Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zama marayun ƙarfi da yaji". yay nisa sannan yace,"ke me zai hana ki kirata ki faɗa ma ta". "Alhassan ni ban san me nayi ma ta ba, tun da ku ka koma bama wani long conversation da ita, kana kallo ma ai tun kamin ku tafi muka koma kamar wasu sirikai, duk yanda naso na keɓe da ita na mata magana bata bani dama". "kunfi kusa, ni da Ummina ido ne namu". ya faɗa, kuma kamin nace wani abu ya kuma cewa,"Ya sauƙin jikin Ya Kabir ɗin?". na sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan nace,"da sauƙi, kawai dai har yanzu ba ya taka ɗaya ƙafarsa...shi ma yace na fita a sabgarsa babu ruwana da lamarinsa, jiya ma saura kaɗan ya mareni shi yasa nace insha'Allahu in dai sunana Maryam tsakanina da shi ido". kuma da haka muka ɗauki hirar makarantar da Mami ke nema min addimission a can Qatar ɗin, sati biyu kenan da zana aprivate waec ɗin da ta biya min, tace wai nayi girma da yawa a secondry, kuma tun da ina da ƙoƙari sosai ƙwaƙwalwata naja to kawai da waec ɗin nafi dacewa...ni kam sam idan muna waya da ɗan'uwana kamar kar mu rabu na ke ji, shi yasa duk na ƙagu Ummi ta dawo daga tafiyar da tayi muma mu wuce Qatar ɗin, dan Allah ya sa ni ina kewan kasancewa kusa da Mamina sosai. *03:00am.* "Yaya dan Allah ki saya min wannan takalmin". Basma da ke shigowa cikin ɗakina da na ke kwance ta faɗa tun bata ƙaraso inda nake ba. na ɗago ido na dubeta ina kallon ikon Allah, ita dai kullum na siya ma ta na siya ma ta, ta maidani kamar wata asusun bankinta, ga shi ni kuma ina bala'in son ƙanwata tilo ɗayan da Gwaggona ta tafi ta bar min. a yanzuma da ta ke shigowan kamanninta suka riƙiɗe suka koma min na Gwaggona, ban san lokacin da idona ya cika da ruwan hawaye ba, da kanta da ta lura da hakan tasa hannu ta goge min. "Yaya za ki saya min ɗin?". ta ƙara tambaya tana marairaicewa, nayi ma ta shiru ina ci gaba da danna sabuwar wayar Mami da na karɓe ranar da za su tafi. wadda babu komai acikinta sai tarin hotunanta, kuma su suka zame min abin kallo a kowanne lokaci da nake tare da wayar, ko ma bana tare da ita hoton surar Mamina ba ya barin haskawa a idona. "shikenan tun da ba za ki saya min ba na fasa shiryaku ke da Ya Kabir". ta faɗa tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon ta fita, nayi saurin kamota ina cewa,"haba mana my little Sis, kin kalla na taɓa ƙin saya miki abu?, Allah kam zan saya maki yi haƙuri kinji". sai ta noƙe ta juya min kai da cewan,"ni dai na fasa shiryaku, takalmin ma na fasa bana so". sai kawai na marairaice ma ta ina cewa,"haba lil sis, Gwaggo fa tace mu zama masu kula da junanmu". sai tayi murmushi tana ce min,"to kije ki ba shi abincinsa, na kalla yana jin yunwa kuma ya kasa ɗaga hannun". maganarta tasa na zuro ƙafata ƙasa babu shiri nayi waje, ina fitowa parlo na tarar da Ya Amadu da Yagana sai abokansu da suka zo yiwa Ya Kabiru sannu, na tsuguna na gaishesu sannan nayi hanyar fita, na sauka daga kan steps ɗin entrance ɗin parlonmu kenan sai naji Ya Amadu ya kirani. ko da na juyo sai