Debora ta sauke numfashi sannan ta dubi Emanuel wanda ya tsareta da ido yana jiran cewarta tace masa,"akwai matsala fa a idanunta, she says she cant see very well". Emanuel ya juyo yana duban Mairo da mamaki, how comes hakan zai kasance, to ko dama ita makauniya ce shi yasa ta sanyo kanta kai tsaye titi har ya kasa kauce mata. Md ya katse masa tunani da cewar,"what are you thinking?". yace da shi, "ina tunanin mene yay cousing na ciwon idon nata, dama can da ciwon ko kuma a accident ɗin nan ne?". Md yace,"gashi kuma babu wani abu da zata iya tunawa bare ta bada amsa". Emanuel yayi shiru, Md ya ƙara cewa da shi,"ya kamata fa Police su shigo cikin lamarin nan, tun da ba za kai ta zama da yarinya ba, ai kayi iyaka yinka tun da ka kawota asibiti akan lokaci". ya girgiza masa kai,"bana so Police su shiga zance i have already told you that...ko asibiti ma da su kai maganar rufe bakinsu nayi da kuɗi". "to kana nufin zaka ke ta zama da ita ne?". ya ba shi tabbacin hakan ta hanyar jijjiga masa kai. "to office fa?". "ai kana nan, ko ba zaka iya aiwatar da aikin company ba idan bana nan?". Md bai ce da shi komai dan ya rasa ta cewa gaba ɗaya.
Debora ce ta bawa Mairo tea ɗin tasha, sannan ta bata magunguna da allura. Emanuel ya tashi daga kan kujerar da yake ya koma gefen gadon ya zauna, yana riƙe da hannunta ya tambayeta,"what is your name?". da mamakinsa sai yaji tace,"my name...". sai kuma tayi shiru. "ehen said it your name is what?". "i dont know my name". a yanda tayi maganar sai ta ba shi tausayi.
su na ta hira shi da Md ita kuma duk tana jinsu bada sanin abunda suke faɗa ba ko kuma ganinsu ba, ita dai har tsawon awannin da suka shuɗe Emanuel bai saki hannunta ba. sai around ƙarfe biyu na rana sannan suka fita shi da Md zuwa restaurant suka ci abinci suka dawo, time ɗin kuma tayi bacci, ya tambayi Deborah ya sauƙin jikinta tace masa, "ai bayan tafiyarku tana ta kuka wai idonta na ciwo". "ko asibitin ido za'a kaita?". ya jefa tambayar ga Md. sai Deborah tace masa akwai likitan ido da yake zuwa da daddare.
misalin bakwa na dare Md ya umarci abokin nasa da ya tashi su tafi, Emanuel yace da shi ya tafi shi zai kwana nan ne. Md ya dube shi da tsantsar mamakinsa yace,"zuwa wane lokaci zaka bar yarinyar nanne ka koma harkar gabanka?". "ni kuma for how many times kake so nata maka repeating cewar zanke zama da ita anan zuwa lokacin da za ai discharging nata". "amma kana tunanin za su sallameta nan kusa ne?, muna fa da meeting cikin satin nan kuma kasan ya kamata kake shigowa office saboda hakan". "zan yi posponding meeting ɗin". "zuwa yaushe?". "time ɗin da zamu bar asibiti". "then sai kayi ya da ita kuma?". "zata zauna tare damu har lokacin da tunaninta zai dawo a nemi iyayenta". Md ya tsaya yana yi masa wani irin kallo, ya lura gaba ɗaya nema yake ya maida al'amarin yarinyar kansa, shi kuwa Emanuel gani yake kome ya faru da yarinyar shi ne sila dan haka dole ya tsaya ya kula da ita.
Md ya nufa ƙofa yana ce masa,"so ni dai good nite". kamar ba zai ce masa komai ba sai yace,"karka kawo mana tea da safe na lura kaman bata sonsa". "to sai mene take so?". Emanuel ya ɗago yana tsareta da ido, dariya ta suɓucewa Md yace da shi,"ask her mana". Emanuel yay masa wani wawan kallo sannan ya ɗauko wayarsa daga aljihu ya kira Deborah, ko minti biyu ba ai ba sai gata tazo, yace ta tambayi Mairo abunda tafi son ci, Mairo ta girgiza kai a san da Deborah ta tambayeta alamar babu komai.
