ta saki jiki sosai da ita, suna hanya ta faɗa ma Innaye cikakken sunanta Karima Idris Madobi.
Kamar wacce ta samu Kakarta ko Yayar mahaifiyarta, haka ta tallabe Innaye suna tafe sannu a hankali da fara'a sosai a fuskarta ta ke ba ta labarin Kakarsu da ta kasance fitinanniyar tsohuwar da ta gallabi kowa a gidansu.
"Ba ma taɓa samun hutu da surutunta idan ba barci tayi ba, ko kuma mu muka fita zuwa wajen aiki ko wani al'amari na daban. Ba wai ni da Yayana da muka kasance jikokinta ba fa, hatta Mummy da ta kasance ɗiyarta duk mun san haƙuri take yi da al'amarin tsohuwar."
Da murmushi sosai a fuskar Innaye ta jefa mata tambayar
"In banda ke da abinki Karimatu ta yaya ƴa za ta gaji da hidimar mahaifiyarta?"
"Ba'a gajiya ko Innaye?"
Ta maida mata tambayar da wata tambaya alamun ƙuruciya ƙarara bayyane a furucinta.
"Eh mana. Ai duk ɗa ko ƴa ta kirki ba ta taɓa gajiya da hidimar mahaifi ko mahaifiyarsa. Yanzu ne fa lokacin nan da Allah ya ce kar ku taɓa ce musu uhhmmm don wata ɗawainiya ko wahala tasu da kuke yi. Sun wahalta muku kuna ƙanana, ku kuma sai ku saka musu suna tsofaffi masu rauni kan rauni. Idan kuma kina tantamar abinda na faɗa miki, wata rana ki gwada aibata ita Kakar taki a gaban Mamanki..."
"Taɓ! Ki ce in janyo ma kaina gaggarumin tashin hankali tsakanina da Mummy. Duk fa wannan wahalar da muke ganin tana yi da Hajja yanzun nan muna fara ƙorafi za ta zazzage mana kwandon masifa tana faɗin ina ruwanmu? Ita ta fi son Hajja fiye da komai da kowa na duniyar nan. Don haka mu ƙyale ta ta hidimta ma tsohuwarta wata rana sai labari."
Faffaɗan murmushi ne yalwace a fuskar Innaye tana jin matsananciyar ƙaunar uwar Karima da ita kanta Karimar a zuciyarta. Suna wannan hirar ƙasa-ƙasa, har suka ƙarasa ɗakin gwajin da Bintu ta umarci Karima ta kai Innaye.
Kuma da yake ita ɗin ƴar arziki ce bata bar gurin ba sai da aka gama duk abinda ya kamata ta sake riƙota suka fito daga cikin Ofishin. Killataccen gurin zama da Nurses suke zama ta zaunar da Innaye, sannan ta bata uzurin tana zuwa.
A gaggauce ta wuce Ofishin Bintu ta sanar da ita an gama komai da ta umarta.
"In shigo da ita nan ne?"
"A'a!"
Bintu ta katse ta da sauri, hankalinta na kan rubutun da take yi a cikin folder na mara lafiyar da ta gama dubawa ko sararin ɗaga kai ta kalli Karima bata samu yi ba. Ita har ga Allah ta ma manta da wata Innaye balle abinda ya shafe ta in banda yanzu da aka zo mata da maganarta.
Taja wani zazzafan numfashi ta fesar. Ɓacin ran da ya bi ruwa sanadiyyar kama aikinta gadan-gadan ya fara taso mata sannu a hankali.
"Yanzu tana ina?"
Ta tambaya a taƙaice, har lokacin bata ɗaga fuskarta ta kalli Karima ba.
Faɗa mata inda ta zaunar da Innaye yasa Bintu ta ɗaga kai da sauri tana aika mata da wani kakkausan kallo.
"How dare you da za ki zaunar da ita inda aka tanada don ma'aikatan asibitin nan?Me yasa baki zaunar da ita a reception inda ko wane mara lafiya yake zama ba?"
