Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya tabbatar da shigarta wurin har ya ƙara kiran matar ya tambayeta ta shigo tace masa ehh sannan ya baɗe wurin da ƙura. *8:30pm.* *more event center.* daga irin yanda kake ganin zuƙa-zuƙan motocin da ke cike da harabar events ɗin har zuwa waje zaka san ehh fa lallai bikin na manya ne masu lokacinsu. sojoji da ƴan jarida zagaye da wurin, da yawa nada ga cikin hall ɗin zaune yayinda wasu kuma yanzu ne motocinsu ke parking wanda yawancinsu dangin amarya ne, alagaitar da ake busawa na shaida bikin na masu sarauta ne. a wannan lokacinne jiniya ta ƙaraɗe ko'ina, a cikin wurin har daga can waje kan titi sakamakon motar Mahaifin amarya da ke shigowa. a yayin da motar amarya ke shigowa daga baya, Major ya fito daga cikin motar cikin dakakkiyar shaddar magic milk colour me cijawa, sannan matarsa Aaliya ma ta fito cikin wani haɗaɗɗan less ɗinta ita ma milk colour, ta zagayo inda mijinta yake suka jera suka nufa cikin hall ɗin sojoji uku na take masu baya. sai bayan shigarsu sannan Almustapha, Imam, Joseph da Alhassan wato yayyan amarya su ma suka fito cikin shaddarsu irinta mahaifinsu da su kai anko gaba ɗayansu, suma sannu a hankali suka rankaya zuwa cikin hall ɗin. [7/18, 12:30] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *_Happy Marriage Life Maryam Mukhtar Afafa._* *(49)* a motar amarya da ango kuwa a kallo ɗaya za kaiwa jigwayen taron zaka san lallai ranar aure ta musamman ce ga kowa. shigar shadda ɗabi'ar Ahmad ce tun kan su zama wasu, kuma ƙoƙarinsa ne ɗinka babbar riga a duk lokacin da wani biki na abokinsa ya kama, amma a yau yanda kayan suka amshe shi yafi na kullum. daga kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen ɗinkin da ke jikinsa, duba da ɗinkin ma bai yi kama da namu na ƙasar nigeria ba. askin kansa sai walƙiya da sheƙi yake ta ƙasan hular da ke kafe a kansa, fuskarsa sai washewa take da murmushi, Hakan ya saka kyawunsa ƙara fito da ɓoyayyan kyansa. Amarya Maryam tayi bala'in kyau da haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. net less ɗin da ke jikinta kalar shaddar angon nata ash, an ƙawata ɗinkinsa da wasu flowers da suka ƙara fito da kyan ɗinkin, sarƙa da ɗan ƙunnenta silver colour masu shegen tsada, haka pos da takalmin dake ƙafarta duk silver, lamarin dai ba'a cewa komai, dan tun lokacin da aka shirya Maryam ita da kanta tasan ta haɗu, sai dai bata san me yasa a wannan lokacin ba zuciyarta ke a raunane, zuciyarta da ruhinta na faɗa mata kamar wani abu zai gifta wanda ba lallai ta iya ɗaukarsa ba, sai Shamsiyya ce me ƙarfafa ma ta gwiwarta da ada ta mutu tun dirarsu a bichi da su kai ido huɗu da Jawad yay mata wannan murmushin nasa da ƙarya ne tace bai da kyau. suka haɗa ido ita da angon nata suka sakarma junansu ƙayataccen murmushi sannan Ahmad ya fito ya zagayo zuwa tata ƙofar, ya miƙa ma ta hannu ta riƙe shi ta fito daga motar, A haka suka shiga cikin hall ɗin da ya gaji da haɗuwa, anyi decoration ɗin wajen da silver colour, komai na wurin silver ne da kwalliyar ash ajiki, kuma komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, haske