wani lokacin, amma ɗan'uwanta fa?, Allah ɗaya yasan acikin rayuwar da ya ke ciki yanzu, Allah kuma kaɗai yasan irin kalaman da yake jifana da su a kowacce rana ta rayuwarsa, hakkinsa kaɗai ba zai barni samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, ita kanta ina shakkar ta san sirrin komai anan gaba domin zuciyarta irinta Kakarta ce, ba zatayi min da sauƙi ba muddin tasan Sirrin Ɓoye...Malam na roƙeka kai da Yaya ku taimaka min da maganin da zamu sha mu mutu, wallahi ba kaina nake tausayi ba, rayuwarta na ke tausayawa...ku bar batun zan koma wajen iyayena domin kuwa zuwa yanzu sun manta da rayuwata...amma ga wannan takardar tana ɗauke da adireshin gidanmu, Bayan raina na aminta akan kuje, idan kunje kun sami mahaifina a raye kuce ina neman gafararsu, ku sanar musu ni da Hussaina mun bar duniyar, amma Hassan yana raye, ina roƙon alfarmar su neme shi su mallaka masa abunda na mallaka gudun kar ya tagayyara a rayuwarsa, idan kuma ya buƙaci mahaifinsa su bashi hoton da yake cikin wannan saƙon yaje yayi yaƙin nemansa"...
Shirunta yayi dai-dai da sandarewar ƙafafuna, shin ta wacce fuska zan fassara Al'amarin Kulu ne wanda yake da matuƙar ɗaure kai?, menene ya faru acikin rayuwarta, jiyo takun motsin fitowa nai saurin barin wajen na koma ɗaki, kuma har ɓarawon bacci ya ɗaukeni Kulu bata dawo ɗakin ba, sai a washe gari dana farka sakamakon hasken rana da ya dallare min idanu wanda ya shigo ta ƙofar taga, nayi zumbur na miƙe na sauka daga gado tunawa da nayi da banyi sallah ba.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maki hajarki cikin farashi mai rahusa, ke dai tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*13)*
"Amadu ya kira yace yanzu haka jirginsu zai tashi, kowa ya sasu a adu'a Allah ya sauke su lafiya".
Sallamewata kenan daga sallah naji Baba na wannan maganar. Nasa hannu na goge guntuwar ƙwallar da ta sakko min, dan banji daɗin tafiyar Ya Amadu ba alhalin banyi sallama da shi ba, ajikina sai nake jin kamar yayi tafiyar da ba zan ƙara ganinsa ba ne. Na miƙe daga bisa sallayar da nake na fita tsakar gida, na ɗauka tsintsiya na hau aikina kasancewar yau nike da shara, Adawiyya na wanke-wanke inata tsokanarta amma ci kanki wannan bata ce dani ba, kamar bata san ina yi ba. Har ga Allah na manta da mun samu saɓani da ita, sai a yanzu da nayi mata magana naga ta ɗago ido ta ɓalla min harara, jikina sai ya ƙara yin sanyi, nai sauri-saurin kammala shara sannan naje na sameta a ɗakinsu, lokacin ta cire kaya zata shiga wanka, tana ganina ta sauya walwalar da ke saman fuskarta zuwa tsantsar ɓacin rai, cikin fushi na ƙarasa inda take nasa hannu na juyo da ita muka fuskanci juna, kamar saukar tsawa cikin ruwan sama naji ta sauke min mari saman fuskata, marin da ya shigeni har kwanyata, na gigice na dafe wurin ina daɗa jin shigar zafinsa. Na dubeta da idanuna da suka kawo ruwa nace,"Adawiyya wanne irin laifi na aika miki haka da har za ki mareni?, shin ɗan Adam ba ya kuskure ne a rayuwarsa?, ko kuma dan yayi ba dai-dai sai ace ba za'a yafe masa ba?, laifin me nayi miki Adawiyya? ki faɗa min dan na kiyaye gaba, wallahi ko menene ban yi miki da san raina ba, dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, ba zan iya jurar fushinki ba".
