taɓa mata haka so a tsorace ta buɗe baki zata saka ihu yay saurin saka hannu ya rufe bakin.
haɓarsa akan wuyanta yace,"Beb its me". jin maganarsa yasa ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ta ɗauke hannunsa da ke kan cikinta, ta gyara ɗaurin towel ɗin da ya kunce yake neman faɗuwa, ta fuskanto shi tana kallonsa da shagwaɓewa tace,"ka bani tsoro". ya bawa kumatunta light kiss sannan yace,"am so sorry". ya faɗa ɗumin iskar bakinsa na sauka a saman breast ɗinta da suke a cike suka yo sama tsagar tsakiyar na neman burkita lissafinsa. hakan ya haddasa jin wata iriyar kasala ajikinta me tattare da wani irin yanayi, yanayin da ta saba jinsa a lokuta da dama, yanayin da tun bata gane masa ba har ta gane masa a matakin da ta ke kai a yanzu, na samun gogewar karatunsa daga wurin ƙawaye.
tun ɗaukewar last two period nata ta fara jin wanzuwar abun, taji tana so ta fitar da abun da ke ƙunshe a mararta, ta hanyar ɗanɗanar wannan daɗin da ta ji su Sarah su na faɗa. ta daki ƙafafu a ƙasa da sakin tsaki alamar ƙorafi, Emanuel ya ƙara matso da ita ya rungumeta a jikinsa tsam, gogayyar da aka samu tsakanin ƙirjinsa da albarkatun nata ƙirjin sai ya haddasa masa ɗarsuwar wani babbu abu, saboda haka ya lumshe ido a yayin da yake ɗora haɓarsa saman gashin kanta yana shafa gadon bayanta.
"menene ya taɓa min Beb?". ya faɗa sautin muryarsa na sauyawa. tana cikin matsala ne a yanzu amma shi ba zai gane ba, ba zai fahimci wannan ƙamshin turaren nasa yana jefata cikin wani yanayi na daban ba, Yayanta ne shi dan haka bai kamata take jin abun da take ji a game da shi ba, amma ta rasa me yasa? me yasa akansa ne shi ɗaya tal? wani ƙwayan mutum da addininsu ya haramta mu'amalar da take so ta kasance a tsakaninsu?.
hawaye kawai taji na sakko mata, domin ta samu sauƙin raɗaɗin abun da take ji ta kewaye shi ta matse tsam ajikinsa, ba shi kaɗai ba da mazantakarsa ta motsa ta miƙe ba, hatta ita sai da taji tsikarin abu ajikinta.
a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sake shi, amma har yanzu bata bar jin wannan baƙon yanayin ba da ke zuwar mata lokaci zuwa lokaci, yake kuma neman cakar da ita, ta janye daga jikinsa tana duban idanunsa da suka kafe breast ɗinta da kallo, kallon irin yanda ƙirjinta ke hurowa sama yana sauka, da ƙasƙantun idanunsa ya figo hannunta ta dawo gab da shi, ya sunkuyo da fuskarsa yana laluben laɓɓanta da yake matuƙar buƙatar tsotsa a yanzu.
hakan ba komai bane a wurinsu, dan haka tayi dariya tana buɗe bakinta kamar yanda taga ya buƙaci hakan, kissing nata yake passionatlly har sai da yaji ya gamsu da hakan tukunna ya ƙyaleta, su ka kalli juna su na sakin murmushi.
"zancewa Dad kana son mace a kusa da kai, ai dama Granny ta faɗa". ta faɗa da sigar zolaya. bai ce da ita komai ba ya juya ya fice a ɗakin, domin idan yaci gaba da tsayuwa tare da ita wannan sirrin zai iya fallasuwa, komai kuma ya iya faruwa, dan tabbas wanzuwar abin da zuciyarsa ke ƙissima masa sai ya faru.