ta ko'ina tamkar rana, fitilu sai walwali suke su na ƙara ɗaukan ido da hankali, Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. dan ɓangaren dangin mahaifinta daban kasancewar su christians, kanta na ƙasa tana kallon wasu wuraren ta wutsiyar ido, zuciyarta da fuskarta na washewa da tarin farin cikin da ba zata iya musaltawa ba. wannan waƙar da ke tashi a hankali na bin jijiyoyin jikinta su na motsata, har ta ƙara tsamke yatsunsu da ke cikin na juna. abokan ango da ƙawayen amarya ne suka masu rakiya har mazauninsu inda ya dace kuma aka tanada domin su. bayan daidaituwar zamansu MC ya bada umarnin ai welcoming nasu nan wuri ya ɗauka da tafi rau-rau, daga nan kuma Bella ta fito cikin takun ƙasaita zuwa waje na musamman da aka aje royal chair saboda ita ta zauna ta shiga kwaroro adu'a, daga bisani kuma Granny Chioma wadda ta ke ƙanwar Granny ta fito tazo ita ma tayi kalar tasu adu'ar ta kiristan sannan ta koma ta zauna. Shamsiyya Sani ita ta fito ta bada biography na amarya, tun da ta fara gaban Maryam ɗin ke faɗuwa dan sai take ganin kamar zata fito fili ta daɗa faɗawa duniya ita shegiya ce, sai dai har Shamsiyya ta gama wannan bayanin bata ji makamncin maganar hakan ba, da zamanta kuma Habib da yake aminin ango shi ma yazo yay biograph na ango. Ummi(Akila) ita ma tazo ta bayyanawa irin jin daɗi da farin cikin da take ciki da kuma muhimmancin wannan rana a gareta. sai bayan ta koma ta zauna ne sannan MC ya umarci amarya da ango su yanka cake ɗin da aka aje akan wani table, dan rashin kunya ko da Ahmad ya yanko cake ɗin a bakinsa yasa shi sannan ya nufi bakin Maryam ɗin da shi, kunya ta hanata karɓa ayayin da ihu ya karaɗe wurin aka ɗauki tafi, sai da ƙyar ta iya buɗe baki ta amsa sannan ita ma ta ciro nata ta miƙa masa, sai dai maimakon tasa masa a baki kamar yanda ya buɗe sai ta shafe masa icing ɗin a kumatukansa gefe da gefe da kuma kan hancinsa, nan ma ihu ya kuma karaɗe wurin, ta miƙa hannu ta ranƙwafo da fuskarsa ta haɗe goshinsu da hancinsu, kamar MC Rahineena ta san me zata yi ta ƙaraso ta sai ta speaker nan muryar Maryam ɗin ta fito a hankali cikin wani amon sauti me motsa zuciyar ɗa namiji tace,"i love you". aiko nan ta ke aka ƙara sakin ihu ana tafi, MC ma tayi ihu tayi ihu sannan ta sauya taken waƙar da ke tashi zuwa wata waƙar me taken 'Baby i Love You' ta Tiffany Alvord, waƙar da ta ƙara tashi da wurin, masoyan biyu suka ƙara shiga shauƙi, Ahmad yasa hannu a weast ɗinta ya janyota jikinsa suka shiga rawa a hankali. a wannan lokacinne Daddy da Mami suka fito su na yi musu liƙi, Dad na watsa musu Doller Mami na watsa masu Qatari Riyal, kafin nan ma Ummi ta shigo cikin mutuwar jiki ta shiga watsa nata kuɗin ita ma, nan da nan kuma hasken camera ya fara shigarsu sound ɗin ƙyas ƙyas kawai kake ji na tashi. duk abin da Akila keyi tana yinsa ne kawai a cikin rashin kuzari, tunda aka shigo wurin nan idanuwanta na kan taga ta ina Kabir zai ɓullo, kuma tana ta kiran wayarsa amma bai ɗaga ba, tasan dai yanzu aka fara dinner amma tana ganin kmar har a gama ba lallai ne yazo ba kaman yanda ya tabbatar ma ta da zai zo ɗin. *10:00am* *a wannan dare wannan lokaci da kowa ke wurin dinner.