su ke nayi maganar, a jikina naji san da yasa hannu ya goge hawayensa sannan yace da ni. "ban isa na hanaki kuka ba domin nima haka nayi a san da na rasa tawa mahaifiyar, amma zan roƙeki da Allah da Annabi karki ƙara min magana da wannan sautin idan har ba so kike zuciyata ta tarwatse ba, kukanki na kar ya zuciyata, yana raunanata, bana son kukanki Mairo, bana sonsa ko kaɗan...". ya damƙe hannuna da ke cikin nasa, ni kuma na buɗe idanuwana na yunƙura na miƙe zaune, na samu na tsayar da hawayena tukunna na tsayar da idona akansa, cikin ƙwayar idonsa, kan fuskarsa, akansa da girmansa da cikar haibarsa suka cika min ido.
gaba ɗaya ya sauya kamar ba shi ba, kamar ba Ya Kabiruna, ya ƙara yin kyau dan hasken har cika min ido yake, yanayin tashin hankalin da nake ciki ne kawai zai hanani fassara abin da nakeji a ga me da shi. shi ma ɗin tun a sanda na ɗora idona a nasa ni yake kallo, ban san me yake tunani ba, amma kallon da yake min kallo ne na kamar wanda yaga sabuwar halitta a gabansa. na sauke kaina ƙasa ina motsa yatsun hannuna, murya a hankali nace,"kuma mutuwar bata tashi ɗaukanta ba sai a san da na dawo, ko ta bari mu gana da ita tsawon lokaci bama tare, ai da saita bari muyi sallama". magana nake cikin ƙarfin halin riƙe kukan da ke neman kubce min.
a tunaninta ya san komai, bata san daga ɓatan nata har ciwon Gwaggon duk bai sani ba, mutuwar ma banda ya kira Kulu yaji tana kuka ba zai sani ba, ba wai kuma dan ta sanar masa ba, a jikinsa yaji wannan kukan nata da kuma jiyo hayaniya ta cikin wayar ya tabbatar masa da babu lafiya, hakan yasa ba shiri ya yanki ticket ya taho, kuma da zuwansa tun a hanya aka shaida masa Gwaggo ta mutu, kuma a cikin gida da ya shigo yake jin su na batun ciwon nata wai har da ƙafa ma saida aka yanke ma ta saboda wani ruwa me wari da ke fitowa, Adawiyya kuma ta tare shi da albishir ɗin wai Mairo ta dawo, ta dawo daga ina?, alokaci ɗaya yaywa zuciyarsa da ita Adawiyyan tambayar mamaki kwance a fuskarsa, sai yaji tana sanar masa da abin da zuciyarsa da gangar jikinsa suka kasa ɗauka, har sai da ya sami tabbacin hakan daga bakin Amarya kafin ya yarda ya amince da abin da ya faru kamar a mafarki.
kuma wai Inna Amarya faɗa masa ta ke sun ɓoye masa ne gudun kar ya shiga tashin hankali acan har yace zai taho, Mutuwar Gwaggo ta da ke shi, amma ɓatan Mairo ya shafe kaso 99 na cikin dukan, banda ana cikin jimamin mutuwa da babu abin da zai hana shi zazzagin Amadu inta kama ma harda duka ya haɗa masa, Allah ne da kullum sai sunyi waya da shi amma bai taɓa nuna masa da alamar wata matsala da ke faruwa acikin gidan ba, ɓatan ɗan Mutum! ɓatan ma kuma na Maironsa!, kuma kowa yake rayuwa hankali kwance, sam shi baima yarda da batunsu na cewar har hukuma ma tayi iya nata wajen binciken nemanta ba, ya ƙaryata hakan, ya ƙaryata hakan daga bakin Amadu da ya kusa kaiwa naushi a san da yake rantse masa, har a ƙarshe suka fusata dukansu.
