dole tayi alkunya, kuma bata da haufi akan kulawar da Inna Amarya zata bawa Mairo kamar yanda zata bata. Inna Zulai ta tattaro wasu ƴan canjikanta na saida mafici ta bawa Malam tace a haɗa da su, Malam ya karɓa ya baiwa Kabiru yace ya haɗa dana wurinsa.
Da zuwansu cikin ikon Allah suka sami ganin likita har aka basu gado, ɓangaren Gwaggo hankalinta yay ƙololuwar tashi da jin zancen, tace zata nemi kuɗi ta taho a yanzu Baba yace a'a ta zauna ai jikin da sauƙi tun da harta farfaɗo daga suman an kuma yi mata allurai bacci ya ɗauketa. A ɓangaren Malam kuwa faɗa ya sha shi a wajen likitoci, na ɓata lokacin da akai wajen kawota, har suke ce masa da sun ƙara wasu lokuta sai dai su kawo gawarta, sun kuma shaida masa a duk iya binciken da suka yi basu gano wani ciwo a cikin nata ba ko kuma wani abu da ya kawo sanadin hakan, sai dai sunyi ƙoƙarinsu wajen ganin sun bata taimakon da zai tsaida aman da shi ciwon da take ji idan ta farka.
An rubuta allurai da magunguna masu tsadar gaske wanda akai umarni da a gaggauta wajen siyo su, Baba yay shiru domin ba shi da ta cewa, dama tun farko abunda ya ke ji kenan, idan sun gudarwa asibitin kuɗi, nan ma fa ba komai ne zasu yi musu a kyauta ba. Yana tsaye ya zubawa Mairo ido, wadda fuskarta tayi muguwar rama kamar wacce ta shekara guda a kwance cikin ciwo. Tsausayin kansa dana iyalinsa ya daɗa kama shi, ya maida dubansa ga Kabiru wanda yasa kai zai fita cikin mutuwar jiki, ya dakatar da shi daga tafiyar da cewa, "Ban amince maka da rancen kuɗin kowa ba Kabiru, idan kuwa kai hakan to bada yawuna ba wallahi, kuma fushina zai tabbata akanka". Kabiru ba shi da tacewa saboda haka dole ya dawo ciki ya zauna, Inna Amarya tasa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata, "To Malam ko can gida zaka kira a ɗebi samiruna akaiwa Matar liman ta siya". Malam ya girgiza kai yace, "babu abunda za'a siyar, mu jira ruwan da aka saka mata ya ƙare, insha'Allahu lafiya ƙalau zata farka".
Har ruwan da aka sakawa Mairo ya ƙare bata farka ba, ma'aikaciyar jinyar tazo ta ƙare jarabarta ta tafi babu wanda ya tankata, dan tun a ɗazu take zuwa tana tambayarsu alluran da akace a siyo su na cewa tukunna dai kamin ruwan ya ƙare, ga shi har ruwan ya ƙare shiru. Wata mata da ke kusa da gadonsu itama tana jinyar yaronta ta taso tazo kusa da Inna Amarya tayi musu ya mai jiki, Amarya ta amsa da Alhamdulillahi. Sannan matar ta dubi Malam tace da shi,"ku ƙara haƙuri nan da ƙarfe tara da rabi akwai wanda yake taimakawa marasa lafiya a wajen sayan magani da abubuwan dai da asibiti suka buƙata...su na yin abin nasu cikin tsari ne zasu bi gado gado har sai an biyawa kowa buƙatarsa". Kabiru ya duba agogo yaga lokacin har tara da rabi saura minti goma, saboda haka suka fasa tafiyar da Malam yace ayi suka ƙara jira.
Tara da Rabi dai-dai kuwa sai ga wasu maza sun shigo su biyar jikinsu da rigunan aikin asibiti, sai mata biyu dake biye da su, ɗaya dattijuwa ɗaya tsohuwa. Madam Merry da Madam Gloria kenan, daga kan gadon su Mairo aka fara amsar katin, Madam Merry ta karɓi katin daga hannun Kabiru ta saka hannu sannan tace ya wuce can wajen karɓo magani ya amso, a haka suka dinga zagaye gado zuwa gado har sai da ta tabbatar ta saka hannu akan katin kowa sannan suka bar ɗakin, masu zaman jinya suka rakata da godiya da kum adu'a.
