Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su yake faɗawa Ummi cikin raunin zuciya. kuma a wannan lokacin da Ummi ke ban labarin mutumin da ban san da shi ba naji ina sonsa, har na iya ce mata tace da shi yazo ga Maryam tasa ce. sai dai a yanzu ko da shi ɗinne yazo bana jin idanuna zasu iya kallonsa ma ballanta har na miƙa masa zuciyata nace zan aure shi, naji ya so ni tsawon shekaru goma, kuma ya so ni tun ban zama mace ba, ya ƙaunace ni duk da ya san asalina, amma a wajena nafi ganin girman soyayyar da aka fara yi min ita cikin lokaci kaɗan, soyayyar da bata haura watanni biyar ba, soyayyar Ya Ahmad ta fiye min duk wata soyayya bayan ta iyayena. "Maryam abin da nake so kawai ki faɗa masu shi ne kin amince za ki aureni, ki bar batun kina sona ko ba kya sona ko taya za ki fara sona, zanji da wannan agaba, ni zan koyar da ke soyayyata idan mun kasance a inuwa ɗaya". maganar Ya Ahmad ɗin ta katse min duk wani tunani nawa, kuma maganar tasa da ta ƙara ɗauke komai da ke cikin kaina, wani dunƙulallan abu ya tokare min a ƙirji. _"Halacci! Halacci Maryam!"._ harafai biyun da suka dira a raina kenan, ban san taya akai ba sai kawai naji saukar hawaye a saman kumatuna, na sauke ganina akan tafin hannun Ya Ahmad da ke tallaɓe da haɓata, kafin naji laɓɓana sun furta,"Ya Ahmad na amince zan aureka". furucin da ya fito a hankali kuma suka shiga raɗau a kunnuwan kowa da ke wajen. sai kuma naji zuciyata ta matse, irin matsewar da ban taɓa ji ba, har ina jin kaman zata faso allon kirjina ne ta fito ta tarwatse a ƙasan gabana. babu zato naji Ya Ahmad ya ƙara janyoni jikinsa ya kwantar da kaina saman chest ɗinsa yana furta min kalman,"thank you". da alama ya manta da mutanen da ke wajen balle yaji kunyarsu, ko kuma yana ɗaya daga cikin mazan da basa shayin nuna soyayyarsu akan abin da suke so a gaban koma wane. a wannan lokacin idona na kan Ya Kabir ne da ke kan kujera kusa da Ummina, kansa yana kan wayarsa yana shafawa, farin hannunsa tar acikin hasken fitilun da suke gauraye a parlon, kallon zoben hannunsa nake da ƙyallin haskensa ke hasken ido a duk san da na kalla na yatsana da ya saka min tun kafin Mairo tasan wace ita. a wannan lokacin babu abin da nake so sama da Ya Ahmad ya sakeni na ƙarasa gaban Ya Kabir, na duƙa a gaban ƙafafunsa, na miƙa hannuna na riƙe nashi ko ya samu ya tsaya daga karkarwar da naga yana yi a yanzu, nasa ɗayan hannuna na ɗago da fuskarsa na ƙarewa wannan handsome face ɗin nasa kallo kamin nace da shi ya buɗe idanuwansa da suke a kulle ya faɗa min damuwar mece nake gani a saman fuskarsa da tayi yawa haka. idan da so samu ma na kwantar da kansa a ƙirjina na dinga shafa sumar kansa har zuwa san da zai sauke ajiyar zuciya ya buɗe laɓɓansa yace min Maryam komai ya gushe, babu damuwar, babu ɓacin ran, komai ya tafi, na daina fushi da ke, zan dawo asalin Ya Kabir ɗinki. ashe abin da ban sa ni ba shi ne, wannan kallon da nake masa har nake ayyana wasu abubuwa shi ne zan iya kira da kallo na ƙarshe, dan tun da Ummi tace,"Masha'Allah, Ahmad na baka auren Maryam". Baba kuma