gama sabo da ita tukunna.
"wai da gaske ne shekaranjiya Suhail yazo miki gaisuwa?". maganar Adawiyya ta shigo cikin tunanin da nake, nace ma ta,"umm sun zo, ai yana da matuƙar kirki". da ace na kalli fuskarta a lokacin da zanga abin da ban taɓa gani a fuskarta ba a gama dani, to amma maganar da ta biyo bayan amsa ma ta ɗin da nayi shi yasa ni waigowa na dubeta babu shiri. "nima ya min gaisuwa, har yake ce min wai ai har fyaɗe ma anyi miki, ba ki ji yanda maganar ta sosa min rai ba har ƙwalla sai da nayi. kuma na tambaye shi aina yaji zancen yace ai maganar ma ta gama baza garin bichi, kuma ya za'ai ma nace masa ban san maganar da ta fito daga cikin gidanmu ba". ban san san da na haɗiye wani baƙin yawu a maƙoshina ba, wani babban abu ya tokare a ƙirjina, na tafi tunanin san da Ya Amadu ke zayyanawa su Baba labarin komai tun daga lokacin da Emanuel ya bugeni har lokacin da yaje gidan ya sameni, nima na basu labarin abin da ya faru damu a can dajin da aka kaimu, Inna Amarya ta dage akan akaini asibiti a dubani, muka je asibitin Malam Aminu kano akai min gwaje-gwaje, aka tabbatar musu da babu abin da ya taɓa budurcina, babu abin da ya sami lafiyata, sai a sannane kowa nutsuwarsa akaina ta gama dawowa.
sai dai a lokacin na shiga wani babban mamaki na tsintar rashin jin daɗin sakamakon a fuskar Inna Amarya, da har ta dage ta tubure akan sai an ƙara gwadawa ko kuma aje wani asibitin, a haka har saida muka je asibiti uku, duk sakamako ɗaya su ke badawa, alamun rashin jin daɗin bayanai ya fito ɓaro ɓaro a saman fuskarta da kuma yanda duk ta ke neman ta rikice, na shiga zuzzurfan tunani akan hakan, dan hatta a maganar da ta faɗa min a ranar uku me ɗaure kai ce, tana kuka ta ke ce min,"ta wani ɓangaren sai naji dama ba'a ganki ba Mairo, saboda ina gudun yanda mutane za su yi ta kallonki, da rabon Suwaiba ba zata shaƙi wannan takaicin ba". ina cikin yanayin da bana iya magana ma kwata kwata a lokacin, shi yasa ban sami damar ɓarar ma ta da abin da zuciyata ta kwararo min ba. haka kurum a yanzu sai nake jin Inna Amarya bata shigewa har cikin zuciyata da wasu sabbin ɗabi'un da nake ganinta da su, sai nake ganin kamar dama can ma tana riƙe dani ne saboda wata manufa tata, to amma duk san da baya ta hasko min cikin kaina, kyakykyawar zamantakewarsu da Gwaggona sai na ture duk wani kokonto a gefe, zuciyata ta koma tuna min wannan Inna Amaryar ce da ta ɗaukeni kamar ƴar cikinta, Inna Amaryar da kullum Gwaggona ke sawa albarka, Inna Amaryar da komai ta rakito na Mairo ne da Gwaggo, to akan me zuciyata zata fara wasi-wasin banza akanta?.
"ke tunanin me kike?". na kore mamakin da yay tsalle ya dira a saman fuskata na yacce na karancin maganar da Adawiyya ke faɗamin ƙarya ne, dan fuskarta da yanayin maganartata sun nuna hakan. na ƙaƙalo murmushi nace da ita,"ba komai". sai kuma ta ɗora zancen daga inda ta tsaya,"ni wallahi ma yanzu fargabata a gaba ta ke Mairo, idan aka zo maganar aurenki wannan soki burutsin ya shiga kunnen mijin da za ki aura...shi kansa Suhail ya faɗa min abin da baki sani ba, yace tuntuni yana sonki kuma aurenki zaiyi, yaso ma ace bayan mutuwar nan ayi maganar aurenku, to amma tun da yaji anyi miki fyaɗe yaji ba zai iya ba". nayi wani guntun murmushi me ma'anoni biyu nace da ita,"au Fyaɗenma har anyi min kenan?". tai wani murmushin da zan iya kiransa dana munafurci dan yayi kama da hakan, sannan tace.