A ladabce Karima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fara ba Bintu haƙuri, hankalinta a tashe. Domin bata daɗe da fara aiki a asibitin ba, tsoronta Allah tsoronta tayi abinda zai sa ta janyo ma kanta matsala daga fara aikin da take tsananin alfahari da samunsa.
"Shi kenan! Amma ki kiyaye gaba. Duk wata doka na asibiti ki tabbatar kin kiyaye shi sau da ƙafa. Bayan haka wannan tsohuwar da kike gani ƙazama ce ta ƙarshe mai ɗauke da cututtuka mabanbanta a jikinta, gara tun wuri kiyi nesa da al'amarinta. Ki maida ita reception ta zauna ta jira ni, zan kira direba yanzu ya mayar da ita inda ta fi wayau. Je kiyi abinda na ce."
Jiki a sanyaye Karima ta fice daga Ofishin tana jinjina maganganun Dr. Bintu a zuciyarta. Haka ta koma inda ta bar Innaye da yanayin da ba shi suka rabu ba.
"Kiyi haƙuri Innaye. Likita ta ce in zaunar da ke a reception ki jira ta. Za ta kira direba ya mayar da ke gida."
"To ba komai Karimatu. Na gode, Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari. Idan kin koma gida ki gaishe min da Kakarki da mahaifiyarki."
Ta faɗa ba tare da ta maganar da nisa ba, ganin yanayin Karima da irin maganar da ta faɗa mata in ji Bintu yasa ta tunanin wata ƙila Bintun ta faɗi mummunar magana ne a game da ita.
Duk da yadda take jin rashin ƙarfin jiki saboda yunwa, haka ta ƙwarara kanta ta miƙe tsaye ta fara tafiya a hankali zuwa waje ba tare da ta san ina ne reception ɗin ba.
Watsar da duk wasu maganganu da Bintu ta faɗa mata tayi ta ƙarasa da sauri ta riƙe ma Innaye hannu. Saɓanin sadda suka shiga cikin asibitin suna hira da dariya, a yanzu babu mai cewa komai har suka ƙarasa reception ta zaunar da ita.
Sallama tayi ma Innaye da addu'ar samun sauƙi sannan ta kama hanyar komawa gurin aikinta. Innaye ta raka ta da idanu.
10)
Tana daf da ɓace ma ganin Innaye sai ta dawo a gaggauce
"Innaye kin karya kumallo kuwa?"
Ta tambaye ta duk da ta san gwajin da aka yi ma Innayen ana yin shi ne kaɗai ga waɗanda basu ci abinci ba.
"Ban ci komai ba Karimatu. Ai an ce wannan gwajin kafin a ci abinci ake yi. Yanzu dai idan na koma gida zan karya, na san abincin kari na can Auta ta ajiye min."
Ta ƙarasa maganar idanunta na kallon ƙaton agogon da ke manne a jikin bangon gurin, wanda ya nuna ƙarfe goma sha biyu saura minti ashirin.
"To shi kenan. Allah ya ƙara sauƙi. Bari in kawo miki Maltina ki sha kafin ki koma gidan. Wannan rashin ƙarfin jikin naki ina ga har da yunwa ne ya galabaitar da ke."
Bata jira amsawar Innaye ba ta wuce ciki zuwa Ofishin da suke zama inda ta ajiye jaka da sauran kayayyakinta.
Maltina ta ɗauka a jakarta da samosa guda biyar a cikin robar take away ta fice a gaggauce ta kai ma Innaye. Bata tsaya amsa godiya da saka albarkar da take mata ba ta koma ciki ta kama ayyukan da suke gabanta.
Da gaskiyar Mal bahaushe da yake ma yunwa take da mare hankali. Innaye bata san yunwar da take ji ya kai ƙololuwa ba sai da taga Maltina da Samosa a hannunta. Jiya da daddare ba wani abincin kirki ta ci ba saboda tunanin rayuwar gidan Abdul-hafiz da makomarsa a can gaba, da wannan dalilin yasa take jin cikinta a rarake kamar wacce ta kwana ta yini bata ci ba. Duk yadda ta kasance dattijuwa mai tsananin kunyar idanun jama'a bata damu da mazauna gurin ba ta buɗe robar Samosa ta ɗauka ta fara ci tana korawa da Maltina. Kafin ace kwabo, ta cinye gaba ɗaya.