Taja tsaki ta bangaje ni zata wuce na riƙeta cikin ɗagin murya nace da ita, "babu inda zaki je sai kin faɗa min abunda na miki, ban iya rayuwar gaba ba saboda haka ba za ki sa na fara ba". Ta fizge hannunta tare da jan dogon tsoki sannan ta wuce ta barni tsaye a wurin, Ni kuma nabi bayanta da ido. Na goge hawayena nace da Inna Zulai wadda ke linke kaya, "Inna kinga Adawiyy ko". Bata kalleni ba balle nasa ran zata amsa min, saboda haka nasa kai na fita daga ɗakin. A tsakar gida na zauna nayi jugum, inata kallon Adawiyya dake wasa da dariya da ƴan'uwanta, ni kuwa ta barni jugum bayan ta san da ita na saba a kaf ƴan'uwana. Saboda nayi zurfi a tunani sam banma ji habaicin da suke ba sai da Basma ta taɓoni tana tambayata mene nake kuka, ko saboda Gwaggo da Inna Amarya sun tafi unguwa ne, na ɗan harareta nace, "saboda ance miki ni kece ko". Ta zauna gefe na tana tambayata ni me yasa ƴan'uwan Gwaggo basu saya min komai ba na gudunmawar tafiya makaranta, nace da ita,"Basma duk tulin kayan da aka bamu ƙarin me kuma zan nema yanzu, sai dai zuwa gaba". Ta kama hannuna ta riƙe tana cewa, "Yaya banji daɗin abunda su Anty Adawiyya ke cewa ba, wai ke baƙin jini ne da ke shi yasa baki da saurayi ko ɗaya, ita gashi samarinta sai kawo mata kaya suke na tafiya makaranta, kuma wai ƴan'uwan Gwaggo duk faƙiran talakawa ne shi yasa babu wanda ya kawo miki ko sabuln wanka, ita kuwa dangin Innarsu kowa sai gwangwajeta yake tunda suka ji zata wuce makarantar kwana, amma ke babu wanda ya tausayawa Baba ya ɗauke masa nauyin wani abun daga ƴan'uwan Gwaggo...". Ban barta ta ƙarasa ba na dakatar da ita da cewar,"shiru...karki kuma kawo min irin wannan zancen ko aina ne ma kika ji anayi, kuma saura naji kin faɗawa Gwaggo idan ta dawo, wallah sai na haɗaki da Ya Kabiru nace kinyi munafurci". Ta gyaɗa kai alamun taji, na kama hannunta muka wuce ɗaki dan na lura yau ƴan ubanci ake nuna mana a gidan. Muna shiga sai ga Kulu ta biyo bayanmu, na kalleta da mamaki dan bata shigowa ɗaki sai dare, na ɗauke kai naci gaba da haɗa kayana acikin jakar bakko dana amso wurin Lukman Saboda gobe zamu wuce makaranta kuma tun safe Gwaggo tace na kimtsa ba sai goben tayi ba azo ana aikin jirana inja mata magana, ina haɗa kayan ina jadaddawa Basma saura idan na tafi ta taɓa min kayan sawa, tunda ita Allah yayi ta da tsayi kamar ɗiyar samudawa, gata da girman jiki nan da shekaru kaɗan sai dai a fara cewa ni da ita sa'anni ne. Dariya tayi tace,"Yaya to ni me zanyi da kayanki, ai ko girma na daɗa yi zasu ɗage min tunda na fiki tsayi, kuma zasu yi min kaɗan tunda kinga na fiki jikin ƙiba ba kamar ke ba aba kamar mariƙin lema". Ta ƙarasa maganar tana dariya, na juyo da jin haushi ina kallonta da tunanin hukuncin da zanyi mata, sai ta tashi daga inda take ta koma jikin kulu tana cewa, "nifa bani na faɗa ba Anty Adawiyya ce ta faɗa ɗazu...Allah Yaya idan kinje makarantar ki dage da shan madara da banbita ko kyayi auki a daina goranta miki". Nayi kanta zan kai mata duka Kulu ta kareta. "Kulu ki barni na koya mata hankali, kawai dan taji wasu na ce min mariƙar lema itama saita ɗauka, ko an faɗa mata ni sa'arta ce". Maganar nake ina kokawar janyota daga jikin Kulu, karo na farko a rayuwata dana taɓa ganin murmushin a saman fuskar Kulu, murmushin da ya bayyanar da fararen haƙoranta ƙal, har malotsin kumatu(dimple) ya loma sosai, ban san na shagala a kallon kyakykyawar fuskarta ba sai da ta shafo fuskata, cikin jin kunya na sadda kaina ƙasa, lallai ubangiji yayi halitta a jikin kulu, domin tana da irin kyan da Indiyawa ke cewa milky cute. Na miƙe naje naci gaba da haɗa kayana, kuma fasa korawa Basma kashedin taɓa min kaya ba har sanda zan dawo, itama tana cewa bama zata saka ba, ai ɗinkin da Gwaggo keyi mata ma yafi wanda Ya Kabiru ke yi min.
