san ta dawo ba". Amarya ta ƙarasa maganar da kaiwa Sadiya duka da ƙafa da ke ta kai lomar nama baki.
Gwaggo tace da Zulai,"wato dai da gaske Adawiyya take ta koma gidan Yagana, yaufa gaba ɗaya ban sata a idona ba, to wallah kice mata ta dawo inba so take kuma na ƙarasa ba, ina zan iya zama babu Mairo ita ma kuma babu ita".
Zulai na gyara zaman mayafi tace,"ai sai dai ki aika Saleh ga shi can a tsakar gida, idan taji saƙon daga bakinki tafi ɗaukansa da muhimmanci...ɗa zu ƙememai tazo tayi dakan yaji babu kowa a gidan amma ƙi tayi, sai ma ɗan aiken da tacewa a faɗa mana Baba Mujibu ya bada garin kunu ta shiga banɗaki awakin Yagana sunbi ta kansa".
Saleh yay caraf ya amshe da faɗin,"ce tayi ma ba zata dawo ba sai ta gama hukunta awakin, yanzu ma dana baro gidan sai yi suke da Yaganar wai Adawiyya ta kar ya mata ƙafar tinkiya".
duk akai dariya. kuma daidai lokacin Malam ya leƙo ɗakin, suka haɗa baki wajen yi masa sannu da zuwa. "ba ku tafi gidan gaisuwar ba?". Zulai tace,"tafiyar zamu yi". yace,"to kuma zaman me kuke yi bayan kun san dare ne, za ku haƙura yanzu ku jira safiya". Amarya tayi saurin amsawa,"rufa mana asiri da faɗan Yagana". ta dubi Zannira tace,"ki shirya gobe kema Sadiya ta rakaki kiyi musu gaisuwa, mijin gidanne ya rasu".
sannan suka fita. haka suke yanzu a ɗakin Gwaggo ake yini jiddan walahairan, aita hira ana shafta saboda su ɗebe mata kewa, kuma hakan kanyi tasiri wataran.
*ƙarfe biyu da rabi na dare.*
Kulu ce a kwance kusa da Gwaggo, ba bacci take ba, a kwance take kawai, tana tunanin rayuwarta, tana tunanin irin yadda rayuwa ke gara mata.
*ZANEN ƘADDARA,* gani take kamar rayuwarta ce kaɗai mai ɗauke da *ZANEN ƘADDARA,* rayuwarta na haskawa ne da ƙaddarori mabanbanta tun a san da su ka shiga shekara goma sha bakwai a duniya, ƙaddara ke bin su kuma bata fasa binta ba, bata sauya ba, sai ma tarihi da take ganin kamar zai maimaita kansa, a tunaninta haɗuwarta da su Gwaggo rayuwar zata dai-daita ko da ba kamar a baya ba, ƙaddarar ta sauya kuma ta tsaya, to amma me?! shekara goma sha biyar, sai rayuwar take nema ta koma irin ta farko.
shekaru goma sha bakwai su a rayuwarsu ta duniya su ka fara kallon ƙaddara, ƙaddarar da ta fara binsu a ko da yaushe tana bin takunsu, tun su na guje mata har ta kamasu ita da ƴar'uwarta, ƴar'uwarta da suka zo a mahaifa ɗaya, Hassanarta, Hassanarta wacce su ka zo duniya tare. ashe dai da gaske ne rayuwa bata taɓa biyewa muradin zuciya, a baya bata yarda da hakan ba, amma a yanzu ta yarda da hakan, ta kuma gasgata, dan hakan ta faru da su ita da Hassanarta, sam rayuwa bata biyewa muradin zuciyarsu ba.
tunanin da Kulu ke yi ya katse sakamakon wayar da ke jikinta ta shiga Vibration, tayi sauri ta jawo wayar daga jikin zaninta da ta soke gudan kar Gwaggo taji ta farka, ta damƙeta a hannu sannan a hankali kuma ta sakko daga gadon ta fita tsakar gida, cikin sanɗa ta ƙarasa ɗakin girki ta ɗaga wayar san da kira na biyu da ya shigo ke ƙoƙarin yankewa.