* ƴan tsirarrun mutanene su kai saura a gidan, hakan yasa hayaniyar gidan ta ragu sosai ba kaman a ɗazu ba kamin su fita. ba su dawo gidan ba sai bayan magrib, zaune take a gabansa a yayinda shi kuma ke kan kujera, hannunsa riƙe yake da nata yay masa wata iriyar matsa, zafin da ke ratsata har cikin kanta, kuma duk yanda ta kai ga mutsu-mutsu dan zare hannun yaƙi bata dama. ba sau ɗaya ba ko sau biyu ta faɗa masa,"Ya Kabir riƙon da zafi". amma sam bai ma nuna ya jita ba, sai dai a yanda ta lura so yake ya sauke zafin takaicin wani abu da yake ji a wannan riƙon, hakan yasa ta haƙura kawai tana jiran har san da zai buɗe idanuwansa ya sauke akanta sannan ya fahimci irin nata zafin da taji da yay mata wannan riƙon nasa, tukunna cikin tsawa ya umarceta da ta tashi ta bar masa ɗaki. a tsorace ta ke da shi sosai tun da suka dawo, koma tace tun da suka taho, dan lokacin da ya je ɗaukota ba haka yake ba, tana iya tunawa sun yi waya shi da Ya Ahmad lafiya, yake masa zancen ya shigo kano ne amma yanzu zai dawo sai ya ƙaraso wurin dinner ɗin, kuma bayan gama wayar tasu ya kalleta da wannan ƙwayar idon tasa da wani yanayi da ta kasa fassarawa, yace da ita,"na ga gyaran gashin". tana iyawa tunawa da yanda tasa hannunta akanta ta zame ɗankwalin duka, tana iya hango yanda ƙwayar idonsa ke kallon gashin da ya sha gyara tarr babu ko ƙifce, a lokacin abin da yace mata shi ne,"Nawwara zan iya taɓawa?". kuma kanta kawai tasan ta gyaɗa masa amma sai ya girgiza nasa yace,"ba yanzu ba". sannan ya umarceta da ta mayar da ɗan kwali kafin nan yace ta nuna masa ƙunshin, ananne bai iya hana kansa ba sai da ya kamo hannun ya shafa sannan ya faɗa mata irin kyan da yay, har yace "amma jan yafi kyau, sai ya ƙara fito da kyawun siraran yatsunki". a wannan lokacin inda zata danganta yanayin da take ciki da kalmar ruɗani, to tabbas ita kanta tasan da ta yiwa kalmar rashin adalci, shi yasa ko kusa bata alaƙanta shi da hakan ba, laɓɓan bakinta dai sun furta masa kalmar,"na gode, na gode sose da kulawanka Ya Kabir, Allah ya biyaka da mafificin alkhairi". kuma har furucin da tayi ya haɗe da wani furucin da bata san sanda ta faɗe shi ba. "Ya Kabir dan Allah nima zanje wurin partyn". tana kallon san da ya gyaɗa kansa har sau biyu a lokacin, kafin ya buɗe baki yace da ita,"Za ki je". ya sauke numfashi ya ƙara da cewa,"sun iya gyaran jiki, kin ƙara haske kin ƙara kyau, ƙamshinki duk ya cika motar". daga wannan maganar kuma har suka dawo gida wata maganar bata ƙara haɗasu ba. sai ma da suka dawo ne ya sata a gaba taci abinci, sannan ya fita ya barta a ɗakin kamar ɗazu da safe yace tayi wanka ta shirya cikin kayan da ya bata a kwali, sai bayan tasa kayanne wannan matar da ya kira tayi mata kwalliya tayi ma ta ta tafi, kwalliyar da bata san ta mecece ba, haka abubuwa da ke ta wakana ta rasa da wanne irin tunani zata masa kuma ta rasa da me zata kira shi. abu ɗaya ta sa ni tunda aka gama kwalliyar ta kalli kanta a madubi, taga ta fita daga siffar waccan Nawwaran ta zama wata Nawwaran