Gefin Yamma muna zaune a tsakar gida muna shan iska, yau dai banda abokiyar hira sai Basma dan Adawiyya da gaske ta juya min baya, shi yasa ko da Basma na tsokanata banji haushinta ba, saboda sau tari Gwaggo kanyi ƙorafin ga ƴar'uwata ciki ɗaya bana janta ajiki. Yaro yayi sallama yace wai ana sallama da Kabir, nayi zumbur na miƙe nacewa yaron,"kace baya nan amma ya ɗan jira". Na faɗi hakan ina gyara ɗaurin zanena, dama tuntuni ina son ganin Suhail saboda na bashi agogonsa daya bani ajiya na manta shima kuma ya manta. Adawiyya da ke kallona ta kyaɓe baki bayan taja tsaki tace,"uwar azarɓaɓi da kika tashi haka jiki na tsuma idan kinje me zaki masa ƴar neman suna". Dama ni shashasha kamar yanda Inna Amarya ta faɗa tunda idan an gwaɓa min magana ba ganewa nake ba, Dan haka ina wucewa ɗaki nake ce mata,"ba na faɗa miki ina son ganinsa ba zan bashi ajiyarsa". Basma ce ta ɗauko min kwallar daga saman sif, saboda tsayina ba zai kai ba kuma kujerarmu ta ɓalle, na ɗauko agogon zan fita nayi karo da Kulu da ke shigowa, ta ɗaga min kai alamar tambaya ina zani. "wurin Abokin Ya Kabiru". Na faɗa ina goge ƙurar dake jikin agogon wanda keta sheƙi, ta ƙara kaɗa min kai alamar me zanyi a wajen nasa. "agogonsa zan kai masa". Na faɗa ina ƙoƙarin raɓawa ta kusa da ita na wuce, saita riƙoni tare da karɓar agogon, ta ɗau tsawon daƙiƙa tana kallon agogon sannan ta ɗago ta dubeni, magana take so tayi amma kuma ta kasa, nayi guntun murmushi ƙasan raina nace, _"haba kulu aini yanzu bana cikin waɗanda kike rainawa hankali da rashin maganarki, dan haka idan za ki magantu ki magantu kawai"._ Na bita da ido ina kallon yanda take daɗa jujjuya agogon a hannunta kamar me neman wani abun ajikinsa, nasa hannu na ɗago da fuskarta ina ɗaga mata gira nace, "magana kike so kiyi ba. To yau kawai ki gwada sa'arki mana ko ikon Allah zai kasance akan maganar taki". Na ƙara ɗaga mata gira dan bata ƙarfin gwiwa. "aina shi me agogon yake?". Ta jefo min tambayar, maimakon na bata amsa sai nayi ɗan tsalle da murna. "kinga ikon Allah ko, dama nace miki ki gwada sa'arki...shikenan yau Kulu ta fara magana". Ta riƙo hannuna daga fitar da nake ƙoƙarin yi tace dani,"ki riƙe masa kayansa da kyau wannan ba zallar ƙarfe bane, Zinare ne, dukiya ce ba ƙarama ba. Da kin ba shi ki dawo". Nayi shiru ina nazarin maganarta kafin na kaɗa mata kai na fita.
