Malam ya maida ita.
Yay ɗan jim yana daɗa nazari akan maganar da Zulai tazo masa da ita, kamin yay gyaran murya ya fara magana da dukansu.
"to ke Zulai a maganar da kika zo min da ita nayi duba wanda magana ce mai kyau, sai dai ina so ya ƙara bamu ɗan lokaci...sannan a yanda nafi so na kuma gama tsarina tuni, so nake na haɗa yaran nan duk su uku na miƙasu ɗakinsu a lokaci ɗaya, duk da nasan da cewar hakan hidima ce babba amma babu komai Allah zai yassare yanda za'ai".
Sai a yanzu ya ɗago kai ya dubi Gwaggo wadda ke fuskantarsa tana sauraronsa yace,"Suwaiba ita Mairo bata taɓa zuwa miki da zancen kowa bane? Ina so ne na haɗasu su duka ukun na sauke hakkin da ke kaina".
Gwaggo tace,"ni ban gama gane maganar su uku ba, Sadiya da Adawiyya da kuma wa?". "Mairo Mana".
Gwaggo ta gyara zama tace, "a'a dai Malam, Allah na tuba Mairo gaba ɗaya nawa ta-ke, bata ma yi girma da hankalin da za'ace za'a aurar da ita a yanzu ba ai...aiwa Yayyun nata dai ita ma idan lokacinta yayi sai a haɗata da sauran ƙannenta".
Zulai ta ce,"ke kuwa Suwaiba wanna girma kike so Mairo ta ƙarayi, idan kuma ba so kike tayi girman da zata taddomu ba. Ga sa'anninsu nan gaba ɗaya anata aurar da su, wasu ma harda ƴaƴansu".
"ke kika ga girman, ni dai banga girman da Ƴata ke da shi ba, shekara sha uku ne fa, shekarun da basu da maraba da shekara bakwai zuwa takwas". Malam ya murmusa fuska ya ce, "yanzu Suwaiba idan ba ƙin gaskiya ba har ace macen data shekara sha huɗj bata girma ba?". Ta karkata kai gefe tana tura baki gaba kamar ƙanƙanuwar yarinya,"ni ƴata ba tayi wannan shekarun ba, ni dana haifi abata nafi kowa riƙon shekarunta, dan Allah dan Annabi ma ni a daina sawa shekarunta ido".
Malam ya sauke numfashi kana yace,"to anji ƴarki bata yi wannan shekarun ba, amma dai kuma ai kin san ta isa aure ko?".
Gwaggo dai taɓe baki tayi bata ce ƙala ba, har sai da Malam ya kuma yin magana sannan tace, "ni fa Malam canji nake so a samu daga kan ƴata, ba aure nake so ayi mata ba, Karatun zamani nake so tayi me tsayi". Tunda Gwaggo ta faɗi haka bata kuma jiran cewar bakin kowa ba ta ɗaga labule ta fita, Malam ya bita da kallo cike da ɗumbin mamaki, ta sauya sosai fiye da tunani, duk ta yanda yaso yayi magana da ita saita tirje taƙi bashi dama, yanzu harma wani ƙin zama ta-ke yi tare da shi, idan shine kuma ya shiga ɗakinta zama na ƴan mintuna ne zasuyi ta tsiri bacci da bata shirya ba.
Zulai taci gaba da faɗin ita kuwa ba za'a sa ƴaƴanta su lalacewa ba, dan haka Malam ma ya bar tunanin haɗa auransu da Mairo, duk ranar da Mairo ta jawowa gidan magana uwarta zata gane ba gata tayi mata ba.
Ɓangaren Gwaggo kuwa tana fita su kai karo da Kabiru ya shigo, wanda dawowarsa daga aiki kenan, yay mata sannu da gida ta amsa masa, Ya tambayi jikin Mairo tace masa da sannu dan har ma tayi bacci tun ɗazu. "Allah ya sauƙe". Ya faɗi hakan tare da nufar ɗakin Gwaggon, a kusa da kanta ya ajiye mata robar ice cream ɗin da ya siyo mata, ya kuma ɗora ayaba da kankana akai.