ta daban, shikenan tayi azamar miƙewa daga kan kujerar da take zaune a gaban madubi, ta sandare a tsaye, irin sandarewa da duk wanda ya shigo ya ganta a wannan tsayuwar kawai zai hankaɗata ne ta ƙarasa faɗuwa, sannan idan gawar tata ta cancanci ai mata kuka ya kurma ihu mutane su shigo ya sanar musu ta mutu. tunanin ya bar kanta lokacin da Kabir ya shigo ɗakin ya ƙaraso gabanta sosai ya tsaya ya kamo hannunta a nasa, ta san wani tunanin ta tafi amma bata san ko tunanin mene ba, hakan yasa hatta riƙon da yay mata da tsayuwarsa bata san da su ba. maganarsa kawai taji, wannan furucin da ya haifarwa zuciyarta yin rawa hatta da gangar jikinta, kuma lokaci ɗaya komai na cikin kanta ya ɗauke, ta ɗauke ƙwayar idonta daga kallonsa ta tsaida su akansa, ba kallo ɗaya kawai tayi masa ba, sai da ta buɗe ido ta rufe sau uku tukunna ta gama shaida kayan da ke jikinsa. Shadda ce arniya ƴar ubanta aqua colour, taji wani azababban ɗinki da zai sa mai kallonsa kusan zaucewa, kalar shaddar kalar kayan da ke jikinta ne, duk da bata san da wanne su na zata kira kayan ba, ta san ba les bane kuma ba material bane, doguwar riga ce ita ma kuma kamar ba ɗinkata akayi ba, ta san dai tana ganinta a jikin turawa a tv. kawai sai ta tsayar da tunanin da ke neman shiga kanta ta natsu akan maganar da yay mata da ya shigo, maganar da sai da ta gama shawagi a iska sannan ta shigo kunnenta da girgiza ƙafafuwanta kaman zata faɗi sai kuma maganar amsar da zata bayar ta riƙe ƙafafun nata. "Nawwara idan naje gidanku nemawa wani aurenki a yanzu Babanki zai bayar? zai iya damƙa min aurenki Nawwara? ko kuma dole sai mun tura wanda yake uba agaremu tukunna?". kaman matsar bakinta yay a lokacin ta bashi amsarsa kai tsaye hawaye na biyo kuncinta. "Ya Kabir ai tuntuni Baba ya bada ni, ba wannan Baban da yake riƙona ba. Babana kafin ya mutu, kuma ita ma Mama kafin ta rasu ta ƙara shaidawa wannan Umman da ke riƙona sun bada ni". zata iya rantsewa taga ƙyallin wata wuta a cikin ƙwayar idonsa a lokacin da ya kalleta, kafin ya jefa mata tambayar,"banbance min Baban yanzu da wancan Baban, da kuma Umma da Mama". a lokacin hannu tasa ta goge hawayen fuskarta da gudunsa ya ƙara yawa, sannan tace da shi,"iyayena sun rasu, inda nake zaune Ƙanwar Mamana ce ke riƙona". a lokacin da yake kallonta taga tsananin tausayinta acikin ƙwayar idonsa ya haska, kuma shirunta yay daidai da saka hannunsa ya goge ma ta hawayen, sannan ya buɗi baki yay maganar da zata ce da ƙyar ta iya jinta. "waye su ka ba ki?". "wani ne Kabiru". "ai na yake?". "nima ban sa ni ba, ban ma san shi ba. Baba dai yace min sai na shekara 18 tukunna za su neme shi, hakan Babana ya bada wasiyya". zata iya cewa wannan furucin nata shi ne silar wannan muguwar damƙar da yay mata, dan shirunta ya haɗe ne da matse hannunta cikin nasa sosai, sannan ya janyota suka ƙarasa bakin kujera, shi ya zauna akan kujerar ita kuma ta duƙa a gabansa. kuma ayanzu in zata iya lissafi sama da wucewar minti ashirin kenan idonsa a rufe yake, haka wayarsa da ke kan ƙafarsa tayi ringingin yafi sau goma bai ɗauka ba. har tsawon wucewar yawan wasu