Share this page
yake jan numfashi yana saukewa a zafafe cikin damuwa shi ne abinda ya ɗan so ɗaga mata hankali. Alal haƙiƙa a yanzu kam shi ya bata tausayi ba halin da Innaye ke ciki ba. Don haka tayi shiru tana tunanin da zai samar mishi da mafita, duk da dai ba ta ƙaunar cigaba da zaman su Innaye a gidanta saboda damuwarsa kaɗai yasa ta cewa "To ko dai za ka mata dabara ne kai tafiyarka Ofis ne ka ƙyale su a gida? Idan bata ganka ba ai dole ta haƙura da zancen tafiya gida ayau ɗin. In yaso idan zan dawo gida sai in taho mata da wasu magungunan saɓanin wanda take sha, duk da dai ba haka na so ba." Da yake wayar da yake yi a ƙofar shiga ɓangaren da Innaye take ne, ya buɗe baki zai ba Bintu amsa kawai sai ganin Zulaikha yayi ta fito tana riƙe da Innaye, sun shirya tsaf! Da alamun gajiya sukai da jiransa suka fito. Ransa a ɓace ya galla ma Auta harara kafin yayi ma Bintu sallama a gaggauce, ba tare da ya bata amsa kan shawarar da ta bashi ba. "Me yasa kika fito da ita ba tare da nayi miki umarni ba? Ko an faɗa miki na gama shirye-shiryen tafiya ne...?" "Yaya ba fa laifi na bane. Tun ɗazu ita ta matsa min in fito da ita, da nace mata baka shirya ba sai cewa tayi mu fito ko a motan haya ne mu tafi. Ta rantse ta sake rantsewa da Allah ita kam ba ta ƙara kwana a gidannan." Sau uku yana buɗe baki da nufin yin magana amma ya rasa ta cewa. Sai kawai ya juya zuwa tsakar gidan suka bi bayanshi, shi kaɗai yake ta ƙwafa yana jan tsaki saboda tsananin damuwa da ƙuncin zuciya. Direba yana kan wanke motar da za suyi tafiya a cikinta ganin fitowar su Innaye a dole ya dakata. Yadda aka tarairayota yasa da saurin gaske ya kai hannu zai buɗe ƙofar baya sai Hafiz ya riga shi buɗewa. Da sassarfa ya ƙarasa ya karɓe ta a hannun Zulaikha ya ƙarasa da ita cikin mota ya zaunar da ita. Idanunshi akan Zulaikha har lokacin bai saki fuskarsa ba ya ce "Shiga kusa da ita ki zauna, idan ta gaji da zama ki kwantar da ita a jikinki." "To Yaya. Amma ban fito da kayanmu ba, bari in je in kwaso..." Da tsawa sosai a muryarsa ya katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta. "Dallah shiga cikin mota zan je in kwaso muku. Kuma ina fatan kin haɗa har da sauran magungunanta da alluran da suka rage?" "Eh." Ta amsa da sanyin murya. A zuciyarta kuma cewa tayi 'Balaƴaƴƴe, ka ci kanka kasha baƙin ruwa. Gidanka ne dai ko kana so ko ba ka so yau za mu bar shi.' Da sauri ta shige cikin mota ganin har lokacin bai daina aika mata da wani fusataccen kallo ba. Kayansu gaba ɗaya a ghana most go ɗaya ne. Don tabbatar da bata manta da magunguna da alluran Innaye ba sai da ya buɗe jakar ya gansu sannan ya maida jakar ya rufe ya ɗauka zuwa mota. Saboda irin jan ƙafar da yai tayi za su tafi baza su tafi ba, ya shiga cikin ɓangarensu ya ƙi fitowa akan lokaci kuma shi ba wani takamaimai abu yake yi ba basu bar gidan ba sai ƙarfe goma da rabi na safe. Tun da Hafiz yayi aure, zuwanshi ƙauye ya kwana ɗaya bai fi sau bakwai ba. Duk sa'adda za su tafi asubanci suke bugawa yadda za su isa da wuri, ya gama duk abinda zaiyi zuwa la'asar su ɗauko hanyar komawa Abuja, komai dare a gida