Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gmail daga office nasu na Fidelity Bank akan an turata course a itally na tsawon wata 6, takaici iya takaici tayi, struggle ta saba da shi, amma a wannan karan kam ta gaji, saboda tayi kewar mijinta sosai, dan haka dole sai Dad ɗinne ya bita can tunda shi ba shi da wata matsala ta office ko wani abu makamancin haka. *3:00pm.* ƙarfe uku da rabi na dare bugawar agogo, Mairo ta farka a lokacin dan shan ruwa, ta duba kan table taga babu roban faro da bata rabo da ajiye shi saboda shan ruwan dare. ɗan tsaki tayi ta duba tulin littafan da ke gabanta, karatu take tayi bacci, baccin da ya ɗauketa bata sani ba. ta sakko daga gadon ta fito, ta sauko parlon ƙasa dan babu ruwa a friedge ɗin parlonta, ta gama shan ruwan zata koma sama sai taji kamar maganar mutum, ta tsorata amma bata fasa dawowa da baya ba ta shiga laluben ganin waye. ta ɓangaren ɗakin ajiyar littafai take jiyo sautin murya na fita a hankali, ta nufa wajen cikin sanɗa, da mamakinta Dad ta gani tsaye riƙe da waya a kunnensa, yana magana ƙasa-ƙasa, maganar da ta yi kama da ta sirri, ba wannan ne karo na farko da ta sha ganinsa a irin wannan lokacin ba yana waya, karo na kusan huɗu kenan, a yau dai ta gama fahimtar akwai wani abu da Dad ke ɓoyewa a gidan wanda baya so a sani, taji muryarsa ta ɗaga cikin faɗa yake cewa, "kai gaba ɗaya ba zaka gane ba...na gama yanke shawarar zan haƙa rami na binnesu, dan haka a gobe ba sai jibi ba, hakan ne kaɗai zai sa na sami nutsuwa hankalina ya kwanta". sai kuma ya ƙara yin ƙasa da murya yana ci gaba da faɗar abunda bata ji, har sanda ya gama wayar ya buɗe ɗakin littafan ya shiga sannan ya fito, da gudu ta bar wajen ta koma ɗaki. ta haye gado tana maida numfashi, _zan haƙa rami na binnesu._ maganar ta ƙara haskawa acikin kanta a karo na barkatai, ba wannan ba ma, me Dad ke ɓoyewa?, me yasa take yawan ganinsa a irin wannan lokacin?, tukunna dai, me yake da bindiga a tsakiyar wannan daren?, lokacin da ya shiga store ɗin littafan me ya fito yana gogewa a hannunsa?, *SIRRIN ƁOYE*, tabbas akwai wani sirri da Dad ke ɓoyewa, ba kuma yaso kowa ya sani, menene shi?, taiwa kanta tambayar a sanda maganarsa ta kuma haskawa cikin kanta _zan haƙa rami na binnesu kawai, hakan zai sa na sami natsuwa hankalina ya kwanta._. jikinta har lokacin bai bar rawa ba, ta miƙa hannu ga landline ɗin da ke kan bedside drower, dole ta sanar da Brother Ema, ya kamata ya san da wannan, ai dama dukansu sun fara suspecting nasa akan wannan keɓewar da yake cikin dare, Obi ma yace sau biyu yana ganinsa, kuma da bindiga a hannu. sai dai kuma me, har tayi dialling numban nasa sai tunaninta ya sauya, ta sauko daga kan gadon, ta nufa tulin littafan da suke cikin wata drower ta ɗauko wani littafi da ta aro a library jiya, Malaminsu yace musu littafi ne guda da ke ɗauke da bayanin duk wasu stratagies na yanda zaka karanci fuskar mutum farat ɗaya. *Vote, Comment & Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _The Pages Completely Goes To duk wani makaranci littafin sirrin ɓoye, na gaisheku, ina kuma yi muku Son So fisabilillah...masu text messages da kirana a waya su na yaba min, ku sani ina jin daɗi kuma ina godiya a gareku._ *24)* *Kano, Bichi.