Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
me ɗauke da ɗai-ɗaikun shuke-shuken fulawowi masu kyau. ƙofofin ɗakuna guda huɗu jera da wurin, biyu daga ɓarin hagu biyu daga dama, du ka doors ɗin colours guda ne, dan haka tasa kanta tsaye ga ƙofa ta biyu da ke a ɓarin dama ta buɗe ta shiga. bedroom ne me girma da medium italian bed acikinsa, wadrobe na fuskantar gadon sai mirrow daga jikinsa, da kuma wani medium glass table a gaban gadon, rabin bangon bedroom ɗin manne yake da stickers na hoton Ronaldo, ɗakin ya haɗu sosai dan sai zuba ƙamshi yake, komai nasa blue and white ne, ta ɗaga labulen da take tunanin window ne sai taga wata ƙofa ce ta daban, nan ta murɗa handle ta buɗe, toilet ne wanda ya haɗu iyakar haɗuwa, komai na cikinsa daga waje akayi order ɗinsa kamar yanda duk wani kaya na gidan yake nunawa, sai ta janyo ƙofar ta rufe. da guntun tsaki ta fito daga bedroom ɗin ta buɗe ƙofan kusa da shi, nan kuma parlo ne me ɗan girma shima, yasha wasu azababbun kujeru da kayan ƙawa na decorating parlo, sai medium plasma manne daga ɓarin gabas, da hotunan ronaldo a mammane a jikin bangon parlon kamar dai na bedroom ɗin, alamu dai sun gama nuna mamallakin ɗakin cikakken ɗan ƙwallo ne kuma masoyin Ronaldo, ta maida ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin parlon da ya gwauraye da sanyin Ac haɗe da wani daddaɗan ƙamshi. zama tayi kan kujera tare da kunna tv ta nemo channel ɗin da ake wani american film, tana kallo tana cin kaza tana kurɓar youghrt irin na wadda hankalinta ke kwance duniya tayi mata daɗi. tana gamawa ta jawo tissue ta goge hannu sannan ta jinginar da kanta ga kujerar taci gaba da kallon, can idanunta suka fara rufewa ta miƙe ta koma bedroom ta kwanta, a yanda take zazzaƙewa ka rantse dama can ƴar gida ce. gidan tsit kake jinsa kowa na ɗakinsa, sai tvn parlo da ke kunne with low volume, ƙarfe biyar na yamma Granny ta fito daga ɗakinta, ta ƙwalawa Buky kira sai gata ta bayyana a gabanta, tana dubanta tace,"where is Gift?". a ɗazu da suka shigo Emanuel sai da ya faɗa mata sunan Mairo(Gift) kafin ya wuce ɗakinsa, dan haka bata tafi tunani ba akan ɓaƙon sunan da ya zo gidansu, kanta a ƙasa tace da Granny,"tun ɗazu ta bar nan, may be she is in her room". Granny ta kaɗa kai, sai dai a tunaninta wanne ɗaki ta wuce dan Emanuel yace da suka shigo bai nuna mata inda zata zauna ba, shi dai kawai ya barta a parlo, ita kuma abunda ya hanata fitowa ta sami Mairo a lokacin kanta na mata ciwo, kuma ko da tace Emanuel ɗin yasa Buky ta kira mata ita tazo ɗakinta sai yace ta kwanta tayi baccinta kawai, in dai Gift ce tazo ƙara mata zafin ciwon zata yi, ba dan taso ba ta kwanta ɗin bata ga Mairo ba a time ɗin, amma tunda Emanuel ya shigo ya bata labarin komai taji zuciyarta ta shiga zullumin son ganin Yarinyar. a ƙasa babu wani ɗaki bayan nata da na su Joseph da Obi, Emanuel da Mom da Dad duka a sama suke, saboda haka tasan da wuya idan ba part ɗin su Joseph tayi ba, tunda hanyar da upStairs yake indai ba kai ɗan gidan bane ba sani