Da yamma su na zaune dukansu anan main parlo suka ji maganar Mom akansu, babu zato ba tsammani dan babu wanda yasan da dawowarta, ba gaban Emanuel kaɗai ba, hatta Obi sai da gabansa ya faɗi, ya san Mom, ya san Mom sarai da abunda zata aikata, a yau wani ikon ubangiji ne kawai zai sa Mairo ta ƙara kwana a gidan.
ita kuwa shigowar tata ma sam bata lura da Mairo ba, tana ta amsa sannu da zuwa daga bakin ƴaƴanta da kuma sirikarta, da ƴar me aikin da ta zo karɓar jakar hannunta.
Mairo kam ko kallon inda take bata yi ba, balle dawowarta ta dameta, haushin Mom ɗin take ji tun a ranar da Granny ta shaida mata ba ita ta haifeta ba, ita Mom dinta ta rasu tun tana jaririya. ta rutsa Granny da tambayar ne san da ta kasa danne damuwar da ke ranta na nuna halin ko in kula da Mom ɗin keyi akanta kamar ba ƴarta ba, sai dai taga kowa na waya da Mom amma banda ita, kuma ko ta yo waya zata tambayi kowa banda ita, sannan ko da aka bata waya numbar Mom ɗin ta fara kira amma sai tace ma ta ai tayi ɓatan number, ita bata haifi wata ƴa mace ba balle ƴa me suna Gift.
wannan maganar yasa ta ɗorawa kanta ayar tambaya in har wannan alamun da suke bayyane da kuma furucin da Mom ɗin tayi mata to tabbas akwai wani ɓoyayyan abu, ta san dai Dad shi ne mahaifinta, to ita ina tata Uwar?. sakkowar da ta yi babu shiri daga sama kenan ta sami Granny da tambayar ina tata Mahaifiyar, Granny kanta tayi mamakin tambayar dan alokacin tsayawa tayi kawai tana bin ta da ido, kuma Mairon bata ba ta damar yi mata wata tambayar ba ta fashe mata da kuka akan ta sanar mata ina tata Mom ɗin, dan Mom ɗinsu Joseph ta shaida mata ba ita ce Mamanta ba, dalilin da ya sa Granny tayi mata ƙarya kenan da cewar Mamanta ta rasu lokacin haihuwarta, kuma Mom ɗinsu Joseph ita Ƴaƴanta kawai take so, kamar bata yarda da zancen Granny ɗin ba dan taga alamun rashin gaskiyar maganar ɓaro-ɓaro a tare da ita, to amma da Dad ya dawo ya tabbatar mata da hakan dole ta yarda, ranar kuwa tayi kuka kamar zata shiɗe, kuma da ta tambayi hoto sai suka bata hoton Cousin Sister ɗin Dad da Granny ta riƙeta ta mutu shekaru uku kenan.
sam batayi niyyar mata sannu da zuwa ba dan a ƙullace take da ita, to amma haɗa idon da suka yi da Emanuel yasa taci wata daraja ta ɗanta, sai ta ɗauke kai gefe tukunna tace,"welcome back Mom". a sannan ne Madam Gloria ta juyo a sukwane daga ɗaukar hanyar stairs da take ƙoƙarin yi, sabuwar murya ce taji, muryar da bata taɓa ji ba balle kuma zamanta a gidan, saboda haka ta shiga bin kan kujerar da kallo har ta sauke ganinta akan Mairo.
sai ta tsaya da bawa Buky jakarta tace,"what are my eyes seeing?, what is this thing?". ta faɗa tana nuna Mairon da hannu kamar wadda taga abin amai, kamin kowa yace mata wani abu ta ƙara da cewa,"heyy who are you?, me ya kawoki gidana?, zaman me kike min a parlo?". duk a cikin saurin murya ta jefa mata tambayoyin, kuma duk a lokaci ɗaya ta maida kallonta ga su Emanuel cikin shouting tace,"kuna ji ina tambaya kunyi shiru da bakinku anan kaman na kwaɗi".
