nasa ne yake masa kwarjinin, da kuma shakkar aikata masa abin da yake niyyar yi.
"Dad kuje kuyi gaggawar abin da ya kamata ga gawar tasu, sannan kuma ku dawo ku karɓi addinin da nake a cikinsa yanzu tun kamin ƙurewar lokaci, domin ita mutuwa bata da notice, ni kuma ba zanso ace duk na rasaku a wannan addini na ƙarya da kuke ciki ba". Dad ya ɗaga hannu zai kai masa mari sai ƙarar wayarsa ya dakatar da shi, ya zura hannu a aljihu ya ɗaukota kuma dai-dai lokacin da kiran wayar ya katse, sai dai saƙon da ya biyo bayan wayar shi ya ɗan dakatar da shi yana kallon lambar wayar da aka turo saƙon da mamaki, da kuma abin da saƙon ke ɗauke da shi, "Akila bint Tamim". gajeren saƙo ne, kuma gajeren saƙon da ya girgiza duniyarsa gaba ɗaya, a fili ya maimaita sunan ba tare da ya sa ni ba. kenan mafarkinsa zai tabbata?, idan bai manta ba sau uku kenan yana mafarkin sun ƙara gauraya da su a wata duniyar, ai shi a tunaninsa tun da ya binne wannan hotunan nasu kamar ya rabu da ƙayar tunaninsu ne, amma ya akai haka?, lambar nigera!, kenan tun san da suka rabu da Akila tana ƙasar nan bata koma gida ba kamar yanda ta faɗa musu?. sai ya lumshe ido ya shaƙi wata iska me zafi, ƙarar saƙon da ya kuma shigo masa shi yasa shi buɗe ido zuciyarsa na me wani irin harbi. yay swapping ɗin wayar ya shiga whatsapp account nasa, ya duba lambar farko da saƙon da ya shigo masa, ya kuma buɗe hoton da tun kamin ƙarasa buɗewarsa zuciyarsa ta raya masa hoton ƴarsa ce. kamar yanda ya zata, hoton na gama buɗewa sai ga hoton Akila da Mairo, hoton Mairo shi yafi girgiza shi har ya kusa faɗuwa a ƙasa, sannan saƙon da ya biyo ƙasan hoton a yanzu yasa shi saurin dafe bango.
_"tsawon shekara goma sha takwas kayi biris da mu. naso ace na ɓoye amma hakan sai ya faskara, a yanzu ƴarka ta buƙaci sanin wane ubanta, kuma na faɗa mata, ta kuma ce sai tayi shari'a da kai, dan haka Major ka shiryawa abin da zai biyo baya. Ƴata zata ɗaukar min fansa, zata lalata duniyarka kamar yanda ka lalata mana tamu"._ sai yasa yatsansa ɗaya tun daga kan goshinsa har kan hancinsa, shikenan abin da yake gudu zai faru, komai ya zo ƙarshe, girmansa! mutuncinsa! ƙimarsa!, shikenan za su zube ƙasa wanwar kamar yanda yake ta jimamin faruwar hakan tuntuni. shi yasa tun a wancan lokacin, yay yay da Akila ta haƙura su kai yaran marayu, ta yanda ko da sun girma ba za su nemi iyayensu ba tun da sun san rashin gata ne ya kaisu wurin, kuma ko da watarana sun buƙaci iyayensu, amsa ɗaya za'a ba su ita ce ba'a sansu ba, shikenan asirin kowa ya rufu, ko kuma kaman yanda Aaliya tace ma ta a yasar da su to amma da yake ita tafi Aaliya kafiya, sai taƙi, tace sam ita ba zata iya ɗaukarwa kanta wannan babban zunubin ba, wannan rashin imani har ina, a haifi jarirai sannan a zubasu a leda aje a watsar. ya ƙara kallon lambar wayar da kyau, sai yabi bayanta da kira, sai dai daga can kamfanin layin MTN maimaita masa suke da cewar babu network, saboda haka yace da Al-Mustapha ya ba shi wayarsa, ya miƙo masa. sai dai ga tsananin mamakinsa ko da ya rubuta numbar a wayar, sai yaga sunan Sectary ya bayyana, wato Ahmad Adam Bichi. aikin Amadu ne, dan tun bayan da suka kawo Kulu asibiti, ya tuna labarin da ta basu, ya ɗau aniyar sai ya girgiza Major, sai ya saka masa tsoro a wannan zuciyar tasa ta rashin imani. dalilin da ya sa ya ɗauki hoton Kulu kenan da Mairo ya turo masa, tare da wannan saƙon.
