kamar ta maida shi cikinta, sauyin weather yasa yayi wani looking fresh, shaddar da ke jikinsa kanta ba ƙarama bace ga wata makekiyar waya da yake riƙe da ita a hannu, cikar haibarsa ta ƙara fitowa, kana ganinsa kaga wanda kuɗi suka soma zaunar masa. ta kamo hannunsa ta zaunar da shi bakin gado tana yi masa sannu da zuwa, shi ma kuma anasa ɓangaren yana ta farin ciki da ganin mahaifiyarsa. ta ɗebo ruwan sanyi a randa ta kawo masa ya sha, suka zauna su na hira duk da cewar shi ɗin dai ƙarfin hali yake amma hankalinsa ba ya kwata-kwata. yana dubanta yace,"Inna ya na ganki ke kina cikin ɗaki ga jama'a kuma a waje". fuskarta na nuna damuwa tace,"to kasan halin Kakarka ai, naga tana neman ɓatan raine shi ne nayo ɗaka kamin zuciyoyinmu ni da ita su huce". ya miƙe tsaye yana faɗin,"Allah ya kyauta". sannan ya zaro dubu biyar ya bata, ya kuma shaida mata zai je kano asa cigiyar Mairo a radio, ta bishi da adu'a da fatan nasara. yana jin Yagana san da zai fita tana faɗin,"miskili kawai".
***
yau kwanan su Mairo biyar a hannun kidnappers, kullum kuma sau ɗaya ne ake kawo musu abinci shi ma biredi ne da zuma za su tsoma suci, daga nan sai washe gari su da ƙara ganin wani abincin, sai uban ruwa da ake ɗirka musu, bayin Allah duk har sun saba da hakan.
Mairo dai gaba ɗaya tafi kowa lalacewa saboda yanda taga anata ɗaɗewa ana barinta, wasu an biya kuɗin fansarsu wasu kuma an gaji da ajiye su ne sai a siyar, ko kuma dan rashin imani sai a kashe su.
Matar da ta saba da ita ƴan'uwanta sun zo sun fansheta, shi yasa bata jin daɗin wurin gaba ɗaya, ita yanzu jira take kawai su kasheta ta huta, domin ta jima da sallamewa da rayuwa tun a sanda taji adadin kuɗin da za a bayar kafin a bayar da ita, da ma ita tasan bata da me biyan wannan kuɗin, dan kaf danginsu babu me shi, yanzu tashin hankalin da aka sasu aciki ma sa iya cinye kuɗin a magani.
la'asar ɗin yau su na zaune aka banko ƙofar ɗakinsu, su ka zabura suka zubawa ƙofar ido, in da sabo yaci ace sun saba da su to amma sanin cewar basa shigowa su fita ba su kashe rai ba yasa basa samun nutsuwa da zuwansu, kuma yau dan mugunta ma ko abinci har yanzu ba'a basu ba.
