zuciyar Kabir ɗin Maryam".
Kabir ɗin ya ƙaraso wurin da ƙaramin table yake me zagaye da ƙananun kujeru guda biyu, ya zauna su na fuskantar juna yana kaiwa Abdurrahim ɗin naushin wasa a kafaɗa. shi ma yasa wuƙa ya yanki pizzar daidai wadda zata shiga bakinsa. "na gaji da irin wannan cimar ta isheni, abincinmu na gargajiya nake so, dan haka ka shirya gobe zaka fara cin abincin tamu ƙasar, zan mana tuwan dawa da miyar kuka me rai da lafiya, wanda idan kaci kaji garɗinsa sai ka damƙa min Atm card ɗinka kace kullum nake mana irinsa". Kabir ya faɗa yana kai pizzar bakinsa.
"Tuwon dawa! tun a sunan ma ba daɗi ina ga anzo ci, Abbu ya faɗa min san da yaje nigeria abincinsu babu daɗi sam, da niyyar sati guda yaje amma kwana ɗaya tal yaji ba zai iya ba...ko Mima ma da take ɗan zuwa da kayan abincinta take tafiya, dan haka ni ba zanci wani abincinkun ba gwara kake mana ordering kawai idanma ƙiwar girkin kake".
ya faɗa yana kai kofin juice bakinsa.
Kabir yace da shi, "aikuwa sai dai ka koma siyen abinci duk ranar girkina, dan wallahi a yanda nasa Gwaggo tai min aiken garin masara dana dawa da kuma daddawa, to Abdurrahim ka shiga uku da ganin abincin nigeria a idonka, sai dai idan banji yunwar ba...ni ba asararre bane da zanta saka kuɗina akan hanyar siyan abincin da ba ƙoshi nake dashi ba, dama ace irin girkin Leemars Mandi ne a ƙasar taku, to da sai nayita saya nasan duk inda naci plate ɗaya ya wadatar, kuɗina yanzu bana ciye-ciye bane, na ginin gida ne, gidan Maryam".
ya ƙarasa maganar fuskarsa na faɗaɗa da murmushi.
"A dai rage buri, dan rayuwa bata tafiya daidai da muradin zuciya, kai ta adu'a kawai".
Kabir yay masa wani kallo ta cikin reflection glass cup ɗin da ya kai bakinsa yace,"Abdurrahim ka rage baƙin ciki, na faɗa maka kuma shawara na ke baka".
dariya ta biyo baya a duka fuskokinsu, san da kuma suka sauya babin firar.
"Fahad yace an fasa yin lectures ɗin...so kaga sai muje ga tafiyarka, na tambayi wani neighbour ɗinmu ya shaida min ranar friday akan iya barin wasu tsirran mutane su shiga Emirate, Sarki yana bada lokacinsa wa baƙin mutane a wannan ranar, so mu tafi tun yanzu ƙila ka taki sa'arka a yau".
Kabir ya lashi leɓensa na ƙasa sannan yace,"kasan me?". "a'a sai ka faɗa". ya jingina zamansa ga kujerar yana sauke numfashi,"nazo ƙasar nanne da manufofi guda uku kamar yanda na faɗa maka a baya, karatuna, aikinyi da kuma binciken sirri da aka sani. kuma tun zuwana na ke a ƙagauce da na shiga cikin masarautar na samo bayan nan da ake so a sani. to amma kamar yanda ka faɗa cewar zan iya taka sa'a a yau, nima kuma nake jin kamar lokacin sanin komai yayi, sai nake jin faɗuwar gaba da fargaba".
"idan har babu rami to me ya kawo rami Kabir?, ai in dai binciken da zaka yi bana cutarwa bane to ka cire wannan daga ranka, go straight forward to your work, shi ne magana kawai".
Kabir ya buɗe lumsassun idanunsa ya sauke kan Abdurrahim yace,"thank you my friend for encouraging me on so many things...tashi mu fita".
su ka miƙe suka fita, sai da suka je wurin mota Abdurrahim ya shafa aljihunsa yana laluben key ɗin motar.
