Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
akeyi dama?". Maimakon ta bani amsa saita kuma fashewa da dariya harda kifawa ƙasa tana riƙe ciki. Sadiya wadda ke zaune kan dakalin ƙofa ta wurgo min tambayar,"yaushe kika shiga ɗakin mazan da ba ƴan gidanku ba?". Nayi saurin girgiza mata kai da hannu,"nifa yanzu ne kawai dana farka a bacci naga na haihu amma wallahi ban taɓa shiga ɗakin maza ba...". "ƙarya kike yi, jiya da daddare ba ina kallo kika shiga ɗakin su Ya Kabiru a salallaɓe ba bayan kuma basa nan sai abokansu". Na dire kan gwiwoyina nace,"to ai fa kawai cinnaka na ɗauka naje na sawa wannan Jawad ɗin da ya zagi Adawiyya a baki, kuma dana ga ya cije shi saina fito da gudu". Sai a yanzu Inna Amarya tasa baki, "ke dilla nutsar da hankalinki wuri ɗaya, babu wani haihuwa da kika yi". "Allah Inna haihuwa nayi, kallafa jini na zuba ajikina kuma har akan gadon Gwaggo ma dana kwanta, dan Allah kice karta kasheni, na shiga uku". Kuka nake wurjanjan kamar zan haɗiyi zuciya, dariyar Adawiyya ta fara ƙular dani na maƙuro wuyanta ina dukanta, "banza, muguwa, azzaluma, wawiya, doluwa, sokuwa, shashasha kawai, kuma saina faɗawa Gwaggo nace baki kaiwa Baaba Lami saƙon ba". Jin haka ta ƙwaci kanta da ƙyar ta shiga bani haƙuri akan na rufa mata asiri. Itama Sadiya ina jiyota tana cewa ai ni ce sokuwar ba Adawiyya ba, ban dai kulata ba saboda Ya Amadu yace na kuma yi mata rashin kunya sai ya zaneni. Inna Amarya wadda ta fita tun ɗazu ta dawo tana ce min na tashi na ɗaura zane akan kayana naje nayi wanka, bata barni na fita ba sai da ta natsar da hankalina wuri ɗaya. Na fito da kayan da na cire rungume ajikina ina kaffa kaffa kar wani ya gani, dan Inna tace duk wanda ya gani za'a yayatani a duniya ace na haihu babu aure, kuma idan Baba yaji da gatari zai faskarani tun kan Gwaggo ma ta yankani. Naja botikin ƙarfe na zuba kayan aciki, da dasu zan shiga bayin sai kuma na ajiye daga bakin ƙofa ta wajen lungun wurin ta yanda babu mai iya gani. Shaf-shaf nayi wankan na fito dan baki ɗaya hankalina yana kan wankin dana ajiye, so nake har na wankesu kar wani ya shigo gidan, sai dai da mamakina ko dana duba babu botiki babu alamunsa, na ko rikice na kama hailala da salati, to wane yazo ya ɗauka?, kar dai a mazan gidan wani ya shigo, ina ƴan dube-dube na hangi Kulu na shanya kayan ajikin garu ta bayan ɗakinsu Lukman, "kutttt". Na faɗa da ƙarfi cike da jin haushinta, da sassarfa na ƙarasa wurin da take, na kama ƙugu ina jijjige jijjige sai cika nake ina batsewa, ni nasan ban isa nayi mata komai ba amma tunanin makeken sharrin da zan ƙulla mata a wurin Gwaggo kawai na ke, ga mamakina sai gani nayi ta dubeni ta lafta min uwar harara tasa hannu ta kaudani gefe, duk da bata kallona amma haka na murguɗa mata baki sannan nace,"wai ke Kulu baki san kin girma bane, sai kita wani shishshige min ala dole sai nayi ƙawance da ke, akan mene na aje kaya zaki zo ki ɗauka ki wanke sai kace na saki, wannan ma ai shishshigi da ƙwala kai a faranti ne, to ni dai bana so karki kuma min irin haka ba ruwanki dani da al'amurana dan bana kula mahaukata irinki...". Ɗiff bakina