Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
in har ba shiga ɗin yay ba, ba zai sami abinda yazo nema ba, kuma idanma zai sami bayanin da ya ke so ɗin daga wajen wani to dole sai wanda yake mazaunin cikin masarautar ne. ya buɗe murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yake kallon masarautar da tunaninka mabanbanta acikin kansa. fitowar wata farar mota ƙirar BMW daga cikin masarautar ya ɗauki hankalinsa, bin motar yake da ido har san da ta hau kan titi idonsa ya sauka akan lambar motar da ke ɗauke da rubutun sunan *Al-Hassan Bin Samin Al-Thalis* da manyan baƙi, ta ke anan maganar Kulu ta gifta a cikin kansa. _"ina ji ajikina Al-Hassan yana tare da ahalina, duk da cewar mahaifinsa ya ƙwace shi daga hannuna, amma na san ba zai iya ɗaukar nauyin riƙe shi ba, so dole ne ma cikin biyun ɗaya, ko ya salwantar da rayuwarsa ko kuma idan da sauran wannan ɗison imanin da na fara saninsa da shi a zuciyarsa to zai miƙa shi gidanmu, zuciyata na cikin zullumin son sanin a wane irin hali Al-Hassan ke ciki, wallahi bana iya bacci saboda tunaninsa, ka taimaka min Kabir"._ bai san ata yanda zai kwatanta yanda yaji ba da ganin wannan motar, suna kawai ya gani ba shi da tabbacin wanda ke cikin motar, dan haka dole ma yay binciken wanda ya wuce acikin motar. "Driver kabi min bayan waccen motar". abin da yace da me taxi kenan, suka shigo ciki shi da Abdurrahim. Driver faɗi yake,"Yallaɓai ina fatan dai silar hakan ba zai sa na shiga wata matsala ba, domin na lura kai ɗin kamar ma'aikaciɓ bincike ne". "kar ka damu babu wata matsala da zata gifta, ni ɗin ba ma'aikaci ba ne akwai abin da na ke nema dai...ka ƙara speed dan Allah kar su ɓace mana". me motar ya ƙara gudu yana bin bayan motar da irin dabarar da ba za'a gane bin ta yake ba. motar bata tsaya ba sai a wani ƙaton building da ke ɗauke da rubutun Qatar Charity. su kuma tasu motar ta tsaya daga baya, Kabir ya rufe ido yana roƙon Allah akan Allah yasa kar motar tasu ta shiga cikin gidan marayun ba tare da ya ga Al-Hassan ɗin da zuciyarsa ke zullumi ba, ga shi shi ba irin shigar da zata nuna shi ɗin me tsananin buƙatar taimako bane balle yayi amfani da damar hakan a dabarar da ke cikin kansa, yasa yatsunsa cikin sumar kansa ya yamutsa gashinsa yana cije leɓensa na ƙasa. kamar ance buɗe idonka, yana buɗewa yaga motar na bakin gate bata kai ga shiga ciki ba, sai kuma biyu daga cikin security ɗin da ke tsaron wajen su ka zo suka buɗe murfin motar na ɓarin dama da hagun. Kabir ya buɗe motar ya fito ya tsaya daga gefe kamar wanda hankalinsa ba'a wurinsu yake ba, ta gefen idonsa yake kallon matar da ta fito daga cikin motar sanye da baƙar abaya, fara ƙal da ita wadda zai iya kira da potocopy ɗin Mairo ta yanda take takun tafiyarta, fuskarta cike da annuri idanunta kuma na ɗauke da gilashin da zai baka tabbacin medical ne. yes! ba shi da haufin cewa wannan ita ce mahaifiyar su Kulu dan ga kamanni nan sun bayyana, ya leƙa cikin motar yana tambayar me taxi, "dan Allah wace ita ɗin?". ya ba shi amsa da,"Yallaɓai wannan ita ce Sarauniya Asma matar Mai Martaba". maida dubansa gareta da zai yi sai yaga wani