Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƴaƴansa ma su shigo cikin lissafin, ta inda na ɗauki aniyar kaudasu 1 by 1, kinga duk sanda akace ba shi da ɗa ko guda kasona zai zama dai-dai da na Zulai, kamar hakanne yasa zan fara ta kan Amadu sai kuma aka sami akasi a jiyan...amma shi Kabir da kike gani sam ban sanya shi a cikin lissafin waɗanda zan rabasu da duniyar nan ba, saboda ina sonsa". sai da ta dubi Khadija da ta zuba ma ta ido sannan ta murmusa kamin tace,"So dai da kika sa ni, ina masa so sosai irin soyayyar da ko ubansa bai sami gurbi a zuciyata ba kamar yanda shi ya samu yay bake-bake a cikinta, tabbas ina so mu kasance tare da Kabir irin kusancin mata da miji, amma da na lura cewar ba zan sami biyan buƙatata a tare da shi ba, sai zuciyar ta karkata akalarta akan dukiyarsa, kuɗinsa kawai na ke buƙata a yanzu shi yasa zan kauda shi amma ba don son raina ba saboda wannan soyayyar tasa na raina har abada, sai dai nasan shi ba zai min amfanin da kuɗi za su min ba a rayuwa". tayi shiru ta miƙa hannu a gefenta ta ɗauko wasu takardu tana murmusawa,"kinga waɗan nan takardun da kika kalla ina kaffa kaffa da su kamar ran mahaifiyata, ba komai bane fa ce takardun gonakin Malam...ni ce na shirya faruwa komai da tsaruwar yanda abin zai kasance ace Gwamnati ce ta ƙwace masa su...wannan ita ce babbar Kadarar Malam kuma da ace nayi haƙuri da Gonakin nan kaɗai da na mallaka ta ƙarfi ƴaƴansa ma ba su isa su gaji kwatan abin da na samu ba...Ya kika kalla kwanyar tawa?". Khadijan ta jinjina kanta, bayan ta sauke numfashi tace,"kin wuce tunani da kuma dukkan hasashe...amma kuma Yaya acikin maganganunki kin faɗi da ace da yawa, kinga kenan cikin tsarin naki ma ba a ko da yaushe nasara ke tare da ke ba". sai Amarya ta kama karan hancinta ta murza, buɗar bakinta za tayi magana wayar da ke kusa da ita tayi ƙara, dan haka tayi saurin ɗagawa ganin sunan Musbahu akai tare da karawa a kunne. "Ya akai?". daga can ɓangaren yace da ita,"an sami mishkila". tai saurin rumtse idanuwanta,"kar ka ce min har zuwa wannan lokacin Kabir bai mutu ba kuma baka sami abubuwan da muke buƙata daga jikinsa ba?". "ehh Hajajju duka babu ɗaya da ya faru, ai na taƙaice miki ma gaba ɗaya jikin Kabiru babu wallet a tare da shi, duk na caje shi wallahi babu kuma har wurin da accident ɗin ya faru babu irin duban da banyi ba amma babu...". "Dakata Musbahu, zan samo mafita akan wannan wuyarta na zurfafa tunanina...mene abu na gaba?". "Amadu ya kuɓucewa shirinmu". "fahimtar da ni". "Ranki ya daɗe Amadu tare da motar jami'an tsaro suka zo, shi kansa Kabirun an sauya masa asibiti zuwa wani babban asibiti...Hajajju tare suke da wata Mata me babban matsayi dan ba ki kalla yanda jami'an tsaro ke nan da ita ba, ance ƴar sarkin Qatar ce tazo nan ƙasar ziyara...Hajjaju babbar matsalar ita ce...". ɗif ta katse wayar kafin ya kai ga faɗa ma ta abun da ba ta shiryawa jinsa ba, a hankali ta furta kalmar,"zanga bayanta, tabbas zan ga bayanta idan har ban sami biyan buƙatata ba, yacca na gama lissafin adadin kuɗaɗen da naji Kabiru na ƙiyastawa a