sauya komai tun ba'a cuci kamilin yaro ba, idan auren ya zama dole a yau ga Hannatu nan ƴar'uwarka Allah sa muku albarka". tana yin shiru mahaifiyar Zulai Kaka Tabawa ta amshe,"to ni dai nama rasa abun cewa, amma ni ban gamsu da wancan dalilin nasu ba, meye wani ƙwayar halitta bata zo yanda akeso ba? dama can basu yi niyyar baka ƴarsu bane shiyasa, abun da suka so shi ne su ɓata maka suna su goga maka baƙin fenti, a cusa zargin wani abu a zuciyoyin mutane akanka, ga shi kuma sunyi nasara...amma banda haka sun san da zasu yi wannan binciken tun can farko me yasa ba'ai ba sai a ranar yau...ko kai acikinsu kwai wanda yace maka kaje kayi gwajin ƙwayalar halittar taka?". nan ma Ahmad ɗin shiru yay bai ce komai ba, sai da ta ɗaga masa murya tukunna,"Amadu bafa da kujerar nan nake magana ba, ka bani amsar tambayata". ya ɗago da jajayen idanuwansa ya dubeta yace,"ko kusa babu wanda ya tunkareni da wannan batun, abu guda ɗaya ne yake nan, kawai dai na gamsu da hujjarsu. sai dai mene yasa za su bawa Kabir ita? hakan shi ne adalci? mafita ce za'a samar ta hakan? me yasa basu bawa Jawad ita ba? wannan ai cin fuska ne, nayi soyayya da ita sannan shima yazo ya aure ta?". a zafafe yake maganar kuma cikin ɗacin rai da zafin kishi. Zulai ta numfasa sannan ta dubi ɗanta cike da tausayawa, murya a matuƙar sanyaye tace,"Amadu da ilminka, dan haka ka tsayar da tunaninka da iliminka a wuri guda ka auna, idan da Allah ya rubuta Maryama matarka ce Amadu ba ƙwayar cutar halitta ba, ko menene babu abunda zai hana fasuwar aurenka da ita...Matar mutum ƙabarinsa, ka ɗauki hakan a matsayin ƙaddararka, sai ka roƙe shi ya sauya maka da mafi alkhairinta, baka san wane tanadi Allah yay maka a gaba ba...ni mahaifiyarka ce, a kullum adu'ata akanku Allah ya haɗaku da abunda yake alkhairi agareku, ya kuma nisanta tsakaninku da abun da yake ba alkhairi bane agareku...damuwa ko ɗaga hankali ba su zasu baka Maryam ba, basu zasu dawo maka da Maryam ba ta ƙarfi da yaji, ka zama mai haƙuri da tawakkali sune suturarka". ji yake kamar yay kuka a wannan lokacin,"to amma Inna saboda rashin dacewa sai a ɗauki yarinyar da ansan nayi soyayya da ita kuma a aurawa Yayana, mene hikimar yin hakan? ba'a tunanin yanda zan dinga feeling a zuciyata idan ina ganinsu tare, me yasa ma Baba zai yarda da hakan, ba sai ya ƙyalesu su maye gurbina da wani can daban ba". "ni dai na faɗa maka Amadu, idan baka ɗauki maganata ba zugar zuciya zata kaika ta baro ka...Umarni ɗaya zan baka shi ne kar naji kar na gani, ka miƙe ka tashi ka tafi wurin ɗaurin auren Yayanka kamar yanda mahaifinka ya umarceka, kar ka taɓa bari huɗubar shaiɗan tayi tasiri a zuciyarka ta ɓata kyakykyawar alaƙar da ke tsakaninka da ɗan'uwanka, jini yafi ruwa kauri dan haka mace karta zama silar rusa tsakaninku, ka gane me nake nufi, idan har ka ƙetare gaskiya da shawarar da na ke faɗa maka kuma, danasani ce zata zo bayan aikata ba dai-dai ba, kuma wata ƙila anan ubangiji ya nuna min ishara ne". sai kawai ta fashe da kuka, kuka irin me ban tausayin nan, tasa hannu ta rufe fuskarta, inda hankalin Ahmad ya ƙara tashi, ya baro kujerarsa yazo ya kamata ya zaunar da ita, cikin muryar kuka taci gaba da cewa,"a baya na yiwa Maryam asirin kan ba