Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ayar tambaya . ai yanda Marigayiya ta dinƙa ƙumbiya ƙumbiya da ke na soma shan jinin jikina, to tunda asiri ya tonu sai kizo ki fi ce ki bar mana gida ki koma inda aka koroki dan ba za kija sunan gidanmu ya ɓaci ba. ina dalili haka kawai babu dangin iya ba na Baba. da ma Allah ba azzalumin bawansa bane, muna cikin gida an munafurcemu an ɓoye mana ai dole Allah ya saka mana". Kulu tai mutuwar tsaye tana duban Amarya da mamaki, sai dai ko kaɗan bataga laifinta ba. duk da cewar a zatonta ma ko Zulai ce zata tanka ma ta to amma ita bata ce komai ba sai ƴan habaice-habaice da ta hau yi, shi ma kuma da Malam ta ke. Yagana ta kama hannunta suka wuce ɗakin Gwaggo, tare da cewa Amadu idan ya idar da sallah ya faɗawa Malam tana nemansa. Yagana tasa gefen mayafinta tana gogewa Kulu hawaye, wacce zuciyarta ke gab da bugawa a halin yanzu saboda wani abu da ta ke ji yana taso ma ta. "ki bar kuka Kulu, ƙaddara ce a rubuce ta ke kuma babu wanda ya isa ya kauce ma ta, matuƙar kinyi imani to ki karɓeta a duk yanda tazo miki. Amadu ya sanar min da irin ɗibar albarkar da shashashar yarinyar can tayi, kiyi haƙuri ranta ne ya ɓaci kuma akwai ƙuruciya akanta dole ai ma ta uzuri, gani za tai koma mene laifinki ne kuma da gangan kika aikata, kafin ta fahimceki dole sai ki fuskanci ɓacin rai". Kulu ta saka hannu ta goge hawaye kan tace,"Yagana ni yanzu tashin hankalina ɗaya ne, idan ba'a riƙeta ba tabbas sai ta aiwatar da abinda ta faɗa. wannan ƙazantar har ina...". tai shiru na tsawon daƙiƙa saboda kukan da ya ci ƙarfinta."Allah ya jiƙan Yaya da ma ta faɗa, sai abin da na gani. kuma tun farko laifinmu ne da bamu nuna mata cewar nima uwa ce ba wai abar ƙyama ba, ta yanda ko ƙaƙane zata ji ƙaina a zuciyarta". Yagana ta shafa bayanta,"kinga komai fa zai zama da sauƙi, yanzu kawai dan tana kan dokin zuciya ne. da zarar ta huce shikenan zata tuna cewar ke ɗin nan kece dai Uwa, Uwar gaske da ake nufi bata wasa ba, Uwa me daraja". Sallamar Malam da Amadu ta karkata hankalinsu garesu, Yagana ce kawai ta iya amsawa, su ka nemi wuri suka zauna, daga ba ya kuma Kabiru ya shigo shi ma har lokacin jikinsa bai bar rawa ba saboda ɓacin ran da ke tare da shi. "ina Adamu". Yagana ta kira sunan Malam. "na'am". "yauwa kana jina ai, yanzu tun da anzo kan wannan gaɓar, to zaman Kulu a tare damu ya ƙare. da ma duk dan wa akeyi?, dan ita wadda ba'aso ta sani ne, to ja'irar yanzu taji komai ta kuma san wace ita. saboda haka kamar yanda muka alƙawaranta cewar duk ranar da Mairo ta girma mu kai ma ta aure to za ki faɗa mana inda iyayenki su ke mu maidaki garesu, to kana taka Allah na tasa ga shi yanda muka tsara ba hakan ce ta kasance ba. saboda ni anawa ganin tun wuri a gobe-goben nan ki shirya mu wuce mu tafi inda kika fito, dan ci gaba da zamanki anan babu abin da zai jawo miki fa ce tsangwama daga mutanen gidan nan da jama'ar gari...Adamu kana ina?". Malam ya ƙara amsawa,"gani nan Yagana". "to me