"Kabir". ta kira sunan nasa a hankali, bai amsa ba sai da ta ƙara maimaita sunan,"Kabir". sannan ya amsa. "ina jinki fa". ta sauke numfashi,"to ya kake ya wajen na ku?". "muna lafiya". muryar Kabiru na fita ne da sautin fushi, ta san fushin yake tun daga yanda yake bata short amsa.
shiru daga shi har ita babu wanda yay magana sai can ta katse shirun da faɗin,"har yanzu baka sami shiga cikin masarautar ba?". yay gajeren murmushin da ta jiyo sautinsa,"Har yanzu kema ba ki nemi dabarar da za kiyi ki saka min muryar Maryam naji a kunnena ba?". ya tari numfashinta, "ai na faɗa miki ba, its a deal cewa ba zan ƙara ba ki wani information ba har sai kin jiyar da kunnuwana muryar da take son ji".
"to ai yanzu bacci take". ya ɗan daga sautin murya kamar wanda zai yi faɗa yace,"kullum abun da kike ce min kenan, bata nan, tayi bacci, zancen kenan kullum. ina so naji muryarta amma kun hanani, duk ranar da na kira kowa da uzurin da yake bani tsakanin ke da Amadu, shi zai ce min idan yazo gida zai haɗani da ita, amma sai dai naji batun yazo ya koma, ke kuma da dabara kawai za kiyi ba wai ki bata wayar ba amma kin gagara, ance Mu'azzam na da waya kun hanani lambarsa...ƙwarau na fara tantama da wannan yawo da hankalin da kuke min tsawon wata takwas, Amadu ba ya saɓa maganar da mu kai da shi, ku daina ɓoye min ku faɗa min gaskiya idan Baba ya aurar da ita ne".
ba wai dan ya gama magar da yake ba, ta katse shi da faɗin,"ko ɗaya ba haka bane, ba'a aurar da Hussaina ba, ai na maka alƙawarin taka ce, ta ya zan yarda a gaban idona a bawa wani ita?, Kabir zan yarda Sirrin da ke ɓoye tsawon shekaru ya bayyana, amma ba dai ka rasa Ƴata ba".
daga in da yake ya wani zuƙi numfashi idanuwansa a rufe, tabbas nema yake ya manta da wadda yake magana, dan ɗaga murya sama yay yana magana a zafafe,"kin san kuwa irin zafin da zuciyata ke min?, kin san irin yanda kunnuwana ke bala'in son jin muryarta?, kin san yanda idanuwana ke kewar ganinta?, kuka nake kullum, kuka bana fili ba na zuciya saboda tsananin kewa, kewa ta Maryam. duk safiya, duk rana, duk dare, duk baccina, wannan harufan guda ashirin da shidda da suka bada kalmomi bakwai da suka fita daga bakinta zuwa gareni amsakuwa su ke a kunnena, _Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani._, kin san yanda naji a lokacin?, idona sai da ya cika da ruwa, bugun zuciyata sai da ya sauya, haƙiƙa a lokacin ban da Sirrin da ke Ɓoye babu abun da zai min shamaki da kama hannun abata na tafi da ita...har yau idanuna hoton wannan lokacin da takeyi kukan tafiyata ne ke haskawa acikinsu, kunnuwana kuma amon sautin kukanta ne aciki". Yay shiru, yay ƙasa da murya, muryar da ta raunana, muryarsan nan mai taushi, ta koma tamkar ta ƙaramin yaron da ke tsananin buƙatar ai masa abu, ta tabbata a wannan lokacin tsugune ya ke akan gwiwoyinsa, kuma zata iya rantsewa hawaye yake yi. "don Allah, don girman Allah ki taimaka min, ki taimakawa kunnawa da saka musu muryar Maryam a san da take cikin farinciki, ki kuma goge min hoton Kukanta da ke haskawa a idona, na koma ganin fuskarta a san da take murmushin nan nata mai sanyi, ki min hakan tun kamin zuciyata ta taɓu...don Allah, don Allah, na roƙeƙi nima ki taimaka min kamar yanda na ke taimaka miki akan halin da ahalinki su ke ciki...wallahi tallahi ina son Maryam, ina sonta, ina sonta da dukkan gangar jiki da ruhi, karki hanani ƴarki don Allah ki cika min alƙawari".
