anan, kuma za ki kalla mai zan maki". a raunane tace da shi,"dan Allah Ya Kabir kayi haƙuri, wallah yau ne kawai banje ba". ya doka mata tsawa,"comon shut your mouth up". sai tayi shiru kaman yanda shi ma yay shirun, can kuma yay nisa yace,"ke me yasa ba'a maki ƙunshin ba?". tace,"mutane sun yiwa mai ƙunshin yawa, tace na bari zuwa gobe idan ta gama yiwa kowa sai ta yi min". sai ya saki guntun tsaki na haush yace,"ita ɗaya ce me yin lalle a duniya?". tana girgiza kai tace,"a'a, Yagana ce dai tace ita zata yi mana". tayi maganar duk a tsorace saboda yanda taga duk ya rikiɗe nata zuwa wani Ya Kabir ɗin na daban, wancan mai sanyi ne amma wannan a zafafe yake. tana cin jinsa ya ƙara cewa,"kuma ita mai ƙunshin da aka ɗaukota sai akace idan ta gama yiwa kowa na gidan ta tsallakeki ta gama yiwa baƙin da suka zo kafin ke ɗin ko?". bata ba shi amsa da baki ba ta girgiza masa kai kawai. ta ɓangarensa yay shiru yana janyo leɓensa na ƙasa cikin bakinsa, ya tsotsa for 1minutes sannan a hankali muryarsa ta fito da cewa,"kar ki wanke gashin, ƙunshinma ko da an ce kije ayi miki karki je. ki jirani na dawo, am on my way, in the next 5hours zan iso insha'Allah, be ready da na dawo zamu fita". murya na rawa tace,"to Allah ya dawo da kai lafiya". sai taji yace,"tsorona kike ji ne?". tayi saurin kaɗa masa kai alaman a'a. "to ɗago ido ki kalleni kiyi adu'an". ta ɗago tana kallonsa tace,"Allah ya tsare hanya, ya dawo mana da kai lafiya, ya kareka da kariyarsa". "ameen ya Rahman...thanks to you. ki nemi abinci kici kinji ko, idan hidiman bikin yasa baku tanadarwa cikinku komai ba ki jira a parlo zan taking maki order yanzu". "ai zuwa anjima za'ai girkin". bai bi ta kan maganar tata ba yace, "me kike son ci?". ya tambayeta with full of concern. tace,"Yaya ba sai ka kashe kuɗi wurin saya ba. aiki ne ma ya min yawa shi yasa ban samu naci ba, yanzu da na gama yankan farcen zan ci". a lokacin da take maganar ji yay kaman ya zura hannu ta cikin wayar ya fizgota zuwa gabansa, yay mata kashedin muhimmancin cikinta a wurinsa da kakkausar murya ko ta samu ta shiga hankalinta tayi masa shiru da wannan surutun wofin. kuma a yanda ita ma take kallon idonsa tana iya hangowa da a kusa da ita yake zai iya ma ke bakinta.
ta cikin shirunsa da yay yana jifanta da wani hargitsatstsan kallo maganarta ta kutsa ciki da faɗin. "Yaya zan ci abincin". fuska a haɗe kamar hadari yace,"me za ki ci?". "komai aka samu Yaya". sai ya gyaɗa kawai, ba tare da yace komai ya kashe wayan, kuma kashewan nasa yay dai-dai da shigowan Basma ɗakin.
"ba sai ki faɗi mani Ya Kabir ne a waya ba kuma kawai sai ki bani ki wuce". Basman ta cuno baki tana miƙa mata hannu da cewar,"oho ni nayi zaton kin gane nufina". Nawwara ta ɗau wayan ta miƙa mata jikinta a sanyaye. Basma ta kuma cewa,"Yarinya kuma yanzu Yaya ta zo". wannan fargabar da Nawwara keji tun a ɗazu ta gushe jin ambaton Maryam tazo , ta miƙe cikin jin daɗi tana faɗin,"tana ina?". "see you kika wani miƙe, to ai har ta tafi". Basma ta faɗa tana dariya. "are you serious?" "wallah, ita da Ummi ne fa, kin san sai yau ta dawo daga Qatar ɗin, kamin su wuce Abujan Ummi tace bari tazo ta gaida Baba". Nawwara na murmushi tace,"Allah sarki Yaya naso na ganta wallah. anyway sai gobe ma haɗe a wurin dinner, Allah yasa dai aje da ni". "karma ki saka ran zuwa, saboda gidan duka za'a daɗe Yagana ma tace sai taje". sai kawai Nawwaran ta gyaɗa kai da rashin jin daɗi a ranta, ta fita domin ci gaba da aiki.