Lumshe idanu tayi tana hamdala a zuciyarta saboda jin yadda a ƙanƙanin lokaci ta ƙara dawowa cikin hayyacinta. Ashe kaso sittin na gajiya da galabaitar da tayi yunwa ce, yanzu kuwa da ta samu mahaɗi sai ga shi ta dawo hayyacinta sosai tana jin ƙarfi a jikinta.
Ƙara gyara zama tayi idanunta a lumshe tana shan A.c a zuciyarta kuma tana Istigfari da Hailala kafin ta ankara ta fara gyangaɗi.
"Wai barci kike yi? Ki tashi ga direba can zai mayar da ke gida."
Ta ji muryar Bintu bagatatan a kanta kamar a cikin mafarki.
A hankali kuma a nutse ta buɗe idanunta ta zuba a cikin na Bintun. Ita ma fuskarta babu walwala ko kaɗan kamar dai yadda fuskar Bintu yake. Sai kuma ta kawar da idanunta daga Bintu ta maida kan agogo, ƙarfe goma sha biyu da minti goma sha takwas na rana.
Bata ce komai ba sai miƙewa da tayi tsam ta tsaya tana kallon Bintu.
A fakaice, Bintu ta harari gefen Innaye, ta ƙara ɓata fuska sannan ta nufi hanyar fita. Innaye ta rufa mata baya zuciyarta na ƙara cika da tsoron halayen Bintu da sannu a hankali suke ƙara bayyana.
Har suka ƙarasa gurin motarta inda direba ke zaune a mazaunin direba bata sake ce ma Innaye komai ba. Ita ma Innaye bata ce mata cikanki ba.
Kamar sadda za su zo asibitin, ƙofar baya na motar Innaye ta buɗe ta zauna sannan ta mayar da ƙofar ta rufe da ƙarfi.
'Ta Allah ba taki ba. Duk muguntarki haka za ki ga motar nan ki ƙyale ko ƙwarzane baki isa kiyi mata ba.'
Bintu ta faɗa a zuciyarta, cike da jin haushin irin bugun ƙofar da Innaye tai ma motar ta.
Dogon tsaki ta ja kafin ta mayar da idanunta kan direba.
"Bala kayi tuƙi a nutse fa. Kana dawowa ka tabbatar ka wanke min motar ciki da waje saboda ƙura da gudun kwasar cututtukan da ban san farkonsu ba bare ƙarshensu. Ina fatan ka gane?"
"Na fahimta Ranki ya daɗe. Sai na dawo."
Ya amsa a ladabce.
Baya ta matsa, shi kuma ya tayar da motar, tana tsaye tana kallonsu har suka fice daga cikin asibitin kafin ta koma ciki tana sake jan tsaki sama-sama.
******
"Hmmm! Na ce ba... Au! Ina kwana Baba?"
A ɗan daburce Zulaikha ta sake gaishe da Rabi a karo na uku.
Ba tare da damuwa ko nuna yanayin gundura ba ta amsa gaisuwar da murmushi fal a fuskarta. Haka kawai, Zulaikhan burge ta take yi, basu taɓa yin wata doguwar magana ba tun da suka zo gidan, amma idan ta je can inda aka sauke su za ta kai musu abinci ta ga irin taɓara da shagwaɓar da yarinyar ke ma mahaifiyarta abin dariya da burgewa yake ba ta.
Tun bayan shigowar yarinyar, da ajiye tsadaddun kulolin abincin mai gidan da tayi ta gaishe ta a karo na farko, ta lura da yadda yarinyar take saiɓi wajen fita kamar akwai wani abu da take so.
Har ta kusa fita sai ta juyo da sauri ta sake gaishe ta a karo na biyu, ko bayan da ta amsa gaisuwar, sai ta ɗan tsaya shiru ta ƙura mata idanu.
A karo na ukun kuma har ta fita sai ta sake dawowa ta gaishe ta.