matsayin mallakinsa idan har su ka kuɓuce min lallai wannan Matar zata shigo cikin lissafina tabbas kuwa". Kuma sai muryrta ta katse tare da katsewar numfashinta, da tsayar da idanunta akan mutanen da ke tsaye a bakin ƙofa, mutanen da bata san da zuwansu ba, sai dai dukkan wata alama ta nuna sun ɗauki mintuna sama da goma a wajen, hakan ya bata tabbacin sun shafci jin wasu daga cikin maganganun da tayi ɓarin faɗawa Khadija. bata san lokacin da taja wata doguwar ajiyar zuciya ba kuma ta kasa sauketa, a yayin da lokaci guda maƙogoronta ya bushe, haɗiyar yawu ya gagareta. me zuwan waɗan nan mutanen ke nufi? Me ke shirin faruwa da ita ne? Wa ya shirya girgiza teburun da ta ke lissafi akansa ne dan komai ya tarwatse?. ƙwayar idonta ta sauka a kan Khadija da ita ta ruɗe saboda ganin abinda bata tsammace shi ba a kurkusa haka. "You are under arrest". kalmomi huɗun da suka fito daga bakin police ɗin da ya ƙarasa shigowa cikin parlon kenan, wasu ƴan sanda biyu kuma suka mara masa baya, lokacin da Amarya ta buɗe baki dan yin magana, lokacin kuma ta girgiza da mamakin ganin Malam na shigowa shima. "idan har ba mafarki na ke ba, kuma abin da kunnuwana su ka ɗauki tsawon lokaci a wurin nan su na ji haka suke, to yallaɓai na baku damar ku kamata ku tafi da ita...Aisha daga yau kuma yanzu ina so yatsanki guda ɗaya da kike amfani da shi wajen zanen tsarinki, to a wannan lokacin ina so ya zana miki rabuwata da ke, rabuwa ta har a bada". Malam na faɗar hakan ya dubi Amadu da cewar,"kwaso min waɗancan takardun". daga haka kuma akasa ma ta ankwa aka fita da ita, da rufaffen bakin da ya kasa furta komai. *Bichi* "Inna kin san dai turancin nan ba sosai na ke jinsa ba, dan Allah ki rabu da ni idan su ka gaji da tsayuwa za su tafi ne". Zulai da ke wanke roba ta ƙwalowa Adawiyya robar akanta,"shashar banza ana sonki da arziƙi kina miƙa kanki da talauci, dan ubanki kin san adadin kuɗaɗen da za ki samo mana idan kin fita ɗin?". Adawiyya ta miƙe ta yafa mayafi tana turo baki ta fita, a ƙofar gidan daga gefen dakalin gidan tayi arba da wata dakakkiyar mota fake a wurin, sai Almustaphaa da ke tsaye jingine a jikin motar ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa, ɗaya hannun kuma yana kare da waya a kunne kuma yanda ya tattara hankalinsa akan wayar gaba ɗaya zaka san waya ce me muhimmanci yake yi. sai kawai taji wani abu ya zarce ta maƙogoronta da bata san ko menene shi ba, tabbas da ta san da akwai surar halittar da ta fi ta Suhail, wannan tsarin halittar da ke gabanta, Allah ya sani da basu wahalar da kansu akan Suhail ba, abin tambayar shi ne, me yasa ne ita Mairo ke sa'ar samun irin waɗan nan tsadaddun mazanne?, sam ta kasa ganewa ita kam. shin da me Mairon ta fita?, har yanzu fa da ta sauya bata fita dirarran jiki ba, wannan sangalallun siraran ƙafafun nata kamar sillan kara su ne dai suke yawo a cikin zane, to kuwa namiji me rai da lafiya ina shi ina kwasarwa kansa mace me sikila, dan ita a ganinta wannan sirantar ta Mairo ba zata rasa nasaba da sikila ba...amma bari shi ma zata kora shi ne, zata shaida masa yarinyar