tun da ƴan biki suka fara zuwa bata zauna ba, duk da cewar akwai iya yanzu da suke aiki tare wadda Kabir yasa aka kawo ta ke tayata aikin, ba damar ta zauna waccan zata bijiro ma ta aikinta, tun ma masu ƴaƴan nan, ita ce wankin kashi, wankin kayan yara, ga ƙawayen Adawiyya ma motsi kaɗan sa ƙwala mata kira. hakanne yasa duk jikinta ke ciwo babu abinda ta ke so a wannan lokacin irin tayi wanka ta ɗan miƙe ko yane ta huta, to amma ita da hutawa sai in kowa bacci yay a fidan.
****
Habib da ke daga kishingiɗe akan 3seater ɗin ɗakin Ahmad, ya ɗan waiwayo kaɗan ya kalli Ahmad ɗin da ke shafa oil akan askin da yay a ɗazu. Yace,"Ahmad tela ya kawo sauran kayan nan kuwa?".
"kai bama dolensa ba. kayan fa da zan saka ne gobe a wajen dinner". Mubarak da ke gefe ya fashe da dariya sannan ya ce,"Daren farko mai sanya zumuɗin angwaye. Ahmad na lura gaba ɗaya a ƙagauce kake da zuwan jibi, gaba ɗaya tun da akace an wayi garin yau ka kasa sukuni". Habib ma na dariya yace,"kai baka jishi bane da muka dawo daga masallaci, ya dokawa Maryam ɗin kira da sanyin asuba wai Mai Kyau 2days remaning fa ki zama mallakina". Ahmad yay dariya da cewa,"Kai dai Habib anyi munafuki. shi yasa ban so kazo ka tare a gindina ba, ba dama nayi waya da matata kunnenka na wajen". Habib yace,"ni wane sa'ido ne baka min ba a lokacina". Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wani ɗan lokaci, hakan ya bawa sautin tv'n da ke kunne damar fitowa sosai. Jim kaɗan Mubarak ya yunƙuro zaune yana cewa,"Yauwa! ya maganar zuwan Umar M. Shariff wurin dinner?". Habib ya kalle shi yana ba shi hankalinsa da cewan. "naso jiya mun sake komawa da Saifullahi office ɗin Umar M Shariff ɗin, amma yau Mai Shadda yace muje around 4 mu same shi sai muje can office ɗin nasa tare, tunda akwai fuskar sani ai ba yayi denying zuwan ba". "Yauwa hakan ma is oak, dan ina son zuwan gayen nan wajen wallah, ina matuƙar ƙaunar waƙoƙinsa over". Ahmad ya ɗan muskuta kaɗan a inda ya zauna yanzu sannan yace,"kuna ta batun M Sharif banji kuna maganan zuwan Moh-bad ba, after all kun san da cewan shi Mai Kyau tafi buƙatan zuwansa wurin". Mubarak yace,"sha kuruminka angon ƙarni, wannan ai su Jemi sun gama magana da shi, har kuɗin buking nasa duk sunyi payment tun last week".
