damar hakan. Shi kuwa bai takura ta ba, ko a hakan ma ya gode, kuma kan tafe kan isa watarana jariri ango ne.
******
Duk yadda ya so ya yakice tunaninta a zuciyarsa ya kasa. Ga wani matsanancin ciwon kai da yake ta addabarsa tun da asubah. Har ya ɗauki jakarsa ta zuwa wurin aiki ya ajiye, ko takalmin ƙafarsa bai samu sararin cirewa ba ya faɗa rub da ciki a kan gado, ƙafafuwansa na lilo a ƙasa.
Hannunsa ya laluba ya janyo filo guda ɗaya ya ɗora kansa, sannan ya sake ɗauko wani filon ya kifa a kansa. Lumshe idanu yayi, a zuciyarsa yake ta addu'ar Allah ya kawo barci ya ɗauke shi ko na awa ɗaya ne.
Cikin hukuncin Allah kuma sai addu'arsa ta karɓu. Barcin ya ɗauke shi, amma irin rikitaccen barcinnan mai tafe da wasu irin birkitattun mafarkai. Kamar dai yadda ya faru da shi cikin dare, wani al'amari da tun bayan rasuwar marigayiya da ya tattara batun aure ya ajiye gefe ɗaya bai sake faruwa da shi ba sai yanzu.
Yanzu ɗin ma kuma akan Zulaikha, Aunty Zulan da duka-duka tsawon lokacin da ya san da wanzuwarta a duniya basu taka kara sun karya ba. Haka ya farka a firgice, ko da ya fahimci abinda ya sake faruwa a karo na biyu tsakanin daren jiya zuwa yanzu wani matsanancin kunya ne ya lulluɓe shi.
Filon da ya ɗora a kanshi ya janye ya rungume tsam-tsam a ƙirjinsa, ya janyo lallausan bargon da ke ajiye a gefen gadon ya lulluɓa har kansa. Ƙara matse filon yayi, zuciya da gangar jikinsa cike da wani irin matsanancin shauƙi da son aure ƙarara.
Shi kaɗai, ya kwaɓe fuska kamar zai saka kuka. A hankali ya ce
"Na shiga uku, Allah na tuba ka yafe ni. Wannan yarinyar za ta lalata ma Mummy ɗa."
Shi kaɗai, yayi ta juyi akan gadon yana ƙara jin yadda sabon al'amarin ke ƙara amsuwa a dukka sassan jikinsa. Ga kansa da yake matsanancin ciwo har lokacin bai sassauta masa ba. A jejjere yake ta sauke ajiyar zuciya. Daƙyar ya yunƙura ya miƙe ya nufi banɗaki, ko da ya tsaya a gaban madubi, sai yaga idanunsa sun yi ja sosai.
Kaɗa kai kawai yayi hannunsa ɗaya dafe da mararsa yana tafe a hankali har ya shige banɗaki. Ruwan sanyi ya sakar ma kansa da tsammanin zai samu sassauci a yanayin da yake ciki, ashe bayan tiya akwai wata cacar, yana gama yin wankan kuma ya fara rawar ɗari. Alamun zazzaɓi na shirin kawo masa farmaki.
Daƙyar, ya iya janyo ɗaya daga cikin rigunan wanka masu kauri da suke ajiye a banɗakin ya saka a jikinsa, ya lallaɓa a hankali ya fice daga bayin. Kan gadon ya sake komawa ya ƙudundune jikinsa gaba ɗaya da bargo, haƙoransa sai haɗuwa suke gaf-gaf.
Ya ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali yana ta jan duk addu'o'in da suka zo zuciyarsa. Hankalinsa a tashe, ga shi ya kasa miƙewa tsaye balle ko waya ce ya ɗauka ya kira cikin gida a kawo mishi ɗauki.
Sannu a hankali kuma sai barci ya fara fisgarsa, haka yayi barcin a jigace, da yake akwai bashin barci a idanunsa fiye da awa ɗaya yana barci sannan ya farka. A lokacin kuma zazzaɓin ya sauka, zufa ya lulluɓe gaba ɗaya jikinsa.