A ƙofar gida na tadda Suhail shi da Adawiyya suna hira, mamakin da nayi da Adawiyya ta nuna kamar bama faɗa da ita, wannan cin maganin da ɗauke kan babu shi, sai jawoni kusa da ita da tayi, ta amsa agogon da ke hannuna tana cewa da Suhail, "kaima Yaya Suhail ina kai ina bawa mashiriranciya ajiya, ai ba'a bawa Mairo ajiya dan idan bata yar ba to zata mantar da mai shi ne ƙarshe kuma ya salwanta". Na murguɗa mata baki nace, "to ai ni da ke sammakal...kuma Suhail idan baka yarda ba ka tambayi Ya Kabiru tsakanina da ita wa yafi wani mantuwa". Ya dubeni yana murmushi yace,"to aiga amsar anan tunda gashi na baki ajiya kin manta da ita tsawon watanni sai yau". "to ai ba mantawa nake ba sha'afa nake...kayi haƙuri". "tom na haƙura kar ayi kuka". Ya faɗa da zolayata sannan ya kuma cewa, "Bella tace na gaida balarabiyar gidansu Kabiru me kama da jininta...kuma tana zuba idon ranar da zata kuma kai mata ziyara". Mu biyun muka kalle shi a lokaci ɗaya sannan a tare muka ce da shi, "wace balariyar gidanmu?". Ya soshi gefen girarsa kana yace,"tace min dai Mairo". Na sunkwi da kai ina murmushi cike da jin daɗi, maganarsa ta katse tunanin da nake na ɗago ina duban ledar da ya miƙo min, nasa hannu na amsa ina cewa yayi ma Bella godiya. Sannan shi kuma yay mana sallama ya shiga mota ya tafi bayan yace mu sanar da Ya Kabiru yazo bai same shi ba.
Muna shiga cikin gida Adawiyya ta fizge ledar hannuna tana faɗin,"dilla buɗe mana muga mene aciki". Nace,"sarkin kwaɗayi kawai". Ta kama hannuna muka shiga ɗakin su Mu'azzam.
*Comment&Share.*
*SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*14)*
Muna buɗa ledar wani daddaɗan ƙamshi ya bugi hancinmu, na fito da kwalin da ke ciki wanda aka nannaɗe shi da abun ado, Adawiyya ta karɓa daga hannuna ta shiga kiciniyar buɗe shi amma saboda irin naɗin da aka masa ta gagara kuncewa. "kinga ki bari Ya Kabiru ya dawo ya buɗe mana". Bata saurareni ba taci gaba da ƙoƙarin yanke abun da reza, na tashi na fita daga ɗakin ina ce mata, "ni dai idan kin buɗe kin gama gani kya kawo min ɗaki". Gaba ɗaya ma na manta da babin wata Kulu, sai da na shigo ɗakin naga ta tsareni da ido. Na turo baki na wuce na zauna ina cewa,"ai kin fara magana dan haka idan ba za ki min magana da baki ba to ki bar kafeni da wannan manyan idanun na ki masu firgitarwa". Naci gaba da abin da nake yi, ihun Adawiyya da ya karaɗe gidan shi yasa ni tashi na fita da gudu, cirko-cirko na samesu bakin ƙofar ɗakinsu Mu'azzamu sai Inna Zulai da ke cikin ɗakin tana watsa ruwa a wutar da ta kama a ɗakin, na zaro ido waje wanda tashin hankali ya cika cikinsu na dubi Adawiyya da ke aikin yarfe hannu nace da ita, "garin ya haka?". Bata bani amsa ba sai Habiba ce tace,"ina ga fa fitila ce ta suɓuce daga hannunta ta fashe, ƙila kuma da kaya kusa da wurin ta kama bata sani ba". "Allah ya kiyaye gaba". Na faɗa ina riƙe yatsan Adawiyya da ta ƙone ina mata tofi, ta rungumeni tare da fashewa da kuka tana bani haƙuri, haƙurin da ban san na menene ba har sai da ta ce min ledar kayan da Bella ta bani ce ta ƙone. Har raina naji babu daɗi sai dai to ya zanyi tsautsayi ne, saboda haka ma ban tsaya jin ba'asin Kyautar mene aciki ba sai dai da Gwaggo ta dawo na faɗa mata, tace to ai babu komai ba rabo bane ita kuma Bella an gode mata.