yake kwana. Ko a yanzu direba ya zaci irin waɗancan tafiyoyin da suka saba yi ne na yini ɗaya. Don haka ya ƙure manejin mota yana ta zabga gudu kamar masu shirin barin ƙasar. Ko da suka isa Kaduna baiyi niyyar tsayawa ba sai da Hafiz ya ce mishi ya tsaya ya sai ma su Innaye abinci, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar azahar a wasu masallatai. Da yake ko bayan an isa Kaduna tafiya ce miƙaƙƙiya zuwa ƙauyen Faƙo, ga kuma tsiya irinta ƙarfen nasara da ba ta da tabbas. Bayan tsayawa gyara da suka yi a garin Kujama basu isa Faƙo ba sai La'asar. Sun isa ƙofar gidansu Innaye daidai lokacin da aka fito sallar la'asar a babban masallacin da yake ƙofar gidan. 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Hafiz ya faɗa a zuciyarsa hankalinsa a tashe. Ko kafin ya waiga yayi ma Zulaikha umarnin ta dakata da buɗe ƙofar sai mazan da suke fitowa daga masallaci sun ragu har ta riga ta buɗe ƙofar ɓangarenta, ta zura ƙafafunta zuwa waje, fuskarta cike da matsanancin farin ciki na ganinta a ƙofar gidansu. Kafin ma ya kira sunanta har ta fita waje. Bai ƙara tabbatar da rashin hankali da wautar Zulai ba sai da yaji ta buɗe murya tana ƙwala ma mahaifinsu da yake tsaye suna magana da Ladan kira. "Baffah... Mun dawo." Hakan bai ishe ta ba sai da ta ƙara da "Zo ka ga Innaye ba ta da lafiya sosai." Wannan maganar da ta faɗa shi ya dawo da hankalin gaba ɗaya mazan da suke tsaye a gurin zuwa kan motar Hafiz. Kun san mutanen ƙauye da kara, ɗuuuuu kusan gaba ɗaya suka yo gurin motar. Babu abinda ke fita a bakunansu sai "Assha! Subhanallahi! Hajiya Rahina jikin ya motsa kenan." Tsananin damuwa da ɓacin ran abinda Zulaikha ta aikata yasa idanun Hafiz suka cicciko da hawaye. Ba shi da yadda ya iya, haka nan ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya fita waje ya tarbi mahaifinsa da sauran mutanen gurin da suka rufu a kanshi suna mishi jajen ya mai jiki? Haka nan yake ta amsa musu cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali. Bai san Yaya aka yi ba yana cikin mazan nan sai ganin matan gidansu abokan zaman Innaye yayi sun fito, suna sanye da zumbula zumbulan hijabai, biye a bayansu Zulai ce tana musu jagora zuwa gurin motar ɓangaren da Innaye ke kwance. Kafin ya ce wani abu har Zulai ta buɗe musu ƙofar, su kuma suka tarairayo Innaye da gajiyar zaman mota da rashin ƙarfin jikin da take fama da shi ya ƙara ramar da ita. Suna riƙe da ita sannu a hankali suke amsa gaisuwar mazan da suke mata ya jiki har suka shigar da ita cikin gidan. Kamar wutar daji, haka zancen gaggarumin rashin lafiyar da Innaye ta dawo da shi ya fantsama a ƙauyen Fako cikin kankanin lokaci. Suna tsaye a ƙofar gida, bayan watsewar maza masu jajantawa yana yi ma mahaifinsu da yan'uwansa biyu ƙarin bayanin ciwon Innaye bazai iya ƙididdige yawan matan da suka shiga cikin gidan duba jikin Innaye ba. Kun san ƙauye da kara da mayar da al'amarin wani nasu. Balle kuma Innaye da ta kasance mace ta mutane, kowa nata ne. Daɗin gushi kuma macece da hannuwanta yake a buɗe, sam abin hannunta bai rufe mata idanu ba. Hatta kishiyoyinta biyu in dai batu na adalci