Hamdala yayi sannan ya janye bargon daga jikinsa ya miƙe tsaye, gurin kayansa ya nufa ya ɗauki wasu kayan marasa nauyi ya canja. Ko da ya kalli agogo, ƙarfe goma sha ɗaya da kwata ne na safe.
Mai ya shafa sama-sama ya fesa turare. Ya yaye zanin gadon da ke shimfiɗe akan gadonsa ya canja wani, sannan ya sake hayewa kan gadon ya kwanta bayan ya ɗauki wayarsa.
Har ya lalubo lambarta zai kira sai kuma ya yanke shawarar bari ya fara dubawa ko tana Online. Ƙwaƙƙwarar magana yake so suyi guda ɗaya, tsakanin jiya zuwa yau irin abubuwan da suka faru da shi sun bashi tsoro, bai san idan ya cigaba da jan lokaci yana lallaɓata me zai iya faruwa a gaba ba.
Gara kawai ya fito fili ya faɗa mata halin da zuciyarsa take ciki game da ita. Yana da kyakkyawar yaƙinin in sha Allahu za ta fahimce shi, za kuma ta bashi damar da yake buƙata, ayi komai a gaggauce a wuce gurin kafin shaiɗan ya jefa shi a halaka.
"Hi Beb!"
Ya fara tura mata, zuciyarsa cike da fatan tana kusa da wayar, ya sani in dai taga saƙonsa za ta amsa mishi a gaggauce.
Minti biyu tsakani ya tsura ma suna da lambarta idanu kafin yaga ta buɗe saƙon, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga alamun tana typing daga can ɓangaren.
"Abban Imam! Ya aiki? Fatan ka isa Ofis lafiya?"
"Ban fita ba fa, ba ni da lafiya Wallahi. Har na ɗauki jaka kawai na ajiye na koma na kwanta."
A ƙarshen saƙon, ya ƙara da hoton kan gwaigwai (Emoji) mai nuna alamar shagwaɓa, da mai nuna zama abin tausayi, da mai kuka ya tura mata.
Mamaki ne ya ɗan kamata, domin tun sassafe suka yi waya, bayan gaisuwa da tambayar yadda ta wayi gari ya tabbatar mata a ranar bazai karya a gida ba. Zaiyi sammakon tafiya Ofis ne, akwai wasu muhimman ayyuka da bai ƙarasa jiya ba, yau zai ƙarasa ya tura su Lagos.
Da damuwa a fuskarta kamar yana gabanta ta ce
"Subhanallahi! Me yake damunka Abban Imam?"
"Ke ce!"
Ya amsa mata kai tsaye, ba tare da wata kwana-kwana ko ɓoye-ɓoye ba.
Da mamaki sosai ta tura mishi da kan gwaigwai na zare idanu. Sannan ta ƙara da rubuta mishi
"Ni kuma?"
"Eh"
Ya sake amsawa, sannan ya tura mata da alamar zuciya mai motsi.
"Allah sarki ni... Me nayi kuma?"
Ta aika mishi da tambayar. Acan ɓangarenta, sake gyara kwanciya tayi akan katifar Hajja tana ƙara riƙe wayar ƙam-ƙam a hannunta. Ta rasa dalilin da yasa duk cikin mutanen da take mu'amala da su lamarin Abban Imam na musamman ne a zuciyarta.
Ko a waya idan suna magana, ko kuma idan suna chatting, irin yadda yake riritata, yana nuna mata ita ɗin ta musamman ce. Yana mata raki da shagwaɓa-shagwaɓa kamar wani Imam, ita kaɗai ta san irin yanayin da take ji a jikinta. Bakinta bazai taɓa iya fasalta irin yadda take ji ba, shi yasa ako wane lokaci cikin jin kunyarsa take. In dai ba akwai su Mummy a gurin ba gaskiya ba ta jin kunya zai barta ta iya sakewa da shi suyi magana ko da na minti biyar ne kacal.
Amma a waya, ko kuma ta kafar sadarwa, tunda ba ganin idanun juna suke yi ba shi yasa har take iya sakewa da shi suyi hira haka.
