Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dole zai tashi daga farashin da muka sa, dan naga yarinyar tafi ƙarfin farashin miliyan ashirin". gabana ya yanke ya faɗi rasss saboda tsananin tashin hankali, da gaske yau ni Mairo aka yi kidnapping?, abun da nake ji a labari, kuma har ake ambato waɗannan maƙudan kuɗin dan fansata, bayan Babana ba shi da su ba kuma shi da me ba shi?, kafatanin dangin uwata da na ubana su kansu aka haɗa ba su kai iya adadin kuɗin ba, gatanmu a rayuwar nan shi ne Allah, shi ke rufa mana asiri ya kuma suturtamu, babu makawa Babana yaji batun wannan kuɗin to la shakka cigaban rayuwarsa abu ne mai wuya. wasu zafafan hawaye suka shiga sitiri a saman fuskata kamin daga bisani na ɗauke wuta gaba ɗaya. tafiya ce me nisan gaske mutanen su kai, tafiyar da kamar ba zata ƙare ba, aƙalla sun ɗauki kusan awanni takwas zuwa tara kamin su iso wani titi da babu gimlawar komai sai ƙarar iska da ke kaɗawa. wajen ƙungurmin daji ne da tsirrai ke rayuwa wurin, motarsu bata jima da tsayawa ba a wurin sai ga wasu mutane dukansu a tsamure sun fito daga cikin dajin hannayensu riƙe da wuƙaƙe da kuma bindiga, a kallo ɗaya za kaiwa halittar fuskarsu ka san baƙaƙen azzalumai ne na ƙarshe, waɗanda babu ko ɗison imanin tausayi a zuƙatansu. ɗaya daga cikinsu ya dubi wanda ke riƙe da Mairo murya a shaƙe yace,"cika aiki ya ne?, ko firgici yasa ta mutu ne?". wanda aka kira da cika aiki ya bushe da dariya tare da yasar da Mairo a ƙasa yace,"haba bandalago zunubin ai sai yayi min yawa, kai kasan duk girman sheɗancina ina tsoron mutuwar rai a hannuna...bata mutu ba ta nan da ranta kawai dai an sata dogon bacci ne ehh yane ka gane kawai". dukanninsu kallonsu ya koma ga Mairo da ke yashe a ƙasa kamar gawa, sanadin jefar da ita ta bugi dutse goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake. "kam bala'i jini naga yana zuba". cewar ɗayan cikinsu. "to Allah na tuba kai yau ka fara ganin zubar jini irin haka, kamar ba'a sha kashewa a gabanka ba...ku ɗauketa kawai kusa kai". haka ɗaya ya saɓi Mairo a kafaɗarsa, kai ba ka ce mutum ya ɗauka ba, dan ɗaukar irin na dabbobi ne da mafarauta ke musu, suka nausa can tsakiyar dajin su na ta tafiya kamar ba za'a ƙare ba, kamin su sake ɓullawa wani dajin shi ma suyi tafiya me nisa kan su yada zango a wata bukka, su na isa suka jefar da Mairo kamar matacciyar dabbar da suka farauto, mutumin da ke zaune kan kujerar ƙarfe yace,"wannan ce yarinyar?". "ehh oga ita ce". "ok, to ku haɗata acikin waɗancan kajin, naga biyar ta kawo kai, idan muka yi sallar asuba sai mu wuce amma kuyi da sauri dan ina so mu shiga gari da wuri saboda aikin gobe me zafi ne". suka amsa umarnin ogan nasu da, "yanda kace Oga". sannan su kai gaba, sai kuma tsamurmurin cikinsu ya dawo da baya yace,"amma Oga na ke ga kamar mu ɗau hanya tun yanzu ko, dan naji fa ance goben nan akwai tsaro me tsamari a hanya". Ogan ya ɗaga masa hannu,"ba case, aikinmu ba ya da matsala da jami'an tsaro". su na idar da sallar asuba suka shiga mota da yara sunfi biyar kuma har wannan lokacin