yace,"Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa". Yagana kuma tai guɗa, kunya kuma tasa Ya Ahmad ya sakeni. a wannan sandarewar da nayi ina kallon lokacin da Ya Kabir ya taso kaman a fusace, ya kuma zo ya wuceni kaman wucewar guguwa, na kuma ji san da zafin hucinsa ya sauka ajikina kaman garwashi, na kuma ga dawowarsa parlon bayan fitar da yay ta mintuna 2, ya miƙawa Ya Ahmad key ɗin dana ji ƙararsa ya dawo ya kuma wuceni a zafafe. daga wannan fitar, kuma wannan ranar ban ƙara ganinsa ba, har muka baro bichi muka koma abuja bayan bikinsu Mami, na taho makaranta, akasa ranar bikinmu naje ethiopia nayi kwanaki duk ban sashi a idona ba haka ma muryarsa. sai dai abin da har zuwa yanzu ban gane ba shi ne me na yiwa Ya Kabir a rayuwa?. da naga kamar banda damuwa da hakan kawai sai nayi wancakali da Ya Kabir daga duniyata, na ƙanƙamo ƙaninsa na riƙe, kuma zazzafar soyayyar da Ya Ahmad ke nuna min ta mantar da ni ma wani abu Ya Kabir da Rayuwarsa, alwashi ɗaya da na san na ɗaukarwa kaina shi ne, ko bayan aurena da ƙaninsa ba zai ga fuskata ba a matsayina na matar ɗan'uwasa, haka ma ba zai sami girmamawan nan ba ta sirikantaka balle ta ƙanwa...domin tuni na riga na gano musabbabin dalilinsa na fita a harkata, na tsanata da ya ɗorawa kansa, ai da hankalina, komai ya sauya ne tun daga ranar da ya san wace ni, ranar da kowa yasan sai da akayi zina aka samar da Maryam, illigitmecy shi ne dalilin tsanata da Kabir yay, kuma banga laifinsa ba dan irinmu abin a ƙyamata ne, sai dai abin da bai sa ni ba shi ne wannan shegiyar da yake ƙyamata a yanzu yana cin arziƙinta ne ta wani ɓangaren, don haka kaf duniyata Kabir na ɗaya daga cikin mutanen da bana ƙauna. bayanin da naji matar da ke cikin tv na kwararowa su suka yanke min tunanin da nake yi, na baro tunanin bichi da abin da ya faru a cikinta, na dawo qatar da kuma abin da ke wakana yanzu a cikinta, na tattara hankalina gaba ɗaya ina sauraron abin da balarabiyar matar ke cewa a tashar aljazeera cikin harshen larabci, kuma tun a kalamar Genotype ɗin da ta ambata allon ƙirjina ya girgiza sakamakon tunawa da saƙon Daddy. _"Dukkan ɗan Adam Allah Ya halicce shi ne tare da wasu ƙwayoyin halitta waɗanda su ke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake, ƴaƴa su na samunsu ne daga irin nau'in wanda iyaye suke da shi, idan iyayen suka zama da nau'i mai kyau, za su haifar da ƴaƴa lafiyayyu, idan aka samu akasi kuma za su haifi ƴaƴa masu rauni da matsalar Amosanin jini wadda ake cewa cutar sicler...Masana sun raba genotype zuwa kaso uku da suke cewa: homozygous dominant, homozygous recessive, da kuma hetrozygous. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, wanda daga gwajin ake samun Genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda 3 kamar haka,  AA, AS, SS...AA su ne masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa Carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukunsu ne SS masu ɗauke da amosanin jini wato Sicler saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura...Abu mai muhimmancin da ya kamata a lura kafin aure idan an duba genotype