sani sanyin Mairo ya soma ne daga lokacin da Baba yay ma ta wata nasiha me ratsa jiki, kuma kowa yay mamakin wannan sauyawar zafin ran nata, zafin kan da idan tanayi zaka rantse kana hasko irin turirin da ke fita ta saman kanta, kuma zaka ji zafinsa ajikinka idan ta fitar da iskar baki.
dan haka ya dubi Emanuel yace da shi,"Sir kayi haƙuri ka tafi kawai, mun gode sosai da taimakon da kayi ma ta". Emanuel ya juya ya fice, bai fita dan jin tsoron abin da zata aikata ba, ya fita ne saboda yanda yake jin kansa a irin yanayin da ta ke jin kanta, shi ma kansa tafasa yake, numfashinsa kuma na fitar da turirin zafi, zai aiwatar da abinda yafi nata muni, idan ta sha a nono to shi ma wannan zafin ran yasha shi a nono na tsawon shekara uku ciff, kuma zafin ran da zai rantse yaci uwar nata, to sa'a ɗaya kawai taci, shi ma da shi ne wasu suka yi sanadin shigarsa addinin musulunci zai yi fiye da hakan dan shi ma me kishin addininsa ne, kuma taci daraja, darajar Amadu.
sai da Amadu ya tabbatar zuwa yanzu Emanuel ya bar asibitin sannan ya dubi Mairo da ke duƙe a ƙasa tana rusa uban kuka, ya doka ma ta uwar tsawa akan ta miƙe su tafi, amma ko gezau ba tayi ba, wannan tsoron nasa da shakkarsa ta manta da su, ji ta ke sama ta ke shi ayau.
ganin zata masa taurin kai kuma tana neman tara musu jama'a ya fizgi hannunta ya miƙar ɗa ita tsaye, ya jata suka fita tana aikin turjiya da ihun kuka ita akan ya barta, ya ƙyaleta ta fara zuwa taci uban waɗancan kafiran, amma inaa bai saketa ba har suka shiga mota zuwa tasha, anan ma taso zille masa dan kwasa tayi da gudu zata koma shi ma yabi bayan nata a guje yasa jamaa suka riƙo masa ita, ya kuma ɓalli reshen bishiya yace,"wallahi ko ki nutsu ko kuma nayi miki dukan mutuwa a wurin nan". ba dan furucinsa yasa ta haƙura ba, ta haƙura ne saboda Gwaggonta kawai, zuciyarta yanzu Gwaggonta ta ke da muradin gani, amma ko ba yanzu ba sai kafiran da suka riƙeta sun gane bala'i suka ɗaukarwa kansu.
tunda suka shigo motar babu wanda yay magana a cikinsu har suka iso cikin garin kano, ai anan ma saita kuma birkicewa Amadu, da suka zo wucewa ta wajen wani store ta kalli kanta a cikin glass ɗin store ɗin.
"Ya Amadu bana son kaina na tsani kaina, gaba ɗaya ƙyamatar kaina nake, dan Allah kafin mu tafi ka kaini wurin da za'a sabule min wannan dattin dana kwaso a gidansu, ko da kuwa da wuta ne, ni ba zan koma gida da dattin fatar arna ba, Gwaggona ma ba zata so ganina a haka ba".
kshi ma sai a yanzu ya kula da Sarƙar cross ɗin da ke wuyanta, dan haka ya fizgota gabansa ya cire sarƙar ya jefar, ita kuma ya matse bakinta yay ma ta nuni da kan titi yace,"kinga wannan ƙaton titin, to ni me iya jefaki kansa ne mota tabi ta kanki dan ubanki, cikin ƴaƴa goma sha biyar da an rasaki ba komai bane".