Ahmad ya ƙara cewa," ƙwamma hakan dai kam. a burge Matata da Ƙawayenta shi yafi, ba wai taku buƙatar ba". ya numfasa sannan yaci gaba da cewa,"ni ina ta jibi, ita tana ta gobe dinner, ai na faɗa mata ta shiryawa jibin nan a jarumarta". Habib ya kai hannu ya doki kafaɗar Ahmad yana cewa,"Ango sarkin zumuɗi, me kana ci na baka na zuba ne. kaman yaune fa, kuma wannan daren dai da ka ƙwallafa rai akansa kaman yanzu ne". dukansu kuma sai su kai ƴar dariya, kuma a wannan lokacinne Nawwara ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shigo. daga bakin ƙofar ta duƙa ta gaida su sannan ta wuce kan ƙaramin table ɗin da ke daga can gefe ta aje tray ɗin flask ɗin abincin da ta shigo da shi.
sannan ta ƙarasa ta bawa Ahmad wayarsa tukunna ta fita ta bar ɗakin. tana shiga parlo taji landline na ƙara, ta ƙarasa da sauri ta ɗauka domin bata manta da maganar Kabir ba. tana ɗagawa deliver Man ke sanar mata yana bakin gate, tace ya bawa mai gadi sannan ta shiga ɗaki ta ɗako hijab ɗinta ta fita taje ta amso.
tabbas a duniyarta bata taɓa ganin mutum mai nutumci, karamci, tausayi, mutuntawa irin Ya Kabir ba, hakan yasa mutumin ke daɗa shiga ranta a kullum, kuma har abada ba zata manta da shi da alkhairansa gareta ba, kamar yanda a kowacce sallah ta kewa kanta adu'a haka shima ta ke masa, kuma kaman yanda ta kewa kanta adu'ar samun miji na gari haka shima take masa adu'ar samun mata ta gari. tasa fork ɗin da ke hannunta ta datsi naman gandar da ke cikin takeaway tare da yin bismilla ta kai bakinta...tana fara tauna ta lumshe ido saboda daɗin ɗanɗanon da ya ratsa harshenta da bakinta, taci green banana salad ɗin kaɗan, sai bayan ta gama tama sha ruwan swan ɗin da ke haɗe sannan ta lura da maganin da ke wata farar leda ta daban, ta ɗauko shi tana duba sunansa da akasa provigil, sai kawai tayi murmushi ta ɓalla ta sha guda ɗaya kaman yanda taga an rubuta ba tare da tasan ko maganin menene ba. sai dai tana sha ɗin bayan ta fito daga wanka sai ta ɓingle akan katifarta bacci ya ɗauketa, haka iya ta shigo ta dinga tashinta amma bata tashi ba, ƙarshe Yagana tace a ƙyaleta ta huta dama ta gaji ai da yawa.
*Please Comment, Share & Vote.*
[7/18, 10:10] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*(46)*
*8:30am na safiya.*
"ina Nawwara?". Kabir da ke tsaye a bakin entrance na parlon Inna Zulai ya jefa tambayar ga Jamila. "Yaya ba zata wuce part ɗin Yagana ba". sai ya zare hannunsa na dama da ke zube cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya sose gemunsa a san da yake kallon sashin Yagana, ya ɗauki kusan daƙiƙa uku yana kallon sashin kaman baƙonsa, nazari da tunani yake akan ta yanda zai iya shiga part ɗin Yaganan da yake ɗinke da jama'a ƴan taron biki da suka zo, ya ratsa su ya wuce zuwa inda zai sami Nawwara ya kamo hannunta ya fito da ita, yay ɗakinsa da ita ta shirya acan sannan ya ɗauki mota ya fita da ita zuwa inda ya gama tsara zai kai ta a gyarata kaman kowa, abin da ya tsara a jiya kenan da zarar ya dawo. sai dai abinda ya hana faruwar hakan tun a jiya baccin da tayi, lokacin da ya dawo tana bacci bata tashi ba, kuma ko da ya shiga ɗakinta ya taɓa jikinta sai yaji da ɗumi da alama ma akwai zazzaɓi jikin nata, wanda ya lura da hakan tun a lokacin nan da yake waya da ita. idanuwansa sun kalleta tar kuma sun fallasa masa yanayi ne na ƙarfin hali takeyi saboda babu yanda ta iya, matsayin ƴar aiki ta ke a gidan bata da batun cewar zata huta kaman yanda ta ke so, hakanne yasa ya haɗo mata da wannan maganin saboda bacci me nauyi ya ɗauketa, ta yanda duk irin tashin da za'a yi mata ba zata san ma ana yi ba, sannan ya saukar mata duk wata tarin gajiye da ke tare da ita da ma sauran ciwukan da ke jikinta.