kace?". yace,"ehh hakan shine dai-dai, wannan shi ne ma abin da ya kamata ayi tuntuni". Yagana ta kaɗa kai,"yauwa, to yanzu ke ina ne garinku?". "ni ƴar ƙasar Qatar ce". "ina ne kuma haka?". Kabiru yace,"can ƙasar larabawa ce, daga inda nake zaune bamu da nisa". Yagana ta wani zabura ta dafe ƙirji tare da waro ido,"kai dan manzon Allah?". "ƙwarai kuwa Yagana". Amadu ya faɗa. sai ta waiga ta dubi Kulu,"Kulu da ma wannan hasken naki na larabawa ne?, kai jama'a ni Rakiya inda raina nata ganin abin mamaki, to garin ya haka ta kasance, me ya jefoki wannan ƙasar tamu?". Malam da ke gefe ya bata amsa da,"Qaddara". Yagana ta jinjina kai da cewar,"ƙwarai sai ita ɗin kuwa, amma abin da mamaki, Kulu to dama kuna da ƴan'uwa ne anan ko kawai kurciyar da aka miki ne ta saukeki anan bichi?". Malam ya ƙara ce ma ta,"ai Yagana wannan kiristan ɗin da Mairo ta faɗa hannunsu san da ta ɓata shi ne yay ma ta cikin". da Yagana ta doka wani uban salati sai da ƴan tsakar gida suka ji, ta zabura ta miƙe tsaye tana karkaɓe zani, "kirista!, yo dama ke kirista ce shi ne har da danƙarawa kanki Hauwa saboda son zuciya. amma kuwa wannan mata ba ki ji daɗin halinki ba, yo ni fa ince ya za'ai musulman ƙwarai suka kasa amsar ƙaddara dan ubangiji ya jarabci ƴarsu da yin cikin shege, wallahi tun a lokacin lissafina ne ya kunce amma nayi ƙoƙarin in ce muje gaban iyayen naki naji ko islamiya ce basu je ba, ashema me ɗungurungun musuluncinma babu bare har ai imani da ƙaddara, taɓɗijam ashe jikar Yesu ce ke". sai da tayi shiru sannan Malam ya sami damar cewa,"Yagana bafa wai ita ce kirista ɗin ba, shi wanda yay ma ta fyaɗen shi ne kirista". tayi guntun tsaki,"to me maraba?, kirista ai ɗan uwansa kirista kamar yanda musulmi sai ƴar'uwarsa musulma". ta fuskanci Kulu da cewa,"to kinga Allah tun da dai anzo ga haka, ki tashi tun daren nan ki kama hannun ƴarki ku tafi, tun ubanta beji kuna nan ba, azo ai mana saukar aradu da ka muna cikin kwanciyar hankalinmu, ina mu ina jawa garin bichi faɗan arna". ta faɗa tana kama haɓa, Kabiru yay guntun tsoki yace,"kefa matsala ce da ke wallah". tace,"Kabiru gidan haya ma nan ya ganni ya ƙyale". yay kamar ya tashi ya bar wajen Amadu ya dakatar da shi. "Yagana ki gane mana wai, ita fa musulma ce shi kuma kirstan, anata miki magana da yarenki amma kin gagara ganewa". ta harari Kabiru tace,"ubana ɗaga muryarka ai ba ita zata sa na fahimta ba". sai kuma ta juyo ga Malam,"ka shiga tsakanina da Ɗanka". Malam yace da Kabiru,"kar na ƙara jin bakinka". Yagana ta dubi Kulu tana rissinar da kai a gabanta tace,"ashe da gangan kika turata can wajen ubanta, kika tashi hankalinmu anan mu bayin Allah. Allah sarki Suwaiba Allah ya saka ma ta. da kika san lokacin komawarta wurin ubanta yayi ai sai ki tattara ku tafi tare gaba ɗaya, mu san sallama ki kai mana, amma kina ganin yacca baiwar Allah nan Suwaiba ta kasance duk akan ƴarki, kika ja baki ki kai gummm saboda mugun hali irin na ku na arna, da ma ance kasa mutum a inuwa ya saka a