ɗauko ka juya da mu inda ka ɗauko mu." "Babu damuwa Hajiya. A fito lafiya." Ya amsa a ladabce. Har sun nufi zauren gidan Raudha ta dakatar da ita, zip ɗin jakarta ta zage, ta cusa hannu a ciki ta ɗebo cingam guda huɗu ta miƙa ma Bintu biyu itama ta ɓare biyu ta watsa a baki ba tare da kunyar idanun mutane da ke kallonsu ba. "Saka wannan a baki ki tauna cikin ƙwarewa ƙawata. Kin san sheggun ƙauyen nan in bi ki nuna musu ke ma ƴar iskar kanki bane baza su baki Aadil a sauƙaƙe ba. Kuma ko da wasa idan muka shiga kar ki kuskura kunyar ƴar iskar tsohuwar nan ya hana ki yayyaɓa mata baƙaƙen maganganu..." "Kin san wannan ai dole ne Raudha. Yadda raina ya ɓaci Wallahi dole nata ya ninka nawa ɓaci. Mu je. Shegu yaran ƙauye dubi yadda suke kallonmu kamar mayu... kurwanmu kur!!!" Ta ƙarasa maganar da ɗan ƙarfi tana kallon wani yaro ɗan tsamurarre da tulelen ciki wanda tun ɗazu yake tsaye gefe ya ƙura musu idanu. Bayan ta ɓare cingam ɗin ta watsa a baki sai ta nufi cikin gidan tana sake tamke fuska. Raudha na biye da ita a baya itama da nata fuskar a haɗe babu sassauci ko kaɗan. ****** A cikin gidansu Innaye, misalin ƙarfe goma sha ɗaya da kwata na safiyar ranar, Aunty Balira, Rakiya, Ladidi suka yi ma gidan dirar mikiya. Bayan barinsu gidan Aunty Balira jiya, da daddare ta kira su kan cewa su tambayi mazajensu su haɗu su ukun su je suyi ma Innaye Allah sanya alkhairin aure da Hafiz zaiyi. Wannan shi ne abinda ya kawo su, ashe rabon suyi kiciɓus da Hajiya Bintu ne. Suna zaune a tsakar ɗakin Innaye kan tabarma suna shan Fate da Mama Laraba tayi, hira suke da dararraku a tsakaninsu ukun, Innaye tana zaune a kan kujera tana saka musu baki jefi-jefi. Suna cikin wannan halin ne suka ga an yaye labulen ɗakin, kwatsam! Sai ga Bintu ta bayyana da Raudha tsaye a bayanta, sai taunar cingam suke yi ƙaras-ƙaras cike da tsantsar raini da fitsara. Da farko duk ƙamewa suka yi ana kallon-kallo a tsakaninsu. Sai Aunty Rakiya ta karya shirun da cewa "A'uzubillahi minasshaiɗanirrajeem." Da matsanancin ɓacin rai a muryar Bintu ta ce "Kan'uba!! Amma lallai Rakiya kin ci uwar rainin wayau. Ni za ki kalla kiyi wa a'uziyya? To Me kike nufi?" "Me kuwa nake nufi in banda korar shaiɗan da nayi? Idan banyi a'uziyya ba me kike so inyi? In ba shaiɗaniya a cikin siffar mutane ba wacece za ta shigo ɗaki mai daraja irinna sarkuwarta babu sallama...?" "Rakiya!" Innaye ta kira sunanta da ɗan tsawa-tsawa a muryarta. "Ya isa haka nan." Ta sake faɗa tana ƙoƙarin sassauta muryarta. A karo na biyu ta mayar da idanunta kan Bintu ƙirjinta na bugawa kaɗan-kaɗan. Ta daɗe da sanin Bintu ba ta da mutunci, amma tsantsagwaron rashin mutunci irin wanda take ƙoƙarin shimfiɗa musu yau bata taɓa ganin ta yi ba. Tunaninta ɗaya ne, Bintu ta ji Hafiz zai auri ƙanwar mijin Zulai shi ne ta zo ta sauke musu rashin mutunci don a tsammaninta da haɗin bakinsu ake shirin ƙulla auren. "Fatima