Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwali yana shafawa a hankali, a hankalin da yake haɗewa da sabon kukan da nake son fashewa da shi, a yanzu da nake lafe a jikinsa ƙamshinsa ya ƙara samun damar shiga hancina yana motsani da kyau, wannan ƙamshin dai guda ɗaya da jinsa ke saka zuciyata ta motsa. kakkausar muryarsa ta fito a hankali, sam bana son jin wannan kakkaurar muryar tasa da ko cikin bacci na jita zan shaidata, wannan muryar da ko mutuwa nayi na dawo ba zan taɓa manta mamallakinta ba, tana da tsiri a gareni sosai, irin tasirin da nake ji a gangar jikina da ƙwaƙwalwata gaba ɗaya. a tausashe muryar tasa ta fito ta ratsa cikin kunnuwana da ambaton sunana, furucin sunan nawa da ya fito cikin wani irin amon sauti, cikin wani irin salo da ya nemi kassara ɗan kuzarina. "Maryam Don Allah". sai kuma ya ƙara tsamkeni yana ci gaba da faɗin,"dan Allah ki daina bana so, bana sonsa Maryam, wannan kukan babu abinda yake haifarwa sai illata zuciyar da babu komai acikinta face sonki da ƙaunarki...". Ya Rabb! a wannan lokacin, babu abin da nake so illa na fito daga hannuwan da nake kewaye a cikinsu, sannan na buɗe idanuna da dukkan fatana na duniya naga akasin abun da nake ji. _____________________________________ *_the only way you people will show your love and appreciation towards me is by voting and commenting on this story. please don't exit any page without dropping a comment, it encourages me to do more._* [7/18, 15:55] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(51)* *washegari* *02:00pm.* akan ƙafafuna nake acikin turakar mai martaba, kaina a ƙasa cikin hular alkyabbar da aka saka min white colour, tunda aka wayi garin yau naji cewar za'a kaini gidana, zanje inda zan fara wata sabuwar rayuwar da ta ke daban da irin wacce nayi a baya, gidana, gidan aurena, shikenan jikina ya mutu gaba ɗaya, wani irin yanayi nake ji da bazan iya kimanta shi ba. a yanzu da nake a tsakiyar turakar mai martaba ina fuskantarsa shi da mahaifina, da Kakana na wajen Uwa da ya sauka a daren jiya, sai Ammi da Bella da Ummina da Mamina, da Hajjah Nashwa da Shamsiyya duk su na zaune, kuka nake amma mara sauti, hawaye wani na bin wani saman fuskata, yana ɓata ƙwalliyar da aka ɗauki tsawon lokaci a safiyar yau ana min ita, kwalliyar da Ummina ta kasa rufe baki tana ta aukin yabawa, faɗa ta ke wai ai Kwalliyar Kabirunta ce, Kabirunta za'a yiwa dan haka Mai Kwalliyar ta baje duka basirarta yau, tayi kwalliyar irin yanda nake sheƙi kaman dafaffan ƙwan da aka ɓare, ni dai ko a lokacin murmushi ma ban iya ba, saboda a cikin fargaba nake, faɗuwar gaban da ta riskeni tun a jiya da na fito daga wannan jikin da ya rungumeni, na buɗe ido nayi tozali da mutumin da tun a ƙamshinsa na gama shaida ko waye. a yanzu da Mai Martaba sarkin bichi yay shiru, Bella ta kada baki ita ma ta kira sunana, nayi shiru na kasa amsawa saboda ƙullutun da ke maƙale a throat ɗina, cikin wannan muryartata da ke fita da zallar izza da ƙasaita ta ƙara kiran sunana. "Maryam amsa min za kiyi". na buɗe baki na amsa kiran da muryata da ta