*A Ɗaya Ɓangaren.*
saukar jirginmu a airpot ɗin Malam Aminu Kano mu ka fito hannuna na cikin na Al-Hassan yana riƙe da ni, tun bayan wasu daƙiƙu da tasowar jirginmu daga can Qatar na ke zubar da hawaye, hawayen da har yanzu suka ƙi tsayawa. Mami na gaba muna biye da ita a baya har mu ka ƙaraso bakin farar motar da aka zo ɗaukanmu, sai dai a san da aka buɗewa Mami murfin motar zata shiga a sannan na zube gwiwoyina a gabanta, cikin amon muryata da ta gama raunana, cikin sautin muryar da ke fitowa da rawa, cikin sautin muryar da zuciya ta ke a karaye, cikin sautin muryar kuka, na tattaro busassun yawun bakina da suka ƙafe na shiga roƙonta.
"Mami dan Allah kiyi haƙuri, dan Allah kiyi haƙuri kar naje wajen police, wallahi ban san a inda zan nemo kuɗi na biya Ya Kabiru ba, kuma idan naje wajensu tsare ni za su yi su kaini prison". kaina na ƙasa nayi maganar, inda ƙwayar idona ke a kan doguwar farar ƙafarta me ɗauke da zara-zaran yatsu. a jikina naji kallon da ta ke bina da shi, tsawon daƙiƙa 1,2,3,4, bata ce komai ba, ko ba'ace ba nasan nazari ta ke, haka zuciyata ta faɗa min, cikin wannan ƙunar da ke zuciyata, ta cikinsa naji gilmawar furucin Al-Hassan da ya ce da ita,"Please Mami, ki min alfarmar idan mun je wajen Kabir ɗin ni zan biya shi kuɗaɗensa". shirunsa ya haɗu da maganar da nayi,"balle ma ba zai taɓa cewa na biya shi ba". sai kuma Mamin tace,"sanin cewar ba zai ce ki biya shi ba shi yasa kika sata kenan?". nayi saurin girgiza kaina da sauri,"a'a wallahi Mami, ba haka ba ne, sharrin zuciyata ne". sai ta ƙara cewa,"to ni ba ɓarauniya bace, dan haka ba zan yarda na haifi ɓarawo ba". sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin,"Mami wallahi tallahi ban taɓa sata ba, ban taɓa ɗaukar abin wani nayi amfani da shi ba, yanzuma tsautsayi ne, dan Allah kiyi haƙuri kar naje gaban ƴan sanda".
zuƙar nunfashi ɗaya tayi sannan tace,"ku shiga mota mu wuce". dai-daituwar zamanmu a motar Al-Hassan yasa handky ɗinsa yana goge min hawayena, muryarsa a hankali ta fito ta cikin shirun motar.
"ba za ki daina kukan ba kuwa". amon muryar ya fito da sautin nuna damuwa da kulawa. nima muryar tawa ta fita a hankali wajen ce masa,"zan daina, amma sai Ummi tace ta yafe min abin da nayi ma ta tukunna". sai yace,"bana tunanin Ummi zata ƙi yafe miki akan wannan laifin da nasan ɗan ƙarami ne a wurinta, abin da kullum Mami ke faɗa min shi ne; Umminka tana da haƙuri, tana da kirki, kuma ƴar aljannah ce insha'Allahu".
