har Amadu shaida ne a yanzu Emanuel ba arne bane musulmi ne, ya zama cikakken musulmi tun a daren jiya kafin sallar isha'i, ya amsa kalmar la'ila ha'illahu har ƙarshenta, kuma ya amsa sunansa na Al-Mustapha. haƙiƙa ubangiji me iko ne abisa dukkan komai, Emanuel ya ƙara amsa cewar zai shiga musulunci ne tun a sanda imani ya ratsa zuciyarsa ata dalilin kalamai na wa'azi da Liman yay masa masu ratsa zuciya da ɓargon jiki. Liman ya faɗa masa musuluncin ba kasuwanci bane, kuma ba'a biyan ko sisi idan za'a shiga addinin musulunci, saboda Allah maɗaukakin sarki ya halicci dukkan halittu ne domin su bauta masa, kuma ya sawwaƙe musu abin da zai taimaka musu na arziƙinsa. kuma Ubangiji da kansa ya faɗa a littafinsa me tsarki, surah ta (51) aya ta (56-58) yake cewa ,"(56) Kuma ban halitta aljanu da mutane ba sai domin su bauta mani. (57) Bana nufin wani arziƙi daga gare su, kuma bana nufin su yi min hidimar ciyar da ni. (58) Lallai Allah shi ne kaɗai mai azurtawa, me ikon yi, me gafara. saboda haka babu abin da ubangiji ke buƙata daga gareka Emanuel fa ce ka amsa kalmar Shahada, ka kuma yi mubaya'a akan ƙa'idar,"annama ilahukum wahid". domin akan wannan ƙa'idar aka gina addinin musulunci. ka shaida babu wani Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah, Kuma Annabi Muhammadu Manzonsa ne, Waɗannan kalmomin su ne ƙofar shiga musulunci, kuma rukuni mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musuluncin mutum sai yay furuci da su, da kuma yin aiki da abin da suka ƙunsa, daga sannane ka tashi daga kafiri ka koma musulmi Emanuel. Liman ya ɗau alƙur'ani yay masa nuni da shi yace Emanuel wannan shi ne zancen Allah, littafin da aka aiko Manzonmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da shi. ka samu damar yin riƙo da shi domin ka tsira daga wannan narkon azabar da zaka riska a ranar alƙiyama in har ka mutu kana kafiri. a cikinsa zancen Allah yake gaba ɗaya, Emanuel ba don san kanmu ko kuma mu yaudari zuciyarka ba, amma babu wani addini na gaskiya sai addinin musulunci, kuma babu wata kyakykyawar hanya saita bin ubangiji, in har kabi Allah, kayi koyi da koyarwar Manzon Allah, Ka yarda ba zaka ƙara yin shirka ga Allah ba, ka riƙe gaskiya da amana, ka yarda ba zaka aikata zina ba, kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ka yarda da haramcin sata, ka tsare kanka daga saɓawa ubangiji, to haƙiƙa ka rabauta daga dukkan wani narko na azabar ubangiji. domin haƙiƙa Ubangiji ya tanadi gidaje guda biyu wuta da Aljannah, ya kuma yi alƙawarin cikasu da mutane, za'a cika Aljannah da mutanen da suka riƙi gaskiya suka tashi a tafarkin Manzon Allah, ita kuma wuta za'a cikata ne da mutanen da suka ɓata, suka yi watsi da gaskiyar da ma'aikin Allah yazo mana da ita. Dan haka Emanuel idan ka shirya zaka karɓi kalmar La'ilaha'illah Muhammadur-Rasulillah. ni kuma zan amsa mubaya'arka, zan roƙa maka gafarar ubangiji domin haƙiƙa Allah mai gafara ne kuma me jin ƙai.