rana". Kulu ta gigice tace,"wallahi Yagana bani na turata ba, ikon ubangiji ne kawai". Yagana ta taɓe baki,"daga baya kenan ingozi...ni wallahi da nasan kema kafirar ce ba zamu taimaka miki ba, tun da dama ai kun saba iskanci a junanku, to sai me dan kin haifi shegu kuma da gida za su koreki". Kulu ta shiga kaɗa kanta,"a'a ni ba kafira ba ce musulma ce, ƙaddara ce ta haɗamu da shi". Yagana ta ɗaga ma ta hannu, "kinga kar ki yiwa ƙaddara sharri, ina dalili, haka kawai da anyi abu sai ku ƙalawa Ƙaddara dan kunga bata da baki". Amadu yace,"ni dai gaba ɗayana kaina a ɗaure ya ke, dan komai ganinsa nake tamkar shirin film ko wani labarin littafi. dan Allah Baba wannan abin da ke faruwa da gaske ne?". Malam yace,"Amadu ya za'ai mu yi wasa da irin wannan al'amarin mai girma". "to amma Baba taya a kai Kabir ya san da hakan ni ban taɓa sani ba?". Malam yace,"za ka san komai daga bakin Kulu, nima ita na ke jira ta faɗa mana ainihin tarihin rayuwarta da kuma yacca aka yi Kabiru ya san komai". Kulu ta fashe da kuka sosai sannan ta soma da cewa,"mu biyu ne kaɗai a wurin mahaifinmu sarkin Qatar, tagwaye ne mu Aaliya da Akila. ni Akila ni ce ƙarama Aaliya ita ce babba. kamanninmu ɗaya tamkar an tsaga kara, hakan yasa ba'a iya banbacemu sai ta awarwaron zinaren da aka saka mana a hannu. a kaf duniya idan aka cire iyayenmu babu wani mahaluƙi da yake gane kamanninmu sai Major. mun girma a wurin kakarmu wadda ta haifi Mahaifiyarmu sarauniyar ƙasar ethiopia. a can muka girma dan bamu koma gaban iyayenmu dindin ba sai da muka shekara goma sha biyu. kasancewar muna da tsayi kuma Allah ya hore mana dirin jiki ga kyau yasa muke da farin jini a wurin duk wani ɗa namiji har ma da matan, gamu da saurin shiga rai. a wata ziyara da shugaban ƙasar nigeria ya kaiwa mahaifinmu na fara ganin Major Tosin, san da na fito zanje lambu shaƙatawa, ni macece mai tsananin son kyau, duk inda kyau yake ina wurin, kuma duk inda naga abu me kyau ina ƙoƙarin naga na mallake shi matuƙar baifi ƙarfina ba, hankaina ma tashi yake idan naga abu mai kyau na neman suɓuce min. wannan dalilin har yasa mahaifiyarmu ke min adu'ar Allah ya rangwanta min gudun kar wataran son kyau ɗin ya cutar da ni. ta in da muka banbata da Aaliya kenan a halayya bayan zafin rai. Major Kirista ne shi to amma a acikin arnan ma shi na dabanne, yana tsarin halitta da kyau taimakar wanda Allah yaywa rahma da samun hasken musulunci, ga duk macen da ta ɗora ido akansa zata so ace ta mallake shi domin ba shi da makusa sai ta ɓangaren addini, ta ko'ina Major yayi, kafin haɗuwata da shi fuskar Aaliya nake sawa a gaba nayi ta kallo ina jin daɗi saboda nasan duk wani abu da zan gani me kyau ya biyo bayan kyan halittar da muke da shi, to amma da na haɗu da Major sai lamarin yasha banban. duk da irin ƙarancin shekaruna a lokacin nasan mene SO domin an rainemu ne a gidan da ake wanzar da So, a kallo ɗaya zuciyata ta tabbatar min da ta kamu da Son Major. har naje lambu na zauna ina shaƙatawa hoton Major