[2/6, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: "Kin hana ni nutsuwa Beb! Kin hana zuciyata samun nutsuwa tun sa'adda na fara yin tozali da kyakkyawar fuskarki. A yanzu kuma ɗan barcin da nake samun yi raba da rabi ma kina neman hana ni. Don Allah ki barni in huta mana Beb."
Ɓurum! Doguwar saƙonsa ya faɗo cikin wayarta. Jikinta na ɗan rawa ta buɗe, domin ko da ta ji shi shiru, kusan mintuna biyar bai ba ta amsa ba. Tayi tunanin ko ya sauka ne.
A yanzu da saƙonsa ya shigo da sauri ta buɗe don jin laifin me tayi masa? Ko da ta gama karanta dogon saƙon, jikinta ne gaba ɗaya ya ɗauka ɗummm! Sannu a hankali ta ɗora lumshe idanunta.
Sai a yanzu ta ƙara zurfafa tunaninta akan irin yanayin da take ji akan Abban Imamu. Duk da a iya tsawon rayuwarta bata taɓa faɗawa cikin kogin son wani mahaluki a faɗin duniya ba. A yanzu kam ko rantsuwa tayi babu kaffara wannan yanayin da take ji a jiki da zuciyarta ba komai bane face alamomin So.
"So dai?"
Tayi ma kanta tambayar a fili tana mamaki.
"So kuma? Wa ake so ko kuma wa yake so?"
Hajja da fitowarta kenan daga banɗaki zancen da Zulaikha tayi ya dira a kunnenta tsulum ta saka bakinta.
"Hajja ba fa magana nayi ba... zancen zuci ne kawai ya fito fili. Wani labari nake karantawa a facebook ya ɗauki hankalina."
Ta amsa ma Hajja da sauri tana ƙoƙarin buɗe wayarta da taji ƙarar saƙo ya sake shigowa.
"Beb! Baki ce komai ba... Ki agaza ma Ɗan Mummy kar kiyi kisan kai... Da gaske nake yi fa..."
Saƙon da Abban Imam ya ƙara turo mata.
Lura da tayi shauƙin da take ji na Soyayyar Abban Imamu zai iya saka ta yanka ihu a ɗakin Hajja, sawunta a likkafa ta sauka akan gadon.
"Hajja ina zuwa, ki gama shiryawan zan dawo yanzu in lallaɓe miki kan."
Ta fice da sauri tun kafin Hajja ta amsa.
Sai da ta shige ɗakinta, ta mayar da ƙofar ta rufe, ta jingina da jikin ƙofar sannan ta iya ba shi amsa
"To ni me zan ce? Ni dai babu ruwana... Kar ma ka bari wani ya ji wannan wasar da kake min."
"Wallahi, Summa tallahi ina son ki Zulaikha."
Ya tura mata da sauri saƙonta na isa gare shi.
"Da gaske nake yi, ina bala'in son ki."
Ya sake tura mata.
"Don Allah, don girman Allah kar ki ce min bakya so na."
A karo na uku ya sake tura mata.
"Na sani akwai tazarar shekaru masu ɗan yawa a tsakaninmu, amma na miki alƙawarin zan so ki, in riritaki, in shagwaɓa ki, in ji da ke, har ma fiye da saurayin da kike tunanin aura."
Saƙon shi ya sake sauka a karo na huɗu.
"Ki taimakeni Beby ki so ni, ko da rabin son da nake miki ne. Ke ni ko bakya jin so na a yanzu, ki bani dama don girman Allah in koya miki so na. In Allah ya yarda baza kiyi da na sani ba."
Tsananin yadda maganganunsa suka kassara mata sassan jiki, yasa bata san sa'adda ta zame zuwa ƙasa ba. Saboda jin ƙafafunta tayi kamar an zare mata duk wasu ƙasusuwa da suke cikinsu. Ta karanta saƙon, ta ƙara maimaitawa, a karo na uku ta sake bitar manya-manyan maganganunshi. Da ta rasa abinda za tayi, kawai sai ta fashe da kuka.
Da saurin gaske ta kashe wayar a daidai lokacin da kiranshi ya fara shigo mata. Daƙyar, da jan mazaunai, da muskutawa, da rarrafe, taja jiki zuwa gefen gadonta. Da tayi iya ƙoƙarinta ta kasa miƙewa ta hau kan gadon kawai sai tayi kwanciyarta a gurin, har lokacin hawayen idanunta basu daina tsere kamar an buɗe famfo ba.
