Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
neman yi min, idan har naga saɓanin abin da ta faɗa to tabbas zan nuna ma ta bata ga komai a ɗanyan kaina ba, hasalima abin da taga na mata ban ko buɗe shafin farko ba. a cikin wannan duniyar saƙe-saƙen nawa, a cikinsa ne muryar Aaliyan da ke kusa da ni ta kutso ta cikin tunanina, amon muryarta ya fita da wani irin sauti a cikin shirun da ya ratsa cikin motar tun bayan shigowarmu, kuma sautin muryar da sai da ya girgiza allon ƙirjina. "kin ce a jiya kika san komai, aina kika sami visa na shigowa ƙasar nan cikin lokaci kaɗan haka?". simple tambaya ce tayi min, amma sai da zuciyata tayi wani irin duka a cikin ƙirjina, wani tsoro na daban ya dirar min, duk da irin daɗin sanyin ac'n da ke busawa a motar, amma maganar tata sai tasa ni shaƙar wata busashshiyar iska ta daban a maƙogarona, na haɗiye wani wahaltaccen yawu da zance ya wuce da ƙyar, ofcourse zuciyata na faɗa min Akila ɗaya ce, to amma na rasa dalilin da ya sa nake shakka da tsoron wannan da ke kusa dani a yanzu  saɓanin wadda na baro a can, na tattaro yawun bakina na bata amsar tambayarta cikin sanyin murya. "babu buƙatar da kuɗi basa biya maka a duniya in har kana da su". "yi min dalla dalla". sai kawai na karkato da kaina ga barin kallon titi na dubeta, kamar ba ita tayi maganar ba, don kanta na kan wata ƙatuwar tab da ke saman cinyarta, kuma zan iya cewa hankalinta ba akaina yake ba, tana tattaro shi ne a san da zata min magana, da alamu tana ji da zallar izza da ƙasaita ne wanda suka bi jininta. kaman nayi shiru naƙi bata sauran amsar, amma tunawa da wannan zafin da ke jinin jikinta yasa ni babu shiri nace. "na biya adadin wasu charges da suka nema bayan na nemi alfamar su barni na fita...". ban kai ƙarashen zancen ba ta jefo wata tambayar a cikin maganar tawa. "aikin me kike?, ko kuma sana'ar me kike?". tambayar tasa na ɗora ganina akanta da har yanzu fuskarta na kan tab, ata gefen fuskartata na hango tambayar da tayi min cike ta ke da tuhuma da kuma mamakin kuɗin dana bayar, duk da ban faɗa ma ta yawansu ba, amma tasan bill ne ba kaɗan ba. a wannan karon yawun da na haɗiya yafi na ɗazu zafi, to amma sai na noƙe naƙi bata amsar, nima na kauda kaina gefe nayi kamar ban jita ba, ina dalilin da zata tsareni da waɗannan tambayoyin, ai kar ma ta bari mu isa nigeria na tabbatar da ita ce ainihin Akilan da na sa ni, ina tantama akan maganganun da ta faɗa min, domin basu yi kama da magana ta hankali ba. kuma a jikina naji shigar kallonta, da na tabbatar da kallon nata gareni ta gefen ido sai naji jikina ya hau tsuma na tarin tsoron abin da zai biyo baya. "yanayin da nagani a tare da ke ya shaida min cewar Akila bata kar ya alƙawarin da tasa muka ɗaukarwa juna ba. hakan yasa bata taɓa baki labarin cewa Uwarki Aaliya bata maimaita magana sau biyu ba, kuma idan har ta jefa tambaya da gaske tayi tambayar amsa kawai ta ke buƙata". shirunta yay daidai da shigar leɓena na ƙasa cikin bakina na ɗan tsotsa sannan na bata amsa da,"bana aikin komai kuma bana sana'ar komai. lokacin da gaskiyar ta shiga kunnena