*1:00pm.*
Agogo ya buga ɗaya na dare, A hankali na shiga buɗe idanuna waɗanda naji sun matuƙar yi min nauyi saboda kukan dana sha, ko'ina na jikina ciwo yake saboda tsananin galabaitar da nayi, bin ko'ina nake da kallo da son tantance a inda nake dan ban fidda tsammanin na mutu ba.
Ina kallon gefen haguna Adawiyya ce ta kwantar da kanta kusa dani, hannunta cikin nawa ta riƙe gam, sai Inna Amarya da ke shimfiɗe a ƙasa da gani bata ji daɗin kwanciyar ba. Na maido idona ga hannun damana inda Ya Kabiru ke tsaye a kaina ya jingina da bango, da alama tsumayin farkawata yake dan ina ɗaga kai muka haɗa ido da shi, ya kuwa sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tare da lumshe ido sannan ya buɗe. "Sannu". Ya faɗa a san da yake taimaka min wajen tashi zaune. "ina ne yake miki ciwo yanzu?". Ya tambayeni yana duban yanda nake aikin cije fuska. Nayi masa nuni da cikina, "Ya cikina ne wani abu ke yawo yana karta min farcensa". Yay gajeran murmushi tare da cewar, "yunwa ce". Na girgiza masa kai cikin ƙarfin hali nace, "Ya wallahi ba yunwa bace, yawo yake yi ta ko'ina fa...zafi sosai". Yay ɗan jim yana dubana da nazari kana yace, "ko lokacin al'adarki ne yayi?". Na kuma girgiza masa kai, "a'a Ya ai a farkon wata nake yi". "to ƙila an sami sauyin yanayi ne, sannu bari kici abinci sai kisha magani za ki ji sauƙi kinji Mairon Yayanta". Na buɗa idona da ya cika da ruwan hawaye saboda irin azabar da nake ji na kalle shi, ina fashewa da kuka nace, "Ya ciwo sosai, zafi yake min, ina jin kamar ana tsatstsagani da reza ne". Ya matso kusa ya kwantar da kaina saman ƙirjinsa yace, "yi haƙuri zai daina kinji".
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*Anyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*15)*
A wannan daren haka Ya Kabiru ya fita ya nemo min abincin da zanci, tuwan dawa ne da miyar kuɓewa busassa, Inna Amarya ta bani abincin da kanta wanda na samu naci shi da ƙyar shi ma kuma kaɗan, bayan na gama ci Baba ya ɓallo magunguna na sha da ruwan tofin adu'ar da yayi, Adawiyya na gefe tana ta aikin jera min sannu cike da ɗumbin tausayina, har tsawon wani lokaci da magani ya tsarga min cikina bai bar yi min ciwo ba, ciwon da nake jin inama zare raina akai na huta, tun ina kuka sautinsa na fita har na koma sai hawaye da ke sauka ta gefen idona, Baba kansa ya sare da lamarin nawa ya barwa Allah yayi ikonsa akai...cikin hukuncin ubangiji kuma wajen ƙarfe uku na dare sai ciwo ya tafi, na neme shi na rasa, kafin asuba nayi garau dan bacci harda munshari, kuma na tashi ras da ni, ƙarfe takwas aka bamu sallama muka koma gida.
Inna Zulai na shara muka shiga gida, ganina yasa ta tsaya kallona da maɗaukakin mamaki, kamin ta wurgar da tsintsiyar ta rungumeni jikinta, sannu da barka take ta jera min ba adadi, lamarin nata har ya bani mamaki, ta sakeni ta kama hannuna mu kai ɗakin Gwaggo, ƙwalawa Gwaggona kira take tana ta fito taga ikon Allah. Gwaggona da ta fito ta ganni tsaye da ƙafafuna kamar ba wadda aka fidda ranta daren jiya ba, tsananin farin ciki yasa duk ta ruɗe ta kiɗime, ta jefar da kwallar da ke hannunta ta rungumeni, godiya take ga Allah tana kuma yi min sannu, ta sakeni ta ɗago tana dubana, tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta ta ce, "Mairo kinga yanda kika rame...babu dai inda ke miki ciwo yanzu ko?". Ta ƙarashe muryarta da damuwa. Nayi murmushi nace, ,"Gwaggona ki kwantar da hankalinki ni kam na warke, babu inda ke min ciwo yanzu haka". Ita da Inna Zulai suka haɗa baki wurin faɗin, "Allah ya ƙara lafiya". Dai-dai lokacin kuma da su Baba suka shigo, Inna Zulai ta wuce tana musu sannu da zuwa tare da amsar kayan hannunsu, ni kuwa binsu na ke da ido da al'ajabin sauyin da aka samu a tsakaninsu.