Emanuel yana latsa wayarsa yace da Md,"abu soft ake da buƙatar taci so please ka taho da curstard and do not be let". Md ya kyaɓe baki yace,"aini ba ɗan aikinka bane da har kake faɗa min wani karna makara, you will see me a duk san da na gama hidiman gabana". "ka barshi ma ba sai kazo ba". Md yay dariyar ƙularwa sannan yace,"anyway no escort?". "kasan hanya ai". Deborah dai murmushi tayi saboda tun ɗazu tana ganin yanda suke buga dirama, kuma duk Md ke jansa da tsokana.
yayi shiru ya kasa ɗauke ido daga kanta, tausayinta yake da dukkan ransa, kansa yake ta ɗorawa laifin duk da cewar ita ma akwai nata na rashin bin ƙa'idar tsallaka titi, dan haka ba zai yafewa kansa ba har sai ta sami lapia completely.
around 9 likitan ido yazo dubata, yay gwaje-gwajensa ya tabbatarwa da Emanuel tana da buƙatar aikin ido a babban asibiti da yake musamman na ido ne, amma for now zai bata wasu maganin da zata yi amfani dasu ciwon ya lafa. tare suka fita da Dr ɗin yaje ya siyo maganin da ya rubuta, tana baccin ya ɗiga mata maganin sannan yaywa Deborah sallama ya wuce makwancinsa.
***
cikin kwanaki goma ciwonta Alhamdulillah ya fara sauƙi, ƙafarma an kunce bandage yanzu tana ɗan takawa a hankali, idonta kuma yanzu tana gani da shi sai dai ba wai yanda ya kamata ba. ta kuma saba da Deborah sosai dan 24hrs su na tare, tana koya mata lesson akan yanda harshenta zai kama da yaren da suke yin magana, wanda Emanuel ne ya sata hakan kuma yana biyanta da tsoka. Alhamdulillah tana ganewa sosai, ko magana akai tana ji sai dai ba komai take iya maidawa ba.
yau bai shigo da wuri ba, a ɗan turancin da bakin Mairo ya fara kamawa ta tambayi Deborah,"Aunt is that tall Man not coming today?". Tayi mata murmushi da cewar, "his name is Uncle". Mairo tace,"ohh Uncle, to zai zo yau?". ta gyaɗa mata kai da cewar,"umm zai zo ƙila ko yaje office ne". tayi knodding kanta kawai sannan ta ɗauki littafinta taci gaba da rubutunta da Deborah ta bata. kuma rufe bakinsu kenan wayar Deborah tayi ringing, ta ɗauka ta kara a kunne tana gaishe shi, amma sai bai amsa mata ba yace ta bawa Mairo. ta miƙa mata wayar ita kuma tana ci gaba da yankan farce. daga cikin wayar ya kira Maira da,"Beb". ta amsa masa, "Yes Uncle Good Morning". "Morning Beb, how was your night and your body?". "Uncle am feeling better". "thats good. did you eat your breakfast?". duk da cewar taci amma sai ta ce da shi, "no". "why?". tayi shiru bata ce komai ba sai yatsanta da ta saka a baki tana cijawa, cikin dabara ta raɗawa Debora cewar ta faɗa masa,"ta kasa cin komai ne tana son ferfesun kayan ciki ne". Deborah ta amsa wayar tana ce mishi,"wannan patient ɗin naka ta cika kwaɗayi, taƙi cin komai sai fefesu take son ci". yace, "me yasa biki faɗa tun ɗazu ba, bari nasa ayi mata order yanzu". kamin ya kashe wayar ya bawa Deborah uzurin rashin shigowarsa, yaje gudanar da wani meeting ne amma da zarar ya kammala zai shigo, hankalinsa gaba ɗaya yana nan ya kasa samun natsuwa. tace da shi, "ka nutsu kayi aikinka jikinta da sauƙi sosai". "sai dai nazo na gani da idona". ya faɗa yana kashe wayar.
