lapton a gaba da zummar yin aiki sai yaji ya kasa, komai nema yake tsaya masa cak, ya saka duka hannayensa a sumar kansa ya yamutsa sannan yasa ƙafa ya ture table ɗin da ke gabansa, kamin nan ya kwanta akan gadon.
tun ranar da ya musulunta yake jinsa tamkar wani sabon halitta, tamkar ba Emanuel ɗin da yake a baya ba, kuma tun wannan ranar yake jinsa da wata iriyar natsuwar ruhi da kwanciyar hankali a tare da shi, ga kuma wani farin ciki na babu dalili da yake yini a cikinsa, komai nasa sakayau ba kamar da ba da yake jinsa da nauyi. ko a jiya da su kai waya da Amadu abun da yace masa,"Sir ka kasance me godiya ga Allah da wannan ni'ima da yay maka, ka zama me gode masa da ya sa ka rabauta, ka gode masa da ya kuɓutar da kai daga duhu zuwa haske, ka ci gaba da roƙonsa akan ya tabbatar da kai acikin addinin da yake na gaskiya ba tare da wannan ni'imar ta yanke maka ba har ƙarshen numfashi".
a yauma abin da ya haddasa masa rashin nutsuwar nan da yake da faɗuwar gaba ta yanda zai tunkari iyayensa da maganar cewar ya musulunta, da waɗanna kalamai zai fahimtar da su cewar a yanzu shi ne akan hanyar dai-dai su kuma su na kan hanyar ɓata, shi kuma a gaskiya ya gaji da wannan ɓoye-ɓoyen da bai saba ba ko kaɗan...ga maganar Malam da yay masa ayau na zancen aurensa da ɗiyarsa, sai kawai ya rumtse idanunsa ya shiga karanto adu'ar da ya gama haddarta a jiya, wadda ya yini a masallaci wani mutum na biya masa ita, dan Amadu ne ya turo masa ita ta waya shi ne shi kuma da yaje sallah sai ya nemi wani yay masa bitarsa. kuma bai manta ba da faɗin Malam da ke ce masa,"duk lokacin da ka ji wani al'amari ya cunkushe maka, ka kasa nemawa kanka mafita, to ka karanta Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan. ma'ana Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauƙi". tashi yayi yay azamar shiryawa ya suri keys ɗinsa ya fita, kowa na zaune a parlo a san da ya sauko ƙasan, bai kula kowa ba ya fice sai raka shi da idanuwa da suka yi da mamakin sauyawar da yay cikin kwanakin nan.
****
kamar yanda Kulu bata so fitowata ba, haka nima ba'a son raina na fito ba, dan har cewa tayi zata je taiwa Baba magana nace babu ruwanta karta shiga lamarin da bai shafeta ba, na riga na amince ba auren dole za'ai min ba.
a zaure muka haɗu da Adawiyya itama zata fita ta tambayeni,"ina za ki da tsakar rana haka?". a harzuƙe nace da ita,"ki shaƙeni sai na faɗa miki". "Allah ba ki haƙuri". ta faɗa tana kyaɓe baki, na harareta da faɗin,"da haƙurin ta mutu sadaƙar nawa kika bani, ni kaucen a hanya ko na bi ta kanki wallahi". babu shiri ta kauce na wuce.
