Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaron. kuma sai hoton lokacin da Maryam ke yiwa Arif wasa ta cikin vedio call ya haska masa a cikin kai, ya rumtse idonsa sosai yana mai jin wani abu na taso masa. "muje ayi wanka sai ai lunch ko?". yace da yaron yana shafa kwantacciyar sumar kansa, Arif ɗin ya ɗaga masa kai. "ehh Abbi ina jin yunwa dama". "baka ci abinci a school ba?". "ba zan iya ci ba idan babu kai". ya faɗa yana shagwaɓe fuska. nan Suhail ya juya zuwa bedroom ɗinsa yana cewa da Jawad. "Yaro kayi aure ka haifa kaima kaji irin abin da ake ji". Jawad ɗin na shafa wayarsa yace,"me ake ji dama?". "Jawad wani irin abu ne da ba zai fasaltu ba". murmushi Jawad yay sannan yace,"soon nima zanyi, Maryam na ke jira...ina so tayi hankali ne kamin nayi requesting ma ta abin da ke zuciyata". Suhail ya waigo ya dube shi da tambayar. "me kake nufi da tayi hankali?, kana nufin zaka ce Maryam bata haɗa hankalin da za ace wani ya mallaketa?". "no ba haka nake nufi ba, just i can't take her bulshit. you know well an raini yarinyar nan da shagwaɓa, kuma har yanzu ban manta da abin da ta min ba wancan ranar...". "ohh idan na fahimci inda zancenka ya dosa za ka aureta ne saboda kai ramuwar gayya". Jawad ya murmusa yana miƙewa. "ko kaɗan, kawai dai". "kawai dai me Jawad?". "Suhail you will not understand, so faɗa maka ma ba ya da amfani". "shikenan, amma ka sa ni, aurenka da ita sai dai idan babu numfashi ajikin Suhail tun da har na gane manufarka...ka gama tsara shirinka ni kuma na maka alƙawarin sai na lalata shi". Jawad ɗin ya motsa laɓɓansa yana wani killer smiling sannan ya fice bayan yace da Suhail ɗin,"na barka lafiya". *Qatar, cikin masarauta.* zaune take daga gefen wani ƙaton dutse da ke acikin ɓangaren masu yiwa gidan hidima, ta haɗa kai da gwiwa jikinta kuma sanye da uniform na bayin gidan, wannan uniform ɗinma aji aji ne kuma nata yana ajin ƙarshe na ƙasƙantattun bayin masarautar. gaba ɗayanta ta sauya tamkar ba ita ba, a halin da take ayanzu ita kaɗai tasan me ta ke ji, wannan wahalar ta kullum ta gaji da ita, gashi dai babu duka babu zagi amma bautar da take yi kaɗai yafi ace dukan nata ake kullum. tasa hannu ta goge guntuwar ƙwallar da ta cika idonta. bata taɓa tunanin ƙaddara zata wanzar da ita a cikin wannan yanayin ƙasƙancin da take ciki ba, domin bata lissafa hakan a cikin tsarinta ba ko kuma hasashen hakan, amma sai gashi tun da alƙalami ya riga ya bushe komai ya sauya mata, bata da ikon dawo da baya ta gyara lissafin tsarinta, balle labari yasha banba da wanda ake kai ayanzu. dama Larai ta faɗa mata, watarana zaren labarin shirinta zai sauya a yayinda akazo kan wata gaɓa da bata taɓa haskowa kanta ba, ashe kuwa hakan zata faru, za kuma ta kasance. wataƙila da ace tayi haƙuri ta barwa lokaci komai, da ta tsinci abin da sauyin mummunar ƙaddara zai kawo mata, wan nan lokacin na ganiyar da Malam da iyalansa suke kai ayanzu, kuma wataƙila inda tayi haƙurin ta tsinci ribar haƙurin, tun da Allah na tare da ita ba mantawa yay da ita ba, haihuwar dai! wannan haihuwar tabbas da tayi