ya ɗauke ganin ta Ɗaga hannu a zafafe zata tsinkeni da mari, ban san me ya hanata ba naji ta sauke hannu, ta ƙarasa shanya zane sannan ta juya ta bar wurin, in da ni kuma a lokacinne na ɗago ina binta da kallon mamaki, abunda idanuna suka ci karo da shi a wuyanta shi ya ɗauki hankalina, abu ne kamar tambari na tauraro baƙi, kasancewarta fara ƙal gashi nan raɗau kana kallonsa, sai da ta ɓacewa ganina sannan na sami damar haɗe murfayen idona ina son tuna in da na taɓa ganin wannan tambarin, na fi daƙiƙa biyar a tsaye acikin wannan tunani sannan na buɗe idona, tabbas idan ba a wuyan Gwaggona ba to a wuyan Jawad ko shi ko Suhail ko kuma Ya Kabiru na taɓa gani. na ɗan ciji yatsana, to amma kuma ai kamar wannan tambarin an taɓa nuna shi a tv a masarautar larabawa, kenan ananne na taɓa gani irinsa?, kai bayan nan ma kamar na taɓa gani a tsakanin mutum huɗu nan da na ke zargi, ɗan ƙaramin tsaki nayi dan sai yanzu na tuna ma ashe a wuyan Basma ne, har nake tambayar Gwaggo ko ƙonewa Basma tayi tace a'a baiwace, nima kuma a lokacin har na ɗau madubi na duba nawa wuyan, da yake hasashe ne nake sai naga kamar nima ina da shi, da na bawa Gwaggo ta duba min sai tace kar na isheta da shirmen banza. Sai da na ɗauki kayana na kuma wankesu sannan na wuce ɗaki, dan acewata wankin Kulu ƙazanta ne, tunda ban taɓa ganin tayi ba sai yau ɗin. Ko da naje ɗakin Inna Amarya sai tace naje wurin Gwaggo, a ɗarɗarce dai na shiga ɗakin Gwaggo sai rakuɓewa nake, ƙasan zuciyata ina ta biya_"dinkimma dinkim Allah ya kafe bakinki"._ dan ni saukar bugu kawai nake jira daga wurinta domin nasan tana sane da komai, jira kawai take Allah ya kawoni kusa gareta ta zartar min da ɗanyan hukunci. "idan kin gama raɓe-raɓen ga kaya can a leda ki ɗauka ki saka, karki sa wando sai kin manna waccan abar". Gwaggo tace dani tana ficewa daga ɗakin. Na ƙarasa na buɗe ƙatuwar baƙar ledar da ta min nuni da baki, na zazzage kayan ciki a ƙasa, na shiga ɗaga kayayyakin ɗaya bayan ɗaya ina dubawa, dogayen riguna ne da nake ganinsu ajikin labarawa idan munje kallo gidan Liman da azumi, a ciki kuwa harda shigen wadda likitar da tayi min allura ɗazu a asibiti ta saka, kalar shuɗi da fari da wasu azababbun duwatsu ajiki masu shegen kyau da ɗaukar ido, murmushi kawai nake wani sanyin daɗi da farin ciki na baibayeni, babu tantama wannan siyayyar Ya Kabiruna ce, gaba ɗaya rigunan guda uku ne, duk da ban san farashin kaya ba amma da gani kasan kuɗi ne ba ƙarami ba a wannan siyayyar, to amma aina Ya Kabiru yake samun kuɗi kwana biyu? aikin me ya samu?. Tunanina ya katse a sanda naji an kamo hannuna an miƙar dani tsaye, Kulu ce riƙe da hannuna da tattausan hannunta me matuƙar kashe min jiki a duk lokacin da ta taɓani da shi, kallona take da dara-daran idanuwanta wanda na kasa ɗauke ganina acikinsu, ban taɓa kallonta ido cikin ido ba, amma yau saboda tsananin kyawun da nagani acikin ƙwayar idanunta sam na kasa daina kallonsu duk da kwarjin da suka yi min, Magana take min da ido wadda tsab na karance me take nufi, saboda hakane na natsu ina dubanta da abunda tace na maida hankalina akai, wani madaidaicin