Mairo bata farfaɗo ba, sannan su ka ɗauki dogon titin da babu kwana balle kwane-kwane, tafiyar awa shida ta kaisu ga in da suke so, nan ma dai daji ne sai dai bai kai wancan dajin hatsari ba, kuma shi anan bukkoki sun kai shida saɓanin can da bukka ɗaya ce, haka aka taso ƙeyoyinsu har zuwa bakin Babbar bukkan, sannan duk mabiyan da ke tare da su suka tsaya, Wani wanda da alamar shi ne babba cikin ƴan bindigan da ke tsaye bakin Bukkar da bindigarsa zungureriya ya kalli waɗanda suka kawo su Mairo yace,"ita wannan me yasa buku ɗaure mata ido ba". "hoda ce ke aiki ajikinta". ya girgiza kai sannan ya sunkuya ya shiga bukkar babu jimawa kuma ya fito yana takewa wani tsohon farin bafulatani baya, wanda alamu ya nuna shi ne babba a tsangayar ta su, Tsohon ya zauna kan kujerarsa su kuma duk suka zube gwiwoyi ƙasa. ya dube su kamin yace,"kun makara". "bamu taso da wuri bane".suka ba shi amsa. ya jinjina kai sannan ya kai dubansa ga kajin da suke ikirarin an kawo, yay musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan yace,"amma ita wannan sumammiyar da ka gani daga gidan yunwa ta fito...ko da yake koma dai yane dole za'ai aman kuɗin karɓarta, ku tasheta su kuma sauran ku kunce musu ido". aka kuncewa sauran ido ita kuma Mairo anata zabgeta da mari amma bata farka ba, hakan yasa tsohon ya saki harbin bindiga nan kake ji duk waɗanda akayi kidnapping ɗin sun cure wuri ɗaya jiki na kyarma, take kuma ƙarar harbi na biyu da ya kuma saki ya farkar da Mairo cikin ɗimauta da gigita, ta tafi ta rarumo ɗaya daga cikinsu ta cukwikwiye jikinsa ta fashewa da kuka tana faɗin,"Ya Kabiru kazo ka ƙwaceni daga wurinsu kar su cutar da ni". maganarta ta haɗiye saboda yanda wanda ta cure a jikinsa ya damƙo gashin kanta ya barƙalar da wuyanta, tsananin azaba yasa ta buɗe nauyayyun idanunta a wahalce ta dube shi da irin dishi-dishin da take gani. ya doka mata tsawa tare da cewa,"yi mana shiru". sai kuma ya sake ce mata,"wa ye Kabiru?". jiki na rawa ta shiga juya masa kai,"babu kowa a firgice nake ne". tayi maganar a rarrabe. daga nan kuma duka aka tasa ƙeyarsu zuwa wani ɗan ƙaramin gini me ɗaki ɗaya da mitsitin windo sai banɗaki da ke ciki, ana saka su aka janyo ƙofar aka rufe. anan Mairo taga ashe ba ita kaɗai aka sato ba, su birjiki sun kusa kaiwa talatin daga manya har ƙanana kusan Manya ma sunfi yawa, dan idan tana iya gani sosai kusan ita kaɗai ce ma budurwa a wajen. ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka me ƙarfin sauti, nan wata dattijuwar mata da ke daga can nesa da ita ta taso tazo kusa da ita ta zauna, ta ɗago kanta tasa hannu tana goge mata hawaye. "kiyi shiru ki daina kuka kinji ƴata, adu'a za ki yi Allah ya fitar damu daga wannan musiba amma kuka ba namu bane. idan kika ci gaba da kuka suka jiyo ki za su zo su harbeki ne suyi miki irin ta wancan yaron". matar ta faɗa tana nuna mata wani yaro ɗan kimanin shekara takwas yashe a ƙasa."kin gansa kuka yake suka zo suka harbe shi kuma har yanzu ba su ƙara bi takansa ba alhalin sun san da cewar ya mutu". Kukan da ya ci