ɗin su ne kamar haka: Rukunin farko wato na mijin, Na biyun kuma na matar, sakamakon kuwa irin ƴaƴan da za'a samu su ne: (1). AA +AA = AA, AA, AA, AA, za'a samar da ƴaƴa masu cikakkiyar lafiya. (2). AA + AS = AA, AS, AA, AS, shi ma aure ne mai kyau kuma babu matsala a lafiyar ƴaƴan da za'a haifa amma bai kai na AA+AA ba. (3). AA + SS = AS, AS, AS, AS, shi ma wannan auren ana iya yinsa duk da akwai ƴar matsala kaɗan akan ƴaƴan da za'a haifa zasu zama AS ne duka ma'ana carriers. (4). AS + AS = AA, AS, AS, SS, akwai matsala domin za'a samu ɗa ko ƴa mai cutar sikila. (5). AS + SS = AS, SS, SS, SS, a wannan gaɓar akwai matsala sose domin kusan kaso 80 na ƴaƴa zasu zama masu cutar sicler ne. (6). SS + SS = SS, SS, SS, SS, inda matsala mai muni ta ke, domin dukkan ƴaƴan da iyayen sicler ne, zasu ƙare ne cikin tsanani da wahala na rashin lafiya...Idan aka lura da waɗannan matakan duka, ba shakka za'a kawo raguwa ko ƙarshen cutar amosanin jini wato sicler da ta ke galabaitar da waɗanda suke ɗauke da ita, kuma ta wannan hanyar kaɗai ake iya maganceta kamar yanda ta nan ta ke samuwa.  Allah ƙara mana lafiya ya kuma bawa marasa lafiyanmu lafiya"._ gama bayanin matar yay daidai da shigowar kira cikin wayata, nayi saurin ɗauka hannuna na rawa bisa rashin sanin dalilin hakan ganin cewar Bro Almustapha ke kirana. na kara wayar a kunnena ina jin wani irin faɗuwar gaba matsananciya, na rumtse idanuwana na kasa yin sallamar da ta kamaceni nayi. "Littile". ban amsa kiran sunan nasa ba sai da na haɗiye wani abu ta maƙoshina da ya wuce da ƙyar sannan nace. "na'am Bross". "kina jina ba, ki buɗe wannan box ɗin da na baki ranar dana zo, akwai wani blue envelop da sunan asibitin da muka je da ke, ki ɓare shi ki duba min menene genotype ɗinki, gaba ɗaya na manta ban duba ba a ranar, kiyi da sauri". na miƙe ƙafafuna na rakani da ƙyar har zuwa bakin dressing mirrow, na tsuguna na buɗe drower na ɗauko box ɗin da ya bani ajiya ranar da zai wuce london, na buɗe kamar yanda yace na shiga karanto masa cewar, "Bross AA ne". sai yace da ni,"oak". kamin ya katse nayi saurin cewa da shi,"Bross ka tambayi Ya Ahmad nasa, ina kiran wayansa ban samu ba kuma Dad yace na kira shi nace yana jiran result ɗinsa". da alama daga inda yake lemu ya kurɓa kamin ya ban amsa da cewan,"no ai nasan ma yana wajena tun wancan ranar da Mami tace na amso". cike da fargaba nace,"Bross shi mene nasa?". nayi tambayar da rawar murya. "result ɗinku is the same, shi ma AA ne". kan na ƙara cewa wani abu ya katse kiran. katse kiran da ya sa na jefar da wayata na faɗa kan gado ina kanƙame pillow dan murna. zuciyata faɗa min take a yanzu ba wata fargaba, babu wani ƙalubale, babu wata damuwa, komai ya kau, aurenmu zai tabbata, Maryam da Ahmad za su tabbata ma'aurata, Maryam da Ahmad zasu kasance a matsayin abu guda, wannan tazarar da ke tsakaninmu zata haɗe a wani dare ta tabbatar damu matsayin mata da miji. *Vote,Comment and Share plss🙏.* [7/18, 09:32] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(45)* *Ethiopia.* *Addis Ababa Bole International Airport* *NOTHING GONNA CHANGE MY LOVE FOR YOU.