Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shekarun bata taɓa waiwayenta ba daidai da rana ɗaya don ta duba halin da ta ke ciki...lallai duniyarta dabance da ta kowa. nasa hannu na share ƙwallar da ta taru a idona, na bita da ido ina kallonta, sai na tsinci kaina a wani irin yanayin da ba zan iya fassara shi ba, yanayin da nake jin wani abu na ratsani tun daga tsakiyar kaina har tafin ƙafata, kafin wata iriyar ƙauna ta uwa ta keta zuciyata da ilahirin jikina, irin ƙaunar da ubangiji ne kaɗai yasan yawan adadinta, lallai uwa uwace, kuma a koma ya uwa ta ke ɗan da ta haifa yana ƙaunarta, haka ita ma a kowanne irin yanayi ɗanta ya kasance ita ma tana ƙaunarsa, ƙwarai kuwa haka ne, domin ga shi akaina, domin ƙaunar da nakewa Gwaggona da Ummi ta banbanta da tata, ban taɓa jin irin wannan ƙaunar me wani sirrin tasiri na daban ba sai akanta, ƙaunar da nasan tata ce, tata ita kaɗai. sai naji a gaba ɗaya duniyata babu wani abu da ya rage min wanda ko da daga shi ne ace na faɗi na mutu burina ya gama cika, shi ne na faɗa jikinta, na rungumeta, na sanya kaina a kan ƙirjinta, naji ɗumin jikinta, wannan ɗumin jikin na uwa, wanda ban samu ba, wanda na rasa shi a iyakar tsayin shekaruna. wani irin shiru ya ratsa cikin ɗakin asibitin, irin shirun da zuciya ke saƙa abubuwa acikinta, Alhassan dai na zaune kawai akan kujera, wanda ya kafe Mami da ido yana kallonta da mamakin da nake ganinsa ƙarara a saman fuskarsa. ni kuwa hannuna toshe yake da bakina saboda kukan da ke neman kuɓuce min tun ɗazu, sai dai naƙi ba shi dama, domin a yanzu gani nake kamar lokacin zubar da wani abu wai shi hawaye ya ƙare min, tunda har gani ga mahaifiyar da ta haifeni, cike da tarin so da ƙaunata da nake gani ƙarara acikin idanuwanta, dama cikin zuciyarta wanda fuskarta ke nuna hakan. tun ɗazu kanta na sunkuye tana aikin share hawaye, na lura da alamu bata so mu gani dan tana gogewa ne ta yanda ba zamu gani ba, kuma sai yanzu ne ta ɗago ta dubeni, ta saki hannun Ummi sannan ta buɗe min duka hannayenta alamun na in taho gareta, ba shiri kuwa jikina na sassarfa na ƙarasa gareta nayi mata wata iriyar runguma, rungumar da sai dana saka ƙashin bayanta amsawa, ita ma kuma ƙanƙameni tayi kamar mai shirin sakani a zuciyarta saboda ƙauna. "kiyi haƙuri Maryam, ki yafe min kinji...". sai nayi saurin ɗago da kaina ban bari ta ƙarasa ba nasa hannu na rufe ma ta baki ina faɗin,"ni babu abin da kika min Mami, Uwa bata laifi ga ɗanta, idan ma tanayi ni dai na yafe miki har abada, nima ki yafe min...abin da kawai nake so naji daga gareki shi ne ki furta min so, wannan soyayyar da kike ikirarin bani da ita a wajenki...". sai tayi saurin rufe min baki nima,"Maryam inji wane yace miki bana sonki?, aina kika taɓa jin uwa na ƙin ɗanta?, ko wancan lokacinma ai wauwta ce akaina, amma wallahi tallahi ina matuƙar sonki, daga ke har ɗan'uwanki...ko kin san da cewar na dawo ƙasar nan neman Akila amma na rasata, sai da na kusan shafe shekara a ƙasar nan amma ban sameta ba ko da labarinta, nasha zuwa ƙasar nan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba duk akan yawon nemanku, sai daga baya naga ashe ɗacin raine yasa naƙi amsarku, amma kewarku Maryam har kusan illata lafiyata tayi...". ni dai kallonta kawai nake gaba ɗaya na kasa kwantanta irin emotions ɗin da nake ji a tare da ni, abu ɗaya kawai na sani, da akwai damar da zan tsaga ƙirjina, na kuma buɗe zuciyata, to tabbas zan ɓoye Mamina acikinta, ko dan saboda wannan nadamar da kuma danasani da suke saman fuskarta su gushe. "Dama nasan za ki zo". Muryar Ummi da ta farka ayanzu ta furta hakan a hankali. wani farin ciki ya lulluɓe Mami sai ta sakeni ta koma gefen gadon ta rungume ƴar'uwarta. "Akila dan Allah ki yafe min...ni ban ma san me zance miki ba, bakina yayi kaɗan ya furta duk wasu kalamai a akanki". Ummi na goge ma ta hawaye tace,"ba ki min komai ba Aaliya, idan ma kin min na yafe miki tuni...ina Alhassan?". Mami ta saketa tana mata nuni da shi, wanda ya taso a yanzu shi ma fuskarsa cike da murmushi, ya tsaya a gabanta yana mai rissinar da kansa tare da cewa,"barkanki dai Gimbiya, Barkanki dai Ƴar Sarki Jikar Sarki, Barkanki dai jarumar Mace, Barkanki dai Macen da babu irinta a wannan duniyar, Barkanki dai Uwa ta gari, Alhassan na gaisheki, yana miƙo gaisuwa da jinjina a gareki, ubangiji yaja zamaninki, Ubangiji ya ƙara miki lafiya, ya wanzar da farinciki a rayuwarki, yay miki katanga da dukkan wani abin cutarwa da zai riskoki...daga ƙarshe ina ƙara jinjina Ummina, Ummin Alhassan, ɗanki Alhassan na neman albarkarki". ya ƙarasa faɗa yana zube gwiyoyinsa a ƙasa, tare da duƙar da kansa a gabanta da dunƙule hannu ya ɗaga babban yatsansa ɗaya. tana murmushin da ya bayyanar da duka haƙoranta ta miƙo hannu ta dafa kansa, tana saka masa albarkar kaman yanda ya nema, sannan ya miƙe yana mai kai mata sumba a goshinta, itama ta sumbace shi tana me rungume shi da faɗa masa iya adadin tarin soyayyar da ta ke masa, da faɗa masa cewar taso ace shi ma ta rayu tare da shi, amma kuma ta godewa Allah daya sa ya rayu tare da mahaifiyarsa, wanda hakan ishara ce gareta, yanzu ta gane baka taɓa tsarawa kanka komai sai wanda ubangiji ya tsara maka. sannan ta jaye shi daga jikinta tana faɗin,"ina ƴata? ina abar ƙaunata? ina masoyiyata? ina farin cikina?". ta faɗa tana mai dubana, wanda ni kuwa a lokacin na ɓata fuska, ina tura baki gaba kamar zan fashe saboda kishi. ta ƙasan ido naga yanda ta faɗaɗa fuskarta da annashuwa, kamar ta shiga zuciyata taga abin da ke ciki sai naji tace,"ko dan gaba wannan Ummin Maryam ce bata Alhassan ba, ina fatan kai da Babarka za ku shaida hakan...taho gareni Maryam ɗin Umminta". ta faɗa tana me buɗe min hannu, na tafi gareta kai tsaye na faɗa jikinta har sai da ƙirjinta ya amsa, na shiga raira kuka a hankali ina bata haƙurin abin da nayi ma ta. "Ammi da Abi fa?". tayi tambayar ga Mami. tace da ita,"nan da anjima kaɗan zamu isa garesu". sai ta ƙara cewa,"anya zan iya tafiya na bar su Malam?, Aaliya bana jin zan iya ci gaba da rayuwar wani wajen ba tare da waɗan nan bayin Allahn ba". Mamin tace,"nima na sa ni, kuma ko da nazo na sami irin karamcinsu gareki sai