da gaskiya za su fad'a ba ƙaramin daɗin zama da ita suke ji ba. Da gangar baza a zage ta ba sai dai son zuciya ko zalunci da ba'a raba zukatanmu na ƴaƴan Adam da shi. Duk nisan da gidajen Yayyinshi suke da shi cikin ƙanƙanin lokaci har labarin yadda ya dawo da mahaifiyarsu ya iske su a gidajensu. Ko kafin ya saɓulewa tambayoyin mahaifinsu ya shiga cikin gidan har yayyenshi sun iso. Shi kanshi idanunshi duk sun faɗa ciki saboda fargaba, gajiya, da tashin hankali. Idan ya kalli direbanshi sai yaji ya bashi tausayi, saboda yau ko arzikin ruwa da furar da ake tarbarshi da shi bai samu ba. Daƙyar ya ƙwaci kanshi a hannun mahaifinshi da ƴan'uwan Innaye da suke ta tuhumarshi yadda aka haihu a ragaya ya shige cikin gidan, lokacin ƙarfe biyar da minti goma na yamma. Ganin yadda Yayyenshi suka tasa Innaye da aka yi mata wanka tana kwance akan darduma a gaba suna ta sharɓan kuka, ita kuma Zulaikha tana gefe cikin nata kukan take ba su labarin mafarin ciwon Innaye yasa idanunshi rufewa, bai san lokacin da ya nufe ta gadan-gadan zai rufe ta da duka yana surfa mata zagi ba. A guje, kuma a tsorace Zulaikha ta daka tsalle ta ruƙunƙume Aunty Rakiya sannan ta ƙwallah ihu tana karaɗin a ceceta zai kashe ta. "Hafizu me zan gani haka?" Ta jefa mishi tambayar tana bin shi da wani irin kallo mai nuna tozarci ƙarara. Kafin ya amsa ta cigaba da cewa "Me tayi maka za ka doke ta? Kawai daga tana faɗa mana yadda aka yi mahaifiyarmu ta kamu da wannan gagarumin ciwon shi ne za ka duke ta don zalunci da son zuciya? Ashe daman ƙarya kake faɗa mana cikin kwanakinnan idan muka kira ka muna tambayar ya jikin Innaye? To me kake nufi? Iye? Na ce me kake nufi Hafizu? Ko so kayi sai ta mutu sannan ka sanar mana da...?" "Kul! Kul!! Kul Rakiya... A kul!!! Kar in sake jin irin wannan mummunar maganar na fita daga bakinki." Mahaifinsu da shigarsa cikin ɗakin kenan ya tarar da ita tana wannan faɗan ya katse da tsawatarwa. Guri ya nema kan kujera ya zauna idanunshi akan Innaye. Har yanzu gani yake kamar idanunshi ne ke mishi gizo, ya kasa gasgata wai Innaye ce tayi irin wannan rama da tsofewar a cikin kwanaki takwas kacal da barinta garin Faƙo. In banda yana da tabbacin duk lalacewar zamani babu ta yadda za'ayi a haɗa baki da ɗa a cutar da uwa mafi soyuwa a zuciyarsa da tabbas zai ce da haɗin bakin Hafizu aka ƙara kwararraɓa jikin Innaye sanadiyyar magunguna da allurai. Amma kuma da ya tuna komai yana faruwa ne da ikon mahaliccin sammai da ƙassai. Sannan wasu cutukan ba sa tashi a jikin mutum sai an sha wasu magungunan, kuma haka kawai idan Allah ya tashi gwada ikonsa ba cikin kwanaki huɗu ba, a cikin yini ɗaya ma yana iya jarabtar bawa da cutar da ta ninka wannan. Sai yayi saurin kore zargin magunguna da alluran da Bintu take ba Innaye har ma yayi istigfari. Kawar da idanunsa yayi daga kan Innaye ganin yadda tun shigarsa cikin ɗakin ƙananun hawaye ke ta tsattsafa a kwarmin idanuwanta ta kasa cewa komai. Ko tunanin me take yi a zuciyarta? Sanin gaibu sai Allah. Umarnin zama yayi ma Hafiz da tun maganganun da Yayarsa Rakiya ta caccaɓa masa yake tsaye kamar mutum-mutumi. Kallo