tsaida aman da ke neman taso min.
cikin fishi na miƙe zan bar wajen muryasa a ɗage yace da ni,"koma ki zauna". ina zama ya haɗa ni da jan dogon tsaki fuskarsa na ƙara haɗo ɓacin rai ta bayyanar.
Sadiya da Adawiyya da Jamila su ka shigo da sallama, su ka gaidasu Yaya sannan su ka gaida Yagana, kamin mu gaisa da su suyi min sannu da jiki. ina dubansu da muryata da har yanzu bata saki ba nace,"ina za ku je?". Adawiyya tace,"ɗinku nan Sadiya zamu kai". da yake an kusa bikinta saura sati huɗu gaba ɗaya. na miƙe tsaye ina faɗin,"dan Allah ku tsayani mu tafi tare". "lallaima ke ɗin nan, ke da ba ki da lafiya". nace,"naji sauƙi ai...ba ku taɓa zuwa dani ko'ina ba fa tun da aka fara shirin bikin nan, kuma ina ta son zuwa, sai dai naji Inna tace kun fita". Jamila tace,"to ba Yagana ce ke ƙunsheki a ɗaki ba ta hanaki fitowa wajenmu, kinga kam ai bama yi tunanin kina son zuwa ba". karaf maganartata a kunnen Yagana da ke fitowa daga ɗakinta.
"ba dan ance ba kyau idan mutum ya tuba daga wani saɓo da yake tafkawa ba a dinga taso da abubuwan da ya aikata a baya, Jamila ai da na yaɓa miki magana akan Uwarki...kuma kije dan kanki idan sharri abinyi ne kar ki fasa". ta zauna akan kujera tana ci gaba da faɗin,"dama na jima da faɗa miki wannan zaman keɓa kan da kike sai ya jawo min magana, ace ina rabaki da su saboda naga yanzu ke ƴar gata ce...gashi nan yanzu ina zaman zamana kinja min zagi da sanyin safiyar nan". Jamila tace,"Allah ba ki haƙuri Yagana ni ban faɗa da wata manufa ba". ta taɓe baki bata ce ma ta komai ba, ta maida hankalinta gun Ya Kabir tana faɗin,"Ɗan Hajara ai na muka kwana da kai?".
"Yagana na shirya na bisu ɗin?". bata dubi inda nake ba tace,"wallahi ba zaki je ba...na gama magana Maryam". tana faɗin hakan nayi ɗakina a zuciye, ina shiga kuma na shiga tattara kayana ina zubawa a trolly, ko ina za ni da su oho.
da yamma ina kwance akan gadona cikin nurƙufanci Inna ta shigo ɗakin, dama tun da safen nan da na shigo na gama haɗa kayana ban kuma fita ba, abincin rana ma da Yagana tazo tai maganar duniya nai ma ta shiru naƙi kulata, har taji haushi tace in dai sunanta Rakiya ba zata ƙara min magana bare na wulaƙantata.
"Maryam jikin ne?". Inna ta faɗa tana zama gefen gadon tana taɓa jikina. zafin da taji yasa ta ɗauke hannu tana faɗin,"subhanallah, kin ko sha maganinki ɗazu?". kai kawai na ɗaga ma ta. ta sake cewa,"Allah ya baki lafiya, tashi muje ga Mu'azzam can yazo zai miki alluranki". "Inna dan Allah bana son wannan allurar". ta ɗagani daga kwancen tana faɗin,"nasan baki son allura amma ya za ki, dole ce tasa...daure ki tashi kinji ƴar albarka, ina aka taɓa zama da ciwo a jiki ba tare da an magance shi ba, abin da ma Mu'azzam ba shi da zafin hannu".