"to Mairo abin da ake ta cewa kenan, kuma kowa ya yarda". "har da ke kenan?". da nuna alamar rashin gaskiya tace min,"haba in yarda da wannan banzar maganar, sai kace ban san wace ƴar'uwata ba, ni dake fa duk mun san cikin juna, idan gaske ne ai tuni kin faɗa min... ai shi yasa da ake ta cewa wannan hasken da kika yi na me ciki ne naji daɗi da Ya Amadu ya kora bayanin komai, kowa yasan gidan hutun kika faɗa ba hannun wahala ba shi yasa kikai kyan gani, wallahi ban san mun tara maƙiya ba sai a dawowar nan taki...ke baki ji yanda aketa baƙinciki da sauyin rayuwar da kika samu ba, harfa da masu zugani wai na fita harkarki tun da kin iya turanci ni ban iya ba...ni duk ba wannan ba, yanzu ta ya zamu goge baƙin fentin da mutane ke miki kallo da shi?".
na sake yin wani murmushin nace,"to ma dai ko me za ai ta faɗa ai ta faɗa, ni ba zai dameni ba, dama tun da na dawo na shiryawa jin waɗannan ƙananun maganganun, dan haka wanda bai faɗa ba ma ya faɗa, wanda yake faɗa kuma yaci gaba da faɗa ni ko a gefen yatsana". da alama maganar da nai ba tai ma ta daɗi ba, taso ace na tashi hankalina ne, dan tun dawowata na gama fahimtar sabuwar zuciyarta, Adawiyya ba irin ta da bace akaina, ta yanzu da banbanci, waccan pure ce, amma wannan cike ta ke da tsatsa.
na sauke tunkuyar daga kan murhu ita kuma ta kashe murhun, sannan muka wuce ɗakin Yagana. ta ke min naganar Nafi'u ɗan gidan me unguwa da ya zo da maganar aurena, tana roƙona akan na yarda na amince.
"shi kuwa kamar wanda bai san mutuwa ba, sai kace gidanmu neman kai da ni suke, daga mutuwar uwata sai maganar aure, ai ya bari na huce zafin mutuwar tukunna ya tunkare ni yaji idanma zan amince masa, amma ba kai tsaye ya kai maganar wurin manya ba. ko da yake dama yanzu ni sai abin da na dinga gani, tun da jajirtacciyar mahaifiyata me tsayin daka akaina she is no more, i have to be patient akan duk wasu challengies da zan fuskanta". na faɗa ina yafa mayafi ina cewa da Adawiyya ta tashi mu tafi gida, yau gaba ɗaya ban leƙa ba. Yagana ta zabgan harara da jan ƙaramin tsaki. "ai na faɗa miki ki daina samin ɗan banzan turacin naku a cikin magana tun da ba iya shi nayi ba. ke ba ki san ma ni yanzu wannan hausar taki ma ba sonta nake ba, ba yanda na iya ne kawai, kina hausa kaman cin kashi... da kin yi zance kaɗan sai ki fara za da mo da yo, haka kawai ki dinga ƙunshe min kai".
murmushi kawai nayi na nufi wajen da nayi sallah ɗazu zan ɗauke ƙaramin ƙur'anin dana karanta, sai ce min tayi,"ki ce ash hadu". a dole tasa nayi ƴar ƙaramar dariya, haka ta ke min yanzu ko alwala zanyi sai tace ki faɗi kalmar shiga musulunci.