"wai jiya dana dawo ban baka key ba?". ya tambayi Kabir ɗin yana tsayawa da laluben. "bayan sai da nayi bacci ma ka dawo". ya bashi amsa.
"to Allah yasa ban yasar da shi ba, dan wallahi ko ɗazu dana duba ban ganshi ba, thats why i din't show you those files". "ka koma dai ka ƙara dubawa yana nan, wani wurin ka jefa shi".
Abdurrahim ɗin ya juya ya koma ciki, ya ɗauki wasu daƙiƙu kamin dawowarsa yana faɗa masa ashe a toilet ya barsu.
Kabir ke driving ɗin yayinda Abdurrahim ke zaune a kujerar me zaman banza, yana yi masa bayanin kan yanda su kai da Abbu(mahaifinsa) akan office ɗin da yake so ya fara zuwa. Kabir yace masa ai ya amsa kawai, ba zai ga alfanun hakan ba sai nan gaba, shi kuma gyaɗa kai yay godiya ga shawararsa.
a wani katafaren store da aka rubuta *HAJARA SHOPPING MALL* Kabir yay parking motar daga wurin da ya saba parking a duk san da ya shigo store ɗin, ya kashe motar suka fito suka nufa cikin store ɗin, store ne da ke shaƙe maƙil da kowanne irin abin buƙata, yana daga cikin store ɗin da a watanni biyu da suka wuce ya shiga sahun manyan shopping malls da akeji da su a ƙasar.
shigarsu ciki sun jima sosai, sai dai babu wani abu da suka siyo, dan ko da suka shiga ba wajen ɗaukan kayayyaki suka nufa ba, direct office ɗin Manager da ke acikin store ɗin suka shiga, kuma Managern bada kowa yay magana ba sai Kabir, Kabir ɗin da yay masa tambayoyi game da yanda ciniki ke tafiya a kwana uku da bai leƙo ba, Manager ya shaida masa nasarar nan dai da ake samu a kullum har yanzu ita ce, babu faɗuwa sai Continuancy da ke ta ƙara haɓɓaka, dan jiya ma ya fitar da lissafin kuɗi naira miliyan shida da suke saka ran haɗasu a wata biyu, sai gashi an haɗasu a kwana biyar kacal, ya ɗauko wani file a sanda yake sanar da Kabir ɗin haka ya miƙa masa gabansa.
"Alhamdulillah, Masha'Allah". Kabir ya faɗa bayan ya gama duban takardar da ke ɗauke da lissafin adadin kuɗaɗen da suka shigo da kuma wanda aka ware za'a ƙara fitarwa wajen yin wata ordar, duk acikin watan kawai, fuskarsa sai fitar da murmushi take.
Hajara Furnitures shi ne kantin da Kabir ya buɗe a tun watan farko na zuwansa ƙasar, da kyautar kuɗaɗen da ya samu daga wurin Bella da kuma kyautar gidan da suka bashi, a tahowarsu ne ya sayar da gidan naira miliyan ashirin da shida dan ba gidan banza bane duk da cewar flat house ne, to amma zubin ginin kaɗai zaka kalla ka sami tabbacin bada ƙaramar dukiya akayi ginin ba. shi a wurinsa zai riƙe kuɗinne dan buƙatun yau da kullum har ya kammala karatunsa, to sai bayan saukar tasu ne kuma ya sami saƙon check na wasu adadin ethopian birr daga wurin Bella, adadin kuɗin da idan ba ɓarnar banza zai yi dasu ba za su ishe shi gama rayuwarsa, yaji daɗin kuɗin sosai ya kuma ƙara jinjinawa mutumci da karamci irin na Bella, macen da bata manta alkhairin mutun a gareta ko mai ƙanƙantarsa.