ɗan saurayi tsaye a kusa da ita tana mishi bayani yana kaɗa kai alamar yana sauraronta, shi ma fari ne ƙal kyakykyawa, dogo, siriri, gefen idonsa akwai abar da ake kira da tusar jaki, akwai kama ta jini sosai a tsakaninsu, bai yi tambayar da zai sake yiwa me taxi ɗin ba ya sami amsarta daga Umm da sautin muryartata ya sauka a kunnensa tana faɗin,"Al-Hassan". ta kira sunan ɗan saurayin da ya juya zai shiga cikin gidan marayun. anan Kabir ya sami damar ƙare masa kallo, sam basa ma kama da Kulu bama zaka ce ɗanta bane indai ba ka lura da kama ta jini ba, kawai dai a surar jikinsa ne suka yi yanayi da Mairo da idan ka gansu tare zaka iya cewa Yaya da Ƙanwa ne. yay wani sanyayyan murmushi na nuna jin daɗi, sannan ya lalubo wayarsa daga aljihu ya danna kiran lambar Kulu amma sai dai yana ta kiran bata shiga ba, sai can kuma ta shiga a bugun farko kuwa muryarta ta shiga kunnensa. "Salamu Alaikum Kabir". sai ya lumshe idonsa ya jingina daga jikin motar, ƙarshen aikinsa yazo, haka kuma ƙarshen komai yazo. ya amsa sallamartata,"wa alaiki salamu da Aaliyah, barkanki da wannan lokaci". bata yi mamaki ba domin tasan dole ayanzu zai san asalin sunanta in har yay binciken da tasa shi, saboda haka ta amsa masa da,"wane tarihi ka samu ga me da wannan sunan?". har yanzu wannan murmushin na jin daɗi bai bar fuskarsa ba yace,"duk wani bayani ki bari ba yanzu ba sai zuwa anjima...yanzu dai babban albishir zan miki". cike da zumuɗi me ɗauke da fargaba tace, "Allah yasa albishir ɗin da zai yaye min wani kaso na cikin damuwata ne, ina sauraronka ɗan halak". Ya shafi goshinsa yana cewa,"gani a kusa da Umm da Al-Hassan". sunayen da ya ambata suka daki zuciyarta bugunta ya sauya,"Kabir ka san waɗannan sunayen a bakina, saboda haka karka yi wasa da ni dan wanzar min da farincikin da ba zai ɗore ba". "wallahi da gaske nake miki, tsakanina da Al-Hassan ma bamu da tazara, gashi nan ya girma ya zama saurayi kamar yanda Maryam ɗita ta zama budurwa". a ɗan shiru da ta yi zai iya rantsewa hawayen farin ciki take, kuma bakinta yaƙi rufuwa saboda farincikin da ya lulluɓeta, ya katse wannan shirun nata da tambayar,"amma ko kusa ko alama babu kamanninki a tare da shi, banda kamanni ta jini da kuma kasancewarsa tare da Umm da zan rantse nace ba shi ne Al-Hassan ɗinki ba". ta bashi a amsa da,"ai shi kamar mahaifinsa yayi tun a ranar farko da ya zo duniya...Kabir ina so na dawo cikin ahalina sai dai ban san ya zanyi ba, ubansu ya zama silar tarwatsewar duk wani farinciki nawa". ya sauke numfashi yana faɗin,"karki damu in Allah yarda komai zai warware acikin sauƙi". ta amsa da,"Allah ya yarda". sannan ta kuma ce masa,"to baka sami labarin Hussainar ba?". yace da ita, "yanzu tunda na gama da nan da zarar na sauka a Ethiopia wurinta zan fara sauka, ita ma zan gano miki ita da lafiyarta, karki damu". ta sauke numfashi sannan tace,"to baka ce min komai ga me da Abi ba". "nace miki sai na tattara dukkan bayanan komai sannan zan sanar miki, nan Qatar dai na gama da ita, Hussainarki ce kawai tayi saura acan ethiopian ma". kamar tana gabansa a lokacin ta gyaɗa masa kai,"to shikenan na gode Kabir". ta