Fitowarsa ya sami Gwaggo ta shimfiɗa tabarma ta zauna tana aikin zogale, yaja kujera ya zauna yana buɗe kwanon abinci, ita kuma ta fara magana kamar ba da shi ta-ke ba.
"Kabiru ka faɗawa Babanku muhimmacin karatun zamani, ka fahimtar da shi karatun zamani ko babu aiki anfi ƙarfin dai a cuci mutum balle a raina shi". "Gwaggo wani abu ya faru ne, ko yace yaran nan zasu tsaya da karatunsu ne?". "yana nufin haka mana, tunda yana kiran aurar da su zai yi, saboda Uwar masu gida tayi magana. To ni kuwa ba aure zan yiwa Mairo tah ba, karatu za tayi ta karanci aikin kotu". Ta faɗi hakan tana ci gaba da zagar zogale, Kabiru yay murmushi, maganar da zai yi ta katse sakamakon sallamar Amadu. Shi ma wuri ya nema ya zauna gefen Gwaggo akan tabarma, jikinsa da alamu na gajiya, Kabiru yace da shi,"wai dama ba kai na gani a masallaci ba". Amadu yace da shi,"ni ne mana, Mai gari ne wai yake neman matasan da suka yi karatun boko a wannan ƙauyen, shi ne na kai sunayenmu". Ya kalli Gwaggo yace,"Gwaggonmu ai mana adu'a Allah yasa a dace". Tace,"insha'Allahu ma za'a dace, ga dai Babanku nan ai yana nema ya yiwa karatun Mairo togaciya, yana ikirarin wai aure zai yi musu, saboda Uwani tayi magana".
Amadu ya miƙe daga kishingiɗen da yake,"aure kuma Gwaggo!"? Ya tambaya da mamaki. "uhmm". abunda ta iya cewa kenan. Ya shiga girgiza kai,"inaa dole ma Baba ya sauya tunani". Kabiru ma yace,"ai yama zama dole, ta ya su ɗin da aka samu suka fara katun kuma ace za'a dakatar dasu, karatun nan fa shi zai ji daɗinsa". Gwaggo ta kuma cewa, "ni dai na faɗa kuma zan ƙara faɗa ko za'a tsayarwa da kowa karatunsa banda Ƴata, dan insha'Allahu Mairo sai tayi karatun zamanin mai zurfi har ta zama lauya".
Amadu ya ce,"ah Gwaggo karatun likita dai ai mu shi ne burinmu akan Mairo, tunda tana da hazaƙa". Kabiru ya ɗora da faɗin, "kuma karatun likita ai yafi kowanne karatu muhimmanci da amfani a wajen Ƴa mace". Gwaggo ta taɓe baki, "in dai babu karatun banza ai babu laifi dan Mairo tayi karatun lauya, dan haka karku sa ma ta ƙahon zuƙa akan wani karatun likita, ku barta tayi karatun da zata shiga kotu ta gwabza da kowanne shege ta ƙwatowa Babanku gonakinsa". Kan su ƙara cewa wani abu Gwaggo ta miƙe ta nufa wurin ruwa dan wanke zogalen da Kabiru ya tayata zagewa.
Kulu dake zaune bakin ƙofar ɗakin Gwaggo ta faki idon kowa ta faɗa ɗakin, har yanzu Mairo bacci ta-ke bata tashi ba, ita haka kawai Allah ya haɗa jininta da yarinyar, tana sonta sosai wanda in da mahaifiyarta ta san irin son da ta-ke yi ma ta da ta mallaka ma ta ita.
ta ƙarasa bakin gadon cikin hanzari tai saurin ɗauke robar ice cream ɗin da Kabiru ya ajiye, dama a ɗazu tana kallon lokacin da ya ajiye kasancewar tana sallah, ta bar ma ta sauran ayaba da kankana, ice cream ɗin kuma ta zura shi ƙarƙashin sif ta yanda babu mai lura da shi.
