Share this page
za su fito, sannan wani gwajin sai washe gari da safe za'a yi mata. Nan take direba ya tuƙa su zuwa cikin gari bayan ya dubo hotel mai kyau da tsada a wayarsa suna isa ya kama musu ɗakuna, shi, mahaifinshi, direba. Kayayyakin da za su buƙata na kwana ɗaya zuwa biyu ya shiga babban shagon da ke jikin hotel ɗin ya siyo musu sannan ya koma ciki. Lafiyayyen abinci mai rai da lafiya yayi musu Oder suka ci sannan kowa a cikinsu yayi wanka ya canja kaya. Duk yadda yake jin gajiya a jikinshi bai zauna ba, ɗakin da Baffa yake ya shiga sai yaga har yayi barci. A hankali yaja mishi ƙofar ya nufi ɗakin da ya kama ma direbanshi. Ko da ya shiga sai ya tarar da shi ya gama cin abinci, yana kishingiɗe akan kujera yana sakacen haƙori. Ganinshi yasa direban miƙewa tsaye da sauri bayan ya amsa sallamarshi. "Oga barka da yamma. Allah ya ƙara arziki yaba tsohuwa lafiya. Za mu fita ne?" Ya ƙarasa da tambayar a ladabce. Ya sani idan za su sake kwana su yini suna yawo a mota da Mal Musa ko a fuska bazai taɓa nuna mishi ya gaji ba. Amma adalci shi ne ko da mutum yana maka hidimar da kake biyansa, yadda kake jin gajiya a jikinka shi ma yana ji, rai dangin goro ne. Haka kawai lokaci bayan lokaci yana da kyau ka dinga nuna ma hadiminka shi ma fa ɗan'adam ne mai ƴanci. Da wannan dalilin yasa shi sakin ɗan taƙaitaccen murmushi, ya ce "Ameen. A'a Mal Musa. Shigowa nayi kawai inyi maka ban gajiya. Fita zanyi yanzu amma ba tare da kai ba, Baffa yana ɗakinsa yana barci. Kai ma ya kamata ka huta, sai na dawo." Cikin fara'a yayi masa a dawo lafiya da addu'ar Allah ya tsare sannan ya miƙa mishi makullin mota. Ya karɓa ya fice daga ɗakin shi kuma ya cigaba da kishingiɗarsa, a zuciyarsa yake jinjina kirki da karamci irinna Ubangidansa. Ko da ya koma ɗakinsa, wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Aunty Balira ta faɗa mishi duk abubuwan da suke buƙata. Bai ɓata lokaci ba ya fice daga ɗakin, kasuwa ya shiga ya lodo musu siyayya a wadace. Har ma da abinda bata ce mishi suna buƙata ba aka loda mishi a bayan mota ya nufi asibiti. Da yake ɗakin da aka kwantar da su kwanciyar mutane biyu ne, shi yasa basu rasa inda za su zuba kayayyakin da ya siyo musu kamar bai san zafin kuɗi ba. "Allah yayi albarka Hafizu. In Allah ya yarda baza ka taɓe ba." Minti ɗaya biyu kalaman da ke fita daga bakin Aunty Balira kenan, fuskarta yalwace da farin cikin yadda bai taɓa nuna gajiya wajen ɗawainiya da su ko mahaifiyarsu. Da fara'a a fuskarsa a amsa addu'ar. Gefen ɗaya gadon da babu mara lafiya akai ya zauna, yana kallon Innaye wacce tunda aka ɗaura mata ƙarin ruwa da allurai da aka zuba a cikin ruwan barci take yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Bai daɗe sosai ba saboda magriba da ta kawo jiki yayi ma Aunty Balira sallama ya fice daga ɗakin. Yana hanya, kiran Bintu a karo na uku ya shigo mishi amma bai samu sararin ɗauka ba, sai da ya isa ɗakin da ya kama sannan ya bi bayan kiranta. Ringing ɗin farko ana biyu ta daga wayar ba tare da jan aji ba kamar yadda ta