sai 7 na dare ya shigo asibitin, kana ganinsa kaga wanda gajiya ta yiwa duka, ya zauna kan kujera yana yiwa Mairo magana sai yaga tayi masa shiru taƙi kula shi, sai baki da ta turo gaba cikin salo na shagwaɓa. yace da ita,"Beb why are you frowning at me?". ya tambaya yana kama babban yatsan ƙafarta. ta kalle shi ta ɗan murguɗa masa baki, yay murmushi ya matso da kujerarsa bakin gadon sosai, ita kuma sai ta kwanta ta juya masa baya. bai saba da ganin rigima irin haka ba, ba su da yara kuma ba shi da me yi masa, dan haka sai yayi tunanin ko wani abun ke damunta, ya ɗauki waya ya kira Deborah ya hauta da faɗan akan mene zata tafi ta barta ita kaɗai, ai kuɗi yake biyanta ba kyauta take masa aikin ba. sai gata ta dawo da sauri har tana haɗa hanya tayi zaton ko jikinta ne ya tashi. tana zuwa ta leƙa fuskar Mairo taga idonta biyu, kawai dai ta ɓata rai ne tana neman fashewa da kuka mara dalili, ɗazu ma abunda ya haɗasu kenan ta fita ta barta da wannan turo bakin gaba. Emanuel dai bai daina faɗansa ba, "idan kin gaji ki faɗa min mana na nemi wata".
ta rissinar da kai,"sorry Sir ba fa wani abu ke damunta ba tana fushi ne akan baka zo ba, tun ɗazu take min complain har da cewan sai mun tashi mun bika. ƙarshe ma abincin da kasa akayi order bata ci ba wai hannun delivary Man ɗin da ƙazanta she cant eat". abun yaso bashi dariya, dan haka ya miƙe ya ɗagota daga kwancen yana bata haƙuri da lallashi, sai da ƙyar ya shawo kanta tayi murmushi ta haƙura, tace masa,"amma Uncle idan ka sake me zan maka?". yace mata,"purnish me...yanzu dai kici abinci". ya faɗa yana buɗe takeaway ɗin da tun safe yake ajiye. ta dakatar da shi da faɗin,"ni fa ba zanci wannan ba, naka nake so". ya mayar ya ajiye sannan ya fita zuwa siyo mata wani.
*_Waiting For Your Warm Comments, likes, and Opinions...Your Support is all i need...LOVE YOU ALL._*
*Vote!Vote & Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*21)*
Har ya isa Lagoon Restaurant shi kaɗai ya kanyi murmushi idan ya tuna da rigimar Mairo, an haɗa mishi komai da ya buƙata ya juya ya shiga mota, har zai mata key sai ya ɗauko wayarshi ya kira Deborah tana ɗauka ya ce da ita, "give the phone to Beb". Miƙawa Mairo tayi wacce ke daga kwance ta amsa murya cike da shagwaɓa ta ce, "yes Uncle". murmushi yayi kafin ya ce, "is there anything you want bayan ferfesun?". cije leɓe tayi tayi shiru tana nazari, ta lura ko ɗazu da ya shigo he looks extremely tired, dan haka kamar tana gabansa tace,"nothing more". "for sure?". yanayin yadda yay tambayar tabi ta ba shi amsa, daga haka ya kashe wayan, sai da ya shiga Mastergrillerz ya siya kaza gasashshiya tukunna ya ɗakko hanyar dawowa shi ma nan sai da ya ƙara tsayawa ya jidi choculates kana ya wuce asibitin.
Hira suke ita Deborah, tana bata labarin wani masifaffen Pastor a church ɗinsu, ita kuma sai dariya ta ke yi, tana ce mata idan zata ce Church ɗin zata bita saboda gansa, kuma idan taje sai ta saka masa ƙafa ya faɗi ya ƙume, tun da dai shi ma ya kori Aunt ɗinta daga wurin ibada, ai da yanzu adu'arta ta amsu ta warke sun tafi gida, dan ta fara gajiya da asibitin kullum mutum na zaune wuri ɗaya, Deborah tace,"zan nuna miki shi idan mun je, ɗan ƙarami da shi sai jarabar tsiya".
Emanuel tun da ya dawo sai ya tsaya a bakin ƙofar bai shiga ba kuma bai fita ba, su ma basu lura da dawowar tasa ba, shi kuwa haka kawai sai ya kasa ɗauke idonsa daga saman fuskar Mairo saboda yanda dariyar tayi matuƙar amsar fuskarta, ba ya so ya shigo ya katse mata jin daɗinta, yanda ta cija yatsa tayi ƙwafa mai ƙarfin sauti tare da tuntsirewa da dariya irin wadda ta tamawa wata muguntar sai abun ya ba shi dariya shi ma, dariyar tasa ne ya karkatar da hankalinsu gare shi yana shigowa fararan haƙoransa duka a bayyane.