ta san zai iya aikatawar tunda ya faɗa, saboda haka ta nutsu ta saita kanta. lokacin da su ka shigo garin bichi, layin gidansu, ƙofar gidansu, gidan Malam Adamu me faskare, idanuwansu suka yi tozali da abun da ya ɗaure kawunan kowannensu, dandazon mutanen da tunaninsu ya kasa sarrafa kansa. lokaci ɗaya kuma suka saki hannun juna, jikinsu ya saki, ƙafafunsu suka gaza ci gaba da ɗaukansu, suka hango Baba ya fito daga cikin gida yana goge hawaye, kuka yake, tabbas idanunsa kuka suke, suka ɗago kai a tare suka dubi junansu. Mairo tasa hannu ta dafe kanta da taji yana neman rabewa, ta rufe idanuwanta ta buɗe, sannan cikin kakkaryewar harafi tace,"Ya Amadu waɗancan mutanen fa?, kuma me Baba yake wa Kuka?". kan ya buɗa baki yace wani abu zuwan Adawiyya wajen ya sanar da su abunda yake faruwa. sun fito daga layin gidan Yagana ta hango Amadu, sai dai bata taɓa tsammanin Mairo bace a tare da shi har sai da ta zo dab dasu, nan ma kuma sai da tai da gaske sannan ta iya shaida Mairon da kamar sake halittarta akai, ta ke taji wani abu ya tokare ma ta a ƙahon zuci, da ƙyar ta iya haɗiye wani ƙullutun abu da ya tsaya a maƙogoronta, sannan ta ƙaraso gabansu, ta fasa ihun da ta ke jin kamar tayi hauka saboda baƙin cikin ganin sauyawar da Mairo tayi da kuma dawowarta, amma sai tayi pretending ihun akan tashin hankalin da gidansu ke ciki, ta faɗa jikin Mairo ta rungumeta tana fashewa da wani makirin kuka, "Mairo! Mairo ina kika tafi ba ki dawo ba sai da Gwaggo ta mutu, Mairo Gwaggo ta rasu tana ta kiran sunanki, Mairo Gwaggo ta mutu ta tafi ta barmu".
take wata tsawa me tsaida sauti ta buga acikin kan Mairo, zuciyarta ta motsa, ta ture Adawiyya daga jikinta ta ɗauketa da mari. "idan kika kuma cewa Gwaggona ta mutu sai na illataki, zan manta da cewar ubanmu ɗaya nayi miki mummunar illa". sai dai kuma me?, kafin ta kai ga ɗaga ƙafa ta taka dan ƙarasawa gida maganar Lukman da ke tabbatarwa da Amadu mutuwar Gwaggo tai sanadiyar zubewarta a wajen.
*_Dan Allah ina barar adu'a daga bakunanku masu albarka akan samun nasara da sa'a akan jarabawata, da kuma wani al'amari dana saka a gaba...na gode muku, Allah ya amsa mana baki ɗaya._*
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*28)*
"innaillahi wa'inna ilaihi raji'un". gaba ɗaya suka faɗa su na duƙawa gaban Mairo, Amadu na ɗago da kanta da ya daki wani dutse a wurin gefen goshinta ya fashe, kuma tuni ta suma, nan da nan sai rabin dandazon jama'ar da ke wurin zaman makomin suka yo wurin anata salati, Baba da ya ƙaraso wurin cikin saurin da za'a iya kirashi da gudu ya shiga raɓawa ta jama'ar da suka yi ma ta rumfa har ya samu ya kutso ciki zuwa gaban Mairo da ke shimfiɗe a ƙasa. me zai yi?, gaba ɗaya ya rasa taƙamemen me yake ji acikin zuciyarsa, abu biyu ya haɗe masa a lokaci ɗaya baƙin ciki da farin ciki, sai dai baƙin cikin ya rinjayi farin cikin, dan ya tabbata yay rashin da ba zai taɓa maye gurbinsa ba a rayuwa a dai auren mace kamar Suwaiba tun bayan Hajara.
yay ƙarfin halin tattaro sauran kuzarin da ya rage masa yasa hannu ya ɗagota zuwa jikinsa. "ai ba tsayawa zaku yi ba, Lukuman maza ka samo ruwa". yay maganar yana me duban Lukman ɗin, sannan ya dubi Amadu yace da shi,"ai na ka samota?". "Baba maganar bata yanzu bace magana ce me tsayi". ya ba shi amsar zuciyarsa na wani irin harbi.