daga gaban gidanmu na hango arniyar motar tasa baƙa sai sheƙi ta ke, na ƙarasa inata faman ɓata raina kamar na kurma ihu. da kansa ya buɗe min wai na shigo ciki, ni kuwa nace babu inda zan shigo ni ba ƴar iska bace, idan yana iya fitowa ya fito, in bai iyawa na koma becouse i have alot to do. murmushi yay sannan ya buɗe ya zago daga ɓangarensa zuwa inda na ke, da yake da yamma ne idon mutane duk a kanmu, kasancewar an daddawo daga kasuwa, kuma duk banji daɗin tsayuwar ba, na haɗiye haushina nace da shi,"faɗi da sauri". oho na manta ba bahaushe bane, sai da naji yay shiru na dube shi ina zabga masa harara sannan na tuna, dan haka cikin yaren da zai gane me nake nufi nace,"yau kuma ina sarƙan cross ɗin?". sai yay murmushi yace min,"ina Al-Mustapha ina sarƙan cross, sai kace wata Gift a baya".ya faɗa da sigar tsokana, dan haka na jiyo ina ƙara haɗe fuska cike da tsiwa nace,"ni kar ka ƙara dangantani da wani Gift idan ba haka ba kuwa zanyi maka ɓarin mahaukaciya, wa ya san ma da zuciyar da ka bar ƙazamin addinin naku, Gaskiyar Yagana ma da tace Uwar bari ka gani". a wannan karan kam siririyar dariya yayi kan yace,"ai ba saboda wani na karɓi musuluncin balle asa naji haushi na sauya ra'ayi...ba wannan ya kawoni ba, zuwa nayi ki bani shawara saboda ke ɗin me kifin basira ce". nace,"aikuwa dai kayi farar dabara, dan babu abin da zai sa na bika na zauna acikin arna, saboda haka ka san da cewa in an ɗaura a gidanmu zanci gaba da zama, idan haɗuwarmu da kai ta zama dole ma ke gaisawa ta waya". "idan baki bar min tsiwa ba zan cafe wannan ƙaramin bakin nan naita kissing ɗinsa har sai jamaa sun taru a wurin nan". na sa ke ɓalla masa harara nace,"iskanci dama ai ba baƙonka bane". yana kallona da wani makirin murmushi yace, "nan gaba kaɗan ai za ki so iskancin kema". wani haushinsa ya tuƙeni, dan haka na bar masa wajen na ɗauki hanyar gidan Yagana, saboda kar ma na koma gida Baba ya saito ni, yau gaba ɗaya ma sallah ce kawai ta ke fito da shi waje, gidan kuma ba kowa Kulu ce kawai, Innata da Inna Zulai duk sunje anguwa yara kuwa duk sun tafi makaranta, sai Sadiya da Adawiyya da ban san inda tsinannan yawonsu ya kaɗasu ba.
ban dawo gida ba sai bayan an idar da sallar magriba, har lokacin gidan shiru babu kowa, Kulu ma ba ta ɗaki sai nayi zaton ko banɗaki ta shiga. dan haka na wuce ɗakin Baba sai dai ina zuwa ƙofar ɗakin na dakata da shiga a sanda naji murya Baba sama-sama kamar yana faɗa.
naja burgi na tsaya jin ya ambaci sunan Kulu yana cewa,"Hauwa wannan hukuncin da kika yanke kan Mairo da Kabiru babu inda zai je, ba kuma shi ne samun mafitarki ba, illa ƙara dagula lissafin komai, abin da ake gudu kuma yazo ya faru, saboda haka ki kauda ido ki bari na aura mata Al-Mustapha kawai, zuwa wannan lokacin da bayan na mutu sirrin komai zai bayyana zata fi samun sauƙi, tun da da aure a kanta, akan wannan lokacin da take ciki...banda an sami tsaiko daga ɓangaren Al-Muspha da tuni tun azahar na jima da ɗaura musu aure".
