ba, hatta Hafizu ba wani daɗinta yaji ba. Saboda yadda ya zaci Innaye za ta nuna ɗoki sosai irinna ƙaunar abin cikin ƙwai da yafi ƙwan daɗi bata wani nuna ba. A taƙaice ma yaron ko cikakken mintuna uku baiyi a hannunta ba ta miƙa shi ga Aunty Balira, ita kuma tana karɓa ta miƙa shi ga Bintu.
Haka suka zagaya ɗakunan sauran matan gidan suka gaishe su, ko ina suka je tambayar ina Zulai? Ya take? Me yasa ba'a zo da ita ba? Gaba ɗaya ya ƙarasa dusashe ɗan hasken Bintu da ya rage a gidan.
Ko tsarabar da aka raba na zannuwa da kuɗi da sunanta a wulaƙai sukai ta yi mata godiya, babu wani rawan jikin da suka saba yi idan ta musu kyauta a baya.
Duk tsawon awoyin da suka yi a ƙauyen Bintu ta kasa cin komai. Sai ɗan ruwan goran swan da ta ciro a cikin jakarta kawai take iya kurɓa saboda yadda bakinta ke ta bushewa kamar mai azumi. Daman ba abincinsu take ci ba, ba ta shan ruwan ƙauyen, amma a cikin babbar jakar hannunta akwai robar takeaway shaƙe da snacks, don tsananin takaici da baƙin cikin da suka shaƙa mata ta kasa buɗe jakar ta ciro balle har ta samu ƙwarin gwuiwar ci a gaban mutane.
Shi kuwa Hafizu ba ruwanshi, kunun zaƙi mai sanyi da Aunty Balira ce tayi aikatau ɗinsa ya sha sosai, shinkafa da miya da Umma laraba ta aiko musu da shi a kwanon samira sabo ya ɗiba ya take cikinsa, ko tayi bai ɓata lokacinsa wajen yi ma Bintu ba. Domin ya san ba ci za tayi ba, ya sani tun da daɗewa tsarinta ne ba ta iya cin abincin gidan sha'ani.
Har suka gama zamansu Baffa bai dawo ba. Amininsa ne ya rasu acan ƙauyen Guraji, nesa da su kaɗan. Tun safe Baffan yayi sammakon tafiya can gurin jana'iza, har yanzu uku da rabi bai dawo ba.
Sai saƙon kuɗi masu kauri Hafizu ya bar masa a hannun Innaye, ita kuma Bintu ta bada shaddoji kala uku da turaruka kala biyu a ajiye masa.
"Sannu da ɗawainiya Fatima. Mun gode, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuri'a."
Innaye tayi ma Bintu addu'a da murmushi a fuskarta, a zuciyarta take jinjina atamfofi kala uku da Bintun ta bata abokan zamanta kuma kala bibiyu.
Ƙarfe uku da rabi Hafizu suka sallaci la'asar, suka yi sallama da mutanen gidan gaba ɗaya, ƴan'uwa suka rako su har gurin mota ana musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya ya mayar da su gida lafiya.
Da Amin suke ta amsawa har suka shige cikin mota, direba yaja suka kama hanyar komawa gida.
Nannauyan ajiyar zuciya Bintu ta sauke idanunta a lumshe, hannunta ɗaya a kan Aadil da yake kwance a jikinta yana barci cikin nutsuwa, a hankali take ɗan shafa kanannaɗaɗɗen gashin kansa irinna jarirai.
'Uhmmm! Allah na gode maka. Idan kun sake ganina a wannan tsinannen ƙauyen naku ku yanka ni.'
Tayi maganganun a zuciyarta. Ranta a ɓace da irin wulaƙancin da su Rakiya suka yi mata a fili, kuma Innaye na gani bata ce komai ba.
[2/3, 10:17 PM] Fareeda Abdallah: ****** ******
Ƙwarya-ƙwaryan liyafar cin abinci Mummy ta haɗa ma ƴaƴanta, da dangi na kurkusa sosai, saboda murnar dawowar Kamal, Baban Imam. Kuma wani abin burgewa da ƙarin farin ciki shi ne yadda tafiyar tasa tayi nasara, gurin aikinsa da suka tura shi sun samu fiye ma da sakamakon da suka tsammata daga gare shi. Da wannan dalilin yasa tun kafin isarsa gida, ya samu ƙarin matsayi mai girma a gurin aiki, da kyaututtuka masu yawa daga gurin shugabanninshi.