kwali ta ɗauko a wata leda ta daban dake gefen wadda na buɗe, ta buɗe shi ta ɗauko wando ɗan ciki(pant), ban taɓa ganin irinsa ba dan irinmu Ƴaƴan Malam Audu na ƙauye ba irinsu muke sawa ba, gajere muke sawa irin na tsaffi wanda ake cewa bantai. Kallon yanda take min bayanai da hannu nake yi, ta ɗauko irin abar da naga an rabawa su Adawiyya kwanaki a makaranta, ta ɓare ledarta ta zaro ɗaya ta manna ajikin wandon, sannan ta miƙo min. "me zan yi da shi?". Na tambayeta cikin muryata da tayi sanyi. A yanzunma dai da ido ta bani amsa, ganin zanyi gardama a maganartata yasa ta zare min ido har saida na firgita na rungumeta ita kuma ta tureni daga jikinta, ina ɓata rai na saka wandon ajikina wanda ya kamani tsam, naji wani banbanci na daban. Tana ganin na saka ta bar wurin, na bita da kallo ina maimaitawa kaina anya Kulu mahaukaciya ce?, ko kuma anya asalin Kulun dana sani a gidan nan ce ba masayen wata akayi ba?, ta ɗaga labule zata fita nace, "kiyi haƙuri da kalmar dana faɗa miki ɗazu". Shuɗiyar doguwar rigar na ɗauka na saka, na ɗaura ɗan yalolon mayafin dake tare da ita, kamar an gwadani kamin a siyo, inata duban kaina acikinta ina zullumin shigowar madubina gidan yazo ya gane min kyan da nayi, ni tun ina ƙarama ban san nayi kwalliya na duba madubi ba, Ya Kabiru shi ne madubina. Daga tsakar gida na jiyo Adawiyya na ƙwala min kira, na ɓata fuska nai saurin tattara kayana na jefa ƙasan gado, ina tsaye na haɗe rai ta shigo banko dubi inda take ba, balle na amsa mata maganganun da take, kallona take tana ƴar iskar dariyar nan tata me ƙularwa, na juyo a fusace zan kai mata duka ta kauce. "ya isheki Adawiyya idan ba haka ba zan gurza miki rashin mutunci, sanin kanki ne hankali ba gama ratsani yay ba walla saina ɗauka wannan langar na rantama miki a tsakiyar ka ki koma sahun su Kulu kema". Ta tsagaita dariyarta tana cewa, "Ke nifa banga dalilin da zai sa ki dinga hanani dariya ba, ai bance dake nake ba". Nayi ƙwafa na girgiza kai tare da cewar,"karki fasa kici gaba". Dariyar ta daina tana faɗin,"yasin tawa tafi taki kyau". Sai yanzu da tayi maganar ma na lura da kayan dake jikinta, doguwar rigace irin tawa amma tata ja da baƙi kuma kwalliyar tawa tafi tata, rigarma dai gaba ɗaya tafi dai-dai da jikina dan ita ta kamata, kuma tsayin yayi mata yawa, ni kuwa daga tsayin har faɗin rigar dai-dai dani, na ƙare mata kallo na kwaɓe baki nace,"arziƙina dai kika ci aka raɓa dake a siyan, kuma wallahi ƙarya kike tawa tafi taki kyau". Sallamar Ya Kabiru a ƙofar ɗakin na bar inda nake da sauri na tafi naje na rungume shi, adu'a nake jera masa tare da sanya masa albarka, ya ɗago kaina daga jikinsa yana kallona, sai dai har yanzu hannuna na kewaye da shi, na ɗan doki ƙafa a ƙasa da cewa,"Ya Kabiru wannan kallon fa kamar yaune ka fara ganina". Acikin sigar zolaya yace,"dama ni na taɓa ganinki ne banda yanzu, wace ke?". Na shagwaɓe ina narkewa jikinsa sai dukan ƙafafu nake a ƙasa nace, "Ya Kabiru ni ce fa". Da kwaikwayon maganata yace, "ke wa?". "ni Mairo". Ya buɗe baki yana riƙe da haɓa yace,"Yaushe Mairon tawa ta zama balarabiya?". Murmushi kawai nayi