cikin matsanancin kuka da muryar da ta fara dakushewa Kulu tace,"Malam ni kaina na gaji da ɓoye wannan sirrin, duk da cewar har yanzu bana so Hussaina ta san gaskiyar komai dan bana so rayuwarta ta ƙuntata, amma bani da yanda zanyi, ita gaskiya duk inda aka kai ga ɓoyeta watarana sai ta bayyana kanta...kayi haƙuri ban taɓa ƙin maganarku ba, amma ba zan iya bari Kabiru ya rasata ba, ba zan iya zuba ido inaji ina gani a ɗaura ma ta aure da wani ba bada Kabir ba, na riga nayi masa alƙawarin aurenta, ba kuma zan iya saɓa wannan alƙawarin ba". sai tayi shiru, Baba kuma ya ɗora da faɗin,"to ni ban yarda ba, ban kuma amince ba in har na isa kamar yanda kike cewa, in har ina da iko akan ƴarki to ban amince da wannan alƙawarin naki ba, ki ɓalla shi. dan sai bayan raina kaɗai na yarda Mairo tasan cewar ita shegiya ce, ta san da cewar an samar da ita ta hanyar zina ne bada aure ba, ta kuma san cewar ni da Marigayiya bamu ne iyayenta ba. lokacin da bana nunfashi kaɗai na yarda Mairo tasan ita ƴar gaba da fatiha ce ita, amma ba yanzu da na ke raye ba, saboda haka batun aurenta da Kabiru da kike magana na soke shi, insha'Allah idan Allah ya bamu tsawon rai gobe zan ɗaura ma ta aure da Al-Mustapha, in yaso daga baya yasan yacca yay ya sanar da iyayen nasa". sai kuma ta ƙara fashewa da kukan da ya fi na ɗazu, a yanzu kuwa muryarta ta gama dakushewa, domin da ƙyar ta ke fita,"a'a Malam, aurenta da wanda kake ikirarin zaka bata shi ma kuskure ne. idan har da gaske ɗan gidan Major Tosin ne to babu aure a tsakaninsu, domin Major shi ne silar zuwansu duniya ta ƙazamar hanya, hanyar da ba aure".
sai naja ƙafata da naji ta daskare, na jingina da jikin garun ƙofar ɗakin, gaba ɗaya kunnuwana sun kasa yarda da abin da suka ji, na sulale na zube a ƙasa. muryar Kulu kuma naci gaba da shiga kunnena,"Major Tosin Afafa shi ne mahaifinta, dattijun da babu imani a cikin zuciyarsa, shi ne silar komai Malam, shi ya zama mafarin koma...na shiga uku ni Akila, ban san ta yanda Hussaina zata karɓi cewar ita ɗin shegiya bace". tamkar saukar tsawa akan dutse cikin duhun dare, tamkar kaɗawar guguwa acikin iska, haka nake jin maganar acikin kaina. _Mairo shegiya ce, Mairo ƴar gaba da fatiha ce, Mairo an haifeta ne ta hanyar zina, kuma wani kafiri can daban shi ne ubana, ni Mairo!._ sai kawai na tsinci kaina da ƙwalla wata uwar ƙara tare da buga kaina ajikin garu, domin na farka daga wannan mummunan mafarkin mara kai mara gindi.
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
_Shafin Gaba Ɗaya Sadaukarwa Ne Ga Masu Sharing Wannan Book Ɗin, Alkhairin Allah ya isa gareku._
*32)*
dukkan wata ma'ana ta tashin hankalin ta gaba fitowa ajikina, a yau ɗaya rayuwata ta sauya, tabbas idan aka tambayeni tarihin rayuwata da wannan shafin zan fara, ta kansa zan soma. yanayin da nake ciki da ni da wanda aka tsamo daga cikin teku bamu da maraba a wajen jiƙewa illa shi ruwa ne ya jiƙa shi, ni kuma zufa ce ta jiƙani sharkaf. tun da na daki kaina da bango naji zafin a jikina na tabbatar da abun da kunnuwana suka ji ba'a mafarki bane, zahiri ne. na koma kamar wadda aka sassaƙa aka dasa a ƙofar ɗakin Baba, babu motsi sai numfashin da shi ma na ke zuƙo shi da ƙyar, idanuna sun kaɗa sunyi jajur. murfayen idanuna su ka haɗe su ka rufe su na fatan daga haka shikenan ba za su ƙara buɗewa ba su gansu a wannan duniyar ba.
hoton rayuwata gaba ɗaya ya shiga haskawa cikin idona, yayin da agefe ɗaya maganar Kulu ke ci gaba da shiga cikin kunnuwana.