na fesar da wata iska daga bakina, tare da sauke gajeran numfashi, dukkan tunanina ya tafi kan rayuwata ta baya kamin na san komai a yanzu, lokacin da na girma na fara wayo, zuwa lokacin da na mallaki hankalin kaina, bakin Ummina a rufe yake da yin magana, idanuwan nan kullum akaina su ke cike da so, ƙauna da tausayi. ta takure kanta a waje ɗaya, a cikin ƙunci da damuwa, ta hana kanta walwala balle ta sawa kanta jin daɗin rayuwa, a gida ɗaya mu ke rayuwa, tana so ta kasance tare da ni, amma gudun halin da zan shiga idan naji wace ni, ta haƙura ta nisanta kanta da ni, ba don komai ba sai don saboda naji daɗin rayuwa, ta fara tsufa tun da sauran ƙuruciyarta kuma wai duk saboda ni. amma na rasa da me zan saka mata sai da waɗannan kalamai na rashin tarbiya, na rashin ɗa'a, na rashin ya kamata. ko da yake ba laifina ba ne, i was very shock a lokacin da naji cewar ni ƴar zina ce, shi yasa na kasa controlling zuciyata, amma wallahi ba da son raina ba, nayi nayi na lanƙwasa zuciyata amma sam na kasa saboda tafi ƙarfina a lokacin, tabbas na aikata babban kuskure, na aikata abin da nake yin nadamar aikatawa a yanzu, amma ko kaɗan, ko kaɗan na san Ummi bata cancanci abin da nayi mata ba, uwata ce, ko a ya ta sameni ya akamata ace na martaba ta, duk lalacewarta sai na bita zan shiga aljanna, sai na bita zan samu rahmar ubangiji.
to wai ma aina na dinga samo waɗannan ƙazaman kalamai da na dinƙa jifanta da su ne?, ko da yake kamar yanda na faɗa ba laifina ba ne, zuciyata ce, sharrin shaiɗanne, babban tashin hankalina a yanzu bai wuce idan na tuno wannan barazanar da ke shimfiɗe a ƙwayar idon Mami sai naji kamar na haɗiyi zuciya, a yanda na ke bana taɓa tunanin Ummi zata iya yafe min abin da nayi mata, ga Al-Hassan ya tabbatar min da Mami bata barazana, tana faɗar abin da tasan cewar zata aikata shi ne, kuma sai ya tabbata, bata da haƙuri ko kaɗan, mafaɗaciya ce, tana da kafiya, cijiya, taurin kai akan abun da ta ƙudurta. shi yasa a kullum kuma a ko da yaushe alƙawari ya ke biyo bayan furucinta...to ni kuwa Maryam idan haka ne na shiga uku, dan tabbas nafi kowa rashin dacewa a duniyar nan. sai kalaman Al-Hassan su ka shiga haskawa a cikin kaina, a wannan lokacin da muna cikin jirgi, lokacin da Mami ta tashi ta koma seat na daban don gudanar da aikin office ɗinta a cikin system, Al-Hassan ya shiga toilet ya fito, da ya zo wucewa ta gabana ne ya tarar da ni ina zubar hawaye, idanuna a rufe su ke a lokacin saboda haka har ya tsuguna a gabana ban sa ni ba sai da naji yana faɗin.
"a rayuwata hawayen mace yana ɗaga min hankali, ki tambayi Mami nah kiji, yanzu-yanzu hawayen mace zai hargitsani, ya kiɗima ni, ya gigita ni, saboda haka ki taimakeni ki goge su.
shin ma me akai miki a duniyar nan da har kike zubar da hawaye masu gudu irin haka?". ban amsa masa ba illa iyaka buɗe nauyayyun idanuwana da nayi na saukesu a kansa ina binsa da kallo kawai, ina kallonsa da hoton fuskar Al-Mustapha, naga lokacin da wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa kafin ya ƙara buɗe baki yace min.