da za'a laƙaba masa ba komai bace fa ce illigemate child, ai idan ta ɗanɗana masa wannan kalmar ta illigitimacy dole ya haƙura da ita, wai tun yaushe ne ma taiwa kanta alƙawarin Mairo ba zata auri mijin kerewa sa'a ba ne?, to kuma na mene zata damu kanta akan abin da take da yaƙinin tabbatuwarsa, a wannnan lokacin da ya bayyana cewar ita ƴar zina ce wa zai ɗauka?, sai tayi guntun murmushi cikin ranta tana ƙara cewa ai ta koma gefe kawai tai dariya son ranta. "Is Father at home?". tambayarsa da ta shiga cikin kunnenta ita ta katse shirmamman tunanin da ta ke yi, dan haka ta ɗago ta saci kallonsa kafin ta ba shi amsa da cewar,"ba ya nan sun tafi asibiti". kafin Almustapha ɗin ya ƙara cewa wani abu, Dad da ke cikin mota ya fito ya jefo mata tasa tambayar,"what about Ahmad, is he around?". sai ta girgiza kanta alamar a'a. shiru ya ratsa tsakaninsu na ƴan mintuna kamin Almustapha ya jefa ma ta tambayar,"wane ba shi da lafiya?". "Maman Mairo ce". sai ya waro ido waje da mamaki,"Maman Mairo kuma?, ita bata mutu ba dama?". anzo wurin da ta ke so, dan haka ta gyara tsayuwarta ta shiga koro masa bayanan da ke buga mata sarewar daɗi a ranta, kuma bata kai ga furta cewar,"amma ba'a san wane Babanta ba". Dad yay saurin cewa da Almustapha ya kira Ahmad yaji su na ina, hankalin Dad a matuƙar tashe ya shiga mota suka bar wajen bayan Amadu ya shaida musu asibitin da suke, a gefe guda kuma sai kiran wayarsa ake akan bikin mutuwarsu Granny da tuni aka kai gawar ta su can chapel ɗin ana jiransa shi da Emanuel. *Apex Consultant Hospital, Kano.* a cikin harabar asibitin, Aaliya na zaune kan plastic farar kujera, yayin da Amadu da Alhassan ke tsaye daga gefen damanta, a gabanta kuma ƴan sanda ne guda biyu sai guda ɗaya da uniform ɗinsa ya banbanta da na sauran yana zaune shi ma a plastic kujera yana fuskantarta, yayin da ta ke sauraren duk bayanin da ke fita daga bakinsa. "mun kama shi yaron da yay causing accident ɗin, bayan an kai shi mara lafiyar asibiti so a time ɗin ya shiga yana laluben aljihunsa time ɗinne wata nurse ta gansa sai tai gaggawar sanar damu. so kamar yanda ita Akila ta bamu waɗancan bayanan akan ita wadda kuke suspecting, mun sami dukkan ƙarin bayani a wayar shi Kabir ɗin, ofcourse kaman yanda Akila ta faɗa akwai record ɗin maganar ita waccan matar mun same shi a wayar Kabir, mun sami bayanin inda ta ke daga bakin shi yaron nata, dan farko munje can gidan shi Malam ɗin bata nan, kuma lokacin da muka je gida sai muka je a daidai gaɓar da ta ke bada labarin abin da ta shuka, duk da cewar ba duka muka tsinta ba amma mun tsinci muhimman abinda zarginmu yake akanta, yanzu haka tana can a cell su na karɓar hukunci ita da yaron nata". Aaliya tayi ajiyar zuciyar da ke shaida tsananin damuwarta kafin tace,"wannan mata anyi sheɗaniya, DPO idan kaji labarin ainihin fuskar da kowa yasanta da ita zaka sha mamaki, za ka rantse kace ƙazafi ne aka ma ta akan wannan abin da ta aikata...yanzu kenan mene ƙarshen hukuncinta?". "ehh to ranki daɗe for now dai zamu yita horasu ne zuwa lokaci zai nuna mana halin da Kabir