lissafin komawa da ke ɗaya ya sauya, ƙafarmu ƙafarsu insha'Allahu, in dai har sun amince". Yagana muka ji tana faɗin,"ni dai ana shiga da hakkina a wurin nan, kusan rabin awa anata magana amma ni Rakiya ban san me ake cewa ba, to Allah yasa dai ba munafurcina ake ba". sai kuma ta dubi Ummi tana faɗin,"ja'ira, ai ki saka ran idan na maida ke gaban iyayenki sai na saka wannan masifaffiyar Kakar taki ta jibgeki". nace,"amma dai Yagana lokacin da bana numfashi ko? dan me taɓa Ummina ko ruwan sama sai nayi niyya, ah toh". sai ta harareni tace,"ke fa ba kya gane mutum na jin haushinki ko?". na ƙyalƙyale da dariya ina cewa,"Hajiya Yagana muyi daɗi muyi tsiya". tace,"inda kike cutata na sakko daga fushin da nake ki haɗa sunana da kalmar Hajiya". sai na ƙarasa gareta na dafa kafaɗarta ina faɗin,"ai kinma gama zama Hajiya da yardar ubangiji, Yagana indai da rai da lafiya kin dinga zuwa hajji da umara kenan har ƙarshen numfashinki, sai dai idan babu familyn Shaik Samin a raye". ta shafa kumatuna tace,"Allah ya amince...yanzu faɗa min abin da wannan baturiyar ta ɗau lokaci tana faɗa muku". nace da ita,"ki tambayi Ya Amadu". ta buɗe ba ki zata masa magana shi kuma ya ɗaga wayarsa da tayi ƙara, kalmar da ya ambata bayan amsa sallamar da yay ita taja hankalinmu gareshi kowa ya tsare shi da ido, ƙirjin kowa na amsawa. "innaillahi wa'inna ilaihi raji'un, aina ne?". bamu san me akace masa ba ta cikin wayar sai ji mu kai yace,"dan Allah Malam ka taimaka ku miƙa shi asibiti mafi kusa, yanzu yanzun nan zamu ƙaraso da izinin Allah, dan Allah ku taimaka kuyi duk abinda ya dace gani nan ƙarasowa". lokacin da ya sauke wayar daga kunnensa kowa ya haushi da tambayar meke faruwa?, yana nufar hanyar fita yace,"Kabiru ne yay hatsari, kuma hatsarin me muni dan yanzu haka ma anata ƙoƙarin ciro shi daga cikin mota ne abin ya faskara". ban san sanda nayi mutuwar tsaye ba, take kuma naji wani dunƙulallan abu game da Ya Kabiru ya nemi waje ya tsaya a zuciyata, kamin furucin Ya Amadu ya shiga haska min hoton faruwar abin a idanuna, hoton Ya Kabiru a cikin jini, a cikin mummunan hatsarin da aka ambata, Ya Kabiruna dai!, sai kawai nayi saurin gimtse idona ina girgiza kaina dan kawar da wannan hoton da ke haska min. daga can kuma sai naji Mami na faɗin,"tabbas wannan hatsarin shirya shi akayi, ba hatsari ne na haka kawai da ya same shi ba, wani ne a gefe ya shirya masa shi saboda yana so yaga bayansa". Ya Amadu da nake gani dishi-dishi naga ya dakata da fita ya juyo yana kallon Ummi. kuma Baba sai yace da ita,"Akila me kike cewa ne?". Yagana tace,"ina ga fa ciwon kamar har da surutai ya sata ko?". tayi maganar tana me gyara ɗaurin zaninta tare da cewa Amadu,"kai shige mu tafi ka bar batun wannan, Kabirun yana ina aka ce maka?". Ummi ta buɗi baki taci gaba da cewa,"Malam akwai ɓoyayyen sirrin da ya jima yana faruwa a gidanka wanda babu wanda ya san da shi sai ni, ni ɗinma daga baya na sa ni, wannan SARAN ƁOYEN da aka jima anayi a cikin wannan gida tun daga lokacin da Maryam ta kamu da ciwon ƙoda har zuwa kan wannan gaɓar ta hatsarin