Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ashraf ke zolayata akan ko shi za'a bar min kawai, nace,"tabɗi me zanyi da takalmin Jawad, duk da yayi min kyau amma bana so, a sayo min sabo irin na ƴan'uwana". Ni da ƴan'uwana mun yi murna sosai da irin kayan da aka bamu, kayan da bai zama lallai ɗan wani mai kuɗin ma ya mallakesu ba cewar Ya Kabiru, ni a ɓangaren kayan zaƙi da aka haɗa mana ma babu ɗaya da na taɓa cin karo da su a rayuwata, ina jin Ashraf na faɗin ai bamu za muke girki da kanmu ba makaranta ce take dafawa, hasalima ko yaji aka kama mu da shi sai an ƙwace kuma sai an horar damu, saboda haka a kula, ya kuma ƙara jaddada mana da cewar duk wani abu da muke da buƙata ko kuma aka buƙata a makaranta mu kira Suhail. Ko da aka zo ɓangaren cike takardun makaranta Suhail yace sam ba za'a saka min Mairo Adamu ba kamar yanda Ya Kabiru ya faɗa, yay ta masa tsiyar idan shi ɗan kauye ne sai akace masa kowa ma zai zauna a irinsa ne, dan haka ya maida min da Maryam Adam Bichi, Adawiyya ma Jakadiyya tace ai Rabi'a ne asalin sunanta, dan haka ita ma Suhail bai sanya mata Adawiyya ba, Rabi'a Adam Bichi shi ne sunanta kamar yanda ya faɗa, Habiba kuwa sunanta ne dama aka saka mata. Na ɓata fuska na tubure akan cewar ni dai a maida min da sunan da Babana ya raɗa min, bana son wani Maryam, Ashraf yace to ai ko wurin Baba akaje zai ce Maryam shi ne usulin sunana ba Mairo ba, Jawad da ke gefe yana aikin latsa waya yake faɗin haka za'a kaini makarantar ƴan gayun ina masu ƙauyanci, Na harare shi ta ƙasan ido nace ina ruwansa, ni kaina daga irin kayan da naga an haɗa mana da irin yanda Ashraf ke lissafowa Ya Kabiru doka da ƙa'idojin makarantar nasan cewar ba irin gajigari-gajigari bace, makaranta ce babba. Bayi huɗun da Jakadiya tasa aka kira mata su ne suka ɗebi akwatunnan kayan da bakko suka fita da su zuwa mota. Naso ace kamin fitowarmu na ƙara ganin Ammi, dan lokaci ɗaya naji matar ta shiga raina, ina kuma sonta da tausayinta tare da son kasancewa tare da ita, dan wallahi duk wannan murna da zumuɗin da nake akan nuna mana kayanmu gaba ɗayan hankalina yana can kanta da son sanin yanayin da take ciki ayanzu, da kuma son ƙara ganin fuskarta dan tabbatar da ganina wanda nake jinsa matsayin hasashe ko gizau. Lallai Masarautar bichi da girma take, dan baki ma yayi kaɗan ya misalta girmanta saboda gari ce guda. Tun da muka fito haraba nake bin masarautar da kallo da burgewa, komai nata mai kyau ne da ƙawa, tsaruwarta har ɗaukan ido yake. Jefa idanuna nake ta ko'ina ina duban Bayi da Kuyangu da ke kai komo a ayyukansu, ƙwarai ne tun daga waje zaka gane tabbas an narka dukiya wajen tsara masarautar balle kuma ka shigo daga cikinta, idan ma ka shigo matsayinka na baƙo zaka kasa tantance wacce ƙofa zaka sada kanka saboda yawan ƙofofinta. Muna nan tsaye a inda su Suhail suka barmu suka dawo muka ɗau wata doguwar hanya mai cike da shuke-shuken fulawowi masu ƙamshin gaske da sanyaya wuri, a lissafin da nai bayan ƙofar Ammi ta biyu da muka fita wannan da muka shiga itace ta shida, tafiya muke muna wuce fadawa da ke tsaitsaye tun daga shigowar get ɗin da