saba. "My dear..." Ta kira sunan da take yawan faɗa masa da wata irin raunanniyar murya. "Laifin me nayi?" Ta sake tambayarsa tub kafin ya amsa da muryar da ke bayyana matsananciyar damuwa. In ji Mal Bahaushe ya ce me kaza a aljihu ba ya jimirin as! A tsammaninta liƙin da ta fara yi ne ya ɓalle, shi yasa tun da ya tafi jiya da yau ko wayarta ba kasaifai yake ɗauka ba. Idan ta ci sa'a ya ɗauka kuma ko ya biyo bayan kiran da ta yi mishi kamar yanzu sam ba ya bata wani nutsuwarsa yadda ya kamata. Tsoron ko asirinta ne ya fara tonuwa har yake ƙullace da ita yasa kawai ta sakar mishi kuka a raunane, irin kukan nan mai bayyana tana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. "Kiyi haƙuri Sweetheart." Ya faɗa a tausashe. "Don Allah kiyi shiru, ki kwantar da hankalinki. Kin san kukanki na ɗaga min hankali." Ya faɗa cikin rarrashi da muryar da ke bayyana damuwa. A hankali ta fara ƙasa-ƙasa da kukan har tayi shiru gaba ɗaya, amma bata ce komai ba, sai sauke ajiyar take yi irinna kuka. "Kin san ko da kinyi min laifi zuciyata baza ta iya jimirin fita daga al'amarinki ba. Kiyi haƙuri, al'amarin ciwon Innaye ne yake ɗaga min hankali... Tun da muka iso jiya ba ni cikin nutsuwa ta. Jikinta har yanzu baiyi sauƙi ba..." "Subhanallahi. Allah sarki Innaye. Allah ya bata lafiya. Tana shan magungunanta kuma ana yi mata alluran safe da dare kuwa?" Ta tambaye shi daga can ɓangaren. Har ya buɗe baki zai faɗa mata gaskiyar abinda yake faruwa sai kuma ya tuna gargaɗin da mahaifinsa yayi masa. 'Hafizu, kar ka kuskura ka faɗa ma iyalinka an daina ba mahaifiyarka maganin da ta siya mata. Ba don komai ba kuwa sai don za ta ga kamar an raina ƙoƙarinta da kulawar da ta ba mahaifiyarka ne. Idan kunyi waya kar ka kuskura ka faɗa mata ma mun taho asibiti. Ina fatan ka fahimce ni?' Tunanin wannan maganar yasa shi amsa mata da cewa "Eh! Ana bata komai kamar yadda kika nuna min. Jikin ne dai har yanzu ba sauƙi sai na musulunci, ki taya ni addu'a..." "Ka kwantar da hankalinka My dear. Za ta samu sauƙi sosai in Allah ya yarda, don Allah ka kwantar min da hankalinka. Ya kake so inyi idan ciwo ya kama min kai?" Ta tambaye shi a shagwaɓe. Kafin ya amsa ta sake cewa "Ka dai san idan kana ciwo ni ce ke jigatuwa ko?" Ta sake tambayarsa. "To yanzu ba ni kaɗai zan jigata ba My Dear. Har da Babynka ɗan wata biyu da yake kwance a mahaifata. Ko za ka so ka zama silar da ɗan tayinka zai bi rariya tun kafin ya fito duniya yayi tozali da fuskar kyakkyawan mahaifinsa...?" "Mmmmme kike nufi Sweetheart?" Ya katse ta da tambayar muryarsa na rawa. "Ban... gane ba? Me kike nufi? Kina nufin ke Bintu kina ɗauke da ɗan tayin cikina a jikinki?" Ta daɗe da sani, shi ɗin mutum ne mai son yara sosai. Tun kafin suyi aure ya sha faɗa mata shi fa yana son yara da yawa, ko da suka yi aure duk sa'adda baƙonta na wata yazo sai ya ɗanyi ƙorafin har yanzu ƙwallonsa bai shiga raga ba? Ya kamata tayi wani abu a matsayinta na likita. Shi yasa a yau da ta samu tabbacin tana ɗauke da juna biyu sanadiyyar amai da tashin zuciyar