ihu, muryar Mami kuma ta fito da furucin cewa,"ba abin da zai miki a yanzu, amma ki san da cewar ni na miki ƙofinsa...kuma ki sakawa ranki matsawar ya zama kece silar kwanciyar ƴar'uwata sai na saka ya shiga jikinki, haka idan na sameta a yanayin da zuciyata ba zata ɗauka ba Maryam ba miciji kaɗai ba, sai kinsha mamakin abin da zan miki". duk sai na tsure na nemi fita acikin hayyacina, da alama dai Mami so take ta haukatar da ni da tsoronta, ban da girmanta a wajena da na kirata da sunan muguwa.
mu ka shiga mota driver yaja, kamar na san zata iya kasancewa, sai na ce da security ɗin da aka haɗomu ya bani aron wayarsa, ya miƙo min na saka lambar Ya Amadu, dan nasan ko na kira Ya Kabiru ba zai tsaya saurarona ba. yana ɗagawa kuwa na tambaye shi inda suke, bai ma shaidani ba kai tsaye ya bani amsa da, "muna international hospital".
da zuwanmu asibitin na hango Yagana a bakin ƙofar room ɗin tana alwala, tun daga nesa na ƙwala ma ta kira, ta ɗago tana dubana kamin ta kai dubanta ga wadda ke biye da ni, sai naga ta miƙe daga sunkuyen da take ta leƙa cikin room ɗin ta window, sannan ta dawo da kallonta kan Mami, kamin tayi fatali da butar da ta ke alwala ta faɗa cikin ɗakin da gudu tana zabga salati me haɗe da kururuwar ihu tana faɗin,"Yau naga ta kaina ni Rakiya, aljanar Kulu ta bayyana".
__________________________________
*Farashin MTN Data 5GB akan 400 masu tsarin Betatalk, ga masu buƙata sai ku tuntuɓi wannan lambar 09060523731.*
*Assalamu alaikum
jama'a na tallatamuku hajar mu ta online/offline business dina wanda zanrin ga sayar muku da data ta mtn a sassaukan farashi Kamar haka*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Whatsapp OR
Call 08066268951*
*Plss Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*NOTE:*
*_Tabbas Abu-Ɗalib Mahaifin Annabi Yana Daga Cikin Mutanen da Suka yi Tasiri Wurin Yaɗuwar Addinin Musulunci Har Ya kai Zuwa Yanzu. Ya Zamo wa Manzon Allah Garkuwa ta Yanda Duk Dukan da Za'a Kawowa Annabi Shi Yake Kare Masa, Kasantuwar Yana Daga Cikin Dattawan ƙuraishawa Yasa Suke Shakkarsa Har Suke Ragawa Annabi._*
*_Bayan Rasuwarsa Manzon Allah Ya tsinci Kansa Cikin tsananin Wahala Saboda Mai Bashi Kariya Daga Cutarwar ƙuraishawa Yau Ubangiji Ya Amshi Rayuwarsa, Da Cutarwar Tayi tsanani ga Sahabban Annabi Raunana, Sai Ya Umurce su da yin Hijira Zuwa Habasha Don Su Samu Sauƙin Wahalar da Suke Sha a Hannun ƙuraishawa. Wanda Daga ƙarshe Allah Ya Umurcesa da Yin Hijira Zuwa Madinah._*
*_Sai dai Duk da Kariyar da Ya Bawa Annabi, Ubangiji Bai ƙaddara Masa Karɓar Addinin Musulunci ba. Wato a Kafirinsa Ya Rasu. Mutuwarsa A Matsayin Kafiri Yana Daga Cikin Abin da Ya Baƙantawa Annabi Rai, Ganin Yanda Ya Tallafawa Da'awarsa. Hakan Yasa Annabi Ya Ɗauki Alƙawarin Nema Masa Gafara, Har Sai da Ubangiji Ya Haramtawa Annabi Yi Masa Addu'a Kamar Yanda Wannan Ayar Ta Tabbatar:_*
*(مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ)*
*_Kuma Hadisi Ya Tabbata Cewa:_*