Kamar baza ta amsa ba, duba da yadda Hajiya Bintu ke ta kwakkwafarta a kan baƙin tun ranar da suka zo gidan sai kuma ta yanke shawarar yi mata magana ganin yanzu ai Hajiyar ba ta nan.
"Ƴan matan Mamanta ya aka yi? Gaisuwa ɗaya biyu ai ya isa ko? Kin ga tun shigowarki na lura kamar akwai maganar da kike so kiyi amma kina ta nuƙu-nuƙu. Kina buƙatar wani abu ne? Kar ki damu, faɗi ko me kike so yanzu in ɗauko miki."
Kamar damar da Zulaikha take buƙatar samu kenan. Da sauri ta ce
"Ummm! Daman zan tambaye ki ne don Allah. Jiya da rana har kika tafi baki kawo mana abinci ba, kin manta da mu ne?"
Ɗan shiru Rabi tayi kamar tana tunani, sai kuma ta amsa kai tsaye da cewar
"A'a! Ban manta da ku ba. Hajiyar ce ta ce ba sai nayi abincin rana ba, ko da na tuna mata da baƙi kuma sai ta ce ba abinda ya shafe ni bane. Ta aike ni can gidansu daga can kuma na wuce gida..."
"Da gaske haka kuka yi Baba?"
Zulaikha ta katse ta da tambayar da yanayin mamaki fal a fuskarta.
"Eh da gaske, me zai sa inyi miki ƙarya? Kin san daman a ɓangaren girki abincin da nake dafawa a gidannan na masu aiki ne kawai, sai kuma baƙi idan akwai.
Abincin maigidan ita da kanta take dafawa. To tunda ta ce ba sai nayi ba ai kin ga ba ni da hurumi ko ikon da zan ce dole sai anyi ko?"
"Uhmmmm haka ne."
Zulaikha ta amsa a mamakance.
"Lallai ma!"
Ta ƙara faɗa tana sake jinjina girman al'amarin. Ita daman tun jiya ta san da gangar Bintu ta hana su abinci, amma saboda tsananin ƙwarewarta a ƙarya da iya shirya zance sai ta ce bata san ba'a kai musu abinci ba.
"Ba damuwa. Ta yi ma kanta."
Ta sake faɗa ranta a ɓace.
Da sassarfa ta kama hanyar ficewa daga kicin ɗin Rabi ta bi ta da kallo.
A zuciyarta take harhaɗa ɗaya bisa biyu tana hasaso abinda ya faru bayan tafiyarta. To ko dai wannan shi ne dalilin da yasa ta ga waɗannan tsadaddun kulolin na abincin Oga a hannun Zulaikha? Kulolin da ko gurin wanke-wanke Hajiya ta jaddada mata lallai ta dinga musu wanki na musamman, sannan da an gama wankewa a kife a kwando a saka towel a goge a mayar da su ma'adanarsu, ba tare da an haɗa su da tarkacen kaya ba...
"Amma Baba Rabi ita Hajiyar ta faɗa miki matsayinmu a gurin maigidannan kuwa?"
Maganar da Zulaikha tayi ya dawo da ita cikin tunaninta ba tare da ta san sa'adda ta dawo cikin kicin ɗin ba.
"A'a! Bata faɗa min ba. Abu ɗaya dai da na sani ku ɗin danginshi ne, don Hajiya Bintu ta sha faɗin shi ke da ƴan'uwa Ƙauyawa..."
"Ba ƴan'uwa ƙauyawa kaɗai bane. Ita wannan tsohuwar baƙauyiyar da kike ganina tare da ita, mahaifiyarshi ce."
Zulaikha ta faɗa idanunta ciccike da hawaye. Kafin Rabi da ta buɗe baki tayi magana ta cigaba da cewa
"Ita ce ta sha wahalar naƙuda ta haifo shi zuwa wannan duniyar. Ni kuma da kike gani kamar ba kowan kowa ba, ƙanwarsa ce da suka fito ciki ɗaya. Saboda Allah da Annabi idan da adalci ya kyautu ace an hana uwar da ta sha wahalar haihuwa da rainon ɗanta abincin da shi wannan ɗan nata ne yake nemowa da guminsa?"