bai bar haskawa a cikin ƙwayar idona ba tamkar yana gabana, a san da Aaliya tazo kirana cewar Abi yace muje zamu gaisa da abokansa ba ƙaramin daɗi naji ba, saboda tun ganina da major nake neman dalilin da zai sa in samu kusanci da shi, har kasa controlling kaina nayi Aaliya da ta gane tayi ta tsokanata. kwanan su Major biyu a gidanmu kuma a wannan kwanaki na sami shiga a wajensa, kasancewar duk safiya ya kan shigo ɗakin motsa jiki kuma muma muna zama a ciki a irin wannan lokacin tare da Abi. nasan cewar shi ɗin Babban mutum ne dan ya ajiye kamata, to amma ko kaɗan hakan bai haneni kwaɗaituwa da shi ba, kuma har na kanji zuciyata na kishi kamar zata zama in to pieces idan naji yana waya da iyalinsa, a yanda ya ɗaukeni yake kula dani har ya kan sumbaceni kamar yanda ya lura al'adar gidanmu ce hakan, yana min ne duk a matsayin ƴa da yake kallona a wajensa, bai san a tawa zuciyar ba haka bane. lokacin da su major za su tafi har da ni aka rakasu airpot, domin maƙalewa Abi nayi nace sai na bisu, son samuna ma Major ya tafi dani, tsarabar da Major ya bar min ita ce kayan kakin soja da yasa aka kawo masa, bayan tafiyarsa wannan kaya sai da suka zame min tamkar uniform saboda kawai idan na saka ina jin kaman ina manne a jikinsa ne. bayan tsawon wani lokaci sai na shiga ran Major fiye da yanda tunani ke hasaso min...hmm wato shi namiji ne da yake da baiwar sarrafa harshe ta ɓangaren soyayya, mutum ne shi me kyan hali da dattako, Major ya ƙara siye zuciyata da irin salon soyayyarsa, kulawarsa da kuma kyautatawarsa. muka fara gudanar da soyayyarmu me tsafta acikin sirri ba tare da sanin kowa ba hatta Aaliya dan itama sai daga baya na sanar ma ta, bayan da soyayyarmu tayi nisa tsakanina da Major, ita ta goya min baya ga cewar mun san abu ne mai wuya al'amarin aure da mu ke burin cimma ya kasance. muna da ilimin addini cikakke tun muna shekara takwas muka sauke alƙur'ani, kuma mun sauke manya manyan littafan addinin tun muna shakara goma. nasan da cewar akwai haramcin aure tsakanina da Major amma hakan bai dakatar da ni daga soyayyarsa ba, ƙoƙarin da nake a kullum shi ne naga na dasa masa son addinin da yake shi ne na gaskiya har Allah yasa yace zai karɓi musulunci. na gama tsara sauran rayuwata ne da Major, hakan yasa nake lissafin cewar rayuwata babu shi tamkar mutuwa ce. ana haka kwatsam sarkin garin bichi ya kai ziyara cikin masarautarmu ta harar wato a ethiopia, da zai dawo Abbu ya ba shi kyautar auren ƴarsa Hauwa. ƙanwar Kakarmu me suna Bella ita ta riƙe Hauwa tun tana ƙarama, san da Bella zata taho ƙasar nan wurin Addi Hauwa ta taho tare damu, mun sami kusan shekara guda a ƙasar nan kafin na sanarwa da Bella halin da muke ciki ni da Major, tun bayan titsiyeni da tayi akan ita bata yarda da yanda alaƙarmu ke tafiya da wannan kafirin ba. ni kaina nasan na tako abin da yake da wuyar kasancewa, dan Bella ce tai sam bata yarda ba, idan har ma ta ƙara jin wannan shirmen maganar a bakina sai ta saɓa min. ni kuma a lokacin