ƙarfin matar yasa tayi shiru. Mairo ta dubeta tace,"Inna to me muka yi musu?". ta girgiza mata kai da cewar,"ba muyi musu komai ba, su na amfani damu ne kawai dan biyan buƙatar kansu, sun manta da cewar akwai wata rayuwar bayan wannan". ita dai Mairo kukanta sai ya tsaya ganin wannan matar tana kuka, jikinta duk yay sanyi, bata san da cewar yaron da aka kashe ɗan matar bane. matar ta yagi mayafinta ta ɗaurewa Mairo ciwonta da ke tsiyayar da jini har yanzu, dan idan ba ita tayi hakan ba to ko jinin Mairo zai ƙare babu mai kulata. *Kano, Bichi.* Yagana na gyara turken awakinta Saleh ya shigo, ta amsa sallamarsa tare da cewar ya shiga ɗaki ya ajiye mata saƙon, ba sai ta fito sun gaisa ba ita yau bata shirya karɓar ciwon kai daga wurin kowa ba. Saleh ya wuce ɗakinta yana faɗin,"wannan tsohuwa ba zata taɓa sauyawa ba". har ya aje mata kwanon abincin ya juya zai fita sai ya hangi ledar awara dan haka ya komo ya nemi wuri yay zaman dirshen, yasa awara a gaba ya fara ci, sai da ya kusa shanye ruwan shayin Yagana ta shigo, tayi turus a bakin ƙofa tare da buga salati,"in da raina na sha kallo, me zan gani haka?". Saleh ya rufe kofin shayin yana faɗin,"Kai Yagana guda huɗu fa kawai na ci". "to daka ci huɗu ce akai mu raba da kai, ƴan bani na iya...mtsww ƴaƴan Zulai ba dai shegen kwaɗayi da neman masifa ba, ko da ya ke laifina ne da banje na sanar da iyayen na ku ba su daina min aikenku ba daɗin sabga gareku ba...ni dai tashi ka fice min a gida tun ban gama harzuƙa ba". ta faɗa tana raraka shi da muburgi, yay saurin ficewa. ta zauna tana ta jan tsaki da mita akan taɓa awar da ta ajiyewa Mairo, amma ɗan ƙwal uba yazo ya cinye mata bayan ita ba cin kaɗan take ba, kullum so take ta burge Mairo amma bata iya mata, ta hana cikinta ta ajiye mata ƙarshe Mairo ta karɓa ta kaiwa almajirai ko kuma kai tsaye tace mata hannunki ya taɓa ni kuma ina da tsantseni. ta kwashi ragowar awarar ta juye cikin kwano tana faɗin,"Allah yasa idan tazo taci, amma wallah tana gani zata ce ci akai aka rage mata alhalin bani naci ba...ni dai Saleh ka cuce ni". har Saleh ya bar gidan sai kuma ya dawo, ya ɗaga labulen ɗakin yace da Yagana,"Gwaggo tace idan Mairo ta tashi taje, idan bata tashi ba kuma ki tasheta tayi sauri taje za su wuce kano yanzu". Yagana na jinsa dai bata tanka shi ba, illa a ƙasan zuciyarta da ta furta,_"a Ƴaƴan Adamu ai kai ne kafi kama da mara lafiya, ashe ma ba iyaka rashin lafiyar jiki bane harda ta ƙwaƙwalwa"._ ita ba ta yarda da zancen nasa ba a tunaninta shirmensa ne, saboda hakane taƙi ce masa kanzil, sai can dai da ta ga ya dage ya kafe kan cewar Baba yace idan bai sako Mairo a gaba ba ransa zai ɓaci sannan ta fara sauraronsa, to su na haka sai ga Sunusi yay sallama, bai ma jira Yagana ta amsa ba ya jefa mata tambayar,"ina Mairo?". Yagana ta miƙe tana gyara ɗaurin zane. "bana son shirmen banza karku cakar min da kai ni ba ƴar sholisho ba, wai wacce Mairo kuke nema ne Mairo da bata kwan anan ba kuma bata doka sammakon zuwa ba". Sunusi yace,"Yagana lokacin wasa ayi shi kawai...amma yanzu ana miki maganar Kawu na kano yazo zai wuce da ita asibiti dan haka dan Allah ki bar wannan wasan kije ki tasota, na san dai tashin nata ne ba kya so shi yasa kike neman fakewa da bata nan". Yagana ta kauce daga hanya tana cewa,"ni naga idi zigidir, Sunusi leƙa ciki ka caje har kwanuka ka gani ko zaka ga Mairo...