Kamar an buɗe famfo, haka hawaye ke kwaranya a idanunta. Ita kuwa Rabi, tunda ta buɗe baki ta kasa rufewa, balle har ta iya ƙarfin halin amsa tambayar da Zulaikha tayi mata. Allah ya sani bata taɓa tsammanin Innaye mahaifiyar Oga Hafiz bane, duk ga tsammaninta ta fi tunanin ko dai wata Gwaggwansa ce daga ƙauye.
Babbar hujjarta kuwa shi ne, duba da yadda daga Hajiya Bintu har Alhaji Hafiz al'amarin tsohuwar basu ɗauke shi da wani gagarumin muhimmanci ba. Hujja ta biyu kuwa shi ne, babu wata kamanni ta musamman tsakaninshi da Innaye, ɗan gara-gara ma Zulaikha, suna yanayi a fisge...
"Ban ƙara sanin haka duniya take da faɗi da tarin abin mamaki ɗauke da mutane mabanbanta ba, sai da Bintu ta shigo cikin ahalinmu. Ko da muke ƴan ƙauye, bamu taɓa tsammanin akwai wani tazara na musamman tsakanin ɗan birni da na ƙauye ba, ko kuma banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi. Duk a tunanina mu da ku bayin Allah ne da babu wanda ya fi wani a gurinsa sai wanda ya fi tsoronsa... Amma a yanzu na samu ƙarin ilimi, ya zama dole mu cigaba da raɓewa a ƙauyenmu don rayuwar birni da mutanen birni sun fi ƙarfinmu ta ko wane ɓangare."
Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin kicin ɗin da sauri, lokaci bayan lokaci take kai hannu saman fuskarta tana share hawaye.
Ta fito tsakar gidan kenan da nufin zuwa can ɓangarensu aka wangale get ɗin gidan. Kamar baza ta waiga ba, sai kuma ta juya sannu a hankali tana kallon motar da ta shigo. Ganin motar Bintu ce yasa ta ware idanu tana kallon motar da kyau domin ganin ta ina Innayenta za ta fito?
Kallo ɗaya za'a yi mata, a fahimci jikinta a sanyaye yake sosai.
Zulaikha yarinya ce mai shekaru goma sha bakwai. Amma irin yarannan ne da tun suna ƙanana suke da masifar wayau da manyancen iya magana. Ko don ta rayu a hannun Dattijuwa Innaye ce? Allah masani.
Ganin fitowar Innaye daga cikin mota ita ma da nata yanayin sanyin jikin yasa tayi ƙoƙarin watsar da nata damuwar ta ƙarasa gurin Innaye da sauri.
"Innaye? Me yake faruwa? Jikin naki ne?"
Ta jera mata tambayoyin da hanzari fuskarta na bayyana damuwa da tashin hankali. A lokaci ɗaya kuma tana ɗan tattaɓa jikin Innayen domin jin ko akwai zafi?
Hannayenta Innaye ta kamo ta riƙe, da murmushi a fuskarta ta amsa da cewa
"Jiki Alhamdulillah Auta. Kawai dai na gaji ne. Amma babu komai, muje ciki."
"To Ma sha Allah! Allah ya ƙara lafiya."
Ta amsa tana jin kwanciyar hankali kaso hamsin cikin ɗari na damuwarta.
Haka suka kama hanyar zuwa ɓangarensu suna riƙe da hannun juna cikin kulawa. Babu mai cewa komai a cikin su biyun, ko wacce da tunanin da take yi a zuciyarta.
Suna ƙarasawa ciki, ta zaunar da Innaye a gefen gado ta sa hannu ta zare mata hijabin jikinta.
"Sannu Innaye. Allah ya ƙara lafiya. Ai dole ki galabaita, jiya fa duk farkin barcin da zan yi sai in ga idanunki biyu. Ga shi yau da sassafe baki samu komawa barci ba kuka fice zuwa asibiti. Ko kinyi barci ne acan asibitin?"
"Barci kuma Auta?"
"Eh mana. To ba naga akwai gadajen da ake kwantar da marasa lafiya ba?"