kuma tsirarrun bayi dake kai komo, duk kuma ta inda muka gimla sai an duƙa anyi gaisuwa da kirari ga Suhail da Ashraf. Mun yi tafiya me nisa naja na tsaya dan tun ɗazu ƙafata ta gaji, nace da Suhail"Buzu wai ina zaku kaimu? ko Anan makarantar ta ke ne?". Ya waigo ya dubeni tare da bani amsar,"a'a ba nanne makarantar ba, nan ɓangaren Kakarmu ne Bella, zan kai ku ku gaisheta ne, kiyi haƙuri ai an kusa zuwa?". Na gyaɗa kai kawai Ya Kabiru ya kama hannuna yana ce min raguwa. a yanda na sani tuta a makaranta ne ake dasata, tun da akwai tutar najeriya a makarantarmu, to amma isowarmu gejin da zai sadamu da wata ƙatuwar turaka sai naga dashen tuta a ƙofar wurin daga ɓarin dama, ƴan sanda biyu na gadinta kowannensu riƙe da bindiga a hannu sun ƙame tamkar dasa su akayi, kalar tutar kore da yelo da ja, tare da kwalliyar tauraro a tsakiya me kalar yelo da shuɗi, na ɗauka tsawon daƙiƙa biyu ina kallon tutar da son sanin ko tutar wacce ƙasa ce, sai dai duk nacina na kasa saboda bata ɗaya daga cikin tutocin da aka koyar damu a makaranta. Cikin makeken falo na gaske muka sanya ƙafafunmu, falo me ɗauke da kayan sarauta ta ko'ina, ni da ƴan'uwana da muke baƙi muka shaƙi ni'imtaccen ƙamshin da ko a gidan waziri da suke gidan turare babu irinsa, da ace zan sami dama da babu abunda zai hana ni roƙar a sammin turaren, nima na kaiwa Gwaggona da Innata suke sawa a ɗakinsu, saboda duk wanda yaji wannan ƙamshin yasan ƙamshi ne na musamman, yanda nake ta zuƙar ƙamshin a hancina yasa na tuna da furucin Sadiya a wata rana, tace ke dai Mairo idan ba'a saceki a ƙamshi ba to za'a saceki a kyau, nai ƴar dariya kawai. A irin yanda kuyangun falon ke nutse da takatsan-tsan ɗin ganin sun cimma ayyukansu zaka fahimci cewar me ɓangaren bata wasa bace, wata tsohuwar mata ce zaune kan kujera irin ta sarauta me shilla mutum a hankali, tana kishigiɗe a jikin kujerar yayin da hannayenta duka biyu ke kan hannun kujerar ta ko wanne ɓari, idanuwanta na ɗauke ne da siririn farin gilashi, yayin da bayi kusan shidda ke tare da ita, biyu na tsaye ta bayanta su na mata firfita, biyu kuma na duƙe ne a ƙasa suna matsa mata ƙafafu, sauran biyun kuma na daga tsaye a gefen hannun damarta, ɗaya acikinsu tana riƙe da ƙaton faranti me ɗauke da kayan marmari, ɗayar kuma ita ce me ɗauka tana sakawa tsohuwar a baki wadda ke ci a hankali. lallai anan ake sarauta me cike da ƙarfin izza da ƙasaita, anan kuma usulin kyan halitta yake da ido ba zai so ɗaukewa daga kansu ba, gabana ya faɗi a san da muka haɗa ido da ita ta cikin gilashinta, na saurin ɗauke idona ina ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yayin da kuma hoton fuskokin mutum uku suka shiga haskawa a cikin idona, na haɗiye guntun yawu a maƙoshina sannan na nemi wurin da Suhail yay mana nuni na zauna . "Ranki ya daɗe barka da wannan lokaci". Ashraf da Suhail suka ce da ita bayan ta baro kan waccen kujerar da take ta dawo ta zauna akan wata kujerar ta daban, ta mayar masa da magana acikin yaren da ban san wane yare bane amma yana shige da larabci, sun daɗe su na magana da ita acikin wannnan yaren kamin Suhail yace,"Bella wannan