Malam yay ajiyar zuciya kawai, ya karɓi ruwan da ke hannun Lukman wanda ya kawo a yanzu ya yayyafa ma ta a fuska, duk da haka bata farka ba sai da ya shafa ma ta ruwan a fuska da wuyanta kamin nan taja wani dogon numfashi. wannan dogon numfashin da ta ja da ke nuni da cewar tana raye shi ya wanzar da ƙullutun baƙin ciki a zuciyar Adawiyya, wadda ke duƙe daga gefen Mairo tana aikin kukan munafurci tun a san da Mairon ta zube, dan ihun da taita zabgawa ne ma yajawo hankalin mutane kansu, ihun da a wurinta yake na farinciki da dukkan fatanta na duniya ace mutuwa ce itama tayi awon gaba da ita, don gani ta ke idan har ita da Mairo zasu ci gaba da rayuwa to zata yi rayuwa tagayyararriya me cike da ƙunci, dan ta tabbata saita rasa duk wata walwalarta, saboda tun da tai ido huɗu da canjin halittar da Mairo ta samu taji duniyarta tayi duhu cike da feshin baƙin ciki tamkar aman dalma. har zuciyarta ke ingizata akan ta caka ma ta kibiyar da idanuwanta suka gani a ƙasa, ta yanda babu mai lura da hakan, kuma alokacin da ta ke ƙoƙarin aikata hakan sai Allah ya kawo Mu'azzam, wanda shi ne yaje ya sanarwa da Baba cewar Mairo ce ta dawo kuma ta faɗi ta suma.
zuciyar Adawiyya ta wani tarwatse in to atoms, gaba ɗaya ji ta ke duniyarta ta gama rikicewa, tayi wani duhu tayi baƙiƙƙirin, ba haka taso ba, sam ba haka taso ba, taso ace tabi bayan uwarta, dan a yanzu abin da ta ke ji game da Mairo yafi ƙarfin ta kira shi da haushi ko kishi, baƙin ciki ne tsurarsa da kuma zallar ƙiyayya.
amma ko a yanzu ma gani ta ke kamar fatanta zai cika, tunda nunfashi kawai ta ke babu motsi kuma idanuwa a rufe, bin ƙirjin Mairon ta ke da ido ta yanda yake nuna fitar numfashinta da sauri-sauri, acikin tunaninta lissafin yanda zata ga bayan Mairo da gaske take, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta ba zata taɓa bari Mairo tafi ta ba, ta tabbata yanda ta fita komai a yanzu to samari zasu daina tururuwar da suke akanta su koma kan Mairon. Suhail ɗin da ta gama mallake zuciyarsa da asiri?, Masarautar da ta ƙwallafa ran shigarta a matsayin sirika!...tai saurin girgiza kai, sam bata shirya rasa abubuwan da ta ƙwallafa rai akai ba, kaf tsarinta babu lissafin cewa Mairo zata fita da koma menene a duniyar nan, ita zata kasance a sama Mairo kuma a ƙasa a ko da yaushe. sai gashi tun ba'aje ko'ina ba lissafin nata na neman tarwatsewa, ta rumtse ido tare da cizon leɓenta na ƙasa tana girgiza kai.
"Baba nah". muryar Mairo da ta fito cikin shashsheƙar kuka ta gifta acikin tunaninta, ta baro daga waccen duniyar gaibun da ta shiga ta dawo duniyar zahiri.