kafin ya taho asibitin sai da yaywa Sadiya da Ƙawarta dukan mutuwa, yaji su ne san da suke tattaunawar wai Mairo da kanta ta ɓata ba saceta akayi ba, yawon iskanci ta tafi, Adawiyya ta karɓe zancen nasu da cewar,"nima haka nake zato dan duk wanda ya kalli Mairo sai ya zargi wani abu dan batayi kama da wadda ta ɓata ba, ai wanda ya ɓace a firgice yake dawowa ,kun tuna Sahura ƙanwar su Zailani?, ita ai kamarma haukacewa tayi, amma ita fa ras da ita, na rantse ma aka bibiya ciki gareta dan irin wannan hasken da tai bana lafiya bane, dana rungumeta ma wani irin wari na dinƙa ji irin na gidan karuwai". shirunta ya haɗe da naushin da Kabiru ya baiwa bakinta har sai da haƙori ɗaya ya fara lilo, bai yi wata wata ba ya shiga fatali da su gaba ɗaya, ƙwallo yake da Adawiyya tun daga Zaure har cikin tsakar gida, da ƙyar aka ƙwacesu daga hannunsa, babu yanda ba'ai ba ya faɗi me suka aikata ba yace su tsumayi dawowarsa bai gama da su ba.
ya cije laɓensa na ƙasa da ƙarfi, tsakanin Amadu da Kulu wa ya kamata yafi jin haushi ne?, ya wani jijjiga kai a hankali kafin ya ɗago ya dubeta yace,"ina yi mana ta'aziyya". na amsa masa da kai kawai, shiru kuma ya gimla, kafin wucewar wasu daƙiƙu na ƙara cewa da shi,"ya akai nazo nan?". ya bani amsa da, "nima san da na dawo akace an kawo ki asibiti, kin yi dogon suma ana tsoron ma Allah sa ba haɗiyar zuciya kika yi ba...Hajiya Hinde tana daga waje, taje alwala". nai wani guntun murmushin da ya tsaya iyaka laɓɓana, zanso ace haɗiyar zuciyar nai nabi bayan Gwaggona, dan gani nake kamar ba zan iya wannan rayuwar babu ita ba, gani nake a yanzu duniyata zata sauya ne ta shiga cikin tsananin ƙunci, gani nake kamar wani babban al'amari me cike da ruɗani na shirin tunkaro ni, gani nake tamkar watan zubar da hawayena ne ya tsaya, ji nake kaman na rasa dukkan gatana.
a wannan daren ƙarfe goma saura muka koma gida, na shigo ciki bayan munyi sallama da Ya Kabiru, Hajiya Hinde na biye damu, muka ratsa ta cunkoson matan da har yanzu basu ragu ba, kaman gidan da ake shirin yin biki, dan ƴan'uwan Gwaggo da Ƴan'uwa Baba yawancinsu duk sun hallara, haka ma ƴan'uwan Inna Amarya ƙwansu da kwarkwatarsu. idanun kowa akanmu cike da tausayawa muka shige ɗakin Gwaggo, tunda na shiga sai mutuwar tata ta dawo min sabuwa, Gwaggona yau ta wuni a makwancinta sai mu kaɗai zamu ci gaba da rayuwa a wannan ɗakin, na ƙyalla idona kan gadonta, idanuna ita suke hasko min a kwance tana baccin nan nata wanda da safe ne kaɗai ta ke samun damar yinsa, dan raya dare ta ke tana ibada bata bacci, idan da rana nace ta kwanta ta huta sai tace min a'a, ai ba zata iya baccin da nutsuwa ba, hankalinta akaina yake.
na ƙarasa ƙafafuna na rawa na ɗauki filonta da zanin rufarta na rungume a ƙirjina, wani sabon hawaye na daban masu ɗumin gaske suka shiga malalo min, a yanzu kam na gama tabbatarwa Gwaggo tayi mana nisan zango.
ban san da shigowar wani cikin ɗakin ba, sai ji nai Inna Amarya ta kamoni ta miƙar dani tsaye, wacce sam na manta da ita, itama idanunta sun kaɗa sunyi jazur da alama har yanzu ita ma kukan nata bai gama tsayawa ba. "kije Babanku na kiranki". ta faɗa tana kama hannuna muka nufa ƙofa, har lokacin ban ajiye filo da zanin rufar Gwaggo ba, a tsakar gida muka same shi inda yake cewa a wuce damu ɗakinsa mu kwana acan, shi kansa Baban tausayinsa nake ji, dan yana tsananin son matarsa, amma a yau mutuwar nan da bata barin wani dan wani yaji daɗi ta raba shi da matarsa kamar yanda ta rabamu da ita.