"Malam in har dai wannan Sojan da ƙasa ke ji da shi ne Major Tosin Afafa to wallah ba zan maka ƙarya ba shi ne mahaifinta, Malam shi ya yaudareni da cewar zai musulunta bayan ya gama dasa soyayyarsa a zuciyata at long last yazo ya yaudareni yaci amanata yay min ciki, a gabansa na haifesu, akan idonsa, da shi aka karɓi haihuwarsu, amma saboda zalunci bayan zuwansu duniya yace ba zai iya karɓarsu ba. shi ne har ya ɗaukesu wai zai kai gidan marayu suyi rayuwarsu a can gudun kar sunansa ya ɓaci, jin hakan yasa na ƙanƙame Hussaina da ke hannuna dan Hassan na hannunsa a lokacin, nace idan ya rabani da namijin ba zai rabani da macen ba, ba zai yiwu duka su tashi a tutar kafirci ba, bai bi ta kaina ba, balle ya tausayawa halin da nake ciki yasa ƙafa ya wuce ya barni. shi ne har ku ka zo ku ka sameni a wannan asibitin, Malam Hauwa ba shi ne sunana ba Akila shi ne asalin sunana, ni ba ƴar nigeria bace ƴar ƙasar Qatar ce, mahaifina shi ne sarkin ƙasar.
yanzu ban san ya zanyi ba, ban san da wani irin kalami zan faɗawa Hussaina ta yarda cewar bada son raina na haifesu ta wannan hanyar ba".
kukan da ya ci ƙarfinta yay dai-dai da ɗaukewar wuta a zuciyata, sai kuma wasu hawaye na daban masu zafi suka shiga sauko min, kukan da ke riƙe a bakina ya suɓuce, bakina kawai naji yana furta,"Ya Allah kabi min hakkina akan Akila da Tosin, ba zan taɓa yafe musu ba, dan sun cutar da ni...Allah ka ɗauki raina na huta da rayuwa ma gaba ɗaya, karka bari na ƙara kwana a duniyar nan dan zan iya ɗaukar...". maganar ta katse daga bakina dalilin toshe min baki da Ya Kabiru yay, wanda ban san da zuwansa ba sai ganinsa nayi tsugune a gabana.
"me yay zafi haka?, Mairo rashin uwa ai ba hauka bane. dan kawai kin rasa mahaifiyarki sai hankalinki ya nemi ya gushe, har ta kai kina furta kalaman da za su fidda ke a addininki, haba karki raunana imaninki mana. ƴaƴa dubu nawa ne suka rasa mahaifiyarsu, ni ma fa kaina bani da mahafiyar nan a raye...". sai yay shiru a san da Baba da Kulu suka fito daga ɗakin, jikinsu a sanyaye, ta gefen idon na ke kallonsu. ya miƙe tsaye daga gabana, ni kuma Baba ya kira sunana,"Mairo". ban amsa ba sai jan hanci da nayi. "Mairo tashi muje daga ɗakin Gwaggonki". nace da shi,"Baba ka kirani da sunana na ainihi mana. domin Mairo ta mutu, Mairo ta mutu tun daƙiƙu kaɗan da suka shuɗe, yanzu Hussaina ce a gabanka".