"Alhamdulillah, Sannu Mairo". Baba yace dani yana mai dubana da idanun tausayawa, na lura so yake ya goge ƙwallar da ke neman sakko mishi acikin dabara amma ya kasa saboda tsaresa da idon da nayi, kuma yay ƙasa da kansa kamin ya yunƙura ya miƙe yana me cewa da Adawiyya,"ki kama hannunta ku shiga cikin gida". kafin na ƙara cewa wani abu ya bar wurin, Adawiyya kuma ta rungumeni da sautin kukan da ke ƙara karyar da zuciyata, ni dai na zama kamar gunki, bana ko motsi illa bin bayan Baba da nayi da ido har ya ƙarasa cikin rumfar da ake zama, ta tsakankanin mutanen da ke miƙo masa hannu su na musabaha na ƙara shaida ehh da gaske rayuwarta ta sauya daga ranar yau, don yanda bakinsa ke fitar da amsar kalmomin ta'aziyyar ko na nesa da shi can zai fahimci me bakinsa ke furtawa balle kuma ni da nake kusa-kusa da shi, don haka a lokacin na gama yarda da gaske na rasa Gwaggona, mutuwar nan dai da ke raba tsakanin ɗa da mahaifa ta rabani da uwata da duk duniyar nan bani da tamkarta.
tunanina da hangena ya tafi akan ta ya zan shiga gidan na tarar da cewar yanzu fa babu rayuwar Gwaggona a ciki?, ta ya zan zauna acikinsa babu mahaifiyata?, ta ya zan ci gaba da rayuwa a cikinsa babu wannan jarumar macen da idan ta ɗaga hannunta ga ubangiji kamin ta roƙawa kanta ta roƙa min?, ta ya zan rayu a cikinsa babu wannan gwarzuwar macen da ta sadaukar da lokacinta, jininta, jikinta, ƙarfinta, zuciyarta tun daga ranar da na zo duniyar har girmana?, ta ya zan rayu a cikin gidan babu Mahaifiyata abar ƙaunata da bata iya kai abinci bakinta sai ina cikin gidan?, ta ya zan iya rayuwa a cikin gidan babu wannan jajirtacciyar macen da bata samun nutsuwa a duk san da bana cikin gidan?, ta ya zan rayu acikin gidanmu babu Gwaggona, babu Gwaggona da ke hana idanuwanta bacci daga san da na fara rashin lafiya har zuwa samun sauƙina?. take naji ƙwaƙwalwata na karanto min kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un acikin raina.
maganar Adawiyya da ke fita cikin matsanancin sheshsheƙar kuka ta gifto ta cikin tunanina.
"ki tashi mu shiga Mairo...har yanzu ba'a kai Gwaggo ba amma nasan an gama shiryata, ki tashi muje kuyi sallama da ita, tun da ciwonta ya tsananta ke ta ke ta kira har numfashinta ya tsaya". kukan da ya ci ƙarfinta kuma yasa tai shiru, kamin ta ƙanƙameni sose cikin sautin da ya fi wancan shiga jikina tace,"Mairo ba ki ga komai bane, har yanzu ba ki shiga ko'ina a tashin hankali balle har ki nutse acikinsa, akan gaɓa kawai kike, tashin hankali naga lokacin da kika ɗora idonki akan gawar Gwaggo da babu ƙafa ɗaya". nayi wata zaburar da na kasa sarrafa kaina a wajen miƙewa da jin wannan furucin nata, kamar na jefa ma ta tambayar da ke raina ne sai naji ta bani amsa,"ciwonta da yay tsanani sai da aka yanke ma ta ƙafa saboda kullum kuka ta ke yi da ƙafar, kuma shikenan daga wannan lokacin, daga wannan lokacin muka rasata Mairo, wayyo Allahnmu"...
me zan bari ta ƙarasa faɗa min?, babu! ai na tashi na ƙarasa cikin gidan shi yafi min, inje idanuwana su gasgata min abin da har yanzu na ke tantama akansa, dan ba zan gama yarda da cewar Gwaggona ta mutu ba sai naga gawarta da idona.