a ɗakin Gwaggo dai da aka yada zango babu hirar da ake sai ta ciwona da ya kiɗima kowa, duk faɗi suke ba su taɓa zaton zanyi rai ba, Sadiya ta kawo min duka tana cewa inda na san ba mutuwa zanyi ba ai sai na faɗa mata tayi bacci harda munshari, ina dariya nace,"yanzu dai ban ce kinyi ƙarya ba amma kina so kice min baki bacci ba jiya?". "hmm ba za ki fahimci halin da aka shiga ba ne". Shi ne abunda ta iya cewa kawai, Inna Zulai ma tace,"to ai ko ni nan wallahi baccina sama-sama nayi shi...ga Kabiru ne kaɗai me waya a gidan balle mu kira muji halin da ake ciki, to tare ku ka tafi da shi, da asubar fari kuwa da naji su Salisu sun buɗe ƙofe gida ba kiji gabana yanda ya faɗi ba". Na ƙyalƙyale da dariya har ina kifawa jikin Gwaggona nace, "wooo ni Mairon Baba ashe dai a gidan nan ana so na har haka". Inna Zulai ta ƙwalo min mafici tana miƙewa ta fita dan kawo min Kunu.
Shigowar Kakarmu Yagana sai gida ya ɓarke da sabon bidiri, ita bata san an sallamomu ba, ashe tun a daren jiya da akace mata an kwantar dani a asibiti sai ta ɓarke da gudawa jin ance an tafi da ni a sume, ta zauna kan dakalin ƙofar ɗakin Baba tana kuka har da su zuƙar majina, Kuka wiwi kamar wadda aka aikawa saƙon mutuwa, faɗi take, "yanzu ko a wanne hali yarinyar nan take ciki oho, ya Allah ka bata lafiya...shi kuma Adamu da rashin azanci ai sai ya dawo ya sanar damu halin da ake ciki ko kuma ya turo shi Kabirun, amma duk sai su zauna acan su yi shiru abin su, ko da ike zani ce ta tadda muje, danma dai Allah yasa ba Amadu bane, in wannan yaronne sai ta mutu ma a binneta bamu sani ba...to yanzun ma wa ya sani ko ta mutu ni Rakiya...yarinya me hankali da tunani kaf jikokina albarka...Allah na tuba kar nayi saɓo ita cutar ga yara nan rututu a gidan amma ta rasa wa zata ɗauka sai abokiyar hira ta". Yagana ta miƙe tana gyara zaman gyalenta da yaƙi zama tana cewa, "ke Suwaiba ɗauko sutararki mubi sahunsu ni ba zan iya wannan zaman jiran tsammanin ba, in jini kawai acan hankalina zaifi kwanciya...ke ma dai banda soluwar Uwa ce ace an kwantar da ƴarki a asibiti amma kina zaune anan hankali kwance wai kin barwa kishiya riƙonta, to idan da mugun nufi aranta fa tayi mata wani abu ta ƙarasata fa...ko da yake ba Zulai bace balle nace, amma ita ma Aishan ba na shaideta ba tun da shi mutum ba sanin abin da ke cikin zuciyarsa kayi ba...yanzu mutane sun zama Allah a fili fir'auna a zuci, kiga su na ta haba-haba da kai su na nuna maka duk duniya ko uwar da ta santoloka duniya albarka, nan kuwa duk buge ne a zuciya ji suke kamar su kasheka...to matsalar idan kasha tabara kasha yasin kuma ka ɗora da tofin Allah ya tsine shikenan ka gama da su, takaicin duniya ya kamasu, su rasa kataɓus". Ta yi shiru tana gyara ɗaurin zani kan taci gaba da cewa, "ki zo muje ƙawata Harira ta kawo min ajiyar kuɗi sai na ara mu yi kuɗin mota da su, na san har da rashin kuɗin motar ma ya hanaki wanke ƙafa kibi sahunsu tun duku-dukun asubahi...ni gaba ɗaya wannan zama naku na rasa irinsa wallahi, ban taɓa ganin kishiyoyi marasa hankali da tunani irinku ba, ace wai idan ɗayanku na cikin mawuyacin hali ba za'a sami mai taimaka masa ba...to s'a kowacce ta kama nata ta ɗaure a gindi, wannan dai ba hali na gari bane sam ku sauya tun kamin ƙasa ta cika muku baki". Ta ɗago tana