har yanzu fuskarsa na nuna bayyananniyar ɗumbin damuwa yace,"Mairo bata mutu ba, da Mairo da Hussaina duk ɗaya ne". "a'a Baba ba ɗaya bane, Mairo da ubanta, ba shegiya bace. Hussaina kuwa bata da uba, ƴar gaba da fatiha ce, shegiya ce, sai da akayi zina sannan aka sameta". kowa yay shiru ya kasa cewa komai, illa sheƙar kukana da na Kulu ko kuma nace Akila ke tashi. na buɗe murfayen idanuwana sosai na kalleta, kallon da zan iya kiransa da na dole, domin ko kaɗan bana ƙaunar sakata a cikin iɗanuwana saboda na tsaneta. kuka ta ke sosai ba don ta tsoshe bakinta da ɗan kwali ba babu abin da zai hana sautinsa fita. na rufe ido na buɗe sannan na lashi leɓena na ƙasa, zuwa wannan lokacin kam idanuwana sun bushe, zuciyata ta ƙeƙashe, nayi gutun murmushi me cike da tarin ma'anoni da yawa sannan na buɗi baki na kira sunanta."Akila". yanayin yanda sautin muryata ta fito kaɗai ya isa ya shaida maka ba kiran kirki bane, sunanta kawai na kira, amma kamar har da Baba da Ya Kabiru na kira, domin duk idanuwansu suka sauke shi a kaina, sai ta ɗago da sauri ta dubeni, nace da ita,"ki nemi wuri ki zauna yanda za ki yi kukan da kyau, yanzu ba komai kike ba hawayenki ɗaya yake da dariya a wurina. ki bari in hukuncin abin da kika aikata ya biyo baya sai kiyi me dalili, dan wallahi tallahi Akila sai na ɗau fansar rayuwata akanki". Ya Kabiru ya ɗaga min murya da cewar,"ke kina hauka ne". maganarsa ta fito a dai-dai lokacin da ƴan gidanmu su ka fara sallamar shigowa ɗaya bayan ɗaya, ban dubi kowa ba, ban kuma bi ta kan kowa ba dan duk bata tasu nake ba. na buɗi baki zan kuma magana Ya Kabiru ya sake buga min tsawa,"karki ƙara cewa komai a wurin nan, ki wuce ki tafi ɗaki...". nima nai saurin dakatar da sauran maganarsa ta hanyar ɗaga masa hannu da cewar,"dakata Kabiru, magana ake ta rayuwata da kuma asalina, so don't interfere". sai kuma na juyo a fusace na fuskance shi ina nuna masa yatsa,"idan kuma kaƙi ji, to ina me tabbatar maka da hukuncin kisan da nake ƙoƙarinyi zai dawo kanka, dan a yanzu zuciyata na azalzalata ne na kasheta, idan har ita bata ji tausayina ba ta biyewa son zuciyarta ta aikata zina sannan ta haifeni, to nima ba zanji tausayinta ba dan na ɗauki kowanne irin makami na daɓa ma ta a ƙahoton zuciya ta shura". muryar Baba ta fita da kalmar,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil". kalamai biyun da yake ta maimaitawa kenan a bakinsa, yayin da a gefe guda Inna Amarya da Inna Zulai ke aikin tambayar me ke faruwa. nasa hannu na ture Inna Amarya daga gabana na ƙarasa gaban Akila na tsaya, da yatsa ɗaya na ɗago fuskarta da ke duƙe tana kwaranyar hawaye. "wallah kin cuceni, kuma Allah ya isa tsakanina da ke, dan kin nakasta rayuwata, me nayi miki da har kika zaɓi ki haifeni ta wannan ƙazantacciyar hanyar?". na ƙarasa faɗa ina damƙar ƙirjinta,"wallahi tallahi ba zan taɓa yafe miki ba, sai na saka ki kuka fiye da wanda zanyi, sai na sakaki baƙinciki fiye da wanda kika saka ni a cikinsa, sai na zama ni ce ajalinki dan baƙin cikin abinda zan aiwatar ne zai sa zuciyarki ta kumbura ta fashe. a cikin daƙiƙa biyu da kunnuwana suka gama jin asalin labarin rayuwata daga gareki, a rabin daƙiƙa ƙwaƙwalwata ta gama lissafi da tsarin yanda zan ɗauki fansata akanki da Major, kuma a rabin minti zuciyarta ta zartar hukuncin kisa akanku, to amma cikin shigar sabuwar daƙiƙa lissafi da tsarin komai ya sauya, naga kasheku ba shi ne mafita ba, idan na kasheku ba shi ne zai sa na sami sauƙin zafi da raɗaɗin da ku ka dasa a zuciyata ba, ba shi zai hanani jin baƙin cikin rayuwata