lafiya? Me yake tafe da ke?" Ta tambayeta bayan ta tuna zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Yatsarta manuniya tasa ta ja gilashinta ƙasa kaɗan, ya zama tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta saman gilashi. Cingam ɗin da ke bakinta ta tauna yayi ƙas, ta huro shi yayi ƙaton balo-balo ta fasa sannan ta fara magana tana yamutsa fuska kamar tana shaƙar warin kashi. "Innaye... Kin ga ina ganin mutuncinki, kuma da gaske ina ganin girmanki. Bana tunanin tunda na auri Hafiz wani sa'insa ya taɓa shiga tsakanina da ke, don haka kar ki bari mu fara ayau. Salin-alin ki bani ɗana in tafi da shi..." "Saurara Bintu! Wani ɗan kike magana akai?" Aunty Balira ta katse mata numfashi da wannan tambayar. "Ɗana Aadil, jinina. Wanda na haifa a cikina..." "Uhmmm! A sanina dai ƙarfe ɗaya ba ya amo... idan kuma ɗan naki ne ke kaɗai ai sai mu ji. In dai har Babanmu ɗan da Hafizu yayi miki cikinshi kika haifa ne, a tunanina yana da ikon yin yanda yaga dama da ɗanshi?" Aunty Ladidi ta katse ta da faɗin haka ranta a ɓace da maganganun da Bintu ta faɗa. Habawa!!! Waɗannan maganganu da Ladidi ta faɗa ina wuta Bintu da Raudha su jefata a ciki wai tana neman sheganta Aadil. Haka suka shigo har tsakiyar ɗakin Innaye suna zuba rashin daraja ko takalmansu basu samu sararin cirewa ba. Suna yi, Rakiya da Ladidi suna basu amsa, nan da nan guri ya fara rikicewa kamar za'a ba hammata iska. Kishiyoyin Innaye da tashin muryarsu Bintu ne ya shigo da su babu abinda suke yi sai aukin bada haƙuri, tunda sun taki babbar sa'a Baffa ba ya nan. Su Baba Abubakar da kusan yini suke yi a ƙofar gidan kuma su ma basa nan, tun sassafe suka hau motar da Hafiz ya ɗauka musu shata suka kama hanyar Abuja don a tsayar da maganar aure tsakanin Hafiz da Kareema. Wannan shi ne dalilin da yasa su Bintu suke cin karensu babu babbaka cikin rufewar idanu. Innaye dai tana zaune ƙiƙam kamar mutum-mutumi. Kanta a ƙasa, a idanunta kuwa babu abinda ke fita sai zazzaafan hawaye. Zuciyarta cike da tunanin yadda Ɗan kuka ke ja ma uwarsa jifa.... Wai yanzu fa wannan matsayin matar ɗanta take. Saboda tsabar rashin kirki ta shiga har tsakiyar ɗakinta da takalmi, kuma take zuba musu rashin mutunci yadda take so. A ɓangaren Aunty Balira da take zaune itama baƙin ciki da takaicin Bintu na neman kai ta kushewa wayarta ta zura hannu a lalita ta ciro. Lambar Hafiz ta lalubo ta danna mishi kira, a niyyarta na tambayarsa wai shin shi ne ya turo Bintu tazo ta zubar musu da mutunci ta ɗaga hankalin mahaifiyarsu? Ko kuwa zuwan na gaban kanta tayi? Acan ɓangaren Hafiz, yana ganin kiran ya ɗaga, da ɗan taƙaitaccen murmushi a fuskarsa. Ya buɗe baki zaiyi sallama kenan sai ya jiyo hayaniya na tashi sosai ta cikin wayar kamar ana faɗa. Ƙirjinshi ne ya buga daram! Don haka ya saurara sosai don jin hayaniyar me ake yi haka a gidan Aunty Balira.? Muryar Baba Laraba da ya fara jiyowa tana magana yasa shi fahimtar hayaniyar a gidansu Innaye ne ba gidan Aunty Balira ba. Raɗau ya cigaba da saurarar muryar Baba Laraba tana magana cikin magiya da roƙo "Hajiya Bintu... kinga Hajiya Bintu ina gama ki da girman Allah da ma'aiki kiyi haƙuri... Tunda dai baki ga alamar wani ɗa naki anan ba ki koma..." Muryar Bintu da ya ji cikin masifa tana mayar da martani yasa shi wuntsilawa daga kan gadon hankalinsa a tashe. Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya ji irin munanan maganganun da ke fita a bakinta. Tana mayar ma da Baba Laraba martani, amma kamar tana yi da ƙanwarta. Lokaci ɗaya jikinsa ya fara rawa kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a tsakiyar ɗakin Innaye bayan ya ji kalaman Bintu. "Ke tsohuwa saurara. Na rantse da Allah tunda na sa ƙafa na shigo wannan tsinannen ƙauyen babu inda zan je sai wannan tsohuwar da munafukan ƴaƴanta sun fito min da ɗana..." Daga wannan maganar, bai sake jin wata ba sai ƙarar saukar marin da daga ji ba ɗaya bane, marin da ya rasa wa aka yiwa? Bintu aka mara ko ita ce ta mari ɗaya daga cikin yayyinsa? Ko kuma haƙurin Innaye ne yakai ƙarshe ta mari Bintu? Kuma sanadiyyar marin ne yasa duk hayaniyar da ake yi ya ɗauke ɗif! Kamar ɗaukewar ruwan sama. Sai da aka ɗauki mintuna biyu kafin ya ji muryar Aunty Balira tana magana cikin kuka, saboda hawayen da sai a lokacin ta lura Innaye tana yi ya ɗaga mata hankali. "Tir da mace irinki Bintu!!! Tir da ke da munanan halayenki Bintu!! Sai yau na ƙara tabbatarda lallai Hafizu yayi asara baiyi sa'ar mata ba. To saurara ki ji, ke kinyi kaɗan ki ce za ki zo ki saka mahaifiyarmu kuka sannan mu zuba miki ido. Idan shi wanda ya auro ki ba ya kishin mahaifiyarsa mu muna yi. Ki je can ki nemi inda Hafizu ya kai miki ɗa, mu kam saboda sanin mugun halinki da baƙin halinki babu wacce tayi gigin karɓar mummunan tsatso irin naki. Zo ki fice mana daga ɗakin uwa, za ki fice ne salin alin ko sai na nakaɗa miki tsinannen duka in barki kwance?" Ta ƙarasa maganar cikin tsawa da hargagi, jikinta sai rawa yake yi saboda yadda kukan Innaye ya ke bugun zuciyarta. Bintu da tunda Aunty Balira ta sauke mata tagwayen maruka ita da Raudha suka ƙame ƙam kamar statue, sai a lokacin ta iya buɗe baki da rawar murya idanunta ciccike da hawaye ta ce "Nnnnnn ni kika mara Balira...?" Ai ko kafin ta rufe baki, Aunty Rakiya da Aunty Ladidi da tun ɗazu hannuwansu ke ƙaiƙayi suka sake gaura mata wasu ƙarfafan maruka a kuncinta na dama da hagu. "An mare ki ɗin! Don abu kaza-kazanki idan kin isa ki sake cewa uffan anan gurin idan bamu yi ƙasa-ƙasa da ke ba." Suka haɗa baki gurin faɗin haka a zafafe. Aunty Rakiya da ta daɗe tana jiran irin wannan ranar da za ta jibgi Bintu a haukace ta cire ɗankwalin kanta ta ci ɗamara da shi. Ta tsaya gaban Bintu tana jijjiga, babu abinda take jira sai Bintu ta ce kule ta rufe ta da mahaukacin duka. Raudha da tun