Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na ke da darajar da zaka ɗaukar min mataki...to ko ba komai ka tuna ni na haifi Adamu kuma na shayar da shi". tayi hanyar kitching tana ci gaba da faɗin,"ni dai na faɗa maka kar ka dawo min da wannan abar, dan ba zan iya zama da masharranciya acikin gida ba, Allah yaso ba wani nake aure ba da yau tasa an damƙa min farar takarda". daidai fitowata daga ɗaki nace,"wai ni Yagana da kike ta faman wannan sababin sharrin me na miki ne?". maimakon ta ban amsa sai ta juyo ta banka min harara sannan ta ƙwalawa Nawwara kira tace tazo ta rufe ma ta ƙofarta idan mun fita. har kitchen na bita ina ce mata bata yi min adu'an fita ba tayi min shiru kamar wadda ke magana da kurma, sai da zan fita ne tace,"wanda yafi ƙarfinka ai yafi ƙarfin adu'arka". siriryar dariya kawai nayi kamin nasa kai na fice ina jin ƙara son Yagana a raina, da roƙon Allah ya daɗa ja min da ranta. "jiya naji wancan abin yana cewa tuwon dawa yake sonci, je ki tambayi Zulai idan ta sami dawar ta bani, in ba'a samu ba kuma na kira ubansa ya taho da ita". Yagana da ke wanke nama tana tsiyaye ruwan acikin sink ta faɗa. Nawwara tace,"Yagana wane waccan abin?". cikin ƙufula Yagana tace,"Ubana da waccan abar ta kai ƙarata wurinsa mana". Nawwara ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa,"Hajiya Yagana ikon Allah, yau kuma Ya Kabir ɗinne wancan abin". Yagana ta wurga ma ta mugun kallo da faɗin,"kin wuce kinje min aiken ko sai kin gama ɗaukar maganar taki". Nawwara ta fito a kitchen ɗin still da dariya a saman face ɗinta, kuma tana jin Yagana na faɗin,"ƴan aiki da yawa suke a ƙauyen nan, dan haka zan koreki na nemi wata tunda naga kema mutunci bai isheki ba". Yagana ta idar da sallar la'asar Adawiyya tayi sallama cikin ɗakinta, ko da Yagana ta ganta sai ta ɗauki lazimin da ba tayi niyya ba, shiru shiru sama da minti ashirin bata katse ba, kuma dama taja musu kunne kar wanda ya ƙara zuwa ya ganta tana lazimi ya dameta da magana, shi yasa ko da Adawiyyan ta shigo sai ta nemi waje ta zauna zaman jiran idarwarta. Yagana kuma na sane taƙi sallamewar, sai can tayi gyaran murya ta kalli Adawiyya da cewa,"irin haka sai ki haƙura kije kya dawo, ba wai ki tasani a gaba ba kamar wadda tazo ɗaukar fansar bashin dana ci mata na hana." "ai naga dole za ki idar ne ba kwana za kiyi a hakan ba shi yasa na kafa na tsare ina jiran sallamewarki". "au toh, da wacce tsiyar kika zo?." "tsiyar arziƙi". "to ina sauraronki, mene dama?." Adawiyya ta sauko daga bakin drower ɗin da ta zauna ta dawo kusa da Yagana ta zauna, sannan tayi ƙasa da murya ta fara magana. "Yagana dan Allah dama akan maganar Ya Suhail ne. na rasa yanda zanyi da shi a zuciyata, duk da cewar na nemi yafiyar Mairo kuma ta yafe min amma wallahi ina mugun jin kunyarta, Yagana dan Allah ki taimaka min ki shige min gaba". ta faɗa tana kama hannun Yagana ta riƙe acikin nata. "to ina ce shi ma Suhail ai kun nemi yafiyarsa ɗin kuma yace ya yafe muku ko?, to mene kuma ya dami zuciyarki da shi?". Adawiyya ta karayar da kai