Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwatsam watarana naje asibiti sai muka haɗu da Major shi ma yaje, an masa aiki an cire masa bullet dalilin wani harbi da ƴan bindiga su kai masa. har ga Allah soyayyar Major ta riga tayi ginuwar da ba zan iya kimantata a cikin zuciyata ba, ina ganinsa sai na manta da duk halin baƙin cikin da soyayyarsa ta jefani a ciki, da baƙin tabon da ya bar min. shi ma cikin tsananin tausayina ya rungummeni yana ƙara bani haƙurin abin da ya faru, abinka da Mace raunin duk sai ya ban tausayi ganin Babban mutum kamarsa yana kuka da kuma tarin nadama ɓaro-ɓaro shimfiɗe akan fuskarsa. tare muka dawo nigeria da shi inda ya sa ni a wani gidansa na kano, duk bayan kwana biyu yana zuwa wajena kasancewar shi yana zaune ne a abuja. ranar da na tashi da naƙuda ba ya garin, Aaliya ta ɗaukeni muka tafi asibiti shi kuma yace yana kan hanyarsa ta zuwa, sai da na kwan ɗaya ina labour ƙarshe sai CS aka min aka ciro min twins, maimakon naji ina sonsu sai naji kaf duniya babu waɗanda nake ƙi sama da su, tun da Major ya damƙa min su a hannuna naji kamar na murɗe musu kai, ko nono da akai akai na basu nace wallahi ba zan bayar ba sai dai a yanke min nonon na zauna a haka, ko kuma su mutu, babu yanda ba'ai da ni ba naƙi, ga kuma ruwan nonon na zuba amma na ƙwammaci na sakeshi yana jiƙa jikina, ƙarshe sai Aaliya ce ta ɗau kofi ta tara ta zuba a fida ta basu suka sha sannan suka daina tsanyara kukan da suke yi. shi kansa Major da farko yana ta murna da ƴaƴan musamman macen kasancewar cikin ƴaƴansa kaf babu mace, amma daga baya sai murnar tasa ta ɗauke, yace shi ba zai iya karɓarsu ba yana gudun girmansa ya zube a idon duniya, nima nace masa bana ƙaunarsu tun da ban samesu ta hanyar da ta dace ba, saboda haka ya zubasu a leda kawai yaje ya yasar da su, ko kuma ya zuba su a kwali yaje ya ajiye me so idan ya gani ya ɗauka...". tarin da ya sarƙe Kulu shi ya dakatar da ita daga bada labarin, abu kuma kamar wasa sai aman jini, nan da nan hankali ya tashi Malam yace ai sauri a kira me chemist, ita kuma tana cikin wannan hali babu sunan wanda ta ke kira sai na Mairo har bakinta ya ɗauke. ***tun da Ya Kabiru ya rufeni bai ko waiwayeni ba, tun ina hawayen har suka ƙyafe, kawai sai na karayar da kaina a jikin bangon ɗakin, na rufe idanuwana ina tunanin irin ƙaluban da zan fuskanta a sabuwar rayuwar da zan shiga, ciki kuwa har da aurena, auren da na tabbata sai an rufa asiri sannan za'a yishi, idan ma na sami me auren nawa kenan, ɗaya ɓari na zuciyata yace,_"to ke Mairo ban da abinki tunanin za kiyi ma yi aure ai bai taso ba, dan babu ɗan halak ɗin da zai auri shegiya, ba ki ga misali ga uwar taki bane, da tayi cikin shegen ai babu wanda ya aureta gata nan har yanzu a zaune...ci gaba da zaman gidan nan ma bai taso ba, yanda ƴan gari suka gama jin kowace ke shikenan kowa zai fara tsangwaramarki ana goranta miki, ai ki tashi kawai ki tafi ki nemawa kanki mafita, shege ai sai shiga duniya. kije kema ki ɗauko musu abin kunyar kizo ki dire musu a gabansu kowanne cikinsu ki bashi ɗai-ɗai."