kuma abin da zai iya cewa shi ne tun a daren jiyan zuwa yanzu da yake tsaye anan hankalinsa da tunaninsa na kanta, yana kan son sanin a wanne hali ta ke ciki, taci abinci?, ta samu damar yin wanka?, ciwon da ke damunta ya warke?, gajiyar jikinta ta barta?, sannan kuma ya tambayeta me take so?. kwanaki da kwanaki kenan yana jin wani abu na wucewa har zuciyarsa akan yarinyar, ya rasa menene shi, abun da kawai ya sani yana so ya zamana yana kasancewa tare da ita, yana so ta sake da shi ta dinƙa faɗa masa wannan ɓoyayyun sirrikan damuwar da ya lura tana tare da ita tun farkon zuwanta gidan, ya sani ba zai magance mata komai ba, amma zai yi duk mai wuyar da zai yi dan ganin ya rabata da damuwar da mutum zai ke iya tsinta a tare da itan.
sai kawai ya kulle idonsa ya buɗe tare da fuzgar da iska daga bakinsa, shi kansa ya san ya sauya 100%, ba ya da walwala a yanzu, ba ya da sukuni, ba ya iya sakewa da mutane, yanayin fara'arsa ta sauya, kullum zuciyarsa matsewa take, forsure yasan ya canja daga Kabir ɗin shekarun baya da yawa, kuma kullum ƙaryata zuciyarsa da Abdulrrahim ya ke akan cewar Soyayya ce ta maida shi hakan, shi ai ba ragon namiji bane, dan haka mace da soyayyarta basu isa su lugwigwita shi ba, basu isa su sauya shi daga Kabir ɗinsa ba, abu ɗaya ne yanzu dunƙule a zuciyarsa, kuma ya kusa kora shi ya wuce da abinda yake ganin shi ne mafitarsa, nan kusa ba sai an kai ga nisa ba, a gobe ba jibi ba. ya sani aure ya ƙunshi abubuwa guda uku; abota, aminci da yarda, sannan so da ƙauna. tabbas waɗannan su ne ginshiƙin aure, in har da su aure zai yi inganci da ƙarko, to sai dai anya ba zai yi kuskure ba akan abinda ya gama yanke tabbatuwar faruwarsa a gobe?, idan shi akwai waɗannan abubuwa ukun to ita fa?. ya sa ni baya tsoron komai goben kawai yake jira, babban fatansa shi ne Allah ya kai kowa lokacin.
ya kai hannu ya ciro wayarsa da ke ringing a aljihunsa, bai ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa kana ya kai kunnensa yana yin sallama. Akila ta amsa masa yanayinta babu yabo babu fallasa. "are you coming to Abuja?". "no Ummi". "but why?". "just like that". "but you will attend the dinner party ok?". bata jira cewarsa ba ta ƙara cewa,"Kabir i want to you to go to the dinner party please, don't say you will not go". to dama me ta ke tunanin zai hana shi zuwa?, zai je forsure, wata ƙila ma Dinner ɗin ta tashi ata mutane biyu, mutane ɗayan da aka shirya da mutane ɗayan da ba'a shiryawa ba.