* wata takwas! watanni takwas kenan rabonsu da saka Mairo a idonsu, Mairon da tun su na saka rai da dawowarta har sun haƙura sun fawwalawa Allah. zata dawo garesu? ba zata dawo ba? tana raye ko ta mutu? Allah ne masani. anyi neman, anyi cigiyar amma shiru, sai adu'a da ba za su daina yinta ba, ba za su taɓa mantawa da ita ba, tarihinta ba zai taɓa gogewa a garesu ba, diman da'iman, ɓatanta shi ne tashin hankali na farko da suka fara cin karo da shi a rayuwa, ko mizani ba zai iya auna alhinin da suke ciki ba na game da rashinta a tare da su. _zuciya sirrin me shi take, ko ka kasa kunnuwa ba zaka jiyo komai ba._ _shi ko SO kamar iska ya ke, ko ka tara hannuwa ba zaka taɓo komai ba._ _ni da ke kamar Laila Majnun muke, ko da mutuwa tazo ba zata ɗau ɗaya ta bar ɗaya ba._ waƙar da ke tashi kenan ta cikin ƴar ƙaramar radion da ke aje kusa da turken awakin Yagana. Yaganar da ke daga cikin turken awakin tana ba su abinci tace, "kiwa Allah ki kashe wannan radion ko kuma ki sauya tasha ki kai inda suke wa'azi, haba abu babu daɗin sauraro tun ɗazu waƙar ke hawar min kai wallahi, na miki alamar da za ki gane kinƙi, da yake ke ƙwaƙwalwar taki cunkus ce". "A'a fa Yagana, ba zai yiwu na zo gidanki ina taimaka miki da aiki ba kuma ki hanani shaƙatawa, ina dalili...ke ba kin san sirrin da ke cikin waƙar bane da ba ki ce na kashe ba, idan na kashe ma aikin ai ba zan iya ba". Adawiyya wacce ke zaune kan kujera tana tankaɗen garin masara ta faɗa. "yo ni ina ruwana da sirrin da ke cikinta...da kike kallona haka har yanzu jimamin rashin Mairo ƴar albarka bai barni ba ƙarfin hali kawai nake, saboda haka ki kasheta kawai ko wallahi idan na fito nabi ta kanta tunda ba tawa bace". Adawiyya ta kyaɓe baki ta shiga ƙunƙuni sannan ta kashe radion, domin tasan sarai Yagana zata iya fasa radion sai dai idan bata fito ba. taja dogon tsakin takaici, yo ai ita zata iya rantsewa ma ta manta da batun wata Mairo, dan anata ɓangaren sam ɓatan Mairo bai tada hankalinta ba balle ya dameta, ai ko lokacin da suka dawo daga makaranta su ka sami labarin ɓacewarta da za'a buɗa zuciyarta za aga kaf duniya tafi kowa farinciki, murna da tsananin farin cikin da ta shiga a lokacin Allah yayi yawa da su. tun yaushe Mairon ta zame mata alaƙaƙai, ta jima da hawar mata kai tana neman hanyar da zata ɓarar da ita, cikin sauƙi sai gashi Allah ya dubeta ya dubi kukanta shi da kansa ya kawo mata ɗoki, kuma insha'Allahu tana fatan har duniya ta naɗe Mairo dai ba za'a ganta ba, ko da za'a ganta kuwa sai dai aga gawarta. "Hmmm". tayi wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, to ai ko alawar da aka ga tana siya tana rabawa yara sadaƙa da tata manufar tayi, kuma ko da Inna Amarya ta shigo ɗaki ta sameta tana aljanu duk na ƙarya ne, rawar jin daɗi take a sa'ilin kawai sai taji an ɗaga labule shi ne ta zarce da aljanun ƙaryar. Ƙaya! ai idan anji ana