da ya sami Kabir, hatsarin da ba shi aka shiryawa ba Amadu aka shiryawa shi sai kuma shirin ya faɗa akansa...sai dai zan iya cewa ba kuskuren aikin aka samu ba, canja tsarin akai". tayi shiru da wani guntun murmushi a saman leɓenta na baƙin ciki da takaici kafin ta furta,"Amarya! Malam Amarya ce ta shirya wannan hatsarin da manufarta da ban santa ba, amma tabbas aikin Amarya ne, aikin amarya ne ɗirkawa Maryam wannan ƙwayoyin da suka haifar ma ta da matsalar ƙoda, kuma aikin Amarya ne zubawa Maryam abin da ban san menene ba har tayi wannan ciwon cikin, kuma aikin Amarya ne yi mata turen wannan macijin da ya rutsa da ita a banɗaki, Malam da sa hannun Amarya akayi kidnapping ɗin Maryam, kuma aikin Amarya ne yin wannan allurar gubar wa ƙafar Gwaggo har ta zama silar mutuwarta, sannan akan gaɓar shirinta na yanzu shi ne taga bayan Ahmad da Kabir...kuma Malam idan nace maka gonakinka da aka ƙwace ba gwamnati bace Amarya ce ba lallai ka gasgatani ba duk da cewar waɗannan magangunan nawa ma ba lallai su zama abin yarda a gareku ba, tunda banda wata hujja, amma idan ba ku yarda dani ba nasan za ku iya Yarda da Kabir wanda ya san komai...fatana da adu'ata shi ne Kabir ya rayu ko dan saboda alƙadarin Amarya ya karye, ko dan ya tsaya min wajen kafa muku hujjar da za ku yarda da abin da na faɗa muku...Ahmad kai gaggawar zuwa inda yake da wuri, ai saurin miƙa shi asibitin da zai sami kulawa duk da ba likitocinne da iyawar ba, ubangiji shi zai yi iyawarsa". abin da zan iya cewa shi ne ba duka naji maganganun nata ba, na san dai ƙafata ta riƙe kamar an kafani ne a wurin, haka kuma ban san lokacin da ƙafata da nake tunanin ba zan kuma iya ɗagata ba sai sanda naga Ya Kabiru a gabana da lafiyarsa, na motsa na kai bakin ƙofa na tsaya daga gefen Ya Amadu, nayi saurin miƙa hannu na riƙo shi saboda juwar da naji tana neman ɗibana, har ga Allah ban san me nake ji ba, ban kuma san meke shirin faruwa da ni ba, idona da basa gani da kyau Ya Kabiru kawai suke son gani sannan su washe, kamar ƴar maye ko kuma wadda ke cikin nauyin bacci na tafi luuu na faɗa jikin Ya Amadu wanda yay saurin daidaita min kaina a saman ƙirjinsa dai-dai lokacin da ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya da zan iya cewa daga ita ban sa ke jin komai ba. *A can ɗaya ɓangaren.* Amarya ce zaune akan kujerar da ke cikin matsakaicin falon gidan, yayin da wata ma ta ke fuskantarta, yanayinta na nuni da na wanda ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga mutumin da ke masa bayani. a wannan lokacin babu abin da zaka tsinta a saman fuskar Amarya face zallar ɓacin rai, babu walwala balle yanayinta ya nuna maka tana tare da wani abu wai shi farin ciki. ta kai hannu ta zame ɗankwalin da ke kanta zuwa baya, sannan ta fuzgar da iska daga bakinta, ta dubi matar da ke gabanta da irin kallon da zai shaida maka girman matsayin da take da shi ga waɗanda suke ƙasanta. wucewar daƙiƙa biyu tana dubanta kamin ta ɗauke idonta daga kanta ta mayar da shi kan wayarta da ke gefenta tana ringing, ta ɗaga wayar ta kara a kunne da cewar,"bana