عَنْ سَعِيدُ بْنُ الْمُسَيَّبِ عَنْ أَبِيهِ، قَالَ: لَمَّا حَضَرَتْ أَبَا طَالِبٍ الوفاة جاءه رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَوَجَدَ عِنْدَهُ أَبَا جَهْلٍ وَعَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي أُمَيَّةَ بْنِ الْمُغِيرَةِ فَقَالَ: «أَيْ عَمِّ قُلْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ كَلِمَةً أُحَاجُّ لَكَ بِهَا عِنْدَ اللَّهِ»، فَقَالَ أَبُو جَهْلٍ وَعَبْدُ اللَّهِ بْنَ أَبِي أُمَيَّةَ بْنِ المغيرة: أَتَرْغَبُ عَنْ مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، فَلَمْ يَزَلْ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَعْرِضُهَا عَلَيْهِ ويعودان بِتِلْكَ الْمَقَالَةِ حَتَّى قَالَ أَبُو طَالِبٍ آخِرَ مَا كَلَّمَهُمْ: عَلَى مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، وَأَبَى أَنْ يَقُولُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَاللَّهِ لَأَسْتَغْفِرَنَّ لَكَ مَا لَمْ أُنْهَ عَنْكَ»، فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: ﴿ مَا كانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كانُوا أُولِي قُرْبى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحابُ الْجَحِيمِ ﴾،
[القصص: ٥٦]
_An Karɓo Daga *Sa'eed bn Musayyib (ra)* Daga Mahaifinsa Yace: Yayin da Ajali Yazowa Abu-Ɗalib, Sai Annabi (saw) Yazo Ya Samu Abu-Jahl da Abdullahi bn Umayyah bn Mughirah. Sai *Manzon Allah (saw)* Yace: *"Ya kai Kawuna, Kace La'ilaha Illallahu, Kalma ce da Zan Kafa Maka Hujja da Ita a Wurin Allah".* Sai Abu-Jahl da Abdullahi bn Abi-Umayya Suka ce: "shin Yanzu Zaka Ƙyamaci Addinin Abdul-Muɗallib? *Manzon Allah (saw)* Bai Gushe ba Yana Maimaita Masa Kalmar Shahada, Su Kuma Suna Ƙara Ce Masa: "Yanzu Zaka Bar Addinin Abdul-Muɗallib". Har Sai da a Ƙarshe Abu-Ɗalib Yace Shi Yana nan Akan Addinin Babansa Abdul-Muɗallib Yaƙi Faɗin La'ilaha Illallahu. Sai *Manzon Allah (saw)* Yace: *"Zan Dinga Nema Maka Gafara Matuƙar Ba'a Hanani ba".* Sai Allah Ya Saukar da:_
*(مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ)*
_*"Bai Dace Ga Annabi da Waɗanda Suka yi Imani ba Su Dinga Nemawa Mushirikai Gafara Ko da Kuwa Sun Kasance Ma'abota Kusancinsu Ne Bayan Sun Bayyana A Garesu Cewa Su Ma'abota Wuta ne".*_
_(Qasas: 56)_
*_Sannan Damuwar da *Annabi (saw)* Ya Shiga Saboda Rashin Musuluntar Baffansa, Sai Ubangiji Ya Sake Jawo Hankalinsa da Cewa:_*
*﴿إِنَّكَ لَا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَنْ يَشاءُ﴾*
_*"lallai Kai Baka Iya Shiryar da Wanda Kake so, Allah Ne Ke Iya Shiryar da Wanda Yaso".*_
*_Har Wayau Hadisi Ya Tabbata Game da Kasantuwar Abi-Ɗalib Ɗan Wuta, Manzon Allah Yana Cewa:_*
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه: أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَذُكِرَ عِنْدَهُ عَمُّهُ أبو طالب، فَقَالَ: *«لَعَلَّهُ تَنْفَعُهُ شَفَاعَتِي يَوْمَ الْقِيَامَةِ، فَيُجْعَلُ فِي ضَحْضَاحٍ مِنَ النَّارِ يَبْلُغُ كَعْبَيْهِ يَغْلِي مِنْهُ دِمَاغُهُ»*
_An Karɓo Daga *Abi-Sa'eedil Khudry (ra)*, Lallai Yaji *Manzon Allah (saw)* Yana Ambaton Kawunsa Abi-Ɗalib Yana Cewa: *“Wataƙila Cetona Ranar Ƙiyama Ya Amfane shi. Za'a Sanya Masa Takalmi Na Wuta Wanda Ƙwanyar Kansa Zata Dinga Tafarfasa”.*_
*_Waɗanda Suka Fara Kawo Maganar Wai Abu-Ɗalib Ya Musulunta Su ne Ƴan Shi'a Kawai Don Su Kambama Sha'anin Aliyu bn Abi-Ɗalib (ra). Daga Baya Kuma Wasu Sufaye Su ka Ara Su ka Yafa._*
'''Wallahu A'alam.'''