batun Ƙaya ɗaya ma kenan, ai Mairo ƙaya ce a gareta, tun ranar farko da ta fara ganin Suhail taji ya mata, ya shiga zuciyarta yayi bake-bake, tana sonsa, tana sonsa da manufa ta aure. amma daga ba ya sai ta fahimci Suhail Mairo yake so, Mairo ce a zuciyarsa, ko ba'a faɗa ba ta sani, masarautar bichi ta ɗauki tallafin karatunsu ne saboda Mairo, saboda da ta sami gogewar ilimin boko ta yanda a gaba zata iya shiga cikin zuri'arsu. shi yasa tun a ranar da suka dawo daga masarautar bichi taji ta tsani Mairo, ba Uba ɗaya ba, ko da ace ciki guda suka fito to ta tsaneta, ita ce ta dace da Suhail ba Mairo ba, ko san da ta fita a sabgarta tayi hakanne dan Mairon ta fahimta amma da ike ƙwaƙwalwar kifi gareta ta kasa gane komai, har take wani kuka a gabanta tana neman afuwar abin da tayi mata, a lokacin ji take kamar ta shaƙeta ta mutu, sai taga wa Suhail ɗin zai aura, ai sai dai su duka su rasa, ta rasa me ya sami idon Suhail ɗin ma, da me Mairon ta fita da har ita ya kasa ganinta ya ƙyasa?, sai wata Mairo da yake ta rawar ƙafar ingantawa rayuwa, Mace ƙirji kamar ɗan malele, baya duk a shafe. sau biyu tana yin mafarkin Suhail ya auri Mairo, hauka ne kawai bai kamata ba, shi yasa ta ƙudurta ɗaukan mataki, matakin da take ganin zai kai ta ga Nasara. tabbas duk duniya Uwar da ta tsuguna ta haifeka ita kaɗai ce me sonka, ita kaɗai ce me ganin ta share maka hawaye, ita kaɗaice me yin duk yanda za tai wajen ganin ta rabaka da damuwa, a yanzu ta sani, ashe a ba ya shirme take da ta biyewa su Gwaggo a ganinta su ne zuciyarsu me kyau, ashe ƴarsu Annoba zata zame mata. dalilin da yasa tayi hankali kenan ta sanar da Innarta komai. babu kwane-kwane ta sanarwa da Mahaifiyarta matsalarta, ai dama Innar ta taɓa tambayarta dalilin da ya sa kwana biyu take ganinta kamar ba'a hayyacinta ba, amma sai tace mata babu komai, Innar kuma bata ƙara bi ta kanta ba saboda tasan dama bata faɗa mata matsalarta sai dai taje can ta faɗawa Gwaggo. a sanda ta sanar da Innar, tayi dariya tace,"ai bari ba shegiya bace tana da ubanta, yanzu kinji uwar bari kenan". tayi narai-narai da fuska ta kamo hannun Innar, ta soma hawaye tana faɗin,"Allah Inna da gaske nake ina sonsa, kuma wallahi idan ya auri Mairo zan iya kashe kaina, dan zuciyata ba zata juri ganinsu tare ba...Inna ni ina faɗa miki ma yanzu na tsani Mairo dan ashe tuni gonata take shiga ban sani ba, wallahi da nasan hanyar da zanbi na kawar da ita Allah sai nabi". kuka take sosai a san da tayi maganar. Innar ta tsaya tana dubanta tsawon lokaci, Adawiyya ta san wace mahaifiyarta, dole zata nema musu mafita. Innar ta saki murmushi me cike da tarin ma'anoni tace,"ke ni fa ba shashashar uwa bace da zan zuba ido Mairo ta auri jinin sarauta, nawa Ƴaƴan kuma su ƙare a auren ɗan ƙauye gidan manomi. saboda haka ki share hawayenki ki bar kuka, asiri gaskiya ne, dan haka in dai akwai boka a duniya Yaron nan sai ya bar kan Mairo ya dawo kanki, in ba haka ba kuwa to ya zo da batun auren nata sai ta aure shin na gani, ai sai dai idan bana numfashi, ko kuma ke da ita ɗin duk