tari numfashinsa akan maganar da zai yi da faɗin,"ina ɗaga wayarka kenan Malam ya aiki su Hussaina, sai dai idan ta dawo zuwa anjima zan kiraka".a sannan wani annuri na fuskarsa ya ƙaru yace da ita,"tom sai na jiki...amma nan da 3hours dai ina jirgi". daga haka kuma suka yi sallama. ya koma mota drivern yaja su zuwa airport, a duniyar tunaninsa ta yau gaba ɗaya cike take da tausayin Kulu, in banda ƙaddara me tsanani me zai baro Kulu daga cikin daularsu ta koma rayuwar ɗan akurkin gidansu. *Ethiopia, 2:00pm.* zaune su ke shi da Abdurrshim su na cin abincin rana, Kabir abincin kawai yake ci amma hankalinsa ba awajen yake ba, yana can wata duniyar ta tunanin ƙalubalen da zai fuskanta akan tabbatuwar mafarkinsa, Aure! aurensa da Mairo. ya furzar da iska daga bakinsa yana maida kansa jikin kujera, idanuwansa a lumshe ƙirjinsa na motsawa. "wai dan Allah ba zaka faɗa min abunda ke faruwa bane Kabir?, a ranar yau kaɗai na fuskanci akwai damuwa a tare da kai kuma kake ɓoye min...duk da ban sani ba amma zan iya cewa akwai alaƙar damuwarka da masarautar Qatar da muka baro, dan Allah ka faɗa min ko zan iya baka tawa gudunmawar wajen ganin komai ya warware maka". idanun Kabir har yanzu a rufe suke bai buɗe ba, yace da shi,"karka damu Abdurrahim, damuwar ƴar kaɗan ce wanda ba zan iya maganceta ba ko wani ya magance min, Allah yana sane da lamarina, shi zai shiga cikin lamarin ya warware min matsalar". rufe bakinsa yay daidai da shigowar kira a wayarsa, Kulu ce dan haka yay saurin ɗagawa, muryata ta fito a hankali da ce masa,"ya ake ciki ka sami ganin Hussainar?". nauyayyan numfashin da ke ƙunshe a zuciyarsa ya saukar, sannan ya fesar da numfashin daga bakinsa. "komai ya kammalu, fallasuwar ɓoyayyen sirrin kawai ya rage...ina jin wani nauyi a ƙasan zuciyata kamar an ɗora min babban dutse, ki saka min muryar Maryam ko zan iya samun ƙarfin jikina ya dawo daidai". daga cikin banɗakin da Kulu ta ke ta dafe goshi a ranta ta furta Ya Salam, yanzu ya zata yi, ɗazu ma fa ƙarya tayi masa, ita dai ko ta sanar masa da gaskiyar ɓatan Mairo ne ta huta da kwane-kwane?, ɗayan ɓarin zuciyarta ya kwaɓeta akan faɗa masa hakan, tana cikin neman mafitar ƙaryar da zata sake yi masa Yagana ta shigo gidan, maganarta kuma ta karaɗe cikin gidan, Kulu ta sauke wata ajiyr zuciya da yin hamdala ga ubangijinta, sannan ta maida wayar ta kara a kunnenta tana ce masa,"Kabir anya kuwa karaɗin Yagana zai barka ka ji muryarta?, ka kalla tunda ta shigo gidan ta ke sababi ta hana kowa magantuwa, ga shi nan ma fita zasu yi da Mairon". bai san ya akai ya tsinci guntun murmushi a fuskarsa ba, murmushin da ya haifar da shan jinin jikin Kulu dan tasan bai yarda da maganar tata ba, amma sai taji yace,"naga ranar da Yagana zata shigo gidan nan bata yi sababi ba, shikenan ki nutsu kamin wani ya shigo banɗakin zan miki bayanin komai". gida biyu ta raba hankalinta, kaso ɗaya a tare da Kabiru kaso ɗaya a tare da Gwaggo wacca ke can ɗaki likita ke kanta jikinta yay tsanani. "kin san me ya faru?".yay mata tambayar yana miƙewa daga living room ya wuce zuwa bedroom, Abdrrahim ya bi bayansa da ido da son gano