na kalla kaman idonsa ba'a kaina yake ba, kiranma kaman ba shi yay ba, kawai sai na tsaya ina kallonsa, ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa gefe tare da kasa tantance abin da yake kallo a wurin. bata san ta ƙasan ido yake kallonta ba, gaba ɗaya ya kasa tantancewa, bai sani ba kyau ta ƙarayi ko kuma akasin haka, idanuwansa na kalle masa ne kullum kamar ana sauya halittarta, abu guda ya sani shi ne kowanne lokaci tana canjawa, a kowanne sakan ya ɗora idonsa sai yaga ta sauya kamar wahainiya. a yau da tayi shigar english wears ɗin da ya taho ma ta da su daga lagos, tabbas idan a hanya ne ya ganta zata wuce ya wuce ne ba tare da ya shaidata ba, ya motsa leɓensa da murmushin da bata gane ba. "Ya Ahmad". na kira sunansa ba da irin wancan sunan ƙauyen da na saba kira ba, dan Ummi ta hanani, tace yanzu mu ƴan gayu ne, dan haka duka sunan ƴan gidan ya sauya a bakina daga yanda na ke faɗarsu ada. a tsakiyar fuskata ya sauke idonsa, yana ƙanƙance shi saboda hasken ranar da ke dallare masa ido. "Ya kamar naji kayi kirana". "ehh aiki zan sa ki ciki, kizo ki dafawa baƙin nan indomie, dukansu basa cin alala." "Ya Ahmad ai Nawwara(ƴar aikinmu) na ɗakinta, dan Allah ka kirata...ni zanje Ya Kabir na kirana ne". wucewar daƙiƙa kamin ya gyaɗa min kansa, sannan na wuce na tafi zuwa part ɗin Ya Kabir, ina shiga na tarar yana ƙoƙarin yanda zai yi ya ɗauko spoon cikin ƙarfin hali, dan haka na ƙarasa gare shi da sauri, ba tare da na bari ya bani dama ba na tsaida hannunsa, sannan na matso da plate ɗin abincin da Basma tace min ta zuba masa, na shiga ba shi abincin yana karɓa bisa dole, cikin ɓacin rai dan ga hakan nan ya haska a fuskarsa. abin da bata sa ni ba shi ne, Kabir ƙara maimitawa zuciyarsa yake yi cewar babu wani abu da zai so a rayuwarsa ya kasa sadaukarwa da ɗan'uwansa, ƙanensa Ahmad, ko menene shi, kuma duk girman abin nan, sai dai idan Ahmad ɗinne da bakinsa ya furta masa cewar ba ya so ɗin ya haƙura. *Plss Comment,Vote&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Shafin Sadaukarwa ne gareku FITATTU BIYAR FANS GRP, ina matuƙar jin daɗin yanda kuke bibiyar wannan labarin da yanda kuke ƙarfafa min gwiwa, I love you so much Allah ya faranta muku._ *(39)* idan har zai iya bada rabin jininsa ga Ahmad saboda kawai son da yakewa ɗan'uwansa, to ba ya ganin akwai wani abu da Ahmad zai biɗa a rayuwarsa yaƙi ba shi damar samu matsawar hanyar samar masa bata fi ƙarfinsa ba. hoton wani lokaci can baya ya shiga haska masa a cikin idonsa, lokacin da ya ke shekara 22 a duniya, Ahmad kuma na 21, wannan lokacin da su kai accident kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta, Ahmad ya sami rauni sose da har saida aka buƙaci jini, a wannan lokacin kuma Malam ba shi da kuɗin da za'a saya ledar jini har guda uku, aka kuma gwada duk wanda ya dace a gwada acikin siblings nasu amma babu jinin wanda yay daidai da na shi sai shi da Malam, shi kuma Malam a lokacin babu damar a ɗebi nasa kasancewar ba shi da cikakkiyar lafiya, dan haka ya zagaya ba tare da sanin