su uku ne su ka shiga su na saita kan bindiga, a tsorace kowa ya dinga ja da baya musamman Mairo da ke daga bakin ƙofa. Ogansu ya nuna wani Dattijo ya manyanta sosai yace,"taso". sannan ya kalli Mairo yace,"ke kuma ki shirya". sannan su ka fice tare da wancan mutumin. manyan mutanen da duk suka san nufin maganarsa akan Mairo sai su ka fara hawaye. ta kalli wata sabuwar mata da aka kawo jiya da ta fara sabawa da ita tace,"Yaya ina za su kaini?". ta rungumeta tace,"nima ban sani ba". hankalinsu ya karkata kan wani mutum da ya kalli gabas ya ɗaga hannu yana adu'a, "ubangiji Allah ka dubi wannan yarinya ka ceceta daga hannun azzaluman nan, Allah kar ka basu ikon keta mata haddi". ya duƙar da kai tare da fashewa da kuka. kamin su ƙara motsi aka kuma banko ƙofa, wanda ya shigo ya kalli Mairo acikin kaushin murya yace,"taso muje". jikinta ya hau rawa saboda tsoro, ta ƙundundune jiki tana kuka tana ba shi haƙuri, uwar tsawar da ya sakar mata yasa ta gimtse baki, ya ƙaraso ciki ya figo hannunta su kai ƙofa, mutumin nan da ke ta bin Mairo da kallo yana jin inama ace yana da damar da zai ƙwaceta yace,"dan Allah ku tausaya mata yarinya ce ita...ku ƙara haƙuri iyayenta za su zo su fansheta amma karku lalata rayuwarta". wani mugun kallo ya juyo yaywa mutumin yana kai sigari bakinsa ya zuƙa, ya saki ƙwafa ya juya za su ƙarasa fita mutumin ya ƙara cewa,"Ƴata kiyi ta ambaton Allah cikin hukuncinsa da ikonsa za ki kuɓuta insha'Allah". yana rufe baki mutumin ya saita ƙirjinsa ya ba shi harbin bindiga take ya mutu, shi kuma yaja Mairo da ke turjewa ya fita.
cikin wata rumfa da suka kafa na leda ya nufa da ita, yana zuwa ya tankaɗata ciki tare da cewar,"Oga gata nan a huta lafiya". tsohon ya taso ya nufo gareta fuska babu annuri, yay tsaye kanta yace da ita,"tuɓe". ya faɗa murya a ɗage. take sabbin hawaye suka shiga kwaranyowa Mairo, tsoro ya ƙara ninkuwa a zuciyarta, tana girgoza masa kai tana faɗin,"a'a". yasa ƙafa ya take mata ƙafa cikin kakkausar murya ya kuma ce mata,"kamin naje na dawo ki tabbatar da kin tuɓe idan ba haka ba kuma zan kasheki". ta rumtse ido ta buɗe kafin ta sami ƙwarin giwar ce masa,"Ya Kabiruna ya faɗa min abun da kake neman yi ba shi da kyau cin zarafin ƴa mace ne ubangiji ya haramta...".bata ida zancen ba yasa bakin bindiga ya gwaɓe bakin nata nan take ya fashe. "wannan ɗan ƙaramin wa'azin naki babu amfanin da zai yi anan dan haka ki rufe min baki, kiyi abunda kawai nace".
"sai dai ka kasheni amma ba zanyi abunda kake so ba". ya jinjina kai sannan ya daki tsakiyar kanta da gindin bindigar, ta saki wata ƙara,"ba za ki gane abunda nake nufi ba saina dawo na sameki a yanda na barki". yace da ita tukunna ya miƙe yasa kai ya fita ya barta da ruzgar sabon kuka, tare da neman tallafin ubangiji.
_"bana tunanin akwai wani abun cutarwa da zai riskeki ki kasa guje masa saboda ke ɗin ƴar baiwa ce. ba wannan macijin da kika gani kaɗai ba, har mutum sai kin so zai ya cutar da ke, dan haka duk sanda wani abu mara kyau ya riskoki ki ambaci Allah sannan kuma kiyi kamar yanda na faɗa miki"._
wannan Kalaman na Kulu suka haska acikin kaina a wannan lokaci, dan haka ban tsaya wani aune-aune da tunani ba na dunƙule hannayena tare da rumtse ido tsam. tsohon ya dawo daga shi sai sauran gajeran wandon da ya rage masa yana ƙoƙarin cire shi. sa'annan na buɗe idanuna na watsa su cikin nasa, sauyin launin da ya gani a ƙwayar idon nawa yasa shi razana yaja da baya, sai kuma ya dake ya ƙara tamkewa yana dawowa zuwa ciki, a lokacin na buɗe tafin hannuna da ya jima a damƙe aikuwa nan take wani abun mamaki da alajabi ya bayyana wanda ni kaina sai da na