ɗiff ya kashe wayar, tabi screen ɗin wayar da kallo, ya zata yi?, ya zata yi ta sanar da Kabiru cewar Mairo ta ɓata ba'a ganta ba?, ba zata iya ba, ba zata iya wannan kasassaɓar ba, haka kawai! iyayensa da ƴan uwansa sun ɓoye masa sai ita ce zata sanar masa. har yau bai san da ɓatan Mairo ba, domin Baba yace kar wanda yayi gangancin faɗa masa, duk da da ma ba samun damar wayar suke da shi ba akai akai, sai idan Amadu yazo ne zai ce musu Kabiru yana gaishesu sannan ya haɗa su.
ajiyar zuciya ta sauke ta fito daga kitchen ɗin, sai taga kamar giftawar mutum dan haka tayi saurin nufar hanyar banɗaki, daga wajen banɗaki kana hango ƙofar ɗakin Gwaggo, mutum ta gani ya shiga ɗakin, babu jimawa kuma aka fito, ba zata ce waye ba, ko wanda take tunani, tun da lulluɓe yake da babban zani hatta kansa baka gani. to waye?, ta fara tsorata fa! wancan satinma ta tashi sallar dare ta shiga uwar ɗaki, fitowar da zata yi taga kamar mutum ya laɓe a bayan ƙofa, saboda sallar da zata yi sai batabi takan ta duba ba, dan lokacin gab ake da ai kiran farko, kasancewar bata farka da wuri ba, kuma tana cikin sallar zata tafi sujjada sai inuwar mutum ta gani ta fita, abun ya ɗaure mata kai a sanda ta sallame tana dube-dube bata ga komai ba. sai ta barshi a cewar idonta ne ya haska mata hakan, gizou kawai take gani, shaiɗanne ke so ya sanya mata wasi wasi, ai dama taji wani Malami ya faɗi hakan, idan shaiɗan ba ya so kayi ibadar cikin dare sai ya dinga sanya maka tsoro.
to amma ayau dai tabbas mutum ɗin ta gani, idonta ba gizo yake ba, kuma koma wane shi ɗin me cutarwa ne, gabanta ya faɗi, tai ɗakin da gudu, tana zuwa ta ƙaro hasken fitila, a sa'ilin ta ƙara ganin inuwar mutum ta gimla ta jikin labule, ba so take ta san wannan ba, lafiyar Gwaggo, dan haka tayi kan Gwaggo da sauri tana taɓata har ta farka, Gwaggo ta bita da ido ganin duk ta rikice, kuma yanda take dudduba jikinta kamar me neman wani abu.
Gwaggo ta farka tace, "Hauwa lafiya?". "kina jin wani abune ajikinki?". ita ma ta jefa mata tata tambayar ba tare da ta amsa tata ba. "babu abun da nake ji, wai menene hala?". Kulu ta haɗiyi wani yawu a maƙoshi tana aikin sauke numfashi da sauri sauri. "kuma da kina bacci ba ki ji wani abu ya taɓaki ba?". "ke ko dai mafarki kika yi ne da ya tsorata ki kika tashi a hargitse haka?". bata so ta ɗaga mata hankali, dan haka dole ta ɓoye mata ainihin abunda ta gani, kuma idanma tace zata faɗi hakan babu mai yarda da ita don babu hujja. "mafarki nayi mara daɗi, kiyi haƙuri na tasheki".