daƙiƙu tukunna ta fara jin hannunsa ya saki daga riƙon nata, ta leƙa fuskarsa kamar yayi bacci ne, saboda haka ta zame hannun a hankali sannan ta fice daga ɗakin da sauri, burinta kawai ta isa ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, har ta wanke wannan kwalliyar ta cire kayan ta maida nata ta dawo asalin Nawwaranta ƴar ƙauye. sannan ta samu wuri ta zauna ta hana ƙafafunta da hannunta rawa, tukunna ta sai ta kanta ga natsuwarta, bayan nan sai ta tashi ta hau aikin gida kafin a dawo daga wurin partyn. *washe gari, ƙarfe tara da rabi na safe, cikin masarautar bichi, turakar Sarauniya Hauwa'u.* Net ɗin da ke jikina wani farin net ne da ya ji adon flowers pich clour ajiki, doguwar riga ce irin tamu ta larabawa da suke sawa ranar biki, an yafa min wani farin mayafi irin namu daga saman kaina, shi ma kamar rigar adon jikinsa da pich colour. bangles da zoben da ke hannuna suma farare ne hakama yari da sarƙar. kwalliyar yau ta ɗauki fuskata fiye da ta jiya, sai dai yau ɗin fuskata fayau ta ke. tun da na farka yau sam bana son yin magana, dan idan nayi maganar muryar na fita ne kaman nayi kuka, tunda na wayi garin yau na tuna cewa yau ɗinne za'a ɗaura aurena shikenan wani kuka ya shimfiɗe a zuciyata, jikina duk yay sanyi na zama kamar mara lapia. ina zaune ne akan ƙasaitaccen gadon Ammi gefen haguna da damana an saka tum-tum kamar wata basarakiya, du ka Ammi ce tayi min wannan shirin, sai bayan ta gama shiryani ne Hajjah Nashwa ta shigo tayi min feshi da wani turare da ban taɓa jin ƙamshinsa ba, zan iya cewa dai naji irin yanayin ƙamshinsa a jikin mutum guda, wannan ƙwayan mutum ɗin da na cire shi a lissafin rayuwata. na rasa faɗuwar gaban na menene duk da Shamsiyya Sani ta faɗa min haka amare ke tsintar kansu a wannan rana da ta ke me albarka da muhimmanci a wurinsu...amma ni nawa sai nake ganin kaman mummunan abu ne zai faru, ina zaune ne kawai dan babu yanda na iya, domin Hajjah Nashwa tace kar na motsa a wurin har sai an ɗaura aure tukunna, idan ango ya shigo shi ne za'a zo a fito da ni. a yanzu da nake zaune muryar Yaya kawai nake sonji, so nake na kira shi ko sunana ne ya ambata wannan taraddadin da ke liƙe da ni ya samu ya barni. na kulle idona sakamakon wani abu da naji ya daki allon ƙirjina ya girgiza a lokaci ɗaya, nayi saurin saka hannu na dafe ƙirjina ina jin wani irin baƙon yanayi a tare dani, irin yanayin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba. daga waje na jiyo tashin algaitu da busar sarewa na tashi, sai na ƙurawa ƙofar shigowa ido kaman ina jiran shigowar wani, ɗora idon nawa akai yay daidai da shigowar Jakadiyar Ammi tana cewa,"Alhamdulillahi, Allah kasa albarka". sai naga ta zube a gabana tana ci gaba da faɗin,"gaisheki ranki ya daɗe, a yau kuma daidai wannan lokaci kin shiga cikin sahun matan nan masu girma da darajara, martabarki ta ɗaga sama, Allah ya sanya alkhairi, ina tayaki murna". kawai sai naji harbawar wani abu a zuciyata ya kuma wucewa, sai na karkato kaɗan na kai dubana ga wayata ina duban agogo, lokaci bai ba, lokacin da akasa na ɗaurin auren bai cika ba, ɗaurin auren