son wani abu wai shi kuskure ya kuma shigowa cikin lamarina, ka faɗa min kawai anyi nasara Musbahu?". ban san me na cikin wayar ya faɗa mata ba sai naji tace da shi,"ka tabbata raunin da ya samu ba zai bar shi ya ƙara shurawa ba?". wucewar wasu sakanni kamin na cikin wayar ya gama bata amsar tambayarta sannan ita kuma tace da shi,"da kyau!, yanzu kayi abin da zaija tsaiko a wajen mutanen da suke ƙoƙarin kaishi asibiti, kuma tunda kace sun kira waya nasan Amadu suka kira, kuma Amadun zai ce zai taho wurinsa, ka kafa ka tsare Musbahu kar Amadu ya ƙarasa wajen nan, domin duka su biyun nake so a rasa a lokaci guda, ta yanda zanyi aikin kwashe duk wata dukiyar da Kabiru ya tara ba tare da hankalin kowa ya kawo kanta ba...sannan a ɗazu da na koma gida na tsinci maganar su Zulai su na batun kamar ita wadda ta zauna a gidan namu ɗiyar wata ƙusan ce, dan sun ga alamun hakan a jikin ƴar'uwarta da tazo, to da zarar ka kawar da Amadu shi ma, ina so ka shiga yi min binciken wacece Kulu, yanzu zan san yanda nayi Malam ya faɗa min a salinta ta yanda aikin zai zo maka da sauƙi....". *Plss Share&Comment and also vote.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *(37)* "an gama ranki ya daɗe, zanyi kamar yanda kika faɗa, ba za'a sami kuskure ba, wannan alƙawari ne nayi miki". Musbahu ɗin ya faɗa daga can inda yake. "shikenan sai naji daga gareka, komai ake ciki kai saurin sanar da ni". ta sauke wayar daga kunnenta tana me yasar da ita a gefenta. sannan tayi wani murmushi mai ciwo, irin murmushin nan na takaicin rashin cimma wani abu da kai burin samu, sannan ta kwantar da kanta ajikin kujerar. "Amma Yaya kina tunanin za ki cimma nasararki a wannan karan?, sai nake ganin kamar lokaci ya ƙure miki ko kuma ma nace lokacin ya tsaya miki cak, domin anzo gejin da ba zai barki kici gaba da amfani da shi ba". Khadija wadda ta ke ƙanwa ce gareta tayi maganar. Amarya ta ɗau lemun soɓo dake cikin kofi ta kafa a baki, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye shi tana mai sauke numfashi. sannna ta dubi Khadija tana murmushin mai bayyana irin yaƙinin samun nasarar da ta ke da shi akan dukkan wani abu da ta rubuta shi a lissafinta sannan tace,"nasara bata taɓa juya min baya ba, kuma zan iya cewa tayi kaɗan ta juya min baya a wannan lokacin, kan wannan gaɓar, akan wannan gaɓar da na ke tunanin na kammala dukkan shirina da na lissafa...tukunna ma! me kike nufi da lokaci ya tsaya min?". Khadija tace,"tun lokacin da kika shirya cewar za ki kauda Kabiru da Amadu na faɗa miki hakan kaman ganganci ne, shi yasa a yanzu da aka zo gaɓar da Kabiru ke kwance a asibiti na ke ganin kamar asirinki zai tonu...". ba ta kai ga ƙarasawar ba Amarya ta dakatar da ita,"ke za ki fallasa ni ko?". ta girgiza kanta,"a'a ko ɗaya ba haka bane...idan aka kai Kabiru asibiti a wannan yanayin da yake ciki dole sai hukuma ta shiga cikin lamarin, shi yasa nake tsoron me ka iya zuwa ya dawo". cikin tsananin ɓacin rai Amarya ta dakatar da ita wajen kiran sunanta a tsawace,"kar ki ƙara min wannan zancen, kar ki ƙara idan ba haka ba kuma ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci...ta ya za ai ki dinga kutso min da wata magana mara daɗi cikin sha'anina, ke kin san kuwa tsawon shekarun da na ɗiba ina gudanar da aikina domin cikar burina, babu boka babu Malam da irin dabaruna kawai da suke cikin kaina nake aiwatar da komai nawa da babu wanda ya isa ya gane ina da wata fuskar bayan wacce kowa yasan ni da ita, wannan kyakykyawar innocent fuskar, bari kiji na faɗa miki, ko da lokacin ya yanke, duniyar Amarya ba zata juyawa ba daga yanda ta ƙawatata da tsarata, duniyar nan da kike gani ita ce al...". caraf Khadija ta dakatar da ita daga abin da zata faɗa, wannan kalmar ce da kullum ta ke faɗa mata a matsayinta na wadda tayi imani da Allah da kuma manzonsa bai kamata ta ke faɗar irin wannan kalmar ba, wanda hakan zai sa ta iya fita daga imaninta, cewa da ta ke duniyar nan ita ce aljannarta, saboda ta gina ta da abubuwan da ko da an shafe tarihin kowacce halitta zata ji daɗinta ba zata wahala ba".(auzubillah), ƙwarai matuƙa Khadija na jin takaicin wannan kalmar shi yasa sau tari ta ke kutso da wani zancen a duk san da Amarya tayi yunƙurin furtata. "Khadija ada ni mutum ce kamar kowa me anfani da zuciyar da ubangijina ya halicceni da ita, amma a yanzu sam ba haka nake ba, tuni na sauya wannan zuciyar zuwa irin wadda nake so ta zama, ta yanda zan cimma burina a gidan Malam, ba dan komai ba sai dan bana so na tashi a tutar babu in Malam yay sallama da wannan duniyar, bima'ana ba zan iya zuba ido naga wasu da ƴaƴansu kaɗai sun wawashe dukiyar da Malam ya tafi ya bari ba, ba zan iya ba!, shekarata ɗai-ɗai har goma sha biyu a gidan Malam amma kullum abin da yake faɗa min game da rashin haihuwata shi ne Amarya ki ƙara haƙura, ubangiji shi ne me yi, yana sa ne da ke, kuma duk wani jinkiri da kika gani a rayuwar mumini wallahi alkhairi ne, dan haka kar muyi azarɓaɓin da zaisa mu iya kauce hanya, saboda kiji daɗi yasa na ba ki Mairo, wannan Mairon da kike jin tamkar ke kika tsuguna kika haifeta". ta rufe ido kafin taci gaba da magana,"ni ba ciwo ba, lafiyata ƙalau amma ace tsawon shekarun nan da nake gidansa banyi shukar da rassanta za suyi irin yaɗon da ba zai sa na jigita ba in bana tare da shi, ehh haihuwa ta Allah ce amma abin yana damuna". tai shiru tana mai jan nunfashi, ta kai hannu ta damƙe glass cup ɗin da ke kan taburin gabanta, wanda tana ƙara sa masa wani ƙarfi zai iya tarwatsewa. "Malam yay kuskure da ya bayyana soyayyar Suwaiba ɓaro ɓaro ga kowa, da kuma kasa ɓoye irin matsayin da ta ke da shi na daban akanmu a wurinsa, da fifitata da yay ya bata wani linzamin matsayi daban da namu acikin fadar zuciyarsa, da irin yanda ba ya yabon kowacce acikinsu sai ita, komai it ta iya, haƙuri ita ce, hali ita ce, nagarta ita ce, sanin ya kamata ita ce, iya kula da tarbiyar yaro ita ce, idan wani sirrin nasa ne ita ce, yabawarsa da bajintarsa duka nata ne...wannan dalilin shi yasa na kasa danne zafin kishin da na ɗebi shakara da shekaru ina yi akanta, na shiga na fita na kauda ita cikin ƙanƙanen lokaci, buƙatata ta biya, kuma