Ya rufe murfin idonsa sannan yace da ita,"zamu zo insha'Allah Ummi". "kai da wa?". "mu biyu". Akila na miƙawa maid wasu kaya tace,"are you sure Kabir?". kaman yana gabanta ya gyaɗa ma ta kai,"ehh Ummi indai ba zai wuce nan kano ba zamu zo". Akila ta sauke numfashi daga inda ta ke kafin tace masa,"ananne mana za ai, komai ai a masarautar bichi zamu yi tarukan bikinmu".
bai ce da ita komai ba yay shiru yana sauraron bugun zuciyarsa da ke harbawa da sauri-sauri. ta katse shirun nasa da faɗin,"Kabir jikina sai yake bani kaman zaren wata ƙaddarar zai gifta kafin ɗaurin auren nan". nan ma bai ce komai ba yay shiru. ta ƙara cewa,"na kasa yardarwa kaina ba zaka mallaki Maryam ba. Kabir mai yasa ba zaka fito ka faɗawa su Baba abin da ke ranka ba?". yay wani gajeren murmushi a saman leɓensa sannan yace,"zan iya faɗa musu hakanne kaɗai idan Ahmad yace ya fasa kuma baya son Maryam. amma muddin Ahmad na sonta ba zan taɓa iya buɗewa kowa zuciyata ba yaga abin da ke dangane da Maryam ba. Ummi hatta raina zan iya sadaukar da shi akan ƙannena balle kuma wata aba soyayyar mace. dan Allah ina so ki manta da na so ƴarki, haka kuma ki daina kawo faruwar wani abu a ranki da zai hana auren nan domin ina son farin cikin ɗan'uwana, ni na cire soyayyar Maryam a raina tuni, zan kuma tabbatar miki da hakan wata ƙila a gobe".
Tayi murmushi mai sauti sannan tace,"kai ma kasan ba zan taɓa yarda da batunka na cewan ka daina son Maryam ba, duk wannan fiffizgewar da kake ƙarfin hali kawai kake, dakiya ce irin taka ta jaruman maza, amma yanayin maganarka kaɗai ya isa ya ƙaryata kalamanka, kuma kaman yanda na faɗa maka sam sam bana farin ciki da auren nan kamar yanda kai ma baka farin ciki da shi". "Ummi ya za'ai ki faɗi hakan. taya zanƙi farin ciki da auren ɗan'uwana, gaba ɗayanmu fa alkhairin auren nan muka nema, kullum cewa kike Allah ya bani ita idan har ita ce alkhairina, to tun da kika ga hakan ta kasance Allah ne zai mana sauyi mafi alkhairi tsakanin ni da ita".
yana gama maganar ɗiff yaji ta katse wayar. sai kawai ya girgiza kai, sannan ya fara tafiya sannu a hankali har ya kai ga parlon Yagana, yana shiga hayaniyar mutanen da ke zazzaune a parlon ana ta hira ta shiga kansa, ta ke yaji wani ɗan ƙaramin ciwon kai na neman kama shi, saboda haka ko tsayawa cire takalmansa bai yi ba ya gaidasu a tsaitsaye, da yake duk ƴan'uwana sai suke ta masa tsiyar ƙaninsa zai yi aure ya barshi, shi dai murmushi kawai yay bai ce musu ƙala ba, har wata Yayar Malam ƴar wan Babansu tace da shi,"Allah Kabiru kaji mun faɗa maka tazarar aurenku ba zata wuce wuta guda ba, wannan ai sai ya zama hauka, so kake ka zama tuzuru...ni shi yasa sam ban so wannan karatun nasaran ba, ga shi nan kun ɗauki aƙidarsu kuna amfani da ita, tsakani da Allah a tsarinmu mutanen ƙauye Ƴaƴanka nawa yanzu? kai ko kunya baka ji, Aminu yayi, ga Amadu zai yi amma kai wai Yagana ma ce min take ta karatunka kake bata aure ba, to naci uban bokon". kansa a ƙasa yace da ita,"za'a yi Umma, ai lokaci ne". daga faɗin haka ya wuce kai tsaye zuwa ɗakin Nawwaran, yana zuwa kuma ya tarar