Gwaggo kallonta take da rashin yardar abun da ta faɗa, tace, "fuskarki bata bani tabbacin abunda kika faɗa ba Hauwa, gaya min gaskiya". "babu komai fa Yaya, ance ba'a son faɗar mummunan mafarki". a yanda take maganar a tsorace da kuma nuna rashin gaskiya sai tayi mata sak Mairo. kai ta gyaɗa,"to Allah ya sauya shi ya koma mai kyau...kinyi sallah ne?".
"a'a, yanzu dai zanyi". "to kiyi adua sosai, ni bana jin ma zan iya yi saboda ƙafata tana min zafi, kamar ana caccaka allura nake ji". Kulu ta tsareta da ido,"to ko kiyi sallar ƙila ta daina ciwon". "ba zan iya ba, ki dai ƙara shafa min maganin da Aminu ya siyo, dan naji daɗinsa ɗazu, har na kwanta ba irin tsamin nan da take yi". hannu na rawa Kulu ta ɗauko maganin, ta kwalɓato shi sai da ta kusan juye mata rabi sannan ta bari, saboda taji Zannira tace maganin da tsada ɗari takwas aka siyo.
bayan ta idar da sallah ta jima zaune akan sallaya, hankalinta ya karkata gaba ɗaya kan mutumin da ta gani a ɗazu, waye?, waye?, so take tasan waye?, macece ko kuma namiji?, daga ina yake?, tana da tabbacin koma wanene Gwaggo yake son cutarwa, ai na zata ganshi ta faɗa masa da kakkausar murya matsawar tana tare da Gwaggo yayi kaɗan ya cutar da ita, saboda haka ya sake sheƙa, ba anan ba, ba anan inda take tare da ita ba, cutarwarsa ba za tayi tasiri akan Gwaggo ba.
Please vote again and again and again.
*Comment,Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*25)*
*Kirkos, Legacy Luxury apartment Addis Ababa, Ethiopia.*
*06:30Am.*
_Here in silence i wait, there's nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how many aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm counting the hours without you, and i dont know how much i can bear, becouse i miss you morethan words can says, and i need you hear in my life always, yeah i miss you._
sautin waƙar i miss you ta Beverley Craven ce ke tashi a hankali acikin madaidaicin living room ɗin, waƙar da ke tafiya haɗe da bugun zuciyarsa, kuma a dai-dai lokacin da kalaman waƙar su ka ɗan tsaya, a dai-dai lokacin ne Abdurrahim ya kashe laptop ɗin da waƙar ke tashi daga ciki, hannunsa ɗauke da ƙaramin towel na wanka yana goge ruwan da ke sumar kansa, yaja tsaki a lokaci ɗaya.
yaci gaba da tsayuwa a kusa da center table, ya ƙarasa sharce sauran ruwan da ya rage a sumar tasa, sannan ya tsaida kallonsa akan Kabiru, wanda ke miƙe akan sofa bed yayi matashi da duka hannayensa biyu ta bayan kansa, idanunsa a rufe, zararan gashin idon nan sun miƙe, in banda shi Abdurrahim ɗin da yasan halin abokinsa, kowaye ya ganshi a wannan yanayin ba zai ce ba bacci yake ba.
yaja tsaki tare da ɗan ɗaga sautin muryarsa yana faɗin.
"waƙa ɗaya! kullum baka da aikin sauraro sai na waƙa ɗaya. to ka miƙe haka kayi wanka lokaci na tafiya, you know very well Malamin nan ba shi da mutumci".
ya sani, ya sani wannan tsakin na ƙorafi da ya zama ɗabi'ar abokin nasa a halin yanzu dole sai yayi shi, dan haka ya murmusa yana ƙara faɗin,"ni dai nace ka tashi, ka tashi kawai Malam. watanni nawa suka rage?, watanni shidda ne kacal suka rage ka koma hutu ka ganta, ka sata a gaba kana kallonta da sauraron muryarta ba waƙar da kake cika min kai da ita a kullum ba".
shirunsa ya haɗe da buɗe idon Kabir ɗin ya saukesu tar a kansa, idon da ya rufesu tun a sanda sautin waƙar ya soma tashi, haka yake a duk san da ya kunna waƙar, waƙar tana tafiya ne da bugun zuciyarsa, yayin da hoton Maryam(Mairo) ke haskawa a idanun nasa.