haƙurin taci gaba da adu'a wataran Allah zai bata in har tana da rabo, to yanzu gashi tayi biyu babu, ba wan ba ƙanen. lokaci guda wani abu yay tsalle ya harba allon ƙirjinta, ta sa ni, ba zata taɓa dawwama a haka ba dole wataran zata fita, duk da bata hango hakan amma tasan rayuwa zata iya rubuta hakan. zuciyarta taji ta matse, tayi saurin matse idnuwanta gam zuciyarta na harbawa da wannan sunan, wannan mutumin, wannan bawan da tunaninsa ke hanata sakewa a kowanne bugawar sakan na agogo tun kamin zuwan wannan lokacin. Kabir! Kabiru dai ɗan mijinta, bata san taya ba, bata san ya akai ba, ita dai kawai ta tsinci kanta cikin matsanancin son yaron a duniyarta, wanda ta ke jin kishi da baƙin cikin duk wanda ya raɓe shi ko da kuwa ace ƴan'uwansa ne, ta kuma sha alwashin haramtawa duk wata ƴa mace shi da sunan mallaka. kuma ko ayanzu bata janye ƙudurinta ba, in har akwai boka, Malam da bori a duniya tabbas sai ta mallaki Kabir, sai dai in bata raye, ba'a cikin nan ba, ko inda yafi nan matsi ne sai ta samarwa kanta Kabir, wannan alƙawarinta ne. _"Mami kar ku kaita kotu, dan Allah ta zama ƙasƙantacciyar baiwar masarautarmu, zuwa cikar wasu wa'adin lokuta da na shirya ta dawo ƙarshin ikona, ta zama mai min bauta"._ maganar Maryam a waccan ranar, wan nan lokacin da ake ikirarin za'a yanke ma ta hukuncin zaman gida yari ɗaurin rai dalilin allurar gubar da tayiwa Gwaggo, furucin ya shiga tariya a cikin kanta, sautinsa a cikin kunnenta.  baƙin ciki da takaicin halin ko'in kula ɗin da Maryam ta nuna akanta ya doki ƙirjinta, ko babu komai, duk da cewar ta ƙaunace ta ne ba don Allah ba sai dan biyan buƙatar kanta, amma ya kamata ace ta tuna da kulawarta da hidimtawarta gareta. ruwan da aka watso ma ta a jiki yasata yin firgigit ta dawo duniyar zahiri. a tsawace shugabarsu ta shiga mata magana. "dilla Malama miƙe kije kici gaba da aikinki". ta faɗi hakan tana jin tamkar ta kai mata duka saboda tsananin haushinta. "Amarya kike ne kowa?, ke wacce iriyar shashar mata ce ne wai, kullum sai anzo ance miki yi kaza yi kaza, gaba ɗaya ƙwaƙwalwan kifi yafi naki jaa...to wuce ga Sadauki can na jiranki, za'a kai ki aikin nome gonaki". maganarta da ban tausayi tace,"dan Allah ayi min afuwa, bana jin daɗi, ina ta fama da zazzaɓi tun jiya kuma bansha magani ba". Matar ta banka mata harara da faɗin,"ko ba zazzaɓi ba, to faɗawa wani ba ni ba...mtswww, kar ki ɓatan lokaci". tayi gaba ta barta anan tsaye tana cije fuska saboda yanda dukkan gaɓɓan jikinta ke mata mugun ciwo. a harabar wajen gate ta tarar da sauran bayin da za'a tafi da su, ta tsaya daga gefe tana matsa kwankwasonta da ke mata ciwo matuƙa, idanuwanta na daɗa ƙarewa kyawu da girman masarautar, ƙwarai rayuwa test and trial ce, yanzu duk wanda zai kalli wanda ke cikin wannan masarautar zai ce ba shi da wata matsala da zata kai shi ga damuwa a rayuwarsa ba, daular da suke ciki tafi gaban ta haifar musu da rashin jin daɗi, to amma sai dai ba anan abin yake ba, sun ɗanɗani ɗaci da baƙin ciki, sun gogi wani tabo da ba zai taɓa goguwa a garesu ba, in dai har da rai da