*#Comment and Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*8)*
Wayewar safiyar alhamis ɗin yau, kowa na gidamu na tsakar gida an zauna ana karin kullo safen, tun daga yaran har manyan, haka ƙa'idar gidanmu take a duk sanda za aci abinci musamman karin kumallon safe to haɗuwa ake gaba ɗaya, yaranmu da iyayenmu mata, su manyanne ake kai musu na su ɗaki, sai Baba ma da yake yin nasa a ɗaki da shi da wadda girki ke hannunta.
Kowa abincinsa yake ci hankali kwance amma banda ni wadda natsuwa ta ƙarauce mata dalilin birkicewar tunani tun kwanaki biyu da suka wuce, abincin na gaba ina kallonsa amma hankalina gaba ɗaya ba ya kansa, tun ina jiyo sokiburutsun Adawiyya har na daina ji, na ma daina ganin komai da ke wakana a wajen, sai hoton Gwaggona da Kulu da ke haskawa cikin idona a wancan daren da kuma maganganunsu.
Tun bayan komawata ɗaki dana samu na miƙe da ƙyar na koma kan gado na kwanta gudun kar Gwaggo ta fahimci farkawata, sun ɗau tsawon lokaci kamin su dawo ɗakin hannun Gwaggo riƙe dana Kulu, Ina kallonsu ta ƙasan ido ba tare da saninsu ba, dan ko da acema sun kalle ni ba za su taɓa gane idona biyu ba, dan nima yanda suka iya takunsu haka na iya nawa takun. Ina kallon yanda Gwaggo ta kwantar da kan Kulu bisa kafaɗarta tana aikin lallashin kuka da take, wanda sautinsa ke fita a hankali, kai baka ce Gwaggona bace wadda ke nuna tsantsar kyara ga Kulu a fili, "ki bar kukan nan haka Kulu, Basma zata iyaji kuma ta farka, duk da yarinya ce ita amma sanin kanki ne tana da wayon da zata iya ɗago wani abu". Kulu ta ɗago a kafaɗarta tana goge hawayenta, Gwaggo ta saki hannunta tana takawa a hankali ta ƙaraso gado, ina jin duk yanda take komai a hankali gudun karna farka, daga can in da Kulu ke kwance ta jefawa Gwaggo tambayar da ta ɗaure min kai matuƙa nake kuma neman wanda zai warware min ita anan kusa, ban da naci na son in gano wani abu da babu yanda za'ai na gane maganar da Kulu tayi, hausa take yi amma fa hausar a harɗe take, hausar da kai kana ji kasan bakin aronta yayi. "Yaya shi rubutun dangana idan ansha ɗin yana aiki?". Tambayar da ta yiwa Gwaggo kenan, kuma kamar ba zata amsa mata ba sai can tace mata,"to Kulu ayar Allah abar wasa ce, sunayen ubangiji fa aka rubuta da niyyar neman waraka ga buƙatar da ake nema daga gare shi...kiyi bacci haka asubahi na ƙaratowa". Ta kuma cewa da Gwaggo,"ina tsoro kar a bata taƙi sha, kin san halinta ba komai ake bata tasha ba musamman tasan cewa magani ne". "zata sha insha'Allahu, nasan da wanda zan haɗata". Daga haka cikinsu babu wanda ya kuma cewa komai, sai ni da suka bari da nisan tunani acikin ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwata, dan ko maganar wanda za'a bawa rubutun da suke magana akai kasa fahimta nayi tsakanin ni da Basama wa za'a bawa, na san dai ni ce wadda ake baiwa abu na sha naƙi sha matsawar aka danganta shi da magani, sai dai duk yanda naso na fahimci waɗancan sauran Al'amura da suka faru na gagara, haka ma na gagara fassara kalmar *DANGANA* da Kulu ta faɗa, kuma a safiyar yau ɗin kaina sai ya kuma ɗaurewa, domin rubutun da Gwaggo ta ɗauko mu uku ta bawa, da ni da Basma da Adawiyya, saboda na fahimci wani abu har turjiyar ƙarɓa na sha nayi amma sai naga Gwaggo ta banzatar da ni ta nawa Basma faɗan in har bata sha ba zata haɗata da Sunusi, anan na tabbatar da rubutun dangana ba nawa bane nata ne, to amma me yasa aka bamu muka sha ni da Adawiyya?, kuma mece Danganar?.