Farin ciki ne ya haɗe musu kan farin ciki. Da wannan dalilin yasa Mummy da ƴan matanta Karima da Zulaikha, da Mai aikinta Rahina suka shafe fiye da awanni biyar a kicin suna dafa ƙayatattun girke-girke mabanbanta.
Da yake kicin ɗin mai faɗi ne sosai sai suka rarraba ayyukan yadda zai musu sauri. Suna aikin Hajja na zaune gefe guda akan kujera ƴar tsugune tana ba su nishaɗi da maganganunta na ban dariya. Sam ba ta gajiya, ta tsokani wannan ta taɓi wancan, hatta Mummy da ta kasance ƴarta bata raga mata ba.
Haka suka gama aikin ba tare da gajiya liƙis a jikinsu ba, suka lulluɓe komai a gayance. Sannan suka fice daga kicin ɗin zuwa ɗakunansu don yin wanka su shirya, kafin mutane su fara hallara. Tunda lokacin da aka saka na fara liyafar ƙarfe huɗu ne da rabi na yamma, yanzu kuma ƙarfe huɗu saura kwata.
Kamal ma ya iso daga Lagos tun ɗazu, yana ɗakinsa shi da manyan aminansa guda biyu, Auwal da Isma'il. Sai Imam da ya ƙi barin mahaifinsa ya huta, duk inda yasa ƙafa yana biye da shi, a ƙarshe nannauyan barci ne ya ɗauke shi acan ɓangaren Daddynsa.
Tsadaddiyar shadda Mummy ta ware zunzurutun kuɗi tayi musu anko gaba ɗaya iyalanta, kuma wani abin burgewa da armashi shi ne, hatta Zulaikha da ta kasance bare a cikinsu bata ware ba, a taƙaice ma, ɗinki da aiki duk iri ɗaya aka yi musu. Ta ƙara da siya musu mayafai masu kyau da za su shiga da kayan, da jaka, da takalma masu sauƙin tsawon dunduniya. Hatta ƴan kunne, sarƙa, zobba, awarwaro da za su saka a wannan rana duk sabbi Mummy ta siya musu. Ƙananun kaya na ciki kuwa abinda yasa bata siya musu da su ba, sati biyu da suka wuce ta kwashe su ita da kanta a mota suka shiga kasuwa, ko wacce ta ɗibi abinda take so, Mummy ta biya kuɗin ba tare da jin zafi ko ganin ƙyashi ba.
A farko-farkon zuwan Zulaikha gidan idan suka yi irin wannan fitar, aka ce ta ɗebi duk abinda take so, ba ƙaramin kunya take ji ba. Sai Karima ce ke warewa ta ɗiba mata kayayyaki masu yawa kamar yadda ta ɗebi na ta, to kuma sai ya kasance idan sun koma gida ta gwada kayayyakin wasu duk sai suyi mata kaɗan. Da taga dai asara take ja ma Mummy a hankali itama ta ware, duk abinda take buƙata na fannin inner wears ko sutura ba ta kunyar ɗauka, da wannan dalilin yasa a yanzu haka manyan akwatunan suturunta uku. Ita da taje gidan daga ita sai ghana must go. Shi yasa ako wane lokaci cikin addu'o'inta ba ta gajiya da yima Mummy da iyalanta fatan alkhairi, tabbas zamanta da su alkhairi ne, sun taka muhimmiyar rawa gurin canja mata rayuwarta gaba ɗaya.
Ƙarfe huɗu da kwata Zulaikha ta shiga ɗakin Karima bakinta a gaba, ta saka doguwar rigar shaddarta, amma ko Zip ɗin bata zage ba saboda yadda rigar ta ɗame ta daga saman ƙirjinta.
"Aunty Karima kin gani ko? Zip ɗin ya ƙi zaguwa. Sai da nace miki a ɗan ƙara kika ce ayi min wani fitted, ai yanzu sai ki san yadda za kiyi da ni..."