wani abun. Kulu tace,"a'a sai ka faɗa". yace,"ban taɓa ganin abinda ya tsoratani ba irin kamanninku ke da ƴar'uwarki, na tsorata ainun a lokacin da na shiga office ɗinta na sameta, tsoro fa bana wasa ba, saboda a tsammanina ma kece, Allah da iko yake, bayan kamarku hatta muryarku ma iri ɗaya ce". tai murmushin da ya sauka a iya leɓenta,"da kamanninmu da muryarmu iri ɗaya ne, amma kuma idan ka ganmu tare zaka iya banbance mu". "ta ya ya kenan?, to kin san Allah san da nai tozali da ita nayi zaton ko wasa kike da hankalina, ƙila kina so ki haɗa min gadar zare ne, san da na kiraki banyi magana ba ai dan na tabbatar da bake ɗin bace yasa na kira, gaskiya ga duk wanda yake da saurin firgita idan ya ganku tare to zai iya suma". tai gajeriyar dariya da cewa,"ka jira ka ganmu a taren tukunna, da kanka zaka zaƙuloni ba tare da rikicewar lissafi ba, akwai abin da ya banbantamu". yace,"to ai shikenan...kamar yanda kika sani nayi duk abin da kika ce, na shiga masarautar Al-Harar harma na sami ganawa da Mai Martaba, sannan naje Qatar ma amma shi ban sami shiga cikin masarrautar taku ba saboda tsaron da ke cikinta, amma naga Al-Hassan kuma naga Umm da idanuna, sannan na sami labarin Abi daga wurin limamin wani masallaci. da ka duka waɗannan ɓangarorin an sami saɓanin tunaninki akansu, daga ta kowanne ɓangare cike suke da kewarki da kuma cigiyarki da basu daina ba har yanzu, liman Shaik Albani ya shaida min ko a sallar asubahin yau sai da Me Martaba yay hawaye akan rashinki, yana adu'a iyakar adu'a akan idan har kina raye a duniya to ubangiji ya bayyana musu ke a duk inda kike...Umm ma akan yawan kukan rashinki ta kamu da matsalar ciwon ido...duk abun da ya riga ya faru ya riga ya faru, burinsu a yanzu na ki dawo garesu ne, fatan iyayenki ki dawo garesu su na raye ba bayan ta Allah ta kasance ba...kin san me?". tace,"a'a ina dai jinka". ta faɗa tana goge hawayen da ke sakko mata. "Hussainarki tana da kirki sosai, naje ma ta a matsayin ɗalibi me neman taimako har ta saka min hannu a takardar da na kai ma ta, kuma tun shigata office ɗinta har fitowata tana kirana ne da Ɗan'uwana. tace min tayi min taimakon dan Allah ne, amma tana buƙatar adu'a daga gareni akan Allah ya bayyana ƴar'uwarta da ta ɓata, na kuma yi ma ta alƙawarin hakan, ita ma kuma ina miki albishir ɗin tana nan cikin ƙoshin lafiya sai dai kallo ɗaya zaka yiwa fuskarta kasan tana ɗauke da wata damuwa a ƙasan ranta, bakinta kuma yana faɗin idan har ta mutu baku gana ba, ba zata yafewa kanta ba". tana tsayar da kukanta tace,"Kabir ta yi aure ne?". "a'a ba tayi ba, kuma a dalilin hakan tana ta fuskantar ƙalubale daga wurin mutane...ita kuma ta yiwa kanta alƙawaarin ba zata yi aure ba sai san da kika dawo". sai kuma ya ƙyalƙyale da dariyar da ke nuna yana cikin nishaɗi, tace da shi,"ni ina hawaye kai kana dariya, mene abin dariyar a cikin wannan yanayin Kabir?". "kiyi haƙuri, da aka ce ne ana cigiyarki within ƙasashen larabawan nan shi ne abin ya ban dariya, nace to dama taya za'ai a ganki alhalin kina ƙasar bichi ƙunshe a wannan gidan ƙasar tamu ba um ba umum sai kallo da ido". ita kanta bata san lokacin