******
Mamaki mai girma ne ya bayyana a fuskarsa lokacin da yaga kiranta na shigowa cikin wayarsa. Abu ne da bai taɓa faruwa ba tun da ya ɗauko ta daga Faƙo zuwa Abuja. A yau da ya faru kuwa kun ga dole yayi mamaki.
Da fari, ya tsammaci kiran daga Aunty Balira ne kamar yadda ya ga sunan, Sai da ya lura babu New a ƙarshen sunan Aunty Baliran, sannan ya gane tsohon layinta ne da ta bar ma Zulai. Kenan a yanzu, Zulai ke kiransa.
Ɓici-ɓici yayi da fuska saboda tsananin takaicin kiran da tayi masa, kamar tana gabansa, a fusace ya ce
"Ko uwar me take nema da take kira na ina tsaka da aiki oho!!"
Ya faɗa a fili. Kiran na gaf da tsinkewa ya ɗaga wayar, ya kara a kunnensa, har lokacin fuskarsa a ɗaure tamau babu walwala ya ce.
"Menene kike kira na a irin wannan lokacin da kika san ina tare da iyalin..."
"Madallah Yaya mai iyali. Kana tare da iyali ko bakwa tare ba abinda na kira in ji ba kenan."
Ta katse shi da shaƙaƙƙiyar muryar da ke bayyana alamu biyu, ko dai tana fama da matsanancin mura, ko kuma ta yi kuka sosai don tana cikin matsanancin damuwa.
Kafin ya sake kwaɓo mata wata baƙar maganar don ba abinda ta kira shi taji kenan ba tayi saurin sake cewa
"Daman tambayarka zanyi, gobe asabar za ka je Faƙo ne...?"
"Bazan je ba. Ko zan je ma ba abinda ya dame ki bane."
Ya katse ta a fusace.
"To ni kam zan tafi gobe in sha Allah. Zanyi sammakon zuwa pack in hau motar haya. A gobe, babu abinda zai hana ni zuwa ga Innaye da Baffa sai dai wani ikon Allah. Daman na zaci za ka tafi ne, in shirya ka biyo ka ɗauke ni mu tafi tare don cigaba da rufuwar asirinka. Amma tunda baza ka je ba ni kam zan tafi..."
"Zzzzzaaaa ki tafi Faƙo kike cewa? Da izinin wa za ki tafi?"
Ya tambayeta bakinsa na rawa, da wani irin bayyanannen tashin hankali a muryarsa duk da yana ƙoƙarin ɓoyewa.
Izuwa lokacin, acan ɓangarenta ranta ya fara ɓaci. Amma tana ta ƙoƙarin dannewa don ba ta so su raba hali kamar yadda suka saba, duk da haka, bata san sa'adda taja mishi wani dogon tsaki ba kafin ta ce a fusace
"Har wani izinin waye zan nema don zan je ganin iyayena? Look Yaya Hafiz, kana iya fitowa gobe ƙarfe bakwai da rabi na safe ka ɗaukeni mu tafi Faƙo a mutunce, kana kuma iya shantakewa kayi zamanka ni kuma in tafi a motar haya. Sai dai kyakkyawan albishir a gare ka shi ne duk abinda ya biyo baya kar kayi kuka da kowa face kanka da son zuciyarka..."
"Zulai??? Umarni kike ba ni?"
Ya jefa mata tambayar a tsawace.
"Ba umarni nake baka ba Hafiz."
Ta kira sunanshi gatsatsau abinda bata taɓa yi ba.
"Ina faɗa maka abinda zai faru ne tabbas! Ko da son zuciyarka, ko babu son zuciyarka. Domin kai baka isa kasa ko ka hana ni yin abinda zuciyata ke so ba."
Ƙit! Ta katse wayar ta barshi sake da baki, ƙirjinsa na wani irin bugawa sauri-sauri saboda tsananin kaɗuwa da firgita da irin kalaman da ke fita a bakin Zulai.