*36)*
ganin yacca Yagana ta faɗo ɗakin, Malam da ke zaune kan kujera ya miƙe da sauri yana tambayarta lafiya, tambayarsa tayi lokaci ɗaya da shigowar Amadu wanda ya karɓo magunguna a pharmacy.
shi ma ganin yanda Yagana duk take a hargitsa ya jefa mata tasa tambayar. ta haɗiye wani yawu da ya wuce da ƙyar tace,"ni Rakiya yau gane-gane na yaja min". ta faɗa tana ɗan haki kamin ta nuna gadon da Akila ke kwance tace,"Yama sunan wannan balarabiyar?". kan su bata amsa ta ɗora da,"kai ku barni da wannan sunan mai kwalmaɗa, mu tafi a Kulun dai...ku ashe duk zaman jinyar nan da muke da gawa muke tare bamu sa ni ba". a tare suka waro ido waje su na tambayarta,"gawa kuma Yagana?". ta gyaɗa kai,"ƙwarai kuwa gawa...yanzu ina alwala naga ruhinta na tunkaroni da wani irin haske, ba shiri nayo ciki da gudu, har fa da Mairo na gani ita ma hannunta kamar da makaman yaƙi, tahowa su ke dadab fuskokinsu duk a fusace..ni Rakiya ko me mu kai musu Allah masani".
Amadu yay guntun tsoki da shi kaɗai yaji kayansa sannan ya wuceta zuwa ciki, tabi bayansa da ido tana faɗin,"au ina faɗa maka ruhinta yazo a fusace kana ƙara zuwa inda ta ke...kai wannan ɗa kai da Mairo ban san waya fi wani rashin jin maganar na gaba ba...Amadu gawa ce fa kake tsaye a gabanta, ni dai ina faɗa maka kazo ka karɓo mana takarda wucewa gida". yay mata shiru yana buɗe ledar magungun nan ya fito da su. Malam yace da ita,"Yagana ƙila kin saka wani abu a ranki ne shi yasa, amma Akila da ranta dan yanzun nan fa bacci ya ɗauketa ko minti uku ba'ai ba...". ta katse shi da faɗin,"Adamu kana ina?". ta faɗa tana zura fuskar hijabinta. Malam yace,"gani Yagana". "to ban hanya na wuce, dan ni kaɗai nasan abin da na gani". rufe bakinta kenan a san da ta ke ƙarasowa bakin ƙofa sai gamu mun ƙaraso wurin, kan ƙiftawar ido Yagana ta ture Malam ta koma ciki tana shimfiɗa hailala tana neman mafaka. Ba Malam kaɗai ba, harta Amadu sai da allon ƙirjinsa ya girgiza da ganin Aaliya, abin mamaki da al'ajabin da zasu iya kira ba su taɓa gani ba shi ne mutane masu kama da juna sak irin haka. da ace Akila bata basu labarinta ba, da su kansu a yanzu da suka ga ƴar biyunta zasu iya tsorata su kirata da fatalwa. to amma sanin cewar sun san komai dan haka sai basu ji wani ɗar ba, ba su yi mamakin ganin nata ba kasancewarta tare da Mairo, dama tun a daren jiyan Adawiyya ta kira waya ta ke shaida musu wai Mairo tace ta shiga yawon duniya, Kabiru ya koma gidan ko Allah zaisa ya gamu da ita a hanya sai dai haka ya ƙaraci bincikensa har a tasha bai sameta ba, kuma da suka koma gida yaje gidan Yagana ɗauko wallet ɗinsa ya tarar babu ita babu kayan Mairo ya tabbatar da cewar zai yi wuya idan ba Qatar ta nufa ba, kuma a safiyar yau ɗin ya wuce airpot dan tabbatar da zuwan nata.