Daga saman kaina na jiyo maganar Inna Zulai na cewa,"ita kuma waccan sillan karan meke damunta ta rafka tagumi kamar wata babbar macen da iyali suka tarar mata". Na buɗe Nauyayyun idanuna da ba su sami isashshen bacci ba daren jiya, na dubeta naga ta gwame baki ta dubi Inna Amarya tace,"waccan yarinyar dai ku dubata akwai abun da ke damunta". Inna Amarya da ke gyarawa Zubaida hijab tace, "ke kina gidan ma baki san bata da lafiya ba?". "to da ma abun da ya shafeku faɗa min kuke?, to Allah ya sauƙe". Tana faɗar hakan ta wuce ɗakinta, Inna Amarya ta rakata da faɗin,"kyaji da gulmarki".
Ni kuma Inna Amarya ta hauni da faɗan matuƙar ban daina wannan tagumin ba raina zai ɓaci, Adawiyya ma tace mata aiko abincinma banci ba, nan ta kuma hawarni da faɗa sosai har sai dana ci abincin ba dan ina so ba kuma ba dan yayi min ɗanɗano a baki ba, ina da saka abu a rai sosai ko ya yake.
Baba ya kira sunana yace na kira masa Ya Amadu ko Ya Kabiru, har na miƙe sai yace na koma na zauna ya manta ban da lafiya, Adawiyya ta tashi taje. Tare suka dawo da Ya Amadu wanda ke biye da ita a baya, ya tsuguna kusa da Baba, sannan Baba ya miƙa masa wasu takardu yana cewa,"duba nan kaga na menene, shaf ni na manta da su sai yanzu, jiya Liman ya aiko ban san na menene ba". Ya Amadu ya gyara zama da faɗin,"Allah yasa abun da na ke tsumayi ne". Ya faɗi hakan yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a. Ya zaro takardun ya dudduba sannan ya fara yiwa Baba bayani farinciki tattare da shi,"ai takardun scholership ne wato tallafin karatun makaranta amma wannan ba daga gwamnati bane na masarautar bichi ne". Baba yace,"ah to masha'Allahu, da sunaye ajiki ne?". Ya ba shi amsa da,"a'a babu sunaye, takardun dai mutum uku ake nema, kuma na yara ne da za su shiga jss1 to ss1 ba wai na ƴan jami'a ba". "to Amadu wacce makaranta ce?". "makarantar gwamnatin tarayya ce da ke Minjibir amma fa ta kwana ce". "makarantar kwana kuma?". "ehh Baba". Gwaggo da ke gefe tace,"kace adu'a tace ta amsu, ni dama ai na jima ina yiwa yaran nan kwaɗayin makarantar kwana". Baba ya dubeta yace,"kin san kuwa makarantar kwana? ke bakiji irin illolinta da ake faɗa ba". Gwaggo ta sake cewa,"babu wata illa acikinta in har zaka bi ɗanka da adu'a, kuma in har ka yarda da tarbiyar da ka bawa ɗanka". Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba na tsawon wasu daƙiƙu, kamin nan ya numfasa yace,"to ta maza ce ko mata, ko kuma a haɗe suke gaba ɗaya?". Ya Amadu yace,"ta Mata ce zallah, dan Allah Baba ka amince a miƙa yaran nan Mairo da Adawiyya da Habiba tun da kaga dukansu jss2 za su tafi". Baba yace da shi,"ni bance eh ba, ban kuma ce a'a ba, kawai dai ka aje takardun a wajenka zuwa lokacin da zan yanke shawara". Daga Habiba har Adawiyya da suke ta murna sai murnar ta koma ciki, ni kuwa da ma ina gefe ina fama da damuwar da na kimsawa raina akan baƙon lamarin da na fara cin karo da shi a jiya, nayi farinciki sosai dana ji batun ɗaukar nauyin karatu, ko babu komai an ragewa Baba nauyi, yanzu sai ya saka sauran yaran a makaranta, da ma bana jin daɗin rashin zuwan Basma makarantar boko, Ya Amadu da bai yanke tsammani da Baba zai barmu muje F.G.G.C Minjibir ba, har da tambayarmu ɗaya bayan ɗaya akan abun da muke so mu karanta, Adawiyya tace masa ita ma'aikaciyar lafiya ta ke so ta karanta, Habiba tace me tuƙin jirgin sama, babu wanda bai dara da maganarta ba a wurin, ni kuwa ko da ya tambayeni nace masa ina so na karanci aikin bincike, ta yanda zanke gano abu cikin sauƙi ba tare da ya caja min ƙwaƙwalwa ba, ya murmusa kan yace,"to gaba ɗayanku Allah ya bada sa'a".