kowa ba, ya fasa bankin ƙasarsa ya bada 20k sannan ya roƙi likita aka ɗebi nasa har leda biyu aka sakawa Ahmad, duk da cewar likita ya gargaɗe shi akan zai iya samun matsala idan aka ɗibi jininsa da yawa haka tun da shi ma jinin ba isarsa yay ba, yace ba shi da damuwa idan har ɗan'uwansa zai sami lafiya, shi zai iya sadaukar da rayuwarsa ma akan Ahmad. kuma tun da aka ɗebi jininsa ikon Allah ne kawai ya rayar da shi, amma yasha baƙar wuya, dan da taimakon Allah da taimakon Gwaggo da tai ta sayar da abubuwanta ana siya masa abincin da zai dinƙa ci na ƙarin jini, tukunna lafiya ta samu gare shi, kuma har yau, har kwanan gobe babu wanda ya san da cewar akwai jininsa a jikin Ahmad...to idan har zai ba shi jini a lokacin da shi ma ba isarsa yay ba, mene a rayuwarsa zai kasa sadaukar da shi gare shi? babu! babu shi ba'a halicce shi ba, ya sa ni babu wanda ya san da cewar Ahmad na son Maryam, kamar yanda ita ma Maryam ɗin bata san da hakan ba, haka kuma shi ma Ahmad ɗin bai san da cewar ya fahimci soyayyar Maryam a tare da shi ba, kamar yanda hakan ta kasance, kamar hakanne zaisa ya zame kansa daga zuciyarta da tasa, ba tare da ya bari kowa yasan dalilin hakan ba, ai dama shi bai taɓa furtawa kowa cewar yana sonta ba illa Akila balle har hakan ya zam masa wani babban ƙalubale, Allah ya sa ni yana sonta, amma akan ɗan'uwansa tabbas zai iya haƙuri ya zama me juriya akan rashinta, zai bar masa ita, wannan alƙawarinsa ne matuƙar yana nunfashi, sai dai idan shi Ahmad ɗinne yace ya fasa, zai ta ɓoyewa Ahmad wannan Son da bai san ya nayiwa Maryam ba kamar yanda shi ma ya ɓoye masa nasa sai shi ne ya fahimta. ɗigar ruwan hawayen da ya sauka bisa cinyarsa ne ya katse dogon tunaninsa, ya juyo da ƙwayar idonsa gareta yana mai kallon fuskarta da laɓɓanta da ke magana cikin muryar kuka, mai shaida wani rauni daga ƙasan zuciya. "Ya Kabir dan darajan Allah kai min afuwa akan laifin da na maka bisa kuskure, wallahi tallahi banyi da gangan ba, ko me nayi banyi da sanina ba, dan Allah kayi haƙuri na tuba ba zan ƙara ba, amma ka daina fushi da ni haka...Ya wallahi zuciyata har zafi ta ke min akan hakan, ka kalla fa yanda ta ke motsawa a irin kumburin da tayi." na ƙarasa maganar ina masa nuni da ƙirjina daidai saitin zuciyata, sai kawai ya tsurawa saitin zuciyar tawa ido, daga can ƙasan ƙwayar idonsa yana hango irin yanda zuciyarta ke harbawa da irin yanda salon tasa ke harbawa. ita ya kamata ta ba shi haƙuri ko shi ya kamata ya bata haƙuri?, shi da ya saba mata da sonsa, kulawarsa, damuwarsa tun bata san kanta ba, ƙwarai ya san zata shiga damuwa, damuwar da ko kaɗan ba ya jin daɗinta, yana ƙoƙarin danniya ne kawai da kauda kai gefe. "Ya Kabir dan Allah". na ƙara faɗa ina kama kunnuwana da karayar da kai gefe, gami da yin narai-narai da idanuwa ina ƙoƙarin fashewa da kuka. sai kawai ya rufe ido for a while kamin ya buɗe ya saukesu a saman fuskata da na kwaɓe baki irin na shagwaɓaɓɓu, wanda hakan ba ƙaramin burge shi yay ba, dan saura kaɗan ya saki murmushi amma sai ya danne hakan, ya