Yagana ta shigo ɗakin ita ma. "ke ki fito ai miki allurarki dan yau ban shirya hana idona yin bacci ba". muryata kaman zanyi kuka na ɗan doki ƙafata a ƙasa nace,"nifa Yagana yau a ɗakina zan kwana Allah ba zan hanaki bacci ba". ta ɓalla min harara sannan tace,"kin san Allah ba ki isa ba allurar nan sai anyita, jiya ni ɗaya nasan me naji a zaman jinyarki...kema Zulai kin wani zauna kin zuba ma ta ido tana abin da taga dama, ta bakin Amadu ki figo hannunta kawai". na ƙara ɓata rai ina cewa,"to ni dai Yagana ki rabu dani mana tun da ciwon a jikina yake". ina faɗin hakan tasa kai ta fita daga ɗakin tana jijjiga kai.
a parlon Yagana, Baba ne da Manyan Ƴaƴansa zaune, cikinsu Ya Kabir ne kawai babu. kuma ganinsu baisa na daina kukan karɓar allurar ba. Mu'azzam ya ɓare syringe ɗin yana zuƙar ruwan alluran, na tafi wurin Baba na ƙanƙame shi ina kukan ni ba za'a min ba, shi kuma Baba nata bani haƙuri.
"ashe ka shigo?". Yagana tace da Baba tana zama a kan kujera. "Ehh Yagana...ina yini". ta amsa masa,"lafiya lau, ya ka baro su Alhaji Ƙaramin?". "su na lafiya duk sunce agaisheku...ashe bikin ƴar gidan Baffayo ma sati guda ne da na Sadiya". tace,"haka Nafisatu ke faɗa min ranar da su ka zo ganin gida, to mu dai baza muje ba sai dai suzo nan a haɗe ayi tare, in ba haka ba kuma maje musu murna daga baya". Baba ya kaɗa kai da rigimar da Yagana ke neman ja sannan yace,"jikarki dai har yanzu taƙi girma". ya faɗa yana zolayata da na ƙanƙame hannayensa, kuma sai na sadda kai a gefen hannunsa ina jin kunya.
Kamar jira dama ta ke yay magana akaina sai ta gyara zama ta fashe da kuka tana dafe goshi. gaba ɗaya idonmu yay kanta hankalin kowa a tashe, abin da ba'a taɓa ganin tayi ba, Baba yace,"Subhanallah Yagana me ya faru?". bata bar kukan ba tace,"Adamu gidana zan koma tunda Allah bai sa an siyar da shi ba, zanfi samun salama idan na koma can". Baba ya ƙara cewa,"Yagana akan me? ko wani abu ya faru a gidan nanne?". ta zuƙi hanci ta fyato majina tana faɗin,"to mene ma bai riga ya faru ba Adamu, kawai ni dai gwara aiwa tufkar hanci tun jinina bai hau ba, ga kayana canma na gama haɗawa tafiya kawai zanyi dama jiran isowarka nake yi, kar na bar gidan ban sanar maka ba kaga rashin kirkina". wannan karan ba Baba ne kaɗai yay magana ba, kowa sai da ya jefa ma ta tambayar,"wai Yagana me ya faru ne?". ni kaɗai da banyi tambayar ba kallon Yagana nake da bugawar ƙirji, me yasa ta kuka? kuma me yasa ta ke maganar zata bar gidan?, nayi tsilli-tsilli da idanu ina kallonta da jiran amsar da zata bayar.
kukanta ya ƙaru a san da take cewa,"ni dai ba muguwa bace, kuma ba ƴar baƙin ciki ba ce. amma ban san me yasa ake min bahagon kallo ba, wallahi ni dai ko ƴaƴan kishiya ba zan iya cutarwa ba balle jikokin da nasan daga tsatsona suke...Adamu a rayuwa me nayiwa ƴaƴanka da za su dasawa zuciyata baƙin cikin da zai kashe ni, idan wani abun nayi musu tsakani da Allah ai sai su fito fili su faɗa min na basu haƙuri tun da ni ba baƙuwar zafi ba ce. amma haka kawai sai su ɗau karan tsana su ɗora min, su ɗauki gaba da ni, ɗabi'ar da ubangiji ba ya so". tayi shiru tana murza idanu, kowa ya sauke numfashi. Baba ya shiga kallonmu kamin ya kira sunan kowa, sannan ya kalli Inna ma yace,"Zulai meke faruwa a cikin gidan nan da ban sa ni ba?, domin nasan indai fitina zata fito daga ɓangarenki ne, me Ƴaƴanki su kaiwa Mahaifiyata da baku ɗauketa a bakin komai ba". yay maganar cikin faɗa da ɓacin rai...Yagana tayi saurin cewa,"a'a kar ka ɗauki hakkinta babu ruwanta babu ruwan ƴaƴanta acikin wannan lamarin...nifa ina maka magana ne akan Kabiru da Mairo". Baba ya juyo yay min wani kallo da yasa na ƙara tsurewa dan ban san wani laifi da nayiwa Yagana ba.