tsorata. kunamu ne manya kamar su na fitowa ne daga cikin jikina, sai dai ba daga jikin nawa su ke fitowa ba, nan da nan kuma suka cika ɗakin kamar a rumbunsu, gaba ɗaya sai suka yi kan mutumin kamin ya farga daga guduwar da yake so yayi tuni sun haye masa jiki, ya fara ihu tare da kiran sunan ƴan'uwan nasa akan su zo su taimake shi, wanda ke gadinsa a baƙin ƙofa shi ɗaya ya iya jin ihunsa, dan haka ya shigo ciki a guje, sai dai abunda idonsa yay tozali da shi yasa ya dakata yana jefawa Ogan tambayar meke faruwa. cikin tsananin azabar da yake ciki yay masa nuni da Mairo wadda ke rakuɓe daga jikin bango tsoro duk ya gama cikata,"ku fita da ita ba mutum bace...wayyo Allah ku nemo maganin kunama karsu ƙarasa kasheni". Yaron yace,"to Oga". ya juya da sauri ya fice ya zagaya ta baya, ya zuge rigar rumfar ta ɗaya ɓarin ya janyo Mairo waje da lallaɓawa yana faɗin ta ɓace musu da gani, sannan ya zuge rigar rumfar duka wai ko da hasken rana zai sa Kunamun su koma inda suka fito ko kuma su mutu, amma ga mamakinsa sai ya ƙara ganin su na sake shigewa jikin mutumin shi kuma yana ihun harbin da suke masa. sauran abokan harƙallar suka yo kansa anata ƙoƙarin ganin an janye shi daga cikin kunamun amma babu hali, ni kuwa a wannan lokacin ba zan iya kwatanta tashin hankalin da nake a ciki ba, dudduba ko'ina nake a jikina, domin gani nake na zama matsafiya, na durƙushe na fasa gunjin kuka dan a ganina idan mutumin can ya mutu to alhakin kisansa na kaina, bayan kuma ni ban san ta ya akai kunamun ma suka fito ba, ni dai nayi abin da Kulu kawai tace mun.
ina duƙen ina faɗin Allah ka yafe min sai naji an janyo hannuna, mutanen da aka yi kidnapping ne duk suka sami daman fitowa saboda babu attention ɗin wani security akansu, hankulansu yayi kan Ogansu da ganin ta yanda za'ai su kuɓutar da shi daga kunamun da suka cika ɗakin.
"zo mu tsira da ranmu". Matar da ke riƙe da hannuna ta faɗa tana jana ni kuma ina turjewa, kai nake girgizawa ina faɗa mata,"Ki tsaya a cire masa wancan kunamar ni ban san ya akai tazo ba". Matar bata saurare ni ba ta ƙara figata ganin sauran mutanen na neman tsere mana. duk yanda naso na ƙwace kaina daga hannun matar amma na kasa, ƙarshema mutum biyu suka haɗar min suka jani ta ƙarfin bala'i. haka muka nausa jeji muna ta gudu, babu hanklin kowa da ya kawo kanmu sai daga baya ne muka fara harbin bindigu. mun yi nisa sosai muka ji wasu na bayanmu na faɗar an yi nasarar harbar ƴan can bayanmu. munyi gudun kusan awa sannan aka fara rarrabewa kowa na ta kansa. ni kaɗai na fito titi ina tangal tangal ina haki, idanuna ko gani basa yi bare na san inda nake jefa ƙafata. nayi nisan tafiya ina yiwa kaina jagora, ƙafafuna kuwa sai zubda jini suke saboda irin abubuwan da na taka kasancewar babu takalmi a ƙafata, ga raɗadin zafin da ƙafar keyi min, ga ban san a inda zan iya tsayawa ba bare na zauna na huta, haka dai na shiga lalube da hannu har na kai ga wata bishiya na taɓota, na sauke ajiyar zuciya nauyayya na jingina da jikin bishiyar sannan naja jiki na sulale na zauna ƙasa. babu abunda nake buƙata a wannan lokacin irin ruwa, maƙogarona ya bushe yawun bakina ya ƙafe. cikin azama na miƙe naci gaba da tafiya a wahalce dan ban manta da maganar mutanen da muka gudo tare ba su na jadadda min akan kar na tsaya ko hutawa sai na tabbatar da na kawo inda mutane su ke, ba su san da cewar ji kawai nake ba amma ganin Mairo ya ɗauke tuni, kuma ganin ana cikin nafsi-nafsi yasa ban faɗa musu a halin da nake ciki ba, illa godiya da nai musu na kamo hanya har Allah ya fito dani, ban san ko ina ne ba nan ɗin, sai dai na kanji kamar sautin gimlawar ɗai-ɗaikun motoci.