kuma lafiya a kowacce rana da bugawar agogo sai sun tuna wannan ƙaddarar, wannan jarabawar ta ubangiji, haihuwar ɗan gaba da fatiha a cikin zuri'arsu. ta karkata hankalinta ga motar sojojin da ke shigowa jiniya na tashi, fadawa da securities na kewaye motar har zuwa lokacin da ta sami waje ta faka, bata ɗauke kai a motar ba da mutanen ciki da take jiran fitowarsu, duk da tasan cewar ba zai wuce Major bane, don yawanci motarsa ce kaɗai ke shigowa jiniya ta karaɗe ko'ina. to amma duba da yanda mafi yawa dakarun gidan su kai kan motar zaka san akwai wani mai ƙafa na gidan a cikin motar. san da ta sosa kanta saboda ƙaiƙayi lokacin idonta ya sauka akan farar ƙafar da ke fitowa zuwa waje, take gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke kai zuwa gefe, dan Allah ya sa ni Aaliya na mata kwarjinin da numfashinta ke katsewa a duk san da ta ganta. ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana kallonta ta gefen ido lokacin da ta fito daga motar gaba ɗaya ita da ɗanta da kuma Major ɗin da taji jiya su Sakina na raɗe-raɗin cewar sati na gaba za'a ɗaura auren Aaliya da Major, ita kuma Akila zata auri wani ministan health da ke saudia. kallonsu ta ke cike da burgewa da sha'awa, da ace tayi haƙuri tabbas da yanzu da duniyar Maryam ta sauya dole ita ma tata ta sauya zuwa cikar burinta, inda ace ta bar wannan soyayyar da ta kewa Maryam a matsayin ta gaskiya babu sirkin yaudara da a farar fuskarta da aka santa da ita, saɓanin baƙinta. lokacin da Aaliyan tazo wucewa sai ta tsinci kanta da saurin zube gwiwoyinta a ƙasa ta shiga roƙon alfarma da magiya akan sassaucin irin wahaltuwar da ta keyi wajen bauta. Aaliya ta dubeta kaɗan tace,"bani da hurumi da matsalarki, ki nemi Maryam". daga hakan suka wuceta, Alhassan na jin tausayinta a ransa, domin a kallo ɗaya zaka ma ta ka gane tana garuwa. "hankalina yayi can gaba ɗaya, na kasa samun natsuwa...ban san me yasa Akila ta hanani zuwa ba". Aaliya ke maganar da Major Mukhtar fuskarta na nuni da tsananin damuwar da ta ke ciki akan lalurar ƴarta da aka sanar mata tun a daren jiya. cikin taushin muryar da ke kwantar da hankali Major ke lallashinta akan haƙuri da tafiyar da ta dage sai ta yi a yau zuwa nigeria. "kuma ki kwantar da hankali, kin ma fa ji muryar Daughter, kinga kuwa ai ta sami lafiya". tayi shiru for some seconds kamin ta ɗago raunannun ƙwayar idonta ta kalle shi tace,"but Major me ya kawo asthma a tare da Maryam?, bayan ni da kai babu wanda yake da wannan cutar". "your Excellency wata cutar ai ba gadonta akeyi ba, jarabawa ce kawai daga ubangiji". ta sauke numfashi da faɗin,"haka ne, Allah ya bata da sauƙi. amma Major ina so Maryam ta kasance a wurina sai dai ina jin nauyin Akila". yay murmushi kamin yace,"ita ma zata ji nauyinki ai, hakan zai sa ta bar mana ita mu tafi da ita gidanmu". Aaliya tasa hannu ta ɗan rufe fuskarta, yana murmushi ya sai ta camerar wayarsa ya ɗauketa saboda kyawun da tai masa a hakan. "idan an ɗaura aure, ko Alhassan ya zauna anan, ko kuma na kai shi wata ƙasar". tayi saurin ɗagowa tana dubansa da son jin