._ sai kuma ɗaya ɓarin zuciyarta tawa ya gargaɗeni da,_"kul, karki soma, ita ma mahaifiyar taki da hakan ta kasance da ita ƙaddara ce"._ sai kawai na rumtse idona gam da ƙarfi na furta,"a'a ƙarya ne ba ƙaddara bace, kawai dai ta zaɓi ta fito dani ta wannan hanyar ne, son zuciya ne irin nata, kuma wallahi sai na sata kuka ba zan janye daga ƙudurina ba". sai nayi shiru naci gaba da saƙe-saƙen neman mafita a gareni, mafitar fita daga cikin wannan ɗakin, ban da ace Ya Kabiru ya ɗaureni da ko daƙiƙa ɗaya ba zan ƙara ba a cikinsa, dan yanda nake jin wani mugun ƙarfi ajikina tsab zan jijjige ƙyauren ɗakin na ɓanɓare shi nai ficewata, kuma ba tare da kowa yay min burki ba, domin yanzu a shirye nake wajen karawa da kowa. Akila ta riga ta goga min baƙin tabon da babu ta yacce za'ai na goge shi, sam ba zan iya ci gaba da zaman cikin gidan nan ba balle cikin garin, to idan ma na tafi ina zan nufa?, ai kawai na biyewa shawarar zuciyata na shiga duniya shi ne kaɗai mafita, domin da shi na dace. duk da cewar a duniya ba zan taɓa mantawa da Baba ba, sai dai shi ma ba zan ƙara waiwayarsa ba tun da ya ɓoye min asalina, mene yasa tun farko ba su sanar min wace ni ba sai da aka zo wannan gaɓar, shi ma kuma da banji ba shikenan haka za su ci gaba ɓoye min?, har sai sun aurar da ni sunja min baƙin jini a wurin dangin miji?, tabbas a yau idan na bar garin nan ba zan kuma waiwaiyen wannan gidan ba illa kawai na san duk inda zan shiga Baba da Gwaggo su na nan maƙale a zuciyata, kuma ba zan fasa binsu da adu'a ba. wani guntun murmushi me ciwo da takaici ya subce min a saman leɓe, wato Akila ma bata da tunani, da har ta ke tunanin ta ƙaƙabawa Ya Kabiru ni ya aura, saboda dai ita zuciyarta azzaluma ce har yanzu bata rissina daga saɓon Allah ba. ban da haka ina Kabiru ina ni Hussaina shegiya, dole Baba yaƙi amincewa dan shi yasan ɗansa bai cancanci auren mace mai gurɓataccen asali irina ba. kuma ni kaina ko da zan mutu babu aure ba zan taɓa aurensa ba, dan yafi ƙarfina, ni shegiya shi kuwa cikakken mutum me cikakken usili, ai abun ma babu gami. ina cikin wannan tunanin naji an buɗe ƙofa, ban ko waigi wajen ba. Adawiyya na gani tsugune a gabana tana kiran sunana, ni dai da ido kawai nake bin ta dan ko motsi ban ba. tasa hannu ta shiga warware ni da igiyar tana ɗan shashsheƙar kukanta, kukan da ko ban tona zuciyarta ba nasan na munafurci ne, ƙasan ranta fal frinciki, yanzu kuwa ko babu asiri sai su karɓe Al-Mustapha da hannunsu, ko ba shi ba ma ni na bar musu kowa ne. "sannu kinji ƴar'uwata". ta faɗa tana rungumeni. sai kawai naji saukar wasu sabbin hawayen na sakko min, na buɗi baki murya na rawa nace,"ashe kema kin jima kina min kallon ƴar zina shi ne ba ki taɓa faɗa min ba". ita ma muryar tata rawa ta ke tace,"wallahi ban sani ba. ni ban taɓa sanin da wannan zancen ba". na haɗiye guntun yawu da cewar,"ta ya akai kika buɗeni?". tace, "dagani sai Inna ne a gidan, Baba da su Yaya da Yagana sun