sunansa Kabir abokina ne, waɗan nan kuma ƙannensa ne, sun shigo masarautar ne shi ne nace bari na rakosu wurinki ku gaisa, su na da mutunci sosai domin a gidansu muka sauka ranar da muka shigo cikin garin nan, an karramamu an mutuntamu a gidansu ba kaɗan ba". Suhail na rufe baki daga Ya Kabiru harmu muka rissinar da kai muna miƙa mata gaisuwa, bata buɗe baki ta amsa ba illa iyaka ɗaga mana kai da tayi, sannan naga tayi nuni wa Suhail da hannu, shi kuma ya dubemu yace an bamu izinin zama kan kujera, to a raina saina kawo ko tsohuwar bata magana ne, bebiya ce. Muna zama kan kujerar nayi zumbur na miƙe a zabure ina aikin zare idanu ina mammatsa hannuna tamkar mara gaskiya, nan kuwa tarin kunya ce ta lulluɓeni duba da yanda aka zuba min ido, Suhail da Ashraf suka haɗa baki wajen tambayata,"lafiya?". Ban basu amsa ba sai dana kalli su Adawiyya da ke kan kujera zaune lafiya, na mayar da kallona ƙasan ƙafata a san da wata baiwa tazo gabana tana tambayata,"me ya faru?". Nace musu,"babu komai, da na zauna a kujerar ne sai naji kamar zan faɗa ciki, laushinta yayi yawa". Takaici ya kama Adawiyya da Habiba dan ina kallo suka harareni, su a yanda suke zaune kamar ma sun saba da zama akan irin kujerar ne, akayi-akayi kuma na koma na zauna naƙi nace ni dai ba zan iya zama akai ba. "ƙaraso da ita nan". Cikakkiyar muryar tsohuwar ta ambata a lokacin da ta ɗago da dubanta kaina, tsoro da fargabar abun da zai faru ya kamani, nai saurin zube gwiwoyina ƙasa na shiga bata haƙuri. "dan Allah ranki ya daɗe kiyi haƙuri ki gafarceni, wallahi ba da gangan nayi ba, ban taɓa zama bane akan irin wannan kujerar mai kamar auduga, su kansu ƴan'uwan nawa sunyi ƙarfin hali ne, kiyi haƙuri dan Allah kar a hukuntani, ni ɗin ƴar ƙauya ce ɗiyar talaka". Sai dai kuma me, duk magiya da ban haƙurin da nake Bella bata ji ba, hasalima kanta na kan wasu takardu ne da rubutun ciki ke kamar jagwalgwalo, haka Baiwar ta kamo hannuna ta kawoni har gaban Bella, nasa hannu na goge ƴar guntuwar ƙwallar da ta sakko min, nayi wurƙi-wurƙi da idanu ina jiran tsatstsaraun hukuncin da za'a yanke min, dan na taɓa jin labarin gidan sarauta basa yin da sauƙi, tausayin iyayena ya kamani saboda halin da za'a jefasu aciki idan suka ji cewar masarautar ta kamani da aikata wani laifi. Bata ɗago ba har tsawon daƙiƙa biyun dana ɗauka gwiwona zube a gabanta, sannan ta kuma kallona muka haɗa ido gabana ya kuma faɗuwa saboda kamanninta, muryar nan tata me baƙuwar hausa tace da ni,"zauna akan wannan". Ta faɗi hakan tana min nuni da tum-tum ɗin da ke ƙasa gefen ƙafafunta, hannu na rawa na janyo shi na zauna ina rumtse ido, dan shi ma taushi ne da shi sai dai bai kai kamar kujerar ba. Wannan lokacinma ba da hausa ta yiwa Suhail magana ba, da yarensu ne. "taya ka san Kabir?". Yace da ita,"zuwan da muka yi ƙasar nan a wancan shekarar, muka raka Madaki masallacin liman a ƙauyen Saye. To anan muka haɗu da shi har muka taɓa hira dan mun jima tare, kyawun hali da nagartarsa dana karanta a lokaci ɗaya yasa nayi sha'awar haɗa alaƙa ta abota da shi, hakanne yasa a wannan zuwanma na kai masa ziyara, saboda lokacin da muka