dalilin hakan. ya kai ƙaramin kofin shayi bakinsa, bayan ya kurɓa yace,"saboda na lura idan yana tare damu ba zai barni na sake da ke yanda nake so ba...ki kalla a hakanma yanda yabi ya sawa dukkan wani motsi namu ido". siririyar dariya kawai tayi bata ce komai ba. "Almustapha zai wuce italy gobe ƙaro karatu". ya faɗa yana dubanta ta cikin reflection glass na cup ɗin. tana datsa nama da fork ɗin hannunta tace,"Imam fa?". ya murmusa leɓensa sannan yace,"burin Imam shi ne football, shi ma next tomorrow zai wuce england". ta ƙara tambayarsa,"ehen what about Ibrahim?". sai da ya ɗaga gira sama sannan yace,"kin manta yace ba zai baro saudia ba sai ya sauke alƙur'ani". ta tsayar da ƙwayar idonta cikin nasa da cewar,"zamu je can fa honeymoon, dan haka shi ma kamata yay ka tura shi da nisa...tun da na lura 1by1 so ake a nisantani da yarana". ta faɗa tana ɗan ɓata fuska kaɗan, yay dariyar da ta bayyanar da haƙoransa tare da kai hannu zai shafo fuskarta maganar Alhassan ta dakatar da shi. "Dad...". tsayuwarsa a gaban dining ɗin ta haɗe da dunƙulewar hannun Major yana cije leɓensa na ƙasa da kallon Aaliya ta ƙasan ido, a hankali ya furta."u see bah...ai dole ma na luluƙa wannan yaron da nisa". Alhassan yaja ɗaya daga cikin kujeran dining ɗin ya zauna, yana naɗe hannun jallabiyarsa yana faɗin,"be a little more patient...next week ne fa kawai". ya faɗa kamar ba da mahaifin nasa yake ba, yana mai janyo plate ɗin chicken burger gabansa. "kuma Mami shikenan haka ake fisabilillah, dan kin sami Dad sai kike mantawa da ni a duk time ɗin cin abincinki da kika san tare muke ci. duk da Dad ɗina ne but am little bit jealous". yay maganar yana kai fork bakinsa, ya kuma haɗe da ranƙwashin da Major ya bashi. Aaliya dai kallonsu kawai ta ke tana murmushi tattare da wani farin ciki a ƙasan ranta. *Nigeria, Bichi.* ƙafafunsa su ka hau kan step na ƙarshe na shiga cikin parlon, hannunsa ɗaya saƙale da waya ɗayan kuma na cikin aljihun rigarsa, yayinda pink lips ɗinsa na ƙasa ke cikin bakinsa yana tsotsa, yana mai sauraron maganar da ke fita ta cikin wayar. "Ummi da gaske na ke miki". ya faɗa muryasa ta fita da amon da ba zai bada tabbacin shaidar abin da ya faɗa ba. daga cikin wayar Akila tayi murmushi sannan tace,"naji, amma sai na gani daga ƙwayar idonka zan gasgata hakan Kabir...yanzu ya jikin nata?". ya ɗan rufe ido sannan yace,"nima ban sa ni ba, sai dai ki kira likitan nata ki tambaye shi". "wa ye likitan nata?". ta tambaya sautin murmushinta na fita. Kabir na ɓata fuska yace,"shi Ahmad ɗin mana". daga cikin jirgin da Akila ta ke tai dariya kaɗan kamin tace,"yaushe kuma Ahmad ya zama likita banda labari, naga ma karatunsa is not related to health ta ya za ai ya zama likita Kabir?". kamar me gunguni yace,"da a gabanki ya dinƙa rawar jikin checking ɗinta da zuba bayanan ciwon za ki kira shi da ƙwararran likita wanda ya amsa lambar yabo". bai bari ta kai ga wata maganar ba yace,"yau ɗin za ki dawo?". tace,"kamar na fasa dai, tunda nasan zaka bawa Maryam duk wata kulawa da ta dace". yay gajeran murmushin da shi ɗaya yasan