sake kauda kai kamar bai ji me na ke cewa ba koma bai san da zuwana wurin ba. ganin ba shi da niyyar saurarena kawai sai na yunƙura zan miƙe cikin rashin ƙwarin jiki da jin daɗi, ga mamakina kamin na kai ga miƙewa sai naji ya riƙo hannuna, na waigo a hankali ina dubansa, still idonsa naga inda yake kallo, yatsunsa ne kawai acikin nawa yatsun, ban san ya akai ba, sai na tsinci wani guntun murmushi a gefen leɓena. ta yanda yake janyoni a hankali na fahimci me yake nufi, dan haka na koma na kuma duƙawa a gabansa, kaina a ƙasa nace,"Ya ka haƙura?". kai ya gyaɗa min alamar a'a. "Ya me yasa to?." nanma kafaɗarsa ya ɗaga ba tare da yay magana ba. sai kawai na tafi zuwa jikinsa na kwantar da kaina saman ƙirjinsa ina faɗin,"please Yayana, kai fa baka fushi, balle fushi da Maryam ɗinka...Yaya idan ma ba zaka min afuwa cikin ruwan sanyi ba to na yarda dan Allah ka hukunta ni ta wata hanyar amma bata wannan hanyar ba, fushi da ni! hakan na min ciwo a zuciya matuƙa." inda ace da dutse a kusa da ni zan iya cewa maganar da nayi da shi nake ba da Ya Kabir ba, dan duk sammakal, ni da za ace zai buɗe baki yace wani abu ko da da faɗa ne wallahi zanji daɗi fiye da wannan shirun da yake min. abinka da mai ruwan ido akan Ya Kabir ɗina, sai kawai naji wasu hawayen da ban san da su ba sun shiga sauka, maimakon na tashi saina ƙara lafar da kaina a ƙirjinsa, yayinda kunnuwana ke juyowa yanda heart ɗinsa ke beating very fast. duk da ba ganinsa nake ba, amma a yanda naji hannunsa me ɗan lafiyar ya ɗago zuwa bayana, na fahimci wannan kewayenin da ya saba zai yi, amma sai naji ya dakatar da hannunsa ga kaiwa hakan a san da Ya Ahmad ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. abu guda ɗaya kawai na sa ni a wannan sallamar tasa, shigowarsa ta haɗe ne a lokaci ɗaya da saukar ajiyar zuciyoyinmu, kuma yanda naji Ya Kabir ya doki ƙasan carpet ɗin a hankali nasan hannunsa a dunƙule yay hakan, tabbacin alamar ƙorafin rashin cimma abin da yaso yi. "No Sir, i don't think that is all planned." yay shiru na ƴan sakanni kamin ya ƙara cewa,"Yes Sir, actually abin da ya faru a lokacin na fita, so i don't know ko after fita ne Joshua ya duba su, saboda tun da nace musu kace they should bering refference before you sign on the pappers suka ce sun haƙura da contract ɗin". ya kuma yin shiru na tsawon daƙiƙa guda kan ya ƙara cewa,"oak Sir i will see on it by tomorrow insha'Allah". "thank you too Sir, bye". cewar Ahmad kenan yana kai ƙarshen wayar da ya shigo ɗakin yana yi, ya zura wayarsa a aljihu yana mai neman kujera ya zauna tare da cire hular da ke kansa ya ajiyeta a gefensa, sannan ya dubi Kabir da ke kallonsa tun bayan gama wayar tasa yace da shi,"Sannu, ya sauƙin jikin?". "da sauƙi, wannan hannunma naji ya daina tsamin kamar da". Kabir ɗin ya faɗa yana nuna masa hannunsa na dama da yatsunsa ke tsarƙe da na Maryam, wacce tun shigowar Ahmad yake cikiniyar ya zare yatsun amma taƙi bari. "Dr Yusuf ɗinma ya kirani yanzu ba jimawa, yace zuwa dare zai shigo wai ayyuka ne sun masa yawa a office ne