dan haka ne yaga da abu ɗaya ya dace da shi, wanda zai kankarowa kansa mutumci da ƙima shi ne ya gina kansa, ginin da ba shi kaɗai zai amfana ba, har na kusa da shi ma. Abdurrahim shi ne abokinsa da suka fara haɗuwa a lectures, kuma halinsu yazo ɗaya, shi ya wuce masa gaba wajen taya shi neman hayar shago, sannan ya ƙara wuce masa gaba ya kaishi inda aka bashi haske aka kuma wayar da shi da shigo da kaya daga ƙasashen waje. Furnitures ya fara zubawa a shagon, kamin wata uku ta rufa kuma tuni ya maida kuɗaɗen da ya zuba, bai fara komai ba sai da ya kira waya ya nemi albarka da adu'ar mahaifinsa da ya rage masa, ya sanar da Gwaggo ma, ya kuma sanar da Malaminsa, shi ma kuma adu'ar yake babu dare babu rana, da sadaƙa, da yin ƙiyamullaili a kowanne dare, saboda haka yake ta ganin bunƙasa ta yacca bai yi tsammani ba.
bayan barinsu store ɗin kai tsaye Emirate of Harar(masarautar ethiopia) suka nufa, da zuwansa ya taki sa'ar da ya ke fatan samu, dan shi ne mutum na biyar a mutanen da akaiwa izinin shiga su sami ganawa da Sarki Abd Ash-Shakur. sai da ya ɗauki tsawon awa guda acikin fadar sarkin da ke ta amsar bayanai daga wasu makusanta shi kamin ya sami damar ganawa da sarkin ya sanar masa shi ɗin masoyinsa ne na haƙiƙa yazo ne na musamman dan miƙa masa gaisuwa, Abd Ash-Shakur yaji daɗi sosai dan har hoto sai da ya sa akayi musu tare, bai baro cikin fadar ba sai da akayi sallar juma'a tukunna.
da fitowarsa kuma ya sami wani dogari da ya kwashe duk wani tarihi da ya kutsa acikin masarautar shekaru goma sha biyar da suka shuɗe har zuwa yau, yaji daɗin samun duk wasu bayanai daga bakinsa, irinsu ne ake jin daɗin samu a harkar bincike, dan sai sun feɗe maka biri da wutsiyarsa a duk abin da suka ji suka gani saboda tsabar iya gulma da sa ido.
ba a haka kawai ya sanar masa da komai ba, aikin kuɗi yay masu yawa, shi yasa ko da ya kammala sai da ya ƙara tambayarsa idan yana buƙatar ƙarin wani abu na koma menene yasa shi ya nemo masa zai ji bayani. murmushi kawai Kabir yayi, ya gama samun abunda ya shigo da shi cikin masarautar, dan haka ya ɗauki hanyar fita a hanzarce, sam ba neman taimako yaje ba, ko kai ƙorafi ba kamar yanda ake kallon duk wanda ya shigo a wannan lokacin.
acikin fadar ma sai da ya dinga ɓoye fuskarsa da p-cap gudun kar su haɗu da Suhail ko Jawad idan su na ƙasar, fitowar tasa daga ciki kuma yayi daidai da ƙarasowar Abdurrahim da ya kira ya sanar masa ya gama yazo su tafi.
Abdurrahim ya so, kuma yana son ya san akan me yayi binciken da kuma dalilin yinsa, to amma a yanda ya gama lura Kabir baya so ya san komai duk da yarda da amincin da ke a tsakaninsu, saboda haka bai takura kansa akan sai ya tambaye shi yaji ba, may be it is a matter that belongs to him alone, and he does'nt want anyone to know.
tunda Kabir ɗin ya shigo mota bai yi magana ba, haka idanunsa a rufe su ke har suka iso gida. duk da cewar Abdurrahim ɗin nata zuba zance amma sai ya lura Kabir ɗin yana sauraronsa ne Absentmindendly, dan haka yay shiru yana bin waƙar da ke tashi ta recorder ɗin motar cikin yarensu na Amharic.
lokacin d suka isa gidanma Kabir ce yayi ya barshi a mota zai shigo daga baya, yaso ya matsa masa yaji akan meke faruwa dan yaga ƙyallin damuwa a ƙwayar idonsa, to tambayar ba a wannan lokacin ta dace ba, ya ɗan huce tukunna, kuma may be ya iya sanar masa ko da bai tambaya ba.