ma'anarsa sannan yace,"Ummi ki dawo ki kula da ƴarki kawai, ni gobe ma zan bar ƙasar". murmushi Akila tayi sannan taci gaba da masa bayani akan maganar da suke yi wadda ta zama musababbin kiran nasa. yay shiru na kusan minti biyar kamin ya amsa da,"tom shikenan sai kin dawo ɗin...hope jakar tsarabata daban da ta kowa?". "kai ma ka sa ni ai Kabir". da haka suka yanke wayar. daga bayansa yaji Yagana na faɗin,"ai Zulai nafi ƙarfin awa biyar tsaye anan wurin tun kamin hudowar rana, ni da ƙofar wajena amma anyi bake-bake an hanani shiga, kinga fa yanda ya wani bubbuɗe hannu ya kankame ƙofar, ni dai Rakiya ina ganin ta kaina a gidan nan, wai sunan gidan ɗana. ko da yake dama duk abin da yake ba mallakin ubanka ba dole sai an nuna maka iko da shi, Allah dai ya jiƙan Babana Manniru, da yana raye duk wannan walaƙancin na jikoki ba zan fuskance shi ba". girgiza kan Kabir ya haɗe da murmushin Zulai wadda tace. "ai Yagana bai san da zuwanki ba ne, ba ki kalla waya yake ba". "a'a fa Zulai ko bai da ido ta ƙeya ai yaji ajikinsa ina bayansa...ki bar mutum ɗan walaƙanci kawai, kuma wallah da Kabiru ba haka yake ba, ko dan yay kuɗi ne Allah masani...bai san ni bana maula ba". sai tayima Zulai nuni da kayan hannunta,"kuma fa kinga tsabagen ƙaunarsa da nake wallah ɗakinsa naje na ɗebo kayansa zan bawa Nawwara ta goge masa...amma sam ba ya ganin kyautawar da nake masa, ke dai ai kin auna arziƙi da kika haifi ɗan ƙwarai kamar Amadu". Zulai ta sake girgiza kai tana riƙe dariyarta, kamar ba jiya ne ta gama cewa Amadu bai da kyan hali ba amma yanzu shi ta ke cewa ɗan ƙwarai. ta karbi kayan hannunta suka nufi entrance ɗin parlon. "Baba Kabiru zan wuce dan Allah". tayi maganar da muryar ban tausayi. Kabir yana murmushi yasa kai cikin parlon, sai dai abinda idanuwansa suka fara tozali da shi ne yasa shi yin reverse babƴ shiri, ganin Ahmad da yay yana feeding Maryam harda wani goge ma ta baki yanata abu sai kace matarsa, yana juyowar ne Yagana na sako kai tasa hannu ta tura shi ya koma ciki,"koma ai dama ina so nayi magana da kai...muje ka faɗa min wannan halin miskilanci daga ina ya samo asali, idan kuma a hatsarin ka samo shi muje asibiti yanzu a cire shi daga kanka dan ba zan ɗauka ba". ya cije fuska tare da dunƙule hannu kamar zai kai mata naushi, yanda ya fesar da huci daga bakinsa in da Yagana ta lura zata ce ko garwashi ne a bakin nasa, muryansa ya fito a ƙufule da faɗin,"ina da wurin zuwa ne fa Yagana". Yagana ta ɓata fuska tace,"Kabiru ka kalleni a matsayin Hajara ba Rakiya ba". maganar tata tasa ya koma ya zauna kan kujera ba tare da ya ko ƙara kallon dining area ɗin ba, don in ya kuma kai idonsa wurin yana jin zai iya yiwa Ahmad illa. daɗin da ya ji ma earpord ne a kunnesa duka biyu, duk da ba komai yake saurara ba amma hakan ya taimake shi, dan yana jin Ahmad na masa magana yay banza da shi tamkar bai ma san da shi a wajen ba. sai da Basma tazo ta zare masa tana ƴar dariya tace,"Yaya anata magana fa". yay kamar da gasken dama bai ji ba, yace. "ban jiki ba Basma". "ai ba ni ba, Ya Ahmad ne". "ohh". ya faɗa