Inna Amarya ce ta zaunar da ni tayi min bayanin jinin haila tas, tun daga lokacin zuwansa da lokacin da zai ɗauke, abun da zanyi da kuma wanda zan bari, da tarin tsoratarwa akan yanda zan kiyaye kaina.
Da yamma ina ɗakin Inna Amarya a kwance Saleh ya shigo yace naje inji Ya Amadu, na tashi kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na fita, a zaure mu kai karo da Mu'azzam yana shigowa, har yay gaba ya dawo baya yana kallona, yay ƴar ƙaramar dariya yace,"Mairo wai lafiya?". Nace da shi,"lafiya lau, me ka gani?". Sai da ya kuma sakin ƙaramar dariya kana ya ce,"gani nai kina tafiya kamar ba Mairon da na sani a baya ba me tafiyar baragada, kuma har na bangajeki ba ki halin tsiwar taki ba, ko dai baki da lafiya?". Ya ƙarashe tambayar yana ɗora hannunsa a saman goshina, baki kawai na ɗan turo gaba na harare shi na wuce na barsa a wajen. Jingine daga jikin bango zaune na tadda Ya Amadu, shi ma tun shigowata yake bina da kallo, da ga ɗan nesa da shi na tsuguna da cewar,"gani Yaya". sai da ya sauke numfashi kana yace,"zo nan". Na tashi na ƙarasa kusa da shi na zauna, ya kamo hannuna ya taɓa tafin hannuna da kuma goshina da wuyana. "me ke damunki?". Na girgiza masa kai alamar babu komai. "yaushe kika fara ƙarya?". Na ɗago ido na dube shi wanda shi ma ni ɗin yake kallo.
Ya kwantar da kaina bisa kafaɗarsa, "faɗa min wani abu akayi miki? Ina kallonki ɗazu ba ki ci komai ba, kuma daga jiya zuwa yau kin rame sai kace kuɗin guzuri, walwalarki tayi ƙasa gaba ɗaya, ko ciwon cikinne har yanzu?". Nanma banyi magana ba na kuma girgiza masa kai. Sai ya yunƙura ya gyara zamansa sosai, ya fuskantoni tare da tallaɓar haɓata, ya sa na buɗe idanuna na sakasu acikin nasa, yaywa idanuwana kallon tsanaki tare da duban nazari sannan yace,"ni Yayanki ne mai tsananin sonki da ƙaunarki, wanda kaf cikin ƙannena idan aka cire Habiba nafi sonki da kowa, ku biyun nan bana so naga kun yi kuka balle wata damuwa ta dameku, faɗa min menene damuwar?, a makaranta ne ko kuma acikin gidan nan?". Na girgiza masa kai da ƙarfi nace,"duka babu ko ɗaya, kawai ina jin jikina babu daɗi ne". Sai naga ya tamke fuska, ya muskuta ya gyara zaman tare da barin fuskantata, "tashi kije". Naji kamar nasa kuka, ni Mairon ya zan yi, ta ina zan fara faɗawa Ya Amadu abubuwan da naji na gani, a hankali na fara magana,"Ya Amadu wasu al'amura ne suka shige min duhu wanda na ke neman sani akansu". kamar suɓutar baki kuma nace,"Ya Amadu wacece Kulu a gidan nan?, kuma menene zina? Ya ya kuma zina take?, sannan menene Dangana?". Naga ya wani juyo akaikaice yana dubana, ku san tambayar tawa ta girgiza shi, irin mamakin da naga ya bayyana ƙarara a saman fuskarsa na gane ba tambayar da yay tsammaci ji daga gareni bane, daga yanda naga ya tsareni da ido yana karantar wani abu tare da yanayin da na nutse a ciki ya saka na ce masa,"Yaya ko akwai wata kalma ta rashin dacewa a tambayana?". yace,"Mairo aina kika ji kalmar zina?". Nayi shiru na rasa abun ce masa, abunda kawai na ɗauka daga yanayin yanda ya mayar min tambayar shi ne kalmar