yarinya ce me taurin kai da ke da wuyar tanƙwaruwa, ina da taurin kai ina da kafiya ina kuma da tsananin zafin rai, banbancinmu da Aaliya kenan a halayya. naga babu dalilin da zai sa Bella ta yanke alaƙar da ke tsakanina da Major dan kawai tana kakata, ai bata kai wannan matsayin ba tun da aurena ba'a hannunta yake ba, mutum biyu nasan za su iya zartar da maganar aure akaina na kasa ƙetarewa su ne iyayen da suka kawoni duniya sai Jadda(Kakarmu da ta rainemu), bayansu ina ga babu me isa da iko akan aurena, haka zalika ba'a isa a hanani abin da nake so ba, bayan tun da nazo duniya ban taɓa son abu na rasa shi ba, ko menene shi Jadda sai tayi yanda akai muka same shi, hakama Abi, mutuwa ce kawai zamu ce muna so ya hanamu mallakarta ita ma kuma dan yana gudun karta rabamu da shi ne. Yarinya ce ni da ban fiya jin shawara ba, hasalima me min magana naji Aaliya ce kawai, ba wai ina da ƙiriniya ko fitina ba, a'a abin da zuciyata tace shi kawai nake yi, ba kuma na abin da zai sa na kauce hanya ba ko in zo ina danasani. shi yasa ko a san da Fadila ke ban shawara na nuna ban jita ba balle har na tunanin ɗauka, ni dai tun da har Aaliya ta mara min baya magana ta ƙare. ganin Bella da gasken gaske ta ke sai ta raba alaƙata da Major, yasa na sanar masa da halin da ake ciki, shi ma ya nuna min cewar ba zai iya haƙura dani ba, nima kuma na nuna masa ba zan iya haƙura da shi ba. dan haka na yanke shawarar ya saya min ticket naje na sanar da Abi shi zai san abin yi, ai Bella ba ita ta isa dani ba, ko Aaliya bata sani ba muka wuce Qatar ni da Major, sai bayan mun sauka ne Bella ta kira Ammi tana tambayata tace ma ta ehh nazo ni da Uncle ɗina babu jimawa. lokacin da na sanar da iyayena ba ƙaramin mamaki da kuma jinjinawa rashin hankali da kuma rashin kunya irin tawa su kai ba. Abbi ya sanar da Major wannan hanyar da aka ɗauko ba me ɓullewa bace, ya haƙura da ni tunda shi mutum ne babba da ya san ya kamata, ni kuma ina da ƙuruciyar da ban gama haɗa hankalin kaina ba, ni kuwa a yanda nake jina zan iya rantsewa nafi kowa ma cikar hankali da sanin abin da ya kamata. duk ta yanda naso abin ya faskara, kowa yaƙi goyan baya, ga Major da nake ganin yabi maganar Abi yana neman ya rabu dani, dalilin da yasa na shiga tashin hankali matuƙa a lokacin, ganin da gaske za'a rabani da abin so na, har na kamu da ciwon zuciya, ciwon zuciyar da ya kaini ga kwanciyar asibiti. lokacin kowa yay fushi dani, a asibiti ma Jadda da Umm ne tare dani kawai, sai Jadd(mahaifin Abi) da ya zo shi ma yay min kacakaca ba dan zuwa dubiya ba. Umm ita ta kira Major yazo ya lallashe ni ya taushi zuciyata ko Allah zai sa a sami sauƙin abin da likitoci ke faɗa, shi kansa da ya zo sai da hankalinsa ya tashi, hakan yasa shi yin alƙawarin da bai shirya ba, na cewar zai musulunta saboda ya aureni, kuma naji daɗin hakan matuƙa dan ko kwana biyu ban ƙara a asibitin ba na warware aka sallamemu. a tunanina ƙarshen matsalar tazo, ashe sabon fegi ne za'a buɗe, dan da muka komawa