sannan na ɗago daga jikinsa ina riƙe da hannunsa nace,"Ya Kabiru kuma Allah daga yau karka kuma saya mana abu tare da Adawiyya, tun ɗazun tazo tasani agaba tana min dariya wai tata tafi kyau". Sai da ya dubi Adawiyya kana yace,"yo dama ita kalar ƙauye ina tasan kyau, baki kalla kayan ko amsarta ba suyi ba ta koma kamar dodo". Na tuntsure da dariya ina mata gwalo, haushi ya cikata zata bar ɗakin ya janyota jikinsa yana cewa,"aike kika fara tsokanarta". Bai bar Adawiyya ta fita ba sai da ya sata dariya kana, ni kuwa har da zungurinta ina ƙara yi mata gwalo, tabbacin ta shaƙa yasa na ƙara da ce mata me wargajejen baki. Duk nauyin da Gwaggo ke cewa ina da shi Ya Kabiru baiji shi ba ya ɗorani saman ƙafarsa guda, ina wasa da gashin sajensa nace, "Ya Kabiru baka taɓa saya min kaya masu tsananin kyau da tsadar waɗan nan ba, na rasa kalar murnar da zanyi, Ya wanne irin aiki ka samu baka faɗa min ba bayan kace ni ce sirrinka". Yana goga haɓarsa saman kaina yace,"wai ni Mairo wanne kaya ma kike nufi ne?". Na zame daga jikinsa ina cewa, "Ya Kabiru waɗan nan mana". Yay ɗan jim yana daɗa ƙare min kallo, bakinsa ya motsa kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, muryarsa a hankali ta fita da cewar, "Mairo yau kinfi ko yaushe kyau, kin ƙara kyau sosai, har kyan naki na neman kashe min idanu". Daɗi ya kamani ina wasa da yatsunsa ina cuno baki gaba nace, "Ya Kabiru amma shi abokinka Jawad haka yace min wai mummuna dani sai rashin kunya, inda za'a bashi ni ma gidan zoo zai kaini". Yaja ƙaramin tsoki da cewa,"ƙyale wannan shashashan, komai shi baya masa kyau...kin sha ice cream ɗin dana kawo miki ɗazu?". Na kaɗa masa kai alamar a'a, "ai ban gani ba, wa ka bawa ya aje min?". "a kusa dake na aje miki, ƙila Gwaggo ta ɓoye miki". "ko kuma wannan kwaɗayyar ƴar tata ta shanye min ba dan nasan dai Gwaggo ba zata adana min ba ko zata ga ƙwari na shiga ciki". Nayi kamar zanyi kuka na ƙwace hannuna daga nasa na fita a ɗakin ina cewa,"Allah Gwaggo in dai ƴarki tasha min abuna yau saina ɓallata acikin gidan nan". Tace dani,"me zai hana ki ɓallata tunda kin samu kara". Ya Amadu kuwa ko da ya dawo sai cewa yayi ai Adawiyya ta fini kyau, kayanta ma sunfi nawa kyau, nawa ma kamar ba sabbi ba, yau ɗinma dana saka kayan larabawa maimakon nayi kyau sai nayi muni, Adawiyya kuma ta zama kamar balarabiya, Naji haushi sosai danni a komai so nake naji ance nafi ƴan gidanmu musamman Adawiyya da take sakuwata. Abincinsa ma da aka bani na kai masa ɗaki ina sane na faɗi da gangan na zubar, na kuma ji daɗi da Inna Zulai tace babu wani sai dai idan ya duba masu awara. Da daddare na shiga ɗakin Gwaggo zan cire kaya, na ɗauki zanen Gwaggo da ke rataye jikin ƙofa na rufawa Kulu da ke kwance, saboda yanda naji garin da ɗan sanyi sanyi. Na gama sauya kaya zan fita maganar Gwaggo ta dakatar dani. "dawo anan zaki kwana". Nace mata,"bari na ɗauko kayan shimfiɗa". "zo ki kwanta nan kusa dani". a kan gadon ƙarfen nata da ta saba kwanciya ita ɗaya na kwanta kusa da ita, na takure zuciyata cike da taraddadi, can naji tayi nisa ta fara ce min. "ayau kin shiga wata sabuwar rayuwa ta ƴa