"Mami bata taɓa yi min wata magana da wasa ba, duk abin da ta faɗe shi to haka yake da gaske. shi yasa ko a yanzu da ta faɗa min kece ƙanwata banyi tantama ba na amince da hakan, duk da zuciyata tana cike da mamakin ta yanda akai ta sameki bayan tsawon shekaru goma sha takwas da aka ɗauka, alhalin kuma tun kina jaririya rabonta da ke da mahaifiyarmu, sai dai da nake kallonki yanzu zuciyata ta kore duk wani tunani da kokonto, na ƙara amsar maganarta, duba da kamanninki, kamanninki zam irin nasu ne, siririyar fuska kawai kika fisu".
sai nace da shi,"yanzu kai kenan baka damu da ta hanyar da aka bi aka haifemu ba?, ka ganka fa hankalinka a kwance, ko baka san komai ba ne?". murmushi me ciwo naga yayi da ya tsaya iyakar leɓensa, kafin ya bani amsar,"na san da cewar ba ta hanyar aure aka haifeni ba, na san da wannan tun ban ma san me hakan ke nufi ba har zuwa san da na girma na san ma'anar kalmar zina, na san ta wannan hanyar aka bi aka haifeni, kuma bayan haihuwar tawa mahaifiyata ta gudu ta barni saboda kunyar duniya. kin san a lokacin da Bella ta tareni da wannan maganar me nayi?". da mamaki na zaro ido waje ina tambayarsa,"ai na kasan Bella kuma?".
"Bella Kaka ce a wurinmu. kuma ita ta shaida min waye ni, a wannan ranar da ta faɗa min kwana nayi ina aikata abin da ban taɓa yunƙurin yinsa ba a rayuwata, kwana nayi ina shan abin da Allah ya haramta saboda baƙin ciki, idan da ace giya na yin tsiro da yanzu tayi rassa ajikina. to amma daga baya da Abi yay min nasiha akan karɓar ƙaddara sai naji zuciyata ta washe. duk da cewar sai da Mami tayi min barazanar yankani idan na kuma yunƙurin shan giya ko kuma na kuma furta zan shiga duniya balle na furta kalmar ɗaukar fansa akan Aaliya, ba barazana ta ke min ba, zata aikata ɗin kamar yanda ta faɗa. ta kuma gwada na gani, dan sai da ta nuna min, domin ba don zuwan Umm wajen ba a lokacin da ta kwantar da ni ta ɗora wuƙa a wuyana tsab sai ta yanka maƙogorona na zama tarihi". furuncinsa na ƙarshe yasa na saki guntuwar dariya da ban san lokacin da nayi ta ba, da mamaki nace da shi,"yankawa dai!, ita Mamin sai ta yanka ka?, wace kalar mata ce ita ne?". tashi yay daga tsugunen da yake ya zauna kujerar kusa da ni yace,"idan aka tashi rubuta sunan masu faɗawa da cikawa to sunan Mami ne zai zo a farko. haka kuma tana sahun masu zafin zuciya, irin zuciyar da bata son wargi. uwa ce ita me daɗin sha'ani, amma kuma sam bata tolerating wani iskanci daga kowaye ba ma yaro ba".
nayi shiru ina nazarin kalamansa, kamin na jefa masa tambayar, "to dama su biyu ne da gaske?". sai ya juyo ya kalleni,"ba ki sa ni ba dama?". kaina kawai na ɗaga masa ba tare da bakina ya furta komai ba.
"twins ne su kamar yanda muke, ba su da wani banbanci a kamannin halittarsu, sai dai kuma a halayya da ɗabi'u. Mami ita ce ƙarama, wadda ta haifemu kuma ita ce Babba me suna Aaliya". "Aaliya kuma?". ya jijjiga min kai tabbacin amsata. sai na shiga girgiza kai ina faɗin,"ya ake neman a rikita min lissafi ne. wadda na tashi a wurinta fa tace sunanta Akila, ita kuma Mami tace min sunanta Aaliya. kai kuma yanzu kana ce min Mami ce Akila, ya haka kenan?". sai yace,"nima a ɗazu da na fuskanci tana kiran waccan da Akila na shiga cikin duhu, kuma Mami ba me son yawan tambaya bace shi yasa kika kalla nayi shiru, amma har zuwa yanzu kaina a ɗaure yake da sunan da ta kira waccan". sai kawai na zuƙi wani numfashi kamin na furta,"to ni dai kome za'ai ba zan fasa ɗaukar fansar shegantani da akai ba". na faɗi hakan har zuwa lokacin zuciyata bata rissina ba. sautin murmushin takaicinsa na jiyo ta gefen kunnena tare da cewar"a kanwa za ki ɗau fansar?". ina rumtse idona nace da shi,"akan Akila da Major, Al-Hassan idan kai ka yafe wallahi tallahi ni ba zan taɓa yafewa ba, sai na ɗauki fansar rayuwata akansu, sai na saka su kuka fiye da wanda suka sa ni, sai na saka sun wulaƙanta a duniyar nan, wannan alƙawarina ne".