da Abi maganar sai ya ce duk da haka ba zai aura min shi ba, sai in har zai musulunta ne domin Allah ba dan auran ƴarsa ba. shi kuma Major ya ce shi mutum ne da ba ya ƙarya balle yaudara, ya faɗa musu gaskiyar abin da ke zuciyarsa kuma wanda zai iya, amma duk da haka Abi da Abbu da Jadd suka ce a'a. ni kuma naga ina dalili tun da dai yace zai musulunta kuma sai a hana shi?, kawai sai na yanke mana shawarar mu tafi wajen wani sarkin musulumin ya amsa musulunci a hannunsa sai kawai a ɗaura mana aure. nasan duk tsiya in har ya musulunta ɗin dole kowa ya haƙura. dan haka a ranar muka yiwa saudiya shigar dare, muka sauka a hotel da zummar da safe zamu isa wajen sarkin musulmai na ƙasar Major ya karɓi musulunci a hannunsa. ashe tsautsayi ne ya kirani wannan tafiyar, cikin dare ina cikin bacci sai ji nayi Major na amfani da ni. sam ba'a hayyacinsa yay min fyaɗe ba, dan ya farka ne shan ruwan dare sai yasha barasa yay overdose har ya fita daga hankalinsa gaba ɗaya. nayi kuka, nayi kuka kamar raina zai fita, yanda nake kuka shi ma haka yake kuka a wannan lokacin, ban da tsine masa babu abin da nake yi shi kuma yana bani haƙuri. nayi niyyar na kai Major kotu amma sai Aaliya ta hanani, amma duk da hakan ban haƙura ba na ƙudurta cewar sai nasa yayi nadamar da bai taɓa yi ba a rayuwarsa. babu wanda ya san da abin da ya faru dan mun rufe abinmu ni da ƴar'uwata, na koma gida naci gaba da rayuwata zuwa lokacin na cire Major a raina saboda babu abin da na tsana a duniya yanzu sama da shi. rayuwata taci gaba da tafiya kamar ta ainihi kowa na murna, kuma har Abi ya haɗa min gagarumar walima dan jin daɗina. har zuwa san da Bella ta dawo gida, kuma da zata dawo nigeria muka kuma biyota, bayan dawowarmu na fahimci cewar ina da ciki, cikin da ban san da shi ba sai da naji bayi na gulmar wai yanayina kamar na masu ciki. aiko ina zuwa asibiti likita ya tabbatar min, na yanke shawarar zuwa nayi abortion Aaliya ta hanani, amma naƙi ji na kama hanya babu wanda ya sani na tafi asibiti, da naje likita ya tabbatar min in har akace za'ai abortion nasa zan sami matsala kasancewata ƙaramar yarinya mahaifata zata mutu gaba ɗaya, nace eh na amince, sai da akazo yi sai akaga ba zai yiwu ba saboda ƙunguna na maza ne, hasalima ko haihuwa zan yi sai dai ayi min aiki. na dawo gida cikin takaici da tunanin neman mafita, nasan duk ranar da aka gane ina da ciki na gama kaɗewa, na ƙudurta barin gida na shiga duniya amma Aaliya ta dakatar dani, tace a'a mu zauna har zuwa lokacin da zai fito muga yanda ubangiji zai yi hukuncinsa. alƙalami yayi kaɗan ya faɗi irin tashin hankalin da nake ciki a wannan lokacin, kuma duk da abin da akaina yake amma tashin hankalin da ƴar'uwata ke ciki ya ninka nawa. na sha magungunan abortion sunfi kala a ƙirga dan har order na dingayi amma duka a banza, ga shi ina ta neman wayar Major na rasa, tsanarsa ta ƙara ninkuwa a saman ta da. wani dare mun fito daga turakar me martaba mun an gama hira, zamu wuce ɗaki Bella ta kira