yana waigawa inda ta masa nuni da shi, ya ɗan saki fuskarsa kaɗan kafin yace,"kai dama kana nan kasa naketa zaryar nemanka". ya faɗa yana ƙoƙarin danne zafin da ke tasowa daga can ƙasan zuciyarsa. ________________________________ Ƴan team ɗin Kabir kuci gaba da cewa Ahmad me ƙaton kai ku ga yanda zamu kwashe da ku🤨, wani yace Kabir ɗin ya bar masa da za ku wani ishemu da Maryam ta Kabir ce, to ba za'a ba shi ba ɗin can yaje ya ƙarata da halinsa🙄🙄._ *Please Vote, Comment& Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *(42)* Ahmad na riƙe da hannun Maryam yana kallon Kabir yace,"mantawa da Yagana kayi ko shi yasa ka kasa nemana a ɓangarenta?". Kabir yace,"kar ta jika kaja min magana fa". Kabir ya faɗa yana shafa wayarsa, shi kuma Ahmad ya ɗan dara yace. "to ya akai?, ai na shiga wajenka baka nan time ɗin...nace kura tayi lafiya kenan". "ka bari kawai, exams enn ce tasa na wartsake ba shiri". bai san me yasa ba, amma a duk wani furuci na Ahmad wani haushinsa ne yake tsarga masa, abin da bai taɓa ji ba dangane da ɗan'uwansa, kai wani ma daban ba shi ba. ga shi yaƙi yardarwa kansa da hakan a matsayin kishi ne, gani yake tun da har yaywa kansa alƙawarin cire yarinyar daga ransa to babu wani abu da zai dame shi game da ita, zai ci gaba da kallonta ne matsayi ɗaya da su Adawiyya, kuma matar ƙanensa. "idan ka tafi motarka fa?". ba tare da Kabir ya dube shi ba yace,"kai zan barwa ai, kaga ka rage yawan huzzeling da ita". "amma kuma da ka barta ba'a kawo ba, sai ka dawo nan ɗin kawai". "idan baka manta wane ni ba, ba zaka mance da rashin sauya ra'ayina da na tsara ba tun farko". "to godiya na ke, Allah ya ƙara buɗi...kaga sai na ƙara tarin kuɗina yanda nima zan mallaki babbar kai irin taka". da kai kawai Kabir ya ba shi amsa, domin ya kai gejin da ba zai iya ƙara tanka masa ba. lokacin Ya Ahmad ya maido da hankalinsa kaina, kaina a sunkuye yake ina zane da yatsana guda ɗaya akan dining table. nayi tagumi da ɗayan hannuna, fuskata na haskawa da damuwar da ke ƙasan raina, ayau kaɗai wani mugun haushin Ya Kabir na ke ji, haushin da inda ace na kai matsayin da zan saka masa duka babu abin da zai hana ni. tun a daren jiya da na dawo hayyacina naga kowa akaina yana min sannu shi ban gansa ba, shikennan na fara jin haushinsa matuƙa, amma kuma a yau da na farka da sanyin safiya naji wai ya tafi kai Nawwara school sai haushinsa ya ninku a raina, wai mutumin da bai da cikakkiyar lafiyar ƙafa shi ne har da su driving, driving ɗinma ba nan kusa ba can da uban nisa. in ace Nawwara ɗiyar wani ƙusan ce sai na kira kulawar da naga yana ta rawar ƙafar bata a matsayin neman gindin zama, to ita ba kowan kowa bace, duk da na san shi ɗin me tausayi ne da son kyautatawa wanda ba shi da shi, ba a yanzu da yay kuɗi ba, tun lokacin ma da ba ya samu a ko da yaushe. ni ban damu da sannunsa ba, tun da ko yayi min ko bai ba zan warke abuna in sami lafiya, to amma na damu da janye min da yay, wannan kulawar tasa gare ni, wannan soyayyar da yake min, wannan fara'ar tasa akaina duk ya ɗauke min kai da su, tsakani da Allah sai