Kamar ba ita ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Me yake shirin faruwa ne?
****** ******
Neman aurensa da Aisha mahaifiyar Imam, nema ne da iyaye suka fara nuna sha'awar ƙulluwar dangantakar. Kafin daga bisani da zancen ya isa kunnuwansu suka riƙa da hannu bibiyu, kasancewar duk su biyun masu biyayya ne da bin umarnin iyaye.
Don haka a wancan lokacin bazai ce ya ɗanɗani zaƙi da guban da ke cikin soyayya ba, duk da dai jagoran aurensa da Aisha babu ƙiyayya ko kaɗan, zallar ƙauna ce da biyayya suka haɗu wajen samar da sassanyar soyayya da shaƙuwa mai tsayawa a zuciya.
Amma a yau, da ya gama fallasawa Zulaikha sirrin zuciyarsa ta bar shi a maƙale, ba tare da ta amsa mishi da eh ko a'a ba duk da yana matuƙar tsoro da fargabar jin kalmar a'a daga bakinta. Ya daɗe bai shiga cikin mummunar yanayi na gagarumin tashin hankali da fargaba irin wannan ba.
Ko da ya kira wayar Zulaikha ya ji kiran ya shiga, daga bisani kuma aka katse sannan aka kashe wayar gaba ɗaya. Wani wawan bugawa ƙirjinsa yayi, lokaci ɗaya kuma kamar aikin asiri zazzaɓin jikinsa ya dawo ɗanye jagab.
Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga shi akan gado yana rawar ɗari. Wani abin dariya da tausayi shi ne, duk da wannan hali da yake ciki ba kansa yake tunani ba, tunaninsa wane irin hali Zulaikha take ciki a wannan lokacin? Me yake damunta? Me yasa ta kashe mishi waya? Har ya ɗaga waya zai kira Mummy ko Karima don a duba mishi halin da take ciki sai ya tuna ai duk sun fice gurin ayyukansu.
Lambarta ya sake gwada kira, a kashe. Ya ƙara gwadawa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, amma duk amsa ɗaya na'uwa take maimaita mishi. Wannan lambar da yake kira a kashe take.
Jikinsa a sanyaye ya ajiye wayar gefe ɗaya, hankalinsa a tashe, ga wasu ƴan ƙananun ƙwallah na matsanancin damuwa da zazaaɓi da suka taru a kwarmin idanunsa.
Ya ɗauki fiye da awa ɗaya yana cikin wannan hali, kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye a wahalce ya fice daga ɗakin, sannu a hankali ya fice daga ɓangaren nasa gaba ɗaya ya nufi cikin gida ɓangaren su Mummy.
Yana shiga, ya hangi mai aiki Rahina tana jera abinci kan teburi. Da rawar jiki ta zube ƙasa, za ta fara gaishe shi ya katse ta da tambayar
"Ina Zulaikha?"
"Tana ɗakin Hajja za ta yi mata kitso..."
Kafin ta gama faɗa har ya bar gurin, kai tsaye ɗakin Hajja ya nufa ba tare da wani tunani ba. Siririyar sallama ɗaya kacal yayi, bai jira an amsa ba ya buɗe ƙofar ɗakin yasa kai ciki, Hajja ya gani, kwance akan kujera. Da alamun tsifa take yi barcin ya kwashe ta, domin ga kan nan a buɗe ta kwance rabi saura rabi.
A hankali ya koma da baya da baya ya fice daga ɗakin sannan yaja mata ƙofa. Daga nan, ɗakin Zulaikha ya nufa kai tsaye, yana tafiya, amma ji yake kamar ba ya sauri don tsananin ɗokin son tozali da kyakkyawar fuskarta da gane ma idanunsa wane hali take ciki?
Ko da ya isa ƙofar ɗakin, ita ko arzikin sallama ɗayan ma bata samu ba. Hannun ƙofar kawai ya kama ya buɗe ya cusa kansa cikin ɗakin.
A firgice Zulaikha da take zaune a gefen gado ta buga tagumi da hannu bibiyu ta miƙe tsaye. Hankalinta a tashe, tsawon daƙiƙu sittin suka ɓata suna kallon ƙuda a tsakaninsu ko wanne ƙirjinshi na bugawa fat-fat.