na juya na riƙo hannun Basma ƴar'uwata da idan na kalleta nake jin zuciyata ta kuma tsinkewa da tausayin kanmu a dalilin rashin mahaifiyarmu. Mama Hadiza ita ta zauna damu a ɗakin tana ta lallashinmu da bamu haƙuri, kowa yazo ce min yake na daina yi ma ta kuka nayi ma ta adu'a, kuma duk yanda naso na tsayar da kukan saina ji wani sabo ya ƙara tahowa, Basma ma harta fini haƙuri da dangana, dan ita zuwa yanzu ta bar yin kukan sai ma idan taga inayi ne ta ke tausata.
Baba ya dawo ɗakin ya tasamu a gaba muka ci abinci, dan kowa nata fama damu muci abinci munƙi ci, haka na dinƙa tura abincin babu wani ɗanɗano, sai da ya tabbatar munci da yawa sannan ya ƙyalemu yace zai tafi gidan Yagana a can zasu kwana su da ƴan'uwan Gwaggo na nesa da suka zo, mu tashi cikin dare muyi sallah muyi ma ta adu'a da samun dacewa da Rahma ubangiji, duk da cewar shi ba ya kokoton Suwaiba ƴar aljannah ce, muka amsa masa da to, bayan fitarsa babu jimawa sai ga Kulu ta shigo, ta shiga tsakiyarmu ta zauna sannan ta kwanto da kanmu jikin kafaɗunta, kusan kowa na gidan yayi bacci a lokacin.
ita ma da tata dasashshiyar muryar da ta sha kuka ta ƙoshi ta ke ce mana, "ba ku kaɗai aka yiwa mutuwa ba har da ni, nima na rasa ƴar'uwar da ta fi min ƴan'uwana da suka kasa riƙeni a lokacin da na shiga cikin tsanani, haƙiƙa ba zan taɓa mantawa da alkhairin Gwaggonku a gareni ba, saboda haka ina mana ta'aziyya gabaki ɗayanmu...sannnan kar ku taɓa saka cewa a ranku rashinta zai sa ku zama marayu, kuna dani, zan maye muku gurbin Gwaggonku, zan tsaya tsayin daka wajen ganin cewar na zame muku Uwa ta gari, zan kwantanta kamar yanda Gwaggonku ta ke dan nasan ba zan taɓa zama irinta ba gaba ɗaya ba, domin ita ta dabance". ta shafo kaina tana ɗago da fuskata na dubeta, bata taɓa kiran sunana ba, kuma ko a yanzuma da yanayinta suka nuna maganar da za tayi tawa ce shi ma bata faɗi sunana ba, illa iyaka kafeni da ido da tayi masu cike da tarin ruwan hawaye acikinsu tace,"Gwaggonki har ta rasu sunanki ta ke ta ambata, tana binki da tarin adu'oin da baki bai isa ya faɗi adadinsu ba, har numfashinta ya ɗauke faɗa ta ke Allah yayiwa rayuwarki albarka, Allah ubangiji ya shiga dukkan lamuranki, Allah ya dafa miki, ya tsareki daga dukkan sharrin masu sharri, ubangiji yasa kiyi kyakykyawan ƙarshe, ubangiji ya bayyanaki cikin amincinsa ya dawo da ke gida...adu'ar da ta dinƙa yi muku kenan kafin yankewar numfashinta, saboda haka ku sha re hawayenku Gwaggo bata cancanci mu dinga yi ma ta kuka ba, fa ce mu bita da tarin adu'oin da ke cikin kanmu".
ta ƙarasa maganar harafan bakinta na karyewa, tana saka hannu wajen share mana hawaye, amma inaa nawa sai suka ƙi tsayawa, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina na kuma fashewa da sabon kukan da nake yi babu ƙaƙƙautawa, domin har yanzu na kasa amincewa raina Gwaggona ta rasu, komai ganinsa nake kamar a mafarki, Kulu haƙuri ta ke ta bani da dukkan wasu kalamai da ta san zasu sa zuciyata tayi sanyi, da karatun alƙur'anin da ta kama a bakinta cikin ƙira'arta me daɗin sauraro, da wannane bacci ɓarawo ya saceni.