saboda na ƙara kunnota nace,"Don't worry Hajiya Yagana i will say it". aiko kamar jira ta ke na rufe baki taja tsaki, ta hau sababi, ta bani dariya sose, da yake yanzu gaba ɗaya ma da turanci muke magana da Ya Kabiru, to idan zamu yi zaman awa guda agabanta muna magana, tai ta jan tsaki tana mitar an isheta da ɗan banzan yaren da bana uwa da uba ba.
a hanya muna tafiya Adawiyya ke ƙarasa min zancen da ba ta ida ba a ɗazu, wai Suhail yace shi yana so ya auri wadda ta fito daga gidanmu, kuma gashi ba zai iya aurena ba, saboda haka idan har ita ta amince masa zai aureta.
ba ƙaramin daɗi naji ba da jin zancen, har na ɗora hannuna a kafaɗarta ina zolayarta da cewa,"wa ya ga gimbiya Adawiyya...dilla ki amince masa mu raƙarƙashe, kinga shikenan mu ma mun zama jinin sarauta".
tai min wani banzan kallo tana cewa,"Allah raba gatari da saran shuka, me zanyi da mutum me ɗaukar maganar mutane". nayi murmushi ina kama hannunta nace,"kema dai Adawiyya ba ki so gaskiya ba, magana ta Allah who ever gets in to the situation am in dole mutane su zarge shi, balle ni da nake mace, shi yasa nace miki na toshe kunne na da duk abinda mutane zasu ce akaina...amma dan Allah ki bar batun wai ba za ki amincewa aurensa ba, Suhail mutumin ƙwarai ne, kuma gidansu ma mutanen ƙwarai".
kamar ba zata ce min komai ba, sai kuma ta numfasa tace,"naji". da haka muka ƙarasa gida inata tsokanarta, ita kuma sai ciccin magani ta ke.
ɗakin Gwaggo da ya koma ɗakin Kulu a yanzu na shiga, tana zaune da hisnul muslim a hannu tana karantawa, nayi sallama na shiga ta amsa min tana hararata. ina murmushin da ya bayyanar da dukkan haƙorana na ƙarasa gareta ina rugumeta nace,"am sorry my second Gwaggo, Allah yau aiki mukaiwa Yagana shi yasa ba ki kalleni ba tun safe". duk da haka taƙi ɗago da kai ita alalla tana fushi, sai na karɓe hisnul muslim ɗin na ajiye shi na kwantar da kaina bisa cinyarta, na shagwaɓe fuska ina kama kunnena nace,"Am so sorry, Allah nima tun ɗazu hankalina na kanki". sai tayi murmushi tana kallona, ta shafo kumatuna tana cewa,"ai idan nayi fushi da ke ko duka jama'ar kano za ki tara su tayaki bani haƙuri ba zan haƙura ba...shikenan haka akeyi fisabilillahi sai kusa na ƙara zama marainiya, ita Basma na ma ta uzurin makaranta, amma ke kin tattara kin gudu wurin Yagana kin barni ni ɗaya a ɗaki kamar mayya, bayan sarai kin san bani da kowa a gidan nan yanzu sai ke, ke kaɗai nake gani naji daɗi, kuma kece ke ɗebin kewar Yaya, dan Allah karki kuma yini baki zo na ganki naji sanyi a zuciyata ba, wallah bana samun nutsuwa idan ba kya cikin gidan nan".
nayi wani fari da ido nace,"to Gwaggo 2". sai taja hancina tana gajeriyar dariya, sannan muka shiga hira, tana bani labarin taji Baba ɗazu yana faɗa akan ba zata bar gidan nan ba, amma bata san a cikin Inna Amarya da Inna Zulai wa yaje masa da zancen ba, wai sun gaji da zama da mahaukaciya tunda dama dan Gwaggo ta ke zaune to yanzu saita bar gidan tun da babu Gwaggon, Baban yace karsu ƙara ce ma ta mahaukaciya, da lafiyarta, zanen ƙaddara ne ya maida ita hakan, kuma zamanta a gidan nan babu fashi, sai dai idan bayan ransa.
tausayinta ya kamani, nayi ɗan jim kafin nace,"to kema Kulu ki koma gidanku mana in dai kin san inda ƴan'uwanki suke". sai naga tayi murmushi me kama da ciwo kan tace,"lokacin hakan yana tunkaro ni, na kusa nan bada jimawa ba".