Joseph yace da ita,"tafiyarki da kwana biyu tazo gidan nan". da ƙifƙiftawar idanu dan son ƙara tabbatarwa ganinta da kuma abun da ɗanta ke faɗa ta buɗi baki tace. "you mean all these while that am not around tana gidan nan?". "yes Mom".
"to me take yi?, ina da ƴan aiki wadatattu nasan bata da wani space da zata karɓa, so zaman me take yi?, ina tambayan ne ga dukanku kunyi shiru sai Joseph ke bani amsa". tayi maganar da dukansu a tsawace.
"wai sabuwar daughter ce a gidan nan". ya ƙara amsa mata. ita dai Granny tana jinta, tayi shiru ne kawai har ta gama kumfar bakin sannan ta faɗi abunda idan ta faɗe shi ya zauna.
amsar Joseph ɗin ce tasa ta jefar da jakarta saboda gigita, da sassarafa me kama da gudu ta ƙarasa gaban Mairo ta kamo hannunta ta miƙar tsaye, ta kai hannu idonta tana faɗin,"kin wane kafeni da wannan ƙwalaƙwalan idanunki za ki cinyeni, to kurwana yafi ƙarfinki...this house is for only me and my childrens, so kinga hanya bi ki koma inda kika fito". ta faɗa tana nuna mata ƙofa.
Mairo ta ƙwace hannunta, ita ma tana cije fuska tace,"ni da gidan ubana ace na fita, to babu inda zani...kawai saboda Mamana bata raye sai ace za'a tsangwameni, daɗin abin my Dad loves me, and he can do anything for me. so kibi a hankali, ke matarsa ce, ni kuma ƴarsa ce, akwai tazarar matsayi me nisa a tsakninmu. ke zai iya rabuwa da ke, ni kuma ƴarsa ce da ba zai taɓa rabuwa da ni akanki ba, saboda...". sauran maganarta ta katse san da taji saukar mari a fuskarta, Mom ɗin ce ta kifeta da shi, kamin ta ɗago gaba ɗaya Emanuel ya ƙara kwasheta da wani marin,"she is my Mom ki iya bakinki akanta, zan iya zuba miki ido akan komai amma banda ita...dama ko Mom bata tambaya ba nasaka araina cewar duk ranar da ta dawo za ki san matsayinki a gidan nan, uzuri ɗaya zan miki na rashin sanin komai amma da sai kin gane ba ki da wayo akan abin da kika aikata". ya faɗa yana huci akanta.
Mom ta kama hannunta tana janta, dai-dai lokacin da Dad ya sako kai parlourn. Sakin baki da hanci yayi yana kallon yanda Mom ke janta ita kuma tana turjewa.
"Gloria mene hakan?, wai ke me yasa sam ba ki san baƙo ba, ba kya kallo ita ɗin yarinya ce, kuma mara lafiya". ta dube shi tana yatsine fuska tace,"baƙuwa! yarinya! mara lafiya!...baƙuwar ce zata zauna a gidana a rufe min saboda munafurci?, ko kuma yarinya ce zata kalleni ta faɗa min cewar nan gidan ubanta ne sai dai ni na fita ba ita ba?, mara lafiyar ce ke tsaye da ƙafafunta haka har tana yunƙurin karawa da ni?...to what ever dai zamanta a gidan nan yau ya ƙare, in har kuma ba kana so na tabbatar da zarginka da zuciyata ta fara a yanzu ba". ta faɗa tana sake figo Mairo da ke ta son ƙwacewa amma ƙarfin ba ɗaya ba ne.