duban Inna Zulai wadda tayi kicin-kicin da fuska tun a ɗazu, tace da ita, "yanzu ke Zulai in da ace matar arziƙi ce ai mai iya yiwa gidan nan kuɗin mota ce duka a tafi asibiti tun da ke da sana'arki me kauri a hannu...ta in da nake godewa Allah kenan da Amadu bai yo mugun halinki ba...yanzu ke da me wayo ce ma ai rawar jiki za ki kama ko dan ki samu fada a wajen mai gida...to matsalar ke ba kya jin faɗa balle shawara, da an soma magana sai kice za ki zumɓurowa mutum baki, shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, ga shi dai gidan ɗana ba na ɗan wani ba...to amma gwara aje gidana a sameni yanda zanyi da dalili idan an min abin da bai gamsarni ba...to Allah dai ya kyauta". Magana take tayi ta hana kowa cewa uffan, da ma ita idan ta fara bata gajiya kamar radio, ta nufi zaure tana mitar Gwaggo da nuƙu-nuƙu a wajen shiri, zuwa asibiti ba wajen biki ba ta rasa shirin me ta tsaya yi. "to ni da nace ki ɗauko sutura ba duka kayanki nace ki ɗauko ba fa, ina nufin ki ɗauko abunda za ki sutarta jikinki". Gwaggo tace, "to ai Yagana ke ce tunda kika shigo kin hana kowa magana". Yagana ta saki baki galala tana kallonta,"au so kike kice da asiri na shigo kenan tunda har za ki ce na rufewa kowa baki...to ni wallah ko da ƙawayena da suke bin bokaye ni dai Allah bai taɓa nufata da zuwa ba har na gama tashen ƴan matancina.....". Gwaggo tayi saurin katseta da cewa, "yi haƙuri Yagana ba haka nake nufi ba, ina nufin kina ta faɗa ne...". Ai Gwaggo bata ida zancenta ba Yagana ta tari numfashinta, "ai da ike ga jarababba ta afko muku gida...to ni kinga ma nayi tafiyata kisha zamanki, ko da kika ga na damu da naje banda Mairo ce babu abunda zaisa na ɗaga hankalina haka, dan da ace su Sadiya ne sai dai na bisu da aiken gaisuwar jinya, wanda yake maka ai shi kake damuwa da shi, Mairo kuwa ai ba daga nan ba". Har ta isa zaure kuma sai ta dawo tana cewa,"ni kuwa ina mara lafiyar gidan nan har yanzu dai bakin bai buɗe ba ko?, wannan Mata tana ganin jarabawar rayuwa, Shekara da shekaru cuta babu sauƙi, Allah dai ya kawo sauƙi, ko da ike ma wa ya san me kika aikata aka garƙame bakin...Saleh ungo ka bata wannan alawar nima Mujibu ne ya bani ita jiya da daddare, to ban samu shanta ba ma har yanzu da ike inata fama da ciwon haƙori kuma babu na arziƙin da ya iya zuwa ya dubani, iyalin Adamu dai sai Allah ya min magani kawai...ungo don Allah ɗayar na sha in haƙorin ya warke, haka kawai Allah ya haɗa jinina da ita mugun tausai take bani wallahi, ace mutum ba um um, wannan baki ai sai ya gume da uban wari". Saleh ya karɓi alawar ya miƙawa Kulu, Adawiyya kuma tace da ita, "to Hajiya Yagana idan kin gama faɗan naki an hutar da ke zuwa asibitin, ki dawo ga Mairon a gida sun dawo tun ɗazu, masifarki ta rufe miki ido kika kasa ganinta". Sadiya tace,"ai da kin barta taje ƙafarta ta gaya mata". Yagana da ta kai zaure ta dawo tana zabga salati,"ke Adawiyya amma ku dai halinku sai ku, yanzu tun ɗazu kun san da hakan baku faɗa min ba ku ka barni ina ta zuba magana ni ma da bana iya shiru da bakina". Na tafi na rungumeta ita ma ta rungumeni, sai ta shiga matsar ƙwalla tana ƙara faɗin ciwona ya ɗaga mata hankali ainun, dan Allah na dinga kiyayewa da shegen kwaɗayina na ciye-ciye, ba komai ake kaiwa ciki ba dan wani abun guba ne.