tare da sake matsowa kusa da Yagana tace,"Yagana ki gane mana, har yanzu ina sonsa fa...". bata ƙarasa ba Yagana ta katseta,"kai amma dai duk inda ɗan iska yake yafita daban, yanzu ke Adawiyya saboda babu tsoron Allah babu kunya a ranki shi ne kike maganar Suhail...to yanzu ni ko shegiya ce Adawiyya ai bana shige miki gaba ba akan wannan zancen sai dai na shige miki baya, to bada ni ba gaɗa a kabari, ni rashin hankalina bai kai intaha ba, kuma wallahi bari kiji yau ko Suhail ne yazo da batun aurenki gidan nan sai na shiga na fita al'amarin ya tarwatse, sai dai nima ku biyo min ta ƙarƙashin ƙasar amma wallahi ba zan bari wannan mai farar zuciyar ya auri macen da ta cutar da shi ba." ta ke ruwan hawaye ya cika idon Adawiyya tace,"haba Yagana karki manta fa ni wace ɗinki, abunda ya faru ya rigada ya faru sai dai a kiyaye gaba, nayi nadamar abin da na aikata kuma har yanzu dana sa ni nake...duk da cewar sun yafe mana amma wallahi har yanzu zuciyata ta kasa samun natsuwa, tabbas yanzu na yarda cewan duk wanda yay ƙudurin hana wani bacci to shi ne zai kwana bai bacci ba, dan Allah ki taimaka min, wallahi da tsarkakkar zuciya nake sonsa tun farko...kuma na rantse miki da Allah yanzu zuciyata fess ta ke akan kowa, Allah ya shiryeni ya ganar dani". "to Allah yasa anyi taubatun nasuha, amma wancan zancen naki kam tun muna ta daɗi da ke ki barni da shi, ki nemi wani a cikin manemanki kawai." Adawiyya tayi shiru tana hawaye, Yagana ta miƙe ta fita ta barta a wurin bata kuma tanka ma ta ba. a ɗaki ta sami Kabir zaune yana kallo shi da Aminu, ta kalle shi tana aikin taɓe baki for a while kamin ta juya ga Aminu ta amsa gaisuwarsa da cewar. "kai kuma yaushe kazo gidan?." "tun ɗazu na shigo Yagana." sai ta ƙara gwame baki tace,"yayi kyau, lokacin da Hajara ta rasu ta bar Yaranta ababen tausayi kishiyarta bugar ƙirji tayi tace babu ɗan da zata riƙe, sai ni Rakiya ce na raini Kabiru da Aminu da ƙarfina da jinina, yo a rayuwa kuwa ai bana zama abar a wulaƙanta ba tun da ance wanda yay maka alkhairi karka manta da shi...amma da yake Aminu kai ɗan halak ne har ka iya shigowa cikin gidan nan baka fara zuwa ka gaishe da ni ba, kai ai ga me ɗan'uwa tun da ba Uwarka a gidan ba wurin wanda zaka, wato da ban zo nan ɗin ba ma ba zamu sami ganawa ba." Aminu ya girgiza kai da cewar,"Yagana ni ɗin banzana in shigo gidan nan banje wurinki ba, wannan ma ai zance ne." tace,"haka ne, to ya wurin su Zannirar?." "su na lafiya." "to ka gaidasu idan kaje, ranar nan ai da na shiga wajejen naku na biya ta wurinta gidan a rufe, sai maƙwabciyarku ke ce min taje asibiti, to Allah ya raba lafiya". ya amsa da,"amin Yagana". Nawwara ta shigo parlon hannunta riƙe da kwandon abinci, Yagana tayi ma ta nuni da inda zata ajiye, bayan ta aje ta gaida Aminu sannan ta gaida Kabiru tare da yi masa sannu da jiki, ya amsa ma ta yana bin bayanta da kallo har ta fice daga ɗakin. daga inda ya jiyo ƙwafar Yagana ya karkatar da kai kaɗan ya dubeta yanda ba zata gane ba, yana kallon yanda ta ke aikin jijjiga kai sai kawai ya