Debora ta miƙe ta isa gare shi ta amshi ledojin da ke hannunsa, Mairo kuma ta bishi da ido har ya ƙaraso sannan tayi masa sannu da dawowa.
ya zauna kan kujera yana faɗin, "ni ma sai an bani labarin tunda dai ba'a jira na dawo anyi dani ba". Mairo tayi ƴar dariya da cewar, "i will gist you Dear Uncle, buh before then fara bani abun da ka siyo min". ta faɗa tana miƙa masa tafin hannu. ya ɗauko ledar ya dire mata a gabanta zai buɗe sai wayarshi tayi ƙara, dubawa yayi sunan Dad ya fito akan screen, kamar ba zai ɗauka ba saboda ɗazu da ya je office Sectery ya sanar masa Dad ya shigo jiya bai same shi ba, kuma ya kira wayarsa bai yi picking ba, and yace ya kira shi bai kira ba, saboda haka yake tsoron ɗagawa dan shi mai laifi ne. sai da kiran ya kusa katsewa tukunna ya ɗaga, tambayar da ya tsammaci ji daga bakinsa ita yaji a yanzu,"i called your number several times but it didn't get through, whats going on?". a yadda yaji muryar Dad ɗin sam babu walwala alamar yana cikin damuwa da rashin samun nasa sai yaji ƙirjinsa ya buga. yay shiru yana tunanin abun da zai ce, Dad ya katse shirun nasa da kiran sunansa, "Emanuel". "yes Dad". yay saurin amsawa. "am asking you something you kept quite, ko akwai wani matsala ne da yake faruwa but you hide it from me?, jiya ma fa baka je office ba kuma na tambaya an tabbatar min da hakan, Oya Emanuel tell me what you are hiding becouse you are not like this, am convinced there is something fishy going". a yanda muryar Dad ta fita ta ba shi tsoro dan bai fiya yi mishi magana a haka ba, sai dai Md ko su Joseph. ya soshi girarsa yana auna abun da zai cewa Dad ɗin, ba ya masa ƙarya kuma ba ya ɓoye masa duk wani abu da ke faruwa da shi, infact ma this time around ne abu ya taɓa samunsa ya rufe bai sanar masa ba, kuma ba dan komai yay hakan ba sai dan gudun tashin hankalinsa tun da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba, amma yanzu tun da har ya gano da kansa ba shi da yanda zai yi dole ya faɗa masa.
ya ɗago ido ya dubi Mairo wadda ta gutsuro cinyar kaza zata kai baki ta dakata da ci ta tsare shi da ido saboda yanda taji amon faɗa na tashi daga cikin wayar. dan haka ya miƙe ya fita daga waje gudun karta fahimci abunda ke faruwa. Emanuel ya kwantar da murya ya shiga yiwa Dad bayanin abunda ke faruwa, da dalilinsa na ɓoye masa bai sanar masa ba, sannan ya ba shi haƙuri akan hakan. daga ɓangaren Dad yay shiru yana nazari akan ɗansa, auna zantukan nasa yake akan mizani na duban hankali da zurfin tunani, wani ɓari na zuciyarsa ya bijiro masa da cewar anya zancen Emanuel gaskiya ne ba bin Mata ya fara ba, banda haka tsawon shekaru bai taɓa ɓoye masa wani abu ba sai da akazo irin wannan gaɓar, gaɓar kulawa da mace a sirrance, sai kuma yay saurin watsi da zancen da zuciyarsa ke raya masa, sam ɗansa ba zai aikata makamancin hakan ba, ya yarda da shi ya yarda da tarbiyar da ya ba shi, Emanuel kaman yasan Dad na tantama ne da maganar tasa dan haka ya katse shirun nasa da cewar, "Dad believe me am not lying to you...idan kuma har zan faɗa maka akasin haka to ƙarya nake, amma if you are still doubting ka kira Onoaka(Md) ka tambaye shi". "is oak na yarda da kai, amma kar irin haka ya kuma faruwa kayi shiru gudun faruwar wata matsalar. yanzu ina ita yarinyar?". Dad ɗin ya faɗa yana sauke murya ƙasa. "tana room, bana so ta fahimci cewar bata da wata alaƙa da ni ne shi yasa na fito waje, idan ta gane hakan zata iya shiga damuwa, she would like to know who she is, and where to find her parents after she is no longer in her thoughts.".