da aka yi marukan farko hankalinta yakai ƙololuwa gurin tashi, a ɗan tsorace ta ƙare ma Rakiya kallo, ta ganta irin sangama-sangaman matannan ne ga tsawo ga ƙiba. Ko dambe aka ce suyi su biyu ita da Bintu su taru ma Rakiya ko rantsuwa tayi babu kaffara tun a mintuna biyun farko Rakiya za tayi ƙasa-ƙasa da su. Domin daga ita har Bintu ba su da ƙiba ko kaɗan, kuma Mal bahaushe ya ce alamun ƙarfi yana ga mai ƙiba. Da sauri ta riƙo hannun Bintu ta fara janta da nufin su fice daga ɗakin. "Zo mu je ƙawata. Idan muka tsaya taron dangi za suyi mana. Idan sun ƙi ba mu Aadil ta lalama ai akwai hukuma. Kuma na rantse da Allah waɗannan marukan da suka yi miki basu ci bulus ba, tabbas za su biya bashi amma a gaduron ɗin sojoji. Zo mu je mu sake sabon shiri." Tana jan hannun Bintu, Bintun tana turjewa hawayen baƙin cikin mari huɗu da aka mata na zuba a idanunta amma bata iya rama ko ɗaya ba, kuma ta kasa cewa uhummm ɗin saboda tsoron kar su dake ta abinda ta san za su aikata tunda shegun ƙauye ne, a haka har suka fice daga gidan gaba ɗaya tana sharɓen hawaye. ****** ****** Misalin ƙarfe bakwai na daren ranar, Bintu tana kwance akan gadon ɗakin Raudha. Ta ci kuka har ta gode Allah, hawayen da tunda suka ɓalle mata a can Faƙo har yanzu sun gagara tsayawa. Duk kuwa da yadda Raudha ta yini tana rarrashinta sam ta kasa daina kuka. A yanzu abubuwa ne suka haɗe mata goma da ashirin. Ga damuwar rashin sanin inda Hafiz ya kai Aadil, ga damuwar irin wannan mummunan cin mutunci da tozarci da dangin Hafiz suka yi mata. "Yanzu shi kenan? An sha ta misilla-banza? Hafiz da ƙauyawan ƴan'uwansa sun ci galaba a kanta? Sun raba ta da ɗanta lokacin da bata yi tsammani ba sannan sunyi sukuwar sallah akan kima da martabarta?" Tunanin hakan kaɗai tayi sababbin hawaye ne ke sake ɓalle mata. Ko bayan da suka koma Abuja a yammacin, kafin su isa gidan Raudha sai da ta kira Hajiya Maama matar Abba Lurwanu ta tambayeta cikin hikima ko Hafiz ya kai mata Aadil? "Bai kawo shi ba Bintu. Hafiz ɗin bai dawo bane ko kin kasa samun shi a waya ne? Kin san Aadil da ƙwuiya na tabbata duk inda yake yana tare da mahaifinsa. Kiyi haƙuri, zai dawo miki da ɗanki." Amsar da Hajiya Mama ta ba ta kenan. Gidan Zulai shi ne guri na ƙarshe da tayi tunanin Hafiz zai iya kai Aadil. Har sun kusa isa gidan Raudha, haka ta sake neman alfarmar Raudha ta juya da kan motar da a yanzu Raudha ke tuƙawa suka nufi gidan Zulai. Suna hanya kamar mahaukaciya haka take ta kuka tana rantse-rantse da shan alwashin duk waɗannan marukan da su Balira suka yi mata akan Zulai za ta rama. Sai dai wani rashin sa'a da suka buga shi ne suna isa mai gadi ya tabbatar musu Zulaikha ba ta nan. Ta tafi can babban gida saboda Oga yayi tafiya. Da fari ta so suje gidan Mummy Saudha tun a daren, amma sai Raudha ta taushi zuciyarta da shawarar tayi haƙuri su bari zuwa gobe da safe. Lokacin Mummy ta tafi aiki sai su