a Wannan lokacin duk wanda ya kalli Emanuel sai ya hangi irin raunin da zuciyarsa tayi, jikinsa gaba ɗaya yay sanyi saboda tasirin waɗan nan kalamai, ya shiga faɗar kalmar da Liman ya umarce shi ya maimaita bayan ya faɗa, Mairo sai da nayi hawaye, daren jiya tare muka yi sallar isha'i da Al-Mustapha a masallaci, kuma yau da asuba ma ni nasa Amadu ya tashe shi, ya roƙi Amadu akan ya dawo da sauri domin ya fara masa bitar karatun alƙur'ani...Mairo ban amsawa Al-Mustapha zan aura masa ke ba sai bayan ya musulunta, kuma hakan ba yana nufin zan tursasa miki ba dan shi ma bai ƙara tunkarata da maganar ba, sai dai a yau da safe nasa Amadu ya kira min shi na shaida masa na basa ke, idan ya shirya ya fito zan ɗaura muku aure, amma duk da haka ki faɗa min ra'ayinki dan ba zan miki dole ba, ba zan tauye miki hakki ba, alƙawarin da na ɗauka kawai nake tsoron saɓawa, dan ban san wane irin hukunci ubangiji zai min ba".
shirun dai na yi ba shiru ne na haka kawai ba, wani irin shiru ne da nake jin guguwa na kaɗawa acikinsa, shirun da acikinsa na kasa zuƙar numfashi me daɗi, tun a sanda Baba ya shiga kora min wannan jawabin nayi mutuwar zaune, gaba ɗaya abin jinsa na ke tamkar almara, yanzu ba maganar auren ce abin mamakina ba, mamakin yana ga musuluntar da Emanuel yayi, kuma tsoro sai ya kamani, naji a zuciyata ban yarda da wannan tuban nasa ba, ban kuma yarda da karɓar musuluncinsa ba, nafi yarda da yay amfani da siyasa ne don kawai Baba ya bashi ni ɗin, domin ya rama abinda nayi masa a waccan ranar, ga Baban kuma ya amince masa.
hawaye suka cika min idanuna, kewar Gwaggona da mararin kasancewarta a wannan lokacin ya kamani, wata ƙila da ta na raye duk ba za azo kan wannan gaɓar ba, ba za aiwa ƴarta abunda taƙi jini ba wato auren wuri, ba za'a aurawa ƴarta wanda bata so ba, ba kuma za'a dakushewa ƴarta karatun bokon da ta cimma burinta akansa ba, dama na sa ni! na kuma ji a jikina tun a ranar da Gwaggona ta rasu wani shafi na ƙaddarar rayuwata ya buɗe. na ɗago da idona a hankali na dubi Baba da idanuwansa ke akaina ƙyam, ko ban shiga zuciyarsa ba amma nasan babu komai acikinta fa ce tsoro da fargabar amsar da zan bashi, kuma ni kaina ɗin ina jin rashin kyautuwar abinda zanyi, to amma me?, alokaci guda sai naji duka ɓarika biyu na zuciyata sun sauya ra'ayi, sun sauya ƙin amincewar da nake shirin yi zuwa yarda, domin idan har naƙi amincewa Baba maganar auren nan tamkar nayi butulci ne a gare shi, sannan kuma shi ma kansa Emanuel ɗin naji ina jin tausayinsa, haƙiƙa ko bana sonsa zan iya amince masa saboda alkhairin da yay mana a sanda ake zaman makokin Gwaggo.