Kamar wacce aka tsikara, aka ankarar kuma sai tayi saurin komawa ta zauna da sauri bayan ta tuna da irin rigar da ke jikinta. Duk da ba mai bayyana tsiraici bace, amma ta kamata ƙwarai. Sannan babu hijabi ko mayafi a jikinta, ga kanta babu ɗankwali, lallausan gashin kanta da yasha gyaran saloon a barbaje, amma tana ga gara shi da ɗan sauƙi sauƙi a bisa ace ta cigaba da tsayuwa a gabansa da matsattsiyar riga. Miƙewa domin zuwa ɗaukar ɗankwali ko mayafi kuma kamar ta ba shi damar ƙare mata kallo gaba da baya ne.
"Allah ya baki haƙuri Beby. Ki yafe min don Allah... kalamaina ne suka jefa ki a cikin damuwa har ya saka ki kuka ko?"
Yayi maganganun da rauni sosai a cikin muryarsa.
[2/8, 9:20 PM] Fareeda Abdallah: Duk da yadda maganganunsa suka daki zuciyarta, ta kasa ɗagowa ta ƙara kallonsa a karo na biyu. Balle kuma har ta iya buɗe baki ta amsa masa. A madadin ɗaya daga cikin biyun ma, sai idanunta ne suka ƙara ciccikowa da hawaye. Lokaci ɗaya suka fara sauka ɗis, ɗis, a jikinta.
Kasancewar idanunsa ƙur yake a kanta, hakan ya bashi daman ganin hawayen da take yi. Hankalinsa a tashe, da wani maɗaukakin sauri yaja jikinsa zuwa gare ta. Ba tare da damuwa ko fargabar komai ba yasa gwuiyawunsa a ƙasa, hannayensa biyu na rawa, yasa hannu ya ɗago fuskarta suka kalli juna a karo na biyu.
"Kuka kike ƙara yi Zulaikha?"
Ya jefa mata tambayar, da wata irin shaƙaƙƙiyar murya kamar wanda zazzafar mura ta riƙe mishi maƙoshi.
"Kiyi haƙuri. Ki yafe min. Ni ma ba yin kaina bane, Allah ne ya jarabce ni. Kiyi haƙuri don Allah... Amma na rantse da Allah ban fara son ki don zan iya dainawa ba. Ki daure ki bani dama Zulaikha..."
"Gobe, zan... tafi gida... can ƙauyenmu..."
Ta katse shi da faɗin haka cikin kuka da karkarwar murya.
"Dummmm!"
Haka ƙirjinsa yayi wani mummunar bugawa, kansa ya sara duk a lokaci ɗaya. Tsananin mutuwar jiki da mummunan tashin hankalin da ya ƙara lulluɓe shi yasa bai san sa'adda ya saki fuskarta yayi zaman ƴan bori a gabanta ba.
Ya haɗiyi wasu kauraran miyau daki biyu daƙyar, masu masifar ɗaci da kaurin da ke barazanar yaga mishi maƙogwaro.
"Saboda... Saboda... Saboda na ce ina son ki ina son aurenki shi yasa za ki tafi???"
Ya tambayeta daƙyar, bayan yayi ta ƙoƙarin harhaɗa kalmomin da zaiyi amfani da su gurin tambayarta suna suɓucewa a harshensa.
Tunawa da tayi da inda suke ita da shi, da kuma tunanin ako wane lokaci daga yanzu Aunty Karima za ta iya dawowa cikin gidan. Kuma da ta dawo, wacce za ta fara nema a gidan bayan Mummy ita ce.
Ba ma a gansu a yanayin da suke zaune ita da shi yayi zaman dirshan a gabanta kaman mai roƙon gafara ba, a ganshi a cikin ɗakinta ma babban ƙalubale ne a gare ta, kuma abin a saka musu ayar tambaya ne da zargi.