baro airpot Sarkin gida ya biya damu ta gidan Liman dan isar da saƙon Me Martaba, shi ne a lokacin tahowarmu nace da Sarkin gida ya tafi kawai zamu iso, da taimakon wani yaro ɗan gidan Ladan muka sami kwatancen gidansu, dalilin da ya sa ma muka kwana acan gudun faɗan Ammi kasancewar dare yayi, Bella su ɗin mutanen ƙwarai ne domin sun karramamu ba tare da sanin su wane mu ɗin ba". Bella ta jinjina kai sannan tace da Ya Kabiru,"na gode da karrama min jikoki da gidanku suka yi, haƙiƙa ina mutunta duk wanda ya karrama jinina, ina kuma kyautatawa agare shi, saboda haka ku saki jikinku daga yau ɗin nan acikin masarautar bichi ɓangaren Bella ku ƴan gida ne ba baƙi ba". Ta juya ta dubi kuyangar da ke tsaye kaina sannan tace da ita,"ace Jakadiya ta haɗo musu abun sakawa a baki". da sassarfa Kuyangar ta juya domin cika umarnin shugabarta. Bella kuma taci gaba da magana da Suhail, "kai kuma wane irin tukwici ku ka yi musu game da karramawar da suka yi muku?". "na faɗawa Ammi sai tace babu wani tukwicin ban girma da za'ayi musu har su kasa mantawa damu sama da ɗaukar nauyin karatun ƴaƴansu, yanzu haka zuwan nan da suka yi sun zo karɓar kayansu ne na tafiya makarantar kwana, shi kuma Kabir ta ba shi ɗaya daga cikin shagunanta dake cikin gari". "shagon ɗauke yake da kaya?". Ta tambaya, Suhail ya kaɗa mata kai,"a'a Bella, babban shago ne dai, zai nemi jari ya zuba". "zancen banza kenan, mutumin da ya bawa naka makwanci, ci da sha, ba kyara ba walaƙanci ai yafi ƙarfin wannan ƙaramar kyautar a wurinka...a yau ɗin nan a nemi kaya masu kyau da inganci a zuba masa a shagon, sannan a mallaka masa maƙullin gidan Hauwa'u da yake Estate ɗin Madaki, dama na gaji da ganin gidan a haka, idan auransa ya tashi ayi min magana...yayi karatun boko?". "ehh yayi yana da certificate na diploma akan aikin wutar lantarki". "masha'Allah, duk da su ɗin mutanen ƙauye ne amma basu bar kansu da duhun jahilci ba, Allah yaywa iyayenku albarka...Suhail a sama masa addmission a ƙasarmu abar tunƙahona". Ta dubi Ya Kabiru tace, "za ka iya zuwa ethopia kaci gaba da karatu?". Kan ya bata amsa Suhail ya amshe da cewar, "ai Bella burinsa kenan yaci gaba da karatu sai dai rashin dama". Tace, "to a mayar da gurbin addmission ɗin da Fawwaz ya samu a matsayin nasa, ina so jirginsa ya ɗaga a ƙarshen wannan watan". Ya Kabiru bai san sanda ya zube gwiwoyinsa ƙasa ba ya shiga jero tarin godiya gareta, Sai dai baija da nisa ba Jakadiyar da ta shigo kamar an jefota ta zube tare da dakatar da shi, "Bella tana yi ne domin Allah, bata son godiya, kayi shiru da bakinka a wurin nan idan kuma baso kake ka fuskanci wani hukuncin ba". Ya Kabiru ya jinjina kai alamar yaji, farincikin da yake ciki na daɗa bayyana a saman fuskarsa, kamin ya kada baki yace,"tabbas duk wani me aikin alkhairi domin sarki rabba baya son godiya sai adu'a". Aiko nan ya shiga yiwa Bella adu'oi ita kuma tana mai murmusa fuskarta da alama tana jin daɗin adu'ar. Ta ɗau tsayin wasu daƙiƙu tana kallona ba tare dana sani ba, sai a yanzu dana bar kallo ga Ya Kabiruna na dawo da shi gareta, muka haɗa ido da ita ta sakar min siririn murmushi