zaka yi ba, haka nata ɗakin ma kamar ba'a parlo yake ba, sai ka san gidan sannan zaka iya sanin ta inda ƙofar part nata yake. kitchen ta shiga ta sada kanta ga ɓangaren su Joseph, bedroom ɗin Obi ta fara buɗewa da ke ɓangaren hagu taga bata ciki, dan haka sai ta nufa na Joseph tana buɗewa kuwa ta ganta tana bacci hankali kwance, taja blanket ta rufe jikinta, Granny ta godewa Jesus a ranta da bai dawo da Joseph a wannan lokacin ba ya sameta akan gadonsa, dan shi mutum ne irin mahaifiyarsa da basa son baƙi sam, idan da ya shigo ya ganta sai ya mammaujeta kafin ya kai ƙorafin a sauya masa komai na ɗakin, tunda har wata stranger da basu san daga inda take ba zata taɓa kayansa. fuskarta na bayyanar da siririn murmushi ta ƙaraso ciki, dama acikin bayanan da Emanuel yayi mata akanta ɗazu, ya shaida mata tana da bacci kamar me laulayin ciki, wuyarta taji ta ita kaɗai ko kuma taji mutum a kusa da ita zata ɓingile a jikinsa. ta isa gadon ta zauna daga gefe tana kallonta, tasa hannu ta shafi gefen fuskarta, yarinyar tana da kyau sosai, a yanda fuskar baccinta ya nuna zaka san me ƙiriniya ce ba irin ƙiriniyar yara ba, tun a ɗazu da Emanuel ya bata labarinta taji ta shiga ranta tun bata ganta ba, tana sonta da tausayin halin da take ciki da dukkan zuciyarta, haka kuma tayi farin ciki da zuwan yarinyar duk da bawai zama ne na dindin ya kawota gidan ba, ko ba komai gidan zaifi mata daɗi yanzu ta sami ƙawar ɗebe kewa, dama basu da mace a gidan ƴan mata. kullum ita kaɗai take zama a gidan tunda Gloria itama ba zaman gida take ba, ƙarfe 7am take fita office sai 6pm idan tana ƙasar kenan. Granny ta shiga tashinta da kiran sunanta da suka raɗa mata Gift, da yake me nauyin bacci ce har sai da tasa hannu tana ɗan taɓa ƙafarta sannan ta shiga buɗe idonta a hankali tana murzasu har suka buɗe duka ta saukesu kan Granny tana miƙa. Granny ta sakar mata murmushin da ya bayyanar da haƙoran tsufanta sannan tace mata,"get up and take shower, we are going out". ta gyaɗa mata kai kawai tana ziro ƙafafunta ƙasa su ka fito tare, zata shiga bedroom Granny ta dakatar da ita da faɗin,"a'a ba nan za ki shirya ba". ta faɗa holding her hand to make her way to her own room after she called Buky tayi informing nata tayi fixing Joseph's bedroom. bata jima a wanka da ta shiga ba ta fito ta shirya cikin tsangallalun kayan da suka koma kayanta a yanzu, ita da Granny suka fito a tare riƙe da hannun juna, a parlo Granny ta danna landline ta kira wayar driver akan ya tada mota zai fita da su anguwa. *Acorns & Gold Boutiques, Abuja.* Granny ce keta aikin jidar kayan sawa acikin store ɗin kamar me shirin haɗa akwatin lefe, kaya masu kyau da tsada take ɗiba, tun daga kan gowns, mini skirts, t-shirts, bomshots, bras, high hill and flat shoes, wrist watch, earings, bangles da sauransu, haka ta dinga ɗiba tana zubawa a basket ɗin da Mairo ke biye da ita, sai da ta ɗibi kayan da take ganin zasu isa Mairo sakawa zuwa ɗan zaman da zatayi sannan suka isa wurin biyan kuɗi tai payment da Atm card. ma'aikacin