da dariya ta suɓuce ma ta ba, daga haka kuma tai masa godiya sosai sannan suka yi sallama da cewar idan Yagana ta tafi zata ƙara kiransa. sauke wayarta daga kunne ta jingina da ƙyauren banɗakin, tana son komawa cikin ahalinta, amma kuma tana tsoro saboda Hassanarta, Hassana zata rusa ma ta duk wani shiri da suka yi idan ta koma, allura ce zata tono garma idan ta koma, saboda Hassana Adamant(kaifi ɗaya) ce, idan ta kafe a abu babu wani mahaluƙi da yake sauya ra'ayinta ko da iyayenta ne, ta inda suka sami banbanci a hali kenan, shi yasa idan Mairo ta kafe a abu takan kalleta tayi murmushi aranta tace Babarki kika yo. *CardioCare Specialty Hospital, Abuja, Nigeria, A wannan ranar.* "to kinji dukkan abin da ya faru da ke tun daga ranar da kika ɓata".  Amadu ya kai ƙarshen zancen da wannan maganar, tun harbin bindigar nan da suka jiyo ta cikin gida, wanda Mom tai silarsa akan fusata Dad da tayi na korar Mairo, tsananin ɓacin ransa da zuciya ke sa shi aiwatar da komai acikin fushi ya ɗauki bindiga zai harbeta, Granny tai saurin ɗaga hannunsa sama ya harbi saman, amma da babu abunda zai hana shi alburushe Mom. kuma Joseph ya fito a rikice yana sanarwa da su Obi Mom tace in har Mairo bata bar gidan ba, to ko Dad bai koreta ba ta rantse da jesus sai ta kashe kanta. dalilin da ya sa suka rikice kenan Obi ya roƙi Amadu akan ya ɗau Mairo su bar gidan da hanzari, dan Mom tana faɗar abin da zata aiwatar ne ba abin da ke tsayawa a iyakar fatar bakinta ba, gwara Dad idan ya fusata ne yake aikata koma menene, amma da zarar Granny ta shiga lamarin shikenan. Obi da duk ya rikice yace da Amadu,"Friend ka ɗauketa ku tafi ko ba dan komai ba sai dan lafiyarta, kaga yanzu ta dawo cikin tunaninta, wannan rikicin zai iya haifar ma ta da wata matsalar, ko ta koma gidan jiya ko kuma wani abu makamancin hakan ya faru". ita Mairo a lokacinma duk a ruɗe ta ke, kuka take kawai tana kiran sunan Gwaggo da Baba da Ya Kabiru, dan tun san da ta ɗago kai taga ƙaton compound ɗin fayau sai shuken fulawowi ta ko'ina ta daɗa hargitsewa, tunaninta har yanzu bata bar wannan ƙaton jejin da suke ciki ba, ko da taga Amadu sunkuye a gabanta sai ta fashe da sabon kuka ta rungume shi, sai kuma ta fara complain ɗin ciwon da kanta keyi ma ta kamar zai rabe gida biyu. dalilin da yasa suka zarto da ita asibiti kenan, likitan da ya dubata ya tabbatar musu da cewar,"ehh ta dawo cikin ainihin tunaninta, amma duk da haka ba wai zata manta duka abubuwan da suka faru da ita a san da take cikin ciwon bane, a'a wasu abubuwan su na nan zaune akanta, kamar yaren da bakinta ya kama, karatu da kuma giftawar wasu tsirarrun al'amuran da ta sakasu a ranta sosai". abu ɗaya ya saka Amadu jin daɗi shi ne karatun da tayi, yana adu'ar Allah yasa karta manta da shi. tun a lokacin da aka cire ma ta drip, lokacin da ke nuna ta gama dawowa gaba ɗaya cikin tunaninta, tambayar da ta farayi masa itace,"Ya Amadu ya akai ka tsinto ni?, hanyar dajin fa da aka kaimu babu kowa sai mu kaɗai da muke rayuwa, har na fito titi ma na rasa wanda zai taimaka min". ya sauke numfashi yay mata nuni da Emanuel da ke tsaye shi ma hannayensa