* _"if i had to live my life without you near me the days would all be empty, the nights will seem so long with you i see forever, oh, so clearly. i might have been in love before but it never felt this strong, our dreams are young and we both know they will take us where we want to go, hold me now, touch me now, i don't want to live without you...nothing gonna change my love for you, you ought to know by now how much i love you..."._ Abdurrahim da ya shigo motan ya kai hannu yay reducing volume ɗin waƙar da ke tashi a cikin motar, Kabir da ke kwance ajikin kujerar motar ya buɗe idanuwansa da ke a lumshe ya saukesu akansa, kallon Abdurrahim ɗin yake da irin kallon dalilinsa na rage masa volume tun da ba shi yake jin waƙar ba, haka kuma motar ba tasa bace balle yay masa iko da abin da ke cikinta. Abdurrahim ya shafo sumar kansa tun da ga ƙasan ƙeyarsa zuwa sama sannan shi ma ya jinginar da kansa jikin kujerar motar, kafin kuma ya kai hannu ya kwantar da kujerar shi ma yana sauke ajiyar zuciya. "gashi, in the next 25mints jirgin zai tashi". ya faɗa yana miƙawa Kabir wata farar takarda. Kabir ɗin ya karɓa ya aje sannan muryarsa ta fito a hankali da cewan,"ka sami damar maida min da volume yanda yake ko kuwa?". idanuwan Abdurrahim na kulle yace da shi,"kana da damu Kabir, wai mene amfanin earpord ɗin da ke kunnenka?, ka maida waƙan kaji kayarka kai ɗaya mana tun da ta zame maka waƙi'a farilla. ni wannan waƙoƙin soyayyan ciwon kai suke samin kasan da hakan amma sai kayi ta shiga da hakkina, muji a gida muji a mota haba abin ai yay yawa. ni wannan Maryam ɗin ma ai jaraba ce agareka". Kabir ya gyaɗa kai sau biyu ba tare da ya ce masa komai ba, sannan ya ɗago daga kan kujerar gaba ɗaya ya kai hannu ya kashe waƙan duka, a zafefe yay kan Abdurrahim da cewa,"duk ranar da ka ƙara min zancen Maryam, duk ranar da ka ƙara alaƙantani da Maryam, duk ranar da ka ƙara haɗa special mood ɗin da nake ciki da Maryam, na rantse maka Abdurrhim sai na sassaɓa maka kamanni, sai na bar maka mummunan tabon da ba zaka iya shaida kanka ba...i told you, don't stop talking to me about someone's wife kaga yanda zan faffasa maka baki". a fusace yake maganar kamar zai kaiwa Abdurrahim ɗin duka, kuma shirunsa yay daidai da buɗe idon Abdurrahim ɗin ya kallesa sau ɗaya yana mai sauke guntuwar dariya a saman fuskarsa, kan yaja tsaki yace,"in ka fasa fasan baki Kabir". gaba ɗayansu kuma sai suka saki ƙwafa a tare, shiru ya gimla tsakaninsu na wasu ƴan daƙiƙu, sai sanyin acn da ke dukan jikinsu, kuma a wannan shirun na shuɗewar daƙiƙu biyu Kabir ya jera guntayen tsaki sunfi biyar, Abdurrahim da ya gaji ya ɗago a harzuƙe yana cewa,"dilla Malam ni ka isheni da wannan tsokin naka. ai bani na kar zomon ba dan haka sai ka bari idan ka hau jirgi ka ƙaraci yin abinka acan, amma ni ka dameni". sai kuma yaja gajeran tsaki yace,"you know i totally forgot". yay maganar yana mai zira hannunsa a aljihu ya zaro wayarsa. "what do you forget?". Kabir ya tambaye shi yana kallonsa a sa'ilin da ya buɗe baki da zummar sauke masa bala'in da