store ɗin da kansa ya ɗauki kayan ya kai har mota saboda yasan wace Granny, a kaf Abuja yankin Asokoro anyi ittifakin babu wani family da suka san darajar ɗan Adam su ke martaba shi da girmama shi irin gidan General Tosin Afafa, ahali ne da suke kyautatawa kafiri ɗan'uwansu harda musulmi, Allah ya wadatasu da arziƙi me yalwa, kuma basu kasance cikin irin masu arziƙin da suke ƙam ƙam da dukiyarsu ba, dukiyarsu su na bada ita ga kowa ne, wannan dalili na kyautatawarsu ya saka suke samun adu'a iri-iri daga musulmi akan Allah yasa su karɓi hasken musulunci. daga nan kuma suka wuce Perfect Trust Cosmetics, anan ma kayan kwalliya ne kit guda ta kwasa sannan suka fito suka wuce Agabason Perfumery, anan ma turaruka ne ta kwasa masu tsada da ƙamshin gaske, kafin daga bisani kuma su wuce wurin saloon, aka wanke mata kai, aka wanke ƙafa akai gyaran farce tare da fixing nails, a taƙaice dai ta ko'ina sai da Granny tasa aka gyara Mairo ta ƙara fitowa sak a ƴar kafirai. sai da su ka biya suka sha ice cream daga bisani kuma suka wuce gida, ba su koma ba sai ƙarfe takwas da rabi na dare. lokacin da suka dawo kowa na zaune a parlo ana hira, ba hirar komai mahaifin nasu ke musu ba sai ta rayuwa, su bar ganin shi me arziƙi ne, ya tara musu kuɗin da ko bayan ransa ba zasu yi talauci ba, namiji yay tunƙaho da dukiyar kansa bata ubansa ba shi ne ya cika namiji, kuma dukiyar kanka ita kake bugun ƙirji da ita, mutum ba ya kaiwa high level sai ya zama ɗan gwagwarmayar rayuwa sannan, shi ma ba haka ya sami wannan dukiyar da yake ganin ta masa yawa ba, sai da yay aiki da jininsa da ƙarfinsa, tun yana ɗan 13years yake fita waje yay cuɗanya da mutane iri-iri, shi ne dako shi ne aikatau, shi ne wanki da guga, shi bai sami gatan da uba zai ɗebi maƙudan kuɗi ya bawa ɗansa ba wai saboda kar ya rasa na kashewa, a'a, tun da ya kai 15years idan ya tambayi kuɗi a gida Babansa cewa yake da shi ka nemi na kanka, su tambayi Granny zata ba su labari. ya tsaida kallonsa akan Joseph yace masa,"saboda haka ka sake buɗe idanuwanka, ka farka daga baccin da kake, har yanzu acikinku kai ne baka da hankali...kaƙi ka tsaida hankali kayi karatu kana biyewa abokan banza su na ɗoraka a motar da zata kaika tashar dana sani...ball kawai ka saka a gaba Joseph, ball kawai, nasha faɗa maka duk sunan da zaka yi sai da ilimi duniya take yayinka, na maka faɗan na maka nasihar kaƙi kaji, kaƙi karatun, na rabu da kai na kai ka company nanma kaƙi zama, ya kake so nayi maka Joseph?, ranar da polive suka biyoka kasan yanda naji?, sai da na rasa jina da ganina na ƴan sakanni, zuciyata har yau bata bar ciwon wannan abin kunyar daka ja mana ba, amma shikenan kaci gaba idan kana ganin hakan shi ne dai-dai, akwai ranar da zaka wayi gari kaga babu ni a duniyar, na mutu an rufe babin rayuwata, na bar maka duniyar". Joseph ya hau ciccin magani, faɗan Dad kullum akansa yake ƙarewa, kamar kullum shi ya ke yin ba dai-dai ba, ya kamata Dad ya ƙyale shi akan batun karatu tunda yace masa ba ya so, ya ƙyale shi da maganar