motsala leɓensa yaci gaba da sauraron labarai. sai da Yagana da Aminu suka gama hira sannan ta dawo kansa da cewar,"Baba kayi haƙuri ni bana gaba, ƴarka ce dai insha'Allahu ba zan kuma taɓa maka ba, dan haka ka sauka daga wannan dokin zuciyar ina mai bada haƙuri...ina yini, ya sauƙin jiki?". ya gimtse dariyar da ke neman kubce masa. "Baba magana na ke, kayi haƙuri dan Allah, a wannan halin da kake ciki ba zan iya ɗaukar shariyarka ba...kuma na maka alƙawarin Ƴarka Mairo ba zan ƙara takura mata balle har ta kuma ƙala min sharri akan abinda banji ba ban gani ba". tana yin shiru yace,"Yagana dan Allah Maryam ba Mairo ba". tace,"to Baba naji na ɗauka...yanzu dai ka haƙura ɗin ko?". ya kalleta yace,"na haƙura tsohuwa". "yauwa Baba Kabiru Allah ƙara maka haƙuri. ban sami leƙowa ba tun safe, sai nace Zulai tazo tayi maka gashin ai anyi ko?". "ehh anyi, yau ina jin daɗin jikin sosai...Ahmad ma nake jira ya dawo mu ɗan zagaya". "ehh ai da yake ya fita kai Ƴar taka yawon shaƙatawa, amma nasan duk inda suke su na kan hanya, Allah dai ya ƙara lafiya...ga tuwan dawar nan nayi maka lafiyayye, har man shanu nasa Mujibu ya aiko min, kaci sosai kaji ɗan albarka, bana son wannan rashin cin naka". "zanci Yagana bari ayi sallar magriba tukunna...tun yaushe suka fita?". yay tambayar yana jin wani abu na tokare masa ƙirji. "ah tun kamin azahar suka fita". sai ta karkata ga Aminu tace, "Aminu ai yau Allah ne yay da sauran kwanana a gidan nan". daga Aminun har Kabiru sai suka waro ido waje su na dubanta da son jin sauran bayani. Aminu yace,"Yagana me ya faru?, ba dai matsalar gas ɗin bace kumawa?". tace,"a'a wannan matsalar ai tafi ta gas...to Aminu kaga ina zaune ina kallon tashar saudiya sai ga Alhaji Amadu yazo kaina yay zandardar kamar sandar ba'are, fuskar nan a murtuke ya hauni da masifa kace Allah ya jiƙan rai Babana Manniru, wai dan me zan hana akai su waccan abar Shufin, na daina yi masa irin haka baya jin daɗi ko babu komai arziƙinta ake ci a gidan nan...wallahi saboda ban san zancen ba sai na riƙe baki ina dubansa, yace min ai ƴar da nake riƙo ne ta kai ƙarata wurin Baba Kabiru to su basa son haka na daina...maganin a zauna lafiya saina basu haƙuri, amma ai akwai Allah, gidan wani zata je idan sharri abinyi ne taci gaba ba, kaina har yanzu ciwo yake saboda ciwon abin". Aminu yace,"Allah sarki, haƙuri za ki amma ɗan riƙo yana da wuyar sha'ani". "ka bari kai dai yau ai nayi danasani, ni tsorona ma maganar taje kunnen Uwarta ko Ubanta, dukansu kasan zuciyarsu a wuya ta ke yanzu sa saka a far min". Kabiru ya katse mitar da cewar ta miƙo masa abincin yaci, ta ɗauko sai ga Zubaida ta shiga tana sanar mata tayi baƙuwa, nan ta tashi ta fita. "ke ki kira min Nawwara". Kabir yace da Zubaida. sai bayan ya idar da sallar magriba ne Nawwara ta shigo ɗakin, lokacin Aminu ya har ya tafi, ta sa me shi yana kaiwa da komowa daga bango zuwa bango, yana taka ƙafa ɗaya da ƙyar. ta cikin madubin da ke kafe a bangon ɗakin da yake fuskanta yake hangota ta bayansa, tun lokacin da ta shigo ta tsaya har san da