gama disashewa da kuka. "Maryam Haƙuri, Haƙuri, zaman aure gaba ɗayansa haƙuri ne, Maryam haƙuri shi ne jigon zaman aure, sai da haƙuri aurenki zai yi lasting Maryam. dan haka Maryam idan ba ki san shi ba to ki nemo shi duk inda yake ki kamo shi, ki ƙanƙame shi, irin ƙanƙamar da ba zai taɓa suɓuce miki ba...haƙuri ba wani abu ne mai wahala ba, mutanene kawai ke ɗaukansa a matsayin kaya, amma muddin mutum ya riƙe haƙuri to tabbas darajarsa hauhawa za ta dinga yi, domin shi haƙuri arziƙi ne babba Allah ya nufe ka da samunsa, dan ba kowa Allah ke bawa ba sai kaɗan daga cikin bayinsa, da haƙuri da tawakkali haka suke". Hajjah Nashwa ta shiga maganar Bella da cewa,"to ai rayuwarma ita kanta haƙuri ce". Bella ta gyaɗa kai,"to dai...dan haka ni iyaka abinda zan daɗa jaddada maki kenan, dan tun jiya kike shan nasihohi a gidan nan". Ammi da naji shigowarta babu jima tace,"Maryam tun jiya nake ce miki ki zama mace ta gari, kuma ko kullu yaumin zanke zuwa gidanki ba zan daina faɗa miki wannan kalmar ba...Mace ta gari Maryam bata fallasa sirrin rayuwar aurenta ga kowa, ki zama mai riƙe sirrin gidanki, ina kuma tunasar da ke akan yin biyayya ga mijinki dan samun rahamar Allah acikin rayuwar duniya da Lahira, ki zama mai gaggawa wajen cika umarnin mijinki, ki zama mai kiyaye dukkan abin da zai ɓatawa mijinki, ki zama mace ta garin da idan mijinki ya kalleki zai ji farinciki ya lulluɓe shi...tun jiya na gama faɗa miki macen da ake kira da mace ta gari, Allah ya baku zaman lapia". Ummina ma ta fara magana da irin muryar da ke shaida rauni na zuciya tana cewa da ni,"Daughter nah dan Allah kar ki zama mace mai halin maza a gidanki kinji, namiji ba ya son wannan, abun da nake nufi kar ya zamana ba ki iya kisisina ba, ya zamana kin iya dabara, girki da kuma shagwaɓa ba, da kwalliya, da soyayya mai rikita kwanya, Daughter da iyaka waɗannan ma za ki mallake zuciyar mijinki...Allah yay miki albarka kinji". sauraronsu na ke tare da saƙa abubuwa da yawa araina, tun jiya zuwa yau komai sai dai ace Maryam ki zamarwa mijinki kaza ko kiyi masa kaza, to shin ni bani da hakki akansa ne da ba za ace yay min duk abubuwan da nake so ba? ko kuma ni banda abubuwan da nake so? ko kuma shi ma za'a faɗa masa nasa kamar yanda ake faɗa min?...nayi shiru ina ci gaba da sauraron faɗan Dad da ya amshe shima, faɗa yake min sosai tare da wasu nasihohin da suka sanya ƙafafuna wani irin sanyi, ni dai wannan aure ji nake kaman nace na fasa, dan har yanzu ma ni ban gama sanin me zuciyata ke ciki ba ga me da Kabirun da aka laliƙa min. nayi mamakin kaina ajiya, nayi mamakin kaina sose dana kasa fesar masa da kalaman rashin kunya da masifar da na tattaro zanyi masa a lokacin da na buɗi ido na gansa...abun da ya faru a lokacin na iya ƙarfin halin saka ƙwayar idona a tasa tarr babu ko ƙifce, sai dai abubuwa biyu da na hasko a cikin idanun nasa suka hanani aiwatar da abunda nayi niyya, wannan kwarjinin nasa, da kuma ƙyallin wani abu da na kasa tantance menene, kawai dai nasan ya zama silar mutuwar jikina gaba ɗaya. da ƙyar na iya kai hannuna da na