sai yay saurin katse maganar tawa ta hanyar rufe min baki da tafin hannunsa,"shhh, Hussaina waɗannan kalaman fa har ina?, ina kike so ki kai ɗumbin zunubi?. to bari na faɗa miki abin da haƙuri bai bada ba rashinsa ba ya taɓa bayarwa, kuma ai idan hankali ya gushe hankali ake sawa ya nemo shi, nima nayi irin waɗannan kalaman a san da aka faɗamin ni ɗan zina ne, amma da na sami tarin nasihohi da wa'azi daga bakin Kakana Shaik Samin, kuma na zauna nayi nazari da tunani sai naga ɗaga hankalina ma nace sai na ɗauki fansa babu abin da zai haifar min fa ce ƙara dagula rayuwata...Hussaina wallahi Allah yana sonmu da Rahma, idan ba ki san da wannan ba to ki sa ni a yanzu, Allah yay mana ni'imar da bai kamata mu butulce masa ba. kina ina!, kina ina Hussaina ake haifar irinmu a watsar da su, wasu kuma asa su a kwalin indomi a rufe, wasu kuma asasu a masai ayi floshing ɗinsu, wasu ma su na jarirai shagaf a kashesu, kije gidan marayu ki kalla irinmu sunfi a ƙirga, waɗanda ba su san iyayensu ballantana danginsu, wasu kuma su na nan su na gantali a duniya cikin ƙasƙantacciyar rayuwa, bakin duniya na binsu...amma mu da ubangiji ya tashi, sai ya rufa mana asiri, bai sa mun wulaƙanta ba, bai sa mun tozarta ba, bai sa mun ɗanɗani wannan ɗaci da baƙin cikin a zuciyoyinmu ba tun muna ƙanana, sai ya barmu a cikin gatanmu, ya barmu a cikin ni'imarsa, to kuma dan me zamu butulce masa Hussaina?...Hussaina babu macen da zata so ace ta haihu bata hanyar aure ba, haka ma banda ƙaddara babu abin da zai sa mahaifiyarmu ta samar damu ta wannan ƙazamiyar hanyar, na sami tabbacin hakanne ta irin shaidar da mahaifiyarmu ta samu daga wajen mutane, idan har kuwa haka ne akan mene ba zamu yi mata uzuri mu yafe mata ba?, mu tayata goge wannan ruwan hawayen baƙin cikin da ta jima tana yinsa tun bayan zuwanmu duniya...a barshi ma da gangan tayi, amma shin ko kin san wannan lamarin tsakaninta ne da ubangijinta, kuma da zarar ta roƙe shi zai yafe ma ta, to idan har shi zai yafe ma ta dan me mu ba zamu yafe mata ba?, kuma da kike ikirarin sai kin saka sun wulaƙanta, to ki nutsu da kyau, ki sakawa zuciyarka salama na lokaci kaɗan, sai ki dawo da hankalinki gareni". a wannan lokacin sai yay shiru, ni kuma sai na ɗan kalle shi, fatarsa tayi jaa, manyan idonsa irin nawa sun yo waje, alamun dai shi ma tasa zuciyar a cunkushe take da tarin baƙin ciki, dauriya kawai yake yi. na sauke numfashi na bar kallonsa, a hankali na rufe idona, na zuƙi doguwar iska kamar yanda yace, sannan na fesar, sai da nayi hakan har sau uku kamin na shiga biya kalmar, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil". ashe a fili na faɗa, ba'a zuci ba kamar yanda nayi tsammani, sai naji Alhassan na ce min,"yauwa, kiyi ta maimaita hakan a fili, akan laɓɓanki da kuma cikin zuciyarki".