ni kuma nai saurin sauke kai ƙasa ina wasa da yatsuna. Na jiyo muryarta tana cewa,"Ashraf ba dan na san duka ahalina ba, da sai nace Maryam jinina ce". Taci gaba da kallona tana ci gaba da faɗin,"idan kayi mata duban tsanaki akwai wasu kamanni sirrantattu irin na jinina a tare da ita". Ta sauke numfashi kana tace,"ina ma ace ke jinina ce Maryam da naji daɗi, kema kuma da kinji daɗi, za kiga gata da ƙauna daga wurina, za ki mo re jin daɗin rayuwa, tun shigowarki a kallo ɗaya naji ina sonki". Ta dubi su Adawiyya tace, "kuma fa ina sonku, amma naji nafi son Maryam". Ta kamo hannuna ta haɗe da nata ba tare da ta ji ƙyanƙamina ba, sannan tace,"idan har kin kammala sakandire nan da shekkara huɗu to zan tafi da ke ethopia ki ƙarasa karatunki acan...me kike son zama idan kin gama karatu?". Ina murnushi nace, "Gwaggona tace Lauya zan zama". "to ki dage kiyi karatu sosai sai Allah ya cika burin mahaifiyarki". Dukanmu muka amsa da amin inda nima nace, "Bella Allah ya ƙara miki llafiya da nisan kwana". Jin shiru banji ta amsa ba yasa na ɗago ƙwayar idona ina dubanta, wadda idonta ya karkata gefen kunnena ta ɗaga yatsa tana nuni da wajen, maganar da zata yi ta yanke a san da Jakadiya ta faɗo ɗakin tana sanar mata da cewar tayi baƙi daga Sudan. Nan Bella ta miƙe ni kuma nabi bayanta da kallo, sai dai kuma abun da na gani a bayan wuyanta ne yasa na miƙe tsaye zumbur cike da al'ajabi. Na rumtse ido na dafe goshi hoton abubuwa da dama na haskawa acikin idona. Mun ci abincin da aka kawo mana me daɗin gaske, ban kuma ji kunya ba na juye saurana a leda in kaiwa Gwaggona da Inna Amarya. Bamu muka dawo gida ba sai magriba, cike da sha tara ta arziƙi da muka samo a wurin Ammi da Bella. _____________________________________ *Binti* *idris* *traditional* *herbal* *medicine* *and* *more* Sanyi mugun ciwo ne sanyi shine babbar cutar da take taka rawa wajen raba ma'aurata ta hana su suku da jin dadi yar uwata kada ki tsaya kunya ki tashi ki nemi magani domin babu cutar da ubangiji ya saukar be saukar mata da maganin ta dan haka ni *Bint* *idris* *ibn* *Abdulwahab* Nake Kira gare ku yan uwana mata da maza kuyi maza ku garzayo ku nema wa kanku lafiya  ga masu neman karin bayani sai su tuntube ni ta wanan number Kira ko WhatsApp 07066959285 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 INA MASU FAMA DA DATTIN MARA KO AMOSANIN MARA WLH GA QAQQARFAN MAGANIN WANKIN MARAR MACE KO NAMIJI DA KASHE DUK WANI SANYIN DAKE MARAR MACE KO NAMIJI 1* QURAJEN GABA 2* 'DA'DEWAR GABA 3* SA'BAR GABA 4* QAYQAYIN GABA 5* WARIN GABA 6* RASHIN SHA'AWA 7* RASHIN NI'IMA 8* YAWAN'BARIN CIKI 9* JIN ZAFI LOKACHIN SADUWA 10* RASHIN JIN DADI YAYIN SADUWA 11* Tsinkewar maniyyi rashin haihuwa 12*ciwan jiki kai kayin jiki 13yawan ciwan kai   Da dai sauran su 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Maza ku garzayu kuzo ku nemi naku maganin a farashi mai sauki munyi ragi kasu talatin cikin Dari na kayan mu kada ku sake wanan garabasar ta wuce ku yan uwa 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *11)* *Area 4, House NO2, Asokoro District, Abuja.