"Daɗina da ke ƙorafi ba ya miki wahala Zuly. To ai fitted ɗin kenan, dama wa ya faɗa miki idan aka yi riga fitted zip yana zaguwa a sauƙaƙe? Juyo bayanki mu gani in zage miki."
Karima ta ƙarasa maganar tana dariya.
Ko da ta juya, a sauƙaƙe aka zage Zip ɗin, sai dai har lokacin matseta da rigar tayi musamman ta wajen ƙirjinta bai saki yadda take so ba, sai ma ƙara fito da shape ɗin su da yayi.
Gaban madubi ta ƙarasa ta kalli yadda rigar tayi mata, ta juyo tana kallon Karima, idanunta sun yi ƙwalƙwal da hawaye.
"Yanzu saboda Allah ta ina mutum zai fara fita cikin jama'a da wannan ɗamammiyar rigar?"
"To miye a ciki? Ba akwai mayafi ba? Kina warware mayafin ta baya kika ɗan yafo shi zuwa gaba tsab zai rufe ɗan matsewarnan da bai taka kara ya karya ba, ke kuma sai wani ƙorafi kike yi. Kin ga ni don Allah yi min sassauƙar kwalliya ki ɗaura min ɗankwali, lokaci ya fara tafiya, tun ɗazu naji muryar su Mummy Balaraba da su Aunty Safina. Yanzu za kiji Mummy ta fara ƙwalla kiran mu fito. Ke ina naki ɗankwali da mayafin?"
"Suna ɗaki."
"Je ki ɗauko da akwatin kayan kwalliyarki mu ƙarasa shiryawa anan. Bari in saka ƴan kunne da sarƙa tunda ke naga har kin saka."
Duk da yadda suke cikin sauri, Zulaikha bata tafi bagazan-bagazan ko kuma ta sa gudu irin yadda take yi da ba. A nutse ta fara tafiya, manyan mazaunanta suna wani irin juyawa a slow motion.
Karima ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da murmushi.
"Ya Allah! Ina tawassali da kyawawan sunayenka da siffofinka maɗaukaka, ka haɗa wannan baiwa taka mai kyawawan halaye da nagartaccen miji ɗaya tamkar dubu. Amin ya rabb!"
Karima tayi ma Zulaikha addu'ar a fili, Allah ya sani tana ma Zuly wani irin ƙauna mai yawa, jin ta take kamar ƴar'uwarta ta jini. A yadda ta saba da ita yanzu, Har ba ta fatan ace ga ranar da Zulaikha za ta bar gidan.
Yana tsaye a gefen babban dining table ɗin da aka ƙayata kanshi da shimfuɗa mai kyau da ɗaukar idanu, kafin aka kawo manyan kulolin abinci aka shirya akan table ɗin. Wayarsa ce a hannunsa yana ɗan dannawa, gurin Karima ya nufa don karɓo kayan Imam. Amma ko da ya tunkari ɗakin nata sai yaji suna magana da Aunty Zulai, don haka ya koma da baya saɗaf-saɗaf ya tsaya can gurin dining table yana ƙoƙarin kiran Karima a waya.
Kamar ance ya ɗago kanshi, karaf idanunsa suka faɗa kan bayan Aunty Zulai da take tafe kamar wata wahainiya, baki da hanci buɗe ya bi ta da kallo da waya riƙe a hannunsa, har ta shige ɗakinta.
Yana nan tsaye ya sake ganin ta fito, matsewar rigar da yaji tana yi ma Karima ƙorafi ya gani a fili. Da sauri ya kawar da idanunsa yana ta'awizi a zuciyarsa saboda yadda abubuwan suka ɗauki hankalinsa cikin ƙanƙanin lokaci.
Ita kuwa da yake hankalinta ba shi akan kalle-kalle, bata ma san yana yi ba har ta sake shigewa ɗakin Karima.
Ya ɗauki fiye da mintuna uku tsaye a gurin, ba tare da ya san takamaimai tunanin me yake yi ba. Muryar Safina da ya ji tana fitowa daga ɓangaren Mummy, yasa shi barin inda yake tsaye da sauri, tun kafin tazo ta ishe shi da balaƴaƴƴen surutunta.