ke cinsa. "I was at the reception Yagana called me, she wanted to speek to you. tana ta kiran naka wayan a kashe". "swithh off?" ya tambaya in surprise trying to pick up his phone from his pocket. "to ni dai haka tace min". Abdurrahim ɗin ya ce ya shiga whatsapp yana serching numbern Mu'azzam ya danna voice call daga nan ya miƙawa Kabir. wayan bai jima yana ƙara ba Mu'azzam ya ɗaga, daga can ɓangaren Mu'azzam ya gaida shi sannan Kabir yace ya miƙawa Yagana wayar idan yana gida. abin da ya ɗaga hankalin Kabir lokacin da Yagana ta karɓa kukan da ta fashe da shi, ƙirjinsa ya buga, fargaba kuma ta dirar masa. ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya kan yace da ita,"Yagana lafiya? me ya faru?". maimakon amsar da ya zata daga bakinta sai yaji ta kuma rushewa da wani kukan, dan haka yay saurin katse kiran ya ɗauko tasa wayar ya kira Ahmad hankalinsa a tashe. "Kana gida?". daga can ɓangaren Ahmad yace masa,"ehh ina gida amma ina shirin fita yanzu. i heard your voice full of anxiety, what happened?". Kabir yay ɗan jimm bai ce komai ba, dan ko a iyaka muryar Ahmad ɗin ya tabbata ba wata matsala bace a gidan, rigima ce ta Yagana kawai, and now he can undertand the reason for her crying. "Kabir kayi shiru, me ke faruwa dama?". tambayar Ahmad ta katse masa shirunsa, ya fitar da numfashi sannan yace da shi,"ba komai, ka kaiwa yagana wayar zanyi magana da ita. vedio call zan kira so on your data". Ahmad ɗin yace da shi "to" ba dan ya yarda da cewan ba komai ɗinsa ba, duba da yanayin yanda yake maganar very cool. A bedroom Ahmad ya tadda Yagana zaune a gefen gado ta duƙar da kai sai kuka ta ke yi, Inna Zulai da jikokinta sun zagayeta, da kuma ƴan'uwanta waɗanda suka fara zuwa biki tun a shekaranjiya da biki ya rage saura kwanaki huɗu. "mene ya faru?". ya tambaya yana ƙarasawa bakin gadon gefen da mahaifiyarsa ke tsaye. "uhmm wa ya san me aka ma ta, tun ɗazu dai ta ke kuka, kai tunda ta tashi ma zance maka. kuma anyi tambayar duniya taƙi cewa komai". ya daɗa maida dubansa ga Yagana yana cewa,"Hajiya Yaganata menene? ko dai ni ne ba ki son rabuwa da ni kawai na haƙura na tare acikin gidan?". sai yanzu taji maganarsa dan haka ta ɗago kai ta dube shi da cewar,"Yauwa ɗan aljannah zo zauna nan". ta faɗa tana masa nuni da kusa da ita. "kukan na menene? ko duk saboda zan miki kishiya ne?". sai kawai tayi murmushin da za'a iya kiransa da na dole kuma na yaƙe sannan tace,"yo ni meye ruwana da amaryarka, me zai ɗagan hankali akan wata kishiya bayan nasan naci gida na kuma gama siye zuciyar mai gida, mtswww ni Allah sauƙe nayi kishi da waccan abar". yay guntun murnushi shi ma yana cewa,"faɗi gaskiya dai". tace, "kaga bar batun wannan sillan karan amaryar taka, kira min Kabiru a wayanka, na kira shi da ta Mu'azzam yaja min tsaki ya kashe". tayi maganar with serious face. yana kunna data kuwa sai ga kiran Kabir ɗin, ya ɗaga miƙa ma ta, a kallo ɗaya da ta yiwa idanuwansa ta kuma rushewa da kuka tare da zabga salati kaman wadda aka yowa aiken mutuwa. Kabir ya matse idonsa yana cewa,"dan Allah dan Annabi ki bar ɗaga min