Muryar Ya Kabiru ta shiga kunnuwanmu a sanda ya ɗaga labulen ɗakin, muka kai dubanmu gare shi, shi ma na lura yanzu yasan Kulu na magana, tun da bata shayin yi agabansa kuma shi ma babu mamakin hakan a tare da shi, muryata a ƙasa nace,"da ɗaya bayan ɗaya kowa na gidan nan sai ya gano gaskiyar kina magana". ƙaramar dariya ta rakani, ni kuma na miƙe na isa bakin ƙofar da Ya Kabiru ke tsaye, na miƙa hannu na amsa ledar kaza da youguht ɗin da ya siyo min, na ɗago kai zan masa godiya ya matse hancina yaja, nai ƴar ƙara ina kama hannunsa zan cire daga hancin nawa.
sai ya kawo goshinsa ya ɗan doki nawa goshin,"kin wani ƙunshe a gidan Yagana, kin bar mutane anan da kewarki". nace da shi,"to ba sai ka bi sahuna ba Ya Kabiru, ai sai kaje kaga ko lafiya tun da kasan safiya nayi nake tahowa nan". yace,"tabɗi! Yaganar nace min me hannun ɓera zanje gidanta, ai ba zan sake komawa ba saita neme ni da kanta".
na ƙyalƙyale da dariya na juya ina bawa Kulu labarin diramar Ya Kabiru da Yagana, ya siyo ma ta dambun nama ya kai ma ta ya ɗiba sai cewa tai yaje da halinsa, ita bata san hannun ɓera gare shi ba da bata ce ya siyo ma ta ba, amma ai gwara da ya nuna ma ta halin ɓerayen da yake da shi, gaba ta dinga kaffa-kaffa da kayanta idan ya shigo gidan, yanzuma dan Allah ya tashi ya fita kafin ta nemi kayan jama'ar da aka bata ajiya ta rasa, ya barta da tsilla tsilla, ita duk ta ƙagu ma ya koma ƙauyen da ya fito.
Da daddare bayan anyi magriba ina shirin tafiya gidan Yagana Baba yace na dakata zaiyi magana da ni. a ɗakinsa na same shi Inna Amarya na zaune a gefensa, sai Ya Amadu shi ma daga gefe, na ƙarasa ciki na zauna kusa da Inna Amarya, gabana ya shiga dukan ukukun dan na san wannan zaman ba ɗaya ba, musamman dana ji Baba yace,"zauna sosai Mairo, zaman naki ne...dukkanmu da kika gamu anan muna zaune ne saboda ke". na ɗago duk na dubesu kafin na mayar da kaina ƙasa naji shi da maganar da banyi tsammani ba.
"maganar aurenki ce Mairo...".
___________________________
*Assalamu alaikum
jama'a na tallatamuku hajar mu ta online/offline business dina wanda zanrin ga sayar muku da data ta mtn a sassaukan farashi Kamar haka*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Whatsapp OR
Call 08066268951*
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Shafin Sadaukarwa Ne Ga Duk Makarancin Wannan Littafi, Alkhairin Allah Ya Isa Gareku A Duk Inda Ku ke._
*30)*
naji zuciyata ta motsa, ba kalmar auren da Baba ya ambata bace ta razana ni, illa sunan mutumin da ya ke ikirarin zan aura shi ya firgitani, mijina dai! hakan yasa na ɗago na dube shi a kiɗime jikina har yana shaking, mamakin Baba yay tsalle daga zuciyata ya fito ya dira a saman fuskata ƙarara.