dunƙule na kai masa duka a kafaɗa, sai kuma na fashe da wani irin kuka da ban taɓa yin irinsa ba, sai ya saki murmushi yana riƙe ɗaya hannun da na kuma kai masa duka dalilin ganin yana wani munafikin murmushi...yasa hannunsa a haɓata yana tambayata menene, sai na ture shi ina ƙara sautin kukana, ina ƙara kumbura sai aukin huci nake, na buɗi baki zan amayar masa da abunda ke dunƙule a ƙirjina cikin ƙarajin bala'i, amma sai naji muryata na fitowa cikin sanyi kuma a hankali nace. "da wacce manufar ka aureni Kabir, wanne irin shiri kai na ganin ka ƙuntatawa rayuwata da har kasan yanda kayi ka rabani da masoyina na gaskiya...to wallah bari ma kaji ta kowacce tsiya da bala'i sai ka rabu da ni, sai ka sakeni yanzu bada jimawa ba dan ba zan taɓa zama da kai ba, bana sonka kuma ba zan taɓa sonka ba, dan Allah ka faɗa musu ka sakeni naje na Auri Ya Ahmad ɗina me so na da ƙauna tsakani da Allah bada wata manufa ta cutarwa ba". na ɗago da ƙwayar idona da tun fara maganata ta ke akan cinyoyinsa, na kalle shi hawaye naci gaba da sauko min, a wannan lokacin ƙwayar idonsa ta kaɗa tayi jajir, haka kuma ya sauya zuwa wani launin halitta na daban. sai na ƙara saka kuka ina kaiwa duk ilahirin jikinsa duka ina faɗin,"Kabir ka sakeni, ka sakeni dan Allah, ba zan iya zama da igiyoyin aurenka a kaina ba, duk abunda kaje ka faɗawa Ummina ƙarya kake yi, kalamai ne na zallar yaudara...". muguwar matsar da yaywa tsintsiyar hannuna ita tasa nayi shiru, sai shashsheƙar kuka da nake ina son ƙwacewa, cikin wani amon sauti yace da ni. "ni ne nake ƙarya Maryam? ni ne mayaudarin?". na jijjiga masa kai da ƙara tabbatar masa sannan nace,"ai zancena gaskiya ne, saboda baka so na...". kuma ban iya ƙarasa faɗin abinda zance ba wani sabon kukan yaci ƙarfina, nayi shiru ina jin wani ƙunci da suya a ƙasan zuciyata. sai ya janyoni jikinsa ya haɗe fuskarmu wuri guda, iskar bakinsa ta sauka ajikina a lokacin da furucinsa ya fito da faɗin,"wa ya ce maki bana sonki Maryam, wa ya faɗa miki hakan? menene hujjarki na gasgata cewar bana sonki? me zan miki dan ki tabbar da duk zancen da na faɗawa Ummi babu ƙarya ac ikinsu?". "ai baka so na da gaske". "shi ne ai nake so ki amsa min waɗancan tambayoyin". "ba kana ƙyamatata bane saboda ni shegiya ce, shi yasa ka tsaneni baka ko son yi min magana, bayan bani nace a haifeni ta hanyar zina ba". sai kawai naji ya galla min wani mintsini a gadon bayana da yasa na miƙe zaune a gigice ina shafa wurin, kan nayi yunƙurin furta wani kalma yace. "naji fiye da wannan zafin a zuciyata, a waccan ranar da kika baɗawa idonki toka, kika yi watsi da tarbiyar da Gwaggo tayi miki, kika ɗauki huɗubar shaiɗan kika dinga faɗawa Ummi son ranki, da gaske tun a wannan ranar na fara jin haushinki, irin haushi sosai ɗin nan da yafi ƙarfin a musalta shi, shi ne dalilin ɗauke miki wutar da nayi Maryam...amma ko kusa ba saboda wannan negative tunanin naki ba ne". sai na saka hannu akan idona ina cewa,"to bana nemi yafiyarta ba kuma ta yafe min...ashe kai ba mutumin da zai iya yin afuwa ne ga wanda yay masa laifi ba, bacin ko