je, yadda za su samu damar cin ƙaniyar Zulai ba tare da anyi yunƙurin hana su ba. Amincewa da shawarar tayi, don haka ta jingina da kujerar mota ta lumshe idanu ta cigaba da hawaye zuciyarta na ƙuna da tafarfasa. Har suka isa gidan Raudha bata sani ba sai da ta taɓa ta cewa ta tashi su shiga ciki. Tunda ta shiga kuwa tayi kwance-kwance tana kuka akan gadon Raudha. Ko ramakon sallolin da suke kanta ta kasa yi, tun Raudha tana rarrashinta har dai ta gaji ta zura ma sarautar Allah ido. Daga ƙarshe ma ficewa tayi zuwa kicin, ta samu abinci ta ci tayi nak, sannan ta koma ɗakin bayan ta yi nakwa-nakwa da fuska, sak yanayin taya Bintu baƙin ciki da jimami. Agogo yana buga ƙarfe tara daidai ta ɗaga jajayen idanunta da suka kumbura suntum saboda yawan kuka ta kalli Raudha. Da ɗasasshiyar murya ta ce "Ina Abdallah? (Ƙanin Raudha da yake zama a gurinta.) Don Allah ki kira shi ya mayar da ni gida... kaina ciwo yake sosai, bazan iya tuƙa mota ba." "Tom! Na dai ji dawowarsa ɗazu ban san ko yana nan ba. Bari in taɓo shi ta waya." Raudha ta amsa, a lokaci guda tana daddanna wayarta. Suna hanyar zuwa harabar tsakar gidan take ƙara tausar Bintu da daɗaɗan kalamai. "Na san izuwa yanzu ƴan'uwan Hafiz sun kira shi sun kitsa mishi ƙarya da gaskiya kan abinda ya faru. Don haka ko kin koma gida don Allah don Annabi SAW duk yadda zaiyi ƙoƙarin tararki da rigima kar ki kuskura ki kula shi. Ki cigaba da tara shi har zuwa sadda za mu gano inda ya kai Aadil mu ɗauko shi, a lokacin kina da damar warware mishi balbalin bala'in da bai taɓa tsammanin kin iya ba." "Hmmm! Ba damuwa. Na gode ƙwarai Raudha." Ta amsa a taƙaice. Ko da ta shiga gidan baya na motar ta jingina da kujera, a jikinta jakarta ne rungume da kuɗi da wayarta da sauran ƙananun tarkace. Lumshe idanu tayi bata ce Uffan ba har suka isa gidanta. Har ciki ya shiga mata da motar, ya daidaita fakin a tsakar gidan sannan ya kashe motar ya miƙa mata makullin. Cike da kasala ta miƙa hannu ta karɓa tayi mishi godiya. Hannu ta cusa cikin jakarta ta ƙirgo naira dubu goma ta bashi, ta sake yi mishi godiya sosai. Ya fice daga harabar gidan, ita kuma ta nufi cikin gidan tana rangaji kamar wacce ta sha ƙwaya. ****** Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe, Bintu ta gama shiryawa da wani sabon ƙwarin gwuiwa na musamman wanda a jiya sam bata kwana da shi ba. Cikin hukuncin Allah jiya da dare har ta gama duk abinda za tayi ta kulle ƙofar ɗakinta Hafiz bai koma gidan ba. Kamar magani haka ta dinga kurɓar furar Rufaida har ta ji cikinta ya ɗauka. Tayi wanka, ta rama sallolin da suke kanta cikin rashin nutsuwa. Sannan ta harhaɗa Magunguna ciki har da na barci ta ɗaɗɗaka. Da yake da gajiya a jikinta ga rashin wadataccen barci tsakanin jiya da yau Mintuna goma da gama shan maganin wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita. Ta kai ƙarfe takwas kafin ta farka, a gurguje tayi sallar