sarƙe a ƙirjinsa, zuciyarsa cike fal da tarin abubuwa mabanbanta, yace ma ta. "bani na tsintoki ba, wannan shi ne ya tsinto ki". ta ɗago ido ta dubi Emanuel, wani irin kallo ta ke masa mai kama da kamar ta san fuskarsa sai dai ba zata iya tunawa ba. "shi ne uban gidana, shi ya bigeki da mota ya ɗaukeki ya kawoki asibiti...". daga nan kuma ya shiga zayyane ma ta labarin duk abin da ya faru har zuwa gaɓar da ake kai yanzu, to amma da mamakinsa tun daga lokacin da ya soma maganar har san da ya kai aya idanunta ƙyar suke akan yatsun ƙafarta, hancinta da bakinta na fitar da hucin numfashi na zafi da raɗaɗin da ke tashi daga zuciyarta, babu wani motsi da ta ke kamar wadda ta suma. Amadu ya zago ta gabanta yaja kujera ya zauna, dubanta yake da irin yacce hawaye ke sintiri saman fuskarta, ya kamo hannunta ya riƙe tare da tambayarta,"mene kuma na kukan?, ki godewa Allah da ya kawoni a gaɓar da ta dace, da banzo ba me kike tunanin zai ƙara faruwa?". ta ɗago da ido ta kalle shi, acikin birkitacciyar hausarta irinta yare tace da shi,"kace har yanzu Gwaggona bata da lafiya?". ya gyaɗa ma ta kai,"tun a ranar da kika bar gida, sai dai ayau nasan ciwonta yazo ƙarshe, yau zata warke idan idanuwanta su kai tozali da ke". ta saki wani murmushi me ciwo, a ƙasan ranta tana adu'ar samun sauƙi ga Gwaggonta, amma hawayen nan masu zafi basu bar sintiri a saman fuskarta ba, hawayen jin ɗaci da zafi akan addinin kiristancin da ta rayu acikinsa tsawon watanni takwas, tsawon wata takwas bata sallah! tsawon wata takwas aka katangeta da bautawa ubangijinta da ya halicceta akan tafarkin Annabi Muhammadu(S.A.W), aka cusa ma ta wata aƙidar ƙazamin addini har tai rayuwa acikinsa, wannan shi ne abin da yafi damunta a halin da take ciki, shi yafi ma ta ciwo, zata so ace keta haddinta Kidnappers ɗin nan su kai akan ƙazamin addinin da ta shiga, zata so ace ta mutu ne akan rayuwa da tayi tare da ƙedararrun arna. zuciyarta tayi wani irin duka, ta lumshe idanuwanta ta mayar da kanta ga jikin gadon tare da rufe ido, tasa hannu ta dafe saitin da ƙahon zuciyarta yake, jin zuciyarta take kamar zata faso ƙirjin nata ta fito saboda irin masifeffen harbawa da ta ke, wata iriyar masifa ce ke azalzalarta akan azzaluman kafiran da suka raineta. wucewar wasu daƙiƙu ta buɗe ido a zafafe ta zubesu akan Emanuel da ke ma ta kallon sabuwar halitta, ta tsare shi da idanu kamar wacce ke kallon tv, a yanda take kallonsa gaba ɗaya masifa ce ke ƙara cin ranta, ita ba taimakonta yayi ba cutarta yayi, cutarwa mafi muni, da ya san irin abin da zuciyarta ke ayyana mata akansa da baici gaba da tsayuwa anan wurin ba, domin ji take kamar ta kashe shi, da niyyar taimakonta yayi da gaske ba zai biye son azzalumar zuciyarsa da babu ƙaunar Annabi Muhammadu acikinta ba ya shigar da ita cikin addininsu, da cigiyarta zai saka a duniya, duk da ita ba kowa bace, kuma ubanta ba kowan kowa bane, amma hakan ba zai sa a rasa wanda ya santa ba ko ya hana ta koma hannun iyayenta. shi kuma wannan kallon da ta ke masa sai yayi tunanin ko tana so tayi magana da shi ne, dan duk maganar da suka yi ita da Amadu bai fuskanci me suke