ɗaya za'a mishi a hango gagarumin ɓacin rai da tashin hankali a tare da shi. "Hafizu ne mi guri ka zauna." Ya sake umartarshi a karo na biyu cikin ɗaga murya, ganin umarnin farko da yayi mishi hankalin Hafiz ɗin yayi nisa cikin tunani har bai san yana mishi magana. Daga nan inda yake tsaye, kawai ya sulale zuwa ƙasa ya zauna ba tare da damuwa da inda ya zauna ko kuma yanayin gurin da ya zauna ba. Nasiha mai ratsa jiki sosai mahaifinsu yayi musu, ƙarara ya nusar da su muhimmancin yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau. "Cuta, mutuwa, rayuwa, abubuwa ne da babu wani bawa da ya isa ya saka ma wani bawa su sanadiyyar magani ko wani allura face sai da yarjewar Ubangiji. Don haka daga yanzu, kar in ƙara ji ɗaya daga cikinku ta ce sanadin magani da allurar da matar Hafizu tayi ma Rahina (Asalin sunan Innaye) ne yasa ciwo suka tasar mata haka. Ina fatan kun fahimce ni?" Ya ƙarasa maganar da ɗaga murya. "Eh! Mun ji Baffa. Za mu kiyaye in Allah ya yarda." Gaba ɗaya yayyen suka haɗa baki gurin faɗin haka. "Ke Zulai?" Ya kira Auta da tsawa-tsawa. A tsorace ta amsa tana sake maƙure jikinta a na Yayarta Rakiya. "Daga yanzu, kar in sake ji kin ba wani ko wata labarin magani da alluran da aka yi ma Rahina. Kina ji na?" "Kayi haƙuri Baffa. Bazan sake ba." Ta amsa a tsorace bakinta na rawa. "Sannan ku kuma ko da wasa kar ku kuskura ku ce za ku bari wani saɓani ya gitta tsakaninku da ɗan'uwanku don ɗan wannan abun da ya faru. Idan za ku yima lamarin duba da idanun basira, tsoro da fargaban irin tashin hankalin da za mu shiga idan muka ji labarin halin da take ciki shi yasa shi ɓoye mana komai. Wannan dalilin kaɗai ya isa yasa muyi mishi uzuri. Kai Hafizu a matsayinka na ƙarami ba Yayyinka haƙuri." Cikin ƙan-ƙan da kai, da nuna nadama a fili ya ba su haƙuri kamar yadda Baffa ya umarce shi. Tare da alƙawarin abu makamancin wannan bazai sake faruwa ya tafka irin wannan kuskuren na ɓoye musu ba. Cike da ƙauna suka karɓi tubansa. Yaya Rakiya da ta jefe shi da munanan kalamai ita ma ta bashi haƙuri. Cikin kankanin lokaci suka fahimci junansu, bayan mahaifinsu ya kara janyo hankalinsu akan kar su kuskura ko da wasa su bari wannan abu da ya faru yasa su canja ma Bintu fuska a matsayinta na matar kaninsu. "Na tabbata irin k'aunar da yarinyar nan take yi ma Hafizu bazai taba bari ta iya cutar da mahaifiyarsa da gangar ba. Kar ku bari shaid'an la'ananne yayi galaba a zukatanku kun ji ko?" "To Baffa! Allah ya kara lafiya da nisan kwana." Kiran sallar magriba yasa Baffa da Hafiz ficewa daga d'akin. Su ma matan fita suka yi waje don d'auro alwala. Kamar 'yar karamar yarinya haka aka tasa Innaye da tarairaya da kulawa ta ko wane 'bangare, ba daga 'bangaren yaranta da mijinta ba, ba daga 'bangaren kishiyoyi, danginta da abokan arzikinta ba. Haka aka tara mata kwanonin abinci fiye da goma a gabanta. Amma saboda yanayin bakinta da babu dad'i dak'yar ta iya tsakurar tuwon dawa miyan gatsiga da aka aiko da shi daga gidan k'aninta Iro. A k'arshe dai shayi aka had'a mata mai kauri shi ma kad'an tasha ta ce ta k'oshi. Farin cikin tsintar kanta