Dad ya dakatar da ita acikin tsawa, "wai ke wace iriyar macece mara tausayi, an faɗa miki bata da lafiya she miss her tought, idan kin kwantar da hankalinki tana zaune damu ne zuwa ranar da zata sami lafiya akaita wurin iyayenta, ki tsaya a fahimtar da ke abu amma kin tsaya kina hargagin banza". a fusace tace da shi,"wane irin alaƙa ne tsakaninka da ita da ka ɗora alhakin kulawa da lafiyarta akanka?...Major ka faɗa min gaskiya tun ban aika da ita lahira ba, aina ka samota da kake cewa da Yarana sister ɗinsu ce, ko hakan na nufin kaci amanata ne?". ƙarashen maganartata ya fito da sautin karaya da kuma tsantsar tashin hankali acikinsa gami da fargabar jin amsarsa, Dad cike da takaici yace da ita,"ke kin san ni ba irin wannan mazan bane, kin san da cewar ni me kare mutunci kaina ne...kuma har kullum ina faɗa miki ba sai kana da alaƙa da mutum kake taimaka masa ba, balle ɗa wanda yake na kowa, ke uwa ce kuma irin uwar da ke tsananin ƙaunar ƴaƴanta, ki kimanta aranki in ace ƴarki ce a irin situation ɗin da take ciki ya za kiji idan wani ya wulaƙantata?, to ni na ɗauketa matsayin ƴata tun a ranar da ta shigo rayuwarmu, saboda haka zata ci gaba da zama acikin gidan nan har zuwa ranar samun sauƙinta...gida nawa ne bana kowa ba, ni ke da ikonsa".
Gloria ta saki wani murmushi me ciwo,"kaga Major, just go streight to the point kace min kaci amanata ka munafurceni ka samar da wata ƴar a waje, ai dama you have said, kana haihuwa har yanzu dan haka zaka haifi ƴa mace ko min daren daɗewa". sai kuma ta ƙara fusata a cikin ƙarajin murya tace,"saboda naƙi baka haɗin kai shi ne ka fita waje kaje ka auri wata?". Dad ya tsinka mata mari rai a ɓace yace,"you know me well ni ba sakaran namiji bane da zan tsaya jin surutan banzanki akaina ba, ga ɗanki shi ne sanadin zuwanta gidan nan, sai ki tambaye shi a inda ya samota". Ya faɗa rai ɓace yana barin wajen bayan ya nanata,"Gift ba zata bar gidan nan a yanzu ba, saɓa maganata zai haifar da babbar matsala tsakaninmu da ke".
Madam Gloria ta juya to dubi Emanuel da ya sunne kai a ƙasa yana murza yatsu tace da shi,"dama nan police station ne?". yay saurin girgiza mata kai alamar a'a. tana ƙara matsowa kusa da shi ta kuma cewa,"nan gidan ophanage ne?". nan ma yace a'a. "So i din't get you well, mene alaƙanka da ita daka maida ita ƴar gidan nan?". "Mom bata da lafiya ne kuma ni ne silar ciwonta". "Ohh yaushe ka zama likita banda labari?, you are just telling me ka bigeta kuma kai ne sila, and so?, da ka bigeta shegiya ce ita da ta rasa iyayen da za su kula da lafiyarta?, shashasha kana 33years amma baka haɗa hankalinka ba, to mace shaiɗaniya ce, kana kallonta haka sai ta jefa ka a ruwan zafi ta wuce ta barka aciki, mumu kawai". ta ƙarasa zancen tana dungure masa kai, sannan ta juya ta koma kan Mairo, ɓacin rai fiye dana ɗazu tace,"yanzu tun da kin gane ba gidan ubanki bane sai ki fita, ki warke acan waje amma ba'a gidana ba...idan kuma kinƙi ji to tabbas zanyi reporting naki to police nace kin maƙalewa ɗana da mijina, su na san za suyi mana tsakani". bata jira wani Abu ba tasa duka hannu biyu ta watsa ta waje, ita kuwa ba komai ya haddasa suman tsayen da tayi ba sai furucin da ta ji anayi akan ita ba ƴar gidan bace.
masifar Madam Gloria da jarabarta ya hana kowa motsi, faɗa kuwa kamar zata zane Emanuel, Granny ɗinma bangajeta tayi ta wuce tana faɗin,"kowa ma munafiki ne a gidan nan, anci amanata kuma ba zan yafe ba...Joseph biyo ni ɗaki". sai kuma ta nuna Emanuel da Obi,"kar wanda ya kusantoni acikinku, tun da da ku zaa haɗa baki a cuce ni...har kun saka na fara tantamar anya ku jina ne?".