Hankalin kowa a gidanmu bai gama kwanciya ba sai da Auwalu yazo yace sunyi waya da Ya Amadu yace sun sauka lafiya, idan ya sauka a masaukinsa zai kira, Nan Baba yayma Auwalu godiya da ƙoƙarinsa. Bayan anyi sallar magriba Ya Kabiru yace nazo na raka shi unguwa, Inna Amarya tana tayi masa tsiyar wai ko taɗi zan rakashi, shi dai murmushi kawai yay bai ce komai ba, ya kama hannuna muka fita, wani shagon kayan kwalliya muka je ya siya min ɗan kunne da turare, akan hanyarmu ta dawo sai dana sa ya siya min tsire tukunna muka ɗauki hanyar gida. "idan kin aje kayan kizo". Yace dani san da muka shigo zaure. Ina shiga na bawa Gwaggo kayan nace ta ajiye min kuma kar aci min tsire, tace na dawo na ɗauki kayana ita bata amsar kayan kashedi, ina ƴar dariya na wuce ina cewa,"ni dai na bada kuma na faɗa kar aci min tsire". na fita fuskana ɗauke da dariya sosai saboda mitar da naji Gwaggona nayi wai tasan saboda Basma nake kora wannan kashedin.
Da sallamata na shiga ɗakinsu Ya Kabiru, yana zaune kan yaloluwar katifarsa da littafi a hannunsa, haka yake shi sam baya gajiya da duba takarda. Na ƙarasa kusa da shi na zauna na sarƙafe hannayenmu sannan na ɗora kaina bisa kafaɗarsa. "Yaya wai baka gajiya da duba takarda ne?". Ya rufe littafin yana ce min,"lokaci ne Mairo kema soon za ki zama irina tun da ba kya wasa da karatu". Ya faɗi hakan yana shafa kumatuna. "Yaya ɗazu Suhail yazo baka nan". "ehh munyi waya da shi yake faɗa min". "yana da kirki sosai...yauwa ka kalla ma Bella ta bada kyauta a kawo min". Ya muskuta yana gyara zama yace, "ahh ke dai akwaiki da farin jini, Allah ya haɗa jininku da Bella, to shi ne kuma ba za'a nuna min kyautar ba". "ta ƙone". Ya kalleni ta gefen ido sannan yace,"kaman ya ta ƙone?". "Tsautsayi, Adawiyya ta ɗauko fitila ta suɓuce ta faɗi kuma a kusa da ledar, kamin ta ɗebo ruwa ledar ta kama gaba ɗaya". Shirun da yay yasa na ɗago na dube shi, kamin nayi magana ya tari numfashina da cewar, "wannan ai shashancin banza ne". Ganin zaiyi faɗa na hau ba shi haƙuri.
Ya sarƙafe yatsun hannunmu wuri guda yana ce min,"Mairo nah". "na'am Ya Kabiru nah". "do you know what i want from you?". Tuni na ɗauke tambayar da yayi min cikin harshen turanci, kasancewar tun da akace zamu tafi makaranta yana zaunar damu ya koya mana kalmomin turanci, kuma ina ganewa sosai dan a makarantarmu ba wani turanci ake mana ba malamai sunfi yin hausa wai saboda makarantar gwamnati ce. Na gyaɗa masa kai, "No Yaya sai ka faɗa". Ya gyara zamansa in da ya fuskantoni, yasa hannu ya ɗago haɓata, ya umarce ni akan in sanya ƙwayar idona cikin nasa.