ba wannan ba ma tukunna, ni yanzu a duniyata ina jin zan iya mallaka komai nawa ga duk wanda yay adu'a ga Gwaggona, balle shi da Baba ya faɗa min ya ɗau tsawon sati guda yana ma ta adu'a, kuma har ya bada kuɗi akai sadaƙa ladan ya isa gareta, Gwaggona da bani da kamarta duk faɗin duniya. bayan wannan ma! Allah ya sani tun ban mallaki hankalina ba nayi alƙawarin babu abin da Babana zai nema daga gareni na kasa yi masa, ko da kuwa rayuwata yace na sadaukar, Allah ya sani na jima ina jiran wannan rana da Baba zai umarceni da auren mijin da ya zaɓa min na amince masa kai tsaye, dan ta hakanne kaɗai zan iya rama masa da irin sadaukarwar da yay a gareni. zan iya yin komai dan ganin na wanzar masa da farinciki, Baban nan nawa da nake mutuwar so, Baban nan da ya sha wahala akanmu a rayuwarsa, ba don komai, sai dan ganin rayuwarmu ta inganta, Babana dai! Mahaifina! Mahaifina da ya sadaukar da ƙodarsa guda ɗaya aka saka min a san da nake shekara goma, Babana da ya ƙarar da komai nasa a san da za'ai min aikin ƙoda, Baban da ya sha wahalar jinya ta sanadin bada ƙodarsa da yay a gareni, wanda har sai da muka fitar da rai da shi, to akan me yanzu zan butulce masa kan wannan ƴar ƙanƙanuwar buƙatar tasa?. to ni kuwa ko da wane nufi ne ma Al'mustapha zai aureni ni kam na amince, ni ba butulu bace, dan haka a yau ko da raina ne Baba yace na bayar wallahi zan bayar in har zaiji daɗin hakan. Baba ya katse tunani, maganar tasa ta shigo cikin kaina da wani irin dagargaza zuciya, nasa hannu na share hawayena, sannan na ɗago na dube shi da murmushi nace masa,"na amince Baba, na amince zan auri Al-Mustapha in har hakan shi ne muradinka, kuma hakan ba zaisa ka saɓa alƙawarin da ka ɗauka ba, na amince zan zauna da shi a matsayin mijina bisa turbar da ka ɗorani akai, Baba na maka alƙawarin zan koyawa zuciyata sonsa idan har hakan shi ne zai faranta maka, ko babu komai nasan ba zan taɓa ganin ba daidai ba idan har na bi umarninka". nai shiru saboda kukan da ya danne sauran maganata. Baba yay murmushi sannan yace,"matso nan gabana Mairo". na rarrafa na ƙarasa gabansa, ya kamo duka hannayena ya riƙe a nasa yace,"na gode Mairo, na gode Allah yayi miki albarka ya saka miki da alkhairi...kuma ina mai tabbatar miki ba za ki taɓa wulaƙanta a hannun wannan yaron ba, ni ba magini bane saboda haka ban duba filin wurin ba, amma ina da yaƙinin Al-Mustapha ba zai cutar da ke ba. a gobe insha'Allahu zan ɗaura miki aure da Al-Mustapha, fatana ɗaya a gidan aurenki kici gaba da ginuwa akan wannan kyakykyawan halin dana sanki da shi, ki zama tamkar mahaifiyarki, mace me gaskiya da amana, Mace me haƙuri, juriya, kawaici da ƙyamar abin hannun wani...Allah yayi miki albarka ya kuma jiƙan mahaifiyarki". na amsa masa da,"amin Babana". daga haka zaman namu ya watse, Baba yace ba zan tafi gidan Yagana ba anan zan kwana tun da dare yayi, ba haka naso ba, dan ko kaɗan yanzu bana son kwanan ɗakin Gwaggo babu ita. lokacin da nake fitowa daga ɗakin Baba, sai naga Inna Zulai da Adawiyya sun bar wurin da sauri sunyi ɗaki, sun ji komai, dan alama ta nuna ba tun yanzu suke laɓe a wurin ba, nai wani guntun murmushi kawai ina girgiza kaina. ko sanda na isa ɗaki na tarar har Kulu ta kwanta, na tura ƙofa na rufe sannan na