ta ke ce masa gata, amma kuma bai amsa mata ba kuma bai juyo ba yana dai ta kallonta ta cikin madubin da irin kallon da ya kasa fassara ma'anarsa a tare da shi. maganar da ta ƙarayi ne yasa ya haɗiye wani guntun yawu a maƙogoronsa sannan ya juyo yana fuskantarta, yay tattaki ya ƙarasa zuwa inda ta ke, inda tazarar da ke tsakaninsu bata wuce inci huɗu ba. "Maryam fa?". har yanzu kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Yaya ba su dawo ba har yanzu". sai kawai ya rumtse idonsa gam tare da ɗaga kansa sama yana jin wani abu me zafi na tsargawa ajikinsa. wucewar daƙiƙa biyu sannan yace da ita,"zuba min abinci". yana faɗa ya koma ya zauna kan kujera, ita kuma ta ɗauki plate ta zuba abincin kaman yanda yace sannan ta kawo ta ɗora akan table ɗin da ke gabansa. "Yaya shikenan?". yay shiru bai ce mata komai ba, ita ma bata miƙe daga duƙen da take ba, ya ɗauki spoon ya fara kai lomar tuwon bakinsa, duk zumuɗinsa na son yaci tuwon memakon yaji daɗinsa sai yaji wani ɗaci ya ziyarci saman harshensa, dan haka yay saurin maida spoon ɗin ya ajiye ya sauke ƙwayar idonsa biyu a tsakiyar kan Nawwara. "wa ya dafa abincin nan?". ta ɗago ta dubi yanda yake yatsine fuska kamin tace,"Yagana ce, wani abu kaji a ciki?". "ɗaci naji, may be ta haɗa da wani abun bata sa ni ba". a ladabce tace,"ƙila daga bakinka ne, tun da har baƙi ma sun ci kuma ba su yi ƙorafi ba". "ci". ya faɗa yana mai mata nuni da plate ɗin da idonsa. "Yaya bakinka ne kam, ni banji komai ba". ta faɗa bayan tayi spoon ɗaya. hannunta taji ya kamo wanda yasa tayi saurin ɗora ƙwayar idonta akan babban yatsansa da ke shafa kan fatarta, kuma kamin ta kai ga haɗiye yawun da ke maƙogoronta taji yace,"wannan ƙonuwar fa?". ƙirjinta na bugawa tace,"jiya ne manja ya zubo min". "kuma shi ne ba'ai treating ɗin wajen ba?". a shirun da tayi kawai ya fahimci bata gane me yake nufi da treating ba, dan haka ya ɗaga mata gira,"ina nufin me yasa ba kuje chemist ba". "ai naga kaɗan ne bada yawa ba, kuma ma Anty Maryam ta min tofi a wurin". ya saki hannun nata yana jinginar da kansa jikin kujera sannan yace,"shiga bedroom ena wajen gado ki ɗauko box ɗin first-aid". ta inda tasan first-aid box ranar da Maryam taji ciwo Ahmad ya naɗe mata hannun da bandage, dan haka ko da ta shiga ɗakin bata jima ba ta fito ta kawo masa. "zo ki cire min wannan". yace da ita yana mata nuni da zaren da aka naɗo hannunsa zuwa wuyansa, ta miƙe ta cire sannan ya miƙar da hannun nasa a hankali cikin ƙarfin hali da dauriya sai rumtse ido yake saboda zafi. gefensa ya matsa yace ta zauna, ta zauna a ɗarɗarce saboda wani baƙon al'amari da ta ke jin kanta aciki, kuma har ya fasa ƙunar ya shafa magani ya naɗe mata wurin bata sa ni ba, sai da yay magana tukunna tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa a lokaci ƙanƙane, kuma sai a sannan ta ke jin zafin ciwo. "ki shirya gobe za ki fara zuwa school, da safe Mu'azzam zai kai ki, sai kiyi ƙoƙarin kammala ayyukanki da wuri". bata san lokacin da ta silalo daga kan kujerar ba ta zube gwiwoyinta biyu a ƙasa