zuciyata ta yanke shawarar barin kusa da duk wanda ya sanni na koma inda babu wanda ya sanni, domin zuciyata ba zata iya naɗar baƙin cikin rayuwar shegantani da jama'ar garin bichi za su dinƙa min ba, dan ko na tambayi ita matar dalilin da ya sa tayi zina ta haifeni bata da wata ƙwaƙwarar hujjar da zata bani wacce zata wanke laifinta a gareni. shi yasa da zan taho na ɗauko wallet ɗin Ya Kabiru na taho da ita, da ATM ɗinsa na biya kuɗin komai tun daga kan Passport har kan ticket...". yanda na lura kamar tana da azarɓaɓi ko me zance?, domin ban idasa zancena ba ta jefo wata tambayar acikin maganata. "da ma ke ɓarauniya ce?". tambayar da tasa babu shiri na ɗago kaina na dubeta kenan, sai dai tsoron wannan manyan idanuwan nata masu kama da na zakanya ba su bar ni naci gaba da kallonta ba, nayi saurin sauke kai ƙasa ina girgiza ma ta kai da cewar,"a'a ni ba ɓarauniya bace. wallahi ban taɓa sata ba, Gwaggona da Babana ba su ɗorani akan wannan bigiren ba, sun bani kyakykyawar tarbiyar da zan nisanci duk abinda yake ba mallakina ba...". yanzunma dai ban ƙarasa ba ta kuma katseni,"kin taho ne bada sanin kowa ba, haka zuciyata ta faɗa min a san da kike furta kalaman rashin ɗa'arki gareni a ɗazu...shi yasa yanzu a maganarki na tsinci cewar bada sanin Kabiru kika ɗauki wallet ɗinsa ba, me hakan ke nufi kenan?". na haɗiye wani yawu na daban, na bata amsa da,"sata". na faɗa muryata na rawa. sai ta jijjiga kanta kamin tace,"da kyau! saboda haka da mun sauka a nigeria kanki tsaye ki wuce police station ki miƙa musu kanki, ki sanar musu kin saci wallet kin kuma yi amfani da kuɗin mamallakinta da suka fi ƙarfin riƙewarki. na san za su nemi Kabir, idan Kabir yace ya yafe miki shikenan, idan yace kuma bai yafe ba ni zan shige masa gaba wajen ganin yayi shari'a da ke kin biyasa kuɗaɗensa da kika satar masa kika biya buƙatar kanki, Maryam ko za ki dawwama a kurkuku sai na tsayawa Kabiru". tayi shiru da maganartata, tare da ɗauke tab ɗin da ke saman cinyarta ta zira cikin aljihun jakar kujerar motar, sannan ta zira hannu a jakarta ta ɗauko wayarta da ke ringing ta kara a kunne, da larabci ta shiga magana saɓanin turancin da muke a ɗazu. kuma har lokacin idona bai bar kallonta ba da dukkanin iyaka adadin tsoron da ke cikin duniyata, tsoronta da tsoron abin da zata iya aikatawa da na tsinci tabbacinsa acikin furucinta da kuma saman fuskarta. a yanzu zan iya cewa da gaske wannan ba Akila da na baro bace, da gaske zai iya zama wannan dabance, me daban ɗin da komai na duniyarta yake daban. sam babu sanyi a cikin al'amuranta, tun daga kan furucinta za ka shaida ita ɗin me zafi ce, da gaske take, kaifi ɗaya ce, ga wani kwarjini na daban da Allah ya bata, irin kwarjin da zaka ji kana shakkar yin magana a gaban mutum balle kuma haɗa ido da shi, ni dai nasan waccan da na baro ina iya kallon ƙwayar idonta, amma wannan sai dai ma na kalli fuskarta a sace, balle ta kai ga na iya saka idona cikin nata na faɗa ma ta abin da naga dama. abu ɗaya na sani idan har da gaske ya zama ba ita ce Akilan da na sani ba, to kuwa in har zan miƙa ƙarar