tunani na ke anya kuwa wannan Babana ne ba wani Baban aka sauya min ba?, zuciyata ta hau tantama akan anya ƙwaƙwalwar Baba bata samu motsuwa ba kuwa?, anya Baba bai sha abin da ya gusar da hankalinsa da tunaninsa ba?, sai dai duka amsar tambayar saɓanin tunanina su ke, domin kuwa naga hakan a saman fuskar Baba, Babana ne! kuma ragagas yake, babu alamar ciwo ko gushewar hankali tare da shi.
to amma a yau me yasa ya ke magana irin ta marasa lissafi?, naiwa kaina tambayar da bani da amsarta, zuciyata tayi wani ƙundun bala ta cure wuri guda, kafin sunan da ya ambata ya haska acikin idona da kyau, ya kuma zana min hoton mutumin da kyau, yana tsaye a gabana, Emanuel! Emanuel dai!, kafirin nan da ba ya sallah, zindiƙin arnan da babu hasken musulunci a tare da shi, mutumin da yay sanadin halin da na shiga, mutumin da har da silarsa a mutuwar Gwaggona, mutumin da akaf duniya babu wanda naƙi jini sama da shi, Allah ya sani ko kaɗan zuciyata bata yinsa, mutumin da zuciyata ta ƙudurta duk ranar da tayi ido huɗu da shi sai na ɗauki fansar mutuwar Gwaggona akansa.
ai sai bayan mutuwar Gwaggona na yarda da maganarta na cewar Arna mugwaye ne macuta masu son kansu, ashe tafi Baba hange shi da ya ke cewa ai kamar yanda Ubangiji ke fitar da rayayye a cikin matacce, kuma ya fitar da mutanen kirki daga azzalumai a cikin musulmai, to hakama kafiran, su ma ana samun na ƙwarai acikinsu, amma ita tata zuciyar taƙi amsar gaskiyar hakan.
lallai banga laifinta ba akan ƙinsu da ta ke, ashe gudun da ta ke kenan kar su dulmiyar da Ya Amadu cikin ƙazamin addininsu, da rabon ba zata shaƙi takaicin da bata taɓa kawo lissafinsa akanta ba ne, lallai mutuwa ma Rahma ce, da Allah kaɗai yasan halin da Gwaggona zata shiga idan taji cewar na rayu cikin kafirai kuma na ginu akan addininsu.
na dubi inda Inna Amarya ke zaune inda ganinta ya maye min gurbinta da Gwaggona, ƙwalla ta taru a idona, Allah ya jiƙanki Mahaifiyata, da ace kina raye tabbas wannan zaman ba za'ayi shi ba, na rufe idanuna da ke min zafi, bayan dukkanin tarin ƙiyayyar da Baba yasan Gwaggona na yiwa su Obi, da wadda ni kaina nake musu a ynzu amma a hakan yake ambatar zai aura min shi, wai zai zama mijina, ta ya ya hakan zata kasance kenan bayan akwai haramcin aure ma a tsakaninmu?, amma tun a san da na kalli ƙwayar idon Baba na gano abin da ya faɗa har cikin zuciyarsa yake, kuma auren da nake tunanin ba zai yiwu ba ƙwayar idonsa na shaida min zai tabbata.
ci gaban maganarsa ta katse dukkan tunanin da ya kutsa ta cikin kaina, na tattare komai na ture gefe, naci gaba da sauraron maganar da yake yi.