Don haka ta daure, ta ƙwarara zuciyarta. Abinda ta lura da shi shi ne tabbas Abban Imam da gasken-gaske yake yi, tunda har ya iya ajiye kunya da kamun kansa ya biyo ta har cikin ɗakinta, abinda bai taɓa ko kwatanta yi ba. Ko ɗakin Karima da taƙe ƙanwarsa ba shiga yake yi ba, balle ita da ta kasance ba muharramansa ba.
Abinda ta lura da shi shi ne, a yadda yake ɗinnan zaune dirshan a gabanta, idan ba wata ƙwaƙƙwaran magana ɗaya ya ji daga bakinta ba bazai fita mata a ɗaki salin-Alin cikin sauƙi da kwanciyar hankali ba.
"A'a!"
Ta faɗa a hankali.
"Wallahi ba saboda ka ce kana so na bane zan tafi gida. Kawai dai na yi ma Innaye wani alƙawari ne kafin tahowata..."
Tayi ɗan shiru, kafin ta cigaba da magana a kunyace.
"Na mata alƙawarin duk sadda na samu wani Namijin da ya nuna sha'awar aure na a yadda nake, zan koma can ƙauye, domin aje can a nemi aure na... Ko baza ka bi ni ƙauye ba Abban Imam?"
"Zan bi ki. Na rantse da Allah zan bi ki."
Ya amsa mata da sauri.
"Ai ko cikin ramin macizai kika shige da sunan asalinki, Zulaikha ni mai iya jure duk wani cizo da sara ne in shiga cikin ramin don zuwa neman aurenki. Daman dai babban buri na shi ne in ji shin kin amince da soyayyar da nake miki? Za ki bani damar mallakar zuciyarki ta hanyar buɗa min filin guri inyi dashen kyawawan furanni? Ina so ki fahimci ni da gaske nake son ki, ki amince min don Allah... In Allah ya yarda baza ki taɓa yin da na sani a tarayyarmu ba."
"Na amince!!!"
Ta amsa a kunyace, sannan ta sa tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana murmushin jin kunya. Wani matsanancin daɗi da farin ciki na ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciya da sassan jikinta.
"Alhamdulillah!"
Ya faɗa da yanayin da ke bayyana matsanancin farin ciki. Da ya rasa abinda zai ƙara bayan kalmar hamdalar kawai sai ya juya zamansa ya fuskanci gabas, yayi sujudus-shukur.
Ya daɗe yana jera kalaman godiya ga mahalicci kafin ya miƙe zaune ya fuskanci Zulaikha itama ya fara mata godiya, da alƙawurra kala-kala na irin yadda zai kula da ita ya riritata idan har Allah ya tabbatar da aurensu.
Ita dai ta kasa cewa komai, sai murmushi kawai take ta jifanshi da shi, zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da ta daɗe bata tsinci kanta a cikin makamancinsa ba.
"Abban Imam, ya kamata ka tafi ɓangarenka pls! Kar a shigo a ganka a cikin ɗakina."
Ta tunatar da shi cikin sanyin murya, ganin kamar ya ma manta a inda yake.
"A'a ni dai, ban gaji da ganin kyakkyawar fuskarki ba gaskiya Beby."
Ya faɗa da dukkan gaskiyarsa, har yana ƙara gyara zaman dirshan a gabanta.
Zazzaro idanu tayi da farko, sai kuma ta ɗan ɓata fuska. A shagwaɓe ta ce
"Ni dai don Allah ka tafi, ba ga waya ba za mu cigaba da magana? Don Allah ka fita. Ka ga fa tun ɗazu kitso zan je inyi ma Hajja, na san yanzu ta gama tsifa. Kuma ma Aunty Karima ta kusa dawowa, bazan ji daɗi ba gaskiya idan aka tarar da kai anan, don Allah ka tafi."
"Zan tafi. Amma bisa sharaɗi ɗaya..."
"Menene sharaɗin?"
Ta katse shi da tambayar tun kafin ya rufe baki.
"Ki ɗaukar min alƙawarin za ki kunna wayarki, kuma idan na kira za ki ɗauka, sannan baza ki sake kashe wayar saboda ni ba."
"Na yi alƙawari. In sha Allah zan kiyaye, bazan sake kashewa ba."
Ta amsa mishi da murmushi a fuskarta. Domin ta zaci wasu sharuɗɗa ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 40