hankali da wannan kukan naki". "to Allah ya jiƙan rai Ubana Manniru nayi shiru". ta faɗa tana sa gefen ɗankwali ta share hanci. ya so yin dariya amma kuma sai ya gimtse yana cewa,"kin san abin da hawayenki yake haifar min ai". tace,"ina kuwa zan sani Kabiru tun da na san ba ƙaunata kake yi ba, Kabiru idan so ka ke na mutu to ka aiko kawai a kashe ni ka huta da jin numfashina a duniyar nan, tun da ka tsaneni baka ƙaunata. wallah Kabiru a yau ko gobe ko jibi ko wani watan na mutu to kai ne ajalina, na faɗa maka wannan sabuwar halayyar taka ita zata zama ajalina saboda zuciyata ba zata ɗauketa ba, duba fa yanda idanuwanka su kayi loko, ga yanda ka rame, ka zuge ka zaftare kaman ragowar yaƙi". ganin yana motsa baki zai magana ta dakatar da shi da faɗin,"kaga kar ka jama min musiba riƙe salatinka da kake ƙoƙarin jaa tun da ni dai Rakiya ba annoba bace....wai Kabiru ko sai ansa dalma an zana sunanka a goshina sannan zaka tabbatar da cewar kafatanin jikokina kai nafi so, to ban ma sa ni ba ko sanin hakan yasa kake galabaitar da sauran numfashin da ya rage min, to matuƙar na mutu Ubanka Adamu ka yiwa ba wani ba". sai kuma tayi shiru taci gaba da kukan. ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace,"kiyi haƙuri Yagana". "yo haƙurinka ko cuta Kabiru, tsakani da Allah watanka nawa baka gidan nan? ka ɗauki ɗabi'ar banza ta miskilanci ka ɗorawa kanka kana neman katange kanka ga kowa, yanzu abin da ban gane maka ba nake so naji shi ne bikin ma ba zaka zo ba kenan? kuma sai yaushe zan kuma ganinka a zahirance ba'a wannan hoton gajimaran ba, dan na gaji da ganinka a wannan iskar nasaran, ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo naji ka a kusa dani na sami natsuwa da kwanciyar hankali". "Yagana yanzu haka ma fa tahowa zanyi me zai hana ni zuwa biki. kiyi haƙuri dan Allah nan da mintina kaɗan jirgin namu zai taso". kawai sai fuskarta ta washe da fara'a ta shiga saka masa albarka da masa adu'ar isowa lafiya, kamin nan suka yi sallama ta bawa Ahmad wayar tana juyawa ga Inna Zulai tace ma ta ai maza a daddafa duk abin da aka san Kabiru naso kamin ya dawo. "ka bawa Basma wayar please". abin da Kabir yace da shi kenan san da yake fitowa parlo. Ahmad ya kira Basma ya miƙa mata wayar da cewan idan ta gama ta kawo masa ɗaki. "Ya Kabir ina kwana". "lafiya lau Basma, ya kike ya shirin biki?". "mu na tayi Yaya, yaushe zaka dawo? ko ba zaka zo bikin ba?". "anjima zan sauka insha'Allahu". "tom Allah ya dawo da kai lafiya. Ya Kabir kar ka manta da kit ɗin makeup ɗina dana ce maka". "insha'Allahu Basma ba zan manta ba. ina Nawwara?". "tana kitchen tana aiki". sai kawai ya ɗan rumtse idonsa for a while kafin ya buɗe yace,"je ki kai mata wayar". tayi knooding masa kanta sannan ta nufi hanyar kitchen ɗin, ko da taje kitchen bata sameta ba dan haka ta nufa ɗakinta, zaune ta sameta kan carpet tana yanke farce, gashin kanta a barbaje wanda ta gama tsifarsa babu jimawa. Nawwara ta tsaya da yankan farcen tana kallonta har Basma ta ƙaraso ta miƙa ma ta wayar ta juya ba tare da tace ma ta komai ba, ita kuma ko da ta karɓi