zata taɓa aure ba, yarinyar nan baiwar Allah bata tare min komai ba amma ni da ƴaƴana muka sa mata ƙahon zuƙar hassadarmu...a ƙarshe saboda tasirin adu'oin tsarin da takewa kanta da wanda Suwaiba da Akila suka dage kan yi mata shi ya karya asirin, boka ya tabbatar min da karyewar asirin dole sai ya taɓa ƴaƴana uku, kuma bayan na tuba na nemi yafiyarsu ban faɗa da wannan ba balle suce sun yafe min, na ɓoye saboda ina ganin kamar saboda shi ɗaya za su iya cewa basu yafe ba...ban yarda da maganar boka ba sai da akazo ana saka ranar auren Adawiyya sama da sau uku tana rushewa, Jamila ma ya zama a ranar aurenta yaron yace ya fasa, ananne na fara shiga tashin hankali saboda asirin da nayi akan Maryam kenan, asirin tozarci ba wai ya zama sam sam babu mai zuwa yace zai sota ba, a'a zata samu masu sonta kuma har ta kai ga ranar aure amma a ranar ace an fasa, wanda silar wannan baƙin cikin ya iya zama ajalinta da mahaifiyarta...shi yasa da naga hakan akan Adawiyya da Jamila nayi hanzarin komawa wurin boka amma na tarar ya mutu...ashe Amadu kai ne zaka zama na ukunsu". muryarta ta sarƙe inda ta ƙara fashewa da wani kukan. "nayi danasani, nayi nadama, Allah na tuba...tabbas Allah ba ya yafe hakkin bawa akan bawansa, Amadu a wannan gaɓar ba zan iya tozali da bayin Allah nan ba, ka nema min gafarar Maryam dan Allah, ko lamura sa samu su daidaita".
sai kawai idanunsa suka bi bayan mahaifiyarsa da kallo a sanda ta miƙe har san da ta bar ɗakin, wani ɓari na zuciyarsa na ƙara faɗa masa ba lallai sai bawa ya aikata wani laifi ba sannan ubangiji ke jarabtarsa, sau da yawa ana shirya faruwar abubuwa amma ubangiji kan juya lamarin, wanda kai bawa baka isa ka tuhumi ubangiji akan hakan ba.
yaja numfashi ya sauke, Allah ya sani yana son Maryam, amma a yanzu dole yay haƙuri da rashinta, dole ya koyi wannan haƙurin da ya gani a tare da Kabir, wanda ya jima da fahimtar cewar yana son Maryam, sai dai bai san dalilin da ya hana shi furtawa ba...kuma dalilin ganin wannan kwantaccen son a tare da Kabir ɗin, da ita kanta Maryam ɗin da bata tantance irin son da take yiwa Kabir ɗin ba, dole tasa shi hanzarin furta mata nasa son tun kafin Yayan nasa yay masa shigar sauri, saboda a lokacin ya naji kamar ba zai iya zuba ido wani ya mallaketa ba, shi yasa tun a asibiti a amsar da ta bawa mahaifiyarta lokacin data tambayeta me yasa take son Kabir ɗin yay saurin sauya ma ta tunani, dan karma wannan nazarin da yaga tanayi yay tasiri akanta, kuma shi yasa bai yi sanya ba a lokacin da ta amince masa wajen koyar da ita zazzafar soyayyarsa, ta yanda za tayi saurin mantawa da Kabir da tunaninsa, ta kuma yi mugun sabon da ba zata iya rabuwa da shi ba, duk da yasan ta amince ne ba dan tana so ba a lokacin, sai dan babu yanda za tayi, abunda kawai zuciyarsa ta faɗa masa shi ne, zai aureta ko da bata son nasa, idan yaso bayan anyi auren zaiji da wannan, shi yasan yanda zai yi ya koyar da ita sonsa, dalilin da ya sa ma kenan tana furta ta amince bai yi wata-wata ba ya zube gwiwoyinsa a ƙasa ya nemi alfarmar Baba akan asa masu ranar aure nan kusa, yasan a hakanne kaɗai zai gama da ita da dukkan wani lissafinta, shi dai ya san yana son Kabir, amma ba zai iya sadaukarwa da Kabir ke yi ba akansa.