kaina, to ita ma zan miƙa tata, shari'ar sai ta zama guda biyu, na miƙa ƙararta akan haifata da tayi ba da aure ba, danni ba zan ɗauki wata kalma ta ƙaddara a cikin wannan lamarin ba. tunanina ya katse lokacin da muka iso filin jirgi, maganar drivern ita ta katseni, dan ko dana dawo duniyar da nake rayuwa a ciki naga sai ni kaɗai a motar, ita ta fice tuni, na zuro ƙafata waje ina duban drivern da ya buɗen ƙofar da girgimamawa. "ga ta can tare da Al-Hassan". drivern yace da ni a san da ya lura da kalle-kallen da nake na nemanta ne. na taka ƙafata ina tafiya kamar me ciwon cinya, sai ƙudundune hannayena nake ajikina har na ƙaraso inda suke tsaye. kuma da alama magana suke me tattare da nishaɗi duba da yanda haƙorin makka ɗinta ya bayyana a waje dalilin dariyar da tayi. nayi tsaye kamar wata munafuka a kusa da wanda ban san kowane shi ba, naji dai sunansa daga bakin direba. tare dai suke da shi, kaina a ƙasa ina wasa da zip ɗin rigar sanyin da ke jikina, ba zan iya kwatanta abin da nake ji atare dani ba, amma dai ina jin wani abu me kama da tsoro, taraddadi da kuma fargaba, ta ƙasan ido na hango ta ɗaga ƙafarta da zummar tafiya bayan tayi magana da Al-Hassan ɗin, amma ban san me tace masa ba, kasancewar da larabci ta faɗa, ita kuma ta tafi tana nufar wurin da jirgi yake. wucewar daƙiƙa biyu na ɗago da ganina ga mutumin da tun zuwana wajen tsayinsa ya bani tsoro, mutumin da Aaliya ta tafi ta barni da shi, Al-Hassan! kuma tsoron da ke cikin zuciyata ya ninku da idona ya sauka akan fuskarsa, nayi wata muguwar razana naja da baya, ina kallonsa da maɗaukakin mamaki da al'ajabi gami da ruɗani. me ya kawo Emanuel nan?, kuma mene haɗinsa da ita?, tambayar da naiwa kaina kenan, sai dai kuma abin da ya gilma ta cikin idona shi ya bani tabbacin ba Emanuel bane me kama da shi ne, wanda zan iya kiransa photocopy of Emanuel. na haɗiye wani abu a maƙoshina da ban san ko mene ba, shikenan ya ƙara tabbata Major Tosin shi ne mahaifinmu, kuma ko ba'a faɗa min ba wannan shi ne wanda aka haifemu tare, duk da bama kama da shi amma kuma ga kama ta jini nan ina kallo ɓaro ɓaro a tare da shi. na buɗi baki zanyi masa magana sai naga ya zabga min wata uwar harara da tasa na ɓata rai kamar yanda shi ma nasa yake, na kuma bishi da tawa harar nima. cikin ɗagin murya yay min maganar da ban san me ya faɗa ba, dan haka ina zumɓuro baki nace da shi bana jin yaren da yake ya faɗa da turanci. sai kawai yaja tsaki yay gaba abinsa ya barni a wurin, nabi bayansa da ido cike da haushi, _wannan miskilinne Yaya na?, tabɗi lallai ma, kenan ta ya zamu haɗa kai da shi wajen ɗaukar fansar haihuwarmu a shegu?