Ta amsa tana tura baki da murmushi a fuskarta.
"Eh haka ne! Amma ai ana kwantar da waɗanda jikinsu yayi tsanani ne. Ni kuwa kin ga har yanzu da sauran ƙarfin jiki a tattare da ni..."
"Amma Innaye kin ci abinci bayan an gama gwajin da aka ce za'a miki kafin ki karya?"
Ta katse ta da sauri bayan ta tuno sun fita daga gidan Innaye bata karya ba.
"Uhmmm!"
Ta ja numfashi ta sauke a kasalance. Kamar baza ta ƙara yin magana ba daga wannan ajiyar zuciyar, sai kuma ta ce.
"Auta! Wato da gaske ne duk lalacewar al'umma ba'a rasa na kirki. Yau ba don Allah ya haɗa ni da wata yarinya ƴar arziki wacce ta san ya kamata ba da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Wata kila, da sai dai matar gidan ta dawo ta sanar da ku babu yadda nake, an kwantar da ni ranga-ranga a asibiti. Amma da yake ko cikin lalatattu ba'a rasa na kirki sai Allah ya agaje ni da taimakonsa na gaggawa a lokacin da banyi tsammani ba. Alhamdulillahi! Je ki tara min ruwan wanka inyi sai in alwala, ga shi can ana kiran sallah a masallaci..."
"Me ya faru da ke a asibitin Innaye?"
Zulaikha ta tambaye ta tana jin babu daɗi sosai a zuciyarta. Daman tun bayan ficewarsu take ta ji a ranta lallai a rashin kirkin Bintu za ta fa iya wulaƙanta Innaye ganin babu idanun kowa a kansu.
Ganin wayar Innaye ajiye a gefen gado yasa ranta ya ƙara jagulewa, tayi tunanin da akwai waya a hannun Innaye, idan ta ga abinda bai gamshe ta ba za ta iya kiran Yayansu yaje asibitin ya ɗau mataki.
"Maimaita abinda ya wuce sam ba shi da wani amfani Auta. Balle kuma kin san hali na abu idan ba na alkhairi bane ban cika son maimaita labarinshi ba..."
"Don Allah ki faɗa min Innaye."
Tayi maganar kamar za ta saka kuka.
"Bazan faɗa miki ba Auta. Domin jin babu abinda zai ƙare ki da shi. Nasihar da zan miki a wannan gaɓar ɗaya ne rak! Mu mutanen ƙauye ne, can ƙauyen, can ne duniyar da muka buɗi idanu da ita. Kuma kaso casa'in da biyar cikin ɗari na mutanenmu acan suke farawa kuma su ƙare rayuwarsu.
A mafiyawancin lokuta duniyar sauyawa take yi. Idan Allah yayo ki cikin masu tsawon rai yanzu kika fara rayuwarki, ban san ko kina daga cikin ɗaiɗaiku kuma tsirarun da Allah ya ƙaddari za su tsallake ƙauyenmu suyi rayuwa a wani guri na daban ba. Idan Allah ya ƙaddara miki haka, ki ji tsoron Allah. Kar ki kuskura don wani ni'ima da Allah yayi miki ki wulaƙanta mutanen ƙauye, ko ki wulaƙanta na ƙasa da ke.
Je ki tara min ruwan wanka, kafin in fito ki je cikin gidan ki samu mai aikinnan ta baki abinci ki kawo min, idan kuma babu, ki zo ki haɗa min shayi."
Duk wasan da ke tsakaninta da Innaye a wasu lokutan kamar jika da Kaka. Ta san irin lokacin da take tubure mata da ƴan rigingimu, ta kuma san lokacin da take ɗaukar abinda ta faɗa da muhimmanci.
Don haka a wannan gaɓar, duk yadda ta so jin abinda ya faru a asibitin sai bata ƙara cewa komai ba. Ta miƙe tsam, ta shige banɗaki ta tara ma Innaye ruwan wanka a bokiti.
Ko da ta fito, sai ta tarar Innaye har ta gama shirin shiga wankan, don haka bata sake ɓata lokaci ba ta fice zuwa cikin gidan da wani irin taku na musamman. Zuciyarta cike da saƙe-saƙen yadda za ta canja tsarin zamansu a gidan kafin su bar garin Abuja.