ƙila dai jiya ina mayen bacci nayi tunanin ko ta tafi ne". Sunusi ya wuce ɗakin ya gama dubansa ya fito bai ganta ba, sannan ya dawo ya ƙara tambayar Yagana tsakani da Allah Mairo bata kwan nan ba, tace da shi". ka san girman Allah bata kwan anan ba, jiya fa muna idar da isha'i ta kama hanyar tafiya...ni abun naku ma ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro, yanzu kana so kace min da gaske bata gida?". "wallah tun zuwanta nan jiya bata koma ba har yanzu, anyi tunaninma ko ta nan ne". Yagana ta zabari Hijabi tana jan salati su kai waje tana faɗin,"ni Rakiya na shiga uku, Yarinya kuma ta rasa ata silar wa zata ɓata sai ni marainiyar Allah salan ta jazamin bala'i". Sunusi yace,"ke wa yace miki ɓata tayi?". "yo gidana fa tazo, daga nan kuma shikenan sai ɓacin rana ta sauka, kaga kuwa ko kame aka tashi Uwarta aini za tasa a garƙame tun da tasan wurina ta aikota...ohh ni Rakiya wannan musiba da mai tayi kama, ina zaman zamana ɗiyar Adamu zata jazamin jaraba, ita Mairo ba ƙaramar yarinya balle kace ko maƙota ta shiga, ba wayayya ba balle kayi tunanin ko ta bi saurayi, ko kuma ta taho bacci ya ɗauketa a hanya oho. to Allah dai masani". haka dai su ka ƙaraso gida Yagana nata zuba zantuka da aikin gyara ɗaurin zanen da ya ƙi ɗauruwa. tun da ta shigo cikin gidan kuwa ta tabbatar dai da babu Mairo sai ta kuma yowa waje a rikice. ta rasa me za tayi me ya kamata tayi sai ta rushe da kuka kuma. daga cikin gida kuwa Gwaggo tuni ta zama mutum mutumi, ta koma bin kowa da ido, cutar hawan jinin da bata da ita na neman kamata, da kunnuwanta su ka gama gasgata da gasken Maironta ta ɓata sai ƙafafun da ke riƙe da ita ada su ma suka gaza, nan ta tafi luuu ta zube Inna Zulai da ta lura da ita tayi saurin taryota tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. gaba ɗaya hankali kuma sai ya dawo kanta, Baba ya ɗebo ruwa aka yayyafa mata nan ta farfaɗo, ta damƙi hannun Inna Amarya wacce hawaye ke sintiri saman fuskarta tana ce mata,"Amarya da gaske ne abunda kunnuwana keji wai Mairo ta ɓata bata nan kusa damu?". "insha'Allahu bata ɓata ba tana nan kusa". cewar Amarya tana ƙoƙarin tsaida hawayenta. Gwaggo ta shiga girgiza mata kai,"ko kusa Amarya, ina ji ajikina ɗauke Mairo akai...tarbiyar da na bata ba zai sa tayi nesa da gida ba akaran kanta dole akwai wani abu a ƙasa". ta juya kan Baba da shi ma yayi jugum,"Malam ba zama ne ya kamace ka ba ku tashi a nemo min ƴata da wuri tun rayuwarta bata gama tagayyara ba". Yagana dai na bakin ƙofar ɗakin Baba a zaune tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure saboda kukan da tasha, ta ƙara sakin wani matsanancin kukan tana faɗin,"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ubangiji ka dubeni ka rufa min