cewa ba tunda da hausa ne suke maganar. dan haka yayo tattaki zuwa gabanta ya tsaya tare da buɗe baki yay ma ta sannu, a zafafe ta diro da ƙafafunta ƙasa ta daki ƙirjinsa da duka hannayenta biyu ta damƙi kwalar rigarsa. a cikin harshen turanci da tasan maganganunta zasu shiga kunnensa da kyau, acikin muryar da ta gaji da kuka take faɗin, "ka cuceni, ƙaton arne ka cuceni, kasa na rayu acikin ƙazanta, kasa na shiga addinin da ba a cikinsa ubangijina ya halicceni ba, kasa na bautawa wanda ba shi ne Allah ba, mugu azzalumi wallahi ba zan yafe maka ba...na tabbata san da ka tsintoni baka ga nayi maka da wadda ta tashi cikin ƙedararrun arna irinka ba, amma saboda zuciyarka azzaluma ce, saita ta ke gaskiyar da idanuwanka suke gani ɓaro ɓaro ka cusani cikin ƙazamin addininku...dama Gwaggona tace ku ɗin azzalumai ne macuta masu bin son zuciyarsu su cuci musulmi...ka riga ka gama dani, tsakanina da kai sai dai Allah ya isa, danni ba kuyi min taimakon komai ba, ba kuyi min gatan komai ba, kuma insha'Allahu ba zaka taɓa samun rabon hasken musulunci ba bare Allah ya yafe maka, haka zaka mutu kana mushiriki makomarka ta zama wutar jahannama". ta ƙarashe zancen tana ɗauke shi da zazzafan marin da ya kai fuskarsa ƙasa,"idan baka bar gabana na daina ganinka ba zan iya ɗaukan komai na rotsa maka, zan iya kai ka lahira, zuciyata na faɗa min na kasheka ne, na kasheka Emanuel". shi kuwa tsantsar mamaki da al'ajabi ne ya hanashi wani motsi sai bin ta da ido da yake, sam yanda ta ke kalamanta akansa ba haka suke ba, dai-dai da ƙwayar zarra ba shi da niyyar cutar da wani a rayuwarsa balle kuma ya cutar da wadda shi ne silar shigarta halin manta duniyarta ta baya, yes! yasan yayi laifi da bai shigar da cigiyarta ba. dukan tunaninsa kuma yay ket ya katse ganin ta rarumo wani ƙarfe tayo kansa da shi yay saurin kauce ma ta. "ka daina kallona a matsayin waccen matsiyacin sunan da ku ka raɗa min na Gift, ka kalle ni a Mairo, Mairo ƴar gidan Malam Adamu Me Faskare, Mairon da zata aiwatar da kowanne irin haɗari saboda kishin addininta". tayi maganar a san da ta kai hannu ta maƙuri wuyansa, tana kuma ƙoƙarin soka masa ƙarfen aciki, lokacin kuma Amadu ya dawo daga fitar da yayi waje dan karɓo wasu magunguna da aka rubuta ma ta. ya ƙaraso ciki da sauri yasa hannu yay cilli da ita gefe sannan ya wanketa da mari, ya hauta da faɗa yana balbaleta da rashin dacewar abinda ta ke yunƙurin aikatawa. "mahaukaciyr banza da wofi, muna farinciki da ganinki ashe ke da dabbanci kika dawo, to dan ubanki ki kashe shi ɗin kiga idan ke za'a barki da rai, ki gani idan shi zai wuce wuta". ta wani ja doguwar ajiyar zuciya ta yarfar da hannun Amadu da ke riƙe da ita, a zafafe ta shiga magana,"ya za'ai ya dake ni kuma kace ba zanyi kuka ba...tsawon fa watanni takwas kenan ya rabani da bautawa mahaliccina, ya dulmiyar da tsaftacceiyar duniyata zuwa tasu ƙazama, to na rantse Ya Amadu idan baka matsa ka bani wuri ba zan haɗa hukuncin har da kai". ya santa, ya san wace Mairo sarai, irin Gwaggonta ce masu zafin rai, masu aiwatar da abun da suka faɗa, masu tsayawa akan ra'ayinsu, shi kansa ya

Chapter 23 of 52