wuce kai Ummanki asibiti tana ta aman jini har ta kai ga ta suma, kuma an yayyafa ruwan amma bata farfaɗo ba, shi ne Idris me chemist yace su wuce asibiti...Ya Kabiru bai sani ba na zare maƙullin a aljihun wandonsa". sai na sake yin murmushin da sautinsa ne kawai ya fita, na furta,"Allah yasa ma mutuwa tayi, ta hutawa kanta daga hukuncina. na gode miki". nasa hannu na hure ma ta ido daga tsareni da shi da tai, na ɗaga ma ta gira da cewar,"yane, ki tashi ki fita kar tsautsayi ya dawo da Ya Kabiru ya tadda ke anan, kin san halinsa sarai". sai tayi azamar miƙewa da cewar,"to kema ki fito dan Allah, Inna ma tace karki zauna ki gudo ɗakinta, ko me ki kai ai ba laifinki bane". "jeki kawai, ki ja min ƙofar yanzu zan fito". bayan fitarta na tsawon daƙiƙa uku kamin zuciyata ta gama ayyana abin da ya dace da ni a yanzu, saboda haka na miƙe na ƙarasa ga ƙatuwar akwatin Ya Kabiru me shegen kyau, na buɗeta na shiga binciketa, har nayi nasarar samun wasu kuɗaɗe masu yawan gaske da ban san iyakar adadinsu ba a cikin wani envelop, na gyara zaman trolly ɗin yanda ba zai fuskanci an taɓa masa wani abu aciki ba. sannan na ɗauki p-cap ɗinsa na saka na fice daga gidan ba tare da ko su Adawiyya sun sani ba. gidan Yagana na wuce kai tsaye, da zuwana na ɗauki ɗaya daga cikin ɓaƙaƙen abayata da Ya Kabiru yay min tsarabarsu na saka, na lulluɓe jikina ruf ta yacce babu me shaidani balle ya nunani yace ga shegiyar can, na ɗauki akwatun kayana nayo waje, har na saka ƙafata akan dakalin ƙofar ɗakin sai idona ya zuƙo min wallet ɗin Ya Kabiru da ya ban ajiya ɗazu haɗe da wayata a ajiye kan shimfiɗar da na tashi, na koma na ɗauko ina goge hawayena ta cikin niƙabi, Allah ya sani zanyi kewar wannan ɗakin da mamallakiyarsa. zuciyata bata yanke shawarar inda zan dosa ba sai da na shigo garin kano, na samu wuri na zauna gefen wani me sai da idomie, ban san wacce unguwa bace, ni dai kawai nace a saukeni a wurin. warin taba sai tasowa yake daga wurin me indomien da alama ƴan shaye-shaye ne mafi yawanci zaune a gun, kuma sai na jiyo ɗaya daga cikinsu na faɗin,"Baaba kaga wata mace da lulluɓin baƙin kaya ajikinta, anya ba ɓarauniyar yara bace". hantar cikina ta kaɗa, kamin na ɗago na kalli inda suke sai ganinsu nayi tsaye a gabana su na tuhumata. na yaye niƙab ɗin ina zazzare ido nace,"wallah ni ba me satar yara bace, matafiya ce dare ne yay min a hanya kuma ban san kowa ba anan". sai baƙin cikinsu wanda duk gashin kansa yafi muni yace,"kuma shi ne saboda ki jawa me so asara za ki zo ki zauna a irin wuraren nan". yana tangaɗi ya kama hannun trolly ɗina yana cewa,"muje na ba ki masauki zuwa wayewar gari". duk na bisu da ido, dan da ganinsu ba mutanen arziƙi bane, sai nayi saurin gyaɗa kaina da cewar,"a'a zanje hotel na kwana acan..". ban ƙarasa ba na tsakiyarsu yay wata iriyar dariya yana faɗin,"au ashema ƴar hannu ce, kawai to kizo muje muma can ɗin da za ki zauna muhalli ne me kyau. inda sabo ai an saba zamu more dare ne kawai". a wannan karan ba ƴaƴan cikina kaɗai