_ kamar Aaliya tasan meke faruwa sai ta dakata da tafiyarta ta juyo, ban san me tace da shi ba, kuma shi ma ban san abin da ya mayar ma ta ba, amma dai a maganar da ta ƙara yi masa da turanci cewa tayi,"eh mana bata jin larabci, ka ma ta yaran da ta iya...kuma nima har muje mu dawo da english ɗin zamu ke magana kaji me nace ai". shi ma cikin harshen turancin yace,"to amma Mami wace ita?". daga in da nake na hangi irin kallon da tayi masa kamin ta bashi amsa da cewar,"uban ƴan kishi, to ƙanwarka ce, Hussainarka da aka haifeku tare". "Hussainata dai Mami?, da gaske kike?". tace masa,"ban san lokacin da na fara maka ƙarya ba balle na dinƙa shigar da rantsuwata cikin maganarmu kamin ka yarda da ni". da alama su na ɗasawa da shi, dan maganar tayi masa ne fuskarta tana washewa da annuri kamar ƙawaye, sai ya sake tambayarta da cewa,"to Mami ba ki faɗa min abin da zai kai mu nigeria ba". sai naji tace masa,"Mai Martaba Abi kayi haƙuri muyi tafiyar nan, idan muka je can duk zan amsa maka tarin tambayoyinka ranka ya daɗe, yanzu duk a matse nake da naje inda zan isa". sai ya juyo yana min harar ƙasan ido, kuma kaman wanda aka tursasawa yin maganar yace da ni,"zo ki wuce". ina ƙunƙuni da mummurguɗa baki na fara tafiya zuwa inda yake, har yanzu kuma Aaliya na tsaye tana kallonmu da jiran tahowarmu.  tace da shi,"ka bata jakar ta riƙe, kai ka huta". maimakon ya bani kamar yanda ta ce sai kawai ya jefo min ajikina, sai naji nayi saurin tarota jikina gudun karta faɗi ƙasa, dan nasan akwai muhimman abubuwa a ciki, ga wannan masifaffar matar.  kamar daga sama naji yace,"gaba nake da ke, so ki biyoni a baya ki daina shiga gabana". na ɗago na harare shi da kyau kamin nace,"ba haka Ya Kabiru yake min ba". "ko a suna akwai banbanci, Al-Hassan na ke ba Kabir ba". yace dani kenan yayi gaba, ni kuma nabi bayansa. duk sun rigani shiga jirgin, kuma sai dana iso gaban jirgin naga a jikinsa an rubuta EMIRATE AIRLINE da manyan baƙi, a ƙasansa kuma an rubuta Shaik Samin Bin Hamad Al Thalis da ƙanan baƙi. nasa ƙafa na shiga ciki, daga can gaba na hangosu kowa kujerarsa daban, na wuce nima ina neman wurin zama sai naji Aaliya tace,"ki zauna kusa da Al-Hassan". na zauna a kujerar kusa da shi, sai naji duk na takura, ga shi bini bini sai yay tawani ja min tsaki, yana hararata ta gefen ido, kamar ma me shirin rufeni da duka. ban san lokacin da bakina ya furta,"Mami ni bana son zaman nan". sai bayan na faɗi hakan kuma na kafeta da ido, gani nayi ita ma tana kallona, wanda na san sunan da na kirata da shi yasata shiga schock. a hankali tace,"halin ku ɗaya. tashi ki dawo kujerar gabansa".  sai yay karaf yace,"Mami ta dai koma ta bayana, ni ne fa babba". kafin tace da shi wani abu nace,"ai sai ka bari ka tabbatar da ni ƙanwar taka ce kafin ka yanke hukuncin kai ne Babba". sautin murmushinta kawai muka jiyo, tayi shiru bata ce damu komai ba, shi kuma sai yay guntun tsoki ya miƙe daga kujerar tasa ya koma kusa da ita. na taɓe baki kamin na nemi wata kujerar na zauna, duk da hakan a kujerar gabansu na zauna, ina sane dan naga shi ɗan rainin hankali ne, bai san duk tsiyar da yake ji da ita ba na fi shi. ina jinsa yana cewa da ita,"Mami da kika tsintota ba ki faɗa ma ta ni jinin sarauta bane, izzata ba zata bari na ɗauki rashin kunyarta ba.". amsar da ta ba shi itace,"to sai ka fara koyawa zuciyarka sonta tun wuri domin ita ɗin dolenka ce". maganar Aaliya ta shiga kunnena a san da na kwantar da kaina jikin kujerar na rufe ido. "a irin furucinki na rashin hankali a ɗazu, na tabbatar da