ta shiga yi masa godiya babu ƙaƙƙautawa har sai da ya dakatar da ita, tukunna ta miƙe ta bar ɗakin cike da farin cikin da ta ke jin tamkar an mata albishir da gidan Aljannah, Allah ya sani ita ma'abociyar son karatun boko ce amma iyayenta basu da halin da za su kaita makarantar boko, domin a samu a sakata a makatantar boko zuwanta aikatau na daga cikin dalilin amincewar mahaifinta, gashi yau Allah ya cika mata burinta tun ba ai nisa ba, dan haka har mutuwarta ba zata fasa saka Ya Kabir acikin adu'arta ba kuma ba zata taɓa mantawa da shi ba. tun bayan fitarta yake jinsa wani iri, ga shi natsuwar da ya ke neman ya samu ta gagara, ya ɗauki waya yafi sau goma zai kira Ahmad amma sai ya mayar ya ajiye ya fasa kiran, dan haka domin ya sami sauƙin abin da yake ji ya ɗingiso ya fito shaƙar iskar waje, yana fitowa harabar gidan ya tarar da Mu'azzam da Lukman su na shigowa gidan, ya buƙaci da su zauna anan kan kujerar da ke compound ɗin suyi hira ko ya samu ya ɗebe kewa. da suka zauna hirar tasu duk akan kasuwancinsu ne, inda yake daɗa ba su shawarwari akan harkar business. hirar su ke amma gaba ɗaya hankalinsa ba'a kansu yake ba yana bakin gate, yana jiran shigowar motar Ahmad amma shiru shiru gashi har ƙarfe takwas da rabi saura. ya buɗe baki zai ce da Lukman ya kira shi a waya kenan sai ga horn ɗin motar, har motar ta shigo ta faka bai sami natsuwa sai da ya ga Basma ta fito daga motar, tukunna ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. ta cikin hoton abin da ke haskawa acikin duhun idonsa yaji Basma a kusa da shi ta kamo hannunsa da faɗin,"Ya Kabir yau kaji sauƙi ka fito?". ya buɗe idonsa ya sauke a kanta da murmushin da a kallo ɗaya zaka gane da wani ɓoyayyan abu a tattare da shi. "na sami lafiya Basma...ya akai ku ka daɗe?". "Yaya ce bata da lafiya muka wuce asibiti". da mamaki ya ke dubanta da tambayarta,"rashin lafiya kuma? ina ce lafiya ƙalau ku ka fita?". "ehh Yaya ai ko acan ma sai a hanyarmu ta dawowa ne ƙirjinta ya fara ciwo, kuma da muka je asibiti likita yace asthma ce". "what?". yay tambayar muryarsa na amayar da tashin hankalin a cikinta. kafin Basma ta kuma cewa wani abu sai ga Ahmad yazo ya wuce da Maryam ya ɗaukota a hannunsa. da lokacin da yay azamar miƙewa tsaye zuwa san da ya faɗa part ɗin Yagana har yay tsaye a bakin gadon da Maryam ke kwance duk bai sa ni ba. tun da yay tsaye a bakin gadon kallon fuskarta yake da wani abu da ke tsargawa ajikinsa from head to toe. bacci ta ke peacefully, sai numfashinta da ke up and down da sauri sauri, yana kallon laɓɓan Ahmad da ke yiwa Yagana bayanin abin da ya faru amma baya jin maganar da yake a cikin kansa, da ƙarfi kuma ya cije leɓensa na ƙasa ganin yanda hannun Ahmad ɗin ke cikin nata yana murza ma ta tafin hannu a hankali. sai ya rumtse idonsa da ƙarfin gaske ba tare da sanin lokacin da ya ɗauko wayarsa daga aljihu ba ya dannawa Abdurrahim kira ba, kuma bugu 1,2,3 ya ɗaga. daga can ɓangaren Abdurrahim ya shiga yi masa tsiya yay saurin dakatar da shi. "Abdurrahim ya isheka". "to sarkin matsifa ya