kallon Abdulrahim ɗin yake, kallo na ka taɓu, kana buƙatar ganin likita. "watanni shidda kace?, watanni shidda nan gaba da za'a haɗa su bada shekara guda da wata biyu, su zan ƙara kaiwa ban sakata a idona ba?, da wanne haƙurin?, daga ina juriyar tawa take?...ba ka da hankali, ba ka da hankali sam Abdurrahim, kaje kaga likita ya duba maka ƙwaƙwalwarka". Abdurrahim ɗin ya zauna akan sofa yana kallonsa yace,"ko makaho ya shafa tsakanin ni da kai zai faɗi wanda yafi cancanta da ganin likitan ƙwaƙwalwa Kabir, kai ka dace da ganin likita bani Abdurrahim Yusuf ba, saboda ni ban zauce ba kamar kai".
a lokacin da Kabir ya miƙe yana sauke ƙafarsa a ƙasa, yake cewa da shi,"baho kawai, na tabbata da ace kana da wadda ta shiga zuciyarka tayi bake-bake ba zaka dinƙa yi min wannan shirmammun maganganun naka ba. har yanzu baka san SO ba, ji kake ana faɗansa, ana kuma aiwatar da shi a aikace, amma baka san daɗinsa da zafinsa a zuciya ba, baka sansa a gangar jiki ba, baka sansa a ruhi ba. dan haka idan ka ƙara furta min zancen zan ƙara wata shidda anan gaba ban koma ƙasata naga Maryam ba sai na daki bakinka ya fashe yayi jini, karka fasa kaci gaba, kaga yanda zanyi da kai acikin gidan nan da muke rayuwa mu biyu".
ya san hakan zata kasance, masifa!, wannan faɗan nasa sai yayi shi, ba a haka Kabir yazo ƙasarsu ba, a me haƙuri yazo, amma yanzu SO yasa ya tashi daga Kabir ɗin da ya sani tun wasu satika na fara rayuwarsu a makaranta tare, ya rikiɗe ya koma wani Kabir ɗin na daban, zautacce wanda ya haukace akan soyayya, soyayyar da yake ganin kamar ta kusa yi masa illa.
gajeran murmushi me sauti ya tsaya a iyaka leɓen Abdurrahim ɗin a sanda Kabir yay shiru da maganarsa, sautin murmushin da ya sa Kabir ɗin dakatawa daga tafiyar da yake zai wuce bedroom, ya juyo ya kalle shi, kuma wannan karanma a zafafe ya shiga magana kamar zai rufe Abdurrahim ɗin da duka.
"banda kuɗin jirgin komawa shi kake wa dariya right?". Abdurrahim ya ɗago da kansa daga barin danna wayar da yake ya kalle shi, tabbas Kabir ya haukace da gaske ba wai a faɗa ba, banda ya haukace a yaushe yaji yayi dariya, murmushi fa kawai yayi.
"to daɗin abin dana zo ƙasar taku ba zaman banza nake yi ba, ina karatuna ina kuma sana'ata, kai ka sani, kuma shaida ne, ka kuma san ayanzu zan iya biyawa kaina kuɗin jirgi kaima kuma na biya maka. ofcourse ni ɗan ƙauyen Bichi ne, amma idan ka tashi rubutu a sabon update list naka na bin ƙwaƙwaf ka rubuta KABIR ADAM BICHI a sahun farko na masu kuɗin garin bichi, labarin baya daban, na yanzu ne ke tafiya, kuma ita ake magana, ka san da wan nan, ka kuma bawa wani labari". yana gama maganar ya juya a fusace ya wuce bedroom, Abdurrahim kuma yabi bayansa da ido yana dariya, yana ba shi dariya idan yana wannan masifar, duk da cewar yana bashi tsoro a wasu lokutan saboda yanda idanuwansa ke sauya launi daga asalinsu, to amma shi wallahi a yanzu Kabir ɗin ya zame masa comedian.