zai kasance a ciki, yanzu dai nauyin kashe duk wasu kuɗi da za ai akansa ya rataya ne a wuyanta...". Aaliya ta tari numfashinsa da cewar,"ka bar wannan batun matsiyaciya ce ba zata iya ba, ko ka taɓa ganin faƙiri ya tallafi wani?, tukunna ma ba kalla duk akan kuɗi ta aikata hakan ba, so just go stregth to the point ɗin da nake son ji". ya jinjina kai,"right! to abunda dai hukunci zai tanadar akanta shi ne, idan Kabir yaji sauƙi case ɗin mutuwa akanta ya zama guda ɗaya kenan, amma idan Allah baisa ya rayu ba case ɗin mutuwa akanta ya zama biyu kenan, so a wannan lokacin zamu danganata ga kotu domin ta yanke ma ta hukunci akan abubuwan da ta aikata". Aaliyan ta ƙara cewa,"DPO matar nan ta shiga rayuwata da yawa, bima'ana ta shiga rayuwar ƴata tun tana ƙanƙanuwarta, dan haka kamar yanda ta ɗau lokaci tana saka firgici a rayuwar ƴata, haka nake so daga yau ta shiga fara ƙidayar mutuwarta da kanta ta hanyar irin gana ma ta wahalar da za ku dinƙayi, DPO da gaske nake maka daga yau Amarya karta kuma rufe idanuwanta da sunan yin bacci, kuyita galabaitar da ita acikin bugawar kowanne sakan na agogo...idan kayi min haka zan biyaka da kaso mafi tsoka". DPO ya jinjina kai alamar za'ai yanda ta buƙata ɗin. sai yanzu Amadu yay magana a sanda DPO ɗin ya miƙe yana yiwa Aaliya sallama. "DPO nace me yasa ita ma ba za'a ɗanɗana ma ta irin allurar da tayiwa Gwaggo ba kamin zuwan lokacin da ake jira ɗin". "kar ka damu, duk wani nauin wahalar da me laifi a cikin aikinmu yake". daga haka yay musu sallama ya wuce, yayin da Aaliya ta miƙe su na nufar hanyar wani dogon corrido da zai sada su zuwa ga room ɗin da aka kwantar da Kabir, zuciyar Amadu na raya masa cewar ko ya sanar ma ta da zuwan su Major da suke kan hanyarsu, kwatsam kuma sai ga kiran Almustapha ya shigo wayarsa, saboda haka ya ɗan dakata da tafiyarsa ya ɗauki wayar, Almustapha ke shaida masa gasu a compound ɗin asibitin, kuma wucewar daƙiƙa ɗaya sai gasu sun iso inda yake. "Alhassan". Alhassan ɗin ya juyo daga tafiyar da yake lokacin da yaji kiran Amadu, "ka tsaida Mami". Alhassan ya juya ya kira sunanta, juyowarta tayi dai-dai da ɗago da idon Major ya kai kanta da Amadu ke masa nuni da ita, ita ma kuma daga tazarar da ke tsakaninsu ta ganshi, ga mamakin Major sai idonsa ya ƙyallo masa saɓanin tunanin da zuciyarsa tayi a sanda ya kai ƙwaya idonsa cikin nata lokacin da ya iso inda ta ke. a yanzu da ya ƙaraso gabanta tana amsa wayar da Ammi ta kirata ne, dama tun ɗazun ta kirasu ta shaida musu halin komai da ake ciki a yanzu da na baya ma da ya wuce, ta sauke wayar daga kunnenta tayiwa Major kallon sama da ƙasa tamkar bata ma taɓa ganinsa ba, ko kuma wacce ta sanshi amma ta manta inda ta san shi ɗin tana dai ƙoƙarin recalling, kafin a hankali muryarta ta fito da faɗin,"why now?". kan yace wani abu ta juya ga Alhassan tace,"ga Ubanku...". sai dai abin da ta gani ne baisa ta ƙarasa sauran maganarta ba, kamar yanda Alhassan da Almustapha ke kallon junan su da mamakin kamanninsu haka ita ma ta ke kallon Almustaphan da mamakin kamar da ke tsakaninsu. "Major ban lissafa