Allah ma muna masa laifi kuma mu roƙe shi ya yafe mana". "ba haka bane Mairo tah, Mairoro wannan sauya mikin da nayi ya haɗe ne da tsananin kishinki da nake". kukan da nake sai naji ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, na tsaya cak ina kallonsa, ina kallon yanda yake murza tafin hannuna a hankali. kamin na ɗago da ƙwayar idona ina kallon Kabir ɗin da idanuwansa ke ɗauke da full of love, kamar ba wannan Ya Kabir ɗin da ya canja ba. sai naji wani sanyi na mamaye min ilahirin jikina, ba zan iya cewa ga halin da nake ciki ba a wannan lokacin, amma dai kalamai sun yi ƙaranci a bakina da zan iya jefa masa tambayar da ke raina. "Mairoro duk maganganun da na faɗawa Ummi gaskiya ne, kuma duk abunda Ummi ta faɗa miki gaskiya ne...Mairon Gwaggo Allah da gaske nake miki, ni ɗan Adam ne ina yin kuskure amma Allah ba na ƙarya kuma kema kanki shaida ce". ya faɗa yana saka hannu ya sake kwanto da ni jikinsa, yaja hancina yana faɗin,"Mairo tah kin san kuwa tun yaushe  zuciyar ɗan Kabiruwa ke ɗawainiya da ke". ba tambayata yay ba amma sai naji na girgiza masa kai. "ba sai na tsaya ina miki dogon bayani ba, amma what i want you to know shi ne na fara sonki tun ba ki san kanki ba, kuma ƙaunar da na ke miki mai zafi ce Mairon Kabiru, Allah ma yasan da wannan...kuma na jingine hakan a raina ne saboda babu damar na furta miki hakan ke kin san dalili...kuma lokacin da ya kamata na furta miki cewar kece zaɓin raina cikin rashin tsammani sai na tsinci soyayyarki a tare da Ahmad, kin san irin halin da.na shiga a wannan time ɗin? ba ki sa ni ba, amma ke na ɗorawa laifin, dan gani nake kamar ke kika ba shi damar hakan...Allah ya sa ni a wannan lokacin da ban janye miki ba wallahi i might loose control zafin kishinki yasa na aikata abunda ba shikenan ba, abunda zan zo ina danasani... lokacin da kika amince masa Allah ɗaya yasan da irin ciwon da kika haifarwa zuciyata, kin gani kin kuma lura da hakan amma tunaninki ya hanaki gane mawuyacin halin da kike neman jefa bawan Allah...ba zan iya ganin kina soyayya da wani ba, ba zan iya ganin kina soyayya da ɗan'uwana ba, shi yasa na bar muku ƙasar kuci karanku babu babbaka...Abdurrahim ne kaɗai zai iya ba ki labarin mawuyacin halin da na shiga a san da naji an tsaida ranar aurenku, shi da Ummi ne kaɗai za su iya ba ki labarin yanda soyayyarki ke nuƙurƙusar zuciyata, duk wannan farin ciki da kuma walwalar da na daina duk akan sonki ne...kuma sai da na gama cire rai da samun ki, nayi giving up da komai na rayuwa ta, sai Allah ya dubeni, ya dubi haƙurina, a lokacin da banyi zato ba banyi tsammani ba Allah ya bani ke, ya bani ke matsayin matata...Alhamdulillahi Rabil Alamin, amma babu ƙarya wannan me bakin tsiwar ta wahalar da ni, kuma nima sai na rama, Allah ya kaimu akai min ke ɗakina, za ki sha mamaki, za ki sha mamakin sonki da ya shekara goma sha daskare a zuciyar Kabir". Allah ma ya sa ni a lokacin ba zan iya cewa komai ba, kuma ba zan iya aiwatar da komai ba, illa bige hannunsa da nayi dake neman shiga cikin rigata. murmushinsa mai sauti ya fito haɗe da