Mairo dai tunda aka wurgota waje ta zube a entrance na shiga parlon tana kuka, kukanta bana korar da akayi mata bane, kukan bala'in da take ciki a tata duniyar ne. idan har da gaske nan ba gidansu bane to ina ne nasu gidan?, kuma Dad ba mahaifinta bane?, Brother ba Yayanta bane?, Granny ba kakarta ba ce?, to su wane iyayenta?, and me ya sameta da har ta kasa tuna komai bacin rayuwar da tayi a lagos zuwa yanzu.
tarin tambayoyin da ke haskawa kenan acikin kanta, sai dai bata san ta ina zata samu amsarsu ba, saboda haka ta kuma cusa kai a tsakanin ƙafafunta ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya, tunda har Dad ya faɗi haka to tabbas hakanne dan haka dole ta bar kokoton alaƙarsu da ita.
Emanuel ya fito yazo gabanta ya tsuguna, ya dafata da faɗin,"Gift kiyi haƙuri duk ni naja miki". bata ɗago ba, domin ɗagowarta a halin yanzu zai iya janyowa tayi masa abun da zai haddasa tashin hankali fiye da wanda take ciki ayanzu, domin shi ne silar wanzuwar komai da ke faruwa a duniyarta.
wayarsa ce tayi ƙara, yasa hannu ya ɗaukota daga aljihu. "Hello Sectery ka ƙaraso ne?". daga can ɓangaren Amadu yace da shi,"eh na ƙaraso, ina bakin layin gidan". "oak ka tsaya ga Obi nan zuwa ku taho tare".
ko mintuna goma ba'a ɗiba ba sai ga Amadu da Obi sun shigo gidan, yazo ne a bisa wasu muhimman takardu da ake buƙatar Emanuel ya saka hannu akai, ba'a kawo takardun ba kuma sai a jiya bayan tahowarsa daga can, saboda haka ne kawai ya biya masa kuɗin jirgi yace ya kawo masa dan bai saka lissafin dawowarsa cikin wannan satin ba.
"me aka mata take kuka haka?". Amadu ya tambayi Obi san da suka ƙaraso wajen, Emanuel ya ɗago ya dube shi, kamar ba zasu ce da shi komai ba kowa yay masa shiru, to amma rashin samun mafitar da su ke nema dole yasa su sanar da shi ɗin, duk da yasan in ya sanar da Md zai sama masa mafita to amma kamin wannan sai ya gama dagula masa lissafi shi kuma bai shirya ɗaukan hakan ba.
saboda haka ya sauke numfashi yana duban Amadu, bai ɓoye masa komai ba ya sanar da shi duk abunda ya faru har zuwa halin da ake ciki yanzu.
"karka damu ranka ya daɗe, ko mai zai warware cikin sauƙi insha'Allahu, amma abun da baka so ɗin dole shi za'ai, hotonta zamu ɗora a media a shigar da cigiyar iyayenta ko kuma wanda ya santa".
Obi ya jijjiga kai tabbacin ya gamsu da shawararsa, Emanuel kuwa ido kawai ya zubawa Mairo da ke duƙe tana ruzgar kukan da har muryarta ta fara dashewa. Amadu ya duƙa a gabanta, da muryar nan tasa da ta ƙware a iya fitar da tausasan lafuza yace da ita, "ƙanwata ki daina kuka kinji, ki ɗago ni zan kai ki gidanku, nasan su waye mahaifanki...amma sai kin daina kuka fa tukunna". tana jin hakan ta ɗago da sauri tana goge hawaye, gefe na zuciyarta na ƙissima irin matakin da zata ɗauka kamin barinta cikin rayuwar mutanen gidan nan.
duk da canjawar da tayi hakan bai hana shi ganeta ba, bai san ya zai kwatanta yanda yaji ba san da idanuwansa suka yi tozali da ita, abu ɗaya kawai ya sani ya razana, razana kuma bata tsoro ba, irin razanar da ta haifar da ɗimbin tashin hankali acikin ƙwayar idonsa da zuciyarsa.