kuma maganar Yaganan ta katse shi daga abin da yake son cewa, a wannan karan kuka ta ke sosai wanda yafi na ɗazu. "kaga Adamu yaron nan Kabiru tun da uwarsa ta mutu ya ɗaukeni tamkar uwa, ba ya ɓoye min komai, halinsa me kyau, nima na ɗauke shi tamkar ɗa ba jika ba, tun da Allah ya sani kaf cikin jikokina nafi ƙaunarsa ba zan ɓoye ba...amma yanzu kashi ma ya fini mutunci a idon Kabiru, gaba ɗaya ya ɗauke min wuta ba ya kula ni, wannan shegiya abar banza gaisuwa Kabiru in zamu doki ƙirji da shi ba zai min ba, kai na taƙaice maka ma ɓangarena ya daina zuwansa...to ni duk ba wannan ya dameni ba, damuwar da nake gani a fuskarsa ita ke ci min tuwo a ƙwarya, juyin duniya nayi da shi ya faɗa min matsalar yaƙi, ƙarshe ɗazu da safe da na tsare shi da tsaki ya bini kafin ya tashi ya fita fuuuu kamar guguwa, to wannan halin kyautawa ne fisabilillah, ni ya riƙe maganarsa amma ka faɗa masa bana son ganinsa a damuwa wallahi". Baba yay ƙasa da murya yace,"kiyi haƙuri Yagana, zan tuntuɓe shi naji meke faruwa". tana shashsheƙa tace,"da ka taimaka min, dan ni dai da wannan halin miskilanci da Amadu ya sauka akai shi kuma ya hau gwara kullum yazo ya dinga faffaleni da mari ko kuma yace na mutu kawai ya daina ganina, hakan zai fiye min da dai naci gaba da ganinsa da damuwa". Baba ya ƙara bata haƙuri tace babu komai, ya kalli Lukman yace ya kira masa Kabiru, sannan yace da Yagana,"ita kuma Maryam me tayi". ta goge fuska tace,"wannan abar ta kusa da kai ai fitina ce Adamu, shi yasa nace barin gidan nan zanyi tun bata ja ubanta yasa an yi min ɗaurin rai da rai ba, ko kuma tasa uwarta ta maidani baiwar masarauta". nayi kicin-kicin da fuska nace,"Yagana nifa babu abin da nasan nayi miki". tace da Baba,"kaga ni baa, duba fa a irin yanda ta ke min magana kamar zata dukeni, kasan kuwa ba ƙaramin haƙurin zama na ke da ita ba. aini tun da ƴar nan ta balaga nasan zan fuskanci babban ƙalubale, to inda Allah ya taimaka ina kai lamarinta wurin Allah amma banda haka tuni tasa an ɗaureni". Baba ya kalleni fuskarsa a ɗaure yace,"me kika ma ta?". "yo ka tambayeta salon ta ƙaryata zancena Adamu, kaima kasan ba zata faɗi gaskiya ba sai dai tayi ƙarya ta kare kanta". Baba yace,"ki barni da ita". nace,"Allah Baba ni dai nasan ban mata komai ba, kawai so ta ke taja min faɗa a wurinka". sabon kukan da ta fashe da shi ya tari numfashina. "Adamu na faɗa maka yarinyar nan fitina ce, idan kaci gaba da tambayarta zata ƙaryata ni ba tare da duban shekaruna ba. abinda ya faru ɗazu fa daga ƴar ƙaramar magana nace ba zata bi waɗancan marasa kunyar unguwa ba shikenan sai ta ɗaura gaba dani, ta shiga ɗaki ta