cewar,"wai duk wannan dogon bayanin da na maki ba ki yarda da ni ba?". cikin sauri na ɗaga masa kai. sai ya lakuce min kumatu da faɗin,"to kar ki yarda ɗin, ni dai ai nasan haka ne, kuma tunda Ummi ma shaida ce kar ki taɓa yarda ɗin...ni ai ba yaronki ba ne da zan tsaya kina min yanda kika so, da ki yarda da ni ma har saina miki kalar tausayi, to sannu Yagana". nace da shi,"in ka iya tsara Ummina ni dai ba zaka tsarani ba...dama ai nasan duk ƙarya ne kake gillawa...". sai ya ɗalle min baki yana cewa,"wai ni sa'anki ne da kike faɗin ina miki ƙarya? ko kin manta wane ni, ni ne fa wannan Ya Kabir ɗin naki". sai naja hancina a lokacin da nake jin wani mixed feeling nace,"kai ɗin, ina ruwana da kai". "zanyi maganinki ne soon, ranar da aka kai min ke ba za ki samu damar faɗa min haka ba". sai kawai nasa kukan shagwaɓar da ban san lokacin da ya zo ba ina faɗin. "ai dama nasan kasheni za kai shi yasa ka aureni, kuma ni ka sakeni ko kuma duk abinda nayi maka a gidan kai ka siya da kuɗinka, ai na faɗa maka bana sonka, dan haka ka rabu da ni tunda kaima ba sona kake ba". na lura wannan kalmar tawa na saka shi a wani yanayin, a jikina kawai na tsinci ɓacin ransa, a irin matse hannuna da yay na tsinci irin ɗacin da yake ji idan nace baya so na, so kawai sai na shiga raira kukana a hankali, shi kuma ya miƙe ƙafafunsa yana jingina da gadon, sannan ya sakani tsakiyar ƙafafunsa ya lafar da ni a ƙirjinsa, lokaci kaɗan naji bacci ya fara fizgata, kafin baccin ya ɗaukeni gaba ɗaya ina jin time ɗin da yake waya da wanda ya kira da su na Abdurrahim yana faɗa masa shi dama ai ba ma'abocin yin abunda mutane suka raja'a akai bane, in dai dinner ce zai yi gagarumar dinner amma a gidansa, cikin ɗakinsa, kan gadonsa, a cikin wannan daren. kuma baccin da nayi ban san lokacin da ya tafi ba, na farka naga babu shi, sai naji na farka da mararin son ganinsa a lokacin, har nake tambayar Shamsiyya wama ya maidani kan gado, ta harareni tace sai na kira shi wanda nayi baccin ajikinsa na tambaye shi. tana ƙara ce min wai wallah wannan Ya Kabir ɗin ba shi da kunya, in banyi hankali da shi ba sai ya dinga bada ni a gaban mutane, nace me yayi tace wai na tambayi Ummi ta ban labarin a yanda tazo ta samemu, kuma ganin nata baisa ya daina abunda yake ba, tayi magana kuma yace wai ai Maryam ɗinsa ce. tsaki kawai nayi a lokacin na sakko daga kan gadon na shiga banɗaki da tunani kala kala acikin ƙoƙon kaina. Anty Iftihal da ta shigo yanzu bayan ta gaida su Abi da Daddy tace,"zamu iya tafiya?". Bella tace,"babu damuwa". Daddy ya miƙe yana faɗin,"da wa zamu tafi?". Ummi ta miƙe tana cewa,"ai ƙafata ƙafar ƴata". Ummi ta duƙo ta ɗagoni na tsaya akan dugadugaina, sandararriyar ƙafata na neman ta watsar da ni na zube. na hangi Mamina na goge ƙwalla sai kawai na ƙwace daga hannu Ummi na faɗa jikinta ina fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar duk mai saurare. Mami ta rungumeni tsam ajikinta itama tana kukan. muryarta na fita da amon kuka tana faɗin. "Allah ya sani bana son rabuwa da ke, amma babu yanda zanyi aure ibada ne kuma sunnar