Dad yace,"haka ne, Allah ya bata lafiya. kai mata wayar zamu yi magana". Kamar yace da Dad a'a, dan ba ya so kwata-kwata Dad yayi mata maganar sanadin ciwonta. yana shiga ya miƙa mata wayar da cewa,"Dad on the Phone". ta karɓi wayar ta riƙe kamar mai son tuna wani abu sai kuma ta kara wayar a kunne. "Hello Dad good evening". "good evening daughter, how is your body?". "am felling better Dad". "Good. Hope your brother is not bothering you?". ta jijjiga kai da cewar,"Yes Dad". ta faɗa tana kallon Emanuel da ya harɗe hannaye idonsa akanta. sannan tace,"Dad When are you coming to check on me?". "i will be there when your Mom comes back". "Where did she go?". "she travel to egypt for her seminer but she will soon be back. bari na barki haka you should rest oak". "oak thank you Dad, Good Night". daga haka ya gimtse wayar. ita kuma ta miƙawa Emanuel wayar tana cewa,"Uncle kamo min irin game ɗin wayar Aunt". tana faɗa tana gutsirar nama. "yanzu lokacin cin abinci ne bana game ba". sai ta dakata da cin naman ta dubi Deborah tace ta bata tissue, ta miƙo mata shi kuma ya tambayeta,"me za ki da ita?". "zan goge hannuna na ƙoshi da abincin". ta faɗa murya a ƙasa irin tayi fushi ɗin nan, Emanuel ya zauna kan kujera yana bata haƙuri, "kici abincin bari na tura miki game ɗin a wayar Aunt". "ni fa a wayarka nake so". yace,"ehh ai zan tura daga wayar Aunt ne, kinga ni banda ita". tayi knodding kanta,"umm". ya karɓi wayar Deborah ya tura game ɗin Rolling Sky sannan ya miƙe ya fita daga waje yana installing na game ɗin, bayan yace da Deborah ta zuba Ferfesun yana ɗayan white ledan ta bata taci. Debora ta zuba ferfesun a plate ta aje gaban Mairo, ita kuma ta ɗauke kai tana aikin tura baki gaba, Deborah tayi ƙwafa da cewar,"kin san Allah ni kam zan fara maganinki da wannan shagwaɓar taki, kinfa ji sauƙin da za ki ke cin abinci da kanki amma ko yaushe sai kice lallai sai na baki". ta kuma gwame baki tana ƙara ɓata rai. Debora taja gefe ta ce,"sai kuma kiyi ai, ni da ƙara feeding naki kam sai da safe". tana gama faɗar haka ta miƙe zata fita sai ga Emanuel ya dawo, tun daga nesa da ya hangi yanda tayi kicin kicin da fuska ya dafe goshi, sannan ya ƙaraso yana tambayar Deborah me yasa bata sa taci abincin ba. "she said she want to it by her self, thats why na ƙyaleta". bai ce da ita komai ba ya ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Mairo da tai frowning face nata sak ƴar baby, sai shi ma ya ɓata fuska da ce mata,"sa hannu kici abinci". dan ya lura idan su na biye mata to taɓarar tata yawa zatai, duk da yana mata uzuri da sabon halin da ta tsinci kanta, may be da ace ba tayi loosing memory ba ba zata ke hakan ba, although a yanda yake kallonta ba ya tunanin ta fara period, kasancewar wani girma na manyan breast bai nuna ajikinta ba.
still fuskansa a ɗaure yace,"ba za ki ci ba?, you want me to start beating you bah?". tai saurin girgiza masa kai alamar a'a, sai ya sassauta muryarsa ganin yanda tasha jinin jikinta da sauyawar da yay, yace da ita," do you want me to feed you?". tayi Knodding kant alamun eh, ya matso da kujeran gaban gadon ya amshi plate ɗin da ke hannunta, ɗan kaɗan ya ɗebo a spoon, daidai bakinta ya kai spoon ɗin sai yaga ta kawar da kanta gefe. "Beb again. kina so muyi faɗa ko?". tana aikin ƙifta idanu ta girgiza masa kai. "oya open your mouth". ta buɗe baki ta shiga amsar ferfesun, bai ƙyaleta ba sai da taci da yawa kana. ta dubi plate ɗin taga mugun cin da tayi, dan haka baki buɗe irin na mamakin yadda taci da yawa har haka tana dubansa tace, "amma Uncle tare ne muka cinye ko?" lakuce mata hanci yayi kafin yace,"ke ɗaya kika cinye, dama ance sirara ci ne da ku". tana murmushi ta ce, "no Uncle wayo ne har da kai ne muka ci". ta faɗi hakan tana ziro ƙafafunta zuwa ƙasa da niyyar miƙewa, da sauri ya tareta da cewar, "to where?". "toilet". "me za kiyi a toilet kuma?". "zan wanke bakina". har bakin toilet ɗin ya rakata kana ya dawo yana jiran fitowarta, sai da Deborah ta dawo ɗakin sannan yay musu sallama ya tafi, wayarsa ma bar mata yayi, amma yaja mata kunne in dai bata yi bacci da wuri ba zai goge game ɗin daga wayar kuma ko sun koma gida zai ce Dad kar ya bata waya.