ba, ni kaina sai da na kaɗa, na shiga rarraba idanuwana ina tunanin ta yanda zan rabu da su lafiya, ga titi sai ɗaikun motoci da ke wucewa. babu shiri na shiga sakawa napep ɗin da ta zo wucewa hannu, Allah ya taimakeni kuwa ta tsaya, ban tsaya faɗa masa inda zai kaini ba na faɗa ciki ina ce musu na gode, nace da me napep ɗin ya shigo min da trolly ɗin, ban sami natsuwa ba sai da naga mun bar wurin gaba ɗaya sannan na shiga sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya. munyu tafiya me nisa sannan me nepep ɗin ke tambayata,"Hajiya ina zamuje ne, dare fa yayi ƙarfe goma yanzu". ina zance ya kaini ne?, ni gaba ɗaya ma ban san wurin da zan dosa ba, kamar nace masa ya kaini matattarar karuwai sai kuma zuciyata ta kwaɓeni da hakan, ban san sanda bakina ya furta masa airpot. "amma kin san kuɗinki zai ƙaru ko?". nace masa,"babu komai muje". a filin jirgin Malam Aminu Kano na sauka, sai da na sauka kuma na shiga tunanin wurin zuwa, da na zo nan da sunan hawan jirgi wacce ƙasar zan nufa to?, tayama za'ai nayi bucking a wannan lokacin?, ba lallai kuɗin da na ɗebo su isheni ba. dama na ɗauka ne dan siyan abincin da zan riƙa ci, da ƙananun buƙatuna. security ya ƙaraso in da nake yana min magana akan na matsa daga wurin, naja trolly na na shige cikin reception, na ɗauko envelop ɗin kuɗin na shiga ƙirgawa, tun ina lissafin dai-dai har ya ƙwace min saboda yawan kuɗin, sai kawai na zuba musu ido ina kallo. can na miƙe na ƙarasa wurin cashier ya ƙirga adadin kuɗin naira miliyan ɗaya, na tambayeshi wacca ƙasa za su iya kaini?, yace min za su kaina ƙasashe da dama in har bani da wani kaya da yawa, har zan ce masa ai min ticket na saudiya sai kuma maganar Akila ta haska acikin kaina, Qatar!, dan haka kai tsaye nace masa Qatar. yace min akwai jirgin da zai tashi ƙarfe sha biyu da rabi, amma na sani in dai ticket na ke buƙata ayanzun nan kuɗin da zan biya sai ya haura ɗari biyar, babu yanda ban da shi ba akan ya haƙura ya samin duka 550 ɗin yace sai nayi addition ɗin 100k. na buɗe wallet ɗin Ya Kabiru na zaro atm ɗinsa na bashi, nace ya zara aciki. ƙarfe sha biyu da rabi jirginmu ya tashi, kuma ƙarfe shida na safe jirginmu ya sauka a ƙasar Qatar. saukarmu a airpot na ciro wayata nayi serching hotel nearby. "Hilton Doha, Diplomatic District". nace da texi drivern na shiga na zauna na daidaita zamana. online booking nayi dan haka ina isa kai tsaye stairs na hau zuwa room ɗin da na kama, ina shiga nayi wanka na shirya sannan na kwanta ina tunani kala kala, tunanin da ke neman tarwatsa zuciyata, hakan yasa na tashi na fito dan naga gari ko na sami sassauci a zuciyata. tafiya na ke ina kalle-kallen yanda ƙasar ta ke gwanin sha'awa, ba irin nigeria ba, kowanne bulding nasu me kyau da tsari, gasu kansu mutanen garin masu burgewa. ina tafe ina karanta wani symbol ban sani ba kawai naji nayi karo da mutum wayoyin hannayenmu duka suka faɗi, muka sunkuya muka ɗauko mu nayiwa junanmu sannu, sai dai a san da hannuna yay gogayya da farin hannun da