ƙarfe goma da rabi ne amma me ya dawo da shi ƙarfe tara da arba'in?. a yanzu da na gama kallon lokacin ba shi lokacin nake jiran gama lissafawa ba, ƙwayar idona na kai ne da jiran shigowar kiran Yaya. "Maryam an ɗaura". na jiyo muryar Shamsiyya na cewa da ni. na juyo na dubeta daga inda ta ke tsaye jikinta a sanyaye. ni da ita duk sai muka tsaya kallon juna, muka kasa yiwa juna magana, kowannenmu idonsa da gangar jikinsa na bayyanar da fargaba da ke ɗauke da ita, sai ita ce naga tasa hannu ta goge ƙwallar da ke shirin sakko mata, kafin ta ƙaraso ta rungumeni tana fashewa da kuka. muryata na shaking nace,"kukan na menene?". "ina tayaki murna". "wai da gaske an ɗaura?". ta ɗaga min kai alaman ehh kafin kuma nace,"amma...". nayi saurin tureta daga jikina nace,"amma me?". "naji Ummi na cewa bada Ya...". ban bari ta ƙarasa faɗin abin da take son cewa ba na tureta daga jikina a zafafe, na diro a saman gadon ina damƙe kafaɗunta, na shiga girgizata da ƙarfi ba tare da bakina ya iya furta wata kalma ba. shigowar Mamina ɗakin na sami amsar tambayata da na gagara yiwa Shamsiyya, abu ɗaya na sani shi ne, naji san da Mami tace,"ina Jawad ɗin?". amma bayan nan ban kuma sanin komai ba da kuma inda kaina ya tafi. *09:40.* a parlon ɗakin Ahmad ne da abokansa ana ta shirin tafiya wurin ɗaurin aure. ango wanda tuni ya shirya yana kar ya hularsa yake cewa da Mubaraq,"ko ka shirya ko kuma wallah muka gama muyi tafiyarmu". "kai dai angon zumuɗi ci gaba da shirinka kawai. ni ka ganni lokaci nayi miƙewa zanyi na bula Babbar rigata". Habib yace da Ahmad,"duk kabi ka ishi mutane bayan da sauran lokaci". bai tanka masu ba ya nemi wuri ya zauna tare da ɗaukan wayarsa, inda yaci karo da message ɗin Maryam wanda ya shigo tun ƙarfe shida, sam bai lura da saƙon ba sai yanzu, kuma kalaman da ke ƙunshe acikin saƙon shi ya saukar da wani annuri da murmushi mai ƙarfin sauti lokaci ɗaya a saman fuskarsa, a lokaci ɗayan da ya fito ɗin sai ya ɗauke sakamakon furucin da ya ji ta bayansa da muryar Baba Mujibu. maganar da tasa shi hanzarin miƙewa ya juyo gare shi yana kallonsa da kyau, da irin tsananin tashin hankali da ruɗanin da ba zai musalta shi ba, haka zalika idan ya kira yanayin da yake ciki yanzu da tashin hankali kaɗai to ya yaudari kansa. ya sani Baba Mujibu uba yake a gare shi, kuma Baba Mujiba ba sa'ansa ba ne, kuma ba sa'an wasansa bane, hasalima basa wasa da shi, dan ba haka babu ta yanda za'ai ya kira wannan furucin nasa da zancen wasa, balle ya kira yanayin fuskarsa da wasa. "Ahmad an ɗaura auren Maryam amma ba da kai ba, sakamakon genotype ɗinka da mahaifinta yaƙi yarda da shi". maganar ta shiga kunnensa tarr kuma ya fahimci me Baba Mijibun ke cewa, amma kafin a warware masa komai abun da yake so ya sani dawa aka ɗaura auren? "Jawad". yaji kiran sunan ya fito daga bakin Kabir da ke zaune kan kujera, amma sai dai sunan bai fito da amsar tambayar da yaywa kansa ba, shi magana yake yi a waya, kuma da alama da Jawad ɗin yake wayar. sai ya maida kallonsa ga Baba Mujibu yace da shi,"Baba babu mahaluƙin da ya isa ya hanani auren Maryam, babu shi. tabbas ko