tsoro nake ji da gaske, tsoro nake ji na shiga gida naga gawar Gwaggona, tsoro nake ji na shiga gidanmu naga babu wannan fuskar da ke tarbata da murmushi a duk san da na fita waje na dawo. jan ƙafafuna nake da suka min nauyi na kasa ɗagasu, jina nake tamkar wadda ta faɗo daga wata sama me nisa. kuma tun da na shigo gida ko'ina a jikina sai ya shiga rawa, yayinda nake bin ɗimbin mutanen da ke cike a tsakar gidanmu, wasu na kuka wasu kuma sun zabga tagumi cikin jimami, idona bai ƙara sauka akan kowa ba sai Basma da ke tsakiyar yayyun Gwaggo su na lallashinta da ba ta haƙuri, ita kuma ihu kawai ta ke tana kukan da ke tsuma zuciyar duk wani me saurarensa.
"Basma ga Mairo ta dawo". Adawiyya ce ke faɗa ma ta hakan, don haka bata san ta yanda akai ta fizge daga hannun Anty Saude ba tayo kaina da gudu. "Yaya". sunan nawa kawai ta iya faɗa tayi shiru muka rungume juna, ita kuka ta ke da sauti, ni kuma kukan nake babu sauti sai tsiyayar ruwan hawaye kawai. "Basma da gaske ne rayuwarmu ta gama rushewa gaba ɗaya? da gaske ne mun zama marayu?". muryata ta fito cikin rishin kuka da kakkaryewar kowanne harafi. ta gyaɗa min kai tana cewa,"Yaya shikenan bamu da uwa, Gwaggonmu ta mutu ta barmu Yaya. dan Allah kije kice ma ta ta tashi ke nasan zata ji maganarki, tun ɗazu inata cewa ta tashi za ki dawo amma taƙi jina, ta tausayawa maraicin da zamu shiga idan babu ita, wannan kulawar tata Yaya, wannan adu'artata, wannan soyayyartata Yaya duk mun rasa su".
na janyeta daga jikina na kama hannunta mu kai ɗakin Gwaggonmu, da dukan fatana na duniya zanje naga akasin abunda nake ta ji tun ɗazu, muna zuwa ƙofar ɗakin naji ƙafafuna sun riƙe saboda kukan da nake ji na tashi acikin ɗakin, Hajiya Laraba wadda take kaka a wurin Yayar Babar Gwaggo ita ke faɗin,"haɗuwarmu ta ƙarshe da ita ranar da taje gidan Inuwa take shaida masa Mairo na fama da ciwon ido kuma halin da suke ciki sai du'ai, ƙila ma har aiki sai anyi ma ta".
sai na yaye labulen ɗakin a hankali ina kallonsu, gaba ɗaya cikin ɗakin ƴan'uwan Gwaggona ne sai Inna Amarya da ke can gefe tana nata kuka, idanuwana kuma suka sauka akan gawar Gwaggo da ke a tsakiya an lulluɓeta da wani sabon zanin atamfarta da Wansu yay musu kyauta da sallah ta ɓoye tace insha'Allahu sai bikina zata ɗinka tunda atamfar me tsada ce. wata tsohuwa ƙawar Yagana ta yaye zanin daga fuskarta tana cewa,"Allah sarki kinga har yanzu annurin fuskarta bai gushe ba". Yagana ta rushe da kuka, ni kuma idanuwana suka kasa karɓar Gwaggona da suke gani a matsayin gawa, gangar jikina kuma nema take taƙi amsar mutuwar Gwaggo gaskiya ce. jiri ya kwasheni nayi tangal tangal zan faɗi akai saurin riƙoni, Kulu ce wadda sam ban lura da zamanta ba a bakin ƙofar ɗakin, idanuwanta da farar fatar nan tata sunyi jawur wadda zasu tabbatar maka da taci kuka ne ta ƙoshi, kuma tana cikin yinsa. ta kama ni ta shigar dani ɗakin na duƙe a gaban gawar da har yanzu nake ganin kamar mafarki nake, a yanzu kam idanuwana sun ƙafe, hawayena ya bushe, na kai hannu na yaye duka zanin da ke rufe a jikin Gwaggona, anan na tabbatar da abin da Adawiyya ke faɗa min, ƙwarai ƙafar Gwaggona ta dama ta zama rabi, domin tun daga gwiwarta zuwa ƙasa babu, jikina kuma sai ya mutu gaba ɗaya, Baba Lami ta matso ta ɓanɓare zanin da nake damƙe da shi a hannu ta mayar ta rufe Gwaggona, Yaya Jummai(ƙanwar Gwaggo) kuma tazo ta janyemu gefe ni da Kulu, wacce ke riƙe da ɗaya hannuna tai masa wata damƙa, sai dai inaa, fizgewa nayi daga hannun nata naja ɗuwawu na koma gaban gawar na kamo hannun Gwaggona na riƙe gam, abu ɗaya kawai na sani shi ne babu wani mahaluƙi da ya isa ya fitar da gawar Gwaggona daga gidan nan, cikin ɗakin nan, babu shi, babu kuma wanda ya isa ya raba hannuna da nata, sai dai idan ita mutuwar ce zata zo ta ɗaukeni nima.