zuwa aiki tunda yace ba zai yi ba, ai su na da kuɗin da yafi ƙarfin ya fita yay aiki ako ina ne, shi ba za'a masa dole ba, yana da ƴancinsa. a gajiye liƙis su ka shigo Mairo na riƙe da handbag ɗin Granny sai lanƙwashe jiki take a lallai ita ta gaji da yawa, a kusa da Joseph ta zauna tana miƙe ƙafafu tare da fadin,"Uncle am very tired". ta faɗa tana kallon Emanuel da su ke facing juna, hararta kawai yayi. Granny taji tana welcoming Dad sannan ne ma ta lura da shi, ita ma ta buɗi baki da cewar,"welcome back Dad". ta ƙasan siririn medical ɗin da ke idonsa ya kalleta ya amsa mata. "sai yaushe Gloria zata dawo ne, this time aroud ta jima da yawa". Dad ya kalla Granny da ta yi masa tambayar yace,"they had just arrive back, sai suka sami saƙon za su yi presenting seminar na oriflame a london, amma tace ba zasu wuce 3-4days ba zasu dawo". "Yayi kyau". ta faɗa tana miƙewa tare da cewa Gift ta tashi ta wuce ɗaki ta ajiye kayan. Mairo ta sami tarba me kyau daga wurin Dad, wanda ya ƙudurta ɗaukanta tamkar yarinyar da ya tsuguna ya haifa, ya ɗau alƙawarin zai kula da ita har zuwa ranar da zata sami lafiya tunaninta ya dawo su maidata wurin iyayenta. a ɗazu da ya dawo niyyarsa a saka hotonta a media da kuma sanarwa a gidan radio, ko Allah zai sa wani nata yaji, to Emanuel ya hana shi ya kafa masa hujja me ƙarfi akan rashin aiwatar da hakan, inda yace masa wani kidnapper ɗinma zai iya gani yazo ya karɓeta ba tare da ansan wane shi ɗin ba tunda ita ba'a cikin tunaninta take ba, Dad ɗin kuma ya gamsu, Obi ma ya goyi bayan Yayansa. ƙarfe tara da rabi na dare suka hallara a dining area yin Dinner kamar yanda suka saba, tun daga breakfast, lunch and dinner duka tare suke yi. tun zamansu Joseph ke aikawa Mairo harara, balle da yaga kowa na haba-haba da ita, kamar ɓarauniya zuwan yau kaɗai ta sace zuciyarsu, a hankali ya saki ƙwafar da ita kaɗai ta ji da take kusa da shi, suka haɗa ido ta turo masa baki gaba, cikin zafin nama ya daki dining table ɗin ya fuskantota yana nunata da yatsa da cewa,"Dad yarinyar nan ta raina ni, kalla fa yanda take murguɗa min baki". Dad ya ɗaga masa murya,"mene hakan kake yi Stupid Brother kawai, is she not your sister...kuma baka kallon bata da lafiya". yabi kowa da kallo da yanda suka yo kansa, abun ya ɓata masa rai ya ƙara jin tsanar yarinyar a ransa, shi ne auta a gidan, zai iya rantsewa da wayonsa dai Dad bai taɓa ɗaga masa murya ba sai a yau, yana masifar sonsa kasancewarsa ɗan auta, amma saboda zuwan wannan banzar yarinyar Yau Dad ne ke yin kamar zai duke shi, dama yasan za'a rina ai, tunda Brother ya basu labarinta yasan sai ta ƙwace masa fada a wurin Dad, saboda yana so ya ganshi da ƴa mace kuma Allah bai bashi ba, yana yawan faɗan yanda yake so ya ganshi da ƴa mace. ba dan yana gudun kar Dad ya hana shi motar da yake so a siya masa ba, da babu abinda zai hana shi ɗaga waya ya kira Mom ya sanar mata da zuwan wata ƙazamar stranger gidansu, to matsalar ɗaya Dad ya gargaɗe shi yaja masa kunne akan cewar ya sake ya faɗawa Uwarsa sai