tana da girma da kuma tsauri, ya katse tunanina da faɗin,"ke yarinya ce Mairo, ina ga lokacin da za ki san ma'anar wannan kalmar bai yi ba tukunna, domin ta yiwa kanki girma, ki jira zuwa wani lokaci za'ayi maku bayani a islamiya". Na kaɗa masa kai kawai sannan nace, "to sauran tambayan fa?". Ya ɗanyi ajiyar zuciya kana yace, "Dangana kalma ce ƴar'uwar haƙuri, irin haƙurin da mutum zai jure zafi da raɗaɗi akan wani abu da ya sameshi na tsanani acikin rayuwarsa, kamar mutuwa ko kuma mummunar ƙaddara".
Na tsare shi da ido ina jiran sauran amsar, yay shiru kamar ba zai ce komai ba, cike da ƙosawa na kuma maimaita masa tambayar wace Kulu?.
"ban san wace Kulu ba, ban kuma san daga ina tazo ba...". Nai saurin tarar numfashinsa,"Ya Amadu ba zan taɓa yarda da wannan maganar taka ba". "to Mairo ai maganar na fara kika yi saurin tarar numfashina ba ki tsaya kinji ƙarshen zance ba...ban san wace Kulu ba, ban kuma san daga ina ta ke ba, abun da kawai na sani ranar da aka haifeki ranar Kulu tazo gidan nan, da yake Gwaggo a can birnin kano ta haihu da suka tashi dawowa sai muka ga sun dawo tare da ita, kuma ko da aka tambayi Baba wace ita yace mara lafiya ce sun tsinceta ne a hanya, suka ga ba za su iya tafiya su barta acikin halin neman agaji da take ciki ba, shi ne suka ɗaukota suka taho da ita za su riƙeta a wurinsu har zuwa ranar da Allah zai sa ƴan'uwanta su nemeta".
Nayi wani guntun murmushin jinjina ala'amarin Kulu, ban yi tantama ko ɗaya ba akan abun da ya faɗa ba dan nasan ba zai min ƙarya ba, tausayin Kulu kuma ya kamani matuƙa. "shikenan abun da kike son sani?". Na kaɗa masa kai,"a'a Ya Amadu, ina so na san sau nawa Kulu tayi magana tun zuwanta gidan nan?". "Kulu ai bata magana, yanda kika ganta haka take ba um ba umum...".
Shigowar Ya Kabiru ta katse maganar da zanyi, muka maida dubanmu kansa, ya zauna yana cire rigar jikinsa, cikin tattausan muryarsa yake faɗin,"Zina na ɗaya daga cikin manyan kaba'iran da Allah ba ya so, ma'anar zina a taƙaice jima'i tsakanin namiji da mace, ba komai ke haifar da zina ba fa ce sharrin shaiɗan, biyewa ruɗin zuciya tare da afkawa matsananciyar soyayyar ɗa namiji da mace zata iya sadaukar da komai nata akansa...ki gujeta, ki kuma kiyayeta, domin abar ƙyama ce, tana da daɗi sai dai daɗinta na lokaci ƙalilanne, baƙin cikinta kuma tabbatace ne har ƙarshen rayuwa, ubangiji kuma ya tanadi hukunci me tsananin gaske ga waɗanda suka aikatata". Yay shiru ya miƙe yay tattaki ya saƙale rigarsa jikin ƙusa, Idona bai gushe da kallonsa ba, ina me cike da mamakin yanda akai yaji zancen da muke, har san da ya dawo ya zauna bakin tulun littafan da ke cikin wata ƴar ƙaramar durowar ɗakinsu ban ɗauke idona akansa ba. Nace,"to Yaya Kabiru mene shi jima'in da ka faɗa?". Ya buɗe baki zai bani amsa Ya Amadu ya dakatar da shi, "haba Kabiru, ya za'ai ka dinga faɗa mata kalmomin da sun fi ƙarfin kanta ne". "ba su fi ƙarfin kanta ba, hasalima yana da kyau ta sansu tun yanzu". Ya Amadu ya dubeni tare da cewar, "tashi kije". Na miƙe sanyi ƙalau na fice daga ɗakin.