akai?". "Abdurrahim bana so tafiyata ta wuce tsakanin gobe da jibi". abin da yace da shi kenan ya kashe wayar, sannan ya ɗora ƙwayar idonsa akan Ahmad da fuskarsa ke nuna tsantsar damuwa. da sassarfa yasa kai ya fice daga ɗakin, halin da ya ke ciki a yanzu ya mantar da shi ciwon da ƙafafunsa ke masa, sai dai yana zuwa parlo bugawar da zuciyarsa keyi ta tsaya cak ganin Nawwara, bata lura da shi ba a san da tazo wucewa ta gabansa sai ji tai an fizgo hannunta da ƙarfi ta dawo gaban mutum ta tsaya, hucin zafin numfashinsa na sauka saman fuskarta, inda shi kuma idonsa ke kulle yana ƙara matse hannunta da ƙarfin gaske tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa, jikinsa kyarma kawai yake yi, ƙoƙarin janyota jikinsa yake ya rungume, wataƙila ya sami sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke yi masa a ɗumin jikinta. *Ethiopia, Masarautar Baharar.* a cikin tangamemen parlon, wasu tsaffi ne su huɗu zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale a saman tiles ɗin parlon, sun ɗora hannayensu akan tumtum ɗin da ke aje a gefensu, yayin da wasu dattijawan Mata guda uku ke daga kan kujera a zaune, sai Suhail da ke kan tashi kujerar shi ma yana mai kaɗa ƙafarsa guda ɗaya, idanuwansa a kulle yana ci gaba da sauraron abin da Bella ke faɗa masa na ga me da saƙon mai Martaba akan aurensa da Maryam. *Plss vote,share&comment.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *(41)* _"Aure! Aure dai! ana nufin babu aure tsakaninsa da Maryam?, yarinyar da ya saka a ransa tun bayan rasuwar matarsa Sanah, to me yasa ma za ai masa haka?"._ zancen zucin da Suhail keyi kenan tun a lokacin da ya kai maganar yana son ya auri Maryam gaban Mai Martaba, kuma har zuwa yanzu da Bella ke ƙara isar masa da saƙon Mai Martaba ɗin na cewar dole ne ya haƙura da batun auren Maryam saboda ƙarfaffan dalili. "Suhail ko kana son ji ko baka son ji Maryam ta haramta gareka, ka zama uba a gareta wajan shayarwa tun da har kunsha nono ɗaya kai da mahaifiyarta...dan haka the charpter close kar na ƙara jin zancenta daga bakinka...ka nemi wata macen kawai". Bella ke maganar cikin ɗaga murya me fitar da sautin faɗa. ya buɗe ido ya kalleta haɗe da sauke dogon numfashi. maganar mahaifiyarsa ta ratsa ta cikin baƙin cikin da yake ji a zuciyarsa. "ni ban san ma dalilin da ya sa baka son Zeenatu ba wallahi, yarinya me hankali da tarbiyya, ga ilimi, tana sonka ba wai bata sonka ba amma sai watsi kake da lamuranta...tukunna ma kana tunin zaka sami macen da zata iya riƙe maka ɗanka da amana ne sama da Zeenatu?". ya mayar da ƙwayar idonsa kan Hajiya, murya a ƙasa yace. "dan Allah Hajjah ki bar min zancen wannan yarinyar, mene haɗin daddawa da kunu?...ni ko banyi wani auren ba zan iya kula da Arif, dan shi ɗaya dai Allah na tuba". Hajjah ta bishi da harara, Bibi(Kakarsu Akila) tace da shi. "ai ni yanda na fahimci take-takenka Suhail so kake kaje ka auro wacce ba jinin sarauta ba. ba kuma zamu lamunta ba, kasan da wannan". yace,"amma Bibi fisabilillahi shikenan sai ace dan kai ɗan sarauta ne auren