yaga yanda zaisa ayi da shi a barrack, shi kuma Dad ba ya hane shi bane saboda gudun fitinar Gloria ba, sai dan ya barta ta kammala agenders ɗin da ke gabanta hankai a kwance, idan ba haka ba yanzu tana jin labari zata baro duk wasu activities nata ta dawo gida. har aka kammala cin abincin acikin ɓacin rai yake, yana jin kamar ya shaƙeta. ɗazu da yamma da Emanuel ya fito ya tarar su Granny basa nan, ya saka ƴan aiki suka gyara extra room ɗin da yake a sama na kusa da ɗakin Dad, both the bedroom and parlo, ya zama shi ne ɗakin Mairo. saboda haka yanzu da za'a tafi kwanciya su uku suka haura sama, da ita da Dad da kuma Emanuel, duk yanda Granny tayi da ita akan tazo su kwana tare taƙi tace,"a'a ni bana kwana da tsoffi,  snoring su ke yi a bacci". basu Obi kaɗai ba, har Dad sai da yay dariya. su na hawa stairs ɗin Dad ne ke agaba sai ita ke bin bayansa Emanuel kuma na biye da ita, ta cewa da Dad,"ɗazu Uncle yay min faɗa akan nayi mistake wurin hawa flight, har yace zai zane ni". Dad ya kira sunan Emanuel ya amsa, yace da shi,"baka san ita ɗin Auta bace, kuma ba'a yiwa Auta faɗa, karka sake idan ba haka ba raina zai yi babu daɗi...ko kaima baka kalla saboda first born bane Mom ɗinka ko hararanka bata yi". shi dai Emanuel murmushi kawai yake, Dad ɗin kuma yace da Mairo,"kiyi haƙuri ba zai ƙara ba daga yau...kuma duk wanda ya kuma yi miki faɗa kice Dad ya hana ke auta ce yana sonki da yawa". "tom shikenan Dad ena nima ina sonka". ta faɗa tana mintsilar hannun Emanuel tana dariya ƙasa-ƙasa, ya kai mata ranƙwashi dai-dai lokacin da suka hayo saman gaba ɗaya kowa ya nufa ɗakinsa dan kwanciya. ****a washe gari ƙarfe shida da rabi Emanuel ya leƙa ɗakin Mairo yace ta shirya da wuri zai kaita school, jiya Dad ya sanar masa a yau ya kaita makaranta, shi mutum ne da ba ya son zaman yaro a gida. ita dai tunda ya tasheta ɗin ya juya ya fita ta koma baccinta, bata farka ba kuma sai quater to 8, tai sauri tayi wanka ta shirya sannan ta fito, ɗakin Dad ta shiga ta tarar shi ma yana shiryawa, ta gaida shi sannan ta fito ta sauka zuwa ƙasa. sakkowarta dining area ta nufa, Eze(me girka musu abinci) har ya kallama girki ya jera a dining ɗin, a yunwace take, dan haka taja kujera ta zauna, ta rasa irin cikinta ita kam ci kamar gara, tana da saurin jin yunwa kuma a asibiti an gwadata babu ulcer. bata tsaya tunanin jiran fitowan kowa ba ta buɗe flask ta fara zuba irishi ɗin da aka soya da ƙwai, sannan ta buɗe tea flask ta zuba tayi haɗin kauri na madara da bounvita. ta ɗauka fork zata kai bakinta Joseph ya isa a wajen, ya ɗaga hannu ya wanketa da mari yana nunata da yatsa yace,"wace ke da za ki zo ki zauna a dining tun Dad bai sauko ba, to bari kiji na faɗa miki karki sake ki ɗauki kanki matsayi ɗaya da ƴan gidan nan, wuyarta Mom ta dawo za ki gane kuranki, banza ƴar tsin....". bai ƙarasa faɗin ƴar tsintuwar ba Emanuel ya sharara masa maruka kyawawa guda biyu ta kowanne ɓari, a gigice ya ɗago yana duban Yayan nasa da ɓacin rai ke kwance a saman fuskarsa, malolon baƙin ciki