gemunsa nan dai me ɗan tsayi shi yake tajewa kamar yanda ya saba ko da yaushe a ƙarshen shirinsa. ɗinkin habesha kemise ne ajikinsa, farar riga da akayi aikin jiki da baƙin zare, da kuma ratsin golden, red and blue, sai baƙin wandon plane yadi me kauri, ɗinkin ƴan ethopia ne, shigar da tun ranar da ya fara yinta yawanci idan suka ganshi sai suce dama shi asalin ɗan ƙasar ne, ba da kayan kaɗai ba, hatta ga zubin halittarsa ma.
ya ajiye ƙaramin cumb ɗin san da ya gama tazar, abu na ƙarshe da ya ɗauko ya saka ayau baƙin glass nasa me O shape, hannaye zube cikin aljihun wandon ya tsaya yana kallon kansa a madubi. Yayi kyau, irin kyan da ke haska ƙyalli a idon me kallo, ya fito a cikakken ɗan gayun birni ba ɗan ƙauye mazaunin can ba. ya ƙara haske akan asalin wanda yake da shi, sumar kansa me zubin ta buzaye ta ƙara cika da baƙi, siririn hancinsa ya ƙara tsayi, sai wannan doguwa kuma siririyar fuskar tasa da ta rame, ramin idon ya faɗa ciki, duk a saboda kewa, kewa kuma ta Maryam, Mairo ta ƙauyen bichi.
ya saki wani murmushi me tattare da tarin ma'anoni, bayyanuwar siririyar wushiryarsa a sanda yay murmushin sai wani kyawun na daban a tare da halittar tasa ya ƙara fita. tana son kyau, tana tsananin son kyawun da Ya Kabirunta yake shi, ya san da wannan, to wane kalar jin daɗi da farin ciki da murna zatayi a sanda fararan idanuwan nan nata masu kyau suka yi tozali da shi a KABIR ba a KABIRU ba?, ta kalle shi a irin yanda take ta hasaso shi a wata rayuwar ta daban, ba irin wadda suke ciki ba, rayuwa ta hutu da jin daɗi, rayuwar cikin birni bata ƙauye ba, rayuwar wayewa da gogewa, rayuwar da kuɗi suka zauna masa ajiki.
_"Ya Kabiru wai idan mutumin da ya haɗa nagarta da cikar kamala ya samu hutu da jin daɗi da kuma kwanciyar hankali, mutum dai irin wanda ba zai rasa wata ƴar mitsitsiyar matsala ba, me gogewa a fannin ilimin addini dana boko, to wai kyau yake yi irin me ɗaukar hankali, haka naji ana faɗa, to wai hakanne?."_ kalaman Mairo a wani lokaci can baya suka haska a kwanyar tunaninsa, a lokacin ya bata amsa ne da, _"ki cire wai ɗin, maganar haka take."_ ta ƙanƙame shi a sannan cikin murna tana cewa,_"Allah ya kai min kai wan nan matakin, matakin da kowa ne ya ganka zaiji ka burge shi...idan Yagana tayi tsawon rai ta tofe min kai da tofin Allah tsine saboda ƴan hasidin iza hasada"._ murmushi kawai yay mata a sannan bai ce komai ba, amma ayanzu zai ce wani abun, dole ma ya faɗi wani abu.
kamar kuma tana kusa da shi ne, kamar kuma da ita ɗin yake magana, kamar kuma tana sauraronsa ne, acikin muryar nan tasa me taushi da zurfi ya faɗa a fili ba a zuci ba,"Kabir ɗinki ya samu, ya samu wannan abun da kike masa fata, na cikin mafarkinki da kuma hasashenki, domin ya kusa kaiwa matakin, ƙiris ya rage, dan komai ya kammala, linta ɗaya ce tai saura acimma ginin, ita ma kuma lintar ba me tsayi ba, kwalin degree da shiga office ne kacal, ofishin nan da kika ce kujerar cikinsa zata ke juyawa dani, irin sanyin ɗakin Bella da ke fitowa daga inda ba'a sani ba yake sauka ajikina, jin daɗi da annashuwa da annuri su ke bayyana a tare dani...daga nan mafarkinki ya tabbata, ya gama tabbata Maryam".