Kulu kam wannan daren ba ta yi bacci ba, Basma da Mairo na kwance akan cinyoyinta, tausayinta kanta da su na sukar kowanne lungu da saƙo na zuciyarta, tana mai taraddadin abin da zai iya faruwa bayan gama zaman makokin Gwaggo. a lokacinne ƙwaƙwalwarta ta shiga tariyo ma ta da zantukan da suka shafe yinin dare su na yi da Gwaggon kamin ta rasu, ganin ciwonta ya tsananta tana ta faɗa ma ta cewar ita ta tabbata lokacinta yayi mutuwa tunkararta ta ke, kuma Gwaggon ta roƙeta akan ta faɗa ma ta asalinta wanda tun haɗuwarsu bata taɓa tambayarta ba.
a sannan ta kwashe dukkan tarihin rayuwarta da na ahalinta ta bayyanawa Gwaggon, ta shaida ma ta abin da bata sani ba na cewar Kabiru ya san komai, Gwaggon tayi mamaki da jin hakan, don duk da cewar da ƙyar ta ke iya magana hakan bai sa muryarta ta fito tar ba a sanda ta tambayeta,"ya akayi Kabiru ya san komai Hauwa'u?". "Yaya akwai ranar da muke ɗakin Malam ni da ke muna tattaunawa akan yanda za'ai na koma cikin ahalina, ku kuma kuci gaba da riƙe Mairo, to da na fito lokacin na tarar da Kabiru a tsaye wanda ya fito daga banɗaki, yanayinsa kuma ya tabbatar min da ya ji dukkan zancen da muke, shi yasa ko a lokacin dana ji cewar zai wuce karatu can ethiopia nasa shi bincika min yanda labarina ya ke yanzu a cikin ahalina...kuma Yaya ita kanta Hussaina ta san da ina yin magana". Gwaggo ta dubeta a firgice da ɗunbin mamaki, mamaki me haɗe da tsoron da ya fallasa firgitar da zuciyarta tayi, ta zabura ta yunƙura zata miƙe amma ta kasa saboda tsananin azabar ciwon da ƙafarta keyi ma ta. tashin hankali a muryata tace da ita,"ya akai Maryam ta san kina magana?, ta ya ya Hauwa?, duk ta yanda naso na ɓoye komai ashe ke kin kasa wannan dauriyar da kika ce min za ki iya". Kulun ta shiga girgiza ma ta kai tana faɗin,"wallahi ba haka bane Yaya, kamawa tayi yasa dolen nayi ma ta magana a lokacin...saboda na tsinci agogon da na san a masarautarmu ne kaɗai ake sa shi, ko da na tambayeta sai ta ke shaida min Suhail ne ya bata, shi yasa na buɗi baki na zaburar da ita akan tai sauri ta dawo, idan mu'amalarta da shi tai nisa zai iya ganowa cewa ita jininmu ce, idanunsa na ƙyallawa kan azurfar hannunta shikenan komai ya bayyana, ni kuma ban shiryawa su san cewa har yanzu ina ƙasar nan ba, dan bana fata ko da gawata ta ƙara shiga masarautar bichi, kuma bana fatan na ƙara yin ido huɗu da Didi, duk da cewar ita ɗin Ƴar'uwata ce, amma ta kasa karɓar ƙaddarar da ta shato mana layi ni da Hassana muka biyota ta kawomu cikin ƙasar nan".