asubah. Tana zaune akan dadduma take tsara muhimman abubuwa biyu da ta ƙuduri aniyar aiwatar da su a ranar. Wayarta da tun jiya bata bi ta kanta ba ta ɗauko, bata bi ta kan tarin misscalls da saƙonnin da suke fuskar wayarta ba ta shiga cikin ma'adanar lambobi. A hankali take wucewa har zuwa sadda ta ci karo da lambar da take nema, ba na kowa bane face na Kwamishinan ƴan sanda da ya kasance abokin mahaifinta. Kiranshi tayi, bayan gaisuwa da gabatar mishi da kanta tambayarshi tayi yau zai samu zuwa Ofis kuwa? "Yau ɗin Monday ce fa, tushen aiki ko nasara na tsoron monday. Ina Ofis tun 8." Ya amsa mata. "Na gode Abba. Zuwa 11am in sha Allah zan ƙaraso..." "Lafiya kuwa Fatima?" Ya tambayeta da mamaki a muryarsa. "Lafiya amma ba lau ba Abba. Maganar ba ta waya bace. Sai na zo dai." "Ok!" Ya amsa a taƙaice, sannan ya kashe wayar. Tana riƙe da wayar, ita kaɗai take sakin murmushi akai-akai. Zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Sannu a hankali kamar allurar soja aka zurkuɗa mata haka take jin ƙwarin gwuiwa yana zagaye duk sassan jikinta. Ɗan ƙaramin frige ɗin da ke ɗakinta ta buɗe, kamar ba safiya ba, coke mai sanyi ta ɗauka ta buɗe, ta lumshe idanu ta kafa a bakinta ta fara sha, tana jin yadda sanyin ke sauka har cikin-cikinta. Bata shirya haɗuwa da Hafiz ba, shi yasa bata buɗe ƙofar ɗakinta ba har ta gama duk shirinta. A yadda ta tsara, gidan Mummy Sauda za ta fara zuwa, tayi ma Zulai tsinannen duka sannan ta ƙwace ɗanta. Daga can kuma ta wuce hedikwatar ƴan sanda Ofishin kwamishina ta kai mishi ƙarar su Aunty Balira. A yau ba sai gobe ba take so a kamo su Aunty Balira a wulaƙance cikin motar ƴan sanda a watsa su a firzin. Za ta kashe ko nawa ne don ganin anyi musu mafi munin wulaƙanci da tozarci, za su san lallai sun taɓo tsuliyar dodo. Tana sauka daga kan step ta ji motsin buɗe ƙofar Hafiz, ko waige bata yi ba, don ma kar ya nemi dakatar da ita ƙara sauri tayi har ta sauka ƙasa ta fice daga falon. Tana cikin mota ta ɗaga waya ta kira Raudha, da dariya a muryarta bayan sun gaisa take cewa "Ƙawata yau fa Wallahi akwai show, za ki samu zuwa ko inyi wucewa ta..." "Haba... ai amana bai ce haka ba Ƙawata. Tuntuni na daɗe da shiryawa, ke kawai nake jira." Raudha ta amsa cike da zakwaɗi. Ko da ta isa gidan Raudha bata shiga da mota gidan ba, hon kawai tayi mata ta fito cikin kwalliya sosai ta shiga ɓangaren mai zaman banza suka kama hanyar wucewa. A hanya take ba Raudha labarin irin tsarin da take da shi na ɗaukar fansa akan su Aunty Balira. "Good! Very good ƙawata!! Kamar kin san dama ƴan ƙauye da bala'in tsoron ƴan sanda. Ki sa aci ubansu dakyau!!! Ta yadda nan gaba ko ɗaga ido baza su iya yi gurin yi miki magana ba, balle har suyi gigin kai ƙazantaccen hannayensu zuwa jikinki." "Ki bari kawai Raudha. Zan koya musu babban darasi a rayuwarsu." Ta faɗa tana sakin ƙayataccen murmushi. "Sannan kuma ga

Chapter 33 of 40