Mu ka koma ɗakin Gwaggo muka zauna aka ci gaba da hira, Ya Kabiru na bada labarin yanda aka karɓemu a asibitin da yanda suka sare da siyan magani, sai da wasu Arna da su ke bada tallafi suka zo kana aka sami magunguna. Yagana tace,"to Allah yasa su na da rabon musulunci". Gwaggo tace mata, "jiya ma ai da za'a tafi babu kuɗin mota Zulai ce ta ɗauko ƴan canjinta ta bayar, da su aka samu na siyan ruwan da aka ƙara mata". Ta ajiye kofin kunu da ta kai bakinta, "to Allah shi albarka yasa kuma dan Allah akayi". Babu dai wanda yace mata ƙala, sai ni da muke hirarmu, tana cewa na shanye kunun tas ko na samu naji ƙwarin jikina. Baba ya dawo ya miƙo min leda, na karɓa nayi masa godiya da adu'a, nama ne balangu aciki, Yagana ta warce ledar tana cewa ba zanci ba, jiya ma aishi naci yasa ni leƙawa lahira amma saboda ban san ciwon kaina ba zan kuma ci, Yaya Kabiru yace mata ai na jiya tsire ne, tace ita dai koma mene ba zanci ba, to ita inta kafe kan magana babu mai iya ja, haka ina ji ina gani dole na maida yawun bakina, ta bawa Saleh tace ya kaiwa tumakinta su ci, ta kuma gargaɗe shi akan shi ma kar yaci.
Su na magana da Baba akan zancen asibiti yana faɗa mata aiko binciken da likitoci su kai sun ce ba daga abunda taci bane, amma shi yana tunanin ba zai wuce shawara ba. Yagana ta kifa kai da hannu tana jero salati,"oh ni Rakiya, idan ance ba daga abunda taci bane to kar dai ace mayu ne suke ƙoƙarin kamata". Baba yace,"ah haba Yagana ciwo ne dai kawai". "hmm Adamu ka bari kawai, amma ni dai zanyi iya dafa qur'ani mayu ne su ke son kamata ko kuma baki, kasan kambun baka ma mugun abu ne". Ta dube ni tace,"ina dai ce har yanzu halinki dana sani ya nan na rashin barin ko ta kwana? Dan ko shekaranjiya yaron nan Auwalu ya labarta min irin ɗibar albarkar da kika yi masa kwanakin baya...to billahillazi Mairo ki shiga hankalinki, idan kin san wani ba ki sa wani ba, in wani ya barki wani ba zai barki ba...to ni dai na roƙi ki rufa mana asiri haka, kar a kuma irin ta ɗan gidan Ladiyo da kika ƙwalawa dutse da kuna yara tasa aka shanye miki ƙafa". Na tura baki gaba nace,"to ni Yagana yaushe rabona ma da faɗa da wani, ko fita yanzu ba yi nake ba...shi kuma Auwalun munafiki da ya kai miki gulma ai shi ya fara zaginmu yace mana ƴaƴan me faskare". Ta gwame baki tace,"to da ƴaƴan shugaban ƙasa kike so yace muku...ko kuwa ƙarya yayi ku ba ƴaƴan me faskaren bane, ni in da yay magana dani ma ai sai in faɗa masa abunda bai sani ba Kakanku ma me faskare ne, kinga idan ya tashi yace ƴaƴan me faskare jikokin me fakare, zancen banza kawai...ke ba ɗiyar kowa ba sai jin kan tsiya...". Na katseta da cewa,"Yagana babu fa zancen jin kai anan wurin, babu ɗan halak ɗin da za'a zagi ubansa yaja baki yay shiru, balle kuma ni Mairo, wallahi kaf faɗin duniya ma ba acikin garin bichi ba babu shegen da zai aibata sana'ar ubana nayi shiru sai na rama...ke fa da kanki kike ce mana kada ɗan banzan da yay mana mu ka ƙyale dan za'a raina mu, balle shi shegen munafikin na san ba gaskiya ya faɗa miki ba, dan da kema alokacin ko baki tsine masa ba sai kin masa iyaka da gidanki...kinga kuwa irin cin kashin da yay mana daga Adawiyya ta bige wani tsamurmurin yaro ba ta sani ba, Wai shi ɗan birnin da naira ta zaunawa ajiki, shikenan su duka suka hauta da masifa saboda sun ga sauna...ni kuwa na bi su har inda suke nayi musu wankin babban bargo". Gwaggo ta hamɓareni daga kusa da ita ta hauni da faɗa,"dama irin abunda kike shukawa a wajen kenan, faɗan ma ki rasa da wa za kiyi sai da Auwalu yaro me hankali...to daga yau ɗin nan na gargaɗeki, kar na kuma ji tunda ba sa'anki bane shi...kuma ita Adawiyyar da ace ta na kallon gabanta ta ina zata bige wani har a zageta...shashashai biyu kawai, to wallahi ku iya talaucin gidanku, dan duk ranar da ku ka kai wani bango naga kadarar da za'a siyar a ƙwato ku". Gwaggo bata rufa baki ba Baba ma ya ɗora da nasa, su ka hau mu caa ni da Adawiyya faɗa suke mana ta inda suke shiga bata nan suke fita ba, haƙurin ma da mu ke bayarwa basa ji. Baba faɗi yake,"idan kuma kun sauya wasu iyayen ne sai naji, dan ni dai nasan ba tarbiyar gidana bace wannan".