a san da naji na ɗora ƙafata bisa kwalta, daga gefe naji an hankaɗani nayi sama na faɗo ƙasa tim. cikin kwakwazo na tsala ƙara, Kafin na samu damar yin wani tunani akan abin da ya sameni ko neman taimako sai naji duk jikina yay collapse, idanuna sun rufe da kansu, sannu a hankali kuma na ɗauke wuta gaba ɗaya kamar zarar rai.
duk yanda mai motar ya kai maƙura wajen taka burkin motar tasa dan ganin ya kaucewa Mairo abun ya faskara. yasa duka hannu biyu ya doki stearing tare da kifa goshinsa akai. yay shiru kamar ba zai ɗago ba, can ya shiga ɗago da kansa a hankali yaja dogon numfashi ya furta,"help me Jesus". muryar tasa ta fita acikin wani irin amo, sannan ya ɗago ya dubi Mairo da ya buge sheme ƙasa jini na malala, da hanzari ya buɗe motar ya fita ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗago kanta, bakinsa motsi kawai yake amma ya kasa cewa komai sai bin jikinta yake da kallo da kuma jinin da ke zuba daga kanta. ya ruɗe, ya rikice, ya dabarbarce ya rasa abun da ya dace yayi, sai yaji kawai ruwan hawaye sun cika masa ido, ya janyota zuwa saman cinyarsa yana tattaɓa fuskarta, "Girl, Girl open your eyes". a sama-sama take jin maganarsa, sai dai sam bata fahimtar me yake cewa, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta zuba ƙwayar idonta akansa tamkar tana ganinsa, sai kuma ta mayar ta rufe, numfashinta na up and down, da murya can ƙasa tace,"ruwa". bai ji me tace ba dan haka ya kai kunnensa saitin bakinta yana cewa,"say it clearly i can't hear you well". ba dan taji me yace ba sai dai ta ƙara maimaitawa dan a yanzu babu abun da take buƙata sama da ruwan, Daga haka bata sake sanin komai ba jikinta ya saki gaba ɗaya. nan take Emanuel ya kuma ruɗewa, kun san inyamuri da tsoro, gani yake da ya miƙe da ita mutane zasu yi masa caa aka duk da hanyar ba hanya ce ta jamaa ba, babban tashin hankalinsa ma kar yarinyar ta mutu.
ya ɗaukota jini duk ya wanke mata fuska, ya buɗe bayan mota ya zirata aciki, hannunta ya faɗi akan ƙirjinsa ta damƙo sarƙar cross ɗin da ke wuyansa ta tsinko. ya dubi sarƙar ya dubi hannunta ya rumtse ido, da ma shi tun tasowarsa daga abuja yaji ajikinsa something bad will happen to him, daɗi da ƙarawa da yaga star ɗin jikin sarƙar tayi duhu.