_Mairo! Mairo dai ƙanwarsu, yau ita ce tayi rayuwar watanni takwas a cikin ƙedarun arna, kuma ta rayu a tsawon watanni takwas ɗin bata ko kallon gabas?._, ya yasar da maɗaukakin al'ajabin da ke lulluɓe da shi yace,"Mairo ce!". ya faɗa da ƙarfin sauti, ya sauke nauyayyan numfashi ya miƙa hannu ya taɓota dan tabbatar da gezon da yake tunanin idanuwansa nayi. tabbas Mairo ce, Mairo ƙanwarsa, Maironsu da suka fitar da rai da sake ganinta, ashe tana raye kuma a kusa da su.
ya ɗaga hannu sama yay hamdala ga ubangiji, tare da ƙara matsowa kusa da ita zai kamo hannunta tai saurin ja da baya, idonsa na kawo ƙwallar tausayinta yace,"me yasa kika baro mu?, kin san tashin hankalin da kika saka mu aciki kuwa?, me yasa kika mana haka?, ko kin san tun ranar da kika barmu har zuwa wannan ranar Gwaggo bata ƙara takawa da ƙafafunta ba, watanni bakwai kenan tana zubar da hawayen rashinki, Mairo me yasa?, me yasa?". ya faɗa kamar zai yi kukan farin cikin ganin nata.
ita dai kallonsa kawai take, binsa take da ido ba dan ta gane shi ba, ko kuma wai ta san shi, mamakinta ɗaya ne da ya nuna yasanta ita kuma bata sansa ba, waye shi? daga ina yake? mece alaƙarsu da yake waɗan nan zantukan da suka saɓa masaniyarta?.
Obi da su ke tsaye mamaki ya cikasu yace da Amadu,"kana nufin ƙanwarka da ta ɓace ne kwanaki?". jijjiga masa kai yayi tabbacin haka, sannan ya umarci Mairo da ta tashi su tafi amma taƙi tace sam ita ba zata bishi ba, shi ma zaije ne ya biya buƙatarsa da ita ya tozartata.
da ya fusata dai ya kai hannu zai kai mata duka, ƙarar bindiga da suka jiyo daga cikin gida yasa duka suka zabura, banda Mairo da tai saurin saka hannu ta toshe kunnuwa tare da rumtse ido gam jikinta na kyarma, kuma acikin muryar kuka, muryar da ke naɗe da firgici da tashin hankali, muryar da babu ƙwarewar hausa acikinta ta fita da ƙarfi wajen furta,"Gwaggo". a lokaci ɗaya duhun da ke cikin ƙwayar idanunta ya hasko mata san da suke gudun fitowa daga cikin dajin nan dan su samu su tsira da ransu daga wurin kidnapers, har lokacin da fito bakin titi tana rangaji, daga nan kuma ba zata ƙara tuna komai da ya faru ba, abu ɗaya da zata tuna sun baro cikin dajin da mutane da yawa, kuma abu na ƙarshe da ta san kunnuwanta sunji shi ne harbin bindigar da ya dinga tashi kamin kuɓutarsu daga hannunsu.