Sai da ya isa ɓangarensa, sannan ya kira Karima a waya yana mata ƙorafin barin masa hidimar Imam da tayi yau don kawai ta ga ya dawo.
"Yaya nima fa tuntuni Imam ya yaye ni, yanzu Zuly ce
. Komai nasa ita take mishi, ba ya yarda inyi masa wata hidima. Ka turo shi ta shirya shi, daman yanzu ta gama ƙorafin ka riƙe shi a gurinka ko shiryawa baiyi ba..."
"Lah! Kai Aunty Karima... Ni de ba ruwana..."
Daga can cikin wayar yaji muryar Aunty Zulai tana faɗin haka a shagwaɓe.
Haka kawai, wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce masa a fuskarsa. Jikinsa a saiɓance ya katse wayar, har lokacin murmushin da yake yi bar kan fuskarsa ba.
"Dude. Ya aka yi ne?"
Isma'il ya tambaye shi.
"Nothing."
Ya amsa a taƙaice.
Sannan ya mayar da hankalinshi kan Imam da yake zaune akan kujera yana daddana sabuwar Tab ɗin da ya kawo masa a cikin tsarabarsa. Da harshen nasara yace
"Imam, oya ɗauki Tab ɗin maza ka tafi cikin gida a shiryaka. Lokaci ya tafi, Aunty Zulai tun ɗazu take jajen inda ka shige..."
"Ok Dad!"
Ya amsa tun kafin uban ya rufe bakinsa. Da saurin gaske ya fice daga falon ya nufi cikin gida.
Alhamdulillah! Anyi liyafar cin abinci lafiya an gama lafiya. Zulaikha da ta kasance baƙuwar fuska a cikinsu ita ce ta dinga shan kallo, da tambayar Mummy wacece ita? Abu ɗaya da yayi ma Zulaikha daɗi shi ne yadda tun ma kafin Mummy ta amsa Hajja tayi karaf ta ce
"Ƴar ƙanwata ce tazo daga can gida."
Da haka ta kashe bakunan ƙannen mahaifin Karima biyu mata da suka fi takura mata da kallo duk inda ta motsa. Daga yanayin fuskokinsu, za a gane sam basu ji daɗin amsar da Hajja ta basu ba. Musamman duba da yadda Imamu ya maƙale ya mata, alamun shaƙuwa ƙarara tsakaninsu har ma fiye da ƴaƴayensu. Domin duk sun je gidan ne da ƴaƴansu mata budarai, zukatansu cike da burin Imamu ya zaɓi ɗaya daga cikin ƴaƴan a sake ƙulla zumunta mai ƙarfi.
Ita Aunty Balaraba, da ta kasance mai bi ma mahaifinsu Karima, ƴarta ta farko Aisha ita Kamal ya fara aura, cikin hukuncin Allah sai zaman baiyi tsawo ba, gurin haihuwar Imam Allah ya karɓi rayuwarta.
Daga baya ƙarara Aunty Balaraba ta sake ɓullo mishi da tayin auren Safina, wacce a wancan lokacin yarinya ce sosai. Ba tare da wani ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana ba ya ce ayi haƙuri, shi kam dai ba ya buƙata a lokacin.
Rasuwar matarsa Aisha ba ƙaramin bugunsa yayi ba, shi yasa ya tattare zancen auren gaba ɗaya ya jingine gefe ɗaya. To tun a wancan lokacin dai basu haƙura ba, shekaru shidda kenan. Safina ta zama cikakkiyar budurwa, kuma ƙarara ita ma take nuna mishi tana ra'ayinshi.
Ita kuwa Aunty Lubabatu da take bin Aunty Balaraba a haihuwa irin abinnan ne na bahaushe da yake cewa a rashin tayi ake barin arha. Tun a wancan lokacin, duk sun san Kamal ya ce baya ra'ayin auren Safina, don haka a yanzu da nata ƴar mai suna Salma ta taso ta zama budurwa sai take cusa ta, da addu'ar Allah yasa rabon a gidanta yake. Domin Kamal miji ne na kerewa sa'a, na bugawa a jarida. Tun Salma tana nuna ba ta ra'ayinshi har dai uwar ta fara cin galaba a kan ta.