wuce na hau kan gadon ƙarfen Gwaggona, na kwanta daga bayan Kulu, wacce idona ke haska min tamkar Gwaggona. na cure a wuri guda, tun da na kwanta babu abin da nake banda hawaye, tun sautin kukan da na ke bai fita har ya fara fitowa a hankali. maganar Kulu daga kaina naji ta ce,"kukan me kike?". nai ma ta shiru har sai da ta ƙara yin magana. "tambayarki nake kukan me kike?". sai kawai na tashi zaune na rungumeta ina ci gaba da shashsheƙar kuka, tasa hannayenta ta kewayeni tana faɗin,"kukanki yana ɗaga min hankali, yana sosa zuciyata, yana hanani natsuwa, idan ba so kike zuciyata ta buga ba to ki faɗa min me akai miki kike kuka?". Muryata ta fito cikin sheƙar kuka ina fizgar numfashi nace,"aure Baba zai min". Maganar tata ta doka tsalle a zuciyar Kulu, mamaki ya bayyana ƙarara a fuskarta, tsoro kuma da fargaba suka cika zuciyarta, wa Malam zai aurawa ƴarta ba ta sa ni ba?, bai kuma sanar da ita ba?, ko dai ƙarya ta ke faɗa ma ta? ko kuma taji maganar tasa ba dai-dai ba?. gudun kar da Mairon ta gane halin da ta shige tai saurin ture komai daga ranta, ta lallasheta da bata haƙuri har ta samu zuciyarta ta sauko ta bar yin kukan. kuma daga hakan sai bacci ya ɗauketa saboda karatun qur'anin da Kulu ke karanto ma ta a cikin kunne. sai da ta tabbata baccin Mairon yayi nisa, sannan ta sauka daga gadon ta fita don zuwa ɗakin Malam, sai dai tana fitowar ne kuma tai kiciɓis da wucewar wannan mutumin da ke lulluɓe jikinsa da daddare, wanda ko a daren jiya taga gimlawar inuwarsa ta ƙasan ƙofar ɗaki, da alama kuma ɗakin zai shigo sai bai sami damar hakan ba, saboda ƙofin da tayi na hana idonsa ganin komai. ta sani shi ne silar ciwon ƙafar Gwaggo, dan rana ta ƙarshe da ya shigo ɗakin ya fita da ta zo ta tarar da syringe a ƙasa wanda aka jefar saboda tsoron tahowar me shigowa ɗakin, ta ɗaga syringe ɗin ta duba na allurar botulinum toxin ne, gubar da zata iya kashe duk al'ummar ƙasar da akaiwa feshinta, ko da ta saka ihu kowa ya fito a lokacin babu wanda aka gani.
daga baya zuciyarta ta saƙa ma ta koma wanene a cikin gidan nan yake, wanda ya ƙware a ɓadda kama, ashe zuciyarta ba zargi ta ke ba, hakanne, don gashi kuwa yau idanunta sun gane ma ta ko wane, dan taga fuskar a san da ta fito lokacin da ake ƙoƙarin lulluɓe kai. zuciyarta ta tsorata da abin da zai iya faruwa, saboda haka ta haƙura da maganar da zata yi da Malam a daren yau, ta jira gobe idan Allah ya kaimu, tana gudun karta fita yazo ya cutar ma ta da ƴa, cutarwa da ba zata bari, dan ko ta Gwaggonma ba tayi shiru ta ƙyale bane, kwanaki ashirin ne kacal da rasuwar, tana jiran mutuwar ta sake barin jikin kowa kamin ta tona asirinsa, kuma lokacin da SIRRIN da ya jima a ƁOYE zai fito fili. dan haka sai ta mayar da ƙofar ta rufe ta dawo ciki, ta kwanta ta rungomo ƴarta jikinta tsam, amma duk da haka tsoro bai bar ranta ba. kuma a cikin baccin nata ne taji wata magana da bata san amon sautin waye ba tana faɗin,"ni ban taɓa tsara abu ya tafi ba a yanda nake so ba, shirina na gaba akan Kabiru da ɗan'uwansa ne, ina so a gobe ku sace Kabiru, kuma ku buƙaci adadin kuɗaɗen da zan lissafa muku, sannan kubi bayan ɗan'uwansa ku haddasa hatsarin da kowa ma zai rasa ransa, babu ruwana da sauran rayukan in har shi ɗin ya mutu...bana