cewa ba ƙaramin ɗibar albarka ki kaiwa Akila ba kamin gudowarki. to umarnin da zan ba ki da zarar mun isa ki duƙa a gabanta, ki zube gwiwoyinki a ƙasa, ki tattaro yawun baki da dukkan wasu tarin kalamai na ban haƙuri da suke cikin kanki ki bata haƙuri, ki nemi yafiyarta, ki bata haƙuri ki nemi yafiyarta...umarni na ke ba ki Maryam, domin akan Akila bani da kyau ko kaɗan, wallahi summa tallahi in har ta nuna min rashin jin daɗin rashin kyautawar da kika ma ta, na rantse da Allah zan manta da zafin naƙudarki, na saɓa miki kamanni ta yacca ba za ki taɓa ganuwa ba a idon duniya...furucina ne wannan, kuma alƙawari ne sai na cika shi". shirunta yay daidai da tambayar da Al-Hassan ya jefa ma ta,"Mami wacce iriyar magana naji kina yi, wace me irin sunanki haka, kuma me kike nufi da abinbda kike faɗa?". duk da bana kallonta amma na san tayi murmushin da ya tsaya ne iyakar leɓenta, kuma sai naji ta bashi amsa da cewar,"kamar yanda ta ke a cikin duhu, kaima a cikin duhun kake, haɗuwata da ƴar'uwata ne zai haska muku hakan, har ku sami amsar tambayar da ke saƙe acikin zuciyoyinku...bana son wata tambayar Al-Hassan". *Abuja, Nigeria.* a cikin ƙaton falon gidan babu abinda kake ji sai sautin kukan da ke tashi daga bakuna da dama. daga tsakiyar kujerun da ke kewaye da wurin gawa biyu ce lulluɓe da jan ƙyalle, kuma daga gefen kan gawar Madam Gloria Joseph ne duƙe yana girgizata da kiran sunanta akan ta tashi. Major ma na zaune kusa da gawar Granny hannunsa a cikin nata yana kukan rashin mahaifiyarsa. mutuwar da su kai ta dalilin hatsarin motar da suke akan hanyarsu ta dawowa daga Ibadan sun je taron buɗe wani flatfom da ita Madam Gloria ta buɗe. *Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ummu Naseem😍, Hajiya Fasilat me sunan labarabawa😘, Labbaiki Ya Zahra🥰, nace ba duk ku matso ku maƙale a katarar juna😅, page ɗin yau domin jin daɗinku ne💃, irin nishaɗin da kuke bani yasa nace dole in miƙo tukwici gareku💋, ina jinjina da gaisuwar ban girma mutanen kirki, Allah ya jiqan mahaifa🤲...shafin yau dai na bar muku shi sai kun so wani zai karanta😉._ *35)* Acikin bedroom ɗin, a bakin gadon, Al-Mustapha ne zaune ya dafe kansa da dukka hannuwansa biyu, a gefe ɗaya kuma hawaye na sakkowa saman fuskarsa da yake jin zafinsu tamkar tartsatsin wuta ajikinsa. ya miƙe a zafafe yay tattaki zuwa bakin ƙofa, ya murɗa handle ya fita, daga saman benen yake hango ƙasan parlon da jama'a ke kukan mutuwar mahaifiyarsa da kakarsa, ya rumtse ido yay taku uku baya sai gashi ya komo cikin ɗakin, a saman gado ya zube tare da saurin dafe kansa da ke barazanar rabewa gida biyu, kafin ya naushin gadon tare da faɗin,"Nooo!!". amon muryar ya fita da wani irin ƙaraji, har sai da ɗakin yay amsakuwa. ya ƙara damƙe kansa sose yana me jijjiga shi kaman wanda zai yi hauka, ya zai yi ne wai?, me yasa mutuwa zata yi masa haka?, sai kawai ya ƙara fashewa da kuka tare da kifa kansa akan ƙafafunsa. Allah ya sa ni, tun bayan musuluntarsa yakewa ahalinsa kwaɗayin wannan addinin mai ni'imar gaske, tun a ranar da ya musulunta ya fahimci akwai tarin ni'imomi