Yagana ta taƙaita faɗan nasu da cewa, "kai Adamu naji kana batun tafiyar makarantar yaran nan anjima...to Magana ta gaskiya banda Mairo za'a tafi, ita a barta sai ta gama warwarewa...". Nayi karaf nace,"warwarewa kuma ta yaushe, ni naji sauƙi". Taja carbi tayi hailala uku sannan tace, "kaga ai irinta, in dai da Mairo a wuri bata barina na magantu, to kace mata tayi shiru da kai na ke maganata". Ta dubi Ya Kabiru tace, "yanzu kai ne zaka shirya ka rakani gidan Malam Kabiru, naje na zayyane masa komai game da ciwonta...ai mata rubutu ya bada turarukan sammu...an fara da irin haka ba zai yiwu ta shiga dokar daji babu tsari ba, dole a miƙe tsaye...tunda iyayen ba masu lura da ƴaƴa bane, kwanaki ita Suwaiban da nayi mata magana ma cewa tayi Allah na tare da su, bayan Allah shi da kansa yace tashi in taimakeka...kuma fa alhalin tana ganin wannan yarinyar halittarta dole a miƙe tsaye akanta saboda baki da kuma ƴan hasidin iza hasadin...Allah ya jiƙan Alhaji da yana raye tun kuna jarirai zaku dinga shan rubutun tsari...dan haka ni dai a matsayina na Rakiya in har na isa ina kuma da iko akan Mairo to babu inda Mairo zata je a yau, a barta sai wani jiƙon".
Baba zai yi magana ta ɗaga masa hannu, dole yayi shiru.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*16)*
To babu yanda dai Baba ya iya, dan bin umarnin Yagana dole in har ana son kwanciyar hankali, sannan kuma Baba yana neman albarka.
Ta yunƙura ta miƙe Sannan tace da Ya Kabiru,"tashi muje ka rakani kamin lokacin tafiyar ta ku yayi". Yace da ita,"A'a fa Yagana ki kama hanya ki tafiyarki ke ɗaya kawai, ni da zan kai yara makaranta, yaushe muka je muka dawo har na shirya". "to amma dai naga ai da sauran lokaci tafiyar, yanzu ne fa zamu dawo ba zama za muyi ba...ina so ne a haɗa har kai da Amadu na amso muku na farin jinin ƴan mata ko Allah yasa a dace". Ta faɗi hakan tana ƙunshe dariyarta. Nace da ita,"abun ai ba rashin farin jini bane kije ki duba kiga irin tururuwar da ake akan su". Ya Kabiru ya kalleni yace,"barta ni tuni ina da matata a hannu, dan haka ta riƙe taimakonta Amadun ma baya so". Ta doki cinya tayi bakin ƙofa tana faɗin,"kwayi da wata". Ta fice tana cewa su Gwaggo sai ta dawo, su ka rakata da adawo lafiya. Tana nufar zaure tana jaddadawa Gwaggo a jiƙa min tagarzaje na sha, shi ma ance yana maganin mayu, kamin dai Allah yasa taje ta dawo ɗin. Ya Kabiru na bin ta a baya yace,"ke dai a dawo lapia...zancen tagarzaje kam ba zata sha ba haka kawai ya kuma hargitsa mata ciki...mu magani in dai ba Nafdac bama sha". Ta tsaya sololo tana dubansa tace,"shi kuma Naufdak ɗin mene?". Yace,"ba ki san shi ba". a ƙufule tace,"saboda ban sani ba ɗin ai na tambayeka, Allah sa kuma ba zagina kayi da harshen nasara ba...daɗin Amadu kenan shi magana bata dame shi ba balle har ya faɗa maka ba daɗi". Ya Kabiru ya girgiza kai,"to ni yanzu Yagana me nace acikin maganata mara daɗi". "yo gashi kuwa ina cewa a bawa yarinya maganin da zai taimaketa kana ce min
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 52