"a cikin hankalina nake Mairo, kuma ki ture zargin da zuciyarki ta kawo miki akan ko kwaɗayin abin duniya ne yasa zan aurar da ke ga kafirin mutumin da addininmu bai halatta aurenku ba, da ilimina, nasan abinda nake...amma ina ƙara faɗa miki Emanuel shi na zaɓa miki a matsayin mijin da za ki aura idan har na isa da ke, kuma nan kusa bada jimawa ba, sai dai ko kaɗan karki zargi cewar na nemi alfarmar aurenki a wajensa ne, ko ɗaya ba haka bane, shi da kansa yazo ya sameni da maganar aurenki, kuma hatta mahaifinsa ma yazo ya sameni. su ɗin mutanen kirki ne, masu ilimi kuma manya wanda ƙasa ke ji da su. tun ranar da Gwaggonki ta mutu yaron nan ke sintirin zuwa gidan nan yana mana ta'aziyya, ko kin san da Amadu ya sanar masa da mutuwar a daren ranar ya sauka a garin nan, kuma da Amadu ya shaida masa yanda muke gudanar da zaman makoki, haka ya kama hotel ya zauna a can shi ma yace har sai an gama zama sannan zai koma gida. a washe garin sadaƙar ɗaya yaron nan da ya tashi zuwa sai ganinsa mu kai da lodin kayan abinci, shinkafa babu ƴar hausa buhu goma haka ya ajiye ƴar gwamnati, banda galolin mai da duk sauran kayan abinci dai da kika san anaci, ruwan jarka na faro kuwa da kika ga kowa nasha mota guda haka yasa aka ajiye a ƙofar gidan nan, ya ɗauki maƙudan kuɗi naira dubu ɗari da hamsin ya bawa Amadu yace a dinga cefane da su, na karɓa nace masa a'a ba zamu karɓa ba, ko waɗancan ma dan ya riga ya kawo ne ba tare da yayi shawara damu ba, kuma ba'a maida hannun kyauta baya, amma da duka za'a haɗa a ba shi, dan haka ya riƙe kuɗinsa an gode. duk yanda nayi da shi ya karɓa yaƙi yace shi bai bayar dan wai mu yi bikin mutuwa irin nasu ba, ya tambaya ne idan musulmi ya mutu kyautar me ake musu akace ba'a kyauta sai dai a bada sadaƙa, dan haka shi duk abunda ya bayar ya bayar da shi sadaƙa ne, kuma wannan kuɗin idanma ba zamu riƙe ba ayiwa Gwaggo sadaƙa da su. ko da yaushe yaron nan yana tare damu a wurin zaman makoki tun daga safe har dare sannan yake mana sallama, tashi sallah ne kawai yake rabamu da shi, kuma haka yayta wannan zaman har akai sadaƙar bakwai, a kullum tambayata yake wace iriyar adu'a muke yiwa mamacinmu, na faɗa masa, kuma tun daga wannan rana kullum sai yayi kyawawan adu'oi masu tarin yawa wa Gwaggonki, ranar sadaƙar bakwai har kuka sai da ya sakani, yace yana tausaya miki ne kina ƴar ƙarama da ke kin rasa mahaifiyarki, kuma an faɗa masa dalilin ciwonta har da silar rashinki a kusa da ita, kuma ba kowa yay sanadin tsayin ciwon nata ba illa shi, shi ma yana da babban kamaso a rasa mahaifiyarki da kika yi, dan Allah na roƙeki ki yafe masa, duk abin da yay bai aikata miki da son zuciya ba, sai ma dan gudun kada ki tagayyara idan yasa cigiyarki, kidnapers za su iya yin ƙarya su ƙarɓeki. amma ki yafe masa, yana kwatantawa ne akansa ranar da aka ce shi ma babu tasa uwar ko uban ya zai yi. ya daɗe a ranar da zai tafi yana cewa dan Allah nace kiyi haƙuri, har Amadu yace ya tsaya a kiraki yace a'a ace yana miki ta'aziyya kawai, ba zai iya haɗa ido da ke ba dan aduniyarki babu wanda kika tsana sama da shi yanzu, kuma za ki iya kashe shi dan kin faɗa masa hakan.