***washe gari likita da ya shigo ya ƙara duba jikin Mairo, da duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata, yaja Deborah gefe ya sanar mata akan idan Emanuel yazo ta sanar masa su taka da yarinyar zuwa bakin titi, may be a samu a dace, ko da bata yi recalling duka ba zata ɗan iya tuna wani abun, kasancewar a accident ne tayi loosing Memory nata so ganin gimlawar motocin ka iya sawa tunaninta ya dawo, ita kanta Deborah tana tausayin yarinyar, dan tun da ta sami sauƙi most of times tana lura da ita zata ga ta dafe goshi kamar mai tunanin wani abu ko me son tuna wani abu, idan ta tambayeta sai ta ce mata she was thinking like there is something crucial da ya kamata tayi, but ta kasa sanin menene shi.
me aiki na mopping akai knocking ƙofa, "yes come in". cewar Deborah. sai taji shiru ba'a shigo ba dan haka ta umarci me aikin ta leƙa ta amso abinci ne. ita kuma taci gaba da kimtsa kayan Mairo acikin medium trolly ɗinta dan likita yace gobe za'a ba su sallama. fitowar Mairo daga wanka ta tsaya nunawa Debora wajen ɗinkin da aka yi mata, tana mata complain akan yana yi mata ciwo, tayi mata sannu tare da ɗauko magani ta shafa mata a wurin, sannan ta nuna mata kayan da zata saka. "ki saka waɗan nan may be idan Uncle yazo ya tafi da ke church tun da kinji dama-dama". tayi knodding kanta kawai sannan ta ɗauki lotion ta shiga rubbing jikinta. Emanuel da Md da Deborah tun a farko sun zauna kan ƙiyasin wanne addini Mairo zata kasance kenan aciki, Md yace masa ai za su yi considering ne da garin da ya sameta, so kuma kan titin ma da ya bugeta ɗin daji ne, amma garin da ke gaban shi 99% ɗinsu there all christians, dan haka suka tsaya akan ittifakin cewar itama christian ce kamarsu.
rigar fara ce long slip me kyau, sai mini skirt ɗin black, haka ta sakasu kuma tayi kyau acikinsu gwanin sha'awa, Deborah wacce ta fita ta dawo ita tayi mata makeup tare da gyara mata gashin kanta da yayi yalayala da shi a gadon bayanta.
ta zauna bakin gado ita kaɗai tana shan ice cream, Deborah ita tuni ta ɗauki hanyar church kasancewar yau sunday, Emanuel ya shigo maƙale da waya a kunne yana magana, ta ɗago tana dubansa har ya ƙaraso ciki ya zauna kusa da ita, ba ƙaramin kyau yayi ba acikin shigar tasa wadda suka yi anko da ita shi ma baƙin wando ajikinsa da farar riga long slip, sai zuba ƙamashi yake kamar wani ango, ita bata taɓa ganinma yay kyau irin yau ba.
ya kama hannunta a sanda yake cewa da MD,"ai kai dai munafuki ne". daga can ɓangaren Md yay dariya da cewa, "munafurcin ƙaniyarka nayi". a san da Emanuel ya juyo da Mairo tana fuskantarsa, ya maƙele wayar a kafaɗarsa yana saka mata sarƙar cross yana cewa da Md,"ai da Dad bai yarda dani ba sai kaga yanda zanyi da kai. da Favour(Matarsa) zan haɗaka na faɗa mata gaskiyar kana cin amanarta a waje". Md yace,"da ka hargitsa min gida kuwa". Emanuel yay ƙwafa da cewa,"zan so haka, dan am tired of ganinka da wasu Matan a waje ahalin kana da taka...Mumu kawai aika kusa haihuwa kayi hankali". sosai Md
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 52