* Gida ne na gani na faɗa wanda aka narka dukiya a wajen gininsa, tun daga waje kana iya ganin Ƙaton balcony da ke fuskantar gate ɗin gidan, dogon namiji ne me cikar zati yana tsaye ne daga cikinsa da irin tsayuwa ta jaruman sojoji ya sarƙe hannayensa ta baya, jikinsa sanye da t-shirt irin ta kakin soja haɗe da baƙin wando jeans, sumar kansa ba wata mai yawa bace sai dai irin askin da ke sumar aski ne bana musulmi ba, idanunsa kewaye da siririn medical glass. Farin dattijo ne kyakykyawa me kimanin shekaru 56-57, a irin tsayuwar da yay zaka ce ko an dasa shi ne a wurin, hancinsa ne kawai ke fitar da numfashi sai ƙwayar idonsa da ke kan get ɗin da yake fuskanta, a kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yayi nisa acikin zurfin tunani. Har tsawon wucewar wasu mintuna bai motsa ba, sai a san da me gadi ya tashi ya zuge gate ɗin da ake dannawa hon da ƙarfi, bayan da farar motar ta nauso ciki sannan ya haɗe murfin idanunsa ya buɗe kana yabi motar da ido har zuwa wurin da aka tanada na ajiye motaci. Mahaifiyarsa Madam Merry tare da Matarsa Madam Gloria suka fito daga bayan motar kowannensu hannunsa riƙe da jaka da alama daga wajen wani taron suke, bayan wucewarsu ne ɗansa Joseph wanda shi yay tuƙin ya fito daga mazaunin driver shi kuma hannunsa riƙe da jarida, yayi tattaki me ɗan nisa sannan ya tsaya yana nazari, sai ya juya ya koma motar ya jefa jaridar aciki, duk abun da yake idon mahaifinsa na kansa wanda ya fahimci dalilin da yasa ya maida jaridar mota, hakan ne yasa shi ɗan murmusa kuncinsa kamin ya daɗa lumshe ido ya buɗe. Madam Gloria ta ɗauki tsawon daƙiƙa 2 tsaye a bayansa amma sam bai san da zuwanta wurin ba, hakan yasa ta ƙara yin tattaki zuwa gabansa ta tsaya, anan ta fuskanci da gasken bai san da zuwanta ba, domin kuwa kansa a ƙasa yake idanuwansa a rufe. Tayi wani ɗan guntun tsaki na ɓacin rai sannan ta ƙara matsowa kusa da shi sosai ta ɗora hannu ɗaya saman ƙirjinsa, ta ranƙwafo da fuskarta saitin tasa, acikin harshen turanci tace da shi, "Me ya sami Jarumina?, ni ce ko kuma wani ne daga waje?". A yanzu ne yasan da zuwanta wurin hakan yasa shi buɗe ido yana dubanta, gaba ɗaya ya ɗago kai lokaci ɗaya kuma cikin zafin nama yay wurgi da jaridar da ke hannunsa ta baya nan ta sauka a saman fuskar Joseph da ke shigowa, Joseph yasa hannu ya dafe jaridar a fuskarsa kamin ta kai ga faɗuwa ƙasa, tsoron abun da ka iya haifuwa yasa Madam Gloria saurin ja da baya, ta maida kallonta ga Joseph da ke tsaye suka haɗa ido yay mata alama da me ke faruwa, ta ɗaga masa kafaɗa na cewar bata sani ba itama. Ta marairaice fuska tayi ƙasa da murya cikin nuna damuwa ta sake cewa, "Oh Jesus Crise, Daddyn Emanuel me yayi zafi haka?, ko wani abu ka gani a jaridar da ya ɓata maka rai?". Zuciyarsa na tafarfasa ya dubeta cikin ƙarajin murya yace da ita,"wai shin har sai zuwa yaushe ne ƙasarmu zata gyaru ne?, sai yaushe shuwagabanni za su gane al'umma amana ne a hannunsu?, har sai yaushe za su yi hani da aikata ta'addanci?, har tsawon wane lokaci za'a ɗauka kamin gwamnati ta fara martaba jami'an tsaro?, me yasa shuwagabanninmu basa tsoron Allah?". Muryarsa ta fita acikin