murmushin fuskana yaƙi ɗaukewa a sa'ilin da ƙwayar idona ta sarƙafe cikin tasa, kallona yake babu ko ƙiftawa ya ce,"ki kula min da kanki a makaranta dan Allah, banda shirmen banza da ƙawaye, Karatu ya kai ki dan haka shi kawai za ki yi, ki dage ki zama mai ƙoƙari abar kwatance a wurin Malamai...sannan ban lamunce miki ba dai-dai da ranar ɗaya Suhail yaje makarantar ya buƙaci ganinki kije, bar ganin su ne silarku a makarantar, wallahi naji labari sai ranki ya ɓaci fiye da tsammaninki, karki ga bana ƙasar kiyi tunanin ba zan sani ba...zuciyata zata ke sanar min halin da kike ciki da dukkan abunda kike aikatawa...kuma ki tabbata in har kika wuce ta ɗaya a aji to la shakka zamu yi hannun riga da ke".
Na gyaɗa masa kai nace,"insha'Allahu Ya Kabiru zan zama mai kiyaye dukkan umarninka". Na faɗa ina ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taru a idona. Ya ɗauko wani zobe a aljihunsa fari mai kyau ya saka min, sannan yace na tashi naje na kwanta da wuri kar azo tafiya gobe bacci bai isheni ba. Ina shiga na tarar kowa na zaune yana cin abinci, yau an makara acin abincin dare kasancewar Inna Amarya ke da girki kuma yau sunje unguwa basu dawo ba sai gabanin magariba. Na wuce na zauna kusa da Adawiyya ina cewa,"lallai ma ke ɗinnan, to kinci rabonki". Fuskar nan tata a haɗe ta galla min harara ta ɗauke kwanon abincin ta juya min baya, idan nayi amfani da hankalina har yanzu dai bata bar fushi dani ba, saboda haka na miƙe naje nace da Inna Amarya ina nawa abincin, tace na tambayi Adawiyya ai haɗe mana tayi, kamar ba zan tambayeta ba kuma sai nace da Basma ta tambayo min ita aina ta aje min nawa. "ta duba ɗakin girki yana murfin tukunya". Abin da tace da Basma kenan a ƙufule. Na shiga na ɗauko, abincin ma naji duk ya fita akaina dan haka na tashi daga kansa na fita na bawa almajirai, dan har ga Allah ni bana jin daɗin cin abincin ba tare da ita ba.
A ɗaki na sami Gwaggo zaune tana sauraran radio, na tambayeta "Gwaggo ina ajiyata?". Tace, "na bawa Innarki". Na wuce ɗakin Inna tana lazimi ta min nuni da inda ta ajiye naje na ɗauka, Basma tazo ta ƙaraci nacin zamanta na hanata ko ɗanɗane nace wallah bata ci. Sai dai tun a yankan farko dana saka a bakina cikina ya ƙulle, ina gama ci kuma sai amai kamar zan amayar da kayan cikina, numfashina ya fara neman sarƙewa, tari yaci ƙarfina babu ƙaƙƙautawa cikin ƙanƙanen lokaci na fita hayyacina. Inna Amarya ta sallame daga lazimin tayo kaina cikin salati da kiɗima, ta shiga ƙwalawa Gwaggo kira itama tazo, ganin abun dai ba me ƙarewa bane Ya Kabiru ya bawa lukman yace yaje chemist ya karɓo maganin amai, babu jimawa sai gashi ya dawo, ba zan iya haɗiya ba saboda halin ha'ula'in da nake ciki, sai Inna Amarya ce ta jiƙa da ruwa kaɗan Gwaggo ta buɗe bakina aka tsiyaye min ya wuce da ƙyar, duk da jiƙe-jiƙen magungunan da Gwaggo keyi tana bani ina sha, da tarkacen magungunan asibiti da Ya Mu'azzamu ya ɗebo, amma abu babu sauƙi sai a wurin Allah dan abu sai gaba yake daɗa yi. Baba duk ya rikice ya rasa abun yi, sai can da ya saita hankalinsa ne yay tunanin yi min tofi, haka Baba ya dinga tofin adu'a ana bani ina kwankwaɗewa.