Abdurrahim na fita a motar ya zaro waya daga aljihunsa ya lalubi nunbar Kulu, shin ya sanar mata kaso 50 na aikinta ya kammala ne ko ƙaƙa?, saƙa da warwara yake akan yin kiran, ya kira ko ya bari?, zuciyarsa ta rasa wanne side zata ɗauka, kiran na da muhimmanci ta wani ɓangaren, ta wani ɓangaren kuma ba shi da amfani. tun wancan ranar yake fushi da ita, fushin kuma da yay zuciyar ba zai ƙara kiranta ba sai dai idan ita ta kira shi.
_"Ranka ya daɗe su din Ƴan biyu ne, su kaɗai Allah ya bawa mahafinsu, mahaifiyarsu ma ita kaɗai ce, nan ba shi ne ainihin gidansu ba, amma kuma sunyi rayuwa mai tsawo a cikinsa, dan tun san da aka yayesu suka dawo wurin Kakarsu da ta haifi mahaifiyarsu, shi sarkin wannan masarautar shi ne wanda ya haifi mahaifiyarsu. shi kuma sarki Sheikh Samin bin Hamad Al-Thalis shi ne mahaifinsu, shi ne sarkin ƙasar Qatar tun bayan da yay aure har zuwa yanzu, Aaliyah da Akila shi ne ainihin sunansu, kamar yanda ka nuna min wannan hoton fuskar a yanzu, haka hoton Poster ɗinsu ne zai fara yi maka maraba a yayin daka isa masarautar Qatar, Aaliyah(Babbar Hassana) ita aka nema aka rasa har yanzu babu labarinta, Akila(ƙaramar Hussaina) kuma tana nan, ita ce minister of education a yanzu na wannan ƙasar tamu ta ethiopia da kake karatu acikinta, macece me halin kirki da nagarta, sai dai ƙalubale ɗaya na zagi da ƙananun maganganu da take fuskanta a wurin mutane shi ne na rashin aurenta tsawon shekarun da take da su, wasu ma har na ganin ko harka da maza ne ya hanata aure"._
bayanin wan nan dogarin suka haska acikin kansa da idonsa, ba yanzu ba, ba yanzu ba ya kamata ya sanar mata da komai ba sai yaje Qatar ya dawo.
_"Distance ɗin da ke tsakanimu nan Ethiopia zuwa Qatar kilomita 2,121 ne, wanda yake dai-dai da 1,318 miles, 3hours, 18minutes kenan. zaka iya zuwa ayau ka dawo"._
bayanin ya kuma haska masa. ya cije yatsa yana tunani, kamin wani bayanin ya kuma haska masa, _"Ƴa ta huɗu a cikin wannan masarautar ta Harar ita ce take aure a nigeria, inda take auren wani sarki a can da ya aureta a sanda ya kawo ziyara wannan masarauta, sunanta Hauwa ƴaƴanta nace mata Ammi, tana rayuwa ne kuma tare da ƙanwar mahaifiyarta da ta riƙeta a wajenta tun tana ƙarama da kowa ke kiranta da Bella, itama matar sarki ce a baya kamin mijinta sarki Mujahid ya rasu."_
a yanzu zuciyarsa ta yanke shawara ne akan ya fara zuwa Qatar ya dawo sannan ya sanar da Kulu komai, dan haka yay dialling number Abdurrahim, yana ɗagawa yace da shi,"Please come take me to airport ko kuma nace kazo muje tare idan ba damuwa".
"ina zaka je?". "Qatar".
"Qatar kuma?". muryar Abdurrahim ɗin ta amsa da sautin mamaki.
"ehh Qatar". "to amma tafiya babu shiri?". "Abudrrahim kuɗi ne suke aikin komai, ka fito kawai, a yau zamu dawo". "tom shikenan gani nan fitowa".