ma'aiki wadda ta zamar mana dole mu rayata...Auta Allah yayi miki albarka kinji, Allah ya albarkaci dukkan rayuwarki, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah ya tsare gaba da bayanki, Allah ya rabaki da sharrin maƙiya mahassada, Allah ya ɗoraki akansu, yasa ki zama mai rinjaye akansu...Ya Rahmanu yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Ya Maliku yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Ya Hayyu ya qayyum yasa masa tausayinki a zuciyar mijinki, ya ƙara ninka soyayyarki a zuciyarsa, Allah kuma ya ba shi ikon sauke nauyin duk wani hakki naki, ubangiji yasa ku zamewa junanku inuwar salama har ranar alƙiyama, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, Allah yasawa zuri'ar da zaku samar albarka, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi...Dan Allah Auta ina roƙonki kiyi riƙo da dukkan tarin nasihohin da aka miki, karki watsi da su dan bana so ki koka ko kaɗan, yin watsi da su dai-dai yake da yin bankwanan farin ciki a rayuwar aurenki...ina sonki, ina sonki sosai ƴata...duk wani abu da kike so ki kirani ki sanar da ni kinji ɗiyar albarka, zanyi kewarki sosai". tayi maganar ƙarshe tana sa hannu ta goge min hawayena alhalin nata ba su tsaya daga zuba ba. cikin kuka nace,"Mamina na fasa auren kinji". sai kawai ta kauda kai gefe dan kar naga sabon hawayenta da zai zuba. da ƙyar da siɗin goshi aka rabani da jikinta. Daddy ya kama hannuna na dama, Ummi ta riƙe na hagu suka fita da ni daga ɗakin, kuma muna isowa haraba busar algaitu ta fara tashi, ana kwararo adu'a da kirari wa ni da su Daddy. gidansu Ya Kabir aka kaini, sai da aka kaini wurin Baba Daddy ya damƙa masa amanata, shima yay min kalar nasa nasihohin da faɗan sannan aka tafi dani ɓangaren Yagana, suka ƙara damƙa ni a hannunta, Yagana tana ƙwallar nuna farinciki take cewa ta amsa, fatanta Allah ya tayasu ruƙo...daga nan kuma su Daddy suka mana sallama suka wuce gida inda suka barni da sharɓar kuka. bayan tafiyarsu babu jimawa Mama Siddiqa wacce ta ke ƙanwa wurin Mamansu Ya Kabir ta shigo ɗakin, ta umarceni da na tashi nayi sallar la'asar, na miƙe jiki a sanyaye da tarin kunya na shiga bayi nayi alwala sannan na fito na gabatar da sallah. da su Adawiyya muka zauna a ɗakin muna ta hira, duk da na kasa sakewa jina nake kamar ban taɓa rayuwar cikin gidan ba, kamar baƙuwa na ke, Sadiya ma sai tsokanata take wai duk gulma ce ni dai bancewa kowa acikinsu ƙala ba. so nake ma duk su tashi su fita na samu sakewa da Basma tah. har magriba muna tare da su, kuma kowa da kalar tsiyarsa da yake min, Yagana ta kawo min wayarta da Shamsiyya ta kira. na amsa ina sallama, ban san lokacin da kukan da nake ta riƙewa tun ɗazu ba ya sauko min. tace dani,"ke dilla ni ba kuka na kira ki min ba". nace da ita,"Shamsiyya dan Allah kizo mu zauna tare kamin gobe mu tafi". sai ta saki wata munafukar dariya tana tambayata wai aina zan kwana yau ɗin da nake cewa tazo. kamar ina gabanta na saki harara nace,"ban sa ni ba, banza ƴar iska kawai". ta kuma ƙyalƙyalewa da dariya tana cewa,"naji dai...ke dama Ummi ce tace