wawiyar ajiyar zuciya sauke sannan ya buɗe hannunta zai cire sarƙar sai yaji ta riƙeta da kyau dan haka ya barta ya rufe murfin ya zaga ya shiga yaja motar with high speed, tuƙin yake amma hankalinsa gaba ɗaya na kanta, ya miƙa hannunsa ɗaya ta baya ya riƙo nata, yaci gaba da dariving da hannu ɗaya, fatansa karta mutu, ga shi there is no any hospital nearby bare ya miƙata, haka dai har ya shigo garin ikoyi.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*20)*
*Lagoon Hospital, 17B Bourdillon Rd, Ikoyi, Lagos.*
shigowarsa cikin hospital ɗin yana yin parking ko rufe motar bai tsaya yi ba ya ɗauketa ya nufi emangency da sauri, nurses ɗin da ke tsaye a emergency su na ganinsa suka turo gado su ka shiga special room da ita, Emanuel na tsaye a varander yana ta kaiwa da komowa hankali a hargitse, tsawon minti ashirin likita ya fito daga room ɗin sannan ya buƙaci nurse da ta ce Emanuel ya biyo shi office.
acan office Dr Simon ke yiwa Emanuel bayanin sai anyi mata surgery aciki saboda glass ɗin da ya caki cikinta ya shige sose, kuma rashin aikin zai iya haifar da matsala babba ga yarinyar at the end ma a rasata. Emanuel ya rumtse ido gam tare da dafe goshi, ba shi da wani choice da ya wuce ya amince, tunda shi ne silar halin da take ciki, kuma ko da ace ƴan uwanta za su zo suma amincewar za su yi saboda ta rayu. ya karɓi takardun da Dr Simon ya miƙo masa, yasa hannu akai sannan ya bar office ɗin ya koma mota, yana kallon yanda wayarsa keta ringing da sunan MD da kuma Sectery amma babu kiran da yayi picking aciki, ƙarshe da ya ga kiran na neman damunsa sai ya kashe wayar gaba ɗaya.
"Nurse! bring injection quickly". Dr Simon ya faɗa yana ci gaba da aikinsa. da sauri Nurse ɗin ta miƙo allurar ya karɓa yaywa Mairo, tunda aka kammala tiyatar Dr ya tsaya yana duban fuskar Mairo da ƙirjinta na tsawon daƙiƙu, sannan ya maida dubansa ga Nurse ɗin kusa da shi yana girgiza kai yace,"her health is fading. Bring the oxygen fast". yana saka mata oxygen ɗin ya ke ƙara faɗin,"Nurse prepare the CPR".
wucewar awa da mintuna shiru-shiru basu fito daga ɗakin tiyata ba, ganin shirun yayi yawa tsoron da Emanuel keji ya ƙara ninkuwa, ya fito daga motar jiki a mace ya nufa ward ɗin da suke, zuwansa yayi dai-dai da fitowar Dr Simon daga ICU da waya maƙale a kunnensa yana magana da wani likitan. Emanuel yasha gabansa dan sam Dr Simon bai lura da shi ba, ya dafa kafaɗar Emanuel yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya tambaye shi,"Dr what is her condition now?". ya tambaya anxiously. "Your patient is in dire state, we can not say anything for now. but relax we are trying all we can". likitan yace da shi yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya nemi kujera yay zaman daɓaro, yanzu idan yarinyar nan ta mace ya zai yi?. acan ɗakin tiyata kuwa ayanzu manyan likitoci uku ne akanta kowanne acikinsu jiki sanyi ƙalau, almost 3hours kenan da gama yi mata surgery ɗin amma har yanzu bata farfaɗo ba, wanda hakan yasa suka fara cire rai da farkawarta, rigima ta fara kaurewa a tsakanin likiticin su biyu, Dr David na faɗa akan mene ma yasa Dr Simon yay gaggawar yanke hukuncin ai mata Surgery, yanzu gashi nan idan yarinyar ta rasa ranta zai iya jawa asibitinsu matsala, shi ma Dr Simon masifar yake masa ai rashin sanin makamar aikinsa ne ya shi yake faɗin haka, Dr Friday da ya zama madiater shi ne me aikin basu haƙuri. sai kowannensu ya nufi ƙofa zai fita a zuciye, amma ƙarar na'urar da ke nuna cewar Mairo na da rai shi ya dakatar da fitar tasu, Dr David ya dawo da sassarfa, haka ma Dr Simon da Nurses suka ƙarasa gareta a hanzarce.