*Abuja, Nigeria, A wan nan ranar.*
_If you want to use your investigative skills to truly fight crime, pursuing a police detective career is the best choice for you. It's a great career fit for people with meticulous attention to detail, a strong ethical compass, and the patience and perseverance to investigate criminal cases that may progress slowly. Qualities of a Good Detective include:- (1)The ability to talk to people. (2)job knowledge. (3)Observation skills. (4)Report writing skills. (5)Attention to detail. (6)Ability to think outside the box. (7)Courtroom testimony skills. (8)Positive attitude and tenacity._
Bayanan na fita ne ta cikin system ɗin da ke ajiye a kan stool, yayin da Mairo wacce ke zaune akan kujera a balcony ta tattara hankalinta gaba ɗaya a wajen sauraren jawabin da farar baturiyar keyi tana fahimtarsa daki-daki. taci ado cikin wata armless gown blue, kan nan babu ɗan kwali an baza gashin a gadon baya, ƙafarta ɗaya akan ɗaya tana girgizasu.
bata san ya shigo wajen ba, bata san da zuwansa ba, haka bata san da tsayuwarsa a kusa da ita ba, domin hankalinta ba anan yake ba, ya tafi ga bayannan da take saurare da kuma hasashen yanda zata cimma karatunta ne.
*Detective Gift Tosin Afafa.* ya kira sunan nata sanda yake saka pause a vedion da ta ke kallo. murmushi tayi da ya tsaya a iyakar leɓenta, a kaikaice ta waigo tare da ɗaga kai ta kalle shi, lokacin kuma da ta saki murmushin da ya bayyanar da haƙoranta. ta kamo hannunsa tana matsa masa kusa da ita ya zauna tace da shi, "what is going on Sir Obi Tosin Afafa?". yay murmushi yana ɗora hannu saman kafaɗarta sannan ya bata amsa,"i salute to the daughter who is willing to find out the secret her father was hiding".
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*26)*
ya ɗora zancen da cewa,"amma ba kya ganin akwai rashin dacewa a game da abin da kike shirin aiwatarwa?, Dad mahaifinmu ne, mun sansa da kyawun halinsa, duniya ma ta shaida kyawun zuciyarsa, to akan mene kike tunanin zai iya aikata wani mugun abun?, yafi mu sanin dalilin da yasa yake ɓoye mana koma menene, shin ba kya tunanin ko abin da yake ɓoyewar abu ne da ya dangancin aikinsa ne kasancewarsa na soja?, idan yana ƙoƙarin kare ƙasarsa ne fa?".
kallonsa take tun daga lokacin da ya buɗe baki ya soma magana har san da yaja baki yay shiru, sannan ta sauke numfashi tace da shi,
"ba wai ina binciken bane dan in gano shi da aikata wani mugun aikin ba...i have 100% sure ba wani mugun abun yake ɓoyewa ba, kai baka tunanin abun da yake ɓoyewar ya shafi rayuwarsa ne kuma hakan zai iya jefa shi cikin haɗari?, to wannan dalilin yasa nake so na koyi yanda zanyi binciken akan abinda yake ɓoyewar, dan muga ta inda zamu taimaka masa mu warware bakin zaren, mu fitar da shi daga tashin hankalin da yake ikirarin acikinsa yake". tayi shiru sannan ta jinginar da kanta a saman kujerar, taci gaba da cewa,"sai dai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, idan har abun da Dad ke ɓoyewa ya zama shi ne me cutarwa, ko yana cutar da iyalansa ko kuma yana cutar da al'umma ta wata hanyar, to ba zan ƙyale ba, zan gargaɗe shi akai, idan kuma yaƙi ji zanyi ƙararsa ga hukuma ta hukunta shi". Obi yay mata wani kallo na baki da hankali, kamar ya sanar mata da matsayinta, sai kuma dai bai yi hakan ba saɓanin wani tunanin da ya gimla masa, dan haka yace da ita,"a matsayinki nawa za ki ƙararsa?".