ku rasa. ba Mairo kaɗai ba har Uwarta wallahi sai sun shiga tsumin wahala, kamar yanda na aika Hajiya lahira to suma tasu rayuwar a tafin hannuna take, ƙiris na ke jira, kuma lokaci yayi, nayi alƙawarin ko zanyi yawo tsirara sai nasa Rayuwar Mairo ta ƙare a tangaliliya. can dama kece mara wayon, kin nane a gindinsu kina nuna min Uwarta ita ce me ƙaunarki bani dana haifeki ba, na sha faɗa miki ba ƙaunarki suke ba amma yarinyar sai kika yi sautin mahaukaciya da ni, to ai gashi nan ta nemawa ƴartata miji me ido da kwalli ke za su barki a gidan ɗan dako. to wallahi ko da ace ba kya sonsa ba zan bari aurenta da shi ya tabbata ba". Adawiyyan ta kuma fashewa da kuka,"ni dai Inna kiyi duk yanda za ki ki tarwatsa sonta daga zuciyarsa, dan wallahi a yanda na gama fahimtarsa aurenta yake so yayi, ranar ma fa da suka kwana agidan nan ina jinsa yana cewa da Ƙaninsa yaga Matar aure a gidan nan, to na rantse miki da Allah Inna in har baki nema min mafita ba zan kashe kaina, kisa Suhail ya bar kanta ya dawo kaina". Zulai ta kuma dafa kanta, tai ƙasa da murya tana ce mata,"ke na fa ce miki ki bar zubar da hawayenki a banza a wofi, zan tabbatar miki da Suhail ke zai aura ba waccan abar kamar sillan kara ba, yanayin jikinki shi ya dace da gidan hutu, matar manya, na faɗa in dai da boka to hawayenki daga yau ya daina zuba. Suhail zai dawo sonki kuma zai aureki, sannan zan yi amfani da basirata da hikimata wajen ganin na tarwats...". bata ida abun da zata faɗa ba Amadu ya ɗaga labulen ɗakin ya shigo, hakan yasa su kai shiru aka ɗora da wani babin zancen na cewar Kanta ke ciwo, saboda Amadu ya tambayi dalilin kukan nata. kuma da suka dawo ɗin, Innar tata ta bata labarin bayan tafiyarsu makaranta ko wata biyu ba'a shafe ba Suhail yazo da kansa har ƙofar gida yasa ai masa sallama da ita Adawiyyar, an kuma shaida masa ɓatan Mairo amma ko jaje bai shigo yaywa Uwarta ba, tun da akace masa ai kina makaranta ya koma mota ya bar unguwar. tayi dariya ta rungumo Uwar tace,"ai yaje har makarantar ya sameni, wallahi Inna a ranar ji nayi kamar nayi hauka don daɗi, ya shaida min yana sona, kuma da zarar na kammala makaranta zai aureni...Inna ranar ban iya bacci ba, yace saboda ni fa ya baro ƙasar Ethopia a lokacin da bai shirya hakan ba, saboda yadda idanuwansa ke masa zugi da zafin son su yi tozali dani". tunanin Adawiyya ya yanke lokacin da Maganar Yagana ta shiga kunnenta. "ke zan leƙa gidan Hajiya Fatsima, yanzu zan dawo. idan kin gama tankaɗen garin sai ki tafi da shi can gida ki bawa Aisha, kice musu Mujibu ne ya siyo gari yace ai sadaƙar kunu da shi ranar juma'a". ta amsa mata da,"to". Yaganar kuma ta fice, ita kuma ta ɗauki aniyar Garin Kunun nan sai dai ayi asararsa, so take yanda ta manta da duniyar Mairo kowa ma ya manta da ita, dan haka ba zata bari ai sadaƙar nan ba, taga nema su ke su jaza mata bala'i Allah ya amsa adu'arsu ya dawo da Mairo, bayan ta gama sawa a ranta Mairo ta tafi kenan tafiya kuma ta har abada. a ɓangaren Gwaggo kuwa tun wannan rana da Mairo ta ɓata ta ke a kwance babu lafiya har yau, ciwon hawan jini, kullum kuma ƙara hawa yake ba ya sauka saboda yawan tunanin halin da Mairo ta ke ciki, ta rame sosai sai kace ba Gwaggo da ke da jikin diri ba, wuyan nan nata ya zama dogo, kuma tun daga wannan rana har iyau bata kuma takawa da ƙafafunta ba, ciwon da ya tsorata Malam ya kuma ɗaga hankalinsa, ciwon ƙafar tata tamkar aikin asiri, dan bata iya komai da kanta sai dai ayi mata. *Dare.