haɗa kayanta wai barin ƙasar za tayi. na tsuguna na bata haƙuri amma duk bata ga wannan ba haka taƙi saukowa. abincin rana ma da na bita da shi ɗaki ƙinci tayi tasa ƙafa tai fatali da kwanon". ta dubi Nawwara tace,"ko ba haka akai ba ke?". Nawwara dai tayi shiru ita kuma taci gaba,"to ɗazu ma daga shiga ɗakin nace tazo ai ma ta allura sai ta balbaleni da masifa, wai na fita a lamarinta na daina shiga sabgarta ita bata son takura. jiya jiyan nan ma fa haka taje ta ƙala min sharri a wurin wancan ɗin, shi kuma sai ya turo ɗan'uwansa, haka Amadu yazo tsakiyar kaina kamar zai zaneni yayta banbami wai na daina takura mata...ka ga fa ba yau ta soma haɗani da mutane ba, kwanaki da nayi baƙi Allah yarinyar nan sai ta koma kamar marainiya a gidan nan, kaga waccan kujerar nan ta zauna ta dinga ɗacin rai da nurƙufanci tana kuka haka kawai ba'a ma ta komai ba, duk dai dan taja min masifa, su kuma da gulma suka dameta da tambayar wai me aka ma ta, to ka faɗa min Adamu duk san da tayi irin haka agaban iyayenta me za su ce tsakani da Allah, ai sai suce sun rufa mana asiri ni kuma ina tsangwamar ƴarsu. ka tambayeta kaji wallah ko bacci bana iyayi sai naga sunyi ita da ƴar'uwarta, amma ta rasa da me zata dinga saka min sai da mugun halinta, kuma da tayi abu nayi ma ta gyara zata turo baki gaba kamar kuratandu, to ni dai na gaji gwara na bar ma ta gidan, tun da dama ba Ummana bace ta siya".
Baba yace,"kiyi haƙuri Yagana ba zata ƙara ba daga yau". tace,"hmm Adamu kenan baka san wace Mairo ba...to ka bar lallamata ina faɗa maka, dan kaima bata ƙi taja maka baƙin jini ba a wurin iyayenta, kaga dai fa ba lafiya gareta ba amma taƙi tsayawa ai ma ta maganin abin, alhalin tasan yau Akila zata dawo, to yanzu idan ta dawo taga ba'a bata magani ba'a ma ta alluran da likitoci suka bada me shegen tsada ba me zata ɗaukemu tsakani fa da Allah?, to ni dai gaskiya asan abinyi, ko zamana a gidan nan ko barinta dan ni nagaji da halinta, ba zai yiwu ta dinƙa neman jefani a masifa ba". "kiyi haƙuri dai Yagana". "to haƙuri ai ya zama dole Adamu. kaga shi wancan ɗin da ka aika a kira tun ɗazu har yanzu bai zo ba, dama ni nasan ba zai zo ba indai yasan kana ɓangarena". Baba yace,"to wai shi da ba shi da lafiya ma, yaushe ya tsiri wannan halin?". maganar Baba ya ke ransa a ɓace. tace,"aini na gama magana, ga dai Zulai nan ka tambayeta kaji. Kabiru ai ya zama sai adu'a". Zulai tace,"aini Yagana duk ban san hakan tana faruwa ba. amma komai zai daidaita". tace,"uhmm daga jiya zuwa yau kawai Kabiru ya zama abin da ya zama, ki faɗa min idan akai gaba sai ya ya? aishi ice tun yana ɗanye ake taƙwarashi".