bata nan sai ƴan ƙunshin kayanta da jakar kayan a tsakiyar ɗakin, da alama tayi wanki ne tana haɗa kan kayan ko kuma ta fito da su dan zaɓan wanda zata saka. jin bai ji motsinta ba a ɗakin ya fito ya koma bedroom ɗin Yagana. tana ganinsa kuwa ta taso tana faɗin,"ɗan albarka ya akai?". yana kanne idanu yace,"ranki ya daɗe babu komai, ganinki kawai nazo yi". sai ta kaɗa kai kawai tana cewa,"ni kuwa kaga jiya gaba ɗaya banyi bacci me daɗi ba. ramar nan taka na bani tsoro Kabiru, duk yanda akai akwai abin da kasa a ranka yake damunka, dan Allah ka taimaka ka faɗa min, na san ban isa na rabaka da ita ba amma zan maka adu'a Allah ya yaye maka koma menene". ya wadata fuskarsa da murmushi a san da idanuwansa suka hango masa Nawwara ta fito daga toilet ɗin Yagana riƙe da wani yaro, alama kuma ta nuna masa wanka ta yiwa yaron tun da gashi nan naɗe cikin zane, ita kuma hannunta da ƙafarta duka da ruwa, ya shafa fuskar Yagana yana faɗin,"Yagana ki kwantar da hankalinki babu abinda ke damuna, idan ma akwai to komai yazo ƙarshe insha'Allah". ba hakan taso ba sai dai bata da yanda ta iya da shi, bata so ta takura masa sam. "to kaci abinci?". yasa hannu yana shafo bayan wuyansa yayinda idanuwansa ke kan ƙafar Nawwara yana bin yatsun ƙafarta da kallo, yace da Yagana. "ban ci komai ba tukunna. na ɗan fita ne sai yanzu na dawo". cikin dabara kuma sai yace da ita,"waccan yarinyar sam bata son tsafta, ana biki kowa na gyara jikinsa amma ita kalleta wani curkuɗe-curkuɗe". ya ƙarasa maganar yana haɗawa da ƙaramin tsoki.
Yagana ta waiga ta dubi Nawwaran da yake magana akai sannan ta dawo gare shi da cewan,"wallah ba laifinta bane...aiki ne ya mata yawa bata zama, kaga ɗazu ma har ta zauna za'a mata ƙunshin kuma wannan yaron sai yasa kuka, shi kuma uwar tazo ba lafiya shi yasa dole ta tashi". a lokacin ji yay kaman ya haɗa uwar yaron da yaron ya yarfa masu zagi, sannan yaywa Uwar yaron kashedin kar ta ƙara saka masa Mata rainon ɗanta tun da ba ita ta haife shi ba, kuma a cikin kuɗin aikinta babu na raino, ba kuma raino aka ɗaukota yi ba.
lokaci guda ɓacin ransa ya ƙaru yana me cewa da Yagana. "jiya ma bata je makaranta ba yauma haka. ɗazu Principal ɗin nasu ya kirani ai...tazo ta sameni a ɗaki su yi magana da shi". Yagana tace,"to Allah yasa su karɓi uzurinta, ni ban san hakan zai zama da matsala ba da ban hanata zuwa ba". shi dai juyawa kawai yay yana daɗa faɗawa Yagana,"ta taho min da kayan abincina".
Kwata-kwata Nawwara bata lura da shigowarsa ɗakin ba, sai lokacin da furucinsa na,"bata je makaranta ba". ya shiga kunnenta. A lokacin ne ta ɗago kai ta gansa, idonta ya shiga cikin nasa, kuma haka kawai ƙwayar idonta ta haska da wani irin tsoro da fargabar da bata taɓa ji ba, bata san ya dawo ba sai cikin dare da ta farka taga kwalaben madarar waken suya acikin leda har guda uku, da kuma tufa guda shida, da bunch na ayaba, kuma a wannan lokacin yunwa ce ta tasheta, dan haka ta tashi Iya dan neman izininta akan taci, tun da babu damar ta fita yanzu neman abinci, ta san ba zata samu ba dan yanzu abinci baya saura a gidan.