asiri ka dawo da Mairo gida cikin amincinka...idan ya Tabbata ta ɓace ban san ya zanyi ba, Allah ka dubi halin da muke ciki ka jiƙanmu. su kuma azzaluman bayinka da suka ɗauketa kai kasan yanda zaka yi da su ya Allah kayi maganinsu". Ƙanin Malam me suna Mujibu wato autan Yagana ya shigo shi da su Sunusi, gida dai ya koma kamar na makoki, ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa ya riƙo hannunta yace,"kiyi haƙuri Yagana za'a ga Mairo insha'Allahu". sannan su ka maida bayaninsu ga Baba, "daga wurin Mai Anguwa muke, yace a hanzarta aje a shigar da report a ofishin ƴan sanda". Baba ya miƙe yana sakin hannun Gwaggo, ko kaɗan tashin hankali bai bar fuskarsa ba, yayi ta maza ne kawai wajen haɗiye rauninsa, jiki babu ƙwari yabi bayan su Mujibu suka yi ofishin ƴan sanda. su na fita Yagana ma ta miƙe tana faɗin,"ai banga ta zama ba Mujibu ku tsayani ƙafata ƙafarku". tana tafe tana haɗa hanya sai jin goshinta tayi ƙumm ajikin garu nan kuwa ta sake rushewa da kuka tamkar ta shiɗe. "ni dai to duk wanda ya sace Mairo Allah ka tattara duka tsinuwarka ka ɗora masa, dan wallahi ba zan yafe ba".  ta dubi maƙociyarsu Gwaggo tana nuna mata goshin tace,"ƴar nan duba min naji kaman ya ɓurma ciki ko?". matar tasa hannu zata lailaya mata gudun kar ya kumbura Yagana ta danƙara mata zagi,"ya daga cewa ki duba min kuma sai ki nemi hanyar da zanbi na mutu banje neman Mairo ba ayi ba wan ba ƙanin, ke kuwa wannan ƴa da ƙeta kike". Matar tace,"yi haƙuri Yagana". "Allah dai ya yafe miki kawai amma cuta ce ai kin cuceni". ta kunce bakin zane ta ɗauko ɗari biyar ta bawa Lukman tace,"maza ka karɓo ƙosai ayi sadaƙa Allah ya bayyana mana ita nan kusa kuma cikin amincinsa, dan Allah Lukman karka ci kaga na sadaƙa ne". shi dai kuɗin ya karɓa ya fice da sauri shi ma hankalinsa duk bai jikinsa, dan Mairo ta wajensa ce. har kusan azahar su Baba basu dawo ba, daga nan kowa ya ƙara sarewa da ɓatan nata, Gwaggo dai na sheme sai firfita ake mata tana fitar da numfashi sama-sama. Kulu na daga cikin ɗaki ta jingina kai da bango, idanuwanta sun kaɗa sunyi jazur, tsabagen tashin hankalin da take ciki ma hawayen sunƙi zuba, sai jakar kayan Mairo da ta zubawa ido, cikin ranta tana cewa,_"yanzu shikenan Hussaina kema na rasaki, ya za kuyi min haka?, a lokacin da nake tsananin buƙatarku tare da ni sai na rasa Hassan na tsira da ke, kin kasance tare da ni kuma kema yanzu sai ki zama babu?...banji da sauƙi ba wajen haihuwarku, ki taimaka ko dan wannan ki tausaya min ki dawo gareni, ba zan yanke tsammani da rasaki ba kamar yanda na yanke tsammani da Hassan, ke kaɗai kika rage min bani da kowa, ke ɗaya ce jinina da na ke gani naji daɗi, na rasa kowa nawa da komaina...ya Allah kaine shahidi ka duba rayuwar da nake ciki ka dawo min da Hussaina"._ duk yanda tayi trying hard tayi controlling tears nata abun ya gagareta, sai ta fashe da kuka tana roƙon Allah ya kula mata da ƴarta a duk inda take ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, sai dai ta gama resolve kan matsawar rana ta faɗi Mairo bata dawo ba to zata bi bayanta ne. *To Fah!!! Masu karatu the Saga begins😖...wa kuma ya san me zai faru next?, Mairo zata dawo kuwa?, haka kawai aka ɗauketa ko kuma sanyawa akai a saceta?, kai to wai ma tsakanin Gwaggo da Kulu wace Uwar ta haƙiƙa ne?.