Ya Kabiru da Lukman su ka shigo, ya zauna a ƙasan carpet kansa a ƙasa. Baba ya shiga yi masa faɗa sosai shi kuma yana bada haƙuri. ya ɗaga kai ya kalli Yagana yace,"Yagana dan Allah kiyi haƙuri". tace,"na haƙura na yafe maka. nima kayi haƙuri ka yafe min". sannan Baba ya juyo kaina da nawa faɗan, faɗan da sai da ya sa ni kuka, na bata haƙuri kuma sai da ƙyar tace ta haƙura.
Baba zai fita nima na kai masa ƙarar Ya Kabiru, kuma bai tsaya ba yace,"wannan kuma laifina ne, may be rashin kunyar da nakewa Yagana nayi masa".
gaba ɗaya na manta da zancen za'a min allura sai bayan da taron kai ƙorafin Yagana ya ƙare, a rayuwata ganin allura na ɗaga min hankali, Ya Kabiru ya tashi zai fita nayi jikinsa na ƙanƙame shi ina kuka, kamar zai janyeni kuma sai ya fasa. ya ɗaga wayarsa da ke ƙara ya kara a kunne. daga yanda naji ya amsa maganar da aka masa daga cikin wayar na gane da ƙyar idan ba Ummina bace. "oak tom gani nan zuwa". sai kawai naji ya ɗora min wayar a kunne, muryasa can ƙasa a hankali yace,"Ummi ce". sai na shiga murna babu shiri, ina tambayarta yaushe zata dawo. abin da na sani kawai shi ne, naji san da Ya Kabir ya karɓi allura daga hannun Mu'azzam amma ban san ya tsira min ba har ya zare sai da Yagana tana lailaya min wurin. na kalli Yaganan nace,"allurar za'a min, nafa ji sauƙi". ta taɓe baki bata ce da komai ba ta wuce ta bar wurin.
ina Kallon Ya Kabir da zai fita nace,"Yaya tun shekaranjiya fa Ummi tasa aka kawo driver, amma kanata driving da ƙafanka bai gama warkewa ba". "who told you so?". na ɗan haɗe fuska nace,"ɗazu ai ka kai Nawwara makaranta". ya ɗaga kafaɗa sannan yace,"am well now. za ki je ɗauko Ummin?". nayi knodding kaina da cewan,"ehh". na faɗi hakan cike da murna, dan sosai nayi kewan Ummina. "to ki fito da sauri". ya faɗi hakan yana sa kai ya fita daga parlon. da ni da shi da Basma mu ka tafi ɗauko Ummi a airport.
for those who viewed, vote, like and comment i really apprciate, thank so much to you guyz, i love you lodi lodi.
*Plss Comment, Share & Vote.*
[7/16, 17:45] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*(43)*
*4Months Letter.*
*Qatar University, Doha.*
"Maryam Mukhtar Afafa". sautin kiran sunan nawa ya fito ta cikin hall ɗin daga can sama, daga bakin Shamsiyya Sani, sanin cewar kiran nata bana arziƙi bane yasa ban tsaya sauraronta ba, naci gaba da tafiya abina, tafiyar da ka kalla yanda nake yinta zaka san nayi matuƙar gajiya.
a hankali na ke saukowa daga steps ɗin bakin hall ɗin namu, hannuna na dama riƙe da matsakaiciyar jaka kasancewar yau ban lodo handouts ba. kamin na kai ga ƙarasa sauka daga step na ƙarshe na zare space glass ɗin da ke kewaye da rabin fuskata, sannan na zura hannun haguna cikin aljihun pink abayar da ke jikina wadda su Shamsiyya su kai ta santinta su na faɗin rigar ta dace da ƙirar jikina.
a bakin hall na tsaya ina jiran fitowar Shamsiyya da Nusaiba amma shiru shiru ba su fito ba, naja ƙaramin tsoki na takaici sannan naci gaba da takuna cikin natsuwa har san da na taka kan titin cikin makaranta, yanda nake ta faman ɓata fuska zaka ce ko banda lafiya ne, haka ina ji wayata na ringing amma naƙi ɗagawa duk da na san mutumin da kiran nasa ke shigowa cikin wayar me muhimmanci ne a gare ni, kamar yanda na banbanta ringing ɗinsa da na saura.