Ina shiga ɗaki kuma na tadda Kulu a bakin ƙofa tana gyara warwaron da ke tsintsiyar hannunta, na kalli warwaron sannan na kuma kallonta, na cuno baki gaba na miƙa mata hannu, "bani abuna". Ta dube ni sannan ta ciro ta bani, na wuceta na shiga ciki, ina ji ajikina da yanda ta ke bina da kallo, abun da ya bani mamaki shi ne warwaron dana ƙwace hannunta ba shi ne nawa ba, irinsu dai ɗaya, dan ina ɗaga ƙasan matashi naga nawa da na cire na ɓoye, kenan na hannunta na Gwaggo ne, na ɗago na dubeta har yanzu tana tsaye tana kallona, na murguɗa mata baki kaɗan sannan nace,"sai na faɗawa Gwaggo kina taɓa mata kaya".
*Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State.*
"Bullshit! taya za'ai Samuel ya ƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin da ya fara take umarnina?". Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin da ke zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin da ke kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar a cikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin da ke sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa.
"ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours". Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin hannunsa ya fita.
*2hours Pass.*
*Emzor Pharmaceutical Industries Limited.*
*#Comment & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*MissAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*9)*
*Parkview Estate, Ikoyi, Lagos State.*
"Bullshit! taya za'ai Yemi zaiƙi sanya hannu akan abunda na tura masa, yaushe ya kai matakin daya fara take umarnina?". Dr Emanuel kenan, ingarman zakin namijin dake zaune kan lumtsatstsun cushion ɗin dake kewaye a matsakaicin parlon ke wannan maganar acikin harshen turanci, muryarsa na fita cikin ƙaraji, ya zare farin glasses ɗin dake sanye a idonsa ya ɗago ya dubi wanda ke tsaye a gabansa.
"ina buƙatar ganin Samuel a office ɗina in the next 3hours". Yanzunma dai acikin harshen turanci yay maganar, Onoka ya rissinar da kai cike da girmamawa ogan nasa, sannan ya karɓi files ɗin da Dr Emanuel ya miƙo masa ya fita.
*2hours Pass.*
*Emzor Pharmaceutical Industries Limited.*
Emzor Kamfanin ne na ƙera magunguna wanda aka kafa tun a shekarar 1984 a ƙasar Najeriya.
Kamfanin da aka kafa da manufar yin samfurori masu inganci na magunguna.
Kamfanin yana daga cikin jerun mayan kamfanunuwa guda goma da suka shahara a nigeria. Tun bayan da Obafemi Afafa mamallakin kamfanin ya rasu, Babban ɗansa me suna Tosin Afafa yaci gadon kamfanin kasancewarsa ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifin nasa. To shi ma ayanzu ya maida Babban ɗansa me suna Dr Emanuel Tosin Afafa the CEO of the company, wanda ya kasance mai ƙwazo da himma wajen ganin kamfani na samun ci gaba ƙwarai da gaske. Duk da a baya bai taɓa zaton zai iya ɗaukar ragamar nauyin kamfanin ba, dan acewarsa ba ya jin zai iya ɗaukar all those responsibilites na shareholdings, business trip and rest, to amma da ya ke mahaifin nasa General Tosin tsayayye ne wanda ba ya magana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 52