wayar sai ta ajiye a gefenta taci gaba da yankan farcen, har a sannan Kabir bai yi magana ba, kallonta kawai yake yana mai hango irin tarin gajiyar da ke tattare da ita. bayan ta gama yankan farcen ta ɗago hannu tana dubawa ta gefen idonta sai ta kalla kaman mutum, hakan yasa tayi saurin juyowa ta kai idonta kan wayar gaba ɗaya. sai tayi saurin waro idanuwa waje tana dubansa da mamaki, sannan tasa tafukan hannunta ta rufe bakinta tana faɗin,"kaii". tayi maganar a irin wadda ta gama cika da mamaki. "Ya Kabir ai ban shina ba wallah, bata faɗi mani kai ne a waya ba kawai bani tayi ta juya, ni kuma nayi zaton ajiya ta ban". bai magana ba sai ƙare mata kallo da yake for some seconds sannan yace,"me ya sami gefen bakinki?". ta kai yatsa tana taɓa wurin kafin tace,"huciyan zazzaɓi ce". "when kika yi ciwon?". "an kwana biyu". irin yanda yake mata maganar da kuma kallon da ya tsareta da shi duk sai ta ji ta kasa sakewa. ta miƙa hannu ta janyo ɗankwali zata rufe kanta taji yace,"kar ki saka". hakan yasa ta dakata tana mai ƙara saukar da kanta ƙasa cike da kunyarsa na yanayin da take na rashin ɗan kwali. "wanne magani kika sha?". "su na da yawa har da allurai ma. Yagana ce ta kai ni asibiti". tayi maganar still idonta na ƙasa tana wasa da yatsunta, sai taji yace,"ba da gashinki nake magana ba da kika wani hasko min shi gaba ɗaya, ki ɗago min fuskarki ki min magana ko na kashe wayata". bata san mene ba amma haka kawai sai taji wani abu ya harba ta zuciyarta, ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya ta ɗan dube shi sannan ta ɗauke idonta. "an gama alluran?". "ehh an gama". "magungunan fa?". "suma sun ƙare na gama sha". "amma me yasa ita huciyan zazzaɓin bai warke ba?". "ai zai warke gaba ɗaya sai a hankali". kaman a tsoroce take da shi a yanda ya lura, ya sauke numfashi da sake tambayarta,"tun yaushe kike aiki da kika tara gajiya haka?". sai tayi saurin ɗago manyan idonta tana dubansa da tsananin mamaki, ƙwarai da gaske ta gaji, gajiya ma iya gajiya amma taya akai yaga hakan shi?. ya katse tunaninta da faɗin,"why din't you go to school today?". taji me yace amma ba zata iya mayar masa a cikin harshen ba, dan kamar yanda ya faɗa mata ne in yay mata magana da hausa to da hausan zata mayar masa, hakana inda english ne ma. sai tayi shiru bata ce komai ba. "am asking you, you kept quite?". sai taji wucewar wani abu ta maƙoshinta kafin nan ta kalle shi da cewan,"aiki ne yay yawa a gidan shi yasa". "ke ɗaya kike aikin dama? ita iya ina ta ke? dan me aka ɗaukota? ba dan saboda ta karɓeki ba a time ɗin makarantarki. ko kuma dama can asarar kuɗina nake ba zuwa makarantar kike ba?, da kika san ba kya son makaranta why can't you tell me eyeee?". muryarsa a ɗage yake maganan kuma cikin faɗa, tuni idonta ya ciko da ruwan hawaye ta shiga girgiza masa kai, ta kuma kasa cewa da shi komai. yaci gaba da faɗan yana cewa,"kar ki sake wannan hawayen su zubo". ya ƙara faɗa very loadly, hakan yasa tayi saurin sa hannu ta maida hawayen. yace,"idan na dawo zan miki exams, idan kika kasa zan sami amsar tambayoyina

Chapter 43 of 52