sunana, tace da Aaliya ita ta wuce ta kwanta. gabana sai da ya faɗi, dan ajikina na san maganar da zata fito daga bakin Bella, domin zuwa wannan lokacin cikina ya fara fitowa, maganar ma da Aaliya tayi min a ɗazu kenan muka kasa samun solution. "cikin wane ajikinki?". tambayar da Bella ta jefo min kenan san da na zauna kusa da ita akan kujera. naji wani ras, na kuma ji maganar da girma, to amma ɓoye-ɓoyen me zan tsaya yi?, ko nayi bai da wani amfani dan shi ciki ba'a ɓoye shi, idan ma na ɓoye akwai ranar da gaskiya zata fito, saboda haka ba kwane-kwane kai na babu tsoro balle fargaba nace ma ta,"cikin Major". amsar da na bata kenan, kuma cikin daƙiƙar da na bata amsar, cikin wannan daƙiƙar tasa aka watsomu daga cikin masarautar bichi. haka ta ke, macece me alkhairi, macece da kaf dangi banga me mutuncinta ba, amma kuma daban ta ke da kowa a wajen yanke hukunci. na ciji yatsa har sai da na karya shi saboda tsananin zafin da zuciyata ke yi, ko kaɗan ba muyi tsammani ta yanda lamarin zai kasance ba kenan. ko kaɗan ban yi hawaye ba, amma kukan da Aaliya keyi a wannan lokacin zaka ce ne ma ko mutuwa ta rabamu da iyayenmu ne. ba wai ban damu ba, zuciyata ce ta ke tafarfasa saboda baƙin cikin irin korar karen da akai mana, kamar mu ba jinin Bella bane, kuma kamar bata taɓa saninmu ba. irin tozarci da cin kashin da aka mana ba zai misaltu ba, hasalima Addi Hauwa cewa tai dama ai ta lura tun da nazo ƙasar nan na ke bin maza, Bella kuwa ce tayi babu mu babu ita ko a lahira kar mu nuna mun santa balle a wata ƙasa da ta ke ƙasar haihuwarmu. da Aaliya na musu magiya ji nayi kamar nasa ƙafa na take ta dan haushi, ehh nayi abun kunya, amma matsayinmu yafi ƙarfin mu tsuguna muna roƙo a gaban wata halittar, ƙwarai ina da wannan izzar kam. dan baƙin ciki ma da nacewa Aaliya ta tashi mu tafi sai ce min tayi wai na duba agogo sha ɗaya na dare ina muka dosa a wannan lokacin bayan bamu da kowa da ya wuce su, tabi bayansu taɓa ƙara roƙon Addi Hauwa akan su barmu zuwa safiya. ni kuwa nace sai dai ita ta koma ciki ta kwana, amma ni ko za'ai gunduwa-gunduwa da nama na babu abin da zai maida ƙafata cikin wannan wajen, masarautar da gaba ɗaya bata fi girman lambun gidanmu ba. gaba da ba ya jinin sarauta ne mu, dan haka why Aaliya zata duƙa tana zubar mana da martabarmu da ƙasaitarmu, na ɗagota dan haushi na bata mari ko Allah zai sa ta sai tu idanma barin hayyacinta tayi, naja hannunta muka bar ƙofar masarautar da ko a mafarki bana fatan na ƙara ganinta. sarƙarta muka siyar mu kayi kuɗin jirgi muka koma, sai dai ko da muka je ethiopia can ma ba sauƙi, domin tuni Bella ta kira waya ta sanar musu, suka ƙi karɓata suka ce sai dai na koma wurin wanda yay min cikin muci gaba da rayuwa tare, Abbu yasa aka karɓe passport namu na shiga Qatar, Aaliya tace ba zata iya zama babu ni ba sai dai ita ma a koreta daga gidan. dan haka bada saninta ba na gudu na bar ƙasar na koma london da zama har lokacin da cikina ya shiga wata tara,

Chapter 30 of 52