ke ɗauke da jan lallai sai naji zuciyata tayi bugawar da ko a san da naji cewar ni shegiya ce batayi ba, haka kuma naji ina shakkar haɗa ido da koma wace idan ta ɗago. ko dana baro gida bana faɗuwar gaban da nake yi a halin yanzu. "Sannu, kiyi haƙuri ba da sanina na bigeki ba". abin da na faɗa kenan cikin harshen turanci, sai dai ita abin da tace min da larabci ta faɗa. da ma nayi goggling akan yaren ƙasar english da arabic kawai suke ji saboda haka ne ma yanzun na bata haƙuri da english. ɗagowar da zanyi da kaina kawai sai naga Kulu a gabana, kallonta nake da maɗaukakin mamakin da ke haskawa a ƙwayar idona, tare da wani kallo na daban da ni kaɗai nasan ma'anarsa. ita ma kallona ta ke da mamakin, mamakin da zan iya kiransa na rainin hankali, dan ko ban rantse ba yacce idanuwanta ke nunawa shaida min yake ba su gane ni ba. sai na buɗi baki nace,"hmm mayaudariya kawai". na faɗa tare da bangajeta zan wuce, ba ganinta a ƙasar ne mamakina ba, yanayin canjawarta shi ne abin mamakina, kai bakace matar da na baro cikin wani hali ba, ta gudo ta barsu cikin tashin hankali. sai naji ta dafo kafaɗata, na dakata da tafiyar ta zagayo gabana. cikin fusata nace,"wai nufinki hakan da kike shi zai sa na sauka akan ƙudurina ne. ko kaɗan bana tausayinki, kije kiyi rayuwarki nima nayi tawa, kije ki ɗora daga inda kika tsaya, nima zan shigo sahunku". da mamakina na rainin hankalinta sai ji nayi tace,"bana jin abin da kike faɗa cikin yaren da kike magana, yare biyu nake ji arabic and english, kina iya min magana da su". nayi mata wani kallo na kin raina min hankali, naja tsaki zan wuce maganarta ta dakatar da ni. "please who are you?". na zuƙi numfashin fusata na sauke sannan nai juyo gareta nace,"ni ce shegiyar ƴarki da kika haifa a yawon tazubar ɗinki, ƴar da sai da ku kai tarayya da ƙazamin abokin karuwancinki wato Major Tosin sannan ku ka samar dani. Akila ina fatan yanzu kin shaida wace ni". idan na lura kamar tayi suman tsaye ne, saboda haka sai na buɗe jarkan swan water ɗin da ke hannuna na fesa ma ta shi duka a fuska ko ta samu ta farfaɗo daga duniyar tunanin da ta faɗa. sai dai me! kamar yanda na tsammaci dawowarta, haka na sami saukar marin da sai da ya kaini har ƙasa, marin da shigarsa ya haddasa ganin tartsatsin wuta acikin idanuna, marin da sai da yasa jina da ganina suka ɗauke gaba ɗaya, azaba tasa nayi zaman dirshan a ƙasa ina jiran dawowar hayyacina, sai dai ji nayi kamar a lokacinne ta ke wankeni da marin, da sauri na dafe kuncina ina sake mayar da numfashi da sauri sauri. a ƙalla na ɗauki tsawon daƙiƙa biyar kamin na dawo duniyar da na bari, kuma ina ɗago kaina naga har lokacin tana tsaye a gabana, da yanayin fuskar da na kasa fassara abin da ke shimfiɗe akanta, tunanina ya tsaya cak san da naji ta ambaci sunana. "Maryam". ta faɗa da kakkausar muryar da ke shaida min da gargaɗi ne zai biyo bayan sauran furucin. sai dai nima zuciyata ta kai maƙura, dan ta jima da bushewa, ko kaɗan bana ma ta kallon wannan sunan na uwa da ake ambata, na miƙe a fusace zan kai hannuna fuskarta ta riƙeni ta watsar da hannun tare da sake sauke min wani sabon marin da ya fi wancan don lokaci ɗaya na nutsu. idonta kamar na mage akaina tace,"ki tsaya ki saurareni kamin na illata fuskarki da yatsun hannayena". idan da ace ban san Akila ba, to tabbas zan rantse wannan ba ita bace, sai dai tambayar da tayi min ita ta wanzar da maɗakakin mamaki da al'ajabi a tare da ni.  "ina Akila?". tambayar da ta min kenan, kuma sai da na ƙara maimaitata a cikin raina kamin nace da ita, "rainin hankalin naki har ya kai nan?, ko a duniyar karuwancin na ki ma...". a wannan karan marin da ta sakar min maganata ce ta ɗauke gaba ɗaya, kuma zan iya rantsewa idan na buɗe bakina babu harshe balle haƙori. cikin tsananin ɓacin ran da zan iya rantsewa a duniyata ban taɓa ganin wani acikinsa ba ta fara ce min, "dan uwar da tai silar ubanki zuwa duniya, Akilan da kike kira da waɗannan kalaman rashin ɗa'ar taki ba ita ce ta haifeki ba, ni da kika ganni a gabanki ni ce uwarki da kika fito daga cikina, ni ubanki yaywa ciki ba Akila ba, ni Aaliya ni ce na haifeki. ita kawai sadaukarwa tayi, kuma akanta babu mahaluƙin da ba zan iya ɗaukan kowanne mummunan mataki akan aibantata ba, saboda haka ki iya bakinki kamin ki harzuƙa zuciyata. ina kallonki zuciyata ta bani ke ƴata ce, kuma sai kika zo da maganganun da suka tabbatar min da hakan". ta ƙara matsowa gabana ni kuma ina ja da baya, har ƙarshena ya kai jikin motarta, ina jin yanda zafin numfashinta ke sauka ajikina, gaba ɗaya nema takeyi ta juye min kamar zakanya, jikina kyarma kawai yake yi, ta miƙo hannu kamar wadda zan bawa wani abu, cikin wata razanniyar murya wadda ba irin ta mutane ba tace min,"ina Akila?, tsawon wannan shekarun ita na ke nema bake ba". shirun da nayi yasa ta bugan tsawan da yafi wancan, har ban san lokacin da na kai hannu ina neman ƙanƙameta ba,"ba za ki faɗa min ba sai na saka ƙafa na ɓalleki". ta faɗa tana zare min idanu. a tsorace nace da ita,"ai tana nigeria". kaman na fesa mata wuta haka ta shaƙo wuyana tana faɗin,"uban me ya rabaki da ita da har kika zo nan?". cikin saurin ba da amsa nace,"ai sai yanzu ta faɗa min asalina shi ne na gudo nan zan shiga yawon duniya". sai naga ta juya tana duban drivern da suke tare da shi tace,"ka kira Al-Hassan yay min buking tafiya nigeria yanzu ba tare da ɓata lokaci ba". sannan ta dawo kaina tace,"karki fasa shiga duniyar, idan kika fasa kuma ba ki haifu shegiya ba Maryam". ta ƙyasta yatsunta,"abu ɗaya da zan gargaɗeki idan bakinki ya kuma furta Akila sai na sa an datse harshenki, sunanta Ummi, sunanta Ummi ". a tsawace tai min maganar, tsawar da sai da tasa zuziyata ta harba, kuma babu shiri nabi bayanta muka shiga mota kamar yanda ta umarceni da idanuwanta. *Pls Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *34)* "Uwa da Uba su na da girma da daraja, Alƙur'ani ya fito fili ƙarara ya nuna mana mu kula da su. wajibi ne ƴaƴa su ɗauki nauyin yin magana ta mutuntawa da darajartawa ga