aikin asiri, da ƙwaƙwalwata nake amfani, a tafin hannuna nake zana duk wata manufa tawa, na kuma juya yanda nake son duk wani tsarina ya kasance, saboda haka a gobe wannan aikin ya gudana". a firgice Kulu ta farka, dai-dai lokacin da ita ma Mairo ta farka a firgicen, dukansu salati su ke tashin hankali bayyane a fuskokinsu. sai da Kulu ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan hankalinta ya sauka akan Mairo, wacce ta takure, jikinta sai rawa yake, ga wata uwar zufa da ta haɗa. "menene Mairo?". ta tambayeta tana me yi ma ta rumfa, ba tare da ta fasa bin kowacce kusurwa ta ɗakin da kallo ba tana biyo adu'oi a bakinta. "mafarki nayi". "mafarki kuma? me kika gani a cikin mafarki?". na ɗago na dubi Kulun a tsorace sannan nace,"wai acikin wani jeji me duhu an ɗauremu ni da Basma, ga kuma wata ƙatuwar rijiya me zurfin gaske a kusa damu, wata Mata da ban san kowa ce ba tazo tana jawomu zata jefamu ciki sai ƙyalƙyala dariya ta ke, tana faɗin wai a tsarin rayuwarta bata lissafa da wani abu da zai shige ma ta gaba, tana dab da hankaɗamu cikin rijiyar sai kawai Gwaggona ta bayyana acikin wani irin haske me kyau, tana kuka tana roƙonta akan karta aikata mana hakan ta duba maraicinmu, Gwaggona na cewa kada na bari ta jefamu na sami ƙarfin da zan ƙwaci kanmu, nai gaggawar zuwa na ƙwaci Ya Kabiru daga mummuna hatsarin da ke tunkararsu kuma duk ata sanadin wannan matar, kar na bari, kar na bari komai ya samemu. daga faɗin haka kuma sai Gwaggon ta ɓace, muka nemeta muka rasa, shi ne Basma ta gartsawa Matar cizo a hannu ba shiri ta sakemu, maimakon mu faɗa rijiyar sai ita ta faɗa ciki...kuma kema sai ga ki kinzo mana kina murmushi da dukkan nuna wata ƙauna ta uwa a garemu, sai dai kina kama hannuna ina fizgewa ina tureki akan sai kin barni kin bar rayuwata, shi ne sai wani farin mutum ma yazo, rabin jikinsa haske rabinsa duhu, yana cewa na taho gare shi, amma sai kika ce min a'a kar da naje, shi ɗin ba abin so bane, shi ɗin mutum ne me hatsari, shi kuma wani saurayi da ke zaune kan wata kujera ya harɗe ƙafafunsa yana kallonmu da wani murmushi me cike da tarin ma'anoni da yawa, yana ta wani abu kamar basarake, bini bini sai yaja shati da yatsu biyu a goshinsa, yana murza karan hancinsa kamar me shirin ɗaukar wata fansa, kuma su na kama da ɗaya mutumin da kika ce kar na je gunsa, duka sai na ji kun bani tsoro, hatta da ke ɗin da kika buɗen hannaye na isa zuwa gareki, amma a lokacin zuciyata wani zafi ta ke ji a kanki...dan haka sai na kama hannun Basma muka shiga dajin da gudu don kuɓuta daga cikinsa, saboda ganinku nake kamar za ku cutar dani ne koma kun cutar dani ɗin...sai dai ashe ba hanyar ɓullewa muke ɗauka ba cikinsa muka ƙara shigewa, daga bakin wata ƙatuwar bishiya sai naga Ya Kabiru a hannun wasu tsamurarrun mutane kayan jikinsu duka baƙaƙe, sun yi masa jina-jina yana miƙo min hannu a kan nazo, wai naje gare shi ba dan na cece shi ba sai dan ya mutu a ƙirjin matarsa, shi ne kawai na tafi da gudu kamin na ƙarasa suka fille masa kai". na ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, jikina banda kyarma babu abinda yake, sai kalmar na shiga uku da nake ambata. na sake ƙanƙame hannun Kulu tare da zare jikina daga nata, na ɗago kai na zubawa fuskarta