ya miƙe jiki babu ƙwari, ya miƙa hannu ya ɗauki babbar rigarsa ya saka, sannan ya dubi su Habib muryarsa a sanyaye yace da su,"ku tashi mu tafi". ya faɗi hakan yana mai tafiya zuwa hanyar fita, tafiyar yake kamar mara laka ajikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji a ƙasan zuciyarsa, abubuwan da suka wakana ajiya ne kawai ke haska masa a idanuwansa, dinner ɗin jiya, da kuma yanda suka gama tsara yanda rayuwar aurensu zata kasance.
a lokacin da suka ƙarasa bakin mota yasa handky ya goge tarin ƙwallar da ya kasa riƙeta, sannan ya shiga motar Mubaraq yaja su.
yana jiyo muryar Yagana a lokacin da ta taho zuwa sashensa tana faɗin,"to Allah na tuba mene na ɗaga hankali tun da ga dalili an bayar, ai da basu bada wani dalilin nasu me ƙarfi ba ni kaina Amadu sai nace an maka rashin adalci, kuma sai inda ƙarfina ya ƙare dan wallah ko ba Kabir suka bawa ba sai na ƙwato maka matarka balle kuma sun wullata hannun wanda nasan na isa da shi...haƙuri kawai za kai Allah baka wadda ta fita, ubangiji ai da zuciya yake amfani zai kalla kyawun zuciyarka ba zai barka kai kuka ba".
*Masarautar Bichi.*
Ɗumbin jama'ar da ke yin tururuwa su na ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin fadar su suka shaida auren Kabir Adam Hashim da Maryam Mukhtar Afafa, akan sadaki naira dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba. motoci kawai kake gani daga ko'ina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa su na ƙara yawan adadinsu. Jama'a kuwa babu masaka tsinke, babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin da ya tara su agurin, manyan mutane masu faɗa aji a ƙasashenmu gasu nan wuri-wuri. Alhaji Adamu yana tsakiyar mutane yana gaisawa da ƴan'uwansa na ƙauye waɗanda aka jima ba'a haɗu ba fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, annurinsa ya kasa ɗaukewa, sam ba zai haɗa farin cikin da yake ji a wannan karan ba da na lokacin bikin Sadiya, wanda shi ne biki na farko a ƴaƴansa.
jama'arsa bata kai wani yawan adadi ba amma amsa gaisuwa yake tayi daga hannuwa kala-kala, dan kusan duk wanda yay hannu da Major to sai yay masa nuni da inda Baban yake yace su gaisa da shi, ya gabatar masu da shine uban ango. ango kuwa a wannan lokacin farin cikin da ke tare da shi Allah yayi yawa da shi, jin abin yake kamar a mafarki, haƙurinsa da Akila take cewa ya cuce shi yau gashi ya zame masa rana, shi ba zai iya misalta irin tarin abun da yake ji a tare da shi ba, abu ɗaya kawai yasan yanayi tun shigowarsa masallacin lokacin da ya tabbatar da maganar Baba Mujibu shi ne godiya ga sarki Allah. ya cire Maryam a ransa tuni, ya gama cire Maryam a lissafin zai sameta, ashe Allah ya rubuta a lauhul mahfuz Maryam mallakinsa ce.
sam-sam ya kasa hana kansa nuna abin da yake ji, duk wanda ya kalle shi zai shaidi yana murna da faruwar abun. shi a yanzu ma an hana shi sukuni dan Major da Mai Martaba sun riƙe shi sai faman gaisawa ake da shi ana ɗaukar hoto, ga Alhassan da Suhail ma basu barshi ba, daga wannan yaja shi can ai hoto da mutanensa sai wannan ma ya kuma jansa.