da ta tashi da shi har ya kai ta ga yin gwaje-gwaje ta a ranta bai kamata ta ɓoye mishi wannan abin farin ciki da ya daɗe yana jira ba. "Eh My dear. Da gaske nake. Yanzu haka da nake zaune takardun gwaje-gwajen da suka tabbatar min ina ɗauke da ciki ne riƙe a hannuna. Ka ce Alhamdulillah..." "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi ala ni'imatihi tatimmussalihat!!!" Ya faɗa a jere muryarsa da karaɗin farin ciki tun kafin ta aje numfashin maganarta. "Na ji daɗin jin wannan kyakkyawar albishir ɗin Bintu. Lallai kin cancanci gwaggwaɓar tukwuici a hannuna. Ina ma ace yanzu haka ina tare da ke? Lallai da kin ga yadda ake nuna matsananciyar murna da tarairaya. Na gode, na gode. Allah yayi miki albarka. A yadda na tsara a ɗazu ko zan koma Abuja sai jibi, amma saboda wannan kyakkyawan albishir ɗin da kika yi min gobe da wuri ina nan tafe kin ji Sweetheart? Yanzu faɗa min, me kike yi?" Sai da tayi fari da idanunta kamar yana kallonta, sannan ta amsa a yangace "Ina zaune ne a tsakiyar gadonka. Zuciyata cike da kewarka Mijina uban ƴaƴana." "Ni ma ina kewarki Matata. Yanzu me kike jin ci?" Ya sake tambayarta a ɗokance. "Babu komai My dear. Tun ɗazu zuciyata tashi take yi, ba na jin cin komai." Ta amsa tana murmushi. Da tarairaya da kulawa haɗe da matsananciyar ƙauna a muryarsa ya fara faɗa mata tausasan kalamai. "Ayya... Yi haƙuri Sweetheart. Sanadin Babyna kike jin haka ko? With time komai zai wuce kin ji? Yanzu dai faɗa min, cikin ya fara motsi ne?" A yanzu kam ta kasa hana kanta dariya, dole ta sake shi amma a sanyaye, da salon jan hankalin wanda aka yi dariyar dominsa. "Dariya na baki?" Ya tambaye ta shi ma yana dariya. "Kar ki ga laifina fa, kin san abinki da sabon shiga..." "Ban ga laifinka ba My dear. Kawai dai tambayar ce ta saka ni dariya. Ciki ba ya fara sai ya kai wata huɗu, ka ga ni yanzu ne nake cikin wata biyu. Amma kamar gobe ne za ka ji ya fara motsi, har ma ka taɓa da hannayenka ka dinga jin babyn yana motsawa." Daga irin yadda take mishi ƙarin bayani, za'a gane cike take da farin ciki. Shi ma da yake saurarenta da farin ciki sosai a fuskarsa ya bata dukkan hankalinsa. Hirar sabon cikin da take ɗauke da shi, shi ya taka muhimmiyar rawa gurin rage mishi ƙarfin damuwar da zuciyarsa take ciki dangane da ciwon Innaye. Sun daɗe suna hira cikin farin ciki da annashuwa, kafin suka yi sallama daƙyar bayan ya ga kiran mahaifinsa na shigo masa. Bayan gama waya da Baffa sallah kawai yayi ya sake ficewa daga ɗakin zuwa na Baffa. Daga can ɗaukarsa yayi kai tsaye suka koma asibiti. Ko da suka shiga ɗakin, barci suka tarar da ita tana yi. Aunty Balira kuma tana zaune akan dadduma tana lazumi, da alamun sallah ta idar. "Ya jikin nata? Barcin take yi har yanzu? Ta farka kuwa?" Baffa ya tambayi Aunty Balira fuskarsa da damuwa bayan sun zauna a gefen gadon da babu kowa akai. "Jiki da sauƙi Baffa. Eh ta farka, har ma ta rama sallolin da suke kanta. Kuma Alhamdulillahi babu galabaitannan kamar da safe, da alamun sauƙi in Allah ya yarda." "Ma sha