Amma dukansu da yake sun san Kamal ɗin ba'a zuwa mishi da wargi. Hatta ƙannan uban nashi a hankali suke bin shi, saboda girmamawa ce tsakaninshi da su gaba ɗaya. Ga alkhairin da yake musu ako wane lokaci kamar bai san zafin kuɗi ba. Shi yasa duk suke abin nasu cikin iya taku da gogewa don kar su ƙona sunkurun kashinsu.
Ita kanta Mummy, duk da ɗan'uwan nasu ya bar duniya. Har yanzu tana ɗaukarsu da girma sosai, kamar ƴan'uwanta ne su ɗin ba na mijinta ba. Sannan duk wani sha'ani nasu idan ya taso da jikinta da aljihunta ba ta jin ƙyashin yi musu hidima. Sosai girmamawa da mutuntawa ke tsakaninsu.
[2/4, 10:46 PM] Fareeda Abdallah: Ko a yanzu, bayan gama liyafar cin abincin ya miƙe tsaye yayi musu godiya sosai. Da yake tun farko Mummy ta tsara abin a ƙayyade ne, ta lissafa mishi duk waɗanda za su halarta.
Ya riga ya gama shirya duk abinda zai raba musu na tsaraba ya damƙa ma Mummy. Yana gama yi musu godiya yaja abokansa zuwa ɓangarensa.
Bayan gama tattare duk abubuwan da aka yi amfani da su Karima da Zulaikha Mummy ta umarta kan cewa suje ɗakin Hajja su kwaso mata jakunkunan tsarabar da suke ajiye a cikin ɗakin. Abinku da ƴan boko wayayyu, masu yin komai cikin tsari, ko wace jaka maƙale take da sunan mamallakiyarta, kuma saman jakar a rufe yake da wani irin abin maƙalewa, babu wacce za ta ce ga abinda ke cikin jakar ƴar'uwarta in dai ba buɗe jakar aka yi ba.
Cikin nutsuwa Mummy ta gama rarraba musu tsarabarsu. Ta ƙara da yi musu godiya sosai, zuwa ƙarfe takwas na dare, gidan ya zama saura su kaɗai, baƙin da suka halarci liyafar duk sun koma gidajensu, zukatansu cike da farin cikin tsarabar da Kamal yayi musu.
Misalin ƙarfe goma da rabi na dare. Kamal ne kwance a gefen katifar Mummy can cikin Bedroom ɗin ta, hira suke yi a nutse. Yana sake bata labarin yadda yanayin tafiyarsa ta kasance, da irin yadda komai yazo masa a sauƙaƙe acan ɗin, da irin nasarorin da ya samu a tafiyar tasa.
Bayan ta gama jera mishi fatan alkhairi da addu'ar Allah ya ƙara ɗaukaka sai ta kira sunanshi a nutse. Da irin salon da ke nuna lallai ko me za ta faɗa muhimmiyar magana ce za ta yi mishi.
"Na'am! Mummyna."
Ya amsa a tausashe. Yana ƙara ba ta dukkan hankali da nutsuwarsa.
"An daɗe idan nayi maka maganar aure kana cewa ka damƙa min wuƙa da nama wajen zaɓin matar aure. Tambayarka zanyi, ka samu matar auren ko har yanzu lalube kake a cikin duhu ko kuwa jiran tsammani kake yi?"
"Mummy, babu ko ɗaya gaskiya. Zancen auren ne fa gaba ɗaya na jingine shi gefe ɗaya. Ko kin sama min matar auren ne?"
Ya tambayeta, da murmushi a fuskarsa.
"Eh! Na sama maka."
Ta amsa da dukkan gaskiyarta.
A nutse ya miƙe zaune daga kishingiɗar da yayi, saboda yadda maganar ta bugi zuciyarsa. Bai taɓa ɗauka za ta ce ta zaɓa masa mata ba, shi yasa a yanzu da ta faɗi ta zaɓa masa maganar ya bashi mamaki.
"Wace ce? Mummy wa kika zaɓa min? Kin sani ni mai biyayya ga umarninki ne ko da zuciyata ba ta so..."