*Qatar, A wannan ranar.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*27)*
"me muka zo yi anan?". Abdurrahim ya tambaya a san da ya waigo ba ya yana duban Kabir, yaji tambayar tasa amma sai dai bai amsa masa ba, dan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya zuwa ga fuskar masarautar da ke fuskantarsu, ba komai yake kallo ba illa hoton da ke ajikin ƙatuwar fastar da aka manna daga wajen ginin.
ya san akwai identical twins, amma shi tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin twins ɗin da su kai tsananin kama da juna ba irinsu, kai ko a labari ma bai taɓa ji ba, duk kamannin da suke da su dole akwai ta hanyar da ake gane su, amma su waɗannan kamanninsu ya zarce tunanin mutum ko hasashensa, idan har ba sa ni kayi ba to zaka rantse da Allah mutum ɗaya ne shege editing ya maida shi biyu.
gaba ɗaya ya rasa wacce a ciki zai nuna ya kirata da sunan Kulu, to ko dan ba'a kusa da hoton yake sosai bane yake ganin hakan?. ya ɗauke kallonsa daga barin kallon hoton fastar ya dawo da kallonsa ga hoton Kulu da ke cikin wayarsa, ya jijjiga kai yana mai ƙara jinjinawa sarautar ubangiji, a sannan kuma hoton Mairo ya haska a cikin idonsa, lallai ne maganar hausawa da suka ce sai kasa aka sannan kake ɗauka, in ba haka ba ai akwai tsananin kama a tsakanin Mairo da Kulu, ana sakata a tsakiyar hoton nan zasu tashi a sahun identical twins su koma identical triplet, banbancinta da su ɗan kaɗan ne fuskarta tafi tasu siranta sun kuma fita hasken fata, amma daga wannan ba zai iya kawo wani abu da zai ce ya banbanta kamanninsu ba.
kunna datar wayarsa yayi ya shiga goggle inda ya tafi kan map yana duban ta yanda zai tsarawa shiga gidan ba tare da tambaye tambaye ba har ya isa ga inda Kulu ke so ya isa, wato turakar mahaifiyarta. yana shafa wayar yana dariya ƙasa ƙasa saboda mitar da Abdurrahim keta zabgawa, shirun da yay masa kuma na ƙara hasala shi har da buɗe motar ma ya fice ya tsaya daga waje, Abdurrahim ɗin faɗi yake,"Kabir inda nasan da wannan walaƙancin naka wallahi da ban biyoka ba, kazo ka shanyamu a waje kamar waɗanda aka sassaƙa, ana tambayarka kuma ka share mutane saboda rashin mutunci". bakinsa kuma ya ɗauke da maganar lokacin da idanunsa suka kai masa kan fastar hoton kyawawan ƴan matan su biyu, kana ganinsu kaga larabawan asali, ga shigar da suka yi ta abaya ta ɗaukesu.
ya murza hannayensa yana me leƙo da kai ta glass yay knocking Kabir ya zuge,"Kabir kaga wasu zuƙa-zuƙan ƴan mata anan, la'ila ha'illallahu ka fito malami ka gani mu san yanda za ai". Kabir na jinsa yay masa banza bai tanka shi ba, shi kuma bai fasa surutan da yake ba, har tambayar me taxi ɗin da ya ɗaukosu yake wai ya bashi shawarar da zai shigar da kansa cikin masarautar ko kuma inda zai sami numbar ɗaya daga cikinsu, shi ma Babansa na da kuɗi dan haka Al'amarin aurensu ba zai yi wuya ba, Me taxi ɗin dai murmusawa kawai yay.
Kabir da ya jishi yay tsaki da cewar,"ashe dai bani kaɗai ne mahaukacin ba". "Malam ban sa da kai ba, kai sabgarka nayi tawa". Kabir ya ƙyalƙyale da dariyar da ta ƙular da shi ya ƙara hawa sama da mitarsa.
_"yallaɓai akwai tsaro sosai a wannan masarautar, in dai ba kana da alaƙa da ita ba to ƙofar wajen ma baka zuwa dan hakan zai iya jefa aka a haɗari...yanzu ma ko da munje daga tsallaken titi zamu tsaya saboda ba'a parking a wajejen"._
maganar mai taxi ɗin da ya ɗaukosu daga airpot ta haska masa acikin ka, ehh tabbas kamar yanda ya faɗa akwai tsaro me tsauri ma kuwa...ba ya jin akwai ta yanda zai yi ya sami shiga cikinta, saboda haka zai haƙura ne kawai ya koma, tunda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 52