yayin da shi hankalinsa ma kwata-kwata ba anan yake ba, yana can duniyar Maryam, so yake kawai taron ya watse, in ace ya san idan ya biyo Baba Mujibu masallacin fada zasu yo to da bai biyo shi sun zo tare ba, duk da yasan ba lallai ne Maryam ta bada hankalinta ta fahimci komai ba a ƙarancin lokaci, amma atleast sai yayi duk yanda zaiyi ya hana hawaye fitowa daga idonta.
an ɗau tsawon lokaci kafin jama'a su fara watsewa lokacin tafiya reception yayi, kuma a wannan lokacin da aka fito za'a tafi ɗinne Baba ya girgiza kansa yace da Mujibu.
"Kaga yaron nan Ahmad har yanzu bai iso ba."
"Yaya kaima kasan ba lallai yazo ba, saboda an riga an kar ya masa zuciya". sai kawai Baban ya juyo da kansa yana hango inda Kabir ke tsaye shi da Suhail a wani sabon cuncurundon ana masu hoto, ya umarci Aminu da ya kira shi, kuma a san da ya iso kansa na ƙasa yace da Baban.
"Baba da baku yi saurin yanke wannan hukuncin ba." Baba yay murmushin manyace tare da dafa kafaɗar Kabir ɗin yace,"a lokacin da ake ƙoƙarin Jawad ya maye wannan gurbin Akila ta faɗa mana komai, komai ɗin tun daga mafari har zuwa yau...haƙiƙa na jinjina maka ɗana, sai dai ban san ko shi ɗan'uwan naka zai iya yin haƙurin da kayi ba". "zai yi Baba, ni na sani, haƙurin ai a jininka ne". Baban ya ƙara girgiza kansa,"inda zai yi me ya hana shi zuwa?". kafin Kabir ɗin ya buɗi baki yace wani abu suka ji Lukman na cewa,"gama Ya Ahamd ɗin nan". duka sai suka karkata hankalinsu ga motar da Ahmad ɗin ke fitowa, a saman fuskarsa kaɗai zaka tsinci abunda yake zuciyarsa. ƙwayar idonsa da ta Kabir suka sarƙe wuri guda na tsawon sakan ɗaya, sannan idanun Ahmad ɗin suka kulle ya rumtsesu da kyau yana jin wani abu na tsaya masa a ƙirji, yana jinsa ya tafi zuwa wata sama mai nisa sannan ya faɗo, yayi zaton idan ya iso zai tarar da komai da yaji a matsayin tatsuniya, dalilin ƙwarin gwiwar da ya samu kenan na zuwa, amma zuwan nasa tun a ƙofar masarautar ya samu shaidar tabbaccin da gaske an ɗaura ɗin, an ɗaura auren Maryam bada shi ba, kuma ganin Kabir ɗin yasa ya ƙara gasgata da shi ɗin aka ɗaura auren ba wani daban ba.
sai ya shiga buɗe idanuwansa a hankali ya sauke su akan duwatsun da ke baje a ƙasa, sannan ya shiga miƙa hannu ga tarin mutanen da suke taya shi murnar bikin ɗan'uwansa, kowa na cewa da shi Allah ya sanya alkhairi, da ace ƙaddara bata shigo lissafin aurensa ba, da yanzu wannan adu'ar Allah sanya alkhairin tasa ce, shi gaba ɗaya ma lamarin nema yake ya zuƙe masa ruwan kai.
yay ƙoƙarin nemo courage ɗinsa ya shiga bin bayansu Habib har suka ƙarasa wurin da su Baba suke, yana zuwa kuma ya miƙawa Kabir hannu yana ƙawata fuskarsa da murmushi mai sanyi, Kabir ɗinma ya miƙa masa nasa hannu su kai shaking tare da rungume junansu. Ahmad na cewa da shi,"Congratulations". shi kuma yana amsawa da,"thank you".
ya rigada dama ya sani, dan haka a yanzu da yake ganin farin cikin da ke lulluɓe da Kabir ba sai ya tsaya wani mamaki ba, nan suka tsaya akai snapping pictures da su tukunna aka ɗunguma aka wuce wurin reception, ƙaton hall ɗin da Major ya kamawa ango dan shagalinsu shi da abokansa.