yay shiru yana me tsuke baki, inda wannan pink lips ɗin nasa su kai wani kyau a tsukewar. zancen da ya gama a fili kuma ya koma na zuci da wata maganar ta daban. _a sa'ilin da nawa mafarkin kuma zai tabbata, lokacin da kika gama makaranta, lokacin zan bayyanar da manufata akanki ga su Baba, su aminta da sun bani ke. a ɗaura mana aure na ɗaukeki na kai ki gidana, mu tabbata abu ɗaya, rayuwarmu ta sauya, ta sauya zuwa ta ma'aurata, na daɗa killaceki a zuciyata kamar yanda na killaceki acikinta na tsawon shekaru goma, na fito da wannan ɓoyayyar ƙaunar dana ke ɓoyeta na nuna miki ita zahiran miraran, a lokacin zan koma miki tamkar yaro, zan zame miki tamkar ƙaramin yaro a sanda nake faɗa miki kalmar SO, irin son da muka cimma a yanzu ba irin na waccen lokacin ba...dan zan shayar da ke madarar so da ƙaunata, ki kasance a kwance a ƙirjina a duk san da muke tare, ki kasance goye a bayana a duk san da na dawo wurin aiki...Alƙawari, Alƙawari ne nai miki da duk irin tsarin gidan da kike so acikinsa za ki zauna._
sai dai me zai faru?, zuciyarsa ce yaji tayi wani irin duka da bai taɓa jin tayi ba, lokacin da yake tunanin ai ya rabu da duk wani challanges na rayuwa, ashe fa a lokacinne zai fuskanci babban ƙalubale mai girma, lokacin da al'umma za su shaida auren KABIR ADAM BICHI da MARYAM ADAM BICHI, ƙwayayen halittar da kowa yake da masaniyar cewa ciki kawai suka raba a wajen fitowa, Uwa daban-daban ta ƙyanƙyashesu, amma abun da aka zuba a samar da ƙwan halittar tasu na uba ɗaya ne, Uba ɗaya Malam Adamu Me Faskare, to wanne mahaukacinne zai karɓi waliccin wannan auren? kuma waɗanne mahaukatan ne zasu tsaya shaidar auren da za'a gina akan haramci?, bayan sarki Allah, sai shi, sannan Baba da Gwaggo da kuma ita Kulun da tayi sanadiyyar zuwan Maryam ɗin duniya, babu wani mahaluƙi da ya san Mairo ba ƴar gidan bace, ba ƴar Baba bace, ba kuma ƴar Gwaggo bace, ba kuma ta gadon komai a gidan...to ta ya shi da mahaifiyarta za su tsira daga hakan su cimma burinsu bayan basa son kowa ya san da SIRRIN ƁOYE?.
zancen zucin ya katse, walwalar fuskar kuma ta sauya, wata walƙiya ta gifta acikin idon nasa, sannan tsawa ta sauka a tsakiyar kansa duk a lokaci ɗaya, lokaci ɗaya da shigowar Abdurrahim cikin ɗakin, saboda haka ya* lumshe idonsa yayi kamar bai san da shigowar tasa ba, duk kuwa da sun haɗa ido ta cikin mirrow.
"Pizza nasa akayi order ba zan iya shiga kitchen ba, kazo muyi breakfast cikina ya fara ƙugi".
ya jisa, kuma Abdurrahim ɗinma ya san ya jisa amma yay kunnen uwar shegu da shi, sai dai ya zai yi da halin abokinsa kuma amininsa a halin yanzu?, haka zai ta binsa ta yanda ya sauya ɗin.
yasa fork ya yanki Pizza ɗin ya kai baki ya tauna, har sai da ya haɗiye sannan ya ƙara cewa da shi.
"fushi?, baka sakko ba kenan?, to kayi haƙuri, Allah ya huci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 52