"to amma dai ba kiyi wata maganar da zata fahimtar da ita Sirrin da ake Ɓoye ma ta ba ko?, Hauwa koma dai kece silar barinta gidan nanne? domin yanzu zuciyata ta fara kokonta akan lamarinki?, in har za ki ce min Maryam ta san kina magana to ban san iya tsawon adadin lokutan da ku ka shafe kuna hira ba". Kulu ta zuƙi wani nunfashi kan tace,"a'a Yaya wallahi bata san komai ba, bamu ma taɓa yin doguwar hira da ita ba". Gwaggon ta rumtse idanunta hawaye na silalowa a kumatunta. "ni dama wannan hukuncin da muka yanke na san babu inda zai je muddin muna rayuwa a doron ƙasa, kuma muddin kina kusa da ƴarki, dole wataran gaskiya saita bayyana, ba za ki iya ci gaba da jurewa ba har ƙarshen rayuwa, dole sai kin fallasa ma ta ke ɗin ke kika haifeta, kamar yanda bamu isa mu binne gaskiya ba muce zamu fito da ƙarya...ko ajiya nayi mafarkin Maryam na kan hanyar dawowarta, kuma ajikina ina jin mafarkina zai zama gaskiya. Alhamdulillahi na godewa Allah da zai kansace bana raye Maryam zata san gaskiyar komai, na kuma gode masa da sai bayan raina zata san da cewar bani na haifeta ba, na gode masa da sai bayan raina ne zata ɗanɗani wannan baƙin ciki da takaicin rayuwarta, na kuma godewa Allah da yasa bana raye zata zubar da hawayen da babu me iya tsayar ma ta da shi...Allah na gode maka da zaka ɗauki numfashina a yanzu, Allah na gode maka da ba zaka barni naga hawayen Maryam ba, wannan hawayen da nake jinsu tamkar ɗigar dalma a jikina a duk sanda naga ƙwalla a idonta". muryatarta ta dakushe da matsanancin kukan da yaci ƙarfinta, taci gaba da faɗin,"ni nasan daga ranar da Maryam tasan komai ni kaina saita tsaneni, zata ji haushina, zata ji takaicina fiye da jin takaicin komai, ba don komai ba sai dan ƙunshe ma ta mahaifiya da nayi a wuri ɗaya na hanata raɓarta, har nake hantararta idan ta kusanceta, nake ma ta tsawa a duk sanda suka kasance da juna, na sani, na sani wallahi saita ji haushina...amma dan Allah dan Annabi Kulu ki faɗa ma ta karta ƙullaceni a ranta ta yafe min, ban raba tsakaninta da mahaifiyarta ba saboda biyan buƙatar kaina ba, nayi hakanne dan sama ma ta rayuwa me ƴanci, nayi hakanne dan bana so ta koka a rayuwa, shi yasa na maye gurbin mahaifiyarta Malam kuma ya maye gurbin Mahaifinta da ya ƙi amsarta a san da tazo duniya, domin daga lokacin da ta gane kece kika haifeta, Malam kuma ba shi ne mahaifinta ba, abin da zata fara tambayarki shi ne ina nata mahafin?, waccen amsa za mu bata?, amsar cewa mahaifinta yaƙi karɓarta ya gudu daga gareki shi ne abin da bama so ki sani...amma dan Allah dan Annabi ta yafe min, daidai da rana ɗaya ban taɓa jin cewa ita ɗin ba tawa bace". ta tsagaita da maganar sannan ta ɗauko wasu ɗan kunnen yari da sarƙa na daham ta damƙawa Kulu a hannu. "Hauwa wannan su ne kaɗai kadarar dana mallaka me tsada da daraja, yayin dana mutu Basma ita zata ci gadon komai nawa, to na bawa Maryam wannan halak malak, ki damƙa ma ta a hannunta kice tayi yanda taga dama da shi. kuma kema Kulu sai kinyi haƙuri da ita a san da ta san cewar kece mahaifiyarta, zata ɓauɗe ne ta juya zuwa asalin Maryam ɗinta da ta ke tun farko, Maryam ɗin da babu mahaluƙin da ke iya tausasar zuciyarta a san da ta ke tafarfasa, sai kinyi haƙuri da dukkannin abin da zata aiwatar". daga hakan kuma maganarta ta tsaya cak sai wata shaƙuwa da ta sarƙeta, a wannan daren suka wuce asibiti da ita saboda yanda ƙafarta ta kumbura kamar an hura balan balan, tana tsiyayar da wani irin ruwa me wari, ana zuwa asibitin akace sai an yanke ƙafar, ƴan'uwanta su suka harhaɗo kuɗi Baba ya siyar da rumfar da yake zuba itacensa aka haɗa kuɗi aka biya kuɗin akai ma ta aikin, dama tunda aka yanke tace ita a dawo da ita gida ta mutu a ɗakin aurenta, mutuwa zata yi rayuwarta ta ƙare.