Su ba wulaƙantattu bane, don haka bazai yiwu Bintu ta cigaba da ɗaukarsu a wulaƙance ba. Ba maula suka je gidan ba balle ace za'a dinga ba su sadda aka so a hana su sadda aka ga dama.
Idan Bintu tana da ƴanci a gidan lallai su ma suna da shi. Da wannan daliln kuwa ko da tsiya ko da tsiya-tsiya za ta ƙwatar musu ƴancinsu, idan Yaya Hafiz yaga dama, yayi ƙuli-ƙulin kubura da ita. Amma tsakaninta da matarsa ba sauƙi ba sauƙaƙawa, shege ka fasa, ɗan halak sai yanka.
Tana waɗannan tunane-tunanen har ta ƙarasa cikin falon gidan, watsar da tunanin komai tayi ta buɗe idanu sosai tana kallon irin ƙayatattun kayayyakin da aka yiwa falon kwalliya da su. Duk da ba sanin kayayyaki masu tsada tayi ba, ido ba mudu bane amma ya san kima.
Kuma da ganin kura za ta ci akuya, ko da ganin kayayyakinnan maƙudan kuɗaɗe suka ja ba ƴan kaɗan ba.
Haka kawai, ba tare da sanin dalili ba sai hoton gidansu na can ƙauye tun daga soro har zuwa falo da uwarɗakin Innaye ya faɗo a cikin idanunta. Babu mahaɗa ko kusa, amma da ta tuna nisan tazarar da ke tsakanin rayuwar birni da na ƙauye sai ta ajiye tunanin komai ta ƙarasa cikin kicin ɗin.
"Baba Rabi an gama abincin ne?"
Ta tambaya da yanayin fuska kadaran-kadahan bayan sallama ƙasa-ƙasa da tayi a ƙofar kicin ɗin.
"Ba'a gama ba Auta."
Ta amsa da sauri cikin girmamawa, domin maganganun da yarinyar tayi ɗazu kafin ta fice daga kicin ɗin tana kuka sun tsaya mata a rai.
Da wannan dalilin yasa ta ƙuduri aniyar in Allah ya yarda ta ɓangarenta dai baza ta sake yin wani abu da zai nuna wulaƙantarwa ga tsohuwa da yarinyar ba, duk da daman dai tana yin komai ne don guje ma kuskurewa Uwarɗakinta. Don ta ƙara warware ma Zulaikha yadda tsarin girkin abincin ke tafiya sai ta cigaba da cewa
"Kin san yanzu ranar ta fara ɗagawa, kuma a ƙa'idar da Hajiya Bintu ta tsara zuwa uku na rana ne zan dinga raba abinci. Shi yasa na tsara komai yadda aikin zai dinga tafiya kan lokacin da ta tsara..."
"To madallah!"
Zulaikha ta katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta.
"Yanzu ya za'ayi? Me za ki samar ma Innaye mai ɗan sauƙi? Daga asibiti ta dawo kuma ta bar gidannan ko karyawa bata yi ba."
"Assha! Jikin ya motsa ne? Allah ya ƙara mata lafiya. To ko dai za'a haɗa mata Tea ne? Domin ya saɓa ma ƙa'idar Hajiya Bintu girka wani abu daban saɓanin wanda za'a dafa gaba ɗaya..."
"Wai wace ce kuma Hajiya Bintu da kike ta sako min sunanta a cikin maganganun da muke yi? Ya ina miki maganar mahaifiyar Maigidannan ta fita bata karya ba kina min zancen wata Hajiya Bintu da ta tsinci mai gidan a sama da haƙwaransa talatin da biyu? Dan Allah ki aje maganarta gefe kiyi abinda ya kamata. Ko Indomie ce da ƙwai ki dafa mata yanzunnan, idan kuma baza ki iya ba kina tsoron saɓa umarnin wacce kike ma aiki, ki kunna min abin girkin ki nuna min inda kayayyakin abincin suke, ni sai in dafa mata da kaina.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 40