da ke cikin wannan addinin na gaskiya. zai iya rantsewa tun zuwansa duniya yana jin kansa da wani irin nauyi, nauyin da zai kimanta da wanda aka ɗorawa wani babban dutse, kuma kamar yana jin yafi kowa matsala a duniya duk da cewar ba shi da ita ɗin, ya sami gata da dukkan komai na rayuwa da yafi ƙarfin yaji zuciyarsa na cunkushewa. to amma tun da ya musulunta sai yaji komai ya sauya masa, wannan nauyin da yake jinsa da shi babu, haka wannan matsalar da yake jin kamar yana da ita ita ma babu, tun daga ranar da ya musulunta sakayau yake jinsa, kuma zuciyarsa babu wannan cunkushewar da yake jin yana da ita ada. idan ya tuna rayuwarsa ta baya sai yaji yana tausayawa kansa, matuƙar tausayi na wanda ya kauce hanyar dai-dai yabi ta gargada, gargadar da ba zata ɓullar da mutum ko'ina ba sai ga halaka. to amma idan ya tuna sabuwar rayuwar da ya shiga a yanzu, ya kuma tuna Rahmar ubangiji ga bayinsa, sai yaji kamar yafi kowa sa'a da dacewa a duniya da Allah ya haska masa hasken musulunci tun kamin ƙurewar lokaci a gare shi. shi yasa yake roƙon ubangiji da ya haskawa sauran ahalinsa wannan hasken suma, domin su samu su rabauta a duniyarsu da kuma lahirarsu. sai ga shi a ranar da ya ƙudurta zai fuskanci ahalin nasa da maganar da yake ganin zata iya zamowa ƙarshensa a wurinsu, sai ga shi mutuwa ta ɗauke masa mahaifiyarsa, ta ɗauketa ba tare da ta tuba ga mahaliccinta ba, ta mutu zata je ta tarar da wannan azabar da aka tanadarwa irinsu. sai kawai yasa hannu ya matse goshinsa, yana kuma ƙoƙarin tsaida hawayensa, babu wani abu da zai iya yi ma ta shi kam, tata ta ƙare. _"Ya Halatta Ka Halacci Jana'izarta Tun da Mahaifiyarka Ce Tana da Wannan Hakkin Akanka. A lokacin da Mahaifin Aliyu bn Abi Ɗalib Ya Rasu, Manzon Allah (SAW) Aliyu Ya Umarta da Yaje Ya Rufe Mahaifin Nasa, Duk da Mahaifin Nasa Ba Musulmi Bane. sai dai karkayi duk abin da Muslunci yace kar ayiwa wanda ya danganci jana'izar waɗanda ba musulmai ba kamar yi musu Addu'ar neman Rahama, da duk wani bukukuwan da ake yi, da raye-rayen da akeyi da sauransu. Allah Ubangiji Ya Baka Juriya da Haƙuri Ya Kuma Tabbatar da kai a Musulunci"._ maganar ta ƙara haskawa acikin kansa a karo na babu adadi tun bayan da ya tabbatar da mahaifiyarsa ta bar duniya. amsar da Malam Liman ya ba shi kenan a da ya kirasa a waya yay masa tambayar,_"Malam shin a addininmu ya halatta na halacci jana'izar mahaifiyata matsayina na musulmi ita kuma kiristan?"._ sai kawai ya kuma rumtse ido gam, tabbas shi yafi kowa rashin dacewa, zai iya kiran kansa da hakan. ganin cewar ba zai iya yiwa mahaifiyarsa wata adu'a ba, babu wani abu da zai iya yi ma ta domin ta dace da wannan Rahmar ta ubangiji, lokaci ya rigada ya ƙure ma ta, to amma kuma a ɗazu Liman yace da shi,"Kul ɗinka Al-Mustapha, kar ka ƙara cewa kai kafi kowa rashin dacewa, Allah yana sonka, domin da ba ya sonka da bai haska zuciyarka da hasken musulunci ba". sai ya haɗiye wani abu da bai san mene ba a maƙoshinsa. kuma yana cikin wannan yanayinne Obi ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya ƙaraso bakin gadon ya tsaya, ganin