a yau ɗin da aka sallamosu, lokacin da suka gama waya da Kabiru tana fitowa daga banɗaki ta jiyo salatin Yagana da Amarya kafin su fashe da kuka, ta ɗaga labule ta leƙa ɗakin ta tarar ashe Gwaggon ce ta rasu.
ta ke maganarsu ta ƙarshe da ita ta haska ma ta acikin kanta,"Hauwa ƙwarai kina da kyakykyawar zuciya, babu makawa ke ɗin ƴar aljannah ce, domin ba kowa ne zai iya yin sadaukarwar da kika yi ba, ashe ni ba komai nayi ba a cikin sadaukarwar da kike ikirarin nayi miki, lallai ke ɗin ta dabance, ubangiji ya faranta miki...idan Allah ya bayyana Maryam a duk san da gaskiyar da muke ɓoyewa ta bayyana ki faɗa ma ta, tayi haƙuri ta barwa Allah komai, Allah shi kaɗai yasan dalilin da yasa zanen ƙaddararta ya kasance a haka...kuma ki faɗa ma ta wasiyyata agareta ita ce ta ɗauki fansa akan mahaifinta, ko da Allah bai cika min burina akanta na zama lauya ba, tayi shari'a da shi, ta tozarta shi kamar yanda ya tozarta rayuwarku".
*Bayan Kwana Ashirin.*
"ni kuwa Jummai duka kayan Marigayiya ta haɗa ta tafi da su?, dan jiya naga kamar wani fallan atamfarta a kan gado". Yagana ce ke wannan maganar, ni da Adawiyya muna zaune muna fige kaji guda biyun da Baba Mujibu ya kawo aiwa Yagana ferfesu. a karo na biyu maganarta ta sa ke giftawa ta cikin shirun da nai zurfi aciki.
"ikon Allah da yawa yake, ni kuwa Mairo kamar da ke nake magana ko?". muryata a sanyaye nace ma ta,"Yagana ta gama ɗiba duka, waɗanda kika gani nawa ne na ɗauka". ta kuma cewa,"Ya rasulillahi, to ke me za ki yi dasu?, ina za ki kai kayan Suwaiba ajikinki Mairo duk da kin ciko ba kamar da ba, magana ta Allah ki fito da su a bayar sadaƙa ba a aje su mutu a banza ba". bance ma ta komai ba, dan yanzu ni magana sam ba ƙaunar yinta nake ba, Allah kaɗai yasan halin da nake ciki na irin faɗuwar gaban da nake yi a kullum, ga mutuwar uwata da bata sakeni ba.
ta kuma cewa,"ni kuwa gashi bana so ina yiwa mutum magana yay sautin mahaukaciya da ni, ke kuma gashi sararki ce Mairo, Kabiru ya goga miki fentin rashin kyautawar nan, alhalin ba abu me kyau bane kuke yi, ni wallah ma nayi zaton zaman gidan arnan ba surarki kawai ya sauya ba har da halinki, ashe hali na nan sai ma ƙara gaba gaba da yake, ko da yake dama me hali ba ya fasa halinsa". Adawiyya tace da ita,"Yagana ke kuma gaki da magana, ki barta taji da abin da ke damunta, Uwarta ce fa rasu amma kinbi kin kwazazzafeta. kaya idan ta ɗauka mene aciki, ba kayan Babarta bane, su zata dinga gani suna ɗebe ma ta kewa".