Malam ne ya amsa sallamar Aaliya tare da yi musu maraba da zuwa, sai dai sam ita ba fuskantar me yake cewa takeyi ba tun bayan sallamar da ya amsa musu. kanta kawai ta ɗaga musu tana sauke idanuwanta akan Akila da ke kwance tana bacci, yayin da gefe guda na zuciyarta ke mata wani susa da ita ɗaya ta san irin abin da susar ke haifar mata.
"Mairo kin kyauta". abin da Malam yace kenan da ni yana duban fuskata, sai na ɗago da kaina daga barin kallon yatsun hannuna da nake na dube shi na sakan ɗaya sannan ta faɗa jikinsa. "dan Allah Baba kayi haƙuri ka yafe min, nayi kuskure kuma na tuba, ina neman afuwarku". sai kawai ya ɗora hannunsa akaina ya shafa tare da faɗin,"babu komai Maryam, ƙuruciya ce taja kika aikata hakan, amma sai dai ina so na tunasar da ke wani abu, ubanjiji ba ya ramuwar gayya kuma ba ya son masu yinta, don haka ko dan gaba ki dinƙa tunawa da wannan...Allah ya sanyaya miki zuciyarki ya kuma baki haƙuri da juriya...kuma Allah yay miki albarka da ayanzu kika zama silar dawowar mahaifiyarki duniyarta ta asali". maganar da Yagana keyi ta karkata hankalinsu gareta.
"yo aini gaba ɗaya na mance da wannan balarabiyar ta shaida mana ita biyu ce, kai jama'a Allah da iko yake, yo ku me iya ganinku ai sai me dakakkiyar zuciya...ka duba dan Allah wata sarauta ta ubangiji...Mairo to ita wannan ɗin aina kika tsintota?, kar dai kice min ɗaukar fansar ta ki ne ya kai ki can Ƙasarun". "kai Yagana mene wani kuma ƙasaru, Qatar ake cewa". Amadu ya faɗa yana miƙawa Alhassan kujerar zama. a cikin larabci Baba da Amadu suka gaisa da Aaliya kasancewar su na jin kaɗan-kaɗan, Yagana ce dai ta ke ta zabga mita akan tana ta kula Aaliyan tayi mata banza tana yi mata kallon hadarin kaji daga ita har shi zololon ɗan nata. sai da Mairo tace mata,"Yagana dukansu fa basa jin hausa, Larabci da turanci suke ji idan kuma kin iya to bismillah". ta riƙe haɓa da faɗin,"ashe abin babba ni Rakiya ƴar gidan larabci da turamci, da dai alu ambaki ne sai na biya...kuma kema tun farko ai sai ki min bayani ba sai ta kai ga na fara jin haushinsu ba, ko da yake kema Mairo yanzu ai kinfi ƙarfina ni Rakiya Mannir". murmushi kawai nayi, na shiga yiwa Aaliya bayanin cewar Yagana na gaisheta, kai kawai ta ɗaga kamin na ƙara cewa wani abu ta tari numfashina wajen faɗin,"ki tambayesu mene silar ciwon nata?". maganar tata ta fito very cool, kuma har sannan idonta na kan fuskar Ummi da tayi looking very innocent, duk ta rame tayi duhu, idonta kuma bai bar saukar da ƙwallar tausayi ba a hankali.
"to mu dai tana cikin bamu labarin rayuwarta ne sai kuma ta shiga wannan halin". Malam kewa Mairo bayanin, ita ma sai ta juyar da shi ga Aaliyan.
"me tace musu a labarin nata?". Mairo ta kuma faɗawa Malam ɗin, kafin yace wani abu Yagana tayi caraf tace,"ke labarin wannan ja'irar uwar taki da kayan haushi yake, ki faɗa mata ta haƙura daji dan Allah tun da dai tasan komai, ni labarin ɓatan rai yake...ƴar ƙaniya kana kallonta fuska a bar tausayi ashe nan iya shege ne fal a cikinta, banda ma dai yarinya da babu hankali da tausayi ina ke ina haifar ƴaƴa kice a watsar da su, kai kaji wani ɗibarwa kai zunubi...yo ba ma dole aman jini ya maƙure miki maƙogoro ba, ja'irar yarinya kawai me kafiyar jaraba. shegen taurin kanki ai duk shi yajawo miki halin da kike ciki, kuma gwanda da rayuwar ta garaki, kinga kya gane taurin kai abin cutarwa ne".