"Babu ma zancen dole a ciki. Shawara ce ba umarni ba. Kaje kayi addu'a, ka nutsu, ka kalli rayuwar ɗanka da Allah ya baka a yanzu da can gaba. Zulaikha, ita ce yarinyar da na zaɓa maka saboda dalilai masu yawa. In dai kaji zuciyarka ta nutsu da ita, ni kam ina maraba da ita a matsayin sarkuwa, domin na yaba da ita ɗari bisa ɗari..."
"Aunty Zulan Imam kike nufi Mummy? Kina ganin banyi mata tsufa ba? Shekaruna talatin da takwas fa, ni ina mata kallon kamar yarinya ce ƙarama."
"Ba wani tsufa da kayi mata, sai dai idan bata yi maka ba, bazan tilastaka ba. Kaje ka huta, kayi addu'a, kayi tunani a nutse. Zuwa nan da sati mai zuwa kazo min da cikakken amsar da ka yanke."
"To Mummy. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Amin ya rabbi."
Da haka suka yi sallama ya fice zuwa ɗakinsa, zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka yi da Mummy.
A wannan dare, duk irin gajiyar da ke jikinsa bai samu wani wadataccen barci ba. Da ya fara sai ya farka a nutse, zuciyarsa sai hasko masa Zulaikha take yi a sadda ya ganta ɗazu babu mayafi, da kuma irin ganin da yayi mata lokacin liyafar nan.
Babu laifi, ta yi daidai gwargwado. Sai dai abin dubawar shi ne ita za ta iya amincewa da shi a matsayin mijin aurenta kamar yadda Mummy take so? Domin shi fa bai wani iya soyayya ba, ko Aisha a haka suka yi rayuwar babu wani romansiyya ta musamman.
Wayarshi ya ɗauko, ya buɗe hotunan status da ƙanwarsa take sakawa na Zulaikha ya fara kallo ɗaya bayan ɗaya.
"Uhmmmm!"
Yaja nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ajiye wayar gefe ɗaya.
Zuzzurfan tunani ya afka a ciki na tunanin makomar rayuwar ɗanshi Imam, kamar yadda Mummy ta umarce shi. Ya sani ko ya ƙi ko ya so duk tsawon zamani dole ya nema ma Imam wacce za ta zame mishi makwafin uwa.
Ada can baya har ya fara tunanin zai iya haƙuri ya auri Safina ko don saboda Imam, amma sai yaga sam babu wata shaƙuwa ko shiri tsakanin Imam da Safina. Idan Imam yaje can gidan yi musu hutu a matsayinsu na kakanninshi, duk dawowa idan Imam ɗin yayi ya dinga mishi ƙorafin Aunty Safina kenan, ya dai fahimci kamar ba ta da haƙuri da yara. Da wannan dalilin yasa lamarinta ya sane mishi a zuciya.
Ita kuwa Aunty Zulai... shi da kanshi idan ya zauna yana mamakin yadda matsananciyar shaƙuwa ta shiga tsakaninta da Imam. Kuma a cikin ƙanƙanin lokaci haka, Imam bai taɓa kai mishi ƙarar Aunty Zulai ba. A kullum alkhairinta yake faɗa mishi.
Daga ƙarshe dai, Kamal tattare tunanin komai yayi ya aje gefe ɗaya. Ya shige banɗaki ya ɗauro kyakkyawar alwalarsa, ya shimfiɗa dadduma ya fuskanci gabas, ya kabbarta sallah don neman zaɓin Allah.
Kwanaki bakwai da Mummy ta bashi yayi tunani, ya shafe su ne cikin yin sallar istikhara ako wane dare. Kuma cikin hukuncin Allah a kullum al'amarin ƙara kwanciya yake male-male a cikin ransa. Ƙara samun nutsuwa yake yi ta musamman.
Da yake an bashi hutun sati biyu a gurin aikinsa, shi yasa yake ƙara samun lokacin zaman gida sosai, kuma ya mayar da zaman nasa ya fi ƙarfi a ɓangaren su Mummy da ɗakin Hajjah.
Ba domin komai ba, sai don ya ƙara fahimtar wai wacece ma Zulaikha? Don haka a fakaice kuma a hankali yake karantar duk yanayinta da ɗabi'unta.