ganinka a yanzu ba, me zuwanka ke nufi?, kuma da wacce tsiyar kazo naji ko kaina zai iya ɗauka?". bai iya cewa komai ba, shi dai yay shiru kawai yana kallonta da wani irin kallo da shi kaɗai yasan me zuciyarsa ke ji a ga me da hakan. gaisuwar da Alhassan yay masa ita ta datse igiyar tunanin da yake, ya juyo gare shi cike da wata iriyar kunya ya amsa masa. sai Aaliyan ta dubi Alhassan ɗin da cewa,"binsa zaka yi ne?". sai yay saurin girgiza kansa,"no Mami, na gaishe shi ne saboda sunan mahaifi da ya amsa a gareni". ranta a haɗe tace,"to kaji, sai ka jira zuwa time ɗin da zan kammala activities ɗin da suka kawoni ƙasar taku, idan na koma ka iya zuwa da ƙafar rashin kunyar naka ka karɓesu". ta faɗi hakan ta juya dan ci gaba tafiya. sai a sannan taji yace,"where is Merry?". ba tare da ta tsaya daga tafiyartata ba ko kuma ta juyo ba tace da shi,"ni ƴata sunanta Maryam, kar ka ƙara kiranta da wannan ɗan iskan sunan tunda ba rainonka bace...kuma abin da ma zan sanar maka shine ka cire lissafin karɓarta dan ba abu ne da zai yiwu ba in har Aaliya na numfashi, kaji da kyau bada wai ba, wannan dai me zubin naka kana iya jansa ko daga yanzu domin shi na rayu da shi, ita kuwa yanzu ne zamu soma rayuwa tare". ***"magungunan da aka rubuta masa su na da tsada sosai, gasu nan ku hanzarta siyo su bada jimawa ba...kar ku ɗaga hankalinku da yawa saboda komai yazo da sauƙi...sai dai allurar da muka yi masa ce zata iya kai shi zuwa gobe, amma kar ku wani damu da rashin farkawarsa muna so ya samu hutu ne." duk wannan bayanin na fitowa ne daga bakin Dr ɗin da ya gama duba Kabir a yanzu, yana isar da bayanan nasa ga Akila(Kulu) da ke tsaye tana sauraronsa, yayin da Yagana ke zaune a kan wata kujera daga can gefe tayi jugum ƙirjinta na luguden fargabar abin da likitocin zasu ce a ga me da Kabir duba da mawuyacin halin da yake ciki, kuma a duk wani motsi na zuciyarta tsinewa Amarya take. Mairo kuwa na zaune akan kujerar da Akila ta tashi ta barta, idanunta na manne akan Kabir da ke kwance kamar matacce, da kuma farar shaddar da ke jikinsa wadda gaba ɗayanta ta ɓaci da jini kamar yanda shi ma fuskarsa ta ɓaci da jini a ɗazu kafin likitoci su gyara shi, an nannaɗe wurin ciwukan da bandage. a wannan lokacin zuciyarta na bugawa ne da motsin fargabar halin da Ya Kabiru ke ciki, yayin da a gefe guda kuma kalaman Ummi akan Amarya ke yawo a cikin kanta, wannan Amaryar da ta ɗauka tamkar Gwaggonta, ta kasa yarda da kowacce kalma ɗaya bayan ɗaya da ke fitowa daga bakin Ummi akan ƙazaman abubuwan da Innarta ta aikata, amma kuma a san da Baba ya kira yana tabbatarwa da Yagana gaskiyar lamarin sai taji kanta yay ma ta nauyi, komai na cikin kanta ya ɗaure. ta sa ni, ba ita kaɗai ba, koma wane zai iya dafa Alƙur'ani ya rantse wajen ƙaryata duk wanda zai zo da shaidar maganar makamancin abinda Amaryar ta aikata, amma wai sai gashi ita da kanta tayi silar ajalin Matar da ta ɗauketa ƴar'uwa, kuma ta jefa mutumin da akaf ƴaƴan gidan babu wanda ya kaishi bata girma, taɓa mata Gwaggo da tayi shi ne babban zunubin da ta aikata, kuma a yanzu taɓa