yau amma kayi haƙuri." "babu komai tun da dai lafiya, ni dama har ga Allah na gaji da zuwansa...ba son allurar nan nake ba wallahi". fuskar Ahmad ta washe da gajeriyar dariya kamin yace,"kai dai ka shiga uku, wai dan Allah sai yaushe zaka daina tsoron allura ne, haba sai kace ba Gentle Man ba". "to ai ba'a bar so bace Malami balle kace min ragon namiji". "kaima gashi nan ka faɗa da kanka ai". Kabir ya ɗan harare shi da cewar. "wai meke faruwa a office ɗin naku?". "ka bari kawai, wani company ne yake neman yasha damu, su na so mu haɗa partnership da su sai MD yay bincike akansu aka gano cewar kuɗaɗen bogi suke turawa, to bamu san wa yay musu signing ajikin takardar ba kuma exactly irin na CEO fa nake faɗa maka, alhalin shi ba ma ya ƙasar". Kabir yace,"tsananta bincike za ku yi, munafikin na cikin staff en...yauwa next week zamu fara exams kuma kasan na faɗa maka". "ehh ban manta ba ai, jiya ma munyi chart da Abdurrahim ɗin, amma insha'Allahu ma kamin time ɗin hannun naka zai yi normal ka sami damar yi, Allah ma ya taimakeka online ce". shiru ya ratsa tsakaninsu, kuma a wannan shirunne Kabir ya lura da irin kallon da Ahmad ke bin Maryam da shi ta wutsiyar idonsa, Maryam ɗin da tayi bacci a yanda ta ke ajikinsa tun shigowar Ahmad, bai san wacce iriyar yarinya bace ita, son jikinta yay ma ta yawa sai kace mage, haka bacci sai dai in bata kishingiɗa a jikin mutum ba, tun da can ma haka suke da shi, da ta ɗan kwantar da kai a kafaɗarsa zata fara lumshe ido, kuma yana ganin hakan zai ce ta miƙe akan cinyarsa dan yasan ƙarshen zancen bacci ne, amma Gwaggo kam ɗaleta takeyi tace ita bata son wannan lalacin. "ita kuma wannan fa?". tambayar Ahmad ɗin ta shigo ta cikin shirun da ya ratsa ɗakin yana mai masa nuni da Maryam. "rigima mana". "me aka ma ta?". "shopping ta ke so akaisu ita da Basma, Yagana kuma tace a'a sai an kwan biyu saboda kashe kuɗinsu yay yawa, to kuma tazo nan tana ƙorafi nace taje ta sameka wai kaima haka zaka ce a'a, kuma kasan hali ai ba sai na ƙarasa maka ba". Ahmad ya sauke numfashi, bayan ya sosa gashin girarsa yace,"kai kake biye ma ta, ya kamata zuwa yanzu kasan yarinyar nan ta girma amma sai kai ta ƙara biye ma ta tana jin kanta kamar ƴar shekara 2 ko 3. kalla fa wata ƙatuwa da ita ajikinka wai sunan baccin kuka tayi, ba sai ka maketa ba ta shiga taitayinta". Kabir ya motsa leɓensa yace,"da kake magana cikin ɗaga murya wani ya hukuntata kaima ai ba iyawa za kai ba...yanzu dai kawai idan zaka fita ka fita da su, kasan dai daga ita har Basma ɗin ƴan auta ne ƴan alallaɓa, dan kowacce ita ɗaya ce a wurin Mamanta". Ahmad na ɗan ɓata fuska yace,"ni ba ruwana da wani ɗan Auta...fita dama zanyi in sun fito mu tafi tare, in sunyi delay kuma nayi tafiyata". ya faɗa yana miƙewa tsaye, ba dan yaso tashin ba, dan da niyyar ya huta ya shigo ɗakin Kabir ɗin, haka kuma ba dan ya shiryawa fitar ba, ba kuma dan yay niyyar kaisu shopping ɗin ba, sai dan wannan kwanciyar, kwanciyarta ajikin Kabir, kuma dama yana so ya faɗawa Kabir ɗin, yana so ya tuna masa cewar