a cikin iyalanta kaɗai ya taka muhimmiyar rawa gurin dakushe rashin ƙarfin da take ji a jikinta. Duk da bata furta ba, amma sosai yanayin fuskarta ke ƙoƙarin nunawa har Auta ta fahimci haka. "Innaye? Ko dai gobe da safe mu bi Yaya mu sake komawa Habuja ne?" Auta ta tambayeta cikin tsokana ganin yadda akai akai take bin ƴaƴanta da kallo tana ƙoƙarin sakin murmushi. A yanzu ma murmushin ta ƙara yi, bata ce komai ba sai daƙuwa da ta ɗaga yatsunta tayi ma Auta. Su kuma sauran ƴaƴan nata suka yi dariya. A daidai lokacin Hafiz yayi sallama ya shiga ɗakin, hannunsa riƙe da jakar kayan su Innaye. A bayansa kuma direbansa ne ɗauke da katan ɗin ruwan gora guda uku, bayan ya gaishe da mazauna cikin ɗakin ya ƙara yi musu ya mai jiki, bai ɓata lokaci ba ya fice daga cikin ɗakin. "Ta ci abinci kuwa?" Tambayar da Hafiz ya fara yi kenan bayan ya zauna, idanunsa na kan Innaye shi ma yana karantar cigaban da aka samu a lafiyar jikinta. "Eh! Ta ɗan ci, amma ka san bakin babu ɗanɗano, dole cin abincin kaɗan-kaɗan ne." Yaya Balira ta amsa mishi. "Haka ne! Allah ya ƙara sauƙi. Yanzu kafin shigowata na duba Chemis ɗin Habu ban ganshi a ciki ba, sai dai idan ya buɗe sai in kira shi yayi mata allura. Yanzu bari a fara ba ta magungunan..." "Magani kuma Hafiz? Anya baza'a haƙura da magani da allurannan ba?" Aunty Ladidi da bata cika magana ba a cikinsu ta faɗa idanunta a warwaje. Da alamun har lokacin bata manta labarin da Zulaikha ta basu ba. Kallonta yayi, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallonsu hannunsa riƙe da ledar maganin Innaye. Yana jin yadda kaso hamsin cikin ɗari na ɓacin ransa da ya sauka sanadiyyar nasihar da mahaifinsu yayi musu yana ƙoƙarin dawowa sabo fil a zuciyarsa. Yaya Balira da ta kasance babba a cikinsu ne ta gyara zama ta fara yi mishi ƙarin bayani cikin tausasa kalamai. "Kayi haƙuri Hafizu, ka kwantar da hankalinka. Kar ka bari ranka ya ɓaci dalilin maganar da Ladidi tayi. Allah yana ganin zukatanmu ba wai mun raina ƙoƙarinka da na iyalinka bane. Amma abu ɗaya da nake so ka fahimta shi ne, ko da muke mutanen ƙauye, daidai gwargwado ka san Baban Yasin (Mijinta) a baya ya ɗauke ni munyi zirga-zirgan asibitoci da yawa na cikin Kaduna saboda matsalar haihuwa da nayi fama da shi. Ina yawan ganin idan magani yayi ma mare lafiya ƙarfi canja mishi ake yi. Idan kuwa likita ya ƙi canja ma mare lafiya magungunan da suka mishi ƙarfi shi mare lafiyan yana da ikon ya canja asibiti don ya gana da wani likitan ko warakarshi anan take. Mu kanmu haka mukai tayi har dai daga bisani muka miƙa ma Allah al'amarin, sai daga baya kuma waraka tazo mana daga Indallah. A lamarin ciwon Innaye ma yanzu kam shawarar da muka gama yankewa kenan, kamar yadda na faɗa maka da farko, ba don mun raina ƙoƙarin Bintu bane za mu ɗauki wannan matakin. A bayyane yake waɗannan magungunan sun yi ma Innaye ƙarfi, don haka gobe da sassafe idan Baban Yasin zai fita da mota zamu tafi da Innaye asibitin dutse ko Barau Dikko a cikin Kaduna a sake dubata a canja mata magunguna..." [12/27, 5:16 PM] Fareeda Abdallah: "Na fahimce ki Yaya Balira. Babu komai, Allah