Allah! Allah yasa sauƙi ya ɗore. Ni gobe da safe zanyi sammakon komawa gida, sai zuwa jibi kuma. Allah yasa dai yau kar ta sake kwana da wannan zazzafan zazzaɓin irin na jiya, domin da alamun kwana da zazzaɓin shi ke sa ta yini a galabaice." "In sha Allah baza ta kwana da shi ba. Domin wani likita ya sake shigowa ya duba ta ɗazu, a lokacin idanunta biyu. Ya tambayeta yadda take ji tayi mishi ƙarin bayani. Ban dai san me ya ce ba don naga yayi ma ma'aikatan jinyan da suke biye dashi bayani da turanci, kuma yayi rubutu a jikin babban katin Innaye da yake riƙe a hannunsu." Tana aje numfashin maganarta Hafiz ya karɓe da cewa "Ba matsala. Yanzu kafin in tafi zan je in samu likitan in ji halin da ake ciki. Ni ma gobe da safe zan koma Abuja, ana nema na a gurin aiki. Duk yadda ake ciki zan karɓi lambar likitan mu dinga magana da shi. Jibi zan biyo jirgi in sake duba jikin nata." "Ai ka ma yi zamanka gurin aiki kar ka samu matsala Hafizu. Tunda ga waya ai Allah ya sauƙaƙa al'amarin, duk yadda ake ciki ita Balira sai ta kira da dinga sanar da kai. Allah yayi albarka ya ba Rahina lafiya." "Ameen Baffa." Suka amsa gaba ɗaya. Kamar yadda ya ce, kafin su bar asibitin sai da yaje gurin Likitan da ke kan aiki a daren ya binciki halin da ake ciki. Babu wata matsala mai girma, sai wasu ƙarin allurai da zai siya saboda gwajen-gwajen da suka fita a ranar. Ƙarfe goma na dare suka bar asibiti zuwa hotel ɗin da suka yi masauki. ***** ***** Yayi mamaki sosai lokacin da Likita ya tabbatar mishi Innaye tana ɗauke da ciwon Suger a jikinta. Jininta kuma ya hau sosai fiye da yadda ake tsammani. Typhoid da Maleria da Bintu ta ce shi ke damun Innaye shi ma akwai, amma kaɗan, basu yi ƙarfin da za'a haɗa ta da manyan magungunan da za su dinga wujijjiga jininta ba. Amma kasancewar shi mutum ne ba mai zurfafa damuwa ko bincike akan al'amura ba sai ya bar komai akan akasin na'urar gwaji aka samu a asibitin da Bintu take aiki. Ko a fuska bai canja mata ba, kuma har lokacin bai sanar da ita an kwantar da Innaye a asibiti ba. Tarairayarta yake yi sosai suna rainon cikin jikinta cikin nutsuwa da soyayya. Duk da ya kwana uku rabonshi da asibitin, amma ya saki kuɗi sosai ana yi ma Innaye duk abinda ya dace. Kuma cikin hukuncin Allah kwalliya tana biyan kuɗin sabulu, sosai Innaye ke samun sauƙi, zazzaɓi kuwa tunda suka je asibitin bata ƙara kwana da shi ba. Jikin Innaye yayi kyau sosai fiye da yadda ake zato. Ƴaƴanta da ƴan'uwa makusanta da suka je asibitin duba ta kowa da kyakkyawan labarin sauƙin da take samu yake komawa gida. Ko da ta kwana huɗu Baffa ya koma duba ta bakinsa kasa rufuwa yayi don murna. Minti ɗaya biyu sai ya kalle ta da fara'a ya ce "Alhamdulillah! Rahina sauƙi ya samu, Allah ya ƙara lafiya." Tun tana amsa mishi har ya koma ba ta kunya a gaban ɗiyarsu ta fari Balira. Ita kuwa sai dariya take ma iyayen nata, daga ƙarshe ma ficewa tayi daga ɗakin ta basu guri domin su zanta a tsakaninsu. Kwanan Innaye bakwai a asibiti aka rubuta musu sallama. Kuma a wannan ranar ne Hafiz ya bi