da ya saba min da hakan kuma sannan zai janye min a lokacin da nake jin kamar nafi buƙatarsa fiye da lokacin baya. ta shiga ƙifta idanu kamar zata fashe da kuka, sanyin hannun Ya Ahmad da naji a saman goshina yasa na ɗago na dube shi da raunannun idanuna. "kin daina jin zafin ƙirjin?". nayi masa knodding kaina kawai ba tare da nayi magana ba. "to asha maganin?". na ɗaga masa kai still ina kallon ƙwayar idonsa da ke nuna tsantsar damuwa da ciwon nawa da kuma nuna kulawa. sai na kwaɓe fuska ina tura baki gaba na girgiza masa kai alaman bana so. murmushi yay cikin murya mai taushi yace,"kiyi haƙuri kisha magani kinji, kinga ba ki da lafiya, kuma rashin lafiyanki ba ya barin kowa ya sami natsuwar zuciya da ta ruhi...ko ba ki son hankalin Mami ya kwanta ne?". tambayar ƙarshe tasa na kaɗa masa alaman a'a, sai ya ɗora tafin hannunsa ƙasan haɓata da faɗin,"to kiyi haƙuri kisha kinji ƴar lelen Mami da Ummi". a karon farko tun tashina daga barci nayi murmushi, na ci gaba da kallon gefen fuskarsa da a yanzu ya karkata yanawa Basma magana. lallai sanadin cuta kana cin wani arziƙin, banda ciwon nan ya ɗaga hankalin kowa ina zan sami wannan tarairayar a wurin boss ɗin gidanmu, Ya Ahmad ɗin da ko kasha magani ko karbka sha ko a kwalar rigarsa, bana mantawa da idan naƙi shan magani bulala yake sawa ya zaule min jiki, shi yasa idan ina gardama kan magani da Gwaggo tace ku kira min Amadu babu shiri nake sha. kuma kawai sai naji wani abu mai sanyi ya tsarga ta jikina da ban san menene shi ba, naci gaba da kallon laɓɓansa dabke motsawa suvna magana da Basma, duk da cewan laɓɓansa ba su kai na Ya Kabir kyau da burgewa ba amma shivma kyan nasa nada iya gwargwadonsa, ko da yake kyan Innah yayi, Inna Zulai tana da kyau sosai kawai dai dan batayi kyan hali bane, dan yanzu kam Alhamdulillah Innah ta sauya hali ƙwarai dalilin isharar da ta gani, kuma ba komai ya firgitata ba irin yanda rayuwar Inna Amarya ta koma, haka zalika da yanda taga ubangiji ya maida ni, abunda ta faɗa da bakinta cewar bata taɓa zaton zan iya taka wani matsayi ba, asheɓma ni ɗin na wuce gaban tunanin kowa. "Ya Ahmad gashi". Basma tace da shi san da ta miƙo masa ledar magungunan da ya sa ta ɗauko a ɗaki. "bamu ruwa mara sanyi". yace da ita yana aje ledan ya fito da tarukan magungunan ciki har da inhaler, gabana ya faɗi, wato a rayuwa kowa da kalar jarabawarsa, kamar ni daga wannan sai wannan, wai yau ni ce da cutar asthma, cutar da ta ɗaure kaina da kowa nawa. ina ganin ya fara ɓallo tablet ɗin na miƙe tsaye zan bar wajen ya ɗago da kansa, idonsa akaina muryarsa na shaida izinin na koma na zauna. kamar nayi masa gardama saibna tuna a gaban wanda nake, da ƙyar da siɗin goshi nasha maganin, dan sai da ya cire tausayina, ya daina lallamina ya shiga zazzaga min wannan faɗan nasa da babu wanda ke ƙaunarsa. "kin san Allah kika dawo da maganin nan sai na ɗauke fuskarki da mari". na kalle shi da idanuna da suka cika da ruwan hawaye amma ba su zubo ba, naga da gasken yake maganarsa, na sauke hannuna daga toshe bakin da nayi, ta dole na

Chapter 40 of 52