ya kaimu gobe da safen. Ki shirya da wuri sai mu wuce da ita asibitin." Ya faɗa a nutse ba tare da fuskarsa ta nuna ɓacin rai ko kaɗan ba. Gaba ɗayansu sun ji daɗin yadda ya nuna sauƙin kai da fahimta cikin ƙanƙanin lokaci. "Allah yayi maka albarka Hafizu." Innaye ta faɗa cikin sanyin murya, da alamun ita kanta ta ji daɗin amincewar da yayi a sauƙaƙe. "Amin Innaye. Allah ya ƙara miki lafiya." Ya faɗa da bayyanannen farin ciki a fuskarsa, sosai yaji daɗin saka albarkar da tayi masa. Ko babu komai a yanzu zuciyarsa ta ƙara gamsuwa Innaye bata ƙullace shi ba kan abinda ya faru. Dukkansu ƴaƴan Innaye mata sun so su kwana a gurinta amma mahaifinsu ya fatattake su zuwa gidajensu. "Sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa muke? Ca nake acan Habujan ma Zulai ita kaɗai take kwana da ita babu abinda ya faru balle nan gida cike da mutane? Kwanan da za kuyi a gurinta ya isa yasa ko hana Allah ikonshi ne?" Da sauri duk suka girgiza kai fuskokinsu a dame. Domin ba haka suka so ba, amma baza su iya mishi musu ba saboda tarbiyar da aka ɗora su akai. Abinda suka sani ne ko sun tafi gida hankulansu ba kwanciya zai yi ba, Zulaikha ta faɗa musu ciwon Innaye cikin dare ne yake tashi gadan-gadan, ba fata suke ba idan wani mummunan abu ya faru da ita a bayan idanunsu fa? Kamar ya san tunanin da suke yi sai ya ƙara da cewa "Don haka ku kwantar da hankalinku. Babu abinda zai faru sai alkhairi in Allah ya yarda. Ku tashi yanzu ku koma gidajenku, gobe idan Allah ya kaimu da safe kafin tafiya asibiti sai ku sake neman izinin mazajenku ku zo ku duba ta. Allah ya tashe mu lafiya." "Ameen Baffa" Haka suka fice daga gidan jiki a sanyaye bayan sunyi ma Innaye da Abokan zamanta sallama. A hanyar raka su zuwa ƙofar gida da Zulaikha za ta yi ne suka jaddada mata lallai komai dare idan ciwon Innaye ya tashi ta kira wayoyinsu ta sanar da su. Kamar yadda Innaye ta saba kwana cikin matsanancin zazzaɓi da kwankwatsar ƙashi ako wane dare, yau ma duk da bata sha magungunan dare ba haka ta kwana cikin azabar ciwo, kamar ma ya fi na kullum a ganin Zulaikha. Baffa da yake da turakarsa yana ta safa da marwa yana duba halin da take ciki, sauran abokan zamanta ma ba'a barsu a baya ba gurin zirga-zirga duba halin da take ciki. To abu ne da babu yadda suka iya sai abinda Allah yayi, addu'o'i suka yi mata sosai kafin suka koma ɗakunansu. Baffa da nauyinta yake a kanshi a ƙarshe dole ya bar turakarsa ya koma ɗakin Innaye, tsawon mintuna goma sha biyu ya ɗauka zaune kusa da ita yana tofe ta da duk addu'ar da tazo bakinshi, hankalinshi a tashe. Duk da faɗin Mal Bahaushe ciwo idan yaji dare ya fi tashi a iya tsawon rayuwar da yayi da Rahina bai taɓa ganin ta yi ciwo makamancin wannan ba. Irin yadda take jan numfarfashi a wahalce tana saukewa ga gurmususu da take yi kamar mai naƙuda shi ne abinda ke ƙara ɗaga mishi hankali. Ita kuwa Zulaikha tana rakuɓe a gefe tana ta hawaye kamar yadda ta saba, hannunta riƙe da jiƙaƙƙen tawul da take goga ma Innaye a jiki don rage mata zazzafan zafin zazzaɓin da yake jikinta. Daga bisani Baffa cikakken alwala ya ɗauro ya shimfiɗa