"Ya Ahmad". angona wanda za'a ɗaura min aure da shi nan da sati biyu masu zuwa. tafiyar da nayi akan titin gaba ɗayar bai fi taku 8 ba naja na tsaya, tsayawar tawa tai daidai da tsayawar motar da ta zo ɗaukana a gabana.
a cikin yaren larabcin da a yanzu ya maye harshena nace da driver,"me yasa kayi late yau?". "kiyi haƙuri ranki ya daɗe, na kai Alhassan library ne, bai kammala da wuri ba ne shi yasa, kuma na yita kiran wayanki ba ki ɗaga ba". "yana ina?". na tambaye shi a sa'ilin da nake duban cikin motar ban ganshi ba. "yanzu zai ƙaraso ya tsaya da abokansa ne su na gaisawa, hangoki da yay ne yace na ƙaraso na ɗauke ki...ga ma shinan naga ya taho". ya ƙarashe zancen yana min nuni da direction ɗin da Alhassan ke tahowa wanda ke gab da iskomu.
"menene? ba ki da lafiya? wani abun aka maki?". tambayoyin da Alhassan ke jera min kenan ya ƙaraso yana ɗora hannunsa saman goshina, yana mai tambayar cike da nuna damuwa da kulawa. na kwaɓe fuska ina karayar da kai nace,"na gaji ne". "to sannu". ya faɗa yana amsar jakar hannuna, sannan driver ya buɗe mana motar muka shiga, ko da shigarmu ban iya zama ba sai kwantawa da nayi na ɗora kaina saman cinyarsa.
"Mami ta tafi?". na tambayeshi a amon muryata na fitowa a hankali. "har ta shirya sai kuma tace ta fasa wai ba yanzu ba". lokaci guda naji wani abu ya tsarga min a zuciyata, wani abu da ya haddasa jin daɗi a ƙasan ruhina. ko kaɗan bana son nesanta da ita, shi yasa ko da na taho karatu wata huɗun nan da nayi babu ita kusa da ni sai nake jina tamkar ina rayuwa ne a cikin kurkuku, irin kurkukun nan da ke da duhun ɗaki da kuma ganiyar azabtar da me laifi.
driver ya tsayar da motar a rumfar wajen da aka tanada dan ajiye motoci, motocin da ake fita da Ammi kaɗai a cikinsu, sai ni da na zama ƴar gidan yanzu, ya fito yazo ya buɗe mana ƙofa, kamin na zuro siraran ƙafafuwana da suke ɗauke da gajiya waje, Alhassan ya kama hannun mu kai cikin gida. sanin cewar a irin wannan lokacin Ammi na tare da Abbi ne, yasa bamu biya ta parlon da ta ke zama ba. muka wuce kai tsaye zuwa ciki inda sauran ɗakunan ɓangarenta su ke wanda acikinsu ne aka fitar min da babban ɗaki guda aka bani tun zuwana karatu ƙasar, dan lokacin da Ummi tayi aure acan saudiya wurinta na koma da zama, sai ma lokacin da za'a saka ranar biki ne naje can abuja inda Mami take na zauna na tsawon sati biyu daga abuja kuma na wuto Qatar, ko su Yagana banjewa sallama ba a lokacin.
"Subhanallah, me ya faru da ita?". muka jiyo muryar Ammi da bamu tsammaci gani ba tana tambayar, na kalleta da gajiyayyun idanuwana ina ƙara kwaɓe fuska nace,"Ammi yau na gaji ne". sai ta miƙa jakar da ke hannunta wa Kuyangar da ke bayanta, sannan tayi saurin tahowa gareni ta riƙoni zuwa jikinta. Alhassan kuma ya wuce ɗakina kai min jakata, akan cushion ɗin parlon muka zauna Ammi ta shiga warware min vail ɗin da ke kewaye da fuskata tana yi min sannu.