mace wadda tasha banban data ƙuruciyarki. Zina da dangoginta, Mairo na horeki da ki kiyayesu, idan ba haka ba zaki ƙare rayuwarki ne acikin ƙunci. Mairo kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina, dan wallahi wallahi sai kinji dama mutuwa kika yi akan rayuwarki, yanzu ke ba yarinya bace, kinyi girman da zaki san komai ki kuma san inda ke miki ciwo...wannan jini da kika ganki acikinsa ɗazu bana haihuwa bane jinin girmanki ne, ada idan namiji ya taɓaki za ki zauna lafiya amma banda yanzu, karki bari hawayen dana daɗe da tsaidasu na tsawon shekaru goma sha huɗu suci gaba da zuba a saman fuskata, ki taimaka ki barsu su tsaya iyaka zuciyar, dan duk ranar da kika kuskura kika ɗauko min abun kunya Mairo saina kasheki kamin baƙin cikinki ya kashe ni". Maganarta ta ƙarshe ita tasa na haɗiye wani dunƙulallan yawu a maƙoshina wanda ya wuce da ƙyar, tsoro ya shigeni, Zina! Zina! Zina, kalmar da nake daɗa nanatawa acikin kaina kenan tun bayan da naji Gwaggo tayi shiru, _"kar ki sake sharrin zuciya ko soyayyar ɗa namiji su yaudareki ki aikata Zina."_ wannan kalaman na Gwaggo suka daɗa haskawa acikin kaina, mene sharrin zuciyar da har zaija na aikata zina?, wacce iriyar soyayya namiji zai nuna min har na aikata zina?, shin da ma ita zinar waɗannan abubuwa biyun ke janyota?, ya ya zinar take ne? Mecece ma ita zinar?, wanne irin hawaye Gwaggo tayi wanda take gudun sake zubarsu a yanzu?. Na rufe idanuwana na mirgina kwanciyata ina fuskantar rufin kwanon ɗakin, ayau dai na tabbata ba zan iya bacci ba cikin wannan daren, saboda maganganun dake tushe acikin kwanyata waɗanda ke neman tarwatsa min kai, ban warware zantukan Baba ba, ga Gwaggo ta kuma ɗura min wasu, na damƙe kaina da nake jin kamar zai rabe gida biyu. Nafi awa biyu ina juyi bacci yaƙi ɗaukata, da na rumtse ido sai naji gabana na faɗuwa, na tuna da wani wa'azi da muka taɓa saurara a radio da azumi, hakan yasa na miƙe na zuro ƙafafuna domin na fita na ɗoro alwala nazo nayi nafilfili, sai naji maganar Gwaggo na tambayar ina zani?, na waigo muka haɗa ido da ita nace zanyi sallar dare ne. Ta kuma jefe min tambaya,"salloli nawa kika yi ayau?". "duka nayi ɗazu dana farka". "to kar ki ƙara yin sallah har sai kinga wannan jinin ya ɗauke miki, ba'a yin sallah idan ana yinsa". Murya na rawa nace,"to Gwaggo yaushe zai ɗauke?". "idan ya ɗauke za ki kalla ya daina zuba. Ki kwanta haka". Na miƙa hannu na ƙaro hasken fitila na dubi fuskarta, muryata sanyi ƙalau nace,"Gwaggo kuka kika yi?". Ta gyara kwanciya inda ta juya min baya sannan tace,"waya mutu da zanyi kuka, hammar bacci ce, ki koma ki kwanta dare yayi sosai". "zanje fitsari". Bata kuma amsani ba, na sakko na nemi ledar ɗazu na zari abar da Kulu ta saka min a wando, dan a karatun bebayen da tayi min a ɗazu har da nuni da sauyata akai akai, na raɓa ta gefen shimfiɗar kulu na fita, da ƙyar na shiga bayi saboda duk a tsorace nake, aikuwa na tsorata sosai da yanda naga jini ya wanke farar audugar, na zareta daga jikin wandona na buɗe murfin masai na jefa aciki sannan na manna sabuwa tukunna na mayar da wandona. Fitowata daga bayi ina