dadduma a tsakar ɗakin ya fara jero nafilfili, yana nema mata sauƙi da rangwame gurin mahaliccin sammai da ƙassai. Kamar aikin asiri, sai gaf da asubah zazzaɓin ya sauka, nannauyan barci ya ɗauke ta kamar ko wane lokaci. Ko da Hafiz ya shiga cikin gidan duba jikinta bayan sun fito daga masallaci irin labarin da mahaifinshi ya bashi na tashin ciwon bai ji daɗinshi ba ko kaɗan. Ya zaci sauƙin da ya gani a yammacin jiya zai ɗore, kuma rashin shan maganin dare da bata yi ba ya ƙara saka shi sakankancewa yayi barci hankali kwance. Tunda ai an ce magungunan da take sha ke tayar da ciwon, tunda bata sha ba menene dalilin tashin ciwon a wannan dare? Haka yai ta sake-sake a zuciyarsa da tulin tambayoyin da ba shi da amsarsu. Ko bayan ficewar Baffa zuwa turakarshi don ya kimtsa zuwa asibitin shi ya kasa ficewa. A falon Innaye ya zauna ya zuba tagumi da hannu bibiyu, ƙwaƙwalwarsa a cunkushe. Ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi? A haka Yaya Balira tayi sallama a ƙofar ɗakin ta shiga ciki ta same shi zaune cikin damuwar da fuskarsa ta gaza ɓoyewa. Ƙirjinta ne ya buga daram! Da sauri ta saki jakar kayan da ke hannunta a ƙasa ta ƙarasa gurinshi hankalinta a tashe. "Hafizu me yake faruwa? Ina Innaye?" Bata jira ya amsa mata ba ta nufi cikin ɗakin da sauri, ganin Innaye tana barci ga Zulaikha zaune akan dadduma tana gyangyaɗi yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta zauna a hankali a gefen gadon tana ƙara kallon Innaye don tabbatar da barcin take yi ko? Bata daɗe da zuwa ba Aunty Rakiya da Aunty Ladidi suka isa gidan. Duk yadda suka so suyi sammakon tafiya asibiti bai yiwu ba saboda dole suka jira Innaye ta tashi barci don kanta, aka tarairayeta zuwa banɗaki aka yi mata wanka. Suka shiryata a nutse, tayi sallah a zaune, suka ba ta abin kari ta karya sama-sama kafin suka ɗauki hanyar tafiya zuwa asibiti. Ƴaƴan gaba ɗaya suka so tafiya asibiti, a dole suka haƙura saboda Baffa ya hana. Daga Aunty Balira sai Hafiz sai Baffa da Innaye da direban da ke tuƙa motar suka tafi asibiti. Kasancewar safiya ce babu go slow a hanya, kuma basu haɗu da sharrin ƙarfe irinna jiya ba. Nan da nan suka isa asibitin Barau Dikko cikin garin Kaduna. Da yake tafe suke da gogaggen ɗan boko Hafiz sai basu sha wata wahala ba, shi ya shige musu gaba gurin yin komai, layi na zuwa kansu aka shigar da file ɗin su suka samu ganawa da babban likitan da yake aiki a lokacin. Bayan taƙaitaccen binciken da likita yayi akan Innaye, da kuma yanayin galabaitaccen jikinta da ya gani, nan take ya rubuta za'a basu gado. Sannan ya rubuta takardan gwaje-gwaje kala-kala ya damƙa ma Hafiz. Ɗaki na musamman Hafiz ya buƙaci a kwantar dasu, kafin ya tafi ɓangaren biyan kuɗin da aka buƙata na gwaje-gwajen da za'a yi mata. Da yake ya saka ma ransa son sanin takamaimai abinda ke haddasa ma Innaye waɗannan cututtukan cikin daren shi yasa ko bayan gama ɗiban jininta don gwaji, aka ɗaura mata ƙarin ruwa bai bar asibitin ba sai da ya tsaya jiran fitowar sakamako. Wasu sakamakon sun fito a ranar, wasu kuma an tabbatar mishi sakamakonsu sai washe gari

Chapter 8 of 40