tayi shiru ta ɗago ta dubeni ta ɗora da cewa,"kema da kika biyo halinta idan kinga dama sai ki sauka tun wuri daga kai...dan ba komai yaja miki zuwa duniya a shegiya ba sai taurin kai...duk da naga jikinki yayi laushi kamar lawashi ban sa ni ba ko ita ƙanwar Uwar taki ta labarta miki komai shi yasa kika rissina...amma ni ai ce nake idan kin tashi dawowa da makamai za ki zo". maganar take min amma ni tuni na bar ganin Yagana da abin da ta ke cewa, tun a san da ta furta kalmar,"ki haifi ƴaƴa kice a watsar!", ba ƙaramin harbawa zuciyata tayi ba, maganar Alhassan ta dawo cikin kaina, kenan suma da tuni yanzu su na a matsayin marayu?, idan ma sun rayu kenan, tun da Jaririn da za'a yasar ai ba lallai ya rayu ba, ita kenan Ummi da bayan laifin zinar ma da ta aikata da sai ta kuma azawa kanta wani laifin?, kamar ta faɗi wani abu sai kuma zuciyarta ta kwaɓeta dan abin da zata faɗa akan mahaifiyartata ba me kyau ba ne.
tasa hannu ta goge hawayen da ke sauka a cikin dasashshiyar muryarta tace,"wai lokacin da ta ke faɗa musu zata zubar damu a time ɗin da ta haifemu shi ne sai kawai ta fara aman jini". "ba ita ta haifeku ba, ni na haifeku". kafin maganar ta kaɗamu ni da Alhassan, ta girgiza Ya Amadu da ke tsaye gefe wanda yay saurin waro ido waje yana faɗin,"what!?".
"Mami kika ce mene?, ke fa kika haifemu? wannan wanne irin batu ne na ɗaure kai?". ta kalli Alhassan ɗin, sannan ta kalleni kana kuma ta kalli Ya Amadu da har lokacin yake mata kallon rashin gasgata maganarta. sai tayi murmushin da ya tsaya iyakar leɓenta kafin tace,"Alhassan kamar yanda ka taso kaji kowa na kirana da Akila ciki kuwa harbda iyayena, to bani bace asalin Akila, ni Aaliya na ke ita kuma wannan ta kwance ita ce Akila, haka kuma ni na haifeku wanda bayan ita da Major da kuma ni ɗin da na haifa Allah kaɗai ne zai shaidi hakan domin shi ne shahidi.
lokacin da na haifeku da ace da wani makami a kusa da zan iya kasheku tabbas a wannan lokacin zanyi amfani da shi wajen ganin na aikata abin da zuciyata ke ingizani akai, na sha baƙar wuya sosai kafin zuwanku duniya, tun daga san da na sami cikinku har zuwa san da aka min aiki aka ciro ku, tun baku zo duniya ba na ke ƙinku, zuwanku duniyar kuma yasa ƙiyayyar taku ta ninku a raina ba don komai ba sai don saboda ban sameku ta hanyar da ta dace ba. a wancan lokacin da na haifeku ni da mahaifinku duk ba ma ƙaunarku, ko da yake zan iya cewa gwara shi akaina, dan ni gaba ɗaya ne bana sonku, shi kuma saboda wani dalili nasa na zubewar mutuncinsa yasa yake jin ba zai iya karɓarku ba balle har ya rayu tare da ku. dalilin da ya sa ya yanke shawarar cewar mu kai ku gidan Marayu idan yaso ko daga baya ne sai mu ɗauko ku, ni kuma nace sam sai dai a zubaku a leda aje a ajiye wanda Allah ya tsaga da rabonsa ya ɗauka, ko kuma ayi floshing naku, muka ɗaukeku da yaƙinin zamu watsar da ku a bola amma sam wannan baiwar Allahn ta hana, tace matsawar muka aikata hakan wallahi sai tayi shari'a damu, shekararmu goma sha bakwai a duniya kuma tun muna yara bamu taɓa samun saɓani da ita ba sai a wannan ranar, wannan rana da kuka zo duniya, wannan rana da ake neman yanda za ai daku. faɗa mukai sosai da ita har Major ya kasa rabamu, nayi mamakin da duk haƙurin Akila sai da na tuƙeta a wannan ranar, dukkanmu muna da baiwar ƙofi amma ita duk zaluncin da mutum zai mata ba zata taɓa yi masa ba, amma a wannan ranar sai da ta min, sai dai sam ba zata iya cutar da ni ba hakan yasa ta maida abinta. na tsira daga baƙar kunamar da ta turo min ta harbeni sai nima na jefa mata nawa ƙofin macijin, macijin da zai iya illata kuzarinta da lafiyarta, to amma sai nayi katari da abin da ya kaini ƙololuwar mamaki akan jaririyar da na haifa a wannan lokacin, abin da kuma har ya tsorata ni. Allah me hikima, me ikon da babu irinsa, cikin ƙudurarsa Maryam ke kika ceci Akila daga wannan macijin da na san ko magani ba zai yi aiki akansa ba, da idanuwanki a waje tar kika kafe wannan maciji da ido da wani irin sauyin halitta ta ƙwayar idonki da tayi har macijin ya kasa tunkararta balle harya cutar da ita, ƙarshema sai ni naji ajikina san da macijin ya ɓace.