na faɗa miki ɗazu tayi mantuwa da humrarki a jakarta, amma Ya Kabir ɗin yazo ɗazu ta ba shi ya taho maki da ita, idan yazo sai ki karɓa". na turo baki nace,"amma dai ba cewa zanyi ya ban ba ko?". tace,"oho ke kika sa ni". duk sai naji ta ɗebe min kewar da ke damuna, mun jima muna hira tana ta zuba min iskancinta da ke cinta, wanda na rasa aina Shamsiyya ta san irin waɗannan abubuwan, da nayi magana sai tace,"oho ni dai faɗa miki nake in ba ki iya abu kaza da kaza ba kina ji kina gani wata can za tayi miki wuff da shi kuma babu yanda kika iya". **** anyi sallar isha'i ina zaune kan sallayan ban miƙe ba ina ta tunanin Mamina, sai ga Nawwara ta shigo hannunta riƙe da tray na kayan abinci, na amsa sallamarta ta nemi kan ƙaramin table ɗin da ke ɗakin ta ɗora akai, sannan ta dawo tace da ni. "Yaya abinci ne Yagana tace na kawo nan, wai ki shirya yanzun Ya Kabir ɗin zai shigo". nayi saurin ɗagowa nayi mata wani duba tare da cewa,"zai shigo yayi me?". sai tayi shiru kafin tace,"ance dai za'a kai muku abincin ɗakinsa yace a kawo nan". ban ƙara mata magana ba ta miƙe ta fita ina bin bayanta da harara kamar wadda tayi min laifi. na miƙe ina ninke hijab ɗin Yagana da nayi sallah sai ga shi ya shigo, ni dai banji sallamarsa ba ƙamshin tararansa ne kawai ya sanar da ni shi ɗin. ya shigo cikin wannan takun nasa da bana iya ɗauke idona akai amma ta yanda ba zai lura ba, ya ƙaraso har gabana sannan ya miƙo min baƙar leda yana faɗin. "ƴar gidan Ummi gashi inji Umminki". nasa hannu na karɓa ina turɓune fuska, na taka zan ƙarasa ga wadrobe ɗin Yagana naji yana tambayata wai menene a ledan, dan tunda aka ba shi yake jin ƙamshi, motarsa ma duk ta cika da ƙamshinsa, nayi kaman ba zance komai ba sai can nace. "me yasa ita da ta baka baka tambayeta ba tun acan". "ke naga damar tambaya ai". na juyo ina masa kallon ƙasan ido sannan nace,"to nima ban sa ni ba". sai kawai ya saki murmushi tare da cewan. "bari naje nayi wanka, yanzu zan dawo muci abincin...visa ɗinmu ya kammala amma goben a abuja zamu kwana sai washegari zamu wuce". ni dai bance masa komai ba har ya juya ya fice. yana fita Yagana ta shigo tana ta maganganunta, ita ma bance mata ƙala ba sai da ta gama abinda za tai zata fita sannan nace,"Yagana kice da wancan jikan naki ya dawo ya ɗauki abincinsa, zan rufe ƙofa ina jin bacci". sai ta dakata ta juyo ta dube ni da kyau sannan tace,"sannu sara mai baƙar takashi, ai mai hali ba zai taɓa fasa halinsa ba. to da za ki rufe ɗaki naki ne zaƙwaƙura?...ai sai ki bari ni da nake da iko da ɗakin in gama abunda nake idan na shigo kya rufe...". ban jira ta kai ƙarshen zancenta ba nace,"to ai dai naga da aka kawoni ke kika kawo ni ɗakin naki ko...to kije kiyi abinda za ki da sauri ki dawo zan kwanta". ta saki baki galala sannan tace,"to Uwar Yagana naji". ta juya ta fita tana faɗin,"ni dama da Amadun aka barki ya sai ta miki hali ba da wannan sanyi ƙalau ɗin mutum ɗin ba...da sonki zai hana shi hukunta ki". na zauna bakin gado ina jiran Nawwara da na kira a waya tazo ta ɗauke abincin da ba cinsa zan ba

Chapter 49 of 52