ko da Iyan ta tashi ta faɗa mata ai tsarabar Kabir ce da ya dawo, ta tsorata sosai da irin baccin da tayi dan tun sha biyu na rana ita ce sai 11 da rabi na dare ta farka, baccin da zata ce bata taɓa yinsa ba tun girmanta, sai dai taji daɗin yanayin jikinta sosai, wannan ciwon kan ya ɗauke gaba ɗaya, haka duk inda ke mata ciwo ajikinta ya saki, amma tayi mamakin baccin sosai. kuma murɗawar da cikinta keyi yasa ta aje mamakin a gefe ta shiga cin tufar tana korawa da madarar waken suyan, tana sha tana lumshe ido daɗinsa na ratswa har cikin kanta.
fatanta ɗaya ne a yanzu Allah yasa bai ganta ba, dan a yanda ta tsara sai lokacin dawowa daga makaranta yayi zata je ta gaishe shi, kuma jin yace ta kai masa abinci taji wani abu me kama da tsoro shi kaɗai ya dira a ƙirjinta. kallonsa take har ya ɓace daga bakin ƙofar ɗakin sannan ta ɗauke kanta da sauri ta shiga shafawa Abbas mai ajiki, jikinta sai rawa yake kamar wacce ta yiwa sarki laifi, yanayin fuskarsa take tunawa da yanayin furucinsa, da kuma kalmarsa na cewar zai yi mata exams idan ya dawo, me zai faru idan ransa ya kai ga ɓaci yace ya zare hannunsa daga ɗawainiyar makarantarta?, zata iya ɗaukan wannan ɗanyen hukuncin?, tana ganin kamar ƙwallafa ran da tayi akan karatun bokon zai iya mata illa a duk san da akace yau karatun ya datse mata?, ya zama dole ma taje ta ba shi haƙuri tun kafin zuciyarsa ta gama yanke hukunci.
dan haka da sauri ta ƙarasa shirya Abbas ta saɓe shi ta goya shi, daga yanda take nishi zaka gane goyon yaron yaywa ƙirjinta nauyi, ta fita a ɗakin cikin hanzari tana jijjiga Abbas dan yay bacci. ba ta kai ga tsakiyar parlon ba kiran sunanta da Yagana tayi ya tsayar da ƙafafunta a lokaci guda. "ga kayan abincin Kabiru can na haɗa, ki ɗauka ki kai masa ɗakinsa". "tom Yagana". sai Yagana ta bita da kallo tare da jefa mata tambayar,"lafiyarki kuwa na ganki kamar a firgice?". tayi saurin girgiza kai da cewan,"a'a babu komai Yagana". Yagana ta kaɗa kai kawai ta wuce ta barta, ita kuma ta nufi kitchen ɗin har tana tuntuɓe.
****
*76 Kafe District, Asokoro, Abuja.*
"i will definetly teach her a lesson, ni ba shashashar matan nan bace da zan bar ƙawa ta ƙulla alaƙar gaisawa da mijina ko saurayina. ni kika sani dan haka da ni za ki zumunci, so Aisha Tayo tell your that stupid friend kar ta ƙara kiran Yaya ko da sunan menene ma, in ba haka ba kuma wallah zata ga ɗanyen hauka". Shamsiyya Sani da ke daga kan gadona a kwance ta bushe da dariya tana yunƙurawa zaune.
"wallah ke dai Maryam anyi masifaffiya, wannan wanne irin kishin jaraba ne. ance miki kiransa fa kawai tayi ta tambaye shi ke saboda tana ta kiran wayarki bata samu ba, amma kinzo kin ishi mutane da bambami". naja tsaki na miƙe daga kan kujerar da nake, na kalli Shamsiyya Sani na banka mata uwar harara kafin nasa kai na fice daga bedroom ɗin, ina jinta ta rakoni da dariyar da ta ƙara ƙular da ni, idan na dawo ciki sai munyi faɗa sosai da ita, to matsalar ina son Shamsiyya.
kai tsaye ɗakin Mami na nufa sai huci na ke, su huɗu na samu a ɗakin su na arraging gift ɗin da za'a bada a wurin dinner, baka jin komai sai ƙarar acn da ke hurawa a ɗakin, da alama yanda suke magana a hankali lissafin kayan suke ba kuma sa so ya kubce masu. na nemi bakin gadon Mami na zauna
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 52