Bayan wucewar wani lokaci Doctor Simon ya fito, Emanuel ya tsaya jingine da bango yana fuskantar ICU ɗin, da sauri ya sha gaban Dr ɗin yana ƙara tambayarsa halin da ake ciki, yay masa murmushi tare da cewar ya biyo shi office, haka Emanuel yabi shi sai dai bai bar waigen bayansa ba, har sai da idanunsa suka ga an fito da Mairo anyi wani room ɗin da ita kana ya sami natsuwar bin bayan likitan, but still zuciyarsa bata bar taraddadin abunda likitan zai faɗa masa ba.
Emanuel ne zaune kan kujera yana facing likitan tare da sauraron bayanin da yake masa, tun a furucin farko da ya ambaci amnesia yaji hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.
"mun samu ta farfaɗo and we thank God jikin nata da sauƙi, sai dai kuma ta sami matsala ta Memory Loose ciwon da muke kira da amnesia saboda buguwar da tayi aka, so she will be Inability to remember her past for a long period of time...".
ya sauke ajiyar zuciya yace da Dr,"for how long will she remember everything?". "zai iya taking nata 3-5months.". ya miƙa hannu ya karɓi kati na magungunan da za'a siya sannan ya fita. kai tsaye pharmacy ya nufa ya siyo magunguna da alluran duk da ake buƙata kana ya wuce ɗakin da aka kwantar da ita. tun daga window yay tsaye yana kallonta yanda aka ɗaura mata drip, fuskarta naɗe da bandage haka ma ƙafarta ɗaya, yafi tsawon daƙiƙu uku a bakin tagar yana jin kamar ba zai iya shiga ciki ba saboda yanda tsigar jikinsa ke tashi, sannan ya dawo bakin ƙofar room ɗin ya tsaya, har san da Nurse ta shigo ta karɓi ledar pharmacy ɗin daga hannunsa, ta ƙarasa taje tayi allura a ruwan drip ɗin, bayan fitarta ya ɗaga ƙafa kamar mara lakka ya ƙarasa bakin gadon, tsananin tausayinta yay mugu mugun kama shi, daga irin yanda take numfashi ya isa ya fahimtar da shi irin mawuyacin halin da take ciki. jin zafin ciwon nata yake ajikinsa, haka duk wani shiga da fitar numfashinta auna shi yake da nasa. ya zauna a gefen gadon ya kai hannu ya taɓa wuyanta yaji temperature nata very high, yayi saurin ɗauke hannu sannan ya miƙe ya fita da sauri ya koma office ɗin Dr Simon ya shaida masa yanayin zafin jikinta da ya zarce tunani, tare suka dawo da Dr wanda yana zuwa ya kuma yi mata aune-aune sannan ya ƙara tabbatar masa da babu wata matsala da zarar ruwan ya ƙare zata farka kuma temperature nata ma zai dawo normal, kuma ko da ta farka kar abata komai becouse aikin da aka mata general anesthesia ne zai iya ɗaukanta 24hrs kamin taci wani abun, amma idan an samu Bowel sound ya zama present to za'a iya bata ruwan tea tasha, Emanuel babu abunda ya iya ce masa sai knooding kansa da yayi.