ba. in sakaku kuka fiye da yanda kuka sani shi ne kaɗai zai sa na sami ƴar salama daga ƙuncin da ku ka jefani aciki, a ƙalla ko ba komai za ku ƙarasa rayuwarku cikin dawwamammen baƙin ciki. Akila za ki ce na faɗa miki, ki aje hakan a ɓangaren tunaninki... wallahi ba za kiyi danasanin samar da ni ta hanyar fasiƙancin da ki kai ba sai na ɗauki mataki akanku tukunna, zan je na sami shi abokin dadiron naki, zan tabbatar masa da cewar ni ƴarsa ce da ya haifa a waje yay watsi da rayuwarta saboda yana so ya tsira da mutuncinsa, bayan yaji wannan zan tilasta masa na tursasa shi ya kwanta da ni ya aikata irin abin da ya aikata da ke, zai mu'amalantu da ni ne yana kuka yayin da nawa hawayen suke a ƙyafe. da zarar buƙatata ta biya zan wuce na nemi ɗan'una na shaida masa ni wace ɗinsa, na kamo hannunsa na kawo shi har gabanki, shi ma ya tursasaki ya aikata the same abin da muka aikata ni da major... kukan da zanga kina yi a wannan lokacin shi ne burina, duk da na san hakan ba shi zai wanke min dattin baƙin cikin da ke zuciyata ba, amma kuma ko banza na dasa muku baƙincikin da ba zai taɓa bari ku ji daɗin rayuwa ba...in Allah ya yarda ba za ku zubar da hawayen ruwa ba hawayen jini za ku yi ta zubarwa".
ta riƙe hannuna ta ɗauke daga kan ƙirjinta, dan ni kaina ina jiyo yanda ƙirjinta ke harbawa tamkar zuciyarta zata faso waje, murya a cikin kuka tace,"ko ba komai ni mahaifiyarki ce, ki tuna wannan a mahanga ta addininki...". ban bari ta ƙarasa ba na shaƙi wuyanta lokaci ɗaya ta kama kakari,"bari na ƙarasaki tun yanzu, ke har kina da bakin da za kiyi min nasiha, ki gama jin daɗin iskancin naki sannan kizo kice za ki min nasiha, gaba ɗaya ba ki fi ƙarfin na kiraki da karu...". sauran maganata ta katse, jina da ganina suka ɗauke na wucin gadi, cikin sakannin da ba su haura ɗaya ba na haɗa hankalina da tunanina na dawo cikinsu, sannan na buɗe idanuwana tangararau suka bar ganin ƙyallin wutar da ta haska a cikinsu, duk ta dalilin azababban marukan da Ya Kabiru ya bani ta duka ɓangaren fuskata, da kuma wanda Ya Amadu ya dawo min da shi bayan ɗaukewar na Ya Kabiru, sai na gigice gaba ɗaya na rasa makama, sai dafe kuncin nawa nayi da nake jin kamar wata jijiya acikinsa na neman tsinkewa.
"Ya Amadu har sau nawa za'a dukeni ka hanani yin kuka,? mene laifina a ciki dan na kira matar da ta lalata min rayuwa da sunan karuwa, yanzu shikenan kowa zai tsananeni, kowa zai koma kirana da shegiya..kuma wallahi ba zan janye ƙudurina akanta ba ko da me za'a min, sai dai in Allah ne ya ɗau raina, kuma na faɗa ɗin Karuwa, ai idan batayi karuwancin ba zata samar da ni ta ƙazamar hanya ba". ƙaton kutufo ya kuma sauka a bakina, halshe da haƙorina suka haɗe wuri ɗaya, jini ya shiga zuba. na ɗago ido na kalli Ya Kabiru, huci yake da jajayen idanuwansa da suka sauya launi su ka rikiɗe zuwa na wata halitta a cikin halittar dabbobi. da kakkausar murya ya ke faɗa min,"billahillazi la'ila ha'illahuwa idan bakinki ya ƙara furta wata magana anan wurin sai na sa ƙafa na mitstsikeki dan ubanki, shashasha mahaukaciya....Amadu saketa". kallonsa kawai na ke da mamaki nace,"dole kace nayi shiru tun da kai igoyoyin uku na aure ne suka samar da kai, ba zaka ji irin zafin da ni nake ji ba, shi yasa ba zaka damu ba, to wallah a yau banga me hanani magantuwa ba duk faɗin duniyar nan". maganar na ke ci gaba da faɗa a san da tuni yasa ƙafa ya fyaɗeni na zube ƙasa, kan yasa hannu ya jani kamar wanda ke jan wasu kaya har zuwa zaure, ya buɗe ɗakinsu me uban duhu babu wutar nepa, ya jefani a ciki sannan yasa mukulli ya rufe.