jirgin ƙarfe takwas na safe zuwa Kaduna, ƙarfe sha ɗaya da rabi a asibitin tayi mishi. Ba ƙaramin murna da farin ciki yayi ba da ganin yadda Innaye ta warke garas! Kamar ba ita ce mare lafiya ba, har wani kumari tayi na musamman saboda kyakkyawan kulawan da take samu a asibitin. Domin a yanzu duk wata harka kuɗi ke magana, yana daga can Abuja yasa aka bincika mishi gidan abinci na musamman a Kaduna safe, rana, yamma suke kai ma Innaye lafiyayyen abinci da ya kamata masu ciwon suger su dinga ci. Ba Innaye da take mare lafiya ba, hatta Balira me zaman jinya ta yi kyau sosai, jikinta ya nuna hutu da cin abinci mai daɗi da lafiya. Bayan murnar ganin Innaye ficewa yayi zuwa Ofishin likita shi da Aunty Balira aka ƙara musu cikakken bayani na irin abincin da za ta kiyaye ci a matsayinta na mai ciwon suger da hawan jini. Da kalolin abincin da jikinta ya fi buƙata a yanzu. Sannan ya karɓi tulin magungunan da likita ya rubuta mata, saboda yadda ya saki kuɗi shi ne ya biyo su canji ma. Amma saboda sanin ya kamata sai bai karɓi ko sisi ba, ya ce ya bar ma marasa lafiyan da ba su da ƙarfi. Aunty Balira tana harhaɗa kayayyakinsu ya fice zuwa kasuwa. Kayayyakin abincin da likita ya lissafa musu na masu ciwon suger ya siya da yawa, sannan ya samu shatar lafiyayyar mota ya biya direba, suka ƙarasa asibiti aka ɗauki Aunty Balira da Innaye suka kama hanya sai Ƙauyen Faƙo. Ƙarfe uku dai-dai suka isa, basu daɗe ba suka juyo saboda a ranar yake son komawa Abuja. Albarka kam Hafiz ya sha ta daga bakin Iyaye, ƴan'uwa, da jama'ar gari. Waɗanda a baya suka dinga hum-hum-hum da zancen yadda ya dawo da Innaye cikin matsanancin ciwo daga gidanshi sai ga shi su ne kan gaba wajen saka mishi albarka. Sun bar ƙauyen bakinshi har kunne. Nutsuwa ta musamman yake ji a sassan jikinsa saboda yadda ya zama sanadiyyar faranta ma Iyaye da ƴan'uwanshi rai, daman kullum abinda yake buri kenan. ***** ****** ***** "Wai me kike nufi Zulai?" Ya tambayeta ransa a ɓace. Ƙara ɗaure fuska tayi tamau ta juyar da kanta can gefe guda. Uffan bata ce ba balle ma yasa ran za ta tanka mishi. Ƙwafa yayi mai ƙarfi. Ya sake jan tsaki a karo na barkatai. Cikin matsanancin fushi da fusata ya ce "Kin san Allah? A wannan karon za mu samu gagarumin matsala da ke. Wata uku kenan ina bin ki kina ja na a ƙasa, a yanzu da bikinmu yazo gaf idan kin isa ki cigaba da wulaƙantani Allah ya tsinen. Zan nuna miki gaba nake da ke ta ko wane ɓangare. In banda iskanci da rainin ajawali irin naki ke har kin isa..." "Wai don Allah Mudan ya kake so inyi ne?" Ta katse shi ita ma ranta a ɓace. "Auwoo!" Ya faɗa baki buɗe yana kallonta da mamaki. "Tambayata ma kike ya nake so kiyi? To bari in sake maimaita miki. Umarni nake baki a matsayina na wanda za ki aura nan da sati uku. Ki shirya gobe da yamma ki je ma Yahanasu matata barkar haihuwar da tayi..." "Uhmmm! Mudan kenan." Ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa. "Ka yi ka gama. Saboda Allah in banda ƙi faɗi irin naka ta ina aka taɓa haka? Don kawai za ka aure ni haifata kayi? Ko kuwa don za ka zama mijina sai aka ce dole idan matarka ta haihu sai na je mata barka? Bayan haka ma duk ƙauyen nan waye bai san irin mahaukacin kishin da Yaha take yi da ni ba?" "Yaha kai tsaye?" Ya faɗa a mamakance. Kafin ta amsa ya cigaba da cewa "Matar tawa ce kuma Uwargidanki kike kiran sunanta kai tsaye kamar wata sa'arki?" Sai da ta murguɗa baki dama da hauni sannan ta amsa da "To ita Yahan uwata ce da bazan kira sunanta kai tsaye ba? Matar da tun kafin in shiga gidanta matsayin kishiya take aiko min da manya-manyan zagi da Alkaba'iran da ta tanadar min iri-iri idan na kuskura na aure ka shi ne don ta haihu kawai ni daɗi miji zan je mata barka? Na rantse da Allah babu inda zan je. Sai dai duk abinda zai faru ya faru." "Au! Haka kika ce?" "Ƙwarai kuwa!" Ta amsa kai tsaye ba tare da wani shakka ko tsoro ba. "To shi kenan! Yayi kyau Zulai. Zaɓi yanzu ya rage gare ki, ko dai ki shirya tsakanin yau, gobe, jibi ki je ma Yahanasu barka ko kuma in fasa aurenki. Zan aiko ƴan'uwana sati na sama su karɓi duk kayan auren da na aika da shi gidanku. In banda ƙaddara ma da ƙuruciyana ke har kin isa in ce zan aure ki tsofai-tsofai da ke? Shekarunki sha takwas fa... Ki faɗa min duk ƙauyen nan wace ganɗaɗemiyar budurwa ce mai shekarunki zaune a gida bata yi aure ko kuma ta taɓa aure ba? Kawai don kin samu za a rufa miki asiri sai ki dinga tsammani tsoronki ake ji? Daman tun kafin in sako kai a neman aurenki mutane da yawa sun faɗa min baza kiyi min biyayya ba, saboda kin gama tsofewa a gida kina goga kafaɗa da gyatumarki gani kike dai dai kike da kowa... To ni ba tsoronki nake yi ba. Kuma ina sake tabbatar miki in banda wasu dalilai babu abinda zai kawo ni neman auren tsohuwar budurwa kamar ki..." Zafafan maganganun da ya saki baki yana yaɓa mata masu kama da saukar ruwan dalma a kunnuwanta yasa bata san sa'adda tasa hannu biyu ta toshe kunne sannan ta ƙwalla wani mahaukacin ihu hankalinta a tashe. Hakan bai ishe ta ba, sai da ta ƙara da duƙewa a ƙasa ta rushe da ƙaƙƙarfan kuka kamar wacce aka zo wa da albishir ɗin mutuwar iyayenta. "Au! Sharri za kiyi min daga faɗan gaskiya?" Ya tambayeta hankalinsa a tashe da irin kukan da take ruwasa kamar ƙaramar yarinya. "To ni kin ga tafiyata. Ina zaune lafiya baza ki ƙulla min jakar tsaba ba in tafi kaji su tsattsaga." Kamar walƙiya, ɓat ya fice daga cikin zauren a gaggauce. Baiyi second biyar da ficewa ba Innaye da abokiyar zamanta Mama Laminde da ƙananun matasan gidan Isiyaku da Labaran suka sawo kai a guje cikin zauren. A hannayen matasan, manyan sanduna ne suka riƙo suna ta zare idanu kamar za su ci babu, domin duk a tsammaninsu wani mugun abun Mudan yake ƙoƙarin aikatawa ga Zulaikha ita kuma ta ƙwala wannan ihun. Ganinta ita kaɗai duƙe a ƙasa tana rusa kuka sannan babu alamar wani mummunan abu ya faru da ita yasa suka yi turus! A tsaye guri ɗaya. "Ina yake?" Matasan suka haɗa baki gurin tambayarta. Ita kuwa Innaye cewa tayi "Me ya faru Auta?" Ta tambayeta hankalinta a tashe. "Ina Mudan ɗin?" Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faɗuwar gaba da bata san dalili ba. Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faɗuwar gaba da bata san dalili ba. Idanu kaca-kaca da hawaye ta ɗago kanta daƙyar tana kallon Innaye ta ce cikin kuka da ɓare-ɓaren baki. "Wai... wai... wai... cewa yayi bazai auri tsohuwar budurwa kamata ba..." "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!" Mama Laminde, Isiya, da Labaran suka haɗa baki gurin jan salatin hankulansu a tashe. Ita kuwa Innaye, Daɓas! ta nemi guri ta zauna a cikin zauren tana jin wani jiri-jiri na neman kayar da ita daga zaunen da take. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai daga cikin gidan Umma Laraba ce ta sake fitowa bayan ta idar da sallar isha'i da take yi a gaggauce. Ko kafin ta bud'e baki ta tambayi abinda ke faruwa ta gansu haka sunyi jugum-jugum ga Zulai tana tsugune a k'asa tana rusa kuka sai ga Baffa ya sawo kai cikin zauren. "Lafiya? Me yake faruwa anan? Waye ya mutu?" Ya jera musu tambayoyin da saurin lokaci ɗaya fuskarsa na rikiɗewa zuwa yanayin tashin hankali. "Baffa. Wai Mudan ne ya ce ma Zulai bazai auri tsohuwar budurwa kamarta ba." Isiya yayi ƙarfin halin faɗa ma Baffa yana sharce gumin da ya lulluɓe goshinsa. "Zancen banza kenan. Don wannan ƴar maganar shi ne kuka tsaya anan kamar anyi mutuwa? Ke kuma Rahina da girmanki maimakon kiyi ƙoƙarin kwantar da lamarin sai ki ɓuge da zama a ƙasa kamar wata ƙaramar yarinya? Ku tashi da Allah mu shiga cikin gida. Ai zancen aure ya wuce lokaci ɗaya ace an fasa kamar wani wasan yara. Kun binciki gaskiyar me ya faru ne? Duk ku kwantar da hankalinku. Babu abinda zai faru sai alheri in Allah ya yarda. Ku wuce mu shiga ciki na ce." Ya ƙarasa maganar da faɗa-faɗa. Da sauri Zulaikha ta miƙe ta shige ciki da gudu tana cigaba da rusa kuka, domin har lokacin zafin maganganun da Mudan ya yayyaɓa mata bai fara sassautuwa ba a zuciyarta. Innaye kuwa saboda yadda maganar fashin auren ya buge ta baga-tatan sai da abokan zamanta suka kamata sannan ta iya miƙewa tsaye, suka rankaya gaba ɗaya zuwa cikin gidan Baffah na biye da su a baya. Kowa a cikinsu da tunani mabanbanta a zuciyarsa. Tun watannin baya da suka shuɗe bayan gama jinyar da Innaye ta sha daƙyar, kamar baza ta kai labari ba. Tana gama warkewa ta ba Baffa labarin duk yadda sukai da Zulaikha a gidan Hafizu, dangane da maganar samarin da suke son ta tana dakatar da su tun ma kafin zancen ya kawo kunnuwansu. "Ikon Allah" Ya faɗa da mamaki a fuskarsa. "To ko menene dalilinta na taka musu birki?" Ya sake tambayar Innaye. "Ai ba ta da wani dalili Baffansu. Akwai wani dalili ne da ya wuce wauta irin nata?" Innaye ta amsa a tausashe. Da ɓacin rai a fuskarsa ya cigaba da magana bayan ta kai aya a maganganunta. "Amma Zulai an yi shashashar yarinya. Yanzu ita daman ta san tana da samarin amma shi ne ko da wasa bata taɓa turo ko mutum ɗaya guri na ba? Tana ganin yadda kullum hankalinmu da na jama'ar gari yake kanta saboda daɗewar da tayi bata yi aure ba? In banda

Chapter 9 of 40