****
*ɗakin Ammi, a dai-dai wannan lokacin.*
nayi saurin kai hannuna saman ƙirjina ina dafewa, ina iya jiyo wani dunƙulallan abu, wannan dunƙulallan abun da ya tsaya min a ƙirji ya hana iska wucewa ajikina. a karo na biyu da Shamsiyya ta kuma saurin riƙoni daga faɗowar da zanyi daga saman gadon, a wannan lokacin idan ka kalleni bai zama lallai ka musa cewar jinya nake ba, saboda cikin wasu mintuna na koma sai aikin riƙoni ake, dan ko a lokacin da na suma Mami tayi zaton ta rasani ne, kukan da na buɗi ido naga tana yi a lokacin zan iya cewa nawa bai kai nata ba. amma kuma lokaci ɗaya bayan ta tabbatar da cewar a hayyacina na ke, sai naga ta koma kamar ba ita ce mai kuka da ihun zata rasa Maryam ɗinta ba, neman fitar hayyacin da nake ya dawo da ita Aaliyan da na fara tozali da ita a rayuwata a ranar farko, a wannan ranar da ta wanwankeni da marukan da zan rantse har duniya ta naɗe ba za'a kuma yin irinsu ba, dan ita kawai ta iyasu, kuma a hannunta ne kawai akwai wannan zafin wutar marin.
dalilin sassauta kukana kenan, dalilin fara natsuwata kenan har nake iya danne gunjin kuka na, dalilin fara lallamar zuciyata kenan akan tayi haƙuri, dama ita bai zama lallai ta zama mai farin ciki yanda taso ba, kuma dama ai na faɗa tun kwanaki, sai tayi haƙuri da duk wani ƙalubale da zata fuskanta, wannan ƙalubalen da Asalina ne zai ta jefata acikinsa.
na ɗaga ƙwayar idona ina kallon Mami da ke hakimce akan one seater tana amsa kiran wayar da aketa ma ta a ɗazu na Allah sanya alkhairi, hankalinta kwance, sai farin ciki take abinta, kamar ba ita ce mai ɗiyar da zuciyarta ke ƙoƙarin bugawa ba nan kusa. hawaye masu zafin gaske suka shiga zubo min babu ƙaƙƙautawa, Shamsiyya na goge min da tafin hannunta, amma da zarar ta goge da wani ya kuma biyo baya. tsoronta Allah tsoronta Mami ta ɗago ta ganni ina wannan kukan, tun ɗazu tayi ƙasa da murya tana roƙona da Allah nayi haƙuri nayi shiru kar Mami ta ganni, dan Mami ce tayi ruwana ne nayi shiru ruwana ne naci gaba da kukan, dai-dai take da iskokan da suke kaina.
har a lokacin ta buɗe min tafukan hannunta ta nuna min yatsunta tace min,"Maryam tun da har ba hannun da za'a kashe ki muka miƙaki ba, to billahil azim rabon wannan yatsun nawa su tsufa ne akan fuskarki yau". sannan ta ƙara nuna min doguwar ƙafarta tace,"sannan rabon wannan ƙafar ta dirje fasonta ne a jikinki...kar ki sami damar shiga hankalinki". ni ba ma sai ta kai ga nan ba, abunda bata sani ba ƙwayar idonta ma kaɗai sawa suke na shiga hankalina. sam taƙi bani damar da zan tambayeta dalilinsu nayi min hakan, taƙi bani fuskar tambayarta sam, ga Ummi ma tun ɗazu ban ganta ba, so nake naji me yasa za su rabani da zaɓin raina?, me yasa za su haɗani da Jawad bayan sun san cewar bana sonsa?...zuciyata ta tsayar dani cak a san da take cewa,"me yasa ba za ki tambayi kanki cewar ko shi Ahmad ɗinne yace ya fasa aurenki ba, ko kin manta ke wace? ko har wata ƴar guntuwar soyayya tasa kin manta ta yanda aka samar da ke ne?". sai naji wani dunƙulallan abu a maƙoshina, na rumtse ido na kora shi da yawun bakina da ƙyar, sannan na ɗago na kalla Shamsiyya cikin rawar murya nace da ita,"Yaya ya kira ni?". "taya za'ai ya kiraki, kema kin jiki da wani zance". sai kawai na maida kaina jikin gadon, wasu sabbin hawayen suka shiga sunturi, dama na faɗawa Yaya tun farko, nace masa ni shegiya ce ba zai iya aurena ba, me yasa ma na sakankance da yawa har haka?.