kallo, idan ba wai kallon rashin fahimta nake ma ta ba, fuskarta na nuna firgici sosai, firgicin da ta ke son ɓoyewa, kuma ta yanda wani abu ya wuce ta maƙogoronta na tabbatar da ita ma ta shiga ruɗanin da na shiga, fararan idanuwan nan nata sun ƙara yin haske kamar fitila, yanayin yanda ta ke kallona na yin nuni da irin tasirin nazarinta akaina ko kuma labarin mafarkin da na bata. sai ta kwanto da kaina saman ƙirjinta, ta ƙarasa zame ɗan kwalin kaina, ta ɗora hannunta saman gashina tana shafawa, muryarta a hankali ta fara magana, cikin muryar nan tata da sau tari na kanji ina samun wata iriyar nutsuwa da jinta. "dukkan wani mafarki ba gaskiya bane sharrin shaiɗan ne, dan haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru a cikinsa sai alkhairi insha'Allahu". "amma fa Kulu har da Gwaggona na gani aciki, sannan kuma ki ce min wannan mafarkin ba zai zama gaskiya ba, ki tashi dan Allah muje mu sami Baba a ɗaki, wata ƙila shi ya iya gane me hakan ke nufi". ina jin san da ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya da hucin zafin numfashinta ya sauka ajikina. tabbas mafarki ƙarya ne, to amma ta yarda da maganar Bella da ta taɓa ce musu, "duk da mafarki ba gaskiya bane, amma wani lokacin yana juyewa tamkar madubi ya iya nuna abin da zai kasance a zahirin". tabbas kuma ta shaida hakan, domin ta gani akan mafarkinsu da ya zama iri guda da Aaliya, ga shi a yauma mafarkin Mairon na nema ya haska ma ta madubin zahirinta.
"ki bini a karatun da zanyi". abunda ta faɗa kenan, sai kuma bakinta ya kama da ayatul kuriyyu, na shiga bin karatun bakina na rawa kalmomin na harɗe min, dan har yanzu tsoro bai bar jikina ba. sai da muka kai ƙarshen suratul falaƙ, sai naji tsoron ya bar jikina, nutsuwata ta fara dawowa, firgicin da nake ciki yabi ta iska, na sauke ajiyar zuciya, sannan Kulu ta umarceni da na sauko muje muyi alwala muyi sallah, insha'Allahu koma wane irin sharri ne ubangiji ya juya shi ya zama alkhairi, ba mu miƙe akan sallayarmu ba har sai da muka idar da sallar asuba, sai dai har a lokacin mafarkin bai bar dawo min ba, kuma cike nake da son sanin ma'anar da ke cikinsa, dan haka kawai ba zanyi wannan mummunan mafarkin ba, dole akwai wata ayar a cikinsa da ta ke zuwa gareni, musamman kalmar mata da naji Ya Kabiru ya ambata.
Kulu kuwa safiyar sai ta sakance ma ta mara daɗi, domin tun a mafarkin Mairo na jiya zuciyarta ta shiga cikin taraddadi, tabbas a yanzu, kuma a yau tasan anzo kan gaɓar, a yau ba sai gobe ba Gaskiyar da suke ta binnewa a matsayin sirri zata bayyana, a yau ba sai gobe ba Mairo zata san gaskiyar komai, domin shi lokaci ba ya wasa da kansa, yana bada mitsitsiyar dama ne ga me shirin yin wani tsarin aiki acikinsa.
bayyanar gaskiyar ba ita ce tashin hankalinta ba, Aaliyah!Aaliyah!!! ita ce zata zame ma ta matsala, ita ce zata zame ma ta tsaiko, ita ce zata wargatsa ma ta duk shirin da ta tsara. ta sani! ta san wace Aaliyah! ta san daga lokacin da suka haɗu zata saka ƙafa tayi fatali da wannan rufaffiyar kwalabar da suka rufe a tsakaninsu, idan ma har fashewar da kwalabar tayi bai yi ma ta zata iya sa ƙafa ta ƙarasa mitstsiketa ta yanda wannan alƙawarin nasu zai karye a lokacin, alƙawarin nan da suka ɗaukarwa juna kamin rabewarsu.