iyayensu. Allah SWT yana cewa,"wala taƙul lahuma uffin". ana so ɗa ya zama me kyakykyawan saurare ga iyayensa. bima'ana idan su na magana kar ka katsesu ko da kuwa faɗa ne suke maka. ka zama me ladabi, haka kuma ya zamana kana tare da su ko da yaushe kar mutum yace zai guje su, haka zalika ka da kayi abin da za ka jawa iyayenka magana. Abu Darda yana cewa naji Manzon Allah yana cewa, "mahaifi shi ne ƙofa ta tsakiya cikin ƙofofin Aljannah,(uwa ko uba), wanda yake so ya shiga Aljannah, to ƙofar tsakiya wadda da ka shiga tsakiyar aljannah zata kai ka ba gefe ba to mahaifi shi ne wannan ƙofar, mahaifiya ita ce wannan ƙofar". saboda haka in har mutum yana so ya shiga aljannah to idan yaga dama ya kula da wannan ƙofar idan kuma yaga dama ya jefar da maƙullin wannan ruwansa ne. hakana kada ka sake ka taɓa yin magana me tsauri ga iyayenka, su iyaye kullum so ake ka zama kana saka su cikin farinciki. kuma wallahi duk lalacewar iyaye sunfi ƙarfin ai ramuwar gayya akansu, haka kuma ba'a yin jayayya da su. saboda haka ina me horanku akan saɓawa iyayenku ko kuma ɓata musu domin Allah na fushi da wanda iyayensa su kai fushi da shi". maganganun da ke yawo a cikin kaina kenan tun bayan shigowata cikin wannan motar, tunasarwar da Malamin makarantar allonmu yay mana kenan a ranar da Mahaifiyar wani yaro ta kawo ƙararsa makaranta. to amma ban san dalilin kutsowar wannan magana cikin kaina ba a halin yanzu, bayan an ɗauki tsawon shekaru da yinta. naja dogon numfashi sanyayyan ƙamshin da ya cika cikin motar yabi bayan iskar da na zuƙa. _"wallahi matsawar mutum yana so ya samu rahmar ubangiji, yaji daɗi duniya da lahira to yabi iyayensa, iyaye duk yanda suke iyayenka ne, balle Uwa da hadisi ya tabbatar da ma'aiki ya faɗeta sau uku"._ maganar Malamin ta ƙarshe ta kuma haskawa a cikin kaina, nayi saurin saka hannayena biyu na toshe kunnuwana, dan sam zuciyata na faɗa min kamar bata so wata nasiha makamanciyar wannan a halin yanzu, ko kaɗan bana so gwiwata ta raunana akan ƙudurinta na ɗaukan fansa akan Akila da Major, shi kansa tunanin rashin kyautuwar abin da nayi da wanda na ke shirin yi tun a sanbda na baro gida nayi watsi da shi, wataƙila zuwa san da na ɗauki fansa tukunna. saboda haka na san yanda nayi na ture hakan daga cikin kaina, sannan na dawo da ruɗani da na shiga a ɗazu, wannan Matar da ke zaune kusa dani, wannan matar da nasan Akila ce amma kuma tana ƙaryata hakan, _to dama ubangiji na halittar surar mutum a guda biyu ne?,_ tambayar da naiwa kaina kenan, kuma amsar da zuciyata ta bani ita ce a'a, babu ta yanda za'ai hakan ta kasance, ita ɗin ba kowa bace fa ce Kulun da kika sani, tana so tayi wasa da hankalinki ne. sai naji zuciyata ta matse, saboda tunawa da nayi da marukan da ta sharara min a ɗazu, to a bisa wanne dalili?, ita fa ta zalunce ni. ta ke na saki wata gajeriyar ƙwafa acikin raina, ƙwafa me tarin ma'anoni a wajena. zan gani idan da gasken najeriyar zamu je, zanga iya gudun ruwanta a wajen rainin hankalin da ta ke

Chapter 31 of 52