ƙoƙarin ɗauraye hannu, nayi saurin tarar butar dake neman faɗuwa daga hannuna ina cije fuska gudun kar aji motsi, ba ƙaramin razana nayi ba ganin Kulu ta shiga ɗakin Baba a wannan silasainin daren, na koma da baya na ɓuya, ina kallo ta fito ta shiga madafa ta ɗauki kwano ta tuttuli ruwa aciki sannan ta koma ɗakin, tana shiga kuwa nayi saurin fitowa na dawo na laɓe a ƙofar ɗakin Baba ta inda babu me iya ganina. Maɗaukakin mamaki da al'ajabi suka lulluɓeni a sanda na jiyo maganar Kulu tana cewa da Baba, "daga ina Allon ya ke?". Muryar Baba ta fita daga can nesa yana amsa mata da, "ɗaga wannan buhun yana wajen". Shiru ya ɗan gimla kamin ya ƙara da ce mata, "kin tabbata ruwan saman kika tsiyayo?". acikin hausarta da naji bata fita sosai tace,"ehh ina da tabbacin shi ne, dan jarkar naga Yaya ta tara daren jiya". nayi wata daskarewa a wajen, ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa da tarin tambayoyin dake cikinta, kenan Kulu ma matar Baba ce? Dama kuma tana magana? Kuma dama lafiyarta ƙalau?, to amma me yasa...?, cak na sume a tsaye ina bin Gwaggo da kallo wadda ta nufo hanyar ɗakin Baba, dai-dai fitowar kuma Kulu, ban mutu a tsaye ba sai da naji Kulu ta kira Gwaggo da,"Yaya". Ta faɗi hakan muryarta na rawa. Gwaggo ta kama hannunta suka koma ɗakin tana cewa,"bana son kuka ki haɗiye shi". ba zan iya faɗar irin ruɗanin dana shiga ba, naja ƙafafuna da ƙyar na wuce ɗaki, sai dai ina shiga ɗakin na zube a ƙasa na zama mutun mutumi, lamuran daketa faruwa da ganina da jina a yau sunfi ƙarfin kaina. *#Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *6)* Ta-ke idona ya firfito waje, gumi ya jiƙe min jiki, tashin hankalin da ban taɓa shigarsa ba ya dirar min, tsorona Allah tsorona irin wawan kallon da Gwaggo ke jifana da shi, na haɗiyi wani wahaltaccen yawu a maƙoshina, na runtse ido ƙirjina na dukan tara-tara, kafin na kai ƙwaƙwalwata ga fara tunanin laifin dana aikata naji wani ƙullutun abu ya faɗo ta gabana, na daɗa rumtse ido sosai saboda zafi da ya ratsani. Da gudu-gudu kuma naji abu kamar ruwa naci gaba da fita daga gabana me ɗumi, na mayar da kaina kwance idanuwana a rufe ina cije leɓe, tsawon wasu daƙiƙu dana ɗauka ƙasan cikina na min azabar ciwo sannan na fara dawowa cikin hayyacina dana bari, numfashin wahala nake saukewa da sauri da sauri, daga can na jiwo muryar Gwaggo na fita acikin faɗa. "rashin hankali ne kawai irin nata, Amarya zuwa yanzu ya kamata ki daina goyon bayan Mairo akan duk wasu abubuwa da take wanda ba dai-dai ba, haba wacce iriyar rayuwa ce wannan da za'ace mutum zai yi ba dai-dai ba a zuba masa ido baza'a nuna masa kuskurensa ba, ni wallahi kuna ɓata min rai idan kuna cewa yarinya ce". Inna Amarya ta fitar da murmushi me sauti sannan tace,"to ai sai yanzu girman ya risketa ko, daga yanzu ne ita ma zata fara sanin kanta da kuma inda ke mata ciwo, wanda da kanta zata gane kuskuren abunda bai dace ba". Shiru na tsawon daƙiƙa biyu Gwaggo bata ce komai ba, sai can naji ta ambaci sunan Kulu tare da cewa mata, "ki duba magungunan muji yanda suke kamin ta farka, allurar kuma za ki yi mata ne ko ya?". Abunda na