tayi wani guntun murmushi tana kora lemu mai sanyi a maƙoshinta,"ba lallai sai na kai wannan level ɗin da nake son kaiwa na Detective ba sannan ne zan iya yin ƙararsa, as far as i got the evidences magana ta ƙare, you know me well akan bigiren gaskiya na ke, kaima kasan da hakan". Obi zai sake magana ƙarar wayarta ya katse abinda zai ce, a shekaranjiya ne Dad da ya dawo daga London yay mata kyautar waya babba mai tsada saboda sakamakon da ta ƙara fitowa da shi me kyau na wannan term ɗin, Emanuel kuma yay mata kyautar system ɗin da take kallo acikinta yanzu. bata ko kalli screen ɗin wayar ba dan ganin sunan me kiran, saboda tuni ta gane me kiran tun a taken waƙar da ke tashi, ringing ɗinsa dabanne dana kowa, Emanuel! Emanuel Brother ɗinta da take so da ƙauna, shi yasa take banbanta komai nasa a wajenta da na kowa.
Obi ya kai dubansa ga screen ɗin ganin taƙi ɗauka, hasalima ɓata rai take. "Brother ne fa ki ɗaga mana". cikin turo ƙaramin bakin nan nata gaba tace da shi,"ka ƙyale shi munyi faɗa". "da Brothern?, Gift kin cika rigima ke dai, to akan mene ku ka yi faɗan?". Obi yay tambayar dariyar fuskarsa bata ɗauke ba. tayi narai-narai da idanu tana shirin fashewa da kuka,"wai haka yake cewa bani da lafiyar tunani, na shirya zai wuce da ni lagos za'a ƙara min hoto a duba lafiyata, Brother Ema ya daina sona at all". kafin Obi yace wani abu Buky ta shigo Balcony ɗin tana sanar musu da kiran Dad.
Da yamma tana zaune a parlo tana bitar karatu, karatun bokon da bata gajiya da shi sam, Dad da kansa har ya fara yi mata faɗan akan ta dinƙa sassautawa, ƙwaƙwalwa na buƙatar hutu. ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ƙwalawa Buky kira tazo,"mai da min da Aljazeera". Buky ta ɗauki remote ta kamo channel ɗin da ta umarceta.
ita kuma ta karkata hankalinta ga tvn gaba ɗaya, tana son labarai sosai, kallonta a tv ba ya wuce sauraron news ko kuma wani program da ake gabatarwa me amfani, shi yasa Dad yake cewa idan aka cire Emanuel to duk tafi sauran wayewa a gidan, ranar taji daɗi sosai kam. Granny ta ƙaraso ta zauna ita ma a ɗayar kujerar, suka ci gaba da sauraran news ɗin tare.
"azumin yau akwai wahala kam". Granny ɗin ta faɗa tana hamma da alamar gajiyawa tare da ita da kuma sautin maganar tata.
Azuminsu ta ɗauka na ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma, ta ɗauka shi ne musamman saboda Dad da ya ce tayi masa adu'a akan wani al'amari da ke neman jagula lissafinsa, tayi masa adu'a Allah ya saita masa kan komai, dalilin da ya sa ta fara azumin tun ayau.
"kema Granny kin san kina fama da ulcer me ya kai ki ɗaukan wani azumi, gashi sai yanzu ma 12 tayi". "azumin Dad ɗinku ne ai". "umm Jesus ya amsa". Mairon ta faɗa tana kai ayabar da ta ɓare bakinta. baccin da ya fara ɗibanta ne yasa ta miƙe, "Granny bari na kwanta a ɗakinki, bana son hawa sama. idan Thomas yazo a taso ni, Dad yace ya fara koya min mota, so nake mu fara a yau saboda zuwa bikin Abigail ina so ace nima na bada gudun mawa wurin kai friends party".