* "Kulu zo ki ɗorani a fo zan yi fitsari". Gwaggo da ke daga kishingiɗe ajikin filo ta faɗa. Kulu ta bar inda take zaune ta taso, ta ɗauko fo ɗin sannan ta ɗauro Gwaggon akai, bayan ta gama kuma ta taimaka mata wurin yin tsarki. bayan ta sauketa taje ta zubar da fitsarin, ta ɗauko kofin silba mai ɗauke da koko ta kawo mata. "Dan Allah Yaya kisha kokon nan, yau gaba ɗaya babu abinda kika saka acikinki, Yaya yanda kike ƙara ramewar nan yana ɗaga hankalina, rashin cin abincinki ba shi zai dawo mana da ita ba, sai dai ya haifar da wata matsalar". Kulun ta faɗa sa'ilin da ta miƙa kofin ga bakin Gwaggon, a gefe ɗaya kuma tana saka hannu ta goge hawayenta, Allah ya sani rashin lafiyar ta Gwaggo shi ne dalilin da ya hanata bin sahun ƴarta, duk kuwa da bata san inda take ba, to amma ai tana zaune a gidan saboda rufin asirin ƴarta ya rufu, yanzu kuma da babu ita mene amfani zaman?, zata tafi ne kawai, tayi rayuwar da take ganin ita ce mafita a gareta. "Hauwa bakina ba shi da wani ɗanɗano, duk abun da ku ka bani ina ƙarfin halin cinsa ɗura ne kawai ku ke min, an riga anzo gaɓar da ba zan iya ƙara saka komai a bakina ba". kuka takeyi tayi maganar, ta kamo hannun Kulun ta riƙe tana ci gaba da cewa, "Hauwa ki yafe min, ki yafe min dan girman Allah, ban cika alƙawarin dana ɗaukar miki ba, na ci amanarki, ban san wannan ranar zata zo ba, ban san da zuwanta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin da na saɓa ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin zan kula miki da Maryam ba kamar ƴar dana haifa a cikina, da ban ɗaukar miki alƙawarin zanga rayuwarta ta inganta ba, da ban ɗaukar miki alƙawarin halin ƙuncin da kike gudun zata shiga ba ba zan bari ta shige shi ba, da banyi miki alƙawarin Malam zai riƙe ta ba, zai mata riƙon da uba ke yiwa ƴarsa ba. yanzu Maryam ta ɓata, ban san a wanne hali take ciki ba, da ace gawarta na gani da nafi samun lafiya da kwanciyar hankali, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". da ita da Kulun sai aka rasa wane zai taushi wani ya bar kukan, Kuka suke sosai, kukan da idan ka gansu kai ma sai ka zubar da hawaye. sai can ne Kulu tayi nisa tace,"haƙiƙa har mutuwa ba zan taɓa mantawa da ke da alkhairanki ba, bani da bakin yi miki godiya, alaƙawari ɗaya!, alƙawarin nan guda da na ɗauka nayi miki adua a koda yaushe zan cika shi har ranar da ƙasa zata cika min baki...Yaya ki daina ɗorawa kanki laifin ɓatan Hussaina dan Allah, ba kece sila ba kuma ba kece sanadi ba, ƙaddara ce, ƙaddararta ce, Allah ya shirya hakan tuntuni, Allah ya rubuta a lauhul mahfuz hakan zata faru da ita, ko kaɗan bana ganin laifinki, kuma hakan ba zai sa