babu irin roƙon da Akila bata min ba akan nayi haƙuri mu tafi da ku gida amma sam naƙi, nace ba zan taɓa bari ku lalata min duniyata ba, domin ina da tarin buruka a rayuwata, burukan da su ke na siyasa da kuma riƙe manyan muƙaman da na nake fatan Allah ya ida min nufina akansu, sai dai matsawar ina tare da ku ƙasarmu ta shaida ta yacca na sameku ba lallai wannan burin nawa ya cika ba.
haka kuma ba zan taɓa bari ku lalata alaƙar da ke tsakanina da iyayena ba, gwara ace babu ku sa iya mancewa da su na da shegun jikoki a gefe, balle suci gaba da min kallon ɓacin ran da na haifar musu. amma sai Akila tace,"idan har haka ne to kiyi min alfarma ki taimaka ki bar min su, ina nufin ki mallaka min su mallakawa ta har abada, ta yanda ko da yaran nan sun taso ba zasu san cewar ke kika haifesu ba, ke kika ɗauki cikinsu, kuma ke kika haifesu, amma ji nake tamkar ni nayi naƙudarsu, wallahi Akila ina sonsu, soyayyar da ubangiji kaɗai yasan yawan adadinta, ni ina sonsu kuma zan zauna da su a koma ya suke, tun da kece kika haifesu".
nace da ita,"ta ya hakan zata kasance bayan kowa yasan ni ce nayi ciki ba ke ba?". tana rungume da ke a ƙirjinta kina kukan shan nono tace,"zan maye gurbinki Aaliya, zan zama ni ce Aaliya ba Akila ba daga wannan ranar, ki min alƙawarin ba za ki taɓa fallasa wannan sirrin ga kowa ba ko da ace Allah ya qadarta zan dawo cikin alhalina". "ban gane me kike nufi da idan Allah ya qadarta komawarki ba". "Aaliya ba zan iya komawa ƙasar da akai watsi da ke ba a lokacin da qaddara ta afka miki, lokacin da ya kamata ace an ja ki a jiki, ba zan iya komawa inda aka ƙyamaceki ba Aaliya, Abi da Ammi har yanzu su na fushi da ke ban kuma san ranar dainawarsu ba, dan haka ba zan taɓa komawa gabansu ba sai a ranar da na san sun yafe miki sun bar fushi da ke, haka kuma zan nesanta duk wani abu da zai haifar miki da damuwa ko kuma ɓacin rai, bi ma'ana zan nesantaki da yaran nan kamar yanda kike so, domin abin da kike so shi nake so Aaliya, Aaliya in har rabuwarki da yaran nan zai sakaki farin ciki to ni na miki alƙawarin nisantaki da su har zuwa lokacin da za ki nemesu da kanki, domin ke uwa ce, kuma ko ba daɗe ko ba jima sai kin buƙace su wataran" banji wani ɗar acikin zuciyata ba, hasalima farin ciki nayi da hukunci da Akila ta yanke, wanda yake mafita ce a gareni, tunanina ɗaya shi ne ta yanzu iyayenmu zasu gasgata cewar ni ce Akila kamar yanda ta shirya hakan. hakan yasa nace mata,"amma ai kin san akwai shaidar da su Abi ke gane mu da ita ko". "shaida ba matsala bace Aaliya, nasan za ki san abinyi akanta. ni dai kawai ki min alƙawarin daga yau kin tashi daga matsayin Aaliya a idon kowa kin koma Akila harta ga yaran nan...duk da nasan akwai ranar da zata zo kiji kina biɗarsu ". na amsa mata dana amince, na kaɗa kaina nayi tafiyata ba tare da tausayinta ba ko ɗar