yacca hawaye ke sunturin sauka ta gefen fuskar Yayan nasa sai shi ma yaji zuciyarsa ta ƙara tsinkewa, yasa handky ya goge nasa hawayen kafin ya buɗa baki yay masa magana. "Bros Dad yace ka kira Michel ka sanar masa yaje Dunamis International Gospel Centre, a can za'ai bikin mutuwar. amma ya hanzarta wajen yin decoration na wurin". maganar ƙanen nasa tasa yaji zuciyarsa ta ƙara matsewa, bai motsa bai kuma amsa masa ba, bai kuma nuna yaji shi ba. tsawon daƙiƙa biyu Obi ya juya ya fita ya bar ɗakin, babu jimawa da fitar tasa sai ga Dad ya shigo. daga tsakiyar ɗakin ya tsaya yana saƙale da hannayensa ta baya, wanda hakan yake ɗabi'arsa, fuskantar ɗan nasa yake da tausayi, kamin ya kira sunansa,"Emanuel". a can duniyar da ya faɗa yaji sautin muryar mahaifin nasa, da sunan da ya fara mancewa da nasa ne. ya buɗe idanuwansa a hankali kamin ya miƙe zaune ya amsa kiran Mahaifin nasa. "ka bar kukan haka, ka tashi ka shirya zamu wuce chapel, Pastor yana jira karmu ɓata masa lokaci, zai bar ƙasar ne yanzu". kansa a ƙasa yaji maƙogoransa ya bushe, da ƙyar ya iya tattaro wata jarumta da yake ganin kamar bai da ita yace,"Dad ni ba zan sami damar zuwa chapel ba don bikin mutuwar Mom da Granny...". bai kai ga ƙarasa zancen nasa ba Dad ɗin yace,"what! are you mad?". ya miƙe tsaye ya fuskanci Dad ɗin sannan yace,"Dad i am not a christian now since last three days past, i am now a muslim...". tamkar saukar tsawa a cikin duhun dare, tamkar ƙarar bindiga a cikin tarzoma, haka maganar ta sauka a kunnen Major, ya waro dukkan idanuwansa waje yana duban ɗan nasa da ɗumbin mamaki. bai ga wani abu related to kayan maye a ɗakinsa ba balle yace Emanuel ya sha ya samu gushewar hankali, haka kuma bai yi masa kama da mahaukaci ba balle yace ciwon ya kama shi ne babu jimawa, to amma me ya shiga ƙwaƙwalwar yaron?, kan ya jefa wata tambaya ga Emanuel ɗin sai ya tsinci kansa da haska masa cewar tabbas zai iya musulunta, kuma ya musulunta ne ata dalilin yarinyar nan da aka ƙi ba shi aurenta, ya yarda ba zai ƙaryata ɗan nasa ba, tun da ga shi nan babu wannan sarƙar cross ɗin da ba ya taɓa rabuwa da ita. gaskiya ne! yanzu ya yarda da cewar so yana sawa mutum ya zare ya zama taɓaɓɓe, gashi ya gani akan ɗansa, sai dai shi ba zai lamunci wannan haukan ba, dole zai yi masa maganin abin, dama shi ba me tolerating wani iskanci daga yaro ba ne, bare kuma yaron yazo masa da maganar da kansa ma ba zai ɗauka ba, yana jin zai iya ɗaukan ciwon haukan Emanuel kowanne iri ne, amma banda wanda ya shafi wulaƙanta addininsu, how comes ma zai fuskance shi kai tsaye yace masa ya musulunta, ina ya samu wannan ƙwarin gwiwar?, ko kuma shi ne dai ya rasa wannan girman kwarjinin da yake da shi ba tare da ya sa ni ba?, ƙwarai zai yiwa tufkar hanci, yanzu kuwa bada jimawa ba. to amma sai dai me? kamin ya kai ga ɗaukar matakin ɓulan kan Emanuel da bindigar da ya zaro a gefen wandonsa, sai yaji Emanuel ɗin na magana, maganar da tasa yayi suman tsaye saboda tsantsar mamaki, babu tsoro balle shakkarsa a idon ɗan nasa, illama shi da yake ganin yau ɗan

Chapter 32 of 52