turancin da ya banbanta dana Matarsa, domin kuwa tamkar baturen america, yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya juya yay tattaki zuwa in da kujera ta ke ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana girgiza su. Madam Gloria ta ƙarasa inda yake itama ta zauna a kujerar dake kusa da shi, sannan tace da Joseph ya bata jaridar, ya miƙa mata jaridar, ya fita babu jimawa ya dawo hannunsa riƙe da glass cup da kuma kwalin exotic na pineapple, yaja ƙaramin glass table zuwa gaban mahaifinsa ya tsiyaya lemu aciki sannan ya ajiye, Dad yay masa kallo ɗaya sannan ya miƙa hannu ya ɗauki lemun yasha, ya ƙara damƙe kofin kamar zai fasa shi. Madam Gloria da ta gama karanta jaridar ta taɓe baki tana duban mijin nata tace,"sai kuma me?, wanne abu ne aciki da ya shafeka da har zai saka damuwa irin haka?". Sai kuma taja tsaki ta ƙara cewa,"kayan haushinka yana da yawa, before duk ka ɗaga hankalina, nayi tunanin wata matsala babba ce, kawai sai kake ɗora damuwa akan mutanen da ba addininku ɗaya ba, if ace there are all chritians shi ne sai ka ɗaga hankali irin haka". Ya kalleta yace,"baki gane rubutun da ke ciki bane?". "na gane mana, ba magana bane akan kidnapping da akayi, to kai mene naka aciki?, akwai ɗanka ne ko kuma ɗan'uwanka?, ko kuma ance maka dani akayi garkuwa ko kuma Mama?". "take a look!". Ya faɗi hakan yayin da yake ɗaga mata hannu da dakatarwa Kansa a ƙasa, sannan ya ɗago ya dubeta da jinjinawa rashin tausayi irin nata yace, "Addininmu bai ce muso namu ba, muƙi wanda ba namu ba...to bari kiji, da har yanzu ina kan matsayina na Major General na rantse miki da saina sadaukar da raina wajen ƙwato mutanen nan...ki kwatantawa kanki idan wani naki akai garkuwa da shi ya za kiyi? Ko da ace kuwa kina da kuɗaɗen amso shi, haka abun yake ga ahalin waɗan nan bayin Allah, su na nan hankalinsu ba'a kwance ba...saboda haka ni na ɗaukarwa kaina alƙawarin fidda dukiyar da Allah ya bani wajen ganin na ƙwato su". Yana kai nan ya kwashi wayoyinsa ya fice ya barsu a wurin, mahaifiyarsa da ke hayowa saman benen ta bishi da ido har sanda ya shige ɗakinsa ya banko ƙofa garamm, ta girgiza kai sannan itama ta wuce balcony inda ta sami Madam Gloria tayi jugum, Joseph kuma na gefenta yana maganar cewar, "Mom ki dinga shiru da bakinki akan nuna tribalism a gaban Dad tunda baya so, hakan shi ne kwanciyar hankalinki dana kowa ma acikin gidan nan...eventhough nima ba wai son muslims nake ba, amma a ɓangaren kidnapping ina tausayin kowa musamman ace mata ne akayi garkuwan da su". Cikin fusata ta kai hannu ta bugi bakinsa, hakan yasa shi tsuke baki yay shiru yana aikin sosa wurin. Madam Merry wadda ke tsaye daga bakin ƙofa tana kallon Joseph tace, "tashi anan wurin". Ya taso ya tsaya a gabanta ita kuma ta kama hannunsa, sannan ta fara magana da Madam Gloria, "wannan ya zama karo na ƙarshe da za ki ƙara saka hannunki ga jikokina, na jima ina faɗa miki hakan da kike babban kuskure ne, ina tsananin son jikokina bana son abunda zai wanzar musu da ɓacin rai ko kuma abunda zai taɓa lafiyarsu". Madam Gloria ta ɗago kai tana duban sirikar

Chapter 8 of 52