Maryam ba muharramarsa bace, ya kamata ya gyara kusancinsu. "na manta, ɗazu Yayan Inna yazo ya shigo dubaka kana bacci, yana maka sannu". Ya faɗi hakan kamin ya ƙarasa fita daga ɗakin, kuma ba tare da ya ji amsawar Kabir ba, sai dai a yanda ya fita ɗin fushi da ɓacin rai na haskawa a saman fuskarsa, wanda a ganin farko ga mai saurin fahimta zai gane cewar kishi ne tsagwaronsa ba komai ba, kuma Kabir da ya gane hakan sai ya murmusa kuncinsa kawai yana girgiza kai. Allah ya sa ni, tun a doguwar ajiyar zuciyar farko da ta sauke, da kuma numfashin da ta shiga saukewa daga baya, yaji ba zai iya tashinta daga baccin ba, dan daga yanda ta ke yinsa yasan baccin yay ma ta daɗi, kuma shi kansa ya sa ni, ba wani baccin daɗi ta ke ba within these days, dan waccan ranar yana jinta da Alhassan tana faɗa masa cewar ita nutsuwa a tare da mutum biyu ta ke, Maminta da Ya Kabir ɗinta, kuma a yanzu duk basa kusa da ita, saboda haka ne baccin bata yinsa a daɗin rai sai dai ɓarawo ya ɗauketa. sai ya lumshe ido ya jinginar da kansa ga pillow da akasa masa ta baya, kamin wucewar awa guda Maryam ɗin ta farka, farkawar tata kuma tazo daidai da shigowar Zulai ɗakin, inda ta nufi wajen da room heater ke ajiye ta kunna bayan ta ajiye flask ɗin abincin da ta shigo da shi. "Ba sai ka kira waya kace azo a kunna maka heater ɗin ba, ɗakin duk ya ɗau sanyi". "ai Inna sanyin ba ya wani ratsani ne shi yasa". "lallai lafiya ta isheka, to da Ahmad ya shigo yay maka gashin ko ya?". "a'a Innah". "to ka shirya dan lokacin yin gashin ma ya wuce". ta faɗa tana buɗe toilet ɗin ɗakin ta shiga. tana shigar na ɗago kaina daga kirjinsa na shiga magana a hankali ina cewa,"lokacin da Inna da Ƴaƴanta ke neman yafiyarmu akan laifukan da suka aikata mana wanda bamu sa ni ba, kai da kanka kace na yafe musu, rayuwar nan ba komai bace, ubangiji ma muna masa laifi yay mana afuwa, balle kuma a tsakaninmu ƴan Adam...to dan me ni ba zaka yafe min ba Yayana?". sai dai abin da ƙwayar idonsa ta nuna min a lokacin shi ne, na tashi na basa wuri. ina miƙewa Inna na fitowa daga toilet ɗin, ta ƙaraso da robar ruwan zafi a hannunta ta ajiye, sannan ta umarce ni da shiga toilet na ɗauko ma ta towel. bayan na kawo ne ta ke cewa dani,"ke ni ai na manta ma Yayanku Ahmad na kiranki". murya a ƙasa na amsa da cewan,"to Inna". sannan na juya na fita daga ɗakin, dama ko babu kiran Ya Ahmad ba zama zan ƙara yi ba bisa dalilai biyu, bana iya zama a san da ake masa gashin karayarsa, kuma ba zanci gaba da zama ba alhalin ya nuna bai son ganina, kuma ba zai ƙara ganina ba a part ɗinsa ba insha'Allahu. a compound na tarar da Ya Ahmad ya fito daga part ɗinsa, ya bini da wani mugun kallon da yasa nayi saurin ɗauke idona daga barin kallonsa. "saƙon da na aika miki ne bai isa gareki ba?, Maryam kin koyi wata rashin kunya ko, me kike nufi da hakan?". ya faɗa cikin muryar faɗa, ni dai baki kawai na tura gaba nayi part ɗinmu, ni faɗansa na ci min rai, ya fiya jarabar masifa, idan yana so ya daki mutum kawai sai ya takali laifi ya ɗora maka, shi yasa