burina ya cika, domin a yanzu dukkan wata daraja tata da matsayi zai dawo kaina". sai kuma tai wani murmushin nasara da ya tsaya iyakar leɓenta taci gaba da cewa,"ƴarta kuwa Mairo, ko kuma nace ƴar zinar da ta riƙe Mairo na zanata a cikin lissafina ne tun bayan shekaruna biyar da zuwa gidan, dalilin da ya sa naso na kassara rayuwarta tun farko kenan amma sai Malam yay gangancin shigar min cikin al'amarina har aka samu aka ceci ranta". sai tayi wani tsaki da ke bayyana tsantsar takaici kamin tace,"ban san dalilin da ya sa Malam ya fifita yarinyar nan akan duka ƴaƴansa ba, Khadija Malam ya shayar da ni ruwan mamaki da na san gaskiyar cewar Mairo ba ƴarsa bace...Malam ya so yarinyar fiye da yanda alƙalami zai rubuta, ke zan iya ƙaryata duk wanda ya nemi ya kwatanta irin yacca Malam ke sonta, saboda ba abu ne da zai ƙiyastu ba dan ko mizani yay kaɗan ya auna irin soyayyar da yakewa yarinyar nan, shi yasa tun kamin na kamu da kishin Uwar riƙonta na kamu da nata, ni da Mairo na fara kishi a gidan aurena, ƴaƴan Malam sama da goma sha uku amma kyace ita kaɗai ya haifa, shi yasa da sirrin ɓoye ya fito fili na ɗora alƙalamin zargina akansa, zuciyata bani ta ke shi yaywa Uwarta cikin nan dan ruwa ba ya tsami banza". Khadija da ke dubanta da tsantsar mamaki tace,"kina nufin Yaya Mairo ma kinsa hannu a cikin rayuwarta?". "ƙwarai kuwa, aini da ita na fara kishi kamin matan gidan...nayi amfani da kissata ne wajen karɓarta a matsayin ƴa ta yanda zan kauda ita cikin sauƙi kuma ba tare da wani abu ya taɓa farina ba, ni na dinga ɗirka ma ta wasu ƙwayoyi da nasa aka min safararsu waɗanda za su illata ƙodarta, kuma sunyi ɗin, amma sai Malam ya sadaukar da ƙodarsa ɗaya gareta, haka kuma ni na ɗauki kwangilar ɗauketa da akai...hmmm cikin hikima na ke gudanar da aikina ta yanda hankali ba zai taɓa gasgata zargi akaina ba, a yanzu idan na dafa ƙur'ani nace ni na zuba ma ta maganin ɓera a tsiren da taci babu wanda zai gasgata ni, illama kallon mahaukaciya da za'a min". sai kuma ta bushe da dariya sannan ta ƙara cewa,"ban taɓa aikin asiri ba sai a san da nasa aka tura ma ta maciji, kuma nayi danasanin wannan lokacin saboda ban sami biyan buƙatar haukacewarta ba kamar yanda na tsara, Mtsssww Yasira ce ta bani wannan banzar shawara, dama tun farko na faɗa ma ta ni ban yarda da wani aikin asiri ba, shi yasa na barta akan komai, dalilin haukar Yasira da kike ganin shi ne wannan silar...Khadija ada Mairo da Uwarta ne kawai a cikin lissafina amma daga baya sai Yasira ta nusar da ni zuwa hanyar da ni ban taɓa ganowa kaina ita ba saboda kishin waɗancan abubuwan da suka rufe min ido, Gado! tsawon shekarun da na ɗauka babu haihuwa a gidan Malam banza a wofi zan tashi in ya mutu, ban mallaki komai daga gare shi ba balle na sami gadon wani abu me tsoka, na ɗauki tsawon shekaru ina rayuwa tare da shi amma ban shuka bishiyar da rassanta za su min amfani ba a san da baya raye?...dalilin shigar lissafi na uku kenan cikin tsarina, da Mairo da Suwaiba ne kawai, amma sai tunanina ya lissafa min cewar ya kamata sauran

Chapter 35 of 52