* ni dai please vote and comment ba dan halina ba kunji ƴan albarka😑, gwiwana na sagewa idan ku ka karanta naji kunyi tsit. *Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *19)* Hankalin Gwaggo da Kulu a tashe yake matuƙa, dukansu sun kasa samun stabilify, sam sun kasa yarda Mairo ta ɓata ɓat, har gwara Kulu ma na iya jurewa, amma Gwaggo kuwa tun da rana ta faɗi ya tabbata babu Mairo babu dalilinta, shikenan ta yanke jiki ta faɗi, shikenan duk wani budget nata akan Mairo ya rushe, nan da nan aka ɗauketa zuwa asibiti, kuma a lokacin ne Kulu ta fito dan ta sulale ta gudu amma halin da Gwaggon ke ciki yasa dole ta janye ƙudurinta domin idan tayi hakan tayi butulci, daga ita sai Inna Zulai aka bari a gida, bata da aikin komai sai share hawaye lokaci zuwa lokaci. Gwaggo ce kwance kan gadon asibiti, a kallo ɗaya zaka gane fitar hayyacin da tai, amma dai for now ta fara regaining conciousness, likita ya shigo ya auna BP ɗinta sannan ya kalli Malam yace,"to Alhamdulillah jininta ya sauka, zuwa Magrib zamu iya sallamarku sai dai a kula dan Allah wajen kiyaye damuwarta, and then da shan magani in time saboda gaskiya lafiyarta na cikin haɗari". Malam ya ɗaga masa kai da cewar,"tom za'a kula...sannu da ƙoƙari". zuwa Yamma aka sallamesu suka koma gida, tun bayan dawowarsu kuma gida ya ɗinke da jama'a sai shige da fice suke ana jaje kamar gidan mutuwa, da waɗanda su ka zo jaje tun ranar farko da masu dawowa yanzu dan duba jikin Gwaggo sai gidan ya zama babu matsaka tsinke. Yagana duk wanda yay mata jaje bata iya cewa da shi komai sai kallo da ido, bini-bini kuma sai ta sa gefen mayafi ta matse ƙwalla. Matar Liman tazo ana gaggaisawa ta tambaya ko waɗanda su kai garkuwar da ita sun kira waya?, Amarya tace da ita,"ai Hajiya babu lallai Kidnappers ne tun da har yanzu babu wani saƙo ta waya, munfi tunanin ko ƴan yankan kaine suka saceta, yanzu kwanciyar hankalinmu ma bai wuce ace ko gawarta ne a gani ba zamu fi samun nutsuwar ruhi". Hajiya Saratu ta girgiza kai cikin jimanta al'amarin,"to ubangiji dai shi ya san a halin da yarinyar nan ke ciki. Allah yasa ta faɗa hannu na gari...in Allah ya yarda za'aita adu'a dan yanzu haka ma tun jiya Malam yasa almajirai suka sauke mata alƙur'ani". Yagana ta face majina cikin muryar kuka tace,"ai duk wanda ya ɗauke yarinyar ba zai gama da duniya lafiya ba, kuma sai Allah ya isar mana tsakaninmu da shi...fatanmu Allah ya tsareta ya kareta a duk hannun da ta faɗa". wata cikin ƴan jajen tace,"kwanaki mu ma fa haka akayi a layinmu, daga fitowar yaro da daddare ke tun ana zuba ido ana saka ran zai dawo shiru har yanzu kusan wata biyu kenan, iyayenma sun cire rai da shi tun da babu irin neman da ba'ai ba, cigiya har gidan talabijin". Marka me koko tace,"ai waɗan nan azzalumai Allah dai yay mana maganinsu shi ne adu'a kawai". Sunusi ya shigo rungume da buhun shinkafa, Lukman na biye da shi ɗauke da kwalin taliya biyu da na makaroni ɗaya, sai ga Mu'azzam shi ma ya shigo da galan ɗin manja. kafin Amadu ya mara musu baya bakinsa ɗauke da sallama, sai dai kana ganinsa kaga wanda ke ɗauke da matsananciyar damuwa, a tsaitsaye ya gaida jama'ar da ke tsakar gidan sannan ya wuce ɗakin Gwaggo. kishingiɗe jikin pillow ya taddata, ya ƙarasa gabanta ya zauna, har tsawon wasu daƙiƙu bai ce komai ba sannan ya buɗe baki kamar mai shirin yin kuka yace,"sannu Gwaggo, Allah ya ba ki lafiya". ta amsa da,"amin Amadu, ashe kana tafe". "ehh da yake ma tafiyar  mota ce shi yasa na makara". Sai Gwaggo ta fashe da kuka,"Mairo dai ta ɓata, ban san a wani hali take ciki ba yanzu". yay saurin kawar da fuskarsa dan ba ya son ganin hawayenta, ya lumshe idanunsa da su kai jazur ya buɗe kana yace,"su da ba fita suke ba dan ubanta gidan uwarwa taje a ranar?". yay tambayar a zafafe. Gwaggo na goge hawaye tace da shi,"to ai ita kasan bata rabo da gidan Yagana, laifinma dai nawa ne kuma duk da haka Allah ya riga ya shirya faruwar hakan, kuma ita Yagana tace lafiya lau su kai sallama da ita ta wuto gida, to ƙarshe sai da safe da ana laluben hanya aka tsinci ledar dubulan ɗin da ta bata a hanya, ananne ma aka tabbatar ɗauketa akayi". yana huci yace,"ni dama gidan Yagana ba son zuwanta na ke ba tunda ba wani iya kula da ita za tai ba...ita ma shashasha da ta ga daren yayi ai sai ta haƙura ta kwana acan". Gwaggo tace,"ko ɗaya ba laifin Yagana bane kasan Mairo ma da shegen taurin kai, kaifi ɗaya ce". "duk da haka akwai laifin Yaganar". Yagana ta faɗo ɗakin tana matse ƙwalla ta hau sababin,"yo ni dama tunda akace min zaka zo garin nan na sallama babu wanda zaka ɗorawa alhakin ɓatanta sai ni, to ni dai sai dai nace Allah ya saka min tunda yana ji yana kuma gani, ai kowa shaida ne ina ƙaunar Mairo, ta ya za'ai nasa a saceta, me ta tare min, kuma ni wallahi ma bani da wannan matacciyar zuciyar da zansa hannu a cutar da rai". tunda ta fara maganar Amadu ke kallonta, har kuma ta gama bai ce mata ƙala ba, sai da ta gama sharar hawaye sannan ta dube shi da cewar,"yanzu kuwa ɗan nan ba zaka nemi yafiyata ba?". ko kallonta bai ba ya miƙe yana zura hannu a aljihun wando, ya zaro ƴan ɗari biyar guda shida ya miƙawa Gwaggo, ta amsa tana saka masa albarka. "yanzu ina zaka je? da kayi zamanka anan ka huta kai da kasha hanya". "Gwaggo zanje asa cigiyarta ne a gidajen radio, idan nace zan zauna babu lokaci kwana ɗaya ne aka bani a wurin aiki". "tom shikenan sai ka dawo...Allah ya bada sa'a yasa a dace". yasa kai zai fita Yagana tace,"ni dai dama bance ka ban silanka ba balle ka dinga hararata har kana neman bigeni, ɓatan Mairo shi ya dameni ba karɓan kuɗinka ba". He is not in the mood ɗin da zai tsaya bata amsa amma duk da haka dai ta ba shi dariya, sai ya gimtse kawai ya wuce ɗakin mahaifiyarsa. ganinsa yasa Inna Zulai ta rasa inda zata tsoma ranta dan daɗi saboda yanda ɗanta ya sauya cikin watannin da basu haura biyar ba. ji take

Chapter 14 of 52