na ƙulle ciki ba, ba ki sanni ba, ba ki san wace ni ba, ba ki san daga inda na fito ba, kuma tsawon shekara goma sha biyar ba ki taɓa tambayata daga wanne ahali nake ba, taimakona kawai ki kai, taimakona kawai kike da kyakykyawar zuciyarki wacce babu tsatsa acikinta, ba ki taɓa goranta min ba, ba ki taɓa hantarata ba, ba ki taɓa ƙyamatata ba, sai ganin kin ƙara ɓoye sirrin da ke lulluɓe dani, abunda ko jinina ba zai iya min ba...ni kaina zanfi farinciki da samun natsuwar zuciya da ta ruhi da ace gawar Hussaina na gani, domin bana so tarihi ya maimaita kansa...". kukan da ya ci ƙarfinta a wannan lokacin shi yasa ta yin shiru. "mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Hauwa, ina jin ajikina lokacina yayi, ƙarshen rayuwata yazo, domin Allah yaji ya gani zuciyata ba zata taɓa iya ci gaba da ɗaukan rashin Maryam a kusa dani ba, ina sonta, ina tsananin ƙaunarta fiye da Basma, ji na ke ajiki da ruhina tamkar ni nayi naƙudarta bake ba, Ya Allah ka dubemu, ubangiji ka dubi halin da muke ciki, ya zuljalalu ka kawo mana ɗauki, Allah kai kasan komai, kai kasan abunda ke faruwa da wanda zai kasance, ya Rahmanu ka sauya wannan ƙaddarar, Allah a duk in da Maryam take ka kula da rayuwarta". ta kalli Kulu da hawaye ya gama wanke mata fuska tace, "idan na mutu ki bar gidan nan kar ki zauna, kuma dan Allah kar ki dawo cikinsa, kiyi nesa da shi kiyi nesa da abunda zai sa ki tuna shi, ina ji ajikina kamar Maryam zata dawo wataran, Allah zai kuɓutar da ita, a wannan lokacin kuma da zata yi rashina na san ba za ki juri ganin halin da zata shiga ba, ni kuma bana so, bana so tayi wani kukan da ya fi na mutuwata ciwo...kiyi min wannan alfarmar Hauwa". Sallamar da ake ta kwaɗawa daga ƙofar ɗaki tasa suka yi shiru, Kulu ta shiga goge hawayen nata da na Gwaggo, Zannira ce matar Aminu da akayi auren sati uku da suka wuce, ƙanin Kabiru ne da su ke ciki guda, wanda yake zaune acan Lokoja yana bugabugar kasuwanci tsawon shekaru uku, ana tsaka da alhinin ɓatan Mairo ya dawo kamar wanda aka aikawa da saƙon ɓatan nata, ya tafi can Lokoja ɗinne ba tare da ya san kowa ba, sai kuma Allah ya haɗa shi da uban gida na gari, mutumin da ba ya da ƙyashi, ya samu ya nuna masa kasuwanci har Allah ya buɗa masa bayan yanke tsammani da Aminun ya farayi, Allah ya saka masa albarka ya fara samun abin hannunsa, dan ɗan ƙaramin shagon da ya buɗe acan Lokoja ɗin na sayar da kayan electronics nasa ne wanda ya mallaka bayan sun haɗa hannun jari da uban gidan nasa, da ya ga samun nasa yana faɗaɗa sai ya sayar da shagon ya dawo gida,  ya kuma buɗe sabon shago anan kasuwar singa ta cikin garin kano, kuma da ike da albarkar iyaye sai shagon nasa ayanzu ya daɗa bunƙasa fiye dana lokacin da yake can Lokoja, domin dai-dai gwargwado yana samu. a yanzu haka ya ɗaukewa Baba duk wani abincin da za'a ci a gida, daman kuma Ahmadu yana aikowa da kuɗin abinci duk wata, wannan yasa babu matsalar abinci a gidansu Mairo a halin yanzu, akwai abinci wadatacce dan hatta gidan kansa ma gyara shi ake yi, shi da Amadu su kai haɗakar kuɗi