dawa aka ɗaura sai ya warware shi yanzun nan...batun irin Ƴaƴan da zamu haifa babu ruwan kowa da wannan". sai ya zube akan kujera yana dafe kansa. "genotype". wannan kalmar da ta haɗu da furucin Baba Mujibu ita ta haska akansa, me yasa tuntuni ba'ai zancen genotype ɗin ba sai a yanzu, sai da akazo kan gaɓar da ba'a isa ai masa abinda ake ganin mafita ce aka samu ba, abinda akasan ba zai ɗauka ba. abunda ya sani kawai bai san genotype ɗinsa ba, ya san dai lokacin da suka je seminer ibadan shi da Md da Almustapha dukansu anyi musu genotype, sai dai bai san sakamakon da result ɗin ya bayar ba kasancewar a jirgi akace zaa sako a biyo su da shi, kuma yasan Almustapha yace masa result ɗinka yazo hannuna amma bai ba shi ba, to shin menene genotype ɗin nasa kenan? "SS kai carrier ne Amadu". maganar ta fito daga bakin Baba Mujibu kamar yasan tambayar da ke ransa kenan, kafin yaji Baba Mujibun yaci gaba da cewa,"wannan dalilin yasa mahaifinta yace ba zai iya baka ƴarsa ba domin ƴaƴan da za ku haifa duka zasu zama carriers. shi kuma bai san yanda ƙaddara ta ke ba amma ba zai so a jininsa a sami wani kuskure irin hakan ba, familynsu ba a aure sai result ya zamana cikin biyun ɗaya, imma AA da AA, imma kuma AA da AS. wannan dalilin ne yasa aka maye gurbinka da ɗan'uwanka Kabir kasancewar shi da ita genotype ɗinsu ɗaya ne AA+AA". ba shi kaɗai ba, hatta Kabir ɗin da bai san meke faruwa ba kawai yaji saukar maganar ne a yanzu, duka su biyun suka miƙe a zabure. "Kabir". Ahmad ɗin ya tambayi Baba Mujibun da tsantsar mamakin da ke haskawa a fuskarsa. "Ni kuma Baba?". shima Kabir ɗin ya sake tambaya da mamaki. "ƙwarai da kai aka ɗaura...kuma bance wani acikinku ya sake yi min wata tambayar ba, abinda Babanku yace da ni kawai shi ne kai Ahmad na sanar maka yanzu aure ba naka bane, kai kuma Kabir kayo shirin angwaye ku taho". Kabir ya ɗauke idonsa daga kan Baba Mujibu ya maida kan screen ɗin wayarsa da ke ringing yana kallon sunan Ummi da ke yawo akai. ya kai hannu ya ɗaga, ya ɗaga ne ba don komai ba sai don ta cire shi daga wannan ruɗanin da Baba Mujibu yasa su. furucin da ya fito daga bakinta zuwa kunnensa kai tsaye shi ne,"Congratulations Dear, You are now the groom of Maryam, i mean you are now Maryam's Husband". bai sani ba ko ta kashe wayar, shi dai sauke wayar yay daga kunnensa kawai ya nufi bakin ƙofa, a wuri ɗaya kawai ƙafafunsa suke so su gansu, gaban Maryam, riƙe da ita a jikinsa, ya hana wannan ruwan hawayen da yasan dole za su zuba daga idonta fitowa. _________________________________ tabbas idan banji comment ba sai na warware auren nan😎 [7/18, 14:11] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *(50)* "me ake nufi kenan?, gaba ɗaya babu abun da na gane ku fahimtar da ni". Cewar Kaka Tabawa. kuma har yanzu kan Ahmad na ƙasa bai ɗago ba, haka kuma Zulai da ke tsaye tun shigowarta bata iya samun wuri ta zauna ba. Yayarta wadda su ke uwa ɗaya mai suna Lubabatu ta rangaɗa guɗa tace,"aini Alhamdulillah, wannan abu yayi dai-dai...dama ina Amadu ina auren ƴar zina, Allah ai ba azzalumin bawansa bane, shi yasa ya

Chapter 47 of 52