"shi Dad ɗin yace a fara koya miki driving? ina ce yace ne sai kinyi candy?...wayar ma fa ya ba ki ita ne dan ta dinga ɗebe miki kewa ba wai dan kin isa riƙewa ba...kuma shi ne saboda samun guri har kike ikirarin wani fara driving yanzu salon ki daina maida hankali akan karatunki".
ta ɗan doki ƙafa a ƙasa tace,"Ohh Granny cikas, karki ɓata min budget mana. ke dai ba ruwanki ido naki kawai, ai kema kin san wace ni, ina son karatu sosai dan haka babu wani abu da zai ɗauke min hankali akansa". Granny ɗin na dubanta tace,"to naji za ki koya yanzu, amma kike fita da ita kam ba yanzu ba sai after kinyi candy, Yayyanki ma duk haka aka masu, bare ke da kike mace". wannan maganar ta Granny yasa ta wuce ɗakinta ta fasa zuwa na Granny cikin fushi.
around 2:00pm Emanuel ya dawo gidan, saboda PTA meeting da za'ai a makarantarsu Gift, dan haka Dad yace ya dawo ya wakilce shi ba zai sami zuwa ba. ya shigo gidan Mairo na ɗakinta dan haka bata san da dawowarsa ba, shi ma kuma har yay lunch bai nemeta ba a zatonsa ko bacci take kamar yanda Granny ta shaida masa, nan kuwa tana ɗaki tana aikin karatun da ta saba babu dare babu rana, Obi har tsokanarta yake da Mangopark da kansa.
ya hayo upstairs zai wuce ɗakinsa yaje ya kwanta dan huce gajiya, sai yaji ba zai iya bacci a yanzu ba tare da ya ga Gift ba, wata guda kenan rabonsa da sanyata a idonsa a zahiri, kuma wannan idanun nasa irin nata masu kama da bacci su na kewar ganinta, haka zuciyar da ke tunaninta a kowacce daƙiƙa tana kewarta, a vedio call kawai yake ganinta, kuma shi wannan ba ya gamsar shi, yayi kewarta sose da rigimarta, kuma dawowar nan tasa ma yasan sai sunyi rigimar, dan yana batun komawarsu asibiti ne, tunda likita ya sanar da shi idan har ta kai watanni shidda tunaninta bai dawo ba to su koma a ƙara bincike, to gashi harma an shiga wata na takwas, ba wai dan zuciyarsa naso zai aiwatar da hakan ba, bama shi kaɗai ba har Dad...sai dan basu da yanda zasu yi ne, domin ayanzu Duniya ta ɗora ido akan ƴar da ba'a san Dad da ita ba tsawon shekaru 35 da aurensa, babu wanda yasan da ita da kuma tarihinta, sai a yanzu da tauraruwarta ta haska a duniyar, dalilin da yasa Duniyar ta fara ƙalubantarsa akanta.
parlonta ya shiga sai yaga bata nan, dan haka ya dawo ya murɗa handle ɗin bedroom ɗinta, fitowarta daga wanka kenan tana tsaye gaban mirrow tana goge jiki da ƙaramin towel ɗin da ke hannunta, ya kafeta da ido yana kallonta daga sama har ƙasa, kallon da ya haddasa tasirin jin wani abu ajikinsa. Shi mamakin cikar girmanta yake a yanzu, dan ba a haka ya sameta ba, lokacin ƴar siririya ce firit, breast ɗinta kaman lemun tsami, amma a yanzu ka kalleta sai ka kuma kallonta, ba'a irin surarta ne lafiyayyan namiji ke ɗora idonsa ya ɗauke ba ba tare da yaji wani abu ba, ta samu cikar diri da komai, samun ingantaccen abinci, hutu da jin daɗi da kwanciyar hankali yasa komai na halittarta ya sauya.
a zatonta ko Obi ne ya shigo saboda haka ba tare da ta juyo ba ta jefa tambayar,"what my brother need?". yay murmushi ya ƙarasowa ciki, yay tattaki zuwa inda take ya rungumeta, babu wanda ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 52