sani Kulu bata magana dan haka ko a yanzu da idanuwana ke rufe banji fitar muryarta ba da amsar maganar Gwaggo, haka kuma maganar da Gwaggo tayi bana da tabbacin da ita tayi, dan magana ce da aka alaƙanta ta da masu hankali bata mahaukata irinsu Kulu ba, to amma sai dai kuma me? a ɗazu dana farka bayan Gwaggo da Inna da Kulu babu wani bayan ni, ko kuma wani ya shigo bayan rufuwar idanuwana ne?, lokaci ɗaya nasa shakku akan maganar Gwaggo, duk ta yanda naso nayi wani tunani akan lamarin sai na kasa, saboda yanda kaina ke sarawa. Har yanzu zuciyata na cikin fargabar laifin da nayi wanda ban sani ba, da kuma taraddadin hukuncin da zan karɓa daga wurin Gwaggona, saboda haka ne na kasa buɗe idona nayi kamar ina bacci, duk maganganun da suke yi inaji, har lokacin kuma da naji ana batun yi min allura, ai lokaci ɗaya tashin hankalin da nake ciki ya ninku, na ƙara rumtse ido gam ina jin kamar kar na buɗesu, alokacin da naji an ɗaure min hannu da igiyar roba na ƙwallara wata ƙara na miƙe zaune babu shiri ina neman hanyar guduwa, Gwaggo ta buga min wata uwar tsawa da ta saisaita hankalina, hawayen da ke maƙale cikin idona suka shiga zuba kafin na ɓare baki na fashe da kuka. Duk da idona rufe suke amma yanda naji an jawoni zuwa ƙirji an rungumeni ya bani tabbacin Inna Amarya ce, bayana ta-ke shafawa tana min magana cikin sigar lallashi, daga can inda Gwaggo kuma ke zaune naji ta kuma ɗaga murya acikin faɗa tana cewa,"wai ba za ki yi ki mata bane kin wani yi tsaye kanta kina kallonta, ke ni nafa gama ganeki, babu wani abu da kike so a yanzu fa-ce baƙin cikin da ke daskare a zuciyata ya ƙarasani, idan kuma na ƙarasa wallahi kece sila, hakkina kuma ba zai barki ba". Ban san dawa Gwaggona ke wannan masifar ba, dan a ƙanƙame nake da Innata, ta kauda kaina ɗaya gefen ta yanda ba zan kalla allurar da za'a min ba, sai dai naji tausayin koma wanene Gwaggo kema wannan masifar cikin hargowa da ƙaraji. Ban aune ba naji shigar tsinin allura a hannuna, na kurma uban ihun da saida Innata tasa hannu ta rufe min baki, kuka nake wiwi ina kiran sunan Baba da Ya Kabiru da Ya Amadu, acan ƙasan maƙoshina kuma ina jera Allah ya isa ga wanda yay min allurar, a hankali nake sauke ajiyar zuciya Innata na aikin ban haƙuri da lallashi, har sanda bacci ya ɗaukeni ba tare dana sani ba. Dawowar Malam daga wurin aiki ya wuce ɗakinsa, inda Inna Zulai wadda girki ke hannunta ta tarbeshi da kyakykyawan abincin da ta dafa na dambun acca kasaancewar Malam ma'abocinsa ne, zaune suke su na taɓa hira shi da ita, tana sanar masa da zancen maganar auren saurayin Sadiya da yake so a bashi izinin turowa. Gwaggo ta shigo bakinta ɗauke da sallama, cikin ladabi ta duƙa tana miƙawa Malam baƙar leda me ɗauke da takardu aciki. "gashi ɗazu Liman ya aiko Muntari ya kawo yace a baka". Malam ya buɗe ledar, takardu ne guda uku kowanne da rubutu ajiki, ya dudduba ba dan ya san meke rubuce aciki ba. Ya mayar cikin ledar ya ɗaure sannan yace,"to Madallah bari na ajiye idan yaran nan sun dawo sa duba muji mene ƙunshe a ciki". "yayi kyau". Gwaggo ta faɗa tana yunƙurawa zata miƙe ta fita

Chapter 5 of 52