tace da ita,"uwar sawa da iyawa ai ba da ke nai magana ba, dan haka ki rufe min baki...kuma da kin gama aikin ki miƙe ki tafi gidanku dan ba nemanki nake ba, inaji jiya Uwarki na faɗin wai na riƙeki ina hanaki zuwa ki tayata aiki, da yake ita bata da godiyar Allah, duk sauran ƴaƴan da ke gabanta suke ma ta hidamar basu isheta ba sai ke ɗaya da ike wurina kike zuwa ita kuma ba ƙaunar hakan ta ke ba, to Allahn da yake sona ya dawo min da ɗiyar albarka, sai ta jiƙaki ta cinye".
daga dukkan alama Adawiyya ta ƙulu da maganartata, ni dai jinsu kawai nake, kafin na bata amsar da ta takura min da tambaya akai wai kayan Gwaggon har kala nawa na ɗiba.
"Yagana babu fa yawa, kala uku ne, sai wannan dungun atamfar da bata ɗinka ba Baba ya bamu kuɗi muka kaiwa Shamsiyya ta ɗinka mana ni da Basma". "to ai shikenan, su ma sai ki kai a rage miki ɗinkakkun tun da nasan sunyi miki yawa". "haka zan ke saka su ba sai na rage ba". "to hakan ma ba laifi ai tunda ke ba jin shawara kike ba, ita dai Allah ya jiƙanta...ke kuma ya sauya miki halin kafiyarki". na amsa da,"Amin".
ta kuma cewa,"shi Liman ɗin me yace a ga me da sallolin da suka bar kanki?". Ya Salam, na rasa kunnen Yagana wane irin kunne ne, da ace yanda bakinta ke da magana haka kunnenta ke da ji da magana ɗaya ta gamsar ba sai ka ƙara ba. a gabanta fa Liman yace,"Ai a Musulunci an ɗauke alƙalamin rubuta lada ko zunubi ga mutane 3. 1- Yaro sai ya balaga. 2-Mai bacci har sai ya farka. 3-Da mahaukaci har sai ya warke.
Kuma shi irin wanda yay ciwona na mantuwa ana sanya irinsu ne a fannin mahaukata tun da dai ba shi da hankali. Kuma duk abin da ya aikata na lada a yanayin ba za a rubuta masa ba, haka ma na zunubi ba za'a rubuta masa ba, Yana farkawa zai ɗora ne daga inda yabari a farko, duk abinda ya faru a tsakanin nan ba zai rama su ba". kuma a sanda yay shiru da bayanin nasa ita ta karɓe da Kabbara, amma yanzu tana ƙara tambayata ya akai.
tare da Adawiyya muka ɗora sanwar dahuwar kazar, dama tun bayan sadaƙar ukun Gwaggo na tattaro kayana na dawo gidan Yagana, dan bana jin zan iya ci gaba da zaman gidan duk da cewar akwai Inna Amarya, gidan gaba ɗaya ba daɗinsa nake ji ba, saboda Basma ma tabi bayan su Anty Ma'u gidan da ta ke zaune a can kano, Ya Kabiru ma kuma yana ikirarin zai koma a sati na gaba, su Adawiyya ma komawa zasu yi dan hutunsu ya ƙare, ni kuma Ya Amadu yace ba zan bisu ba na zauna anan za'a nema min wata private school ɗin naci gaba da zuwa, Ya Kabiru yace kuɗin makaranta ko ya kai dubu ɗari ne akaini zai biya, tun da har yanzu duk ban manta da karatuna ba, komai yana kaina.
dan har yanzu ma hausar bakina kamar bata cikakkiyar bahaushiya ba, maganarmu da Ya Kabiru da Ya Amadu ma yanzu da turanci muke yi, hatta Kulu ma wadda nayi matuƙar mamakin hakan daga gareta, ta iya turanci sosai dan idan tana yi ma zaka rantse wata baturiyar ce, naso kuma nayi ma ta wasu tarin tambayoyi akanta da suka tarar min akai, to amma ba ayanzu ba, nafi so mu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 52