*_ME KUKE TUNANI, ME KUKE TSAMMANI?_*
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*31)*
tun bayan da na idar da sallar asuba zuciyata ke faɗamin tabbas mafarkin da nayi gaskiya ne kuma zanga gaskiyar ta bayyana a zahiri nan ba da jimawa ba. a wayewar garin yau ina ji tamkar an buɗe min kundin rayuwata ne ina karanta haƙiƙanin abin da zai yi tasiri akaina a yau. sai naji wata iska me zafi ta shura ta fuskata kamar yanda iska me ɗumi ke bin cikin iskar guguwa, kuma a hankali sai naji wani abu na ɗiga ajikina me zafi kamar ruwan da ke tafarfasa a cikin tukunya, tabbas akwai abin da ke shirin faruwa da ni, sai dai ban san menene ba tunda shi ɗan Adam ba ya sanin lokacin da masifar rayuwa zata kasance da shi, sai dai kawai ya tsinci faruwar musifar akansa. na zuƙi wata iska a hancina wadda nake jin ta banbata da irin iskar da nake shaƙa tun bayan zuwana duniya, Ya Rabb! kasa koma me ke shirin faruwa dani na iya tunkararsa, ka bani ikon ɗauka, ƙaddarata a rubuce ta ke kuma ban isa na guje ma ta ba, ya ubangiji ina roƙonka da ka juya mummunar ƙaddarar da zata sameni zuwa me kyau.
na ɗago daga tagumin da nayi na kalli Kulu da ke gefena, a cikin idanuwanta da ba su ƙarasa rufewa gaba ɗaya ba na hango tarin baccin da ke cikinsu, nai guntun murmushi dan da alama gyangyaɗi ma ta ke bata sa ni ba, sai na miƙe daga kan sallayar na ɗauko bargon rufarmu na shimfiɗa a ƙasa, na kamata zan kwantar da ita saita farka, mu ka haɗa ido nai ƴar dariya ina cewa,"gyangyaɗi fa kike, ki kwanta kinga dai bacci ba'a ɗaukar bashinsa". murmushin da ya tsaya iyakar leɓenta tayi,"ai tare muka raya daren da ke, kema zo ki kwanta ga idanunki nan duk a kumbure". "ki fara kwanciya nima yanzu zan kwanta". na faɗa ina gyara ɗaurin zanina. naji tace,"ina za ki hala gari ko gama wayewa bai ba, yara ma ga su can ina jiyo dabdalarsu ba su gama wucewa makaranta ba". "wurin Baba za ni". sai tayi saurin yunƙurawa ta miƙe zaune,"kar ki sa ke ki ba shi labarin mafarkin da ki kai, kin dai ji na faɗa miki". da sigar faɗa tayi min maganar, kuma naji na ɗauka, domin ina ganin girmanta, dan haka na bata amsa bayan sauya ra'ayina da cewar,"ba zan faɗa masa ba wallahi, ina so ne na koma makarantar asuba saboda na ƙarasa cike haddata, shi ne zanje nai ma Ya Amadu zancen tunda kinga yace gobe zai wuce da wuri". ta gyaɗa min kai,"hakan yayi kyau, Allah ya taimaka, sai kin dawo, ki kula da kanki, Allah ya tsare". "amin". na amsa ina nufar hanyar ƙofa, duk jikina yay sanyi kamar yanda na ke aiwatar da komai cikin sanyi tun mafarkin jiya da nayi.
a tsakar gida na tarar da Inna Amarya tana shimfiɗa tabarma, na saka takalmina ita kuma har ta kai kicin ta ɗauko botikin koko da ta dama, na ƙarasa da sauri na karɓa ina faɗin,"sannu da aiki Inna". "yauwa har an tashi?". "ehh Inna, yau kin kammala sanwa da wuri".
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 52