Zulaikha kuwa tun tana ɗari-ɗari da sakin jiki har dai sannu a hankali ta fara sakin jikinta. Saboda ko ta janye jikinta shi da kanshi ko Mummy ko Karima ko Hajja sai sun janyo ta, a dole ma ta fara sakin jikinta.
Matsakaitan akwatuna ya kawo musu shaƙe fal da tsaraba ita da Karima. Sai dai kusan gaba ɗaya kayan na turawa ne, ita kuma bata saba saka su ba. Don haka ta nemi guri ta adana akwatin, ba tare da tunanin ranar da za ta iya saka ɗaya daga cikin kayayyakin ba.
Kwanaki bakwai na cika cif! Da kanshi ya samu Mummy a ɗakinta ya sanar da ita ya amince.
"To Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Sai ka dage kayi ƙoƙarin neman soyayyarta..."
"Soyayya kuma Mummy? Sai kace wani ƙaramin yaro?"
Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.
Daƙuwa tayi mishi da ƴan yatsunta kafin ta amsa mishi da
"A'a kai ka yanke ma ƙasa cibiya saboda tsufa Baban Imam! To ina tabbatar maka idan baka nemi soyayyarta ba baza ta taɓa aurenka ba, kana zaune garin kallon ruwa kwaɗo zaiyi maka ƙafa. An faɗa maka irin waɗannan kyawawan yaran masu nutsuwa ana sake da su ne? Uhmmm! Ka zauna nan dai, sai dai kaji wufff! Wani ya yi awon gaba da ita..."
"Haba Mummy... wannan fa kamar kina min baki ne. Bayan kuma ke da kanki kika kwaɗaita min aurenta a raina."
"Eh! Duk da haka kuma ai ban ce zan tilastata ta so ka ba. Idan kana son ta ka zubar da duk wani girma ka nemi soyayyarta, na faɗa maka."
Da haka suka rabu da Mummy, ya fice daga ɗakin yana tunanin shi ta ina ma zai fara?
Bayan ɓata hankalin dare da yayi yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin kwarkwanta notikan Autar Innaye cikin kwanaki ƙalilan. Mataki na farko da ya fara bi shi ne karɓan lambar wayarta ta hannun Karima.
"Yaya?"
"Lafiya kuwa?
"Allah yasa dai ƙanwar tawa ba laifi tayi ba?"
Ta jera mishi tambayoyin a firgice.
"Kin shiga uku da sa'ido Karima. To tambaya zanyi mata akan Imam."
Har za ta sake jefa masa wata tambayar, wani ɗan tunani da tayi kuma yasa ta sakin murmushi. Katse kiran tayi, cikin ƙasa da minti ɗaya ta tura mishi lambar Zulaikha, a ƙasan lambar ta ƙara da
"Allah yasa mu ji alkhairi Yayana."
Dariya kawai yayi, ya amsa addu'ar a fili amma bai mayar mata da martani ba.
******
Sannu a hankali cikin kwanaki ƙalilan shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin Abban Imam da Umman Imam. Kamar yadda Zulaikha take kiranshi shi ma yake kiranta, amma ƙarfin shaƙuwar tasu ta fi a waya, gurin chatting da kuma kiran da yake yawan takura mata da shi da cewar ya kira ne suyi hira, yana gidan ko ba ya gidan.
A cikin kwanakin ya hana ta da zuciyarta sakat! Duk inda ta bi da tunaninsa maƙale da ita, saboda yadda yake yawan sakota cikin al'amuransa. A cikin hirarrakin da suke yi, cikin hikima ya bata labarin kaso saba'in cikin ɗari na rayuwarsa.
Yanzu har an kai matakin da idan ya tafi gurin aiki kafin ya dawo zai kira ta ya faɗi abincin da yake so ta dafa mishi. Ita kuma bata taɓa ce mishi a'a ba, yana dawowa zai tarar da abinda yake so an jera mishi a dining ɗin ɓangarensa. Sai dai ba ta taɓa yarda ta ƙetara iyakar addininta wajen mu'amala da shi, a taƙaice ma, ta fi sakewa da shi suyi hira sosai ta waya, a fili ba ƙaramin kunyarsa take ji ba.
Tana zama a inda yake suyi hira ne kaɗai idan su Mummy suna gurin, duk yadda yaso su dinga keɓewa ta ƙi bashi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 40