ya tokare shi a maƙogoro, ko tantama ba zai ba Yayansa ya hauka ce, kai kowa ma ya haukace akan wannan Yarinyar. "Brother mari na fa kayi bayan ita ya kamata ka hukunta". Ema ya ce da shi,"ba ka kalla ita ɗin bata da cikakkiyar lafiya bane, kuma jiya me Dad ya faɗa maka?, to ka shiga hankalinka Joseph". duka su biyun huci suke kowa a wuya yake da ɗan'uwansa, a fusace Joseph ya bar wajen yana ƙananun maganganu, sai dai a masifar da ya tafi yana yi bai rufe baki ba Granny ta buga masa remote a baki, zafi biyu ya haɗar masa, saboda haka yayi fushi ya fice daga gidan gaba ɗaya. taso ta fahimci wani abu a maganganun da Joseph ya faɗa mata, iyaka haɗe fuskar da ya dinga nuna mata a daren jiya, da kuma hantara duk tayi zaton ko dan ita ɗin tana sakuwarsa ne, to amma a yanzu kuma mari da kalaman da yayi mata ta gane ba faɗan sako da sakuwa bane, rashin so ne zallarsa, da abunda take son ba da tabbacinsa akai, cikin abu biyu kwai ɗaya, ko ya zama ba Mamansu ɗaya da shi ba kamar yanda taji yace Mom zata dawo zata gane kuranta, ko kuma ya zama ba Mamansu ɗaya ba kuma Dad na nuna mata so fiye da shi. sai kuma ɗaya ɓari na zuciyarta yace mata _duk cikin hasashenki babu ɗaya, ki tuna a asibiti Uncle yace miki za'a dawo gida kuci gaba da rigimar da ku ka saba kamar kaji ke da Joseph._, me yasa ne take jin wasu abubuwan kamar bata taɓa sanin da su ba?, ko da yake ai Aunt Deborah ta faɗa mata saboda bugewar da ta yi hakan zaisa ba komai zata ke tunawa ba na baya. Emanuel ya dafa kafaɗarta ya zaunar da ita kan kujera, yasa handkey yana goge mata hawaye yace,"ki ƙyale Joseph mahaukaci ne yana da cutar Bipola disorder, har ma ya kai matakin ƙarshe na Mania, kinga kuwa shi abin aiwa uzuri ne". "what concern me da ciwonsa". ta faɗa tana rufe ido tana girgiza kai. ta yi ƙwafa da faɗin,"Mom zata dawo saita yi mana tsakani da shi idan ba haka ba kuma nake jangwalo ciwon nasa in kulle shi ɗaki babu wanda ya sani, ba zan buɗe shi ba har sai ya jiwa kansa rauni". "shirmen banza kawai ke da shi duk baku da hankalin...ki nutsu tun kan Dad naku ya sauko yasa miki belt ajiki, ai dama ƙafa yake ɗaga miki ganin ba ki da lafiya". Granny tace da ita a sanda take jan kujera ta zauna. cikin fushi ta miƙe zata bar wurin ta kuma cewa da ita,"tabbas kina so kiyi kwanan cell, karki hankalta ki gani, gashi nan sakkowa ai". "ni dai dariya ce tawa dan ko haƙuri ba zan bayar ba akan cuɗa yara". Obi ya faɗa a shi ma yana jan ɗaya daga cikin kujerun ya zauna. lokacin da Dad ya iso ya tambaya ina Joseph, suka haɗu suka rufa masa asiri da cewar Principal nasu ne ya kira shi, dalilin da ya sa yay fitar wuri kenan. har da Obi aka tafi kaita makaranta, Lead British International School Abuja aka kaita, kuma kasancewar speech ɗinta da kyau SS1 suka karɓeta, sai dai sun faɗa mata idan bata dage ba to zata yi repeating tunda yanzu su na ƙarshen second term ne. bata fara attending class ba sai da aka kaita asibitin ido aka mata medical glass, kullum driver ke kaita ya ɗaukota, kuma da yake tana da