ranar nan da Jamila ta kai ƙararsa wurin Baba naji daɗi, ta ko'ina Ya Kabir ɗina yafi shi daɗin sha'ani, yanzun me na masa da har yake kiran na koyi rashin kunya. ina shiga parlo na gamu da sababin Yagana wadda ke tsaye bakin ƙofar ɗakina tana jiran dawowata, ta riƙe ƙugu sai karkaɗe karkaɗen ƙugu ta ke yi, tana jefa min harara tace, "yauwa Uwar masu Sharri barka da dawowa, dama dawowarki nake jira ai kowacce wacce...kamin na juye miki masifar tawa, ina da ina kika je kika yanka min mugun sharrinki me hawa kai, kamin gurin shi Uban nawa da kikai ƙarata wurinsa". da shirunta da dariyata suka haɗu a lokaci ɗaya, ban ankara ba ta ƙwala min ludayin hannun Nawwara da ta karɓa, na sa ki ƙara ina ja da baya ina sosa wurin. "ni dai Rakiya iyakar tsayin rayuwata ba'a taɓa min sharrin da ya kai naki ba, ban san haka kika girmama a wajen yiwa mutum sharri ba Maryam Guntsi, munafuka ai da kin faɗa min kina da wannan mugun halin da tuntuni na raba hanya da ke". ni dai dariyar ma da nake ta hanani jin ba'asin wannan bambamin da takeyi, da ta kai maƙura da dariyar tawa sai ta wawuri takalmin Basma tayo kaina da shi, ni kuwa na arta zan fice da gudu sai karaf mu kai karo da Ya Ahmad na ƙumu da ƙirjinsa. ta ke yaja wani dogon tsaki ya hauni da faɗan rashin nutsuwa, da kuma cewar na wuce na ɗakko mayafina ko yay tafiyarsa ya barni, na ɗago na kalle shi da son jin inda zamuje sai dai banzan kallon da ya wurga min yasa ni gimtse maganata nayi ɗakina. na bar Yagana da faɗin,"Allah yaji ya gani ba zan iya ba, ina dalili haka kawai ina zaman lafiya Yarinya zakije ki ƙunduma min sharrin wai na hanaki fita shufin, kai jama'a kuji wani mugun ƙulli...yanzu tsakani da Allah idan wannan maganar ta kai kunnan Uwarta ai sai tace min butulu, saboda naga ta gina mana ƙatoton gida shi ne zan azabtar ma ta da ƴa ta hanyar hanata shaƙatawa, to ai akwai Allah yana ji kuma yana gani, shi zai saka min...ke Basma tsakaninki da Allah yaushe waccan abar tazo tace min zaku je Shufin?, dan Allah ma yau ni na haɗu da ita ne banda ɗazu da zata fita, to amma kinji yarinya saboda baƙin sharri taje tacewa Kabiru wai na hana akaita shufin, kiji zancen nema min masifa a wajen Uwarta da bata barin ta kwana...to ba zan iya ba gaskiya, ni dai Amadu idan kun fita da ita ka kaita can gidan ƴan'uwansu suci gaba da riƙonta acan kamin ita Akilar ta dawo, ba zai yiwu ta jazamin bala'i ba da mugun sharrinta tasa a ɗaureni, dama yanda take da gata nan ta ko'ina wannan uban nata da ba fuskar imani gare shi ba, ba zai duba tsufana ba zai sa sojoji su ɗaureni, Mairo dai yanzu ta zama annoba kam dan tafi ƙarfina, gwara ki tafi na samu salama...kuma sharrin da kika min kije da halinki na rashin kyautawa ban yafe ba". *Please Comment, Share&Vote.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(40)* "ke kuma Yagana gaki da kambaba zance". tayi lakato tana duban Ahmad da yay zancen kamin tace. "dama tunda ba Zulai akaiwa sharrin ba ai ba zai dameka ba, ni kuwa da na ke abar banza da wofi a wurinka Amadu ina

Chapter 38 of 52