bayan wannan a washe gari sai gashi ya turo min mahaifinsa da maganar wai yana so ya aureki, mahaifinsa ya rantse min yay alƙawarin ba za su cutar da ke ba, kuma ba zasu rabaki da addininki ba, banbancin addini ba zai sa su ƙyamaceki ba, na faɗa masa cewar addininmu ya haramta auren musulma mace da kuma namiji kafiri, dan haka ba zan iya bawa ɗansa auren ƴata ba. ya tafi cikin rashin jin daɗi, amma a washe gari sai ga Emanuel ɗin da kansa yazo, a jiya kenan, har hawaye sai dai yay min akan magiyar aurenki, ban yarda da irin tsananin son da yake ikirarin yana miki har cikin zuciyarsa ba sai da na kalli ƙwayar idonsa, ya faɗa min soyayyar ba wai ta yanzu bace, tun ta sanda ya haɗu da ke ne, kuma inda yayi niyyar cutar da ke da tuni ya cutar da ke, dan zuciyarsa ta daɗe tana ingizashi akan ya aikata wasu abubuwa marasa kyau a gareki amma ya dinƙa kwaɓar zuciyarsa saboda son da yake miki na gaskiya ne. sai dai duk ta yanda naso na fahimtar da shi rashin yiwuwar abin ya gaza fahimtata, yace shi kawai bana so na basa ke ne, har wata ƴar'uwarsa ya kira min a waya dan naji wace ita, arniya ce ita amma mijinta musulmi ne, saboda haka idan har auren waɗan can zai kasance kuma na ku zai kasance. da ƙyar da ƙyar yaron nan ya fahimceni daga ƙarshe, san da ya miƙe ya tafi ba kiji yanda zuciyata ta tsinke ba, da ace addininmu bai haramta auren Kafiri da Musulma ba da babu abin da zai hanani aura masa ke, ba don komai ba sai dan karamcinsa a garemu, mutumin da ya zauna tsawon sati guda acikinmu ba ƙyamatarmu talakawa ne ballantana addininmu, abin da muka ci shi yake ci, kuma kullum adu'a yake ga mamacinmu, ta ya zaka ƙi karɓar buƙatarsa ta alkhairi a gareka?.
ba wannan ba Mairo, wallahi ban rufa daga tunanin da na faɗa ba sai ga yaron nan ya dawo yana shaida min idan har zan aura masa ke to tabbas zai musulunta, nace masa a'a ni ban yarda ba, sai dai ya musulunta saboda Allah ba dan ke ba, yay min rantsuwa iya rantsuwa da gaske yake yi zai shiga addininmu idan har zai sameki, saboda ba zai iya rayuwa ba idan har babu ke a tare da shi, nace ni ba zan mallaka masa ƴata ba saboda zai musulunta dan ita, nafi so ya musulunta saboda Allah, ni kuma idan har ya musulunta dan Allah nayi masa alƙawarin zan aura masa ke a washe garin ranar, ta yanda zuciyarsa ba zata sauya shawara ba anan gaba bayan ya aure kin. bai ƙara cewa da ni komai ba yay shiru, anan bakin masallaci muka bar shi muka shiga sallar magriba, har muka fito yana nan a zaune, ya kira Amadu yace yazo ya kai shi wajen limamin masallaci, Amadu shi yay masa jagoranci zuwa gaban Malam Liman, Liman da kansa yace in har da gaske wurinsa yazo to a shigo da shi cikin masallacin, ya zube gwiwonsa a gaban Liman ɗin, ya duƙar da kansa ƙasa, ya shaida masa cewa yana so ya shiga cikin addinin musulunci, ba wai don saboda wani ya tursasa shi ba, ko kuma don bin umarnin wani, sai don saboda ra'ayin kansa, ra'ayin zuciyarsa, saboda kwaɗayin wannan ni'imar da hasken da Amadu ya jima yana masa nasiha akansu. saboda haka a faɗa masa adadin kuɗin da zai biya ko da ya kai nawa ne, idan ma da abin da a keso bayan kuɗi a faɗa masa duka zai bayar, shi ma yana so ayau ya shiga cikin wannan addinin da tun wayonsa yaji ana faɗin shi ne addinin gaskiya. Mairo bayan ubangiji, sannan kuma da Liman da babu shi anan, daga Innarki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 52