wucewar daƙiƙa 1,2,3,4,5 sai naji wani sanyi na daban yana ratsa zuciyata, kuma sai naji Al-Hassan yaci gaba da cewa,"to ki faɗa min shin za ki so ace mahaifiyarki ta wulaƙanta a duniya?, shin za ki so yau ace mahaifiyarki ta tozarta?, to idan ma kinyi hakan ke mene makomarki? kuma mene ribarki?...haba Hussaina, yanayinki bai yi kama dana yarinyar da bata da ilimi ba, ko kuma bata sami tarbiya ba, idan ace tunaninki ya gushe, to ina iliminki fa?, ki tattaro hankalinki wuri ɗaya ya dawo miki da iliminki, wannan ilimin naki ya tuna miki cikin rukunan musulunci akwai yarda da ƙaddara me kyau ko mara kyau tare kuma da fawwwalawa Allah komai. sannan ilimin naki ya tuna miki faɗar Allah SWT da yake cewa, "kuyi haƙuri, haƙiƙa ubangiji yana tare da masu haƙuri, kuma yace ku zama masu afuwa ga wanda ya saɓa muku, haƙiƙa ubangiji me afuwa ne". Fansa! Fansa dai! Hussaina idan har za ki tuna wannan faɗin na ubangiji to ki faɗa min mene amfanin ɗaukar fansa?, kuma ma abu mafi muni da tashin tashin hankali ɗaukar fansar akan uwa, wadda sai ta ɗaga miki digadiganta ne tukunna za ki samu wucewa zuwa aljannah. Macen da ita ce ma'aiki ya faɗeta har sau uku kamin ya ambaci uba, Uwa Hussaina, Uwa ba'a bar wasa ba, ki shiga hankalinki, ki kuma shiga nutsuwarki, domin ɓacin ranta shi zai kai ki wuta, hawayenta kuma ya turaki jahannah. shin ni kin san tsawon shekara nawa na ɗauko ina roƙon Allah ya haɗani da ita, na jingina a kafaɗunta, na goge mata dukkan wani datti na damuwa da ke cikin ranta, na maye ma ta gurbinsa da farin ciki, ba don komai ba sai dan kwaɗayin wannan ɗumbin ladan na kyautatawa iyaye. to wallahi Hussaina indai ba so kike ki ɓata lahirarki ba? tun wuri ki tuba, yo zunubin ki kai shi har ina?, kiyi ƙoƙari ki gyara lahirarki tun wuri, kuma tun lokaci bai ƙure miki ba, mutuwa na nan zuwa, ko ta ɗauke ki ko ta ɗauke Mahaifiyarki...Hussaina dukanmu masu laifi ne in one way or the other, kuma a kullum burinmu da fatanmu shi ne a yafe mana, kiyi tunani, ki ƙara tuna wannan girma da darajar na iyaye kamin ki zartar da hukunci".
tun da ya soma maganar naji numfashina yana yin sama sama da har ta kai ga na gagara wajen in fesar da shi, ƙwaƙwalwata kuma naji tana bugawa da wani irin duka dum dum, kaina ya cushe gaba ɗaya.
"kice astagfirullah, kiyi istigfari ko kya sami sauƙi a zuciyarki, dan wallahi wannan mummunan ƙudurin kaɗai da kika ɗauka ba zai barki jin daɗi ba". Alhassan yace da ni a sanda ya lura da yanayin da nake ciki, kuma cikin wata iriyar murya da ba zan iya kwatanta yanayinta ba na shiga faɗin,"Astagfirullah, Allah na tuba, Allah na tuba". faɗa nake ina ƙara maimaita, a lokacin babu a inda nake so na ganni illa agaban Ummi nah, babu abin da idanuwana ke son gani sama da Ummi nah, ita kawai, ita kaɗai don inje in nemi yafiyarta.
a hankali na shiga buɗe idanuna ina mai jin zuciyata a matse, na sauke idona akan titin da muke cikin go slow, sai naji Alhassan na saka min earport a kunnena, suratul yusuf ce ke tashi cikin ƙira'ar Shuraim, a hankali sai naji ina samun nutsuwa.