bare ya haramta a gareka, a wanne hadisin ko ayar aka ce haka?...magana ta gaskiya ni bana son Zeenatu ba kuma zan aureta ba, kuma ni ba ƙaramin yaro bane da za'a min dole a wajen aure, like i said zanyi breaking record for sure". yana faɗin hakan ɗacin da ke ƙasan zuciyarsa na haskawa a saman fuskarsa. "to in haka ne ka koma ka nemi auren ita yarinyar da ta asirceka mana...". Maama tayi maganar, bata kai ga ƙarasawa ba yay saurin cewa,"wa ɗin?". tayi guntun murmushi,"ah tou Suhail wadda tayi asiri akan samun soyayyarka ai masoyiya ce ta haƙiƙa, dan haka a shawarance kawai kaje ka nemi aurenta yanzu tun da ta tuba, kuma ina baka tabbacin zaka sami tsantsar soyayya daga gareta kamar yanda ta nuna maka, ni naga hakan a ƙwayar idonta ta cikin vedio call ɗin da akai da su, kuma ƙwarai haƙiƙa zata kula da Arif". yay guntun murmushi na takaici,"ai ko matan duniya sun ƙare babu abin da zanyi da wannan abar kam, kima daina wannan zancen Maama, haƙurin da nayi ma ban hukuntata ba wallahi darajar Maryam taci". "to yanzu dai ai an faɗa maka kuma kaji, wata ɗaya kacal Mai Martaba ya baka...kuma Suhail Zeenatu kawai zaka aura muyi farinciki da aurenka". ya dubi Bella da kyau sannan ya taje gemunsa da yatsunsa, kana ya miƙe tsaye yana zira hannu a aljihu da nufar hanyar fita yana faɗin,"ni dai na faɗa zanyi breaking record, kamar yanda ba zanyi auren zumunci ba haka matar da zan auro bata da alaƙa da sarauta, idan ta zama mallakina ta sami wannan jinin". Bella ta bishi da faɗin,"ka jima ba kai breaking record ba Suhail...zamu gani mu da kai wa ya isa da wani". a hanyar lambu ya tarar da Jawad, suka wuce ɓangrensa tare. inda yana shiga ya sami baiwar da ke aiki a ɓangarensa tana jera kayan abinci a saman dining. tana ganinsa ta zube ƙasa tana miƙa gaisuwa, ya amsa mata fuska a sake sannan ya wuce bedroom nasa ya bar Jawad anan parlo. ya ɗau kusan minti goma sha biyar kamin ya fito, a parlon ya sami Jawad na ma Arif wasa wanda aka ɗauko shi daga makaranta, ganin ɗan nasa yay smiling ɗin da haƙoransa suka ƙi rufuwa, dan matuƙa yana son Arif da tausayinsa. Mamansa ta rasu tun a ranar da ta haife shi dan ko ganinsa ba tayi ba ta amsa kiran ubangijinta. shekaru huɗu kenan da rasuwarta har yau kuma ya kasa ƙara aure saboda Arif, ya kasa mantawa da ita, gani yake tamkar yaci amanarta ne idan yay tarayya da wata macen, kuma yana ganin kaman duk wadda zai aura ba zata riƙe masa ɗa da amana ba, haka ɗan ba zai ji daɗin zama da ita ba...tun bayan rasuwar matarsa Sanah bai ƙara jin son wata ƴa mace ba sai akan Maryam, wadda kawai yaji yana kwaɗayin ya mallaketa kuma zuciyarsa tayi masa amanna da cewar yarinyar zata iya kula masa da Arif gwargwadon yanda yake buƙata, duk da yasan cewar ita ma Maryam ɗin rainonta ne zai yi, to ashe ita ɗin ba rabonsa ba ce. a hankali ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya kira sunan Arif din, Arif ya sakko daga kan cinyar Jawad ya tafi wurin mahaifinsa da gudu shi kuma ya ɗauke shi ya rungume shi ajikinsa yana ta sumbatar fuskar

Chapter 39 of 52