"Keee". Mami ta kirani a tsawace, nayi saurin ɗagowa ina dubanta a diririce. kallona take tana cewa,"kar ki ƙullaci ɗan mutane a ranki, Ahmad ba shi yace ba ya sonki ba, result ɗin genotype ɗinku shi ya rusa komai". jikina na shaking muryana na breaking nace,"how comes Mami?, result ɗinmu fa ɗaya ne, kawai dan kuna so lallai sai na auri Jawad shi ne zaku fa-ke da wani result". ban ƙarasa rufe bakina ba naji saukar wayarta da ta jefo min a bakina ba tare da gudun wayar ta fashe ba, jifan wayar ya fashe min baki dan ba wulli mai sauƙi tayi ba. zafi yasa nayi saurin saka hannu a wajen ina rumtse idona zafin na daɗa ratsa jikina.
na kalleta sau ɗaya nayi saurin ɗauke idona saboda irin kallon da take jifana da shi, tantanma nake anya kuwa Mami na sona. "miƙon wayata". maganartata ta kutsa cikin kaina da wani amo mai firgitarwa, na zuro ƙafafuna ƙasa na shiga takawa jiri na neman ɗibata ya zubar, sarai tana kallo da ƙyar nake tafiya amma ce min take faɗuwata ba damuwarta bace, na faɗi wayarta ta sami matsala shi ne damuwarta, kuma babu abinda zai hanata sauke wannan takaicin akaina.
wannan furucin nata shi yasani isa gabanta cikin taku uku ba tare da na shirya ba, na zube gwiwoyina gabanta na miƙa mata wayar, maimakon ta karɓa sai ta kamo kunnena ta murɗe da iyakar ƙarfinta tana ce min,"mu ke da iko da ke bake ke da iko damu ba...kinyi kaɗan ki tsaremu da tarin tamboyinki Maryam, muke da ikon zaɓa miki miji, dan haka maganar ma mu biki ta maslaha da lalama ko na fahimtar da ke bai taso ba, ubanki zanci wallah idan ba ki daina min wannan kukan ba, zanci ubanki major ne idan ba ki hankalta ba...zai fiye miki ma ki fara koyawa zuciyarki sonsa tun yanzu, tun kamin gobe na miƙa ki ɗakinki...in yaso idan na kai ki ki haƙa rami ki binne kanki aciki shi ne ƙarshen da za ki nuna min cewar ko waye yayi kaɗan ki zauna da shi". sai da tayi kamar zata tsinke kunnuwana kafin ta cika su, sannan a hankali na jiyo muryar Ummi da ke bin iska tana shiga kunnena da cewa.