Ya Kabiru na sassarfa ya fita ya kira Ado me chemist anan kusa damu, yana zuwa ya duba ni yaga mawuyacin halin da nake ciki, nan ya shawarci Baba akan a tafi asibiti kawai, Baba ya amsa masa da "to" ya kuma yi masa godiya dan yayi min allurar tsaida amai yace a bar kuɗin. Kowa yay jigum ana jiran ganin ikon Allah akan allurar da aka min, amma ina amai yace bai san wannan ba, ciwon ciki ma haka, kuka nake kawai ina kiran mutuwa zanyi, ina kiran a yafe min, furucina yasa jikin kowa yay sanyi, tashin hankali ya ƙara bayyana a fuskonin kowa.
Gwaggo kuwa kuka kawai ta ke tana riƙe dani ajikinta, ni dai na tabbata a yanzu babu abin da ya rage acikina illa kayan ciki, amma abinci da ruwa kam babu su, dan a yanzu haka idan nayi kakarin aman sai dai na tofar da jini, hankalin kowa ya daɗa tashi, ƴan'uwana duk kuka suke su na ta jera min sannu.
Ya Kabiru yace da Baba, "Baba mu wuce asibitin tun da kaga babu sauƙi". Baba wanda damuwa ta bayyana ɓaro-ɓaro a fuskarsa, yay shiru bai ce komai ba, Inna Zulai da ke shafa min ruwa ajiki saboda zafin zazzaɓi ta ɗago ta dube shi tace, "Malam kayi shiru, halin da ta-ke ciki fa yafi kamata da asibitin". Baba kamar zaiyi kuka yace,"ku kun san halin da ake ciki, asibiti wajen kashe kuɗi ne masu yawa, a yanzu kuwa idan muje wa zai bamu?, aina zamu samo?, ni da ban ajiye ba ban bawa wani ajiya ba, yanzu haka babu ko kuɗin mota ajikina...dan haka mu zubawa sarautar Allah ido insha'Allahu sauƙi zai sauka gareta". Sunusi yace da Baba, "to ai Baba ba asibitin kuɗi za'aje ba, na gwamnati zamu". Baba yay murmushi mai ciwo sannan yace, "Sunusu ina nusar da ku ne ku gane ko munga likita kyauta akwai kuɗin magani, ko shi ma maganin kyauta zasu bamu?". Shiru ya ratsa biyo bayan tambayar Baba, can Ya Kabiru ya laluba aljihunsa yace, "Baba muje ga ɗari biyar ajikina zata ishemu zuwa asibiti, magani kuma ko ba'a siya duka ba sai a nemi mai muhimmanci ciki a siya". Baba yana dubansa yace, "kana dana siyan magani kenan?". "Allah zai kawo Baba". Gwaggo na gefe tana goge hawaye tace da shi,"Kabiru jeka da sauri samo mota, kaga numfashinta neman ɗaukewa yake gaba ɗaya". Ya fita jiki na sassarfa jikinsa gaba ɗaya ya wanke da zufa, yana fitowa ƙofar ɗaki kuma yay karo da Kulu a tsaye tana kuka. Ya tsaya yana dubanta da kuɗin da ke hannunta, kuɗaɗen da bana ƙasar nan bane, yaja numfashi ya sauke, kamar zai ce da ita wani abun sai kuma ya wuce kawai, ta bi bayansa da ido a san da hawaye ke daɗa sauka saman fuskarta, sannan ta koma ɗaki taci gaba da ruzgar kukanta tare da nemawa Mairo sauƙi a wurin mahallicinta.
Babu jimawa Kabiru ya dawo da mai adaidaita, yana shigowa ya kinkimi Mairo wadda ta jima da sumewa, an watsa ruwa an watsa amma babu alamar zata farfaɗo. saboda a sami sauƙin kuɗin mota Malam yace Inna Amarya da Adawiyya ne kawai zasu je asibitin, Gwaggo dai taso da ita aka tafi, sai dai babu yanda zatayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 52