mata Ya Kabir ya zama mafi munin kuskuren abubuwan da ta aikata a rayuwarta, za kuma tayi danasanin da zai zame ma ta mara amfani. dan a yau tambarin laifinta ya kafu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taɓa goguwa ba, tunda har ta haddasa faruwar wannan tashin hankalin, ta zama silar da Ya Kabir ɗina ke kwance a gadon asibiti cikin wannan mawuyacin halin, ta zama sanadiyar fitar wannan jinin da ke ɗaga hankalina tun ina yarinya, ko ƙaƙa jini ya fita a jikinsa ina kasa samun natsuwa balle irin wannan jinin da ya zubar me bala'in yawa. sai kawai na rufe idona tare da kifa kaina a gefen gadon nasa, ta daidai hannunsa da drip ke shiga, na kasa ganewa, ni ban san menene wannan dunƙulallan abin ba da ya tsaya min a zuciya na game da Ya Kabir, abu ɗaya kawai na iya ganewa da fahimta shi ne ƙudurin da zuciyarta ta ɗauka akan Amarya, tabbas idan har ni ɗiyar Mami ce, ƴar da nake da gata ta kowanne fanni, to sai nasa Amarya ta wulaƙanta, wannan alƙawarina ne. Shigowar Aaliya room ɗin yasa Yagana miƙewa da sauri tana tambayar yanda ake ciki game da binciken Amarya da akasa. sai dai kuma Aaliyan ba jin me take cewa ba balle ta bata amsa, sai Amadu da ya shigo daga baya ne yake mata bayanin komai, har da shaida mata sakin da Malam yay mata, wanda tace hakan shi ne dai-dai. "wacce iriyar shaƙuwa ce ke tsakaninsu?". "ina Alhassan?". tambayoyi biyun suka fito a tare daga bakuna mabanbanta, suka kalla juna inda Aaliya ta ɗagawa ƴar'uwarta kai,"ki fara bani amsar tawa, wacce iriyar shaƙuwa ce ke a tsakaninsu?". ta faɗa tana ƙara maida idonta kan Mairo da har yanzu bata ɗago daga kifa kanta da tayi ba daga gefen hannun Kabir. "shaƙuwar me ƙarfi ce, kamar shaƙuwar hanta da jini...shi na zaɓa ma ta, kuma shi nayiwa alƙawarinta in har muna raye, ina roƙon Allah da izininsa su kasance a inuwa guda". har yanzu idon Aaliyan na kansu biyun tace,"kenan da mun koma sai bikin aurensu?". Akila ta dubeta da mamaki,"auren Maryam kuma very soon haka?." "ƙwarai, domin a irin critical condition ɗin da yake ciki ya kamata su kasance a tare...ina ce kin ce min Mamansa ta rasu?". "ehh ba ya da Mama a raye, amma ni kuma ai ba haka na tsara auren Maryam ba, so nake sai ta kammala karatunta tukunna". "Kabir ɗin jahili ne?". Aaliyan ta wurga ma ta tambayar san da tayi shiru. Akila na girgiza kai tace,"kaf gidansu ma ai babu me iliminsa". "so me ilimi kamarsa kina tunanin zai hana mace yin karatu?, ko da bata so tayi ba dole zai tursasata, dan haka a irin shauƙin son da nagani a idanun Maryam kasancewarsu a tare shi zai wanzarwa da zuciyarta natsuwa...wanne time suka ce zai farka?". "zuwa gobe suka ce". "zuwa goben kenan zamu wuce gida, haka Ammi tace". tayi maganar tana neman kujera ta zauna, tana kuma cewa da Akila,"Major ne yazo, Alhassan na tare da shi, tunda na gansa tafin hannuna ke ƙaiƙayi, kije kiji da shi." fuskar Akila na haskawa da mamaki ƙarara tace,"Major kuma, me zuwan nasa ke nufi?, kar dai karɓan yarana zai yi?." Aaliya ta sauke jarkar ruwan faro ɗin da ta kai bakinta sannan tace,"ni na kawo shi?." bata