magana nan da nan sai tayi ƙawaye duk da ba kowacce ƙawa take kulawa ba musamman wadda take ganin ba level ɗinsu ɗaya ba, zaɓa ta ke ta dirje, idan taga wadda kuɗin ubanta yay kusa dai-dai dana su, tukunna zata kulata. to haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata acikin tunanin da ta rasa, sosai ta samu sauyin rayuwa na jin daɗi, hutu da kwanciyar hankali, a wata guda curr da tayi a gidan ba zaka taɓa yarda da cewa ita ɗin bace, ta ko'ina ta sauya, irin kalar ingantaccen abinci da take ci da kuma hutu yay bala'in amsar tsarin garkuwar jikinta, hasken fatarta har ɗaukan ido yake saboda sheƙi, kyawunta na tun usuli shi yake fitowa a yanzu, kalar ƙauye ta bar jikinta, ta sami wata wayewa da gogewa kamar ba ƴar ƙauye ba, ta waye da cuɗanya da ƴaƴan manya da ita kanta rayuwar, ta kuma goge da ilimin boko da na addininsu, ayanzu haka ita makaranta ke ɗauka ta wakilcesu a duk wani debate, turanci a bakinta kamar baturiya, idan tana speech har tsuma jikin mutum keyi, kwanaki da aka haska vedio ɗinta a BBC tana fighting against irin taimakon da gwanati ya kamata take bawa ɗalibai da kuma samarwa matasa aikin yi, Dad sai yaji gaba ɗaya duniyarsa ta rikice da daɗi, inama ace, inama ace ƴarsa ce da ya haifa a cikinsa, kuma shi ma sai ya tafi irin fatan da Emanuel keyi akan kar tayi regaining tunaninta, amma har ayau da shi da ɗansa cike suke da fargabar dawowar tunaninta, basa so ko kusa tayi musu nisa, a halin yanzu dai idan akace maka Mairo Adamu Bichi ce zaka rantse da Allah ba ita bace, dan babu ta inda alama tayi nuni da hakan. ƴaƴan manyan masu kuɗi suntiri su ke akanta, duk da sun san ita ɗin yarinya ce, ba yanzu zaai mata aure ba, amma kuma kowa na so ta saurare shi ne ta ba shi damar shiga zuciyarta, to amma ita tace bata da lokacin wannan shirmen ayanzu, karatu ne nata, karatu na boko burinta. har ɗan gidan mataimakin shugaban ƙasa Ayamandi Kola sai da ubansa yazo nema masa aurenta, ta buga tsalla da ƙafafunta a ƙasa tace da Dad, da zarar an kuma yi mata wannan batu, daga lokacin zata ɗauke ƙafarta daga gidan ta tafi wata ƙasar ta barsu har sai ta gama karatu zasu ji labarinta, Dad yace to shikenan anyi an gama, ba za'a ƙara ba. bata samun matsala da kowa a gidan, ta zama cikakkiyar ƴar gida, Joseph ne kawai matsalarta da yake nuna mata tsangwama, dan Allah ne da kullum sai sunyi faɗa, duk ranar da yayi mata dukan da taga ba zata iya jurewa to fa dakuwa suke ita da shi sai kace ƴan restling, randa kuma yay mata lami ƙalau sai ta ɗana masa tarko ta wani ɓangaren, yabi ya mayar da kansa kamar wani sa'anta saboda kawai ba ya sonta, Granny kuwa ido take zuba musu, babu wanda take tsawatarwa tunda baji suke yi ba, shi zuciya da tsokana, ita kuma rashin haƙuri. kuma kullum a waya faɗawa Mom yake ta dawo gida akwai matsala, idan ta tambaye shi yace sai dai ta dawo ɗin matsalar ta girmi magana a waya. ita kuma tun seminar ɗin da suka yi na oriflame a london na kwana huɗu, ranar ta shirya zata dawo sai tsintar saƙo tayi ta

Chapter 18 of 52