"ranki ya daɗe gamu mun shigo garin bichi". security ɗin da aka haɗa Aaliya da shi ya faɗa, yana daga gaban motar a zaune. sai tace da ni,"ke gamu a garinku, sai ina?". na buɗe idanuwana na sauke su a cikin garin bichi, garin da na fita da niyyar barinsa har a bada, na haɗiye abin da ke dunƙule a maƙogorona sannan nayiwa driver ɗin nuni da hanyar da zai ɗauka. tsayuwar motarmu a ƙofar gida na riga kowa buɗe murfin motar, Mami na fitowa abin da bakinta ya furta shi ne,"anan Akila ta ke rayuwa?". na ɗaga ma ta kai kawai, sannan na wuce zuwa cikin gidan. a tsakar gida na sami Inna Zulai da Adawiyya da Sadiya da Zubaida, kuma dukkansu sai suka miƙe a razane saboda ganina kamar wacca aka jefo.
"Mairo". Inna Zulai ta faɗa, Adawiyya ma da ke dafe da ƙirji tace,"me kika dawo yi? hankalin kowa ya tashi anata cewa kin gudu kema kin shiga duniya". na sharesu na wuce zuwa ciki, dan bata su nake ba, hasalima a yanzu bana son wani abu wai shi ɓacin rai, sai dai ƙofar ɗakin Gwaggona a rufe da kwaɗo, saboda haka na dawo nace da su,"ina Ummina?". da mamakinsu su ke tambayata,"wace kuma haka?". "Babata ta ainihi". Inna Zulai tace,"ohh ai tun jiya da suka wuce asibiti basu dawo ba, ɗazun nan ma Kabiru yazo ya ɗiba kayanta wai an basu kwanciya".
"innalillahi kwanciya kuma, a wane asibiti?". "asibitin bichi, za ki je ne?". kamin na basu amsa sai ga Mami ta doko sallama, kuma kafin wani cikinsu ya amsa Inna Zulai da ke daga bakin ƙofa tace,"ikon Allah ba dai ma su ne suka dawo ba, kinji maganarta ƴar halak". sai nace,"ba ita bace". "amma kuwa maganar zam ita...wa'alaikum salam, shigo". Innar ta faɗa tana dawo daga inda nake tsaye tana leƙan zaure, a tsorace kuma taja da baya tana dafe ƙirji kamar wadda taga mugun abu,"na shiga ni Zulai, Kulu kece haka?".
na ƙara bata amsa da,"ba ita bace Innah, ƴar'uwarta ce". sai ta kalleni tana ƙifta idanu da cewar,"me?, ke kinji yarinya zata manna min hauka...Kulu yanzu da gaske kece a cikin wannan shigar ta alfarma, a'a ke ni nama kasa ganewa, kamar fa ba wadda ke kwance hajaran majaran ba". na sake cewa da ita,"Innah wannan ba Kulu bace". nayi ƙoƙarin kallon Mami da ke bin gidan namu da kallo, sai na kasa saboda kwarjinin da ta ke da shi me kassara kallon mutum.
kaina a ƙasa na shiga mata bayanin cewar tana asibiti, a kiɗime tace da ni muyi waje, a cikin sakan ɗaya nema ta ke ta firgice daga jin batun rashin lafiyar ƴar'uwarta. direct bichi general hospital muka nufa, muna zuwa muka ji batun cewar jikin nata yay tsanani an turasu asibitin AKTH. hankalinmu duk ya ta shi, ban ankare ba naji saukar wani gigitaccen mari a saman fuskata.
"duk da ace ba ki gudu kin barta ba da ba ta shiga wannan halin ba". kuka nake sose kuma micijin da na gani ta wajen ƙafata shi yasa na razana na doka tsalle zuwa bayan Alhassan na maƙalƙale shi ina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 52