ina jiyo Baba Lami na cewa da Kulu,"kiyi haƙuri ki daina kuka, domin ba shi da wani amfani, mutuwa ce Suwaiba tayi kuma kukan ba zai dawo da ita ba, illa ma ya ƙara dagula zuciya da raunana imaninta...dan haka mu bawa zuciyoyi haƙuri mu bita da adu'a ita tafi buƙata a halin yanzu".
ta ke zuciyata ta kuma karyewa, sai kuma murya Baba Mujibu ta shiga kunnena a san da ya ɗaga labule yana faɗin, "Amadu shigo da makarar". jinsu kawai nake, babu wanda idona ke kansa, so kawai nake naga me ƙarfin halin da zai iya zuwa ya ɗauki Gwaggona ya sakata a cikin makarar har yace zai ɗauka. na rantsewa kaina sai dai idan nima numfashin na daina sannan ne za'a iya fita da gawarta daga ɗakin nan, amma ba ina raye ba kuma a kusa da ita.
Baba ya shigo ya tsuguna a gefen kanta, da wata iriyar raunanniyar murya yake faɗin,"Suwaiba na yafe miki, Allah ya yafe miki, halinki na gari ya biki, yasa mutuwa ta zama hutu a gareki, haƙiƙa ke ƴar aljannah ce Suwaiba". sai kuma yay shiru yasa tafukansa ya rufe fuskarsa saboda kukan da ya ci ƙarfinsa. a sannan na kurma wata ƙara da ta cika gidan gaba ɗaya, ba komai ya haddasa hakan ba sai ganin Baba Mujibu da Ya Amadu sun kama Gwaggona sun sakata a cikin makara sun ɗauka za su fita da ita, ban san taya akai suka cire hannuna daga nata ba. inaji ina gani suka fice min da uwata daga ɗakin, su na ikirarin wai zasu kaita wani gidan wanda yake shi ne gidanta na gaskiya. nai wani kukan kura na warce daga riƙon da Anty Jummai tai min nabi bayansu da gudu na danƙo bayan rigar Baba Mujibu, kuka nake ina roƙonsa da dasashshiyar muryata akan,"dan girman Allah Baba Mujibu karka rabani da Gwaggona, ka tausaya min ku ajiye min ita, na yarda na amince ta mutu amma dan darajar Allah ku bar min gawarta na dinga gani ina rage raɗaɗin zafin rasata". gunjin kukana da na Basma dana Kulu ne kawai ke tashi acikin gidan, Inna Zulai ce kawai tayi ƙarfin halin iya zuwa ta janyeni sannan suka iya samun damar fita da gawarta. _"Mairo ina sonki, a duk duniya bayan iyayena duk wani bawa ko wani abu da nake so to ya biyo bayanki, dan Allah ki rage zafin rai kinji, ki koyi haƙuri, ki zama me haƙuri da tawassali a rayuwarki, kuma a duk wani hali da za ki shiga na tsanani a rayuwarki ki riƙe Allah...saboda haka ki bar kuka dan Babanku ya siyawa Adawiyya da Sadiya kaya babu ke, tun da kika ga yayi haka ba shi da kuɗinne, kiyi haƙuri kinji ko, zan ɗauki waccen kwallar tawa na siyar na cika da kuɗin gurina kema na siyo miki kayan da za ki fitar suna da su, kema ba za'a barki a baya ba, muddin ina raye Mairo ba zan taɓa bari ki koka akan wani abu ba, sai dai idan ta Allah ce ta kasance dani, ko kuma nayi iya fafutukar samu na rasa"._ wannan maganar ta Gwaggo a can kwanakin baya ita ta haska a cikin kaina, kuma daga wannan kallon da na yiwa ƙofa naga shigowar Ya Aminu yana ajiye buta yana faɗin,"ehh har anyi ma ta sallah ma gasu can sun tafi". daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti.