jira cewar wani abu daga bakin Akilan ba ta ƙara cewa,"tunda ba ni na kawo shi ba sai ki rabani da waɗannan tambayoyin naki". Akila ta girgiza kai sannan ta fice daga ɗakin a zafafe. tun bayan fitar tata Aaliya ta maida kallonta kan Maryam da Kabir, kuma kamar yanda ta ƙura ido a kallon nasu haka Amadu ya zuba ido akan Mairo da wani irin kallo da fassararsa ke ga me yinsa shi kaɗai. a hankali Aaliyan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe taja kujerar zuwa kusa da Mairon. duk da cewar bata leƙa taga yanayin fuskar Mairon ba, amma tasan da cewar idonta biyu ba bacci ta ke ba kamar yanda saukar numfashinta ke nunawa, haka kuma ta tabbatar hawaye ne ke bin kuncinta duk da bata kalla fuskarta ba, saboda haka cikin muryarta da ta bada wani irin amon sauti tace,"Ya Mutu". kuma kalmar ta doka wani irin tartsatsi a zuciyar Mairo ta ɗago a rikice tana duban Mahaifiyartata, bakinta a buɗe yana rawa ta kasa cewa komai sai aikin girgiza kai da ta ke alamar,"a'a maganar ba haka ta ke ba". da ta ga hakan sai ta kaudar kanta daga barin kallon. Mairo tace,"ai bani na faɗa ba Maryam, ga file ɗinsa nan ki duba ki gani mana". sai kawai Mairon ta fashe da wani kuka mai ƙarfin sauti ta faɗa jikin Aaliyan tana faɗin,"a'a Mami dan Allah, bana so ya mutu yanzu dan Allah Mami, ki taimaka min Maminah, kiyi wani abu kar Yayana ya mutu don Allah". *Comment&Share and also Vote kunji ƴan aljannah.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *(38)* "me yasa ba kya so ya mutu?". "saboda ina sonsa, dan Allah Mami karya mutu". na faɗa ba tare da sanin ma'anar da furucin nawa zai haifar ba, ina ƙara ƙanƙameta kamar zan karya ƙasusuwan jikinta, sai naji tayi wani murmushi da sautinsa kawai na iya ji, sannan tace da ni,"akwai wasu kalmomin dake bada tarin ma'anoni da yawa...Maryam a shekarunki goma sha bakwai nasan kin san ma'anar So, haka kuma kin san rabeben So...ina so ki faɗa min wanne irin so kikewa Kabir bayan na ƴan'uwan taka?...ba daga fatar bakinki nake son jin amsar ba, ki ba ni ita daga ƙasan zuciyarki". sai naji na tsaya cak daga motsi na wucewar wasu sakanni, yawun bakina kuma ya ƙafe, abinda Mami ta faɗa daga ƙarshe shi ƙwaƙwalwata ke ƙara biya min, "bayan so na ƴan'uwan taka, wane irin so kikewa Kabir?."_, tabbas tambayar na ɗauke da ma'anar da nake ganin kamar taiwa kaina girma. to ma wacce amsa zan bawa Mami a yanzu bayan wacce nake da ita ta riga ta faɗeta acikin tambayar da zata min, bayan so na ƴan'uwantaka dama akwai wani so ne da nakewa Ya Kabir wanda ban san da shi ba?, so ɗaya na san ina masa soyayyar Yaya da Ƙanwarsa, irin so na amatu ɗin da zan iya shiga wani hali in har mutuwa ta rabani da shi. "ehen...". maganar Mami acikin shirun da nai tasa kayan cikina hautsinawa, sai dai a lokacin da zan buɗi baki nai magana a lokacin na godewa Allah da kuma Ya Amadu da maganarsa ta katse zancen na mu. "Mami likita na magana". "oak Ahmad jeka mana". "no yace ke yake son gani". Mami ta jayeni daga jikinta sannan ta miƙe ta fita, ni kuma na zauna kan kujerar da ta tashi na tsurawa Ya

Chapter 36 of 52