duk kururuwar da nake akan ya buɗeni na fita ɗaukar fansa amma sam yaƙi, illa ma buɗewa da yay ya dawo ciki ya ɗaureni da igiyar shanyar da ya ciro. nabi bayansa da ido ina kallon yanda yake goge ƙwallarsa. amma ban fasa jaddada masa ba, sai dai idan bana numfashi ne kaɗai zuciyata zata ƙi aiwatar da ƙudurinta akan Akila da Tosin, insha'Allahu sai nasa sun zubar da hawaye fiye da wanda nake yi, wannan alƙawarina ne, kuma nasan wace zuciyata ba zata taɓa rissina akan hakan ba.
daga can zaure na jiyo Yagana ta shigo gidan tana faɗin,"ai wallahi tunda Adawiyya taje tace min wai Mairo tayi shaye-shaye tana ta wasu surutai marasa kan gado nasan zai yi wuya idan ba SIRRIN ƁOYE ne ya fito fili ba. oh oh na shiga uku ni Rakiya, a garin ya hakan ta faru?, wa ya sanar da ita cewar ita shegiya ce duk wannan rufa-rufar da muka dinga yi, kai munafiki bai ji daɗin halinsa ba, dole sai da aka samu wanda ya faɗawa yarinyar nan ita ƴar zina ce, to Allah ya isar ma ta, ke kuma ki bar kuka muje ɗaki...ina Mairon ta ke?".
"shegiya kuma Ƴar zina!". kalmomin suka ƙara maimaituwa a cikin kunnena, "Akila kin cuceni". na fada tare da kifa kaina akan gwiwoyina ina fashewa da matsanancin kuka. duk bidirin da ake tsakanin Yagana da Ya Kabiru akan ya fito da ni ina jinsu.
*Plss Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*33)*
Yagana ta gyara ɗaurin zani ta gyara zaman mayafi ta fuskanci Kabiru da kyau sannan tace,"Kabiru, ka buɗe min ɗakin nan yarinyar nan ta fito, shin da wanne kuke so taji?, memakon ku lallasheta sai a ƙarke da kulleta, tsakani da Allah wannan ai ba kyautuwa bace...ka buɗe dan Allah". ya kaɗa kansa ya juya ya fi ce bai ce da ita komai ba, tabbas ya riga ya sani a irin taurin kai na Mairo kamar kafirunal ula babu abin da zai dakatar da ita daga abin da tai niyya a wannan lokacin, shi yasa ba zai buɗeta ba ko da kuwa zata mutu aciki ne, in dai taurin kaine ba ita kaɗai ta iya ba, shi ma ya iya, kuma zai iya rantsewa ya takata ya dame.
ganin ya fice Yagana ta juyo cikin gida jiki a mace kamar wadda akaiwa duka, ba don komai ba sai dan yanda cikin ƙanƙanen lokaci wai har wannan maganar ta baza gari dan abin takaici. ƙofar gidansu maƙil jama'a kowa na tofa albarkacin bakinsa, hatta Malam da ya fito zuwa masallaci kasa fita yay sai dawowa yay.
"amma dai wallahi anji kunya, a haka kamar ta Allah ashe fir'auna a zuci ne. ni dai zaman haukar nan naki dama ba tun yau na dasa masa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 52