*Assalamu Alaikum*
jama'a na tallatamuku hajarmu ta online/offline business ɗina wanda zan ringa sayar muku da data ta mtn a sassauƙan farashi Kamar haka*
*I sell MTN data with this cheap price:*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo also available.*
*Whatsapp OR
Call 08066268951*
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*29)*
nabi ɗakin asibitin da nake ciki a kwance da kallo ɗaya, kafin na haɗe murfin idona na maida na rufe, wasu tafasassun hawaye kuma suka shiga bi ta gefen idona, a yayin da hoton lokacin da aka ɗauki gawar Gwaggona aka fita da ita ya shiga haskawa a idanuna, maganar Baba Mujibu da ke faɗin an tafi kaita itama ta kutso cikin hoton, na buɗe idanuna a zabure na saukesu akan Basma da ke gefena a zaune, tana goge hawayen fuskarta a hankali.
zuciya da ruhi suka ƙara tabbatar min da Gwaggona ta rasu, kuma ni da Basma mun zama marayu, bamu da kowa sai Baba. na mayar da idona na rufe ina ambaton kalamar innalillahi wa'inna ilahi raji'un, faɗa nake ina ƙara maimaita yayin da zuciyata kuma ke min wani irin zafi. kafin can kuma naji shigar wani sanyayyan ƙamshin turare acikin hancina, sannan wani sanyayyan hannu me taushi ya shiga cikin nawa, ban dai buɗe idon nawa ba, sai zuciyata da ke bugawa fat fat.
"musulmi na ƙwarai me cikakken imani shi ne wanda ya yarda da Allah ɗaya ne, me bayarwa kuma ya karɓa, wanda ke yin dukkan yanda yaso akan bayinsa, a gare shi muke kuma gare shi zamu koma, gaba ɗayanmu da muke rayuwa cikin ƙunci ko jin daɗi cikin jiran mutuwa muke...saboda haka kiyi haƙuri, ki zama me tawassali ki zama me dangana, ki kuma bi Gwaggo da adu'a domin ita tafi buƙata daga gareki, ba wannan kukan ba, yanzu ne lokacin da za ki nunawa Gwaggonki ƙaunar na kike ikirarin kina ma ta da gaske, ta hanyar yi ma ta adu'a da roƙa ma ta gafarar ubangiji". muryar nan me zurfi da kauri ta shiga kunnena da wannan tausasan kalaman nasihar tasa, muryar nan ta Ya Kabiruna da ko mutuwa nayi na dawo zan shaidata, ada ina jin kamar Baba ne kawai ya rage min, ashe ina da Ya Kabiru wanda nasan duk tsanani yana tare dani, duk da ban kalle shi ba amma shi ma nasan kukan yake yi ƙarfin hali da dakiya kawai yake yana faɗin wannan maganar.
na buɗe baki cikin murya da ke harɗewa da kuka nace,"Ya Kabiru kaga Gwaggona ta tafi ta barni ko, Mahaifiyata me tsananin so na, me kowa me komai ya amsa abarsa, shikenan yanzu bani da Uwa sai dai na kalli ta wasu". idona a rufe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 52