"ba haka kawai muka hanaki Ahmad ba Maryam, sanin kanki mu ba mutanen banza bane, ba ƙanan mutane bane da zasu aiwatar da hakan babu wani ƙwaƙwƙwaran dalili...kawai abin da nake so ki fara fahimta shi ne ki yarda da cewar dama tuni Allah ya ƙadarta cewar ke da shi ba zaku zauna a inuwa guda ba...Almustapha ya faɗawa Daddynki result ɗin wani Ahmad ɗin daban ba tare da shi kansa ya san da hakan ba, kasancewar time ɗin da Daddynki ya kira shi yana cikin aikin da yaywa kansa yawa, kuma sai a safiyar yau da Daddynki na duba takardu a motarsa, ananne yaci karo da ainihin takardar da ke ɗauke da result ɗin Ahmad na SS, ke kin san wane mahaifinki ba sai na ɓata lokaci wajen yi miki dogon jawabi ba, dan haka nasan yanzu kin gane dalilin da ya sa aka fasa aurenki da shi. ni na faɗa miki ma hope ɗina ba akansa yake ba, sai a yau nake farin ciki da aurenki Maryam, wallahi sai a yau nake murna". naja majinar hancina muryana a dashe nace,"to amma auren dole ne ba sai a ƙyaleni ba...". kuma ban kai aya ba, bayan yatsun Mami suka sauka akan laɓɓana, kan ciwon da taji min a ɗazu, sai na kuma fashewa da wani sabon kukan ina cewa,"ni dama Mami na san ba kya sona, shikenan, indai wannan ɗan'uwan naku Jawad ne naji zan zauna da shi amma ba dan ina sonsa ba, kuma ba dan zanyi tolerating duk wani yayinsa da zai zuba akaina ba...". "balle ma ba Jawad ɗinne mijinki ba, barrantana ki sami damar walaƙanta mana ɗan'uwa son ranki". na juyo ina duban Ummi cike da ruɗani, kafin na buɗi baki da ƙyar nace da ita,"Ummi to to wane mijin?". nayi tambayar ina mai ƙara fashewa da kuka, murya a rarrabe.
"wannan mutumin da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha ɗaya yana sonki, wannan mutumin da ya fara sonki tun a lokacin da ya san wace ke, ba wai wace ke a wannan matsayin da kike kai ayanzu ba, wace ke a wancan lokacin da ya san ke shegiya ce, wannan mutumin da zuciyarsa ta cika da sonki da kuma tausayinki, wannan mutumin da yake kwana yana tashi da fargabar ki san asalinki, wannan mutumin da ya fara zubar miki da hawaye tun kafin naki su fara zubarwa...". ni dai ban bari Ummi ta ƙarasa zancenta ba na katseta da cewar,"na shiga uku Ummi, Ummi kar ki fasa min kai, kar ki sa ƙwaƙwalwata ta tarwatse...wai shi wannan mutumin da kike ta faɗa tsawon lokaci ba shi da su na ne?, ko kuma ba mutum bane da idanuwana ba zasu iya ganinsa ba ne?...". maganar na ke idanuwana a kulle, ina jujjuya kaina, kuma ban ƙarasa abin da nake son cewa ba maganar da naji Ummi na faɗi tasa nayi shiru. "ka shigo kaji da rigimammiyar matarka, ba zan iya da tambayoyinta ba". ban kai ga buɗe idanuwan nawa ba naji cikar girma da haiba na mutumin da Ummi ke magana sun cika ɗakin baki ɗaya, take naji wani sanyayyan ƙamshi na bin hancina, ƙamshin da ya shiga jikina ya wanzar min da ko wanene tun kamin na kai ga buɗe idona, a jikina nake jin takunsa, a rufaffun idanuwana nake hasko yanda doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu ke takowa suna isowa inda nake, san da ya tsunguna gabana ya kamo hannuna da sanyayyan hannunsa mai taushi ya tabbatar min da mutumin da nake zargi, amma duk da haka ban buɗe idona ba, illama ƙara runtsesu da nayi sosai, sannan na kai hannunawana duka biyu na ɗora a kunnena dan toshe su daga jin dukkan wanzuwar wani abu da ban shiryawa jinsa ba a tare da ni.
tukunna na buɗe ƙaramin bakina duka zan kurma ihu, amma sai duk wani shirina ya tsaya cak, san da ya tarairayoni jikinsa gaba ɗaya, yay min matashi da ƙirjinsa, yay min rumfa da faffaɗan kafaɗunsa, ya kuma ɗora hannunsa kan sumar kaina da babu ɗan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 52