akayi facefacen inda ya lalace, dan kowanne ɗaki yanzu da fenti, gidan ya koma kamar ba shi ba, banɗaki ma kansa shi Aminun yasa an maida masan zamani. "shigo mana Zannira". Gwaggo tace, da ike har a wannan halin Gwaggo dai bata bari Kulu ta nuna tana magana ba, duk da taso yin hakan a san da wani Malami yace da wuya Gwaggo ta kuma takawa da ƙafarta sai dai wani ikon Allah, to Gwaggonce ta hanata da ce mata da hakan kaɗai za ki biyani da abunda nayi miki. "Gwaggo sannu da jiki". Zanniran ta faɗa tana zama. "Yauwa Zannira sannunmu dai, ya ɗawainiyarku to Allah ubangiji yay muku albarka, an gode Allah ya ƙara arziƙi". "Amin ya Allah Gwaggo, kema kuma Allah ya ba ki lafiya". ta faɗa tana duban Kulu tace,"sannu Kulu kina ƙoƙari kema mun gode Allah ya ba ki lada ya kuma ba ki lafiya". Kulu dai kallonta tayi tai murmushi kawai. "Gwaggo da ma ganda ce yazo da ita, to yayi niyyar kawo miki da kansa kuma sai Baba ya kira shi yaje masallaci ya same shi, shi ne yace na kawo miki, idan bai yi dare ba zai shigo". ta faɗa tana buɗe kwanon tana saka cokali aciki ta miƙawa Gwaggon. "Allah dai yayi muku albarka". Zannira ta buɗe jaka ta ciro magani a ƴar kwalaba shi ma tace,"magani yaji wani malami ya faɗa a radio shi ne ya taho da shi, Malamin yace za a dinga shafa shi lokaci zuwa lokaci insha'Allahu za'a dace". ta buɗe ta lakuto tana fara shafa mata. Amarya ta shigo ita ma hannu ɗauke da kwanon abinci, ta ƙaraso tana faɗin,"ai ni nayi zatonma ko bacci ku kai da naji Zannira nata kwaɗa sallama, ni kuma ina banɗaki a sa'ilin". Gwaggo da ke ta ƙarfin halin magana tace,"gyangyaɗin dai muka fara, ban ma san Kulu ita ma ta kwanta ba". "to ga abincin, tuwon semovita ne da kuɓewa ɗanya". Gwaggo tace,"ai na kuma kika sami semovita?". Amarya na murmushi tace,"ai biki ji daɗinsa da naji ba, kuma wallahi musamman danke na tuƙa shi tunda lokacin da muka je gidan Gwarzo naga kinyi santinsa. a kayan da Amadu yayo aike jiya ya sako, bamu lura da shi ba ma duka sai da Zulai take ɗiban wake take ce min laa kinga ashe Amadu har da semo ya haɗo". "amma kuwa Allah yaywa yaron nan albarka. mu dai mun zama ƴan gata yara nata samun buɗi". cewar Gwaggo. "ai dama ance komai lokaci ne, Allah dai ya ƙara sanya albarka a cikin dukkan lamiransu". Zulai ta shigo ita da Sadiya da aka tsaida bikinta jiya watan mauludi. tun daga bakin ƙofa Sadiya ta hango gandar da ke gaban Gwaggo cikin kwano, ta ƙaraso ciki tana cewa,"Allah ya kawoni a sa'a, ke dai Gwaggo ubangiji ya ƙara miki lafiya". tai maganar tana zama tasa hannu ta ciro nama ɗaya ta kai baki. "ɗakinki na leƙa ai ba kya nan". cewar Zulai ga Amarya. "kuma fa shigowata kenan".inji Amarya. "hala kin manta zamu shiga gaisuwar gidan Hajiya Fatsima, ɗazu ma saida Yagana tayo aiken tuni, tace maƙota na ta shiga mu muna ɗinke a gida babu wacce ta leƙa, to tace dai kar mu wuce daren nan ba muje ba". "bari na ɗauko gyale na, da ma tunani na Gwaggo, ba'a fita a barta ita kaɗai ba, to tunda Zannira ta shigo shikenan sai mu tafi...ni wannan ƴar ƙaniyar ma ai ban

Chapter 19 of 52