ta kwantar da kaina bisa kafaɗarta tana jera min wata sannun, sannun da bata da adadi tun daga lokacin da ta riƙoni. cushion ɗin da muke zaune na fuskantar steps ɗin da su ke cikin parlon, ta nan na jiyo takun tafiyar takalmi ƙwaf-ƙwaf na sakkowa daga upstairs ɗin, kamin wucewar sakanni biyu kuma naga ɓulluwar Mamina, tana sanye ne da butter milk ɗin abaya wadda tasha stones a jikinta, ta kuma matuƙar amsar kyawun nata, ta ƙarasa saukowa tana sauya hannu na riƙe wayar da ke kare a kunnenta zuwa ɗayan hannun da ke riƙe da ƴar ƙaramar jakarta haka ta ƙaraso wajen cushion, ta cikin wayar da ke kare a kunnen nata ta ke faɗin.
"a'a i just want to stay more for a while". tayi shiru kamin ta ƙara magana,"oak hakan ma Yayi Your Excellency. muyi waya letter". daga haka ta katse wayan a yayinda ta ke zama acikin ɗaya daga cushions din. "sannu da hutawa Ammi". "yauwa". lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawayen da basu kai ga sakkowa ba, muryana na rawa nace da ita,"Mami sannu da gida". "yauwa sannu". ta faɗa ba tare d ta nuna halin in kula a gareni ba, wanda hakan ke damuna sosai, kuma da dukkan alamu bata gane ina cutuwa da wannan shariyar tata ba, haka ko time ɗin da na zauna a abuja zaman da mu kai da ita tamkar wani zaman kishiyoyin da basa jituwa ko kuma zaman sirikan da, ƙwaƙwƙwarar magana bama yi da ita, sai dai na bita da ido, nayi tunani kala daban daban ko wani laifin na mata amma na gagara gano komai, kuma taƙi bani damar da zan zauna da ita naji laifina na bata haƙuri.
nasa hannu na mayar da hawayen da ke neman sakko min, kamin muryarta ta ƙara fito min da faɗin,"Daddynku na gaidaki, wai bai sameki a waya ba". tayi maganar idonta na kan wayar da ta ke shafawa. "mun yi lectures da yawa ne yau shi ne nasata a silent". bata ƙara cewa komai ba sai Ammi da ke cewa,"ina ga ki kira doctor ya duba Maryam, ban yarda da yanayinta na yau ba, kanta ma naji da zafi". nayi saurin ce da Ammi,"Ammi lafiya fa nake wallah, kawai stress ɗin yau ne". "eh duk da haka dai yazo ya ba ki wani maganin kisha...tashi kije kiyi wanka ki ɗan huta kamin ya ƙaraso".
Alhassan da ya ƙaraso wajen yana zama kusa da Mami ya ɗora hannunsa a bayan wuyana ya dafa ni ya kalleni yana cewa,"zama ki rabu da wannan son jikinne, kwana nawa ya rage". na turo baki gaba ina hararsa. sai yasa hannu ya ɗago fuskar Mami yana ce mata,"kalla yanda ƴarki ke hararata, to ki faɗa mata na rigata shaƙar iskar duniya, ta kiyayeni kafin taji ajikinta". Mami ta murmusa kuncinta ba tare da ta ce masa komai ba ta maida kanta kan wayar. Ammi tace da shi,"shegen son girma kaman gyaute...kai yanzuma aka ce ka daketa sai ka taɓata?". ina siririyar dariya nace,"rabu da shi Ammi, ai yanzu ko Bro Almustapha ba zai ɗaga hannu akaina ba, kasan kenan kuwa na girmi gaban dukanka". sai ya jijjiga kai bai ce komai ba, sannan ya sumbaci Mami a kumatunta ya miƙe tsaye yasa hannu a cikin aljihun wandon suite ɗin da ke jikinsa, ya dubi Ammi yana ce mata,"mijinki ne fa yace na kira masa ke, kiyi sauri sauri kije fita zamu yi". Ammi ta kai masa hannu ya kauce yana dariya. "kai ni wai yaushe ma zaka koma inda kafi wayo ne, na gaji da ganinka ina faɗa maka". yana nufar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 52