bayan fitar likitan Emanuel ya roƙi Nurse ɗin da ke gyara table ɗin da aka ɗora magunguna alfarmar ta zauna ta kula da ita zai je ya dawo. baifi 30minutes ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da manyan ledoji, ya zaro 5k a aljihu ya bawa Nurse ɗin ta amsa tana ta murna. shaf ya manta da batun wata waya sai ayanzu da ya jiyo ringing ɗin wata wayar daga waje sannan yasa hannu ya ɗauko tasa a aljihu ya kunna. yay dialling number MD sai da kiran ya kusa yankewa sannan MD ya ɗaga yana masa masifar ina ya saka wayarsa. yace da shi,"i got an accident...hankalina bai dawo jikina ba sai yanzu". a zafafe Md yace,"Emanuel are you Mad?, you have an accident kuma ba zaka kira ka faɗi situation ɗin da kake ciki ba...yanzu kana wane hospital?". "ka bari zuwa safiya zan sanar da kai, amma please karka bari Dad ya san da wannan. idan ya tambayeka akaina ka san ƙaryar da zaka yi masa". dan haushi ma Md ya kashe wayar ba tare da ya amsa shi ba, shi kuma yaƙi faɗa masa ne gudun kar ya faɗawa Dad ko kuma shi yace yanzu zai taho alhalin kuma yana da iyali.
har drip ɗin ya ƙare bata farka ba, sha biyu na dare yana tare da ita kamin ya tashi ya tafi hotel ya kwana acan, ya barta da Nurse ɗin ɗazu yace ta kwana da ita. washegari bai shigo asibitin ba sai around 9, hankalinsa gaba ɗaya na kan Mairo da ita ya kwana a ransa, abunda ma ya hana shi sammakon shigowa sai da ya biya office. kai tsaye ɗakin da take kwance ya shiga, tare su ke shi da Md, da mamakinsa sai yaga bata kan gadon kuma babu kowa a ɗakin, yana dube-dube sai yaga Nurse ta fito da ita daga toilet tana dafe da kafaɗar Nurse ɗin tana takawa da ƙyar, ya zuba mata ido sai ya miƙe ya ƙarasa ya ɗaukota ya kawota kan gadon ya jinginar da ita ajikin pillow. Nurse ɗin tayi masa bayanin jikin nata da sauƙi dan Dr ma yace zuwa dare za'a iya warware mata bandage ɗin fuskarta. Mairo tayi shiru tana sauraronsu dan jinta take a wata sabuwar duniyar, ita kanta maganar da suke yi ba ganewa take ba, gashi ba ganinsu takeyi sose ba hasalima sai ta kusa rumtse ido gaba ɗaya ne take samun ganin abu very tiny. "How are you feeling now?". Emanuel ya tambayeta yana kamo hannunta ya riƙe cikin masa. ta dai ji maganar da yayi amma bata san me yace ba, tayi shiru sai Nurse ɗin ce tace da shi,"i noticed like she is not hearing english".
Md ya girgiza kai da cewa,"i also noticed that". Emanuel ya dube shi yace,"to mene abun yi kenan?". "amma ai lossing memory ba ya shafar language na mutum". Debora tace"um ba ya shafar yaren mutum, ita ɗin bahaushiya ce tun da ɗazu da hausa tayi magana". Md ya ɗaga kafaɗa,"alright, shi ma english ɗin da sannu ai zata iya making".
"me taci da ta farka?". Emanuel ya tambaya. Deborah tace da shi,"babu komai yanzu dai za'a iya bata". ta ɗauki ƙaton tea flask ɗin da suka zo da shi ta zuba tea a mug sai ƙamshi yake, ta miƙawa Mairo cup ɗin tana cewar ta amsa da yake ita tana jin hausa kaɗan-kaɗan kasancewar tayi zaman Kano. Mairo ta miƙa hannu tana laluben ta inda zata amsa Cup ɗin, suka tsaya dubanta da mamaki kafin Debora tace da ita,"me ya sami idon naki ne, ga ta inda na ke miƙo miki abu ke kuma kina miƙa shi ta wani wurin". muryarta na rawa kamar zata yi kuka tace,"ai bana ganinki ne". "ba kya gani?". Mairo ta ɗaga kai,"ehh ina ganin duhu amma bana ganin hannun naki".
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 52