a raina, ba kuma tare da tunanin wanne hali zata shiga ba, tunda buƙatata ta rabuwa da ku ta gama biya. fitata babu jimawa sai ga Major ya fito da kai Alhassan, wanda ban san ya suka ƙarke da shi ba har ta bari ya fito da kai, kamar yanda bai saurareni ba, haka nima ban bi ta kansa ba...daga nan ban wuce ko'ina ba sai germany, inda nasa aka min aikin a wuyana, aikin gaira babu dalili sai don kawai na samu shaidar amsa sunan Akila, muna yara tayi ciwon maƙogoro da har ta kai ga sai da aka ma ta aiki, tabon wannan ɗinkin bai goge ba wanda kuma ta shaidar ɗinkinne su Ammi ke iya ganemu. ban koma gida ba sai da na shekara guda bayan aikin ya warke tabonsa ya fito raɗau dai-dai da na Akila. na rayu a ƙasar Germany ba tare da kowa ba, kuma kullum ina ganin yanda ake cigiyarmu a kafafen sadarwa, ranar dana koma gida naje musu ne a zuwan waɗanda akai garkuwa da su, mun kuɓuta sai dai a hanyar tahowarmu da muke gudu muka rabe ni da Aaliya, ban san inda ta ke ba da ita da yaranta. bayan shekara biyu kuma sai ga wani ya kawo mana Alhassan lokacin yana shekara uku, yana faɗin wai an tsinci yaronne tun yana jariri to azurfar da aka gani a hannunsa me tambarin wannan masarautar ita ta bada shaidar cewa shi ɗin na nanne. wannan shi ne silar zuwanka garemu Alhassan, sai dai har kwanan gobe ina tantama akan mutumin da ya ce tsintarka akayi, nafi tunanin mahaifinku shi ya kaika, wataƙila dan ya rasa yanda zai yi da kai. to kunji abin da ya faru, tabbas na aikata muku babban laifi Ƴaƴana, ina kuma roƙonku dan Allah ku yafe min".
tun da Mami ta fara maganar na ɗora kaina akanta nake kallonta har san da tayi shiru, tana saka handky ta goge hawayenta, har tsawon wannan lokacin hannayenta na cikin na Ummi a damƙe kamar wacca ake shirin a ƙwaceta. gefe ɗaya na zuciyata na jinjinawa Ummina Akila, da ta iya wannan sadaukarwar dan kawai rayuwar ƴar'uwarta ta inganta, ta ƙwammaci ita ta shiga wannan ƙuncin rayuwar, da gatanta da komai amma tsawon shekaru goma sha takwas tana raye a cikin ƙauye, lallai samun zuciya kamar tata abu ne da zan iya kiransa mara yiwuwa. kallonta nake da irin kallon mamakin da za'ace matashiya kamarta ta ajiye ƴaƴa kamarmu, dan idan ba wanda ya sani ba yana kallonmu tare da ita zai kirayemu da ƙannenta ne. tabbas ban da uwa ce, ban da ina son albarka a cikin rayuwata, kuma ina so duniyata da lahirata suyi kyau, da na kirata da irin kalaman ɗacin da ke ƙasan zuciyata, infact ma ni ban san a wanne irin sahu zan sakata ba, amma haƙiƙa ita me son